Arubuce Ta Ke Hausa NovelHausa NovelsHausa Novels

Arubuce Ta Ke 18

Sponsored Links

Page 18

Shi kansa zancan yazo masa a bazata,sai ya ajjiye spoon din hannunsa yana duban hajjaa

“Abbas….abbas nawa fa” kai ta gyada

“Eh shi” kamar me jiran hajjaa ta tabbatar masa da batun sai ga kiran hajiya ya sake shigowa wayarsa,ya kalli wayar na wasu sakanni zuciyarsa na gaya masa da gaske hajiyan take,tunda har ta kasa sakat saita samu tabbacin isar saqon kunnensa,ya dauka wayar a nutse ya kara a kunnensa

“Ina fata saqon nawa ya riskeka?” Kai ya gyada kamar tana gabansa

“Eh hajiya,yanzun take isarmin dashi”

“To alhamdulillah” ta fadi tana sauraren ji daga gareshi

“Amma hajiya….wani hanzari ba gudu ba,kina ganin babu matsala daga wajen shi abbas din?” Yayi tambayar saboda sanin halin abokin nasa,sun jima a tare tun zuwanshi bauchi,duk da cewa ya girmewa abbas din,amma suna tare dashi,don itama dama abota ba sai da sa’anka ba,takan iya zuwa ta kowacce fuska,Itama hajiyan kai ta kada kamar yana wajen

“Bani da haufi akan abbas ko kadan,bamu ita din shine mai wuyar” sosai hajiyan ta aza masa nauyin da bazai iya kufcewa ba,tana masa kallon mazaunin uba a wajen widad,tasan kuma ya isa ya zartar da hukunci a kanta shi yasa ta nemeshi kai tsaye,uwa uba kuma abbas din wani irin mutum ne mai kima da daraja a wajensa,yafi kowa sanin irin qaunar da yakema mahaifiyarsa,kamar yadda ta dauki shi shima a mazaunin d’a,bai kyautu ya dubi tsabar qwayar idanunta yace mata bazasu bada auren widad ga abbas din da yana sahun farko farko na wadanda zasu bada shaidar kyawun hali da nagartarsa,bayan gajeran nazarin da bai wuce shurun sauraren hajiyar ba ya amsa mata

“Hajiya ai abbas nawa ne,babu damuwa,an bashi widad,zan kuma sanar da can gida in sha Allah”. Irin addu’ar da yaji hajiyan tana kwararo masa sai da abin ya bashi mamaki,wanne irin so take mata haka?,lallai da bai amsa ba Allah ne kadai yasan rashin dadin da zataji,duk da ba zata nuna masa ba.

Wayar ya ajjiye gefe,ya daga kai yana duban hajjaa data tsareshi da idanu,kafin yace komai ta rigashi

“Abbaa,aure fa kake bayarwa,auren widad din da ummu ta baka aronta?,ba tare da sahalewar ummu ko yaaya mahmud ba?” Dan gajeran murmushi ya saki

“Yadda zan bada auren nujood kai tsaye babu haufi haka zan bada na widad,ina da wannan license din”

“Amma kana ganin aurenta da abbas yayi dai dai?” Ta sake tambayarsa cikin jin d’ar d’ar da fargaba

“Yana da wani aibune da musulunci yace idan namiji yana dashi bai cancanci ku bashi auren diyarku ba?” Kai ta girgiza da sauri

“Ko kadan,abbas nagartaccen mutum ne mai kyawawan dabi’u abun kwaikwayo,amma abba kada fa ka manta yana da mata,sannan matarsa din nan ko kwanaki na danji ana kuka da ita,bata da kirki abba,zamansu da widad mai qananun shekaru a mazaunin kishiya zai yiwu?”

“Duka ba wannan bane abun dubawar ba,tunda ba ita zata zauna da ita ba,indai ya cancanta magana ta qare” sai ya dauki spoon dinsa yaci gaba da cin abincinsa,dama tasan haka zaya fada,su maza nasu hangen daban dana mata,gaba daya hanakalin hajjan bai kwanta ba,bawai don abbas bai cancanta bane,aah,tana duba wani abu na dabanne,don haka ta gaza barin maganar

“Gaskiya abba bazan tayaka gayawa ummu wannan maganar ba wallahi,kada ka sani a ciki” dariya yadan saki

“Matsoraciya,yo waye ya sanya dama dake?”

“Amma zataga a gidana aka shirya fa,gashi widad dinma ta matsu tana son zuwa gida,ya za’a yi kenan?”

“Dama ina tunanin next week qarshensa taje taga ummu din,saboda ita kanta ummu kwanan nan maganar na dawo mata da yarinya taketa yi” shuru ya ratsa tsakaninsu,har uncle muhsin din ya fuskanci kamar ta shiga damuwa ne,don haka yayi gyaran murya

“Ni banji komai game da haka ba hadiyya,abbas yana da nagartar da ko nujood yace yana so zan bashi,zai riqe mana widad da amana, sa’annan kuma ina da tabbaci hundred percent karatunta bazai yanke ba,zataci gaba da karatu har zuwa inda takeso,so kinga babu wannan haufin”

“Gaskiya kam” ta amsa masa tana dan jin nutsuwa kadan,to amma batun zama da kishiya tasan ba abu bane mai sauqi,koda ga babbar macace bare yarinya irin widad,GOYON KAKA.

**********

Tunda hajiya ta samu tabbacin samun widad daga wajen uncle muhsin wata nutsuwa da farinciki ta dinga saukar mata,haka kawai ta dinga jin nutsuwa da gamsuwa da al’amarin,ta dinga ji kamar ta daga waya tace yazo tana son ganinsa,to amma tasan zuwa qarshen wata zai zo ganinta,babu buqatar ta daga masa hankali ta sanyashi biyo hanya,sai tayi amfani da wannan damar ta yawaita addu’a kan Allah ya sanya dukkan alkhairinsa akan lamarin,yasa ayi a sa’a,ya kade dukkan fitina.

************

Dukka shirin da yakeyi tana zaune gefan gado tana kallonsa,a yanzun da zai tafi bauchi tana jin inama yace ta shirya ta bishi,zaman garin ya gama kai mata ko ina,daurewa kawai take tana cijewa,ita kam duk inda zama zai kaita indai ba cikin garinta ba bataso.

Bugu da qari taga sabon key din mota garin bincike bincikenta,tana sake dauriya akan dauriya ne cike da fatan wannan motar ta zamana tata ce kamar yadda anty ummee data baiwa labari tayi mata hasashe.

Tsaf ya shirya cikin yadin kufta,wanda yayi matuqar masa kyau,ya fidda kwarjininsa da kuma kyan zubi da Allah ya bashi,saita sake karkata kai tana qare masa kallo,sau tari ita kanta takan gayawa kanta tabbas abbas wani rabo ne nata da Allah ya tsaga mata sai ta sameshi,amma ita kanta idan ta tsaya ta kalli kanta tana gano tarjn banbance banbance tsakaninta dashi,shi yasa take qara matsa qaimi wajen kishinsa,saboda tana tsoro…..tana tsoron kada idanun wata ya fada kansa,ta kuma sani wasu ‘yammatan indai suka baza komarsu sai sun samu,bata fiya damuwa dashi ba,tasan sam mata basu a lissafinsa,amma shi din yana cikin lissafin gomayyar mata da suke kwana su kuma tashi da soyayyarsa,koda cikin danginsa kuwa tana da wannan information din akansa.

Hure mata idanu yayi da sassanyar iskar bakinsa,abinda ya sanyata ja da baya da sauri,sai kuma ta saki murmushi

“Har ka bani tsoro” ta fada tana dan harararsa

“Ni kika bawa tsoro,wannan kallon kamar zaki cinyeni?” Murmushi ta saki

“Da da hali cinyekan zanyi,don banason kowacce mace ta kalleka kota rabeka,ni kaina bansan adadin kishinka da nake ba” daga kai yayi ya kalleta daga daura agogon da yakeyi,har launin fuskarta ya sauya,sai ya maida kai yaci gaba da daura agogonsa ba tare da yace da ita komai ba.

Ya rasa wanne irin dan banzan kishi take dashi,wanda kullum baya raguwa saima daduwa da yakeyi,abun takaicin har yau batasan yadda zata tsare masa komai ba,inda yadda take kishinsa haka ta tsaya masa wajen komai da lallai ya gama yin sa’a.

Ganin bai bata amsa ba tasan bazai ce komai ba,don haka ta sauya akalar maganarta

“Nidai da zaka barni Allah wannan watan zan bika,kamar na shekara banje gida ba haka nakeji”

“Sai next month kamar yadda nace” ranta tadan bata kadan,har ya gama shirinsa ya fito bata sake magana ba.

“Rakiyar ta isa daga nan” ya fada yana dakatar da ita daga qofar falon,saboda akwai driver daga waje da zasuyi tafiyar tare,mutum ne shi mai tsananin kishin iyalinsa,yakai bakinsa saman goshinta yayi kissing dinsa yana fadin

“Sai na dawo,ki kula da gida da yaran”

“A dawo lafiya” ta fada a taqaice tana dubansa har ya fice,tana tsaye ta window tana leqensa har motarsu ta fice,taja da baya ta zauna saman kujera tana jan tsaki

“Babu biki ba suna ba barka,an takure a baqon muhalli” ta sake fadi a fili,sai kuma ta miqe ta nufi dakinsa,ta buda ta shiga ta isa inda taga key din motar,ta jawo da zummar sake duba motar wacce ce?.

Wayam taga wajen babu muqullin,ta shiga birkitawa kamar wadda ta bashi ajiya,saidai babu shi ba alamarsa,da alamu ya dauka kenan,to amma me zaiyi dashi?,ta tambayi kanta tana zurfafa tunaninta,to ba tata bace kenan?,amma kuma motar da suka fita cikinta ai tasan motar,ba sabuwa bace,gaba daya sai ranta ya baci,ta jawo waya kamar zata kirashi ta tambayeshi sai wata zuciyar ta hanata,ta shawarceta ta bari ya isa gida tukunna.

*_RUMBUN K’AYA_*
*_IDON NERA_*
*_DAUDAR GORA_*
*_KI KULANI_*
*_A RUBUCE TAKE_*

Littafi daya—400
Biyu—600
Uku—-800
Hudu—–1k
Biyar din duka—-1200

*ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥

0022419171
Maryam sani
Access bank.

Shaidar biya tanan👇🏻
09033181070

*MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN*

09166221261

🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa ‘yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

+227 90 16 59 91

Littafi daya—450CFA
biyu—650CFA
uku—-850CFA
hudu—-1050 CFA
Biyar—-1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*

*SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!*

*Thanks for choosing us*🔥[2/16, 9:04 PM] It’s Queen Meenali👸🏻: *H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)
*Arewabooks: Huguma*

Leave a Reply

Back to top button