Blog

  • Arubuce Ta Ke 6

    Page 06

    “Gaskiya ne,kema kinzo da naki hanzarin,sannan a zahiri cikin musulunci babu auren dole,duk da shi mahmudu yana ganin kamar gata ne zaiyi mata,kuma hakan shine dai dai,to amma kuma duk da haka tana da damar da za’a bata zabi,iyaka idan aka duba ya zamana akwai kuskure ko rashin dacewa a ciki sai a soke lamarin”,tana tausayin widad,tasan akwai maqiya da magauta fal cikin rayuwarta,shi ya sanya take a tsaye ga duk wani abu da zaya cutata mata.

    Bangaren widad kuwa haka ta yini ta kwana,ummu nata dakon zuwan mahaifinta suyi magana da alhajin,bai shigo gidan ba sai a washegarin da azahar,akayi sa’a alhajin shima yana nan amma yana shirin fita.

    Shuru abban yayi sanda alhaji ke masa maganar gami da bashi umarnin janye wancan qudurin nasa

    “Alhaji,naso ace an hada abun nan saboda a qarfafa zumunci,sannan yanzun bansan da wanne ido zan kalli isma’il ba(mahaifin mahfood)” murmusawa alhaji yayi

    “Akwai dangi da yawa,ba lallai sai mahfood ba tunda jininsu baizo daya ba,kada azo ayi abinda za’a zo daga baya ana dana sanin aikata shi,isma’ila kuwa shi da mahfood din kabar komai a hannuna zan magana dasu” kansa a qasa amma ransa a matuqar bace ya amsawa da alhaji,gami da yi masa godiya da fatan samun qarin shekaru masu albarka da lafiya me dorewa.

    Ummu da kanta ta shiga dakin inda widad keta fama kwanciya don yi mata albishir,a kwancen ta sameta,ta janye rufarta tana cewa

    “Tashi……ruwa sarkin kwanciya” sake curewa tayi waje daya tana turo baki gaba,don har ta gaji ma da kukan

    “Nace ki tashi hakanan, kwanciyar ta isa,maganar aure ce an janyeta an fasa” da sauri ta waiwayo tana kallon ummun gami da jin fitar maganar daga bakinta kamar almara,ko kuma tayi hakanne don ta tashi ta sake?,babanta fa?,wanda baya fadin abu ya canja,wanda baya magana ya sabata,tsayayyen akan duk abinda ya sakawa ransa zai aikatashi,to amma kuma……ummu bata qarya sam sam tasan halinta,fadi da cikawa ce,sannan yadda take qaunarta ta tabbatar ita da alhaji ne suka aikata hakan,sai kawai ta bugo wani tsalle ummu bata ankara ba sai jinta tayi a jikinta ta dane mata wuya cikin madaukakin farinciki.

    Murmushi ummu keyi tana jin farinciki cikin ranta itama,tasa hannunta tana banbanreta a jikinta tana cewa

    “Zaki qarasani ‘yar nema,ashe duka iskanci ne,mitsitsiyarki dake wai kinsan meye auren dole,maza saiki sauka ki shiga bandaki ki wanka ki shirya ki shiga cikin ‘yan uwanki” ummu kuwa bata kai qarshen zancan ba ta dire sai bandaki,tayi wankanta sarai,akwai kayan dama da taketa cin burin sakasu,yau kuwa zata gwangwaje kwalliyarta,latifa ta zuba mata abinci taci da kyau,sannan ta tsala kwalliyarta cikin wani lace mai azabar kyau da tsada da ummu ta dinka mata ita kadai,ta zauna ta tsara kwalliyarta dai dai da shekarunta da kuma iyawarta,sai gata ta fito dagwas dagwas gwanin kyau.

    A falo ta samu ummu tare da baqin da suka fara zuwa mata yawon sallah,wanda duka ‘yan uwa ne da surukai,batulu ce matar baban widad din,haka suke rabawa duk sallah,wata zata fara zuwa gaida ummu dayar ta zauna a gida,washegari ko wata washegarin sai dayar tazo.

    Jakarta ummu ta kaba ta zuba mata sababbin kudi ‘yan biyar biyar,duk da tasan halin kayarta,qila sai a gama yawon sallar a ci a cinye bata kashesu ba,daga qarshe dasu da wadanda ta samu duka dawo mata dasu zatayi

    “Ga barka da sallah ta nan” rungume ummu tayi tana dariya cikin farinciki

    “Na gode ummu” sai a sannan ta waiwaya ta rusuna kadan tana gaida batulu.

    Can qasan zuciyarta maqare fal da baqinciki da takaicin yarinyar,amma a saman fuskarta kadaran kadaham,tayi qoqarin gyara mood nata ko don ummu dake wajen ta amsa mata

    “Yammatan ummu,lafiya lau sai ina?”

    “Wajen anty madina zani” ta amsa mata tana yin gaba,duk da qarancin shekarunta,amma kwanyarta na iya tuna wasu abubuwan da suke gudana tsakaninta da matan baban nata,suke kuma kan gudana din,shi yasa dai dai da wuni guda bata marmarin zuwa gidan nasu bare ayi batun kwana,ummu ma ba zata bari ba,koda kuwa babanta yana da muradin hakan.

    Kamar ko yaushe chamber ta hadu a sassan anty madina,shigarta wajen kallo ya koma kanta,masu tankwa da yabawa nayi,masu baqinciki suna nasu aikin,ko meye saman fuskarka kusan ta saba dashi,uwa uba ga quruciya da bata sanyata daukan abubuwansu da muhimmanci,fatanta da burinta kawai ta shiga cikin ‘yan uwanta ayi mu’amala da ita kamar kowa.

    Wunin ranar gaba daya cikin walwala ta yita,sai takejin kamar wadda aka daddaure ayau ta samu ‘yanci,sai dare ta dawo sassan umnu,tana gefanta tana bata labarai na abinda suka faru,kowa cikin jikoki na zaune saman carfet suna cin abinci amma ita na nanuqe da ummunta,tare suka ci abinci kafin dare ya miqa su wuce dakin kwanciya.

    Sai bayan isha’i a ranar alhj mahmud ya koma gida,har lokacin akwai sauran damuwa da bacin rai a tattare dashi,yayi wanka ya canza kaya,umma dake da girki ya gabatar masa da abinci,sannan ta zauna a gefansa tana sake karantarsa,bakinta cike fal da tambayoyi da kuma son jin qwaqwafi,don tunda ya shigo ta karanci akwai wani abu daya faru.

    Ganin shuru yana ta cin abincin baice komai da ita ba,sai ta danyi gyaran murya tana gyara zama

    “Amma abbansu fuskarka kamar akwai damuwa,Allah yasa lafiya?” Tsaki yaja yana ajjiye cokalin hannunsa,ya kalleta

    “Bari kawai hauwa’u,yarinyar nan ce ta watsamin qasa a idanu,takeson ta kunyatani a dangi”

    “Wa fa?” Ta tambaya tana yamutsa fuska,duk da zuciyarta ta gama gaya mata wacece

    “Widad mana,qiri qiri yarinyar nan ta fandare taqi mahfood,har sai da alhaji yasa baki a maganar ya dakatar da abun” baki hauwa ta riqe tana sakin salati cikin sake kambama abun,lallai yarinyar shafaffa da mai ce,tana cewa su din akwai yaransu da aka yiwa haka?,kuma suna zaune lafiya lau a gidajensu har kwanan gobe sai tashin zancen

    “Yanzu abbansu,lamarin da aka faro zancansa tun yarinyar nan bata cika mutum ba,amma yanzu saboda idanunta sun fara wayewa zata ce bataso?,kuma alhaji shima ya biye mata?,wannan wacce irin tabara ce?,ah to lallai abu ya girmama,billahillazi idan ba’a yi wasa ba gaba sai abinda tace za’a yi mata,idan ba haka ba ran kowa ya baci harda mu iyayenta” fushin abba ne ya motsu sosai akan widad din,kuma dama abinda hauwan keso kenan

    “Haba ita din banza?,wallahi bata isa ba,ita ta haifemu ma ashe kenan”

    “To tana ganin haka tana faruwa tun yanzu gaba basai abinda taga dama ba?,aure kuma dama ai uba ya isa da diyarsa budurwa ya zaba mata miji,bare wannan da ko minzalin budurwa bata kai ba” shuru yayi yana juya zancan,abun ma sai yanzun yake sake bata masa rai,tabbas bazai barta haka ba,duk da ya sani rayuka zasu iya baci,don ummu ba zata lamunci takura ga widad din ba.

    A wannan daren da taimakon zugar hauwa ya kwana cikin tunani,washegari.batulu da hauwan ta bincina mata abinda ke faruwa itama ta dora da tata zugar,sai ya sake hawa sosai

    “Banason wannan maganar,ku qyaleni haka” yace dasu daga bisani,ya riga ya gama yanke matakin da zai dauka akan maganar.

    Widad kuwa walwalarta takeyi sosai abinta hankali kwancw,tunda ta samu akwa kwance ta daga daurin talala na auren mahfood,bikin sallarta take abunta gaba gadi,koda abbanta yazo gidan bayan kwanki biyu bata kawo komai a ranta ba,batasan cewa yazo da sabon alqawarin bada ita ga ma’aruf,ma’aruf dai,ma’aruf din da kalmar zo na kasheki bata taba shiga tsakaninsu ba,ma’aruf din da tsakaninta dashi saidai ido,saidai bata da labarin wannan alqawarin,domin ummu ta rufe zancan don kada a katseta daga walwalar data samu cikin bikin sallar,ta sakaya zancan bayan ta cewa abba

    “Mahmudu ni bazan dakatar dakai ba daga baiwa yarinyarka duk wanda kakeso ba,amma muddin babu haduwar jini ko taji bata sonsa bazan lamunci a kaita inda zafa quntata ba,don ina kallonta ne kamar amana a hannuna,idan tasu tazo daya da ma’aruf zanyi farinciki da hakan,don atika(mahaifiyar ma’aruf,jika ne shi cikin gidan,d’an mace ne)tamkar ‘ya take a waje na”.

    Ci gaba tayi da sabgoginta abinta,ta.maida kanta ga islamiyyar da take zuwa,don tunda aka koma hutu boko bata koma ba,alhaji yace ya isa hakanan,su maida hankalinsu ga islamiyya,ita dasu Aafiya,yayin da zancan bada ita ga ma’aruf ya fara yawo cikin gidan.

    Zancan ya zowa anty madina ta bakin mijinta uncle mulhim,ta jinjina lamarin sosai

    “Tirqashi” ta fadi,saboda tasan irin rashin jituwar dake tsakaninsu,duk sanda widad ta shigo tana binta da kallo yadda take sabgoginta da alama batasan abinda yake faruwa ba,tana tausayinta itama,tana yarinyarta amma sai abubuwa ke zuwar mata kamar wata babba?.

    Bata tashi sani ba sai wata rana suna dawowa daga islamiyya,a hanyarsu ta zuwa gida sun biyo ta wani layi,tun daga nesa suka hangi ma’aruf din yana tahowa shi da wani abokinsa,kunnensa maqale da earpiece suna hira kadan kadan da abokin nasa,kafin su qaraso Aafiya tasa hannu tadan bugi widad,wai tanason mata nuni dashi,saidai ko daya ita widad din bata ma fahimci me take nufi ba har suka qaraso dab dasu.

    Aafiya ce ta gaisheshi tana rusunawa,ya amsa mata suka wuce,widad kam da idanu ta bisu har suka wuce din,sai taja tsaki

    “Yanzun ya kusa zama angonki ma ba zaku fara magana ba widad?” Wani kallo tayi mata cikin quruciya da sakalci

    “Waye angon nawa?,ni ba wanda zan aura na gaya miki ina wajen ummu na,tare zamuyita zama”

    “Tabdijan,ni kuwa ana cewa aure za’a yimin zan yarda,bakiga kayan lefen da aka kawowa su anty ramziyya ba?,ga kayan girki da gadajen da aka siya musu masu yawa fa,ke don har yanzu bakije gidajensu ba,baki gani ba gwanin sha’awa,su dafa abinda sukeso,suyi kwanxiyarsu a gadonsu,ba duka ba aike ba fada,ke…..hmmmmm” Aafiya ta fada da alama abun yana burgeta,fuskar widad ta dan sauya zuwa fara’a

    “Su ai sun girmemu,ko auren za’ayi mana ba za’a yi mana irin nasu ba” kama baki Aafiya tayi tana fidda ido gami da kallonta

    “Inji wa?,wallahi momma tace qila ma mu samu abinda yafi nasu”

    “Allah?”

    “Wallahi” sai widad din tayi shuru tana jinjina kai,hadi da tuna yawan kayan da aka fitarwa kowacce cikinsu ramziyya daga gidan aka sa amota zuwa jeren gidanta.

    Sam ta manta ma da wani zancan ma’aruf,har suka isa gida suna zancan kayan auren,a harabar gidan suka rabu kowa ya shige sassansu.

    *RUMBUN K’AYA*🔥

    *DAUDAR GORA*🔥

    *IDON NERA*🔥

    *A RUBUCE TAKE*🔥

    *KI KULANI*🔥

    *_uhmmmm_*😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊

    *Nasan zakuce ya da murmushi haka?*

    *Wanda bai shigo ba bazai gane ba*

    *Sai kin shigo daga ciki zaki gane me nake nufi*☺️☺️

    *KE DAGA JIN SUNAYEN LITATTAFAN MA KADAI KASAN CEWA AKWAI WANI BABBAN ABU MAI MATUQAR JAN HAKALI TATTARE DASU*

    *KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?*

    *KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?*

    Littafi daya—400
    Biyu—600
    Uku—-800
    Hudu—–1k
    Biyar din duka—-1200

    *ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥

    0022419171
    Maryam sani
    Access bank.

    Shaidar biya tanan👇🏻
    09033181070

    *MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN*

    09166221261

    🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
    *Ina yan uwa ‘yan nijer?*
    *Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

    +227 90 16 59 91

    Littafi daya—450CFA
    biyu—650CFA
    uku—-850CFA
    hudu—-1050 CFA
    Biyar—-1250CFA

    *A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*

    *SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!*

    *Thanks for choosing us*🔥[2/3, 4:25 PM] +234 813 343 4840: *H U G U M A*
    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • Arubuce Ta Ke 3

    Koda ta shigan bata zauna ba kamar yadda anty deena tace tayi sauri,ta sameta tana yankawa momma albasa,sai zabga gumi taje gami da hawaye,duk da cewa kitchen din kitchen ne irin na zamani,da ya wadatu da iska da manyan windows,dukka a qoqarin momman na koya mata girki,kada ta tashi kamar widad,wadda bata cas bare as a gidan,abinda ya damu wasu cikin gidan,yake kuma basu haushi sosai,suna gajun gatan da ummu ke nunawa widad din yayi yawan da ya kamata ta rageshi ta sanwa wasu cikin jikokinta.

    Budewa Aafiya kayan tayi tana cewa

    “Zabi duk abinda kikeso a ciki” kanta ta leqa cikin ledar tana cewa

    “Ummm,yar gatan ummu,inda nice nace mata ta siyon kayan nan qi zatayi,sai tace naje na tambayi yayuna maza”

    “Yaaya mahfood ne nima ya kawomin” daga kai tayi ta kalli widad,dududu itama Aafiyan ba zata wuce sa’ar widad din ba,saidai ta danfi widad din girman jiki kadan

    “To me yasa ba zakiyi amfani dasu ba?” Tura baki tayi tana tsuke fuska

    “Banaso,ni bana son sa,banason ana min zancensa,ki dauka anty deena zata aikeni” ido ta fidda

    “Yaushe tazo?”

    “Yanzu” saita ajjiye wuqar tana zura hannu a ledar,ta zabi abinda takeso tana cewa

    “Aiko na godde wlh,bari nayi sauri na gamawa momma aikinta na fito” tana dan lila ledar ta fice abinta ba tare data tsaya sauraronta ba,ta samu anty deena a falo,ta bata leda tace ta kaiwa anty madinan,ta amsa ta fice da dan guntun gudunta.

    Ta dan samu yaran sassa sassan gidan da dan dama a sashen anty madinan,kasancewarta mai fara’a haba haba dasu da jan kowa a jiki,kowa nata ne,hakanan kowa yana jin dadin xama dasu,bayan sa’anninta masu kamar shekarunta data samu,harda yayyensu da ake dab da bikinsu,kuma suna tare da anty madinan,da alama akwai abinda take koya musu,sauran sa’annin nata suna daga gefe sun buda tasu chamber din.

    Bayan ta miqa mata ledar sai ta kalleta

    “To wannan dayar kuma fa?”

    “Kayan kwalliya ne na kawowa su rafi’ah”

    “A ina kika samu kayan kwalliya masu yawa haka?” Basma cikin ‘yammatan dake shirin amarcewa ta fada tana dubanta bayan ta dago kanta daga danna wayar da takeyi,kanta tsaye ba kwana kwana ko damuwa tace

    “Yaa mahfood ne ya kawomin”

    “Shine kuma zaki rabar?” Anty madina ta tambayeta tana bada hankalinta sosai a kanta,kamar zata saki kuka tace

    “Banaso anty wallahi,ni banaso”

    “Barta don Allah ta rabar,miqomin na zabi nawa” basman ta sake fadi tana miqa hannu,ba wani damuwa tattare da ita ta miqa mata ledar ta qara gaba tana cewa

    “Anty basma idan kun gama su na’ima zasu zaba” anty madina data bita da kallo tana kallon zallar quruciya ta saki ajiyar zuciya

    “Allah ya zaba abinda yafi zama alkhairi,baaba mahfood dai kam to”

    “Uhmmm,wai laifin widad kuke gani?,ni nafi ganin laifin baaba mahfood din ai,kamar maye,yarinya tun tana ‘yar tamilo kake faman mata hidima,jikinka da aljihunka basu huta ba,ta fara wayo ta nuna baka so basai ka haqura ba,dui gidan ita dayace ‘ya?,ko ita kadai ce jika?” Kai anty madina ta girgiza

    “A’ah fa basma,har yanzu widad akwai quruciya tattare da ita,ai ba’asan maci tuwo ba sai miya ta qare”

    “Uhmmm,anty madina,yarinyar nan fa daurin gindi ta samu,Allah kuwa,kuma sai yaushe?,bayan mu kadai ne muka haura zuwa SS,mu dinma gashi SS one kawai aure ya tashi,bare su da jikinsu da alama mai saurin girma ne,Allah yasa su gama JS ma”

    “Allah ya shiga lamarin” anty madina ta amsa mata

    “To Ameen”basman ta fada tana maida kanta ciki ledar,don tuni marwa ummee da nujood suka gama zabar nasu,anty madina nata musu tsiyan girma ya fadi,raqumi ya shanye ruwan ‘yan tsaki,su da za’a kawo musu akwati me zasuyi da toshin qanwarsu.

    Widad kam bata sake bi takan kayan ba,a nan suka gama gantalewa,duka ta rabar,dan abinda yayi saura ya gangarar dashi anan wajen anty madina,tayi komawarta sassansu.

    Sanda ta koma tuni abbanta ya tafi,sai ummu kawai

    “Ina kikakai kayan?” Ta tambayeta tana tallafe da kuncinta tana dubanta,maimakon ta amsa saita narke fuska,ta kuma shige cikin kujera abinta ta lafe taba mus mus da baki,juyin duniya ta gaya mata inda takai kayan taqi,dole ga qyaleta,tasan indai cikin gidanne zata ji.

    Tun tana zaman likimo har bacci yayi awon gaba da ita,bata tashi ba sai kusan azahar,sanda latifa ta kammala abincin rana,ta kuma tattaro panties da undies din widad din zata wanke.

    Sai datayi sallar azahar kamar yadda ummu ta horar da ita,ta karba abinci,saita zagaya baya inda latifan ke mata wankin,ta zauna tana ci suna hira da latifan…

    ***********

    Kamar kowacce safiya a ranakun makaranta,school bus din gidan ke tattara kan duka yaran gidan zuwa makaranta,wanda kusan yawancinsu makaranta daya suke zuwa,wadanda kuma suke mabanbantan makarantu sai ta miqa su sannan ta dawo gidan zuwa lokuttan tashinsu.

    Daga can sassan ummu widad ce zaune saman kujera,sanye da sabbin uniform dinta kamar yadda komai nata a ranar yake sabo a matsayinta na dalibar da ta shiga secondry school a ranar,ummu na zaune daga qasan carfet hannunta riqe da plate tana miqawa widad din plantain din ciki

    “Maza maza kici kafin ‘yan azalzalar nan su biyo sawunki,idan ba haka nayi miki ba haka zaki tafi,yanzun latifa zata kawo miki lunch box dinki” fuska a nake a kuma sakalce take duban ummu

    “Wallahi na qoshi ummu,ya isa haka”

    “A’ah,qarashe wannan dai” ta fada cikin nuna kulawa,hakanan ba don taso ba ta daga cup din hannunta dake cike da tea tana shanye ragowar na ciki,dai dai lokacin basma ta shigo,sanye take da kayan gida,kasancewar ita din a yanzun sai daina zuwa,saboda kusantowar bikinsu,bawai don sun gama bane,haka al’adar gidan take,alhajin salim mai fata tsoho mai ran qarfe,kaka kuma uba ga ahalin gidan wannan sbine tsarin da ya dora dukka yara da jikokinsa,mutane da yawa ‘yan bani na iya da kuma ‘yan gaza gani kance

    ‘Gidan me fata ai da wuri suke aurar da yaransu,da sun ga mai kudi sai su cire yarinya daga makaranta,basa ko gamawa,don sunga suna samun masu danshi ne,suma masu kudin da shegen kwadayi,suna ganin kyawawan mata sai su rude’ duk da wannan jita jita na dawo musu kunne amma sunyi banza da zantukan mutane,abu daya tsoho kuma dattijon ya sani shine,mutuncin mace dakin mijinta,hakanan duk wadda tayi katari da samun mijin dake da ra’ayin karatu tana ci gaba da karatunta ne cikin dakin mijinta.

    “Goyon kaaka,sai a fito ko?,kin tsaida mutane kina bata musu lokaci” ta fadi tana harararta,ganin yadda ummu ta zauna dafa’an tana bata abinci kamar wata yarinyar goye,waiwayowa ummun tayi tana danqara mata harara

    “Ke kuma da bake za’ayi tafiyar wa ya sakoki a maganar?”

    “Yo fisabilillahi ummu saita makarar da kanta fa makarar da wasu?” Tayi maganar tana miqa hannu gami da fusgar sabuwar school bag din widad din dake ajjiye kusa da ita,kafin su sake cewa komai.muryar dattijon ta ratso falon

    “To….to,ya akayi?” Ya fada yana qarasowa a hankali zuwa cikin falon,kafin ya samu waje ya zauna yana dubansu.

    Russunawa basma tayi ta gaidashi,dai dai lokacin latifa ta qaraso dauke da lunch box din widad din

    “Gashi an gama” ta fadi tana ajewa gabanta

    “Ko muje motar na rakaki dashi” latifan ta sake fada tana kuma dauke lunch box din daga gabanta,tabe baki basma tayi sannan tace

    “Tabdi!,gigin primary,kina shiga dashi ansan burbushin primary ce,meye hadinki da wani lunch box tsabar sangarta?,Allah latifa ke kike sake taya ummu ana sakalta yarinyar nan” ta qarashe maganar tana hararar widad din

    “Wato kedai anyi babbar banza ko?” Alhj salim ya fada yana duban basma

    “Allah alhaji bata sanin ta fara girma”

    “Wuce ku tafi ga iliya can yana horn” ya fada yana daga musu hannu,sai a sannan widad ta sauko daga kan kujerar,ta maida takalmanta suka fice ummu tana muta addu’ar dawowa lafiya.

    Ajiyar zuciya ta sauke bayan ta tabbatar da fitarsu,ta maida dubanta ga alhj salim din

    “Yaran nan sam basu da zurfin hankali,ta yaya zan banzatar da widad ta gaza samun kulawata?,yarinyar da tun tana watanni a duniya mahaifiyarta ta tafi ta barta?,idan ban kula da ita ba waye zai kula da ita?” Murmushi dattijon yayi yana qarashe janye ragowar carbin da ya rage a hannunsa sannan ya ajjiyeshi gefe

    “Iya tasu fahimtar kenan,amma duk da haka saboda gudun ci gaba da samun sabani da yadda suke jin haushinta ganin kamar kinfi sonta,kiyi qoqarin boyewa da rage wasu abubuwan”

    Dan sunkui da kanta ummu tayi

    “In sha Allah” ta amsa masa cike da ladabi,duk da bata da tabbacin yiwuwar hakan.

    “Kunun za’a kawo maka ko dumame?”

    “A fara kawomin kunun da qosai tukunna” ya amsa mata yana gyara zamanshi sosai saman kujerar,ta yunqura ta miqe zuwa kitchen da kanta,duk da tsufanta hakan bai hanata yi masa tasa hidimar da kanta ba,koda zata bawa latifa tata hidimar tayi mata,amma ta alhajin ita keyi.

    Awannin da tayi a makaranta a ranarta gane banbamcin secondry school da primary,sosai makarantar tayi mata dadi,lokacin tashinsu da yayi tun a cikin motar suke hayaniya,labarin sabon aji da kuma sabuwar makaranta

    “Don Allah kuyi mana shuru,kun cika mana kunne ha’an” ramziyya wadda take cousin a wajen widad ta fada,ita din gaba take dasu,don a qalla ta basu shekara kusan biyu,ita dinma wannan shekarar ta shiga js three,kuma akwai yiwuwar shekara mai zuwa a karba kudin aurenta kamar ‘yan uwanta,dole suka rage hayaniyar,saita maida hankalinta ga iliya driver

    “Ko ka wuce damu gidan baaba mahmud?,muga lefen najwa tunda yau babu islamiyya”

    “To shikenan,babu laifi” ya amsa mata.

    Kicin kicin widad tayi,ko kusa ko alama bata qaunar zuwan gidan nasu,koda hutun makaranta akayi kuwa,gidan ba gurin zuwanta bane,zata iya cewa banda mahaifinta bata da kowa a cikinsa,sai yayanta wanda.ba kasafai kake samunsa cikin gidan ba,yawancin lokutta yana makaranta,duk da yadda mahaifinta ke nacin ta dinga zuwa din amma ummu ta hana,idan ta kama saidai ta wuni ta dawo.

    Tun daga harabar gidan matan gidan suka fara jiyi hayaniyarsu,babu wadda ta motsa,don kowacce dan data haifa kadai shine nata,har suka qaraso cikin ainihin babban falon gidan

    “A’ah,kada dai kucemin daga makaranta kuke?” Ta tambayesu tana tafa hannuwa cike da yaqe da kuma riya,saboda mai gidan na nan,daga inda yake din kuma zai iya jiyo komai

    “Ga alama kuwa umma” najwa dake fitowa daga dakinsu ta fada tana dariya gami da qoqarin daura dankwalinta

    “Lefe mukazo gani” widad ta fada tana dan dariya,ganin yau yau umman ta sake mata fuska,ramziyya ta harareta

    “Shegen son kallon kayan lefe,caraf ta bada amsa”

    “Da gaskiyarta,gaba su za’a kawowa ai” umman ta amsa bayan ta qwalawa me aikinta kira kan ta zubo abinci, murmushi widad tayi maganar tana bata mamaki da dariya,yanzun wataran itama sai a ciko akwatuna da kayan lefe ace nata ne?.

    A nan suka ci abincin rana suka kuma baje suka kalli kaya son ransu,alhaji mahmud ya fito a shiryensa,suka hau gaisheshi ya amsa musu cikin fara’a da jin dadin ganin ‘ya’yan ‘yan uwansa,ya bisu da kyautar dari bibbiyu sababbi,duka harda widad din bai banbantata da kowa ba a cikinsu,sannan ya fice yabar gidan.

    “Ni kunzo a dai dai ma,ku taimakamin na fidda kayan da zan kai dinki” ramziyya ce ta dinga tayata zabin,widad na hade mata su waje daya

    “Basuyi yawa ba wadan nan kayan anty najwa?, duka zaki kai dinkin?” Inji widad dake zaune daga gefe

    “Saina ma qara wasu,kin manta haka amare keyin dinki da yawa?” Kai ta jinjina kawai tana ci gaba da kallonsu,bayan sun gama najwa tace

    “Ki kwana anan widad,saiki rakani nakai dinkin,gobe saina maidaki gida”.

    Cikin murna da zumudi ta amsa da to,ko ba komai zata yita kallon kayan lefen dake burgeta sin ranta,don haka ta baiwa su Aafiya jakarta suka wuce mata gida da ita.

    Sanda ummu taji shigowarsu sai tayita sanya idanu taji shigowar widad din amma shuru,har ta gaza daurewa ta aika latifa sassan su marwa ko sassan anty madina ta dubo mata widad din me ta tsaya yi bata shigo taci abinci ta sake wanka ta canza kaya ba.

    Da latifa ta dawo mata da batun sun barta gidan baaba mahmud shuru tayi,cikin ranta duka babu dadi,don bataso ko kadan widad din tayi nisa da ita,to amma tasan mawuyacine itama ta yarda ta kwana din,ta tabbatar da wahala bata nema a kawota gida ba.

    Sanin hali yafi sanin kama inji hausawa,don kuwa tun bayan sallar magariba bayan sun dawo daga wajen dinkin ta lafe a kujerar falon gidan tana raba idanu,ta cika tayi fam,gida kawai takeson komawa,har umma ta fahimci haka,itama hakan ya mata dadi,don duk randa yarinyar ta kwana a gidan ko yaya ne sai sunga wani abu na bacin rai daga mai gidan dangane da yadda yake nuna mata kulawa

    “Rabu da ita umma,kin ganta fa ta fara girma,Allah har qirga dangi naga ta fara,amma.har yanxu bata girma da kwana a bayan ummu ba,yau dai a gidan nan zaki kwana,idan bikin nawa yazo ma ba zaki iya kwana ba kenan?” Itadai batace komai ba har zuwa sanda baaba mahmud ya dawo,tare suka zauna da ita suna cin abinci amma sam taqi sakewa,qarfe takwas na dare ta fara musu hawaye,dole ya tashi driver ya maidata gida

    “Maidata,kada ta hanamu barcin dare” cewar abban nata.

    Karfe tara saura suka isa gidan,sanda motarsu ta tsaya daidai sanda motar uncle haisam abban su marwa qani ga mahaifinta ta tsaya

    “Aah,wa nake gani haka da daren nan kamar widad?” A ladabce drivern ya amsa shi

    “Itace,taqi zama ne abba yace a dawo da ita”

    “Ikon Allah,to muje ciki” ya fada yana kulle motarsa,sukayi sallama da drivern yabi widad din zuwa sassan iyayensa.

    Ummun da kuma alhaji suna falo a zaune,sai a sannan yake cin abincin dare sunadan taba fira sama sama da ummun.

    Bataji sallamar widad ba sai fadowarta jikinta data ji,tana shirin dagata sallamar uncle hisham ta biyo baya

    “Tare kuke ne?” Ummu ta jefa masa tambayar,yana rage tsahonsa gami da neman wajen zama yace

    “A’ah,can na ganta drivern gidan yaaya mahmud ya sauketa”

    “Yar nema,shine kike biyo dare kika gudo?,ba zaki qyalemin mata dai ta huta ba kenan?”cewar alhaji yana tsokanarta,daga ummu tayi tana turo baki

    “Bakaji dadin gani na ba?,bayan ko cigiyata ma bakayi ba….. shikenan” tayi maganar tana miqewa daga jikin ummu tana wucewa daki

    “Ahaf……me kika sani banda takura?”. Bata ansa ba har ta isa daki ta tura ta shige abunta,dariya suka saka gaba daya, alhaji ya girgiza kai

    “Quruciya me dadi” ya fada a hankali,sai ya maida dubansa ga hisham yana tattara hankalinsa zuwa gareshi.

    *_RIGIJI GABJI!_*🔥🔥

    *_WANI KAYA SAI AMALE_*🔥🔥🔥

    *FITATTUN ZAFAFAN DA BABU NA BIYUNSU*🔥🔥

    *JERIN GWANON LITATTAFAI ABOKAN TAFIYAR JUNA MASU MABANBANTAN LABARAI DA FASAHA*

    *_’YAN BIYAR DIN NAN NE FA_*

    *_SARAKAN LABARUN_*

    *NISHADI*
    *CAKWAKIYA*
    *GWAGWARMAYA*
    *BARKWANCI*
    *TSANTSAR DARASIN RAYUWA*

    *TARE DA*

    *ZAZZAFAN SALO NA SOYAYYA MAI RIKITA TUNANI DA TSUNDUMA MAI KARATU CIKIN TAFKIN SHAUQI*

    *SUN SAKE SHIRYAWA TSAF,DAUKE DA WANI TARAGO MAI CIKE DA LABARAI MASU ZAZZAFAN ZAFI!!!*

    *KIN SHIRYA MADAM?*

    *MAZA ANTAYA NAKI KUDADEN KIBI SAHUN AYARIN MATA MASU AJI TA HANYAR BIYAN KUDIN NAKI KARATUN WADAN NAN LITTAFAI KAMAR HAKA*

    *DAUD’AR GORA* Billynabdul

    *KI KULANI* Missxoxo

    *IDON NERA* Mamuhghee

    *RUMBUN K’AYA* hafsat rano

    *A RUBUCE TAKE* Huguma

    *ZAKI IYA BIYA KAI TSAYE TA WANNAN ACCOUNT DIN*

    0022419171
    Maryam sani
    Access bank

    Saiki tura shaidar biyanki ta wannan number

    09033181070

    *MASU TURA KATIN MTN KO VTU KUMA ZASU TURA WA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANSU*

    09166221261

    *Yan nijer kuwa zasu tuntubi wannan number*

    +227 90 16 59 91

    *Muna godiya da ci gaba da zabin zafafa biyar a koda yaushe*🙏🏾🙏🏾
    [1/23, 6:13 PM] It’s Queen Meenali👸🏻: *HUGUMA*
    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addara ta)

    Page 04
    —————————————————-
    *MAAB LUXURY HOME*

    *_idan kaji gangami akwai labari_*
    *_SABUWAR DUNIYA CE_*
    *ALFAHARIN UWAR GIDA*
    *FARINCIKIN AMARYA*
    *MAIDA TSOHON GIDA SABO*
    *DUNIYAR QYALE QYALE*
    *KAYA NA ALFAHARI DA TAQAMA*

    *_Ba iya kyawun idanu suka tsaya ba,harma da ingancinsu da kuma qwarkonsu,ka dade kana mora kana kece tsara a tsakanin tsararraku da sauran mutane_*

    *nasan zaku tambaya ina ne nan?*

    *MAAB LUXURY HOME*

    😊 *Kai daga jin sunan ma babu tambaya*

    *_duniyar qawata muku gidajenku ku ganku kamar a wata nahiya ko wata duniyar_*

    *Suna kawo kayan kitchen rankatakaf manya da qananu*

    *Kayan gado dana parlor*

    *Kai…suna kawo kowanne nau’in kayan ado na cikin gida*

    *Karkiyi qasa a gwiwa kuma kada kiyi sake ma dafe,maza garzaya ki nemesu a*

    _adress dinsu dake No 22 Ahmadu bello way,kano state_

    *Ko kuma kuyi order din kayanku kuna daga gida ta shafinsu na instagram*

    @maabluxuryhome

    *Facebook*
    @maabluxuryhome

    *Ko ku nemesu ta lambar wayarsu kamar haka*
    08034631010

    *Kyau inganci da rahusa shine takenmu*😊😊🤝🤝🤝🤝
    _______________________

  • Duk Karfin Izzata Book 2 Page 29

    Duk Karfin Izzata Book 2 Page 29

    Page 29

    Uk

    Tun da tayi sallar asuba bata mai da barciba take shirye shiryen tafiya Nigeria shiru shiru yaya Prince bai dawo daga masallaci ba har karfe 6 bai dawo ba ta gama duk shirin abun da ya dace sai murna take zata koma naija shiru shiru har 7 yaya Prince bai shigoba ɗaukar hijabin ta tayi ta sanya akan riga da wandon ta ta fito palo baya palo ɗauko remote na ɗakin binciken sa tayi ta sai ta sama ta danna stair case ɗin ya sauko chikin sauri ta haura sama har tana haɗawa da gudu tsaye gaban na’urori ta hango sa ya bawa hanyar shigowa baya daga shi sai Short yana aiki watsawa tayi a guje taje ta haye bayan sa tana murmushin,a sukwane ya juyo tare sauko da ita cikin zafin nama ya damko wuyar da tsawa yace “ke baki da han… Bai karisa maganar ba yayi shiru tare da zame hannun sa daga kan wuyar ta ya rungumeta yana ɗan sosa kai “yaya Prince laifin me na maka yau kuma? Kara matse ta yayi a jikin sa “babu komai Sister na mantane ai daman na faɗa miki ba zai yiwu na sauya lokacin guda ba sai a hankali” “to yaya Prince ya banu yafi Nigeria bane? Ɗan sakin ta yayi tare da juya baya ya goya ta ya chigaba da aikin sa da ita a bayan sa “na sanar da su Abba akoi aikin da ban karisa ba dan haka jirgin mu sai da yamma zai tashi” hannayen ta ta zuro ta wuyar sa ta chigaba da magana “yauwa yaya Prince tun da sai da yamma zamu tafi pls ka kaini yawo naga gari kafin mu tafi” girgiza kai yayi kafin yace “no baki yarda dana cemiki duk macen da tayi tarayya da ni idan ba sojaba zata shiga babban haɗari ba kon? To ko sojojin ma suna chikin haɗari bare dan Kafin nazo wanna matsayin da nake na Brigadier general Safras na kashe mutane da dama na tarwatsa rundunar yan ta’addan da dama a kasashe da dama ta ko ina ina da tarin makiya shi ya sanya bana yarda da kowa kuma dukkan yan uwana nake kula da duk wani motsin su zamanki lfy shine kiyi zaman ki a matsayin baki sanni ba yafi miki” kai ta ɗan ɗaga sama kafin tace “yaya Prince to ya akayi ranar mukaje shopping tare kuma har ka tafi kabar Ni? Sauke ta yayi daga bayan sa yana faɗin “kema ai ba wani motsin da zakiyi ban sani ba da gangan na barki a shopping ɗin dan nasan gaba ɗaya wajen yana karkashin kulawar sojojin mune shopping na matar general dest ne so na san ba abun da zai faru” “to yaya Prince dan Allah ka faɗa min taya akayi kasan yaya Khalid ne ya ɗauke ni” guntun tsaki yaja dan hiyana ta fara bata masa rai baya son yawan magana ganin ta tsare sa da ido ne ya sanya yace “sister nifa bana son yawan magana kai na chiwo yake min idan nayi magana sosai ina da tarin abubuwan da ya kamata na kammala please leave” tsuke fuska tayi ta turo baki chikin shagwaɓa ta fata magana “yaya Prince ka manta kai kace na koya maka magana to me yasa kuma ina koya maka zaka che baka so” jan hanchin ta ya ɗan yi baya so ya mata tsawa dan ya ɗau alkawari ba zai sake hakan ba sai ya zama dole gashi ta kule sa bai san magana tana sanya shi dole ji yake kamar ya sharara mata mari ya koreta a ɗakin amma sai ya danne yace “sister dole ne zan san Khalid ne ya ɗauke ki mana kije kiyi searching akan sunan Brigadier general Safras ba a banza mutun zai taki wanna matsayin ba kuma kin manta ne? nache maki duk wani motsi na yan uwan mu na sani” “yaya Prince to dan Allah ni dai ina son zuwa yawo na kalli kasar nan kafin Mu koma” shiru ya ɗan yi ba dan yazo ba yace “ok to jeki fitar kin da kayan hausawa da face mark ina zuwa sai muje yawon muyi breakfast a chan amma dai gaskiya kin takuramin dayawa” tsalle tayi ta rungume sa sosai tana dariya tana faɗin “nagode yaya Prince” ɗaga ta yayi gaba ɗayan ta ya ɗaura ta saman kirjin sa yana tsaye a miƙe ya sanya hannu ɗaya ya chire mata hijabin jikin ta ya jefar kasa a nitse ya zame ɗan siririn hannun rigar da ta sanya ya ganganrar da rigar zuwa chikin ta zubawa tula tulan ta ido yayi na ɗan mintoci yayin da ita kuma ta runtse ido hannu ya ɗaura saman bakin nipple nata yana dubawa “sun dai na yi maki zafi ko? Kai kawai ta gyaɗa masa alamar eh ba tare da ta buɗe ido ba “why are you closing your eyes? chikin shagwaɓa tace “kunyar ka nake ji” “kunya?” ya mai mai ta kalmar gyaɗa masa kai tayi alamar eh “menene kunya? Yayi magana lokacin da yake mai da mata da hannun rigar ta girgiza masa kai tayi tana faɗin “nima ban sani ba” shiru yayi yana kallon face nata “ok open your eyes” slowly ta waro idon nata a kan kyakkyawar face nashi matso da face nashi yayi ya haɗe da nata kasa kasa yace “duk da ban san me ake nufi da kunya ba amma bana son ta as from today karki sake rufe mun ido idan muna tare” hannu ta sanya chikin gashin kan sa tana faɗin “to”

    “ash” ya furta lokacin da hannun ta ya sauka chikin gashin kan sa da sauri ta zame hannun ta dan kartaje ta ja masa wani abun da baya so chikin zafin nama ya haɗe bakin su waje guda tare da kama hannun ta ya mai da chikin gashin kan nasa,watsa gashin nasa ta fara yi tana shafa daga kansa zuwa wuyar sa “oh god” kawai yake furtawa ba karamin jin daɗi wasa da gashin sa da take yi yake ji ba kara kankame ta yayi sosai bakin sa na chikin nata yana kokarin zame mata rigan jikin ta ko me ya tuna sai ya fasa slowly ya zame bakin sa daga nata da kyar ya iya sauke ta kasa yana faɗin “muje mu shirya mu tafi ko? Faɗawa tayi saman kurjin sa ta zagayo da hannun ta ta bayan sa tare da kwantar da kan ta a saman faffaɗar kirjin sa tana faɗin “yau kam yaya Prince ba zaka ɗagani zuwa ɗaki bane? “Kin min nauyi ni ba zan iya ba” waro ido tayi waje tana faɗin “kai da kullun da hannu ɗaya kake ɗauka ta kamar yar baby shi ne yau zaka che nayi nauyi” ta karisa maganar kamar zatayi kuka girgiza kai kawai yayi yana danne zuciyar sa yana addu’ar Allah ya ba ni ikon chika mata alkawarin da na ɗauka mata amma gaskiya yarinyar nan tana mani abubuwa dayawa da baya so wayan da ban ma taɓa kwatan tasu ba a rayuwar ta duk yadda muke da Aryan ban taɓa ɗaukan 10mins ina magana da shi ba amma yarinyar nan ta tasani a gaba da tambayoyi da hira haka no dole na san ya zanyi da ita
    “Yaya Prince mu tafi mana” hannu ya sanya ya ɗauke ta chak ya saɓa ta a kafaɗar sa suka fice daga ɗakin yana saukowa palon ya chi karo da su Hisham Khalid Yusuf Ahmed Fahad da matayen su suna zaune a palon suna hira bai bi ta kansu ba ya nufi bedroom na shi yaya Khalid ne saurin chewa “Bgs bakaga Hisham bane? gaisheka fa yazo yi” ko kallon in da suke bai yi ba ya wuce chikin bedroom ɗin sa kallon juna suka fara yi Hisham yana son yin magana amma yana tsoro

    saman gado ya kwantar da ita ya wuce toilet chikin sauri ta miƙe ta wuce dressing room na shi ta fito masa da daddakiyar farar shadda mai bala’i kyau da tsada ta haɗo masa da hula fara tas mai kyau almost 5mins ta tsaya gaban glass na gera agogon sa tana tunani ta rasa wanne zata zaɓa masa daga karshe ta ɗauka masa wani dangareren agogon diamond mai matikar kyau da tsada ta fito ta ɗaura masa kayan saman gado ta koma dressing room ɗin ta ɗauko masa takalma mai bala’i kyau tsayuwa tayi ta zubawa takalmar ido mamaki take kafar yaya Prince ɗan karami kamar kafar mace sanya takamin tayi a kafar ta dai dai da ita kamar nata murmushi tayi ta chire ta ɗauko masa face mark ta fito ta ajiye masa takalmin kusa da gado ta ɗaura masa face mark da links a saman kayan sa ta wuce wajen trolley ɗin ta ta chire kayan jikin ta ta duba doguwar riga mai ɗan hankali ta sanya a jikin ta tana kokarin tara gashin kanta ta ɗaure sai jin hannun sa tayi saman gashin nata ya zame hannun ta ta saki gashin ya watse har bayan ta zuro hannun sa yayi ta kugun ta ya juyo da ita suna fuskantar juna kasa kasa yace “love your hair” murmushi ta ɗan yi kafin tace “to nabaka kyauta” shiru yayi ya sanya hannun sa ya fara tara mata gashin nata “yaya Prince daman ka iya ɗaure wa mutun gashi ne? “na iya ɗaure nawa dai yau shine first time dana fara ɗaure gashin da ba nawa ba ni idan ba Aryan bama ban taɓa taɓa gashin wani ba” ya kai karshen maganar dai dai lokacin da ya gama ɗaure mata gashin nata ya zuba mata jelar gashin a bayan ta ya zuba mata ido yana kallon face nata “you look so good” murmushi tayi tace “nagode to kai ma kaje ka shirya mana na” juyawa yayi ba tare da yayi magana ba kayan da ta ajiye masa ya ɗauka ya wuce dressing room

    jim kaɗan ya fito shirye chikin kayan da ta fitar masa “wow” shine abun da hiyana ta furtawa “tsarki ya kara tabbata ga Ubangiji da yayi wanna halittar yaya Prince kagan ka kuwa innalillahi ni na ma rasa me zance kai wlh kamar dan kai akayi kayan hausawa” harara ya watsa mata kafin yace “dan ke na sa kayan ai nasan idan nayi irin wannan shigar ba wan da zai yi tunanin nine bare su sawa mutane da nake tare da su ido” kwashawa tayi a guje ta faɗa jikin sa tana faɗin “nagode kuma bazan taɓa mantawa da wanna rana ba a rayuwa ta yau yaya Prince yayi abu saboda ni” shafa gashin kanta ya farayi yana faɗin “it’s ok tun da kinyi farinciki muje da wuri dan time ya tafi almost 12 yanzu kuma kinga zamuyi tafi anjima kaɗan” sakin sa tayi ta ɗago ido tana kallon sa “yaya Prince to ya baka sanya hulan ba? Ɗagata yayi ta ɗaurata saman gado ya juya mata baya yana faɗin “ɗaure min gashin nawa sai ki samin hulan mugani ko kin iya” duk da ya ɗaura ta saman gado sai da ta ɗaga kafa kafin ta iya ɗaure masa gashin kan na shi

    Tana gama ɗaure wa ta diro daga gadon ta shige dressing room nashi yana tsaye awajen har ta fito ta haye gadon tana faɗin “yaya Prince juyo na sanya maka hular” juyowa yayi ya ɗan sunkuyar da kansa kasa ta sanya masa hulan asalin kyan sa na fulani ya sake bayya
    face mark ta ɗauko ta sanya masa yana tsaye yana kallon ta yana mamaki da yaba mata a ransa tana da kyakkyawar zuciya sosai hannun sa ta kama ta ɗaura masa agogon
    shi dai yau gaba ɗaya mamakin kansa yake ji yake kamar ba shi ba yayi nisa chikin tunanin sai jin ɗan karamin bakin ta yayi saman kumatun sa hot sumbata ta bashi tana murmushin tace “muje to” bai san lokacin da ya rungumota ba yana faɗin “kina da kyan hali sosai” “yaya Prince ai daga wajen ka na koya” kallon gefen ido ya mata kafin yace “a yaushe kika koya awaje na? ɗaura dan yatsan ta tayi saman wuyar sa tana masa yawo da yatsan awajen ta fara magana “awajen Ammi na koya kenan kaga duk abun da Ammi take da shi mu dukkan mu yaran ta muna da shi” first time a rayuwar sa ya saki cool murmushi tare da ɗaukan ta chak ya nufi dressing room nashi da ita yau yana matikar farinciki sosai dan yana bala’i son Ammi duk wan da zai so Ammi to koda makiyin sane ba shakka zai zama masoyin sa

    Tsakiyar dressing room ɗin ya sauke ta ya buɗe glass na face mark nashi ya ɗauki ɗaya ya sanya mata ya ɗauko jaket nashi ya sanya mata har guiwa jaket ɗin ya tsaya mata kai kallon sa yayi kafar ta Booth nashi ya ɗauko tare da safa ya miƙa mata ya ɗauko rawanin wuya ya ɗaura mata ita dai Hiyana tana ganin idon Allah duk ya chika mata jiki da kaya duk da chewa hakan ya mata daɗi dan garin akoi sanyi sosai har safan hannu da kansa ya sama ta sak turawa ta dawo hannun ta ya ruke suka fito tsayuwa yayi a tsakiyar ɗakin ya saki hannun ta ɗago kai tayi tana kallon sa kai kallon sa yayi kan ta ba tare da yayi magana ba wucewa tayi ta ɗauko karamin hijabi a trolley ɗin ta ta sanya ta dawo ta rike hannun sa suka fice daga ɗakin

    har yanzu su Khalid suna palon wucewa yayi ba tare da yayi musu magana ba zame hannun ta tayi daga nashi ta tsugunna kasa ta fara gaishe da su yaya Khalid, Zahra na son yin magana tana tsoron yaya Prince dan yana tsaye a kofar part ɗin yaya Aiman miƙawa ilham matar Hisham tayi ta nufo Hiyana tana faɗin “wannan itache amaryan ogan naku? A sukwane su Khalid suka juya a tare suka bi bayan Bgs da kallo Ilham na kokarin kira musu ruwa yanzu ma da yaya aka samu ya sauko ita ko ilham sai surutu take “kai amma gaskiya ogan ku yayi sa’ar mata jiya na hangota a kitchen ai kafin na fito ta wuce sama kyakkyawa kamar ita tayi kanta gata shiru shiru gaskiya ya more mata” yana jin su amma bai tanka ba
    ɗago ta ilham tayi ta rungume ta ta chigaba da surutu “sai ki tsaya ki kula mana da oga da kyau dan kin ga….bata kai karshen maganar ba bgs ya dakawa hiyana tsawa “ni dan ki ne da zaki bar ni a tsaye!!” ba shiri Ilham ta sake ta tana kallon Bgs bata taɓa tunanin haka ogan nasu yake ba sarkin tsoro jikin ta har rawa yake da sauri ta koma kusa da Hisham ta zauna

    juyawa Hiyana tayi chikin taku katsaita ta nufesa dan yanzu kwata kwata ta dai na tsoron tsawar sa dan tasan ba zai bugeta ba hannun sa ta kama tana faɗin “muje” jawota gaban sa yayi da karfi a zuciye ya buɗe baki zai yi magana sai kuma ya fasa ya yarfar da hannun sa gefe ya fisgi hannun ta suka bi ta part ɗin Aiman mamaki Hiyana take ina zai kai su bata gama mamaki ba taga ya buɗe wata kofa kamar kofar sirri ta kofar suka shiga sai gasu sun fito ta wajen parking motacin su dan dankareriyar Mercedes-Benz baka ya shiga gidan gaba ma zaunin driver da sauri ta buɗe ɗayan gefen ta shigo gaba ta zauna tayar da motar yayi suka fita ta ɗayan gete ɗin gidan ba tare da sojojin sa sun sani ba dan fitar sirri sukayi.

    sai da su Khalid sukaji fitar motar su sannan suka sauke ajiyar zuchiya a tare kallon Ilham Hisham yayi ya fara magana “my wife wlh duk abun da zakiyi a gidan nan karki kuskura hanya ta haɗa ki da Bgs idan ba haka ba….bai kai ƙarshen maganar ba ta rufe masa baki da hannun ta tana faɗin “ba ma sai ka faɗa min ba ido na ya gane mi tun da ya fito na lura gaba ɗayan ku kun nitsu ba wanda ya iya yi masa magana a chikin ku har kannen nasa shiya sanya nima ban masa magana ba nayiwa matar sa kawai gaskiya yana da zafin rai sosai” “hmmmmm amaryan mu kenan ke dai Allah ya raba ki da haɗuwa da Bgs” chewar Khalid Yusuf ne ya an sa zanchen da chewa “yaya Khalid amma da alama yaya Prince ya sauko fa kaga ya fara fitan sirri da sister” girgiza kai kawai Khalid yayi ya miƙe ya kama hannun Zahra yana faɗin “muma mun fita yawo sai 3:30 zamu dawo tun da sai 4 jirgin mu zai ɗaga a tare su Hisham da su yaya Yusuf suka miƙe kowa ya riƙe hannun matar sa suka bar palon.

    Tuki yake chikin kwanchiyar hankali ba wan da yayi wa ɗan uwan sa magana bakin wani katafaren gidan abinci yayi parkin motar sa ya fito ya nufi chiki
    chikin sauri itama ta buɗe motar ta fito tabi bayan sa zama yayi saman haɗaɗiyar kujeran da akaware a ɗaki na musamman kusa da shi ta zauna tana bin wajen da kallo “yaya Prince amma a nan wajen akoi abincin musulmai kuwa dan naga duk kan su turawa ne kuma basuyi kama da musulmai ba” kallon wajen yayi ta kasar idon sa mutun hudu ne a chikin ɗakin kowannen su da matar sa dawo da kallon sa yayi kan ta yana kokarin yin magana mai an san order ya zo takeaway yace a musu dan ba yaso su chire face mark na face nasu baya son kowa ya gane su shi ya sanya ya saka kayan hausawa tun da nan ba wan da ya taɓa ganin sa da kayan hausawa zai yi wuya a gane sa

    Bayan an kawo kusu takeaway hiyana ta ansa suka fice daga wajen suka koma mota chikin daji ya nufa da su yana tuki chikin kwanchiyar hankali
    bakin wani katon dutse mai dubar da ruwa yayi parking na motar ya fito ya zauna saman bayan motar fitowa tayi itama bin wajen ta farayi da kallon wow wajen ha haɗu iya haɗuwa wajen kewaye yake da dogayen furanni masu kyau launin fari da kuma yellow daga gefe katon dutsene wadda ruwa ke zuba daga chikin sa kamar faffo yana taruwa akansa kamar rafi ga dogayen bishiyoyi koraye shar shar kewaye da dutsen wajen shiru baka jin kokai sai sautin kukan tsuntsaye
    dawo da kallon ta tayi kansa ya chire face mark nashi ya ajiye a gefe yana kallon ta “yaya Prince wajen nan yana da kyau sosai” shiru yayi yana kallon bai yi magana ba takawa tayi a hankali ta karisa wajen dutse dake zubar da ruwa hannu ta sanya ta tara ruwar da mamakin ta sai ta ji ruwan da zafi kamar an sa a wuta kasa kasa taji sexy voice nashi yana faɗin “yinwa nake ji” da sauri ta juyo ta dawo wajen motar ta ɗauko musu abinchi ta kawo masa dirowa kasa yayi daga saman motar ya ɗauke ta chak ya ɗaurata saman bayan motar kafin shima ya haura ya zauna a tare suka chi abincin gwanin ban sha’awa sosai yau Bgs yaci abinci har mamaki hiyana keyi bata taɓa ganin sa yaci abinci mai yawan wanna ba suna gama chi ta diro kasa ta kwashe kayan abincin ta zubar ta koma wajen dutse ta tsaya tana kallon ruwan ta zubawa tsuntsayen dake zuwa shan ruwan awajen ido ji take kamar ta shiga ruwan tayi wanka tayi nisa chikin tunanin sai jin sa tayi ya rungumota ta baya ya kwantar da kan sa saman kafaɗarta ya zuro hannun sa saman kugun ta kasa kasa yace “zaki shiga ruwan ne?” Hannu ta ta ɗaura saman hannun sa dake kan kugun ta tana shafawa chikin shagwaɓa tace “eh zan shiga kai ma zaka shgane? Juyo da ita yayi suna fuskantar juna “ba yadda zan yi in shaga chikin ruwan nan da kayan jiki na ɗin nan” kallon sa tayi da kyau kwafa tayi a ranta tace zaka shigane ma ai na san me zan maka sakin sa tayi ta faɗa chikin ruwan tare da sakin ihu dan duk tunanin ta ruwan dake taruwa a kasan dutse bai da zurfi sai ta ji akansin haka dumin kuwa ruwan ya haɗiye ta gaba ɗaya gashi bata iya ruwa ba diyana ta fita iyawa ko a garin su ita bata shiga rafi diyana ce mai shiga yana tsaye yana kallon yadda take shan ruwa sai mulewa kasa take tana ɗagowa sama sai da ya barta ta jigata sannan ya chire agogon hannun sa da wayar sa tare da hulan kan sa ya ajiye ya faɗa chikin ruwan kamota yayi ya daurata saman kirjin sa yana kallon face nata langwaɓar da kai tayi a kafaɗar sa tana jan numfashi “kin kyau ta da kika jika mu yanzu dame zamu koma gida? Kankame sa tayi ta kasa magana domin tasha ruwa sosai takawa yayi zuwa in da ruwan ke zuba kamar fanfo ya tsaya a dai dai wajen, ruwan na zubo musu daga kai “har yanzu baki dawo dai dai ba kenan? Sai lokacin ta ɗago kai da kyar ta iya chewa “yaya Prince dan Allah ka fitar da Ni” matso da face nashi yayi dab da nata “no ai tun da kika sani na shigo ruwan nan tofa sai ki shirya ɗaukan duk abun da zan yi” chizon sa tayi a saman lallausan lips nashi chikin shagwaɓa tace “yaya Prince wlh bana numfashi sosai ka fitar da ni daga ruwan nan kar na mutu” lasan lips nashi in da ta chijesa yayi kafin yace “kina so kenan” bai jira amsar ta ba ya haɗe bakin su waje guda ga ruwa na zuba musu daga kai yana jikasu almost 10mins suna haka kafin ya zame bakin sa daga nata yana kallon face nata yana kokarin yin magana wayar sa ta fara ringing kai kallon sa in da ya ajiye wayar yayi kafin ya dawo da kallon sa kanta gaba ɗaya ta jiggata da kyar take iya buɗe ido zame mata ɗan karamin hijabin kan ta yayi ya shiga watsa mata gashin kan ta ruwa na jika gashin kwantar da kanta tayi saman kafaɗar sa tana numfashi da kyar da kyar juyo da face na shi yayi yana kallon ta wani irin yanayi mai daɗi da annashuwa ke ratsa shi ya shagala da kallon ta bai ankara ba sai ji yayi tana kokarin sume masa a sukwane ya juya da ita ya fice daga chikin ruwan wajen motar su ya koma ya jinkina da jikin motar ya fara kiran sunan ta kasa kasa “Sister sister” da kyar ta iya waro idon ta da suka sauya daga blue zuwa jaa sosai,waro ido yayi yana kallon ta bai ɗauka ta jigata haka ba ta sha ruwa sosai buɗe gidan baya na motar yayi ya kwantar da ita dukkan su sai ɗigan ruwa suke

    guntun tsaki yaja ya koma wajen da ya ajiye wayar sa ya dauko tare da agogon sa ya dawo kusa da ita kunna wayar yayi ya shiga latsawa da alama wani sakon yake turawa bayan ya gama ya duba miss call Aryan ne ya kira shi,kiran layin Aryan ɗin yayi bugu ɗaya Aryan ya ɗaga manna wayar tayi a kunnen sa daga ɗayan ɓangaren Aryan yace “blood ina ka bar wayar? Tsaki yaja kafin tace “menene?” “Na gama aikin da ka sani yanzu shigowar ka kawai nake jira amma akoi wata yar matsala” “matsalar me? “Har yanzu bai iya gane ɗan leken asirin dake chikin muba na binciki sojojin mu dukka ban samu ba” “No karka damu da wanan ni dai nace maka karka yarda da kowa idan na shigo zan kama koma wanenne yanzu dai zamuyi waya anjima yanzu akoi abun da nake” “ok to ina sister na take? Juyowa yayi yana kallon ta da kyar da kyar take numfashi sai rawan sanyi take “ban san in da take ba” dariya Aryan yayi kafin tace “amma Bgs kai fa ɗan duniya ne ka gama yiwa yar mutane mugun ta jiya instead of yau ka zauna ka bata kulawa amma sai kayi fitar ka ko? Allah dai yana kallon ka…bai bari Aryan ya gama maganar sa ba ya katse kiran yana kallon ta kawar da kansa gefe yayi yana ɗan jan tsaki ajiye wayar yayi chikin motar ya harɗe hannun sa ya kirji yana kallon sama kamar mai tunani

    Almost 10mins suna haka sai ga Abdol ya danno hanchin motar sa wajen kusa motar su yayi parking sanna ya fito chikin sauri hannun sa rike da jaka mikawa Bgs jakar yayi sanna ya shiga motar sa ya juya ya koma buɗe jakar Bgs yayi ya fito da duguwar riga abaya ce baki kayan jikin ta ya fara chire mata sauri sauri ya sauya mata doguwar rigar sai rawan sanyi take yana kokarin chire nashi kayan yar karamar nauran dake gaban motar sa ta fara kara chikin sauri ya fasa chire kayar na shi ya rufe kofar baya na motar ya buɗe gidan gaba ya shiga ya kunna motar da gudun gaske ya bar wajen kai tsaye gida ya wuce dan sai rawan sanyi hiyana ke yi shi kan shi kayan jikin sa sun takura masa

    Yana shiga gida bai ɓata lokacin ba ya fito ya ɗauke ta chak ya shiga chikin gida kai tsaye bedroom nasu ya wuce saman gado ya shinfiɗe ta ya wuce toilet wanka yayi da ruwa mai zafi sosai ya fito ya shirya chikin kayan sanyi dan shima daɗewar da jikakken kayan sukayi a jikin sa ya sanya yana jin zazzaɓi kayan sanyin sa ya ɗauko mata tare da safa da hula ya sanya mata tana kwance tayi shiru sosai ya shirya ta chikin kayan sanyin sa ganin har yanzu sai rawan sanyi take ya sanya ya kunna na’uran ɗumama ɗaki ya jona hand dryer da kansa ya busar mata da gashin kanta bayan ya gama komai ya duba time 2pm alwala yayi ya fito ya gabatar da sallah ya miƙe ya hauro saman gadon duba time ya sake yi 3pm saura 1h jirgin su ya ɗaga kwamciya yayi saman gadon ya jawota jikin sa ya jawo bargo mai laushi ya rufesu sosai ta shige jikin sa tana shan ɗumin jikin sa kasa kasa da murya kamar mai raɗa yace “sister are you okay now?” gyaɗa masa kai tayi alamar eh shafa kan ta ya fara yi suka yi shiru kowa da abun da yake tunani

    To masu karatu sai mun haɗe gobe a Naija zamuga ya wasan zata kaya akoi fa shagali akoi sharholiya yanzu zaa fara buga asalin game ɗin mu damalmale da ku gobe zamuga wazaiyi winning 💃💃

    💖The talent troupe writer’s 💖

     

    💋Duk Karfin Izzata 💋29

    By Star Lady

     

     

  • Arubuce Ta Ke 9

    Page 09

    Suna tafe a hanya uncle muhsin din yana janta da hira,ta saki jiki sosai sunata hirarsu da yake abokin hirarta ne dama,a nan ya fahimci interest dinta itama game da karatu,da yadda take da kaifin basira,tun suna hirar har suka gaji kowa yayi shuru,saita maida hankalinta ga kallon titi da yadda suke wuce dazuzzuka,can qasan ranta ta dinga jin wata kewa tana shigarta,zuciyarta ta karye,suna dada yiwa kano nisa.

    Tun tana iya bin hanya da kallo har baccin ya soma fusgarta,babu jimawa kuwa yayi awon gaba da ita,ta saki jiki sosai tana barcinta abinta.

    Bata tashi farkawa ba sai da uncle muhsin ya iso qofar gidanshi ya tsaya yana jiran mai gadi ya bude masa qofa,idanunta ta bude a hankali tana murzasu hadi da budesu da kyau tana qarewa wajen kallo.

    Tun a sannan tasan ta shigo baqunta,ta kuma shigo sabon waje,quaters ne dake da qarancin jama’a tare da qarancin gine gine,saidai kuma duka manyan gidaje ne ta wajen,tana nan zaune har ya buda gate din gidan ya dawo ya shigar da motar.

    Sanda ya kashe motar waiwayo yayi yana tsokanarta

    “Yar qauyen kano yau gata a bauchi” kasa magana tayi saboda kewar ummu data fara shigarta,sai murmushi kawai data saki,dai dai nan matar gidan ta iso.

    “Kai kai kai…..abba wa nake gani haka?” Ta fada tana dariya gami da murza bdanunta,saboda baice mata da widad din zasu taho ba

    “Wa idanunki suka gani?” Shima ya fada yana dariyar

    “Tabdi,wai Allah na,anya kuwa ba gizo idanuwa kemin ba?”

    “Shafa kiji dai” ya sake fada yana dariya gami da qoqarin fitowa daga motar yana duban widad din

    “Fito mu shiga ciki” yace da ita yana fita daga motar

    “Gaskiya na ciri tuta,abba wacce irin addu’a ne ka yiwa ummu ta baka widad?” Ta sake fada tana karbar jakar hannun widad din tare da sake bude mata qofar motar sosai.

    Tare suka jera zuwa ciki hadiyya matar uncle muhsin da yaranta ke kira hajjaa nata mamakin zuwan widad din

    “Saurin me kike ne?,zakiji komai fa” cewar uncle muhsin.

    Tunda suka shiga falon gidan ta gane yaran gidan basa nan,da yake ranar makaranta ce,har dakin yaran hajjaa ta rakata sannan tace da ita

    “Ki alwala ki sallah,ki shiga kitchen da abinci ki diba kici,su nujood din sun kusa dawowa,yanzun nan zaki gansu” a nan dakin ta barta ta koma wajen mijinta.

    Tun bai gama kintsawa ba ta sashi a gaba,yana shiryawar yana bata labarin dalilin tahowa da widad din,gyara zamanta tayi tana sauke ajiyar zuciya

    “Gaskiya abba gwara daka taho da ita,duka duka nawa take da za’a dameta da batun aur,baya ga haka ma naga ko yayyen nata da aka yiwa auren duka sun fita datawa,tunda a qalla suna kaiwa sha bakwai sha takwas,sai ita tun tana ‘yar sha hudu?”

    “Nafi tunanin farinjinin da yaaya yaga tana da shi ne fiye dana ‘yan uwanta ya daga masa hankali yakeso yayi ya kawar da ita,amma gaskiya ni dama nafi mata sha’awar karatu,da zan samu ummu tabarmin ita karatunta zatayi sosai”

    “Gaskiya dai abba,Allah yasa ummu ta bari”

    “Ba tabbas” ya amsa mata yana zura jallabiyyarsa

    “Ki dauko system dita ki sakamin ita a charge,nabar ayyuka da yawa ban kammala ba,inaso na rage kafin gobe” ta amsa masa da to tana miqewa,shi kuma yana fita don zuwa masallaci sallar azahar.

    Hankalinta duka yana kan widad tunda ta barta a dakinsu nujood,widad din ba baquwarta bace,tasan yadda take da wahalar sabo da rashin sakin jiki,qilan yanzun tana can zaune a takure,kamar yadda ta zata kuwa haka ta sameta,tayi sallar dai amma tana zaune,cikin dariya tace

    “Anya widad za’a zauna mana a bauchin nan kuwa?,taso muje kuci abinci kafin su qaraso,yau sunyi delay ma,Allah yasa ba school bus din tasu ce ta sake basu matsala ba,don haka tayi musu jiya”.

    Tare suka fito tana biye da ita,a falo suka samu uncle muhsin din,shima shirin cin abincin yake,sai hajjaa ta zuba musu tare,tana daga gefe suna hirar kano da uncle muhsin din,jifa jifa suna sanya widad,har ta fara sakin jiki,da yake daga uncle din har hajjaa mutanenta ne.

    Basu ko kai ga gama cin abincin ba sukaji ana taba gate din gidan

    “Tohm,ga ‘yan makaranta nan”Hajjaa ta fada hayaniyarsu na ratsowa falon tun kafin sukai ga qarasowa.

    Tsam widad ta dauke hannunta daga plate din abincin cikin hanzari,kafin sukai ga qarasowa ita ta fita suka hade a farfajiyar gidan.

    Cikin murna nujood ta riqeta tana ta ihun murna kamar wadanda wani abu ya sama,banda uncle muhsin sun san abinda ke faruwa babu abinda zai hanasu tsorata,amma sai ya kada kai yana murmushi

    “Allah ya shirya,kamar basusan sun fara girma ba”

    “Banda abun abba ina hankali a nan,ai saidai aikin quruciya”.

    A nan falo ranar aka wurgarwa da hajjaa kaya da jakar makaranta,sauqinta daya ranar babu islamiyya ta tabbatar da babu abinda zasu,baga nujood din kawai ba,har duka sauran ‘yan uwanta sunji dadin zuwan widad din.

    Cikin kwanakin da basu da yawa taji ta qagu ta koma wajen ummunta,duk da cewa gidan yana mata dadi amma sam batason garin,hakanan take,ta fiya baqunta da rashin saurin sabo,abu daya ne yake sanyawa taji komawar ta fitar mata a ka,batun ma’aruf da kuma mahfood da taji rannan uncle muhsin suna zancan da hajjaa hadiyya sunayi cewar har yanzun bai haqura ba,yace idan Allah yayi rabonsa ce shikenan.

    Zumbura baki tayi gaba ba tare data baiwa zancan muhimmanci ba,duk da qarancin shekarunta amma ta fuskanci zallar nacin da mahfood ke dashi,ta rasa da wanne suna ya dace ta kirashi,takan kirashi da maye a ranta,taja tsaki ta dauki marker din zanen da tazo dauka suna wani zane ita da nujood ta fice zuwa farfajiyar gidan inda suka sanya kujeru suka zauna.

    *******
    Baqar mota ce wuluk qirar BMW take ratsawa a hankali ta saman titin,daga cikinta tana dauke ne da mutane uku,dukkansu sanye suke da police uniform (kakin d’an sanda,matuqin motar akkauran dan sanda ne baqi dake hakimce a mazaunin driver yana sarrafa sitiyarin motar cike da qwarewa,yayin da wanda ke zaune a gefansa ya kasance siriri sosai,hakanan kuma dogo ne,duk da cewa a zaune yake zaka fahimci hakan.

    Na ukun nasu kuwa yana zaune daga bayan motar,tashin farko zaka iya kiranshi da matashi,don duka duka shekarunsa na haihuwa ba zasu haura talatin da biyar ba,mara hasken fata ne da zaka iya kiransa sa chocolate color,irin fatar dake da tsada da kuma daukan hankali,saboda yadda take a kwance kadai zai nuna maka zallar jin dadin da ma’abocin fatar ke samu.

    Yana da matsakaicin tsaho,wanda inda ace siriri ne kai tsaye zaka iya kiransa da dogo,saidai murjewar jikinsa ta shanye tsahon nasa ta sanyashi a sahun matsaikatan maza,manyan idanu gareshi masu daukan hankali,girmansu bai hanasu lumshewa ba a duk sanda yaso hakan,kamar yadda yake da wasu irin lips kai kace na mace ne.

    Sosai uniform din suka zauna masa a jiki,kai kace saboda jikin nasa aka qerasu,qafafunsa da yayi crossing nasu socks ce kawai,boots dinsa na aje gefan qafafun nasa.

    Duk da hirarrakin da mutum biyun dake gaban motar sukeyi shi sam ko sau daya bai tsoma musu baki ba,hasalima tafin hannunsa ne shimfide saman fuskarsa kamar mai wani tunani,abinda kuma zai iya hanaka ganin ainihin fuskar tasa sosai kenan,sai kyakkyawan agogon Rolex dake daure a tsintsiyar hannunsa.

    Yanayin zaman da yayi kamar na mutumin daya gaji tubus,sam zaka zaci baya cikin motar ne,duk da hirar da sukeyi din ta shafi aikinsu,dukansu cikin zuciyoyinsu suna muradin ya sanya baki,saidai sunsan abune mawuyaci,shi yasa cikinsu ma babu wanda ya sanya rai da hakan suka ci gaba da hirarsu ba tare da sun daga sauti yadda zasu dameshi ba.

    Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke yana zame hannun nasa daga saman fuskar tasa,kyakkyawar zagayayyar fuskarsa dake cike da wani irin kwarjini gami da haiba ta bayyana,ya dan bude idanunsa kadan da nauyin gajiya ya cikasu.

    “Samuel” ya furta cikin muryarsa dake da kauri da nauyi

    “Yes sir” mamallakin sunan wanda shike tuqin motar ya amsa a ladabce

    “Ka saukeni gidan hajiya tukunna”

    “Consider it done sir” ya sake amsa masa cikin nuna qarfin bin umarnin sa.

    Kafin wani a cikinsu ya sake cewa wani abu wayar dake tsakanin seat din gaba guda biyu ta dauki tsuwwa,mutumin dake zaune a kujerar dake zaman banza ne ya miqa hannu yana dubawa,kana yadan waiwayo kadan dai dai sanda yake qoqarin maida boot din qafarsa

    “Sir,dan jaridar nan ne” shuru kamar bazai amsa ba,da alama ba ma’abocin son magana bane,sai kuma yace

    “Ka katse kiran ka tura masa saqo,gobe qarfe biyu su sameni a zone one”

    “Yes sir” shima ya amsa yana juyawa cikin qoqarin idar da umarninsa.

    Dai dai sanda ya gama sanya takalman yana gyara zamansa motar ta soma gangarawa cikin unguwarsu,sai ya juya gefansa yana daukar tarkacensa dake zube akan seat din gami da maida hularsa saman kansa yana dakon motar ta isa qofar gidan.

    *ZAFAFA BIYAR 2023*

    IDON NERA Mamuhghee

    KI KULANI miss xoxo

    A RUBUCE TAKE Huguma

    RUMBUN K’AYA Hafsat rano

    DAUDAR GORA Billynabdul

    Account number

    0022419171
    Maryam sani
    Access bank

    Saiki tura shaidar biyanki ga
    09033181070

    VTU OR MTN RECHARGE CARD
    09166221261

    AL’UMMAR NIJER SU TUNTUBI WANNAN NUMBER

    +227 90 16 59 91

    Thanks for choosing us*H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • Duk Karfin Izzata Book 2 Page 33

    Duk Karfin Izzata Book 2 Page 33

    Page 33

     

    Kurawa alluran ido yayi kamar mai tunanin wani abun,abun da mamaki gasu dai alluran da ya saba yi ne,5mins ya ɗauka yana kallon alluran kafin ya ajiye ya fito da kayan test yana kokarin jan jinin jikin sa domin ya tabbatar wa kan wani allurane ya shiga jinin jikin nashi,sai jin hiyana yayi ta kwanta a bayan sa tana faɗin “yaya Prince ni dan Allah kasa a….bata kai karshen maganar ba ya fisgota da karfi ya dawo da ita ta gaban sa rai a matukar ɓace yace “idan kika kuskura kika sake kusan tata ran ki yayi dubu sai na ɓata miki get out!!” ya kai karshen maganar tare da sakin ta,da gudu ta ɗauki wayar ta dake gefen gado ta fice daga ɗakin.

    Tana fita ta kira layin Aryan bugu ɗaya ya ɗauka manna wayar tayi a kunnen ta cikin sauri tace “yaya Aryan ba zan iya ba nayi kamar yadda ka rubuta min a massage nayi kokarin shashantar da shi karya gane amma yace na fice masa a ɗaki” daga ɗayan ɓangaren Aryan yace “me yake yi yanzu? “Gwada kan sa yake yana son tantance wani allura yayiwa kan sa dan naga ya nemi kwalban alluran da yayi ɗazun ɗin bai gani ba” dogon numfashi Aryan yaja tare da sauke nauyayyar ajiyar zuciya kafin yaci gaba da magana “ni na dauke kwalbar alluran bayan na ɗauke ne na dawo masa da alluran sa na asali dan nasan zai iya zuwa ya bincika na manta cewa bgs ya wuce nan yanzu wlh nasan idan ya gane ba mai kwatata sai Allah kuma tun da ya fara bincike a kai sai ya gane bana son ki shiga case ɗin nan dan haka ki goge duk wani text dana tura miki kiyi kamar baki san komai ba sanna karki yarda yau ki kara haɗuwa da shi zan sa Ammi ta bashi umarnin a ɗauko ki a kawo ki hospital sai yamma zaki koma gida” murya na rawa ta fara magana “yaya Aryan ni fa ina tsoron in ga kuna samun matsala da yaya Prince saboda ni ba na son ganin hakan” “karki damu da hakan ke dai kije ki shirya da wuri yanzun nan Shahram zai kawo ki nan dan ban son ki zauna kusa da shi yau za’a iya samun matsala dan ina da tabbacin yana cikin matsanancin ɓacin rai” “to” kawai tace tare da ciro wayar daga kunnen ta ta katse kiran cikin sauri ta karisa Part ɗin Ammi gudu gudu ta shirya tana fitowa ta duba time 1:30pm komawa tayi ta ɗauro alwala ta gabatar da sallar azhar sanna ta kira Aryan ta sanar masa ta gama shiri umarni ya bata akan ta fito Shahram ya kawo ta idan ya kawo ta sai suce Ammi ce tace a ɗauko ta idan Bgs ya tambaya haka ko akayi Shahram ya kai ta asibiti tana shiga ta samu yaya Aryan a wajen parking space yana jiran ta a tare suka wuce ɗakin da su diyana ke kwance.

    Ammi da Ummi suna zaune saman sofa dake cikin ɗakin suna yar hira gefen gadon da diyana ke kwance ta zauna ta zuba mata ido har wani hasken wahala ta kara ta shagala da kallon diyana sai ganin hannun ta na motsi tayi cikin sauri ta miƙe tsaye tana faɗin “yaya Aryan tana motsi” a tare suka kariso wajen shi da su Ammi. zuba mata ido sukayi suna kallon ta tun bata buɗe ido ba ta fara sambatu “bana son ka yaya Aryan mugu azzalumi….hiyana bata bari ta karisa maganar ba ta rufe mata baki tana faɗin “diyana!!ki buɗe idon ki kinsan me kike faɗe kuwa? da karfi ta waro manya manyan idon ta waje wadda sukayi ja sosai suka kumbura kyakkyawar fiskar hiyana ta fara cin karo da shi ganin ta ɗan nitsu ne ya sanya hiyana ta zame hannun ta daga kan bakin ta kamar jira take ba tare da ta lura da su Ammi ba ta fara surutu “hiyana wlh yaya Aryan mugune azzalumi kuma….sake rufe mata baki hiyana tayi tana girgiza mata kai “diyana koma me yaya Aryan ya miki bai kama ta kice masa mugu ba wato kin manta karatun da na koya miki ko ba’a zagin miji kome zai miki kici gaba da hakuri Allah na kallon ku kuma da ki cuci mujin ki gara shi ya cuce ki karki kara zagin yaya Aryan zaki shiga wuta wato ke duk karatun ma da na ke koya miki bakya ɗauka ko?” ta kai karshen maganar tana zama kusa da ita sai lokacin diyana ta ga su Ammi dake tsaye ta bayan hiyana “kuka ta saki tana kallon Ammi tana faɗin “Ammi dan Allah ki mai dani wajen Aunty farida”jiki ba kwari Aryan ya juya ya fice daga ɗakin yana godewa Allah da sanya hiyana ta rufe masa bakin diyana ba dan haka ba ai da ta kwanto masa ruwa

    Zama Ammi tayi kusa da ita tare da riko hannun ta cikin nitsuwa ta fara bata hakuri da nasiha mai ratsa jiki da kyar suka samu diyana ta hakura ta dai na kuka amma ta kafe akan bata son yaya Aryan sai dai ya sake ta bazata zauna da shi ba su Ammi basu da zaɓi dole su yardan mata akan yaya Aryan zai sake ta sai a mai data gidan Aunty farida da haka suka samu tayi shiru. ganin ta hakura tayi shirune ya sanya hiyana ta miƙe tabi bayan yaya Aryan

    Chan ta hangosa zaune saman kujera kusa da shi taje ta zauna tana faɗin “sannu da hutawa yaya Aryan” ba tare da ya kalle ta ba ya fara magana “yau na kwanto kura nayi abun da ban taɓa yi ba ina da tabbacin idan Bgs ya gane alluran da na sanya mishi idan ba Ammi ba ba wanda zai iya tare wanna rikicin ban taɓa tunanin Bgs zai gane alluran nan ba domin dana canza alluran bayan yayi wa kan sa na dawo na ɗauki wayan da na sa masa na mayar masa da na asalin na shi na ajiye dan in yazo ya ga masu kyau ɗin ne na ɗauki guda ɗaya na fasa na zubar da ruwan na ajiye masa kwalbar a dustbins domin idan yazo bincika wan da yayi wa kan sa ya ga kwalbar ban taɓa tunanin jinin jikin sa zai bincika ba hmmmmm akoi kura” “to yaya Aryan wani allurane wanna ka sa masa yayi da har kake ganin idan ya gane akoi matsala?” dogon numfashi yaja tare da sauke ajiyar kafin yace “hmmmmm sister ba zaki gane allun ba ke dai bari na ɗan miki example idan kayiwa kan ka wanna alluran to ko kayi wancan da Bgs yake bazata maka amfani ba shi ya sanya nake tsoron rikicin da zamuyi da shi yau” “to amma yaya Aryan daman wani irin allura yaya Prince yake wa kan sa ne? sai lokacin ya ɗago ya kalle ta chanza topic ɗin hiran yayi da cewa “ya jikin my jidda ta dai na kukan ne? gyaɗa masa kai tayi kafin tace “eh ta dai na kuka” miƙewa tayi yana faɗin “bari na duba ta” miƙewa ita ma tayi suka jera zuwa cikin ɗakin.

    Diyana na ganin Aryan ta fasa ihu tayi wurgi da cup ɗin tea dake hannun ta ta runtse ido tana faɗin “bana son sake ganin wanna mutumin Ammi kice ya fita wlh ban son sa” chikin tsawa Ammi tace “ke diyana kina da hankali kuwa? “aa Ammi kar ki mata tsawa zan fita pls ku bita a hankali” yana kai karshen maganar ya fice daga ɗakin, girgiza kai hiyana take tana mamakin hali irin na diyana kamar ba yanzu aka gama yiwa yarinyar nan natsiha ba.

    Bin bayan Aryan Ammi tayi tsaye a bakin kofa ta same sa ya dafe kai yana tunanin yadda zai yi da bgs zama sukayi da Ammi a kujerar dake wajen suna ɗan tattaunawa akan ya zasuyi da diyana.

    4pm Aryan ya umurci dr John akan su rubuta masa takardan sallama zaa cikaba da kula da ita a gida,ba musu dr John ya rubuta musu sallama ba tare da ɓata lokacin ba suka bar hospital ɗin sukayi gida

    Suna isa Aryan ya raɗawa hiyana akan taje ta ɓuya karta bari su haɗu da bgs yana gama faɗa mata hakan ya nufi part na shi bayan ya kai diyana part ɗin Ammi, part ɗin Ummi hiyana ta nufa ta shige ɗakin Aunty farida ta kwanta Ummi da Ammi kowa tayi part nata.

    Aryan na shiga part na shi ya wuce toilet jim kaɗan ya fito ɗaure da towel a kugun sa gaban mirror ya tsaya ya fara gyaran lallausan bakin gashin kan sa,waro manya manyan idon sa waje yayi ganin green eyes ta cikin mirror na kallon sa a sukwane ya juyo yana kallon bgs dake tsaye a bakin kofar shigowa fuskar nan tasa tamkar an aiko masa da sakon mutuwa waskewa Aryan yayi da cewa “my blood lfy na gan ka a awanna yana yin?” Shiru yayi kamar bai ji me Aryan yace ba wajen sau uku Aryan na mai mai ta tanbaya ɗaya amma shiru bgs bai yi magana ba,da Aryan ya ga dai da niyar magana sai ya juya ya cigaba da gyaran gashin kan sa zuciyar sa na dukan uku uku addu’a yake a ran Allah ya raba da bgs lfy

    “Me ya sanya ka chanza min allura Aryan?” Slowly ya juyo cikin dakiyar zuciya yace “wani allura kuma bgs?” ɗaure fuska sosai bgs ya karayi kafin ya fara magana “gaba ɗaya gidan nan babu wanda yake da,dakiyar zuciyar da zai iya shiga ɗaki na ya chanzawa tsinke wajen zaman sa ba tare da izinina ba sai kai akan wani dalili kamin hakan?” ajiyar zuciya Aryan ya sauke kafin yace “ba lalli ni ɗin bane domin bayan ni Abba zai iya shiga part naka yayi abun da yake so” takowa yayi zuwa gaban Aryan a zafafe ya sanya hannu ya danki wuyar Aryan ɗin ya shake sa,zuba masa ido Aryan yayi batare da yayi koda motsi ba ko wani yunkuri na kwace kan sa “ka kashe Cameran ɗaki na karfe 07:07 after 5mins kasake kunna cameran sanna ka dawo karfe 9am ka sake kashe Cameran after 5mins again kasake kunnawa me kayi bayan kashe kashen Cameran nan da kayi?” Shiru Aryan yayi ya kasa magana dan shakan da bgs ya masa zubawa juna ido sukayi ba ko kyaftawa. lokacin guda idan Aryan ya fara ruwa ya canza kala zuwa ja saboda shakan da bgs ya masa ba,ganin hakan ya sanya bgs saurin zame hannun sa daga wuyar Aryan ɗin yana kawar da kai gefe cikin kasalalliyar murya Aryan ya fara magana “me yasa ka ɗauke hannun ka? ai da ka barshi kawai in dai zaka iya yiwa sister abun da kake mata to nima zaka iya shakeni na mutu har lahira ka huta” a fusace bgs ya juyo da niyar ya damki Aryan karan wayar sa ya katse su dogon tsaki yaja tare da fito da wayar daga aljihun wandon jeans ɗin jikin sa dadyn Junior shine sunan da ya bayyana akan screen ɗin wayar guntun tsaki ya kuma ja kafin yayi picking call ɗin tare da sanya wayar a H-free yana faɗin “hello” daga ɗayan ɓangaren dadyn Junior ya fara magana a birkice “hello bgs yanzun nan farida ta yanke jiki ta faɗin muna hanyar hospital” waro ido waje bgs yayi da sauri yace “daman bata da lfy ne? Amma ɗazun na ganta lfylou ai” anshe wayar Aryan yayi daga hannun sa yana faɗin “kuyi sauri karisawa asibiti da ita da safe zamuyi sammakon zuwa pls abata kulawa sosai” anshe wayar bgs yayi yace “No karku kai ta hospital ku mai da ta gida a kira likitoci su bata kulawa karfe 7 gobe zamu shigo” yana kai karshen maganar ya katse kiran ya juya chikin sauri ya bar ɗakin ajiyar zuciya Aryan ya sauke yana faɗin Alhamdulila Alhamdulila ko ba komai yau dadyn Junior ka taimake Ni juyawa yayi ya cigaba da gyara gashin kan sa.

    9pm ta gama komai ta shirya cikin kayan barci tana kwance saman gadon Aunty farida a ɓangaren Ummi tana buga game a wayar ta sai murmushi take. Lokacin guda taji gaba ɗaya ta tsargu kamar mutun yana kallon ta cike da tsoron abun da idon ta zai yi karo da shi ta ɗago ido tana kallon kofar shigowa zubur ta miƙe zaune tana zaro ido waje murya na rawa tace “yaya Prince ina wuni?” tsaye yake a bakin kofar shigowa jikin sa sanye da short da bai rufe masa cinya ba sai singlet fari tas ya saki gashin kansa fuskar nan a ɗaure tam kamar bai san menene dariya ba. gently ya tako juwa gaban gadon hannun ya sanya ya ɗauke ta chak ya saɓa ta a kafaɗar sa ya fice da ita,shiru ta lafe a jikin sa tana addu’ar Allah ya sa ba wani mugun hukunci zai mata ba kai tsaye part nashi ya nufa da ita

    Saman gatafaren gadon sa ya shin fiɗe ta tare da hayewa shima kashe wutar ɗakin yayi ya bar blue light, shiru tayi tana mamakin duk ɓuyan da tayi sai da yaya Prince ya gano ta wai shin ai na mutun zai shiga ya ɓuya ba tare da yaya Prince ya gano shi ba? tayi nisa cikin tunanin sai jin sa tayi ya jawo ta jikin sa ya matse ta sosai kasa kasa yace “me kuke shirya min ke da Aryan?” waro ido tayi tana kokarin ɗago kan ta daga jikin sa, da sauri ya mai da ta yana faɗin “am sa zaki bani bance kin ɗago ba” girgiza kai tayi “babu komai yaya Prince” “wai ni yau she kika fara karya ne? Shiru tayi ta rasa wani amsa zata bashi,hannu ya zura cikin hijabin jikin ta ya fata shafa lallausan bakin gashin kan ta yana watsawa “zaki faɗa min ne ko ni in faɗan miki?” hannu ta ɗaura saman wuyar sa tana shafawa a hankali ba tare da tayi magana ba chije lips nashi yayi da karfi ya furta “wash” a zafafe ya ɗago ha barta tare da haɗe bakin su waje guda ya shiga bata hot kiss.
    5mins ya ɗauka bakin su a haɗe kafin ya zame bakin sa tare da zame hijabin jikin ta ya shi murzata ta ko ina tula tulan ta sun sha murza ba kaɗan ba sai fitar da numfashi da sauri sauri yake cikin fitar hayyaci ya zame short ɗin jikin sa yana kokarin shigar ta lokacin guda ya dawo hayyacin sa tare da sauka daga kanta ya fasa shigar nata ya kwanta gefen ta yana juyi tare da mai da numfashi, mirginowa tayi ta dawo jikin sa tana faɗin “yaya Prince lfy naga ka riƙe ciki ko dai cikin kane ke ciwo? Shiru yayi bai yi magana ba sai ma damko ta da ya kuma yi ya matse ta a jikin sa yana jan doguwar numfashi,shiru tayi bata sake magana ba tana jin yadda yake mutsu mutsu a jikin ta, lokaci guda tunanin maganar da yaya Khalid ya mata ya faɗo mata a rai in da take cewa “ki rinƙa yawan zama a jikin sa dan kusa ba ina da tabbacin ba zai miki komai ba dan yana tunanin ba zaki iya ɗaukan komai yanzu ba tuna hakan ne ya sa ta gane dalilin da ya sanya yaya Prince baya taɓa jikin ta sosai kara shigewa jikin sa tayi ta lafe shiru tana jin yadda yake ta fama kafim ya samu nitsuwa. Kankameta yayi yana mai bakin cikin abun da Aryan ya masa

    To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu

    Aunty babba ko zaki mutu ba zan dai na cewa to masu sai mun haɗu gone ba idan kina so na dai na cewa tom kisa yaya ya sai min system sabo 😎😒

    💖The talent troupe writer’s 💖

     

    💋Duk Karfin Izzata 💋

    By Star Lady

     

     

  • Arubuce Ta Ke 1

    Arubuce Ta Ke 1

     

    A nutse ta bude k’ofar toilet din ta fito daure da babban towel fari sol,lallausar farar fatarta mai santsi da sheqi tana ta daukan idanu.

    Gaban dressing mirror din dake dakin ta isa,ta ja kujera ta zauna tana kallon fuskarta a ciki,gaba daya jin ranta da jikinta takeyi babu dadi,fuskarsa ke gilma mata cikin idanuwanta,sam jikinta bai bata ba,ta kasa nutsuwa gami da gamsuwa da wannan tafiyar da ya qirqirar mata bagtatan lokaci guda,tana tsaka da hidindimunta,tun daga yanayi fuskarsa da kuma yadda ya dinga tuqi daga bauchi zuwa katsina takejin kamar ba abbas dinta ba,tabbas akwai abinda ke faruwa,akwai wani muhimmin abu dake gudana,tayi tunani har babu iyaka,ta laluba dalilin tas tun daga randa ya sanya qafa ya fita daga gidan zuwa dawowarsa da kuma isowarsu katsina……tayi zagaye cikin tunani da abubuwan da suka wanzu kaf! Ta kasa gano abu guda daya farun.

    A iya saninta sun rabu suna masu kewa da kuma shauqin juna kamar ko yaushe,hakanan koda safiyar ranar sun jima ita dashi akan waya suna hira,wata irin hira irin wadda ke fallasa sirrin zuciyar masoyi zuwa ga dan uwansa,yana ta mata qorafin a takure yake acan din tare da mita tana lallabashi tana kuma masa dariya,har suka rabu kyawawan kalamai ne bisa fatar baki da zuciyar kowannensu,to amma me ya canza hakan?

    “AKWAI WANI ABU” ta fada murya qasa qasa tana motsa tausasan lips din bakinta tare da zare idanunta daga kallon da take qarewa fuskartata,ta dauki lotion dinta mai taushi da qamshi ta fara shafawa fatarta cikin kasala taraddadi da kuma damuwa.

    Duk bayan wasu mintuna saita kalli wayarta dake gefe tana tsammanin kiransa,saboda ta sani haka suka sabarwa juna,duk inda zashi cikin nigeria….. matuqar tafiyar mota zaiyi itace abokiyar hirarsa har ya isa inda zashi,idan kuma hakan bata kasance ba…..zaiyita kiranta har ya isa din,amma wannan karon ko gilmawar miscall dinsa bata gani ba bare kiransa,a qididdigen da tayi a yanzun kuma, tabbas koda baije gida ba yana gab da isa

    “Waishin meke faruwa?” Ta sake jefawa kanta tambayar wata irin damuwa tana tabata tun daga qasan zuciyarta.

    Cikin dauriya ta shirya kanta cikin doguwar rigar atamfa,ta fidda ainihin kyanta da surarta sosai,duk da yanayin da take ciki sai data tsaya gaban mudubi ta kalli kanta,lokutta da dama takan dubi kanta da kanta tana tuna WACECE ITA A SHEKARUN DA SUKA SHUDE,a yanzun sai taga kamar ba ita ba…..komai yana zuwa yana shudewa da wani irin sauyi mai ban mamaki.

    Lausasan slippers ta zurawa qafarta,sannan ta isa bakin qofa ta kama handle din ta bude tabi siririn corridor din da zai sadaka da ainihin falon gidan.

    Tun bata qarasa ba ta hangeta zaune cikin falon,halittace mai girman matsayi a wajenta,halitta dake sahun farko cikin halittu mafi soyuwa a wajenta,a duk lokaci irin wannan da zatayi balaguro ta taho takanas saboda kasancewa da ita…..duniyarta kan cika da farinciki,takanji a duniya yanayi irin wannan bashi da tsaara a wajenta.

    A jikinta taji tahowarta,saita dauke idanunta daga kan tv din da take kalla ta maida kanta,kusan lokaci daya suka sakarwa juna murmushi,ta kuma rigata magana

    “Wannan nauyin wankan naki dai yana nan,affan ya fara kuka har sai da aka fitar dashi” cikin karaya da rauni da takeji cikin gangar jikinta da zuciyarta ta qaraso dab da ita ta zauna,tana shirin amsa mata…..kamar me kiran yana jiran dai dai lokacinne kira ya shigo wayarta,a hanzarce ta daga wayar tana duba me kiran, zuciyarta cike da fata da burin ganin wanda ranta ke darsa mata.

    Batasan sanda murmushi ya subuce mata ba hadi da fitar siririyar ajiyar zuciya ba

    “Ina zuwa” tace da mommie,ba zata iya amsa wayarshi a gabanta ba,ita kadai tasan hottest words da suke gayama junansu,kuma muddin aka samu mishkila mommie taji daga ita har shi sun gama tafka abun kunya.

    Kai tsaye dakin ta koma,ta samu gaban madubin data tashi dazu ta zauna tana yunqurin daga wayar

    “Assalamualaikum” ta fada a shagwabe tana karyar da wuyanta gefe,abu mafi soyuwa kenan da tasan yana so tattare da ita,har yau kallonta yake cikin madubin da yake kallonta shekarun baya da suka shude,bata canza a idanunsa ba

    “Wa’alaikumus salam” mummunar faduwa gabanta yayi daka jin sautin muryarsa me taushi da sanyi da yake mata magana da ita koda yaushe ta juye zuwa wata iriyar murya,irin muryar da yake magana da cirminals a yayin da aikinsa ya biyo ta kansu…..irin muryar da yake magana da juniors dinsa a yayin da suke hurumin aiki……irin muryar da yake magana da ita a duk sanda ya shiga qololuwar bacin rai da fushi,muryar da bata taba jin yayi mata magana da ita ba.

    Kowacce gaba ta jikinta tayi sanyi,tayi namijin qoqarin tattaro nutsuwarta da juriyarta tace masa

    “Ka sauka lafiya?,ya kaje gida”

    “Me yasa zaki aikata min haka?” Ya fada muryarsa tana ninka ta da kaushi da ban tsoro,daga cikin wayar tana iya jin hucinsa,da alama a matuqar bacin rai da kuma fusata yake, tambayar tasa kuma ta dilmiyar da ita kogin tunanin ina ya nufa ne?,kafin ta lalubo amsa kunnuwanta sun fara isar mata da saqo mafi muni cikin rayuwarta,daga bakin halitta mafi soyuwa a gareta

    “Ashe haka kike?,ina miki kallon saliha ashe mayaudariya ce ke?,maciyar amana ce?,macuciya ce ke?,na baki dukkan yarda,na damqi miki rayuwata ashe zaki wasa da rai na da lafiyata?” Wani irin tashin hankali ne ya sauko mata,me abbas ke fada ne

    “Me nayi maka?,abban affan me ya faru?,kasan me kake fada kuwa?”

    “Na sani!,nace miki na sani, tsahon yaushe tsahon kuma wanne lokaci kika dauka kina cin amanata kina kuma ha’intata WIDAD?” Kasa zama tayi,ilahirin jikinta ya dauki tsuma,sai ta miqe tsaye qafafuwanta suna rawa

    “Kana cikin hankalinka kuwa abban affan?,a ins kake yanzu?” Ta tambayeshi don ta tabbatar da cewa he’s safe,ba gusar masa da hankali akayi ba yake gaya mata hakan

    “Har kinyi wayon fara bin maza?,ki kwana a hotel?,hakan bai isheki ba har sai kin dauko gardi kin kawomin gidana?,kin kuma kaishi har gadona na sunna widad?,wane laifi na aikata miki haka dana cancanci irin wannan hukuncin?” Yayi maganar ta qarshe muryarsa a wani mugun karye,saidai zafi da kaushin nan suna nan taf a muryarsa

    “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” ta fada a bayyane,qafafuwanta suka hau rawa,gabanta yayi wani irin bugawa da zuciyarta ta hasko mata abinda yake magana a kai.

    “Hotel kuma?” Ta tambayeshi muryarta na wata mugun rawa,irin rawar dake bayyanar da zallar daburce wa a sanda aka ritsaka bisa wani abu na rashin gaskiya

    “Bakije bane?,ko zaki shiryamin irin qaryar da kika saba?”

    “Naje,tabbas naje….amm……”

    “Ya isa!!!!” Abinda ya fada kenan a tsawace

    “Abinda nakeson ji kenan kuma naji,kije ke da Allah,bazan taba yafe miki ba,amanata da kikaci ubangiji ne kawai zaiyimin sakayya,Allah ya isa ban yafe miki ba!!!” Kit! Wayar ta katse

    “Abban affan,daddy!!!” Ta fada a gigice,saidai tuni ya katse layin

    “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” ta sake maimaitawa jikinta na wani irin kyarma tana yunqurin binsa,saidai a take kamfanin sadarwa suka gaya mata is switched off,saita saki wayar ta sulale a wajen tana sakin wani azababben kuka,wani abu mai tauri da zafi yana tokare mata qirji.

    “Waye ya ganta?,waye ya gaya masa?,waye???” Ta soma nacin gano daga inda maganar ta fita

    “Hafsah” taji an bata amsa daga can tsakiyar zuciyarta,kukanta ya tsaya cak na wasu sakanni,sai ta sake rushewa da kukan tana jin kanta yana sara mata,tana son miqewa amma ta kasa,idan tayi kamar zata tashi sai jiri ya maidata ya kayar,a haka aka turo qofar dakin,ta daga idanunta da taji kamar basa dauko.mata hoton komai da kyau ta tsurawa qofar idanu tanason tantance mai shigowar.

    *_A RUBUCE TAKE KADDARATA_*

    *DAGA TASKAR ZAFAFA BIYAR*

    *TARE DA ALK’ALAMI SAFIYYA HUGUMA*

    *TAFIYA CE MAI DAUKE DA DUMBIN*

    @ILIMI
    @ZAZZAFAN KISHI
    @SOYAYYA
    @KIYAYYA
    @SHARRI
    @MAKIRCI
    @KIRSA DA KISSA
    _________________________________

    *RUMBUN K’AYA*🔥

    *DAUDAR GORA*🔥

    *IDON NERA*🔥

    *A RUBUCE TAKE*🔥

  • Arubuce Ta Ke 15

    Arubuce Ta Ke 15

    Page 15

    Qwayar idanunsa ya daga kan takardun yana dubanta sanda take shigowa dauke da kwanukan,ya sauke boyayyar ajiyar zuciya yana qarewa dressing dinta kallo,baisan sai Yaushe hafsat zata canza ba,baisan me zaiyi da zai canza ta ba,duka wani burinsa a kanta ya dade da tarwatsewa,wani lokaci sai ya dinga gani kamar ba hafsat dinsa ba.

    A gabansa ta ajjiye abincin sannan ta koma gefansa ta zauna tana maida idanunta ga takardun da yake dubawar shima

    “Ga abincin” ya daga takarda daya yana juya bayanta ba tare da ya kalleta ba

    “Shi zai zubamin kansa da kansa?” Jim ta danyi sannan ta tabe baki,wani lokaci ya fiya jin kai da izza,hutsu ne na gaske,sai yayi kamar ya sauko ko ya canza sai kuma ya sake hargitse mata,ita kanta tana sarawa kanta yanda take haqurin zama dashi,sai ta sauka tana zuba masa ta ajiiye gabansa tana komawa mazauninta.

    Sai daya qara minti kusan biyar sannan ya ajjiye takardun ya sauko,tana ta satar kallonsa,tana son masa maganar motarta data fara bata matsala tana shakka,dazun sun rabu ba ta dadi ba,yanzun kuma taga yana hada kaya,ta tabbatar kayan tafiya KD ne,wala’alla ya haqura ne ya janye qudurinsa?,idan hakanne ita tafi mata nono fari,saidai tafi kowa sani,shurunsa bashi da sauqi,mataki ne zai dauka daga baya ta ruwan sanyi,koma dai yaya ne idan har ya janye din shikenan its buqatarta ta biya,a hakan ta daure dai tayi gyaran murya kadan.

    Ya jita sarai yayi kamar baiji ba,sai data gaji da gyaran muryarta sannan ta magantu

    “Wai kayan tafiyar kake hadawa?”

    “sune” ya bata amsa a taqaice

    “Allah yasa a koma a sa’a,mudin ko weekend ma dinga zuwar maka,kaga bazai shafi karatun mimi ba” ta fada har qasan ranta tana jin ta fada ne kawai don ta wanke kanta,bawai don zata iya wannan jigilar ba

    “Yayi” ya amsa mata a taqaice kawai,don baison doguwar magana.

    Shuru ya sake ratsa tsakani,tana ta tauna yadda zata gaya masa zancan motar,don so take kafin bikin qawarta din nan ya sauya mata,taje a hajiyar ta da sabuwar mota,ba wannan qaramar motar da kowa ya sanya da ita ba

    “Nace ba” ta fada a darare

    “Uhmmm,kikace me?”

    “don Allah ba…..abban mimi motata…wallahi matsala take ta bani,sannan ma tayi tsufa da yawa,kada kunya na dinga shigarta bayan mutane sunsan matsayinka” shuru kamar bazai amsata ba,yaci gaba da cin abincinsa,yayin data kasa ta tsare ta kafeshi da idanu tana jiran ta cewarsa,har sai data gaji da jiran amsa ta sake magantuwa

    “Bakace komai ba abban mimi” plate din hannunsa ya ajjiye,ya waiwayo ya dubeta

    “Bani da kudi a yanzu” fuska ta dan bata

    “Abban mimi baka da kudi fa kake fada?,ko allowance dinka ya isa ka canza min babbar mota bama qarama bafa”

    “Kudina a yanzun bana canza mota bane,ina da abu me muhimmanci da ya fishi” daga haka ya miqe yaci gaba da aikinsa hankali kwance,cikin bacin rai taci gaba da zama wajen,tana ta baqin rai ita kadai,zantukan yayarta take tunawa

    “Kada fa kiga mijina ya canzamin mota ki dauka kema wannan mijin naki me ra’ayin riqau zai canza miki mota ta sauqi,mafi kyau ki haqura da maganar zancan mota yanzun,nasan halinsa sarai ba canza mikin zaiyi ba” a sannan baki ta tabe tana dan kada qafarta

    “Kiyi haquri umman walida,amma banjin yadda abbas ke kashemin kudi da yadda yakeji dani kina samun haka wajen baban walida…..”

    “Ke kinga dakata,karki gayamin baqa mana” ta dakatar da ita,duk da cikin wasa suke maganar

    “Kowa ya san abbas yana jiqaki,amma kuma duk cikinmu babu wadda juya miji ke mata wahala irinki koba haka bane?” Ta fada tana duban sauran sisters dinta dake wajen,dariya suka danyi suna gasgata maganar maman walida din da suke kira da anty balaraba,wannan ya hasalata,ta kuma ci musu alwashin kawo sabuwar mota don ta nuna musu ta isa da mijinta kamar kowacce mace.

    Har yaci qarfin aikinsa tana zaune a wajen bata sake tofa tata ba,ta tattara fushin duniya ta azama ranta,me yasa koda yaushe abbas din sai ya kunyatata yakejin dadi?,kafin ya kammala aikin ta tattare tabar masa wajen,sai kawai tayi komawarta sashenta,tayi kwanciyarta acan.

    Shima daya gama komai kwanciyarsa yayi,bai wani tsaya bi ta kanta ba,bayason rainin wayo da kuma rashin hankali,ta kuma fi kowa sani abinda baya tolerating kenan.

    Washegari haka tayita kumbure kumburenta,sai ya nuna baisan ma abinda takeyi ba,ayi masa laifi kuma a fishi fushi?,yayita hidimarsa da yaransa,yana kuma yin breakfast ya shirya zai fita,mimi ta maqale masa sai ta bishi,ya kaita gidan hajiya,hafsat din nata danqara masa mata harara amma yarinyar batasan tana yi ba,ya shiga dakinsu ya shiryata da kyau cikin sabbin kayanta dake danqare a cupboard ba’a sanya musu,baisan uban me takeyi da kayan ba,yasan dai wani lokaci takan diba ta rabar,duk cikin fariya da alfaharin shi din wuyansa ya isa yankan da yake danqaro musu suttura ya ajjiye.

    Yana fita ta bishi da tsaki ta kuma miqe abinta saman doguwar kujera tana gunaguni,duk yadda take sonshi yana sanyawa yana fita a ranta gaba daya,bata isa ta sashi yayi abu ba sai abinda yayi niyya ya kuma tsarama kansa,kallo ta kunna abinta tana daga kwance,nawwara da yau suka samu albarkar wanka tun safe tana ta kaikawo tana wasanta qasan carfet,har bacci ya dauketa ta bingire a nan.

    Har biyu ta buga tana kwance tana kallo bata da niyyar tashi ta kintsa gidan,sai da taji sallama daga qofar falo sannan ta miqe tana sauke qafafunta qasa.

    “Anty ummee,ni banma dauki murya ba wallahi”

    “Ina zaki dauka kin tasa tv a gaba” ta fadi tana duqawa ta dauke nawwara daga qasa ta maidata saman kujera sannan ta zauna daga gefanta tana cewa

    “Yanzun da banzo ba a qasa zaki barta har tayi barcinta ta tashi” baki ta tabe,bacin ranta da ya dan lafa yana motsa mata

    “Hmmm,a qufule nake anty ummee,ubanta yaja mata,shi ya qunsan takaici”

    “Ke kam damuwarki da abbas bata qarewa,gashi dai baki rasa komai ba amma ko yaushe cikin complain?”

    “Na rasa ya zanyi dashi anty ummee,dan bada umarnin nan da mata kewa miji ni bansanshi ba” baki ta tabe tana jingina sosai da kujera

    “Ke kikaso hafsa” bata motsa daga wajen ba ta zayyanewa anty ummee din komai,itace wadda take bi a dakinsu,uwarsu daya ubansu daya,sai data gama tas sannan ta dubeta

    “A cikin banza ma ke banza ce wallahi hafsat,ke ko asiri kike fa saikin hada da kissa da kisisina yake ci maka yadda kakeso,ke dan makircin nan na mata ma ace baki iya ba?,ko da yake ko an doraki ma sauka kike” ta qarashe maganar tana yaada kanta gefe cike da takaicin ‘yar uwartata.

    Matsowa tayi sosai kusa da ita

    “Zanyi wallahi anty ummeee” sai data qare mata kallo sannan ta zauna sosai tace da ita

    “Ki tattara kayanki ki bishi kaduna kamar yadda yakeso,yaran idan ta kama ko gida ko hannun hajiyarsa basai ki barsu ba?,bama mimi bace ita kadai?,idan kuka tafi can daga ke saishi,ba ‘yan uwansa akusa ba ‘yan sanya idanu,Allah ne kadai yasan nawa zaki tatsa daga jikinsa,masu aikin damarar nan fa ba qaramin iya soyayya sukayi ba,amma ke gaba daya komai naki a rikice?ki bishi ki kwantar da kai,dadin yadda kika faranta masa ma wallahi baisan sanda zai sauya miki motar ba babu wanda yaji ba wanda ya gani” Fuska ta bata,don ta dauka wata mafitar zata bata ba wannan ba,sai itama anty ummee din ta zuba mata idanu tana dubanta

    “Ba zakije ba kenan?” Cikin tsuke fuska tace

    “Ni anty ummee,kaduna fa wa na sani wa ya sanni?”

    “To ai shikenan saikiyita zama bauchi ki tsanana uwar da zaki tsinana” ta fada tana buga cinya. Shuru tayi na wasu sakanni tana nazari,yayin da anty ummee ke qarewa qawataccen falon nata kallo yadda ta barshi komai a zaune da duwawunsa,babu tsari bare kintsi

    “Shikenan anty ummee,an gwada aiki da shawarar taki,zanje”

    “Yadaifi miki” ta bata amsa sannan ta maido dubanta kanta

    “Yanzu kika tashi a barci ne wai?” Kai ta girgiza tana dubanta

    “A’ah,me kike gani?”

    “Bakiji bashi bashin da jikinki yakeyi ba?,sannan wannan uwar bolar da kika barwa falonki ta mece?” Shinshina jikinta ta soma yi,sannan ta bata fuska,don ita bataji komai ba

    “Ni ba abinda jikina yakeyi,hancinki ne dai,falo kuma wallahi yara ne suka bata su da ubansu kafin su fita,don jiya da daddare fes na shareshi kafin na kwanta,yanzu kuma ina shirin tashi na sake gyarawa kika shigo”

    “Allah ya sawwaqe” kawai tace da ita,tasan halinta ba yau ba ba jiya ba,koda ta tsaya gaya mata qarancin tsaftarta ma uzurin yara zata yita kawo mata,kamar ita tafi kowa haihuwa a duniya.

    Suna taba hira tana gyara falon har ta gama,ta shiga kitchen tana tunanin me zata dafa harda abbas din,don ba zata iya girki biyu ba,tayi yanzu tazo tayi musu na dare?,sai kawai ta dora.taliya da miya,suka wuce uwar dakan hafsat din anty ummee na sake jaddada mata muhimmancin binsa kadunan,tare da dabaru na kissa na yadda zata samu yadda takeso.

    Ita ta tayata suka hada kayanta dana yara,don tasan iya wannan sai ya zame mata aikin gabas,cikin kayan nata taga wasu night gown,tasan kudinsu saboda ta gansu wajen wata qawarta kwanaki da tayo order dinsu

    “Kai….wadannan nighty din fa?”

    “Sunyi kyau ne?” Ta amsata tana zuge qaramar jakar data zuba undies dinsu

    “Sosaima,ke bakisan kudinsu ba?” Baki ta tabe

    “Bana ce ba gaskiya,shi ya siyomin su kwanaki,ni kuma Allah ya gani bazan iya sanyasu ba,kamar waga kafira,shi yayita wani aiki kamar dan iska dan iska,ko kunyar yaranshi biyu baya ji” galala anty ummee ke kallon hafsat din,idan tayi wani abun kamar batayi karatu ba,ita yanzun just shekara ashirin da takwas zuwa da tara har tayi tsufan da bazatayi gyara ba?, Amma da yake itama kayan takeso sai bata bata shawarar komai ba,ta ninke abinta ta sanya a jaka,ita tasan darajarsu.

    Da ta tashi tafiya ta sake tambayar wasu designers turare da ya siyo mata,guda uku ne,guda biyu dubu ashirin da bibbiyu ya siyosu,guda daya dubu talatin,hakanan yake,mayen qamshi ne,shi yasa baya siyan banzan turare,ko su mimi zai siyawa turare baya siya musu na qaramin kudi,bata damu da su ba shi yasa.batasan daraja ko tsadarsu ba,tace ta dauka wanda takeso,ta kuwa dauke dan dubu talatin dana ashirin da biyun guda daya tayi tafiyarta,dama yawa yawan zuwanta gidan abinda ke kawota kenan,don ta qaru da ‘yar uwarta,duk da tana bata shawarwari na gaskiya a wasu lokuttan,rashin daukan shawara ke damun hafsat din,data fara saita tattara ta zubar,tafi ganewa yawan qorafi da kai k’ara.

    *_RIGIJI GABJI!_*🔥🔥

    *_WANI KAYA SAI AMALE_*🔥🔥🔥

    *FITATTUN ZAFAFAN DA BABU NA BIYUNSU*🔥🔥

    *JERIN GWANON LITATTAFAI ABOKAN TAFIYAR JUNA MASU MABANBANTAN LABARAI DA FASAHA*

    *_’YAN BIYAR DIN NAN NE FA_*

    *_SARAKAN LABARUN_*

    *NISHADI*
    *CAKWAKIYA*
    *GWAGWARMAYA*
    *BARKWANCI*
    *TSANTSAR DARASIN RAYUWA*

    *TARE DA*

    *ZAZZAFAN SALO NA SOYAYYA MAI RIKITA TUNANI DA TSUNDUMA MAI KARATU CIKIN TAFKIN SHAUQI*

    *SUN SAKE SHIRYAWA TSAF,DAUKE DA WANI TARAGO MAI CIKE DA LABARAI MASU ZAZZAFAN ZAFI!!!*

    *KIN SHIRYA MADAM?*

    *MAZA ANTAYA NAKI KUDADEN KIBI SAHUN AYARIN MATA MASU AJI TA HANYAR BIYAN KUDIN NAKI KARATUN WADAN NAN LITTAFAI KAMAR HAKA*

    *DAUD’AR GORA* Billynabdul

    *KI KULANI* Missxoxo

    *IDON NERA* Mamuhghee

    *RUMBUN K’AYA* hafsat rano

    *A RUBUCE TAKE* Huguma

    *ZAKI IYA BIYA KAI TSAYE TA WANNAN ACCOUNT DIN*

    0022419171
    Maryam sani
    Access bank

    Saiki tura shaidar biyanki ta wannan number

    09033181070

    *MASU TURA KATIN MTN KO VTU KUMA ZASU TURA WA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANSU*

    09166221261

    *Yan NIJER 🇳🇪🇳🇪zaku tuntubi wannan number*

    +227 90 16 59 91

    *Muna godiya da ci gaba da zabin zafafa biyar a koda yaushe*🙏🏾🙏🏾

    *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)
    *Arewabooks: huguma*

  • Duk Karfin Izzata Book 2 Page 30

    Duk Karfin Izzata Book 2 Page 30

    Page 30

    Uk

    Barci mai matukar daɗi ne ya kwashe su yana rungume da ita a jikin sa. yana tsaka da barci wayar sa ta fara kara da kyar ya iya waro idon sa waje kusan tare suka farka da shi da ita ɗauko wayar yayi daga saman drawer sunan Khalid ne ya bayya na a kan screen ɗin duba time yayi 3:55pm tsaki yaja tare da kai kallon sa kan kyakkyawar face nata dai dai lokacin ta waro blue eyes nata a kan kyakkyawar face nashi da kyar ya iya futa “are you okay? Gyaɗa masa kai tayi kafin tace “yaya Prince ya muka dawo gida? Ya baka kai ni yawo sosai ba? “Eh duk da munyi fitar sirri akoi wayan da suka bi bayan mu ne shi ya sanya muka dawo gida yanzu dai tashi mu wuche lokacin tafiya yayi” yana kai karshen maganar ya miƙe ya sauko daga gadon.
    kasa tashi tayi dan yana miƙewa wani mugun sanyi ta ji ya rufe ta,har ya kai bakin kofa ya juyo yana kalle ta tana kwance kamar yadda ya barta “sister ba zakai je Nigeria bane? Shagwaɓe fuska tayi kamar zatayi kuka ta fara magana “yaya Prince sanyi nake ji kuma na kasa tashi” dawowa yayi chikin ɗakin ya ɗauke ta chak ya fice da ita sai rawan sanyi take har ya kai palo sai kuma ya juyo ya dawo ya ɗauki ɗan karamin trolley sa daya shirya tana kwance saman kafaɗar sa kai tsaye waje harabar gidan suka nufa.

    Already su Khalid sun fito kowa ya shiga motar sa tare matar sa Hisham da Ilham suna tsaye a harabar gidan suna musu bye bye ganin Bgs ɗauke da Hiyana ba karamin mamaki ya basu ba tunani Khalid ya shigayi anya Bgs ba wani abun yayiwa sister ba da ta sanya yau tun safe yake ta ɗaukan ta kai da biyu wlh ba haka nan ba. Ilham kuwa matsowa tayi kusa da kunnen Hisham tace “baby wai haka ogan kunnan yake? Baya barin matar sa ta tafi da kafar ta kai gaskiya ya iya soyayya da kula da mata” harara Hisham ya watsa mata kafin yace “ki dai iya bakin ki wlh idan ya jiki ba mai iya tare miki.

    da gudu Abdol ya buɗe ma Bgs mota ya sauke ta a gidan baya sanna ya juyo yana kallon Hisham ba tare da yayi magana ba chikin sauri Hisham ya tako ya kariso gaban sa hannu Bgs ya miƙa masa Hisham har jikin sa na rawa ya bawa Bgs hannu sukayi mu sabaha chikin nitsuwa Bgs ya fara magana “to Hisham ka dawo mu kuma zamu tafi amma 2 weeks zamuyi ka kula da aikin ka sai mun dawo” yana kai karshen maganar ba tare da ya jira amsar Hisham ba ya saki hannun sa ya shige chikin mota sosai Hisham ya musu fatan alkhari da fatan adawo lfy sai murmushi yake.

    Bayan tafiyar motocin su Bgs Ilham ta matso kusa da Hisham ta fara magana “baby me ya faru? Naga kana ta murmushi da baka taɓa yin irin sa ba” “my wife kin san matsayin Brigadier general kuwa? Bgs yana gaba da mu nesa ba kusa ba ina murmushi ne saboda yau na gaisa da shi hannu da hannu tare muka taso da su amma ban taɓa gaisawa da shi hannu da hannu ba ke ko baki da baki ma idan kika gaishe sa ba amsawa yake ba bare hannu da hannu shi idan kin gansa yana magana to umarni yake badawa idan za’a tafi filin yaki banaji awajen Aikin mu akoi wan da zai che miki ya san kalar voice nashi akoi manya manyan sojoji ma da basu taɓa jin voice na shiba duk yadda zan faɗa miki wanene Bgs ba zaki fahimta ba ni dai ina farinciki yau” a kule Ilham tace “to baya kula ka me ya sa zamu zo gidan su mu zauna? ” “My wife ki sani nifa mun taso tare ne amma su Khalid ne abokai na ko Aryan ban kai matsayin da zanyi abota da shi ba tare Bgs ina ga baki san me kike faɗe ba ne kin san miliyoyin mutane nawa ne ke neman irin daman da na samu wasu sojojin ma nema suke ko a masu sharan gida ya ɗauke su su dai suga suna kusa da Brigadier general Safras amma ke shine kike wata magana” ajiyar zuchiya ta sauke kafin tace “tom shike nan muje mu shirya muje yawo” hannun ta ya riko suka wauce chikin gida.

    A ɓangaren su Bgs kuwa lokacin da suka isa Airport an gama shirya musu komai suna isa ba tare da ɓata lokacin ba suka fito daga mota suka shiga katafaren jet ɗin Bgs mai ɗauke da tambarin sunan sa da manyan baki PRINCE SAFRAS zama yayi saman haɗaɗiyar kujerar jet ɗin hiyana ta zauna kusa da shi bawani ɓata lokacin su Khalid kowa tare da matar sa ya zauna har jirgin su ya ɗaga hiyana bata dawo dai dai ba. sanyi zazzaɓi take ji sosai chikin rawar murya da kakkarwan sanyi ta fara magana
    “Yaya Prince sanyi nake ji sosai” kallon ta yayi da kyau kafin ya nuna mata saman chinyar sa da hannu ba tare da yayi magana ba da kyar ta miƙe ta dawo saman chikinyar sa ta zauna buɗe zip ɗin jaket ɗin jikin sa yayi ya kwantar da kan ta saman faffaɗar kirjin sa ya rufeta da jaket ɗin iya kan ta kawai ya bari awaje shiru ta lafe a jikin sa tana mai da numfashi. “Are you okay now? Ya tambayeta yana kallon face nata sai lokacin ta ɗago ido tana kallon kyakkyawar face nashi ɗan kwanto da kai sa yayi ta gefe yana kallon chikin idon ta girgiza mata kai yayi ya ɗaga gera ɗaya alamar lfy kike kallo na cool murmushi ta saki kafin tace “kamin kyau sosai ne shi ya sanya nake kallon ka” kawar da kansa gefe yayi yana murnushin gefen fuska.

    Kallon Yusuf Khalid ke yi yayin da shima Yusuf ɗin ke kallon sa suna son yin gulma amma suna tsoro yau suna ganin ikon Allah domin idan ba ikon Allah ba ba abun da zai sauya Bgs haka wai har da kawar da fuska yana ɗan murmushi lallai sister ta chiri tuta lallai yau hakuri yayi rana daman duk wanda yayi hakuri zai yi nasara a rayuwan sa. waya Khalid ya chiro ya fara yi musu video ba tare da sanin su ba a ɓangaren Yusuf ma hakane waya ya chiro ya fara ɗaukan Romeo and Juliet ɗin nan ba tare da sanin su ba sai hira hiyana ke zuba masa shiko ya zuba mata manya manyan green eyes nashi yana kallon face nata a haka har barci ya ɗauke ta kasa ɗauke ido yayi da kallon ta gyara mata kwanciya yayi da kyau a jikin sa yana kallon face nata wani irin nishaɗi da farinciki ne ya dira a zuciyar sa lokaci guda. Shafa kan sa yayi ya furzar da iska mai zafi chikin ran sa yana tunanin “why? duk lokacin da nake kallon face ɗin yarinyar nan nake jin nishaɗi da farinciki ne why? Ko da yaushe nake son kallon face nata? why Nake jin ta har chikin raina? why Yanzu nake tunanin ta sosai?” ɗayan ɓangaren zuciyar sa ne ta bashi amsa da cewa “so mana son ta kake” da sauri ya girgiza kai yace “no so kuma ni? Ina never babu wanna wajen a rayuwata dogon tsaki yaja tare da kawar da kansa gefe ya fito da wayar sa ya fara latsawa. Mamaki ne ya kama su Khalid murmushi Khalid yayi a ransa yace “ai kaɗan ma ka gani in dai mace ce ai baka fara magana kai kaɗai bama yanzu ne zaka fara wlh inaga sai sister ta sa ka zama kamar mahaukaci muje zuwa yanzu wasan ya fara.

    9:30pm jirgin su yayi landing A malam Aminu Kano International Airport Kano har lokacin hiyana barci take ga jikin ta yayi zafi sosai

    Ako da yaushe Bgs shine na farko fita idan jirgin su ya sauka dan shi baya son ɓata lokacin amma awan nan karon su Khalid sun fita sun barshi yana tunanin ya zaiyi da hiyana dake barci a jikin sa baya son tashin ta dan tana jin zazzaɓi kuma bai san ɗaukan ta ya fita da ita dan sojojin da yan sanda ga manya manyan yan siyasa awaje, Airport ɗin a chike yake da jama’a so baya son kowa ya san yana tare da mace kusa da shi. Almost 30mins yana zaune ya kasa motsawa ga dubbanni jama’a na waje suna jiran fitowar sa ga taron yan jarida Aryan na zaune a cikin mota shi da jiddan sa shiru shiru Bgs bai fitoba buɗe mota Aryan yayi ya fito ya nufi cikin jet ɗin diyana na son fita ta bishi amma ya riga yayi nisa tana tsoron jibga jibgan sojojin dake kewaye awajen

    Aryan na shiga chikin jet ɗin Fahad ya biyo bayan sa “lfy my blood baka fito ba” yayi maganar yana karewa Bgs kallo sai lokacin ma ya lura da Hiyana dake kwance saman kirjin sa kawar da kai gefe bgs yayi ya fara magana “tamin barchi ajiki ne Aryan bana son tashin ta dan bata da lfy kuma ban san fita da ita kasan ni ba sai na sanar da kai ba akoi tarin masoya a waje kamar yadda akoi tarin makiya” Aryan na kokarin yin magana Fahad ya rigasa da cewa “ok bari to na ɗauke ta tun……bai kai karshen maganar ba ya ɗagata sakamakon mugun kallon da Bgs ya wurga masa chikin sauri ya fice daga jet ɗin ya koma chikin motar su. murmushi Aryan ya ɗan saki kafin yace “zaka iya ɗaukan ta ai sai ka rufe mata face da mayafinta yanzu ma darene ai duk da akoi hasken wuta ba lallai aga face nata da kyau ba” kallon face nata yayi kafin ya chire face mark na face na shi ya sanya mata ya ɗauke ta chak ya nufi waje da ita a saman kafaɗar sa Aryan ya bi bayan su.

    Suna fitowa jama’a suka fara tururuwan ɗaukan su hoto masu mamakin ganin Bgs ya ɗauko mace sunayi masu tambayar kansu wacece Bgs ya ɗauko haka suma sunayi. Diyana na ganin su sun fito ta buɗe kofar mota ta fito tana faɗin “yaya Aryan shine ka tafi kabar ni ko? Buɗe mata hannu yayi ta tawo da gudu ta faɗa jikin sa tana faɗin “ina hiyana na take? Kallon Bgs dake tafiya a gaban su yayi ba zai iya faɗawa diyana ga hiyana awajen Bgs ba zata iya musu hauka dan ba karamin aikin ta bane tayi tsalle ta rungumo hiyana a jikin Bgs daman yanzu ma daya aka samu ya sauko katse masa tunani tayi da cewa “yaya Aryan ko dai hiyana bata zo bane? Hannun ta ya kama suka nufi motar su yana faɗin “tazo idan mukaje gida zaki ganta”
    sai magana jama’a keyi shin Lefternal general Aryan yayi Aure ne ko dai sister sa ne ga Bgs ya ɗauko mace a kafaɗar sa sanna kuma ga Aryan ya rungumi mace a bainan nasi ga general Yusuf rike da hannu mace wai shin ko sunyi Aurene wasu daga chikin su suna musa nawa akan ko bgs yayi Aure wasu chewa suke “ba yarda za’ayi Bgs yayi Aure duniya bata sani ba” haka dai jama’a sukayi ta surutai shi dai Bgs bai bi ta kan kowa ba motar sa ya wuce ya zauna tare da Hiyana a jikin sa sai sharara barcin wahala take

    Aryan kuwa ya tsaya yana amsa gaisuwa da manya manyan mutane da suka zo tarban Bgs yaki kula su

    tsaki Bgs yaja chike da ɓacin rai yace “Aryan zaka wuce mu tafine ko kana tsaye? Yana gama yiwa Aryan magana ya juya ya bawa sojan da zai jasu umarni akan ya wuce da su gida ba musu driver ya tada motar da gudun gaske suka bar Airport ɗin motar su Khalid ya rufa musu baya motar su Aryan ne a baya sai motar jibga jibgan sojojin su

    horn ɗaya su kayi sojojin dake tsaron gate suka wangale musu tangamemen gate ɗin suka kutsa motocin chikin gida kai tsaye parking space suka nufa driver’s ɗin suna kashe motocin Bgs ya fito ɗauke da Hiyana kai tsaye part nashi ya nufa su Aryan ma suka fito kowa ya nufi part na shi da matar sa Khalid ne kaɗai ya kama hannun Auta suka nufi part ɗin Ammi dan shi duk lokacin da suka zo Naija Ammi ce first wadda yake fara zuwa wajen ta kafin kowa.

    Saman katafaren gadon sa ya shinfiɗe ta ya wuce ya nufi toilet yana kokarin shiga toilet ya jiyo zazzakar voice nata tana faɗin “yaya Prince zanje wajen Ammi na” wani farinciki ne ya dira a zuchiyar sa lokaci guda yaji kaunar ta na ratsa shi slowly ya juyo yana kallon ta kwance take kamar yadda ya kwantar da ita sai dai ta waro idon ta tana kallon sama “zo kiyi wanka sai kije” miƙewa tayi da kyar ta zauna tana kallon sa “ayya yaya Prince zanje nayi a part na Ammi wlh bani da burin da ya wuce na ganta” ɗaga mata kai yayi kafin yace “ok jeki” da sauri ta miƙe tana tangal tangal har ta fice bin ta da kallo yayi har ta fice sannan ya shige chikin toilet ɗin yayi wanka ya fito yayi shirin barci chikin kayan barci sky blue riga da wando basu kyau da laushi hayewa saman gadon sa yayi ya ɗauki wayar sa ya duba time 10:55 ajiye wayar yayi ya jawo blanket zuwa kirjin sa ya kashe wutar ɗakin tare kunna blue light dake gefe gefen gadon ya lumshe ido da niyar barci amma ina barcin taki zuwa sai juyi yake a saman gadon ƙwaƙwalwa sa na tunano masa irin barcin da sukayi jiya da sister sa ganin kyakkyawar face nata yake a face nashi ɗazun da ya jiƙa mata gashin ta a Uk wajen dutsen nan matse idon sa yayi yana kokarin kawar da tunanin ta amma ya kasa sai kara tunano masa ita zuciyar sa da ƙwaƙwalwa sa keyi ya kasa barci sai juyi yake
    Tsaki yaja tare da miƙewa zaune ya laluɓo wayar sa ya kunna haske screen ɗin ya shiga contact dialling number ta yayi ya fara kira

    Lokacin da kiran shi ya shigo wayar ta tana kwance a saman gadon Ammi ta tada kai da chinyar Ammi Ammi na shafa lallausan bakin gashin kanta suna yar hira tayi wanka ta shirya chikin riga doguwa na barci mai buttir a gaba.
    tana kallon call nashi amma taki ɗauka dan tana jin kunyar Ammi har call ɗin ya yanke bata ɗaga ba call na biyu ne ya sake shigowa wayar nata “Hiyana ki ɗauki kiran mana wanenen ma yake kiran ki a wanan lokacin?” Chikin sanyin murya tace “yaya Prince ne yake kira” “to ki ɗauka mana kiji me yake so” chikin jin kunya ta sanya hannu zata ɗauki kiran call ɗin ya yanke ajiyar zuchiya ta sauke ta gyara kwanciyar ta ajikin Ammi chikin dabara ba tare da Ammi ta lura ba ta sanya wayar ta a silent.

    Sau uku Bgs na kiran ta bata ɗaga ba chike da ɓacin rai ya miƙe ya fito palo kai tsaye ya fice waje ya nufi part na Ammi babu kowa a palon kai tsaye ya wuce bedroom na Ammi kasa kasa yayi sallama ba tare da ya jira an bashi izini ba ya tura kofar ya shige da kyakkyawar face nata ya fara karo chikin tsoro ta miƙe ta zauna kai kallon sa yayi kan wayar ta dake kusa da ita kafin ya dawo da kallon sa kan razanannen face nata harara ya shiga wurga mata duk abun da suke Ammi na kallon su a chikin ranta tana godewa Allah da ya sanya har Bgs yake kallon hiyana
    “Kai lfy ka shigo ka tsaya ma mutane a kai?” Sai lokacin ya dawo da kallon sa kan Ammi ɗan shafa kan sa yayi chikin girmamawa yace “barka da hutawa Ammi” kallon sa tayi tana mamakin yau Bgs ne ranar da ya dawo ya shigo part na abun da bai taɓa yi ba wani lokaci ma idan ya dawo sai ya kai 2dys ban samu ganin saba kome ya kawo sa yau kuma oho” voice nashi ne ya katse mata tunanin ta dacewa “ke wuce kije ki kai min fruits ɗaki na” yana kai karshen maganar ya juya ya fice daga ɗakin. miƙewa tayi sai kunbura kumatu take tace “Ammi ina dawowa” “to” kawai Ammi tace

    Bedroom nasu ta nufa ta ɗauko hijabi dogo har kasa ya sanya saman kayan barcin jikin ta ta fito ta wuce kitchen a gurguje ta haɗa masa fruits da black tea ta ɗauka ta fito ta nufi part nashi. Da sallama ɗauke a bakin ta ta shigo yana kwanche saman gadon sa saman bedside drawer ta ɗaura masa plate na fruits ɗin ta juya ta nufi hanyar fita kamar daga sama taji sexy voice mashi yama faɗin “sau nawa na kira layin ki? Slowly ta juyo tana kallon sa dai dai lokacin ya miƙe zaune tare da sauke kallon sa kan face nata shiru tayi batayi magana ba tsawa ya kuma daka mata “sau nawa na kira layin ki!!? Da gudu ta juya zata fice dan bata son jimawa a ɗakin sa. chikin zafin nama ya miƙe taku biyu yayi ya chapko ta ta baya ihu ta fasa masa chikin sauri ya sanya hannu ya toshe mata baki tare da juyo da ita suna fuskantar juna

    girgiza masa kai ta fara yi tana zaro ido “sau nawa na kira wayar ki? Ya kai karshen maganar tare da zame hannun sa daga bakin ta murya na kerma ta fara magana “kayi hakuri ina jin kunyar Ammi ne shi ya sanya ban ɗauki kiran ba” zuba mata ido yayi yana kallon ɗan karamin bakin kasa kasa yace “ina zakije yanzu da kika nufi hanyar fita” “wajen Ammi” ta bashi amsa a ta kai ce matso da face nashi yayi dab da nata suna kallon juna tana son rufe ido amma tana tsoron karya mata faɗa “why zaki je wajem Ammi? Me zaki yi a chan? Ajiyar zuchiya ta sauke kafin tace “hira muke yi da ita kaga ai mun daɗe bamu haɗu ba” shiru ya ɗan yi yana kallon lallausan lips nata kafin ya matso da nashi lips ɗin ya haɗe bakin su waje guda tare da ɗaga ta chak ya wuce saman gado bakin su na chikin na juna kwanciya yayi tare da ita a kirjin sa.

    Hot kiss yake bata babu kama hannun yaro chikin dabara ya zame hijabin jikin ta ya shiga murzar ta tun tana ɗan kame jikin ta har ta saki jiki ta shiga mayar masa sa da martani. kamar ingiza shi tayi chikin zafin nama ya ɓalle botiran rigar jikin ta ya zame rigar nata ya fara murzan tula tulan ta hannu ta tura chikin gashin kansa tana watsawa sambatu ya fara yi mata “oh god sister it’s so sweet wash, ash, keep doing,i love your ball’s” gangaro da hannun ta tayi zuwa wuyar sa tana shafawa a hankali zame bakin sa yayi daga nata ya mai da saman wuyar ta yana lasa a hankali yana murzan tula tula. Slowly ya kai bakin sa saman nipple nata da ɗan karfi ta furta “wash zafi” kamar kara ingiza shi tayi ya shiga tsotsar su kamar baby chikin fitar hayyaci ya kama hannun ta ya ɗaura saman marar sa. Ihu ta fasa da karfi wadda yayi sanadiyar dawowar sa chikin hayyacin sa kokarin guduwa take yayi saurin rikota yana kallon face nata runtse ido tayi chikin sanyin murya tace “dan Allah yaya Prince ka kwaleni na je Ammi na jirana” rungumeta yayi da kyar ya buɗe baki chikin tsarkewar murya yace “kwanta kiyi barci” zatayi magana ya ɗaura ɗan ya tsan sa a saman lallausan lips nata yana girgiza mata kai shiru tayi ta kwantar da kan ta a saman kirjin sa sukayi shiru

    har 1:30Am basu yi barci ba a hankali ta ɗago kai kasa kasa kamar mai raɗa tace “yaya Prince baka sha fruits ɗin ba” mai da kan ta yayi ya kwantar dan bai san ta motsa ko kaɗan idan ta motsa za’a iya samun matsala da kyar ya iya buɗe baki ya fara magana dan yana cikin wani hali “no ba zan iya sha ba” “to yaya Prince in tafi wajen Ammi? yatsa ya ɗaura mata a saman lips nata kafin yace “karki sake magana kiyi barci dare yayi” shiru tayi tana son komawa part nasu amma ba hali kunya take ji da safe ta tashi ta haɗa ido da Ammi ita da tace zata je ta dawo da haka har barci ya ɗauke ta. Sai 2:30 sanna ya kwantar da ita ya miƙe ya nufi toilet wanka yayi ya fito ya sanya wani kayan barcin ya haye gado ya kwanta ya juya mata baya

    kasa barci yayi ji yake tamkar ya rasa wani abu gaba ɗaya ya rasa me ke masa juyowa yayi ya jawota jikin sa nauyayyar ajiyar zuchiya ya sauke tare da ja musu blanket ya rufe su da haka barci ɓarawo ya ɗauke sa

    5:30am

    Tana idar da sallar asuba ta naɗe daddumar sauri sauri tana kokarin fita daga bedroom nashi ta tafi part ɗin Ammi sai sauri take kar ya dawo masallaci ya same ta. dai dai zata fita palo shi kuma yana shigowa karo sukayi kan ta ya bugi faffaɗar kirjin sa dake tsaye dam dam baya tayi zata faɗi yayi saurin damko wuyar hijabin ta ya fiskota ta faɗa saman faffaɗar kirjin sa a tare suka sauke ajiyar zuchiya kasa kasa yace “where are you going? “ɗakin mu zanje” “na baki izinin tafiya ne? Chikin sauri ta ɗago kai yana kallon sa “izinin kuma? Ta tambaya tana saukar da idon ta kasa “eh izini” “yaya Prince idan matar Aure ce iya mijine kawai ake neman izinin sa idan za’a je wani waje idan kuma budurwa ce to wajen baban ta zata nemi izini ka ga kai kuma a matsayin sister ka ɗauke ni kaga kenan ba sai na nemi iznin ka ba” matse bakin ta yayi da ɗan karfi kafin yace “ni yayan kine kuma ya zama dole ki nemi izini na kafin kiyi abu ba lallai sai miji ko uba ba awajen yaya ma ana neman izini” hannun ta sanya ta zame hannun sa daga rikon da yayi wa bakinta tare da riko yatsar sa manuniya ta sanya a bakinta ta ɗan chiza chikin wasa “wash” ya furta chikin zafin nama ya sunkucheta ya goma da ita chikin bedroom

    A tare suka faɗa saman gadon ya jawota kirjin sa tare da ja musu blanket chikin raɗa yace “kiyi barci” lumshe ido tayi ta lafe a jikin sa ba jimawa barci yayi awon gaba da ita dan dama bata sami ishesshen barciba, hannun sa ya tura cikin hijabin ta yana ɗan shafa tula tulan ta a hankali har barci yayi awon gaba da shi

     

    To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai

    Duk Karfin Izzata comments section group ina matikar godiya da comments naku yana ƙaramin karfin guiwa sosai Allah ya bar zumunci da qaunar juna 🥰🥰

    💖The talent troupe writer’s 💖

     

    💋Duk Karfin Izzata 💋

    By Star Lady

     

     

  • Duk Karfin Izzata Book 2 Page 16

    Duk Karfin Izzata Book 2 Page 16

    Book 2

    Page 16

    ……Aunty farida ta kasa magana dan ganin abun take kamar a mafarki, shi kan shi Aryan ji yake Kamar mafarki yake, kuka diyana ta farayi tana jan hanchi, chikin sauri Aryan yace
    “kukan me kuma keke? Me akamiki?”

    Chikin kuka tace “ni ku mai dani gidan mu wlh tsoron ku nake ji kuma dan Allah kar ku dake ni”

    jawota Aryan yayi ta faɗa jikin sa ya rungume sosai a jikin sa, chiki sanyin murya ya fara magana

    “ya isa kukan haka kinji ko? Wayan chan da kika zauna da su basune yan uwan ki ba wanchan gidan ba shine gidan kuba, nan shine gidan ku kunji ko?

    Dago kai tayi daga kirjin sa chikin kuka ta fara magana “daman yaya Ahzan ya faɗamin ina da iyaye da yan uwa, sai dai bai san in da yan uwan nawa suke ba, Shiyasa ba zai mai da ni gida ba kenan yanzu kune yan uwan nawa? Mai da kan ta yayi saman kirjin sa ya kwantar yana shafa bayan ta ganin hakan yasa Aunty farida ta miƙe ta bar palon

    “Kin san me nake so dake? Tana kokarin ɗago kai daga kirjin sa tayi magana ya mai da kan nata ya kwantar yana faɗin “ban che ki ɗago kai ba ban che kiyi magana kiyi kwanchiyar ki kawai kiyi shiru ki saurare ni”

    shiru tayi ta lafe a jikin sa, tana kuka kasa kasa, chigaba da magana yayi
    “daga yau karki sake zanchen wayan chan kazaman, mune yan uwan ki, nine mijin ki, kuma yayan ki, ki manta da wayanchan idan ki kayi kuskure sake yimin maganar su tofa zan hukun taki dan a yanzu duk duniya ba abun da na tsani ji da kuma gani kamar su, yanzu zamu koma asalin family hause namu mai yiwuwa idan munje chan zaki iya tuna wani abun kin ji ko?”

    daka tawa yayi da magana yana ɗan shafa wuyar ta, ji yayi numfashi ta ya sauya alamar ta masa barchi a jiki nauyayyar ajiyar zuchiya ya sauke tare da sanya hannu ya ɗago haɓar ta sosai ya zuba wa face nata ido, godiya da kirari mai tarin yawa yarin ƙa yiwa Allah, ji yake sabuwar son ta da kaunar ta na ratsa shi kasa jure kallon face natan yayi, ya rankofo da kan sa dai dai sai tin face nata, Slowly ya kawo ɗan bakin sa kan nata sai kerma lips na shi keyi, sumbatar ɗan ƙaramin bakin nata yayi chikin sauri ya chire bakin sa dan ji yayi tamkar an tsira masa allura from head to toe gangan jikin sa ta an shi sakon.

    a hankali chikin da bara ya kwantar da ita saman sofan ya miƙe tsaye ya chiro wayar sa ya kira layin Aunty farida, har wayan ya katse Aunty farida bata ɗaga ba, mai da wayar aljihu yayi ba tare da ya sake kiran taba.

    Sauri sauri Aunty Farida ta sauko daga sama ta dawo palon tana faɗin
    “Aryan lfy kake kirana?”

    “Lfy daman zamu wuche ne”

    “haba Aryan why ba zaku bari sai gobe ba?”

    “No Aunty farida ga dukkan alamu yarinyar nan ta samu matsala a brein nata kwata kwata fa bata san wacece ita ba bata san mu ba ta manta kowa da komai,so nake mu koma kano a yau adu bamin lafiyar brein nata da ma lfy jikin ta gaba ɗaya”

    dogon numfashi Aunty farida ta ja tare da sauke ajiyar zuchiya kafin tace
    “hakane Aryan to shikenan Allah dai ya sa ba wata matsala babba bane”

    kasa kasa yace “Amin tare da juyawa ya sanya hannu ɗaya ya ɗauki diyana ya saɓa ta a kafaɗarsa suka nufi waje, sai addu’a da fatan alkhairi Aunty farida ke musu har suka fice daga palon.

    Kano

    Zaune saman sofa a ɗakin sa haidar yake shikaɗan yana latsa waya shiru ɗakin kamar babu kowa sanyin A.c da daddaɗan kamshin Air freshener ke tashi,

    chike da yanga da duniyan ci zulaihat ta shigo ɗakin babu ko sallama, jikin ta sanye da wasu shegun riga da wando wadda suka matseta sosai, gaba ɗaya halittar jikin ta a bayya ne, bata sanya breaziya ba wayan nan shayyayyun breast natan kamar silifas awaje, ta sanya wani shegun takalma a kafarta sai wani taunan chingam take, kusa da Haidar taje ta zauna chikin kissa da kisisina irin na yan duniya ta fara magana “hiii Haidar Ykk? ba tare da ta jira amsar shi ba ta chi gaba da magana Amma kai daga gani kanin wanchan mutumin ne ko? Maman ku ɗaya ko? Dan naga kuna kama sosai gaskiya ba karya kaima kyakkyawa ne tun ranan da na gan ka awajen chin abinci a palon Abba naji na kyatsa, idan ba damuwa zamu iya ɗaukan hoto?

    Ko kallon in da take Haidar bai yi ba bare ta sa ran zai mata magana da alama bai ma jin me take faɗe dan ya sanya blth a kunne, kara matsowa tayi kusa da shi ta chi gaba da Magana

    “am pls zaka kai ni shan ice cream? Daga nan sai muje wajen shakatawa idan zamu dawo sai mu biya ta wajen shopping dan inason sayan kayan haɗin shisha da ita kanta tukunyar shishan” ta karisa maganar tana kokarin rungumar sa.

    chikin sauri ya miƙe tsaye ya buɗe baki yana kokarin yin magana,

    miƙewa tayi chikin sauri ta rungume shi, nan take ya ɗauke diff kamar an ɗauke wutan nefa kamar ya sume turesa tayi daga jikin ta da iya karfin ta ya faɗa saman sofa bet ɗin, wani shu umin dariya tayi chikin sauri ta chiro wayar ta, ta shiga Camera ta saita video ta fara ɗaukan su saman dressing mirrow ta ajiye wayar, ta sai ta tana daukan su sosai

    kayan jikin ta tafara chirewa, ta chire wando tana kokarin chire riga kamar daga saman taji diran jibga jibgan sojoji 4 a chikin ɗakin, kai tsaye wajen mirrow suka fara nufa wayar nata suka ɗauka da karfi suka buga wayar da kasa ta tarwatse kacha kacha, wani razanannen tsawa daya daga chikin su ya daka mata

    “wuche mu tafi!! A tsorache ta ɗago tana kallon su gaba ɗayan su fiskan nan nasu babu alamar ya taɓa sanin menen dariya,

    jiki na rawa ta ɗauki wandon ta ta mai da jikin ta sojojin suka tasa ta a gaba sukayi waje da ita, suna fita Aryan na shigo ɗakin chikin sauri yana waya da Bgs

    “amma Bgs kai a tunanin ka me yasa zata yiwa Haidar haka? Daga ɗayan ɓangaren Bgs yace

    “turota akayi domin su samu makamin da zasu rusa farincikin gidan Alhaji Abubakar Saraki”

    “to amma abun da mamaki taya kasan turota akayi kuma waye ya turota?”

    “Aryan ka fara damu na fa, sai kace ba soja ba da kakemin irin wanan tambayo”

    “sorry my blood ai kasan dan ban san komai bane in da ina gidan nan tun safe ba zan tambaye ka ba, kilama kafin ka ga Camera zan rigaka gani, kana sane fa yanzu shigowa ta gidan nan kuma ba wani lfy ne da ni ba”

    “ok naji, abun da yasa nace turota akayi shi ne wayar da ta saita video ta fara ɗaukan su, idan da don ra’ayin kan tane bazata yi masu video ba yanzu dai ka dubamin jikin Haidar menene ya sanya shi suma”

    chikin sauri Aryan ya kariso wajen gadon, ba tare da ya katse kiran ba, chike da mamaki yace
    “kaiii bgs Haidar ai bai suma ba kawai tayi amfani da powder sagar da jijiyoyi ne ta yadda zatayi abun da take so da shi, idon sa biyu ba zai iya hanata ba, dan ta samu hujjan da take so, lallai yanzu na kara tabbatarwa turo ta akayi kuma wanan yarinyar ba karamar criminal bace, ai na ta samu wanna powder da muke yaki akan a dai na shigo mana da shi kasa nan, kai kowace kasa ma ta dai na yin amfani da shi kwata kwata, lallai yarinyar nan ba karamar criminal bace, amma anjima zanje wajen DPO kan case ɗin wayan chan criminals ɗin sai na fara bin chike a su tukun nan in in dawo kan ta dan muga suwanenen suke neman rusa family mai cheke da zaratan jarumai”

    it’s ok idan kaje zamuyi magana” yana gama faɗin hakan ya katse kiran ba tare da ya jira ansar Aryan ba,

    chiro wayar Aryan yayi daga kunnen sa ya mai da aljihu, gyarawa Haidar kwanchiya yayi da kyau, tare da yi masa addu’a ya juya ya fice daga ɗakin, ya nufi fada

    Uk

    8am kwanche take saman sofa mai zaman mutun 3 a palon part nasu, tana jiran dawowar Bgs, har barchi ya ɗauke ta Bgs bai dawo ba

    chan chikin barchi taji wayar ta na kara a firgiche ta miƙe tana lalubar wayar chan kusa da hannun kujerar taga wayar, daukowa tayi lokachin har kiran ta kusa katsewa.

    chikin sauri ta goge idon ta dan tabbatar wa kan ta ba mafar ki take ba, da gaske ne sunan da take gani ya bayyana kan screen nata ko wasa, tabban sunan yaya prince ne kamar yadda tayi saving dan already ta ansa number sa wajen Zahra tasa a wayar nata tayi saving mamakin ai na ya samu phone number tane yasa har wayar ta katse bata ɗaga ba, ganin kiran ya katse ne yasa ta miƙe chike da ruɗu da tashin hankali gaba ɗaya sai tajima kamar bata taɓa jin wani abu wai shi barchiba tsabar tashin hankali da ta shiga, tunani ta farayi ya dawo ne ko bai dawo ba, kai kallon ta tayi wajen time na wayar 11:30am chikin sauri ta ajiye wayar ta nufi betroom nashi tsabar sauri kamar zata tashi sama.

    Da sallama ɗauke a bakin ta ta shigo betroom ɗin, zaune yake saman sofa ya sanya system a gaba da alama aiki mai muhimmanci yake ko wani binciken, daga shi sai Short, faffadar kirjin nan nashi a buɗe asalin murɗaɗɗen suran jikin sa nan a bayyane, kallon ɗamtsen hannun sa kawai hiyana ke yi mamaki ma hannun nasa ke bata ita tunani ma take taya akayi hannun sa yayi wanan girma haka ga kirjin sa kamar na mata, breast nashi da girma kamar na wata mace, gasu a tsaye dam dam, yau da bai sanya riga ba ba karamin rikita hiyana yayi ba domin bata taɓa kallon ainahin suran jikin sa a fili haka ba sauko da blue eyes nata tayi kan lallausan bakin gashin dake kwanche saman kirjin nashi, wow kawai take ta mai mai tawa a zuchiyar ta, dan gashin wajen ba Karami kyau yake mata ba, yana matikar tafiya da imanin ta aduk lokachin da taga gashin wajen jitake kamar taje ta shafa wajen, chike da tsoro ta tako zuwa in da yake zaune, tana tafiya tana satar kallon baki kwantachen kuma lallausan gashin dake kwance a chinyoyin sa da hannayen sa, wani fitinannen kamshin yake tamkar anyi barin turare a jikin sa, sai shakan manshin take tana lunshe ido dan ita dai aduniya tana bala’i san perfume na shi ba karamin tafiya da imanin ta yake ba.

    Gaban sa tazo ta tsugunna chikin tsoro da sanyin murya tace
    “sannu da dawowa yaya prince ina wuni” shiru yayi tamkar bai san da mutun awajen ba, shiru itama tayi tana satar kallon dogayen yatsun kafar sa, almost 10mins

    daddaɗa kuma sanyayyar voice nashi ne ya daki dodon kunnen ta

    “jeki kawomin Black tea mara sugar,ki ɗan matsa lemon juice kaɗan” yana magana chikin nitsuwa yana aikin dake gaban sa a chikin system.

    chikin sauri ta miƙe har ta kai bakin kofa sai kuma ta juyo, chike da tsoron amsar da zai bata tace

    “yaya prince in kawo maka har da abinci zaka chi?

    Shiru yayi bai bata amsa ba kuma bai ɗago ya kalli in da take ba, aikin sa kawai yake tamkar ba da shi tayi maganar ba.

    shiru shiri tana tsaye tana jiran amsa, shi kuma yana aikin gaban sa ko kallon in da take ma bai yi ba, almost 15mins da ta ga dai bai da niyar sake magana, ta wuche jiki a mache ta fice daga ɗakin ta nufi kitchen

    baafi 2mins ba ta haɗa masa Black tea mai zafi kamar yadda ya umarchi ta, ta dawo betroom ɗin Gaban sa tazo ta tsugunna

    “yaya prince ga tea ɗin tayi Maganar murya na rawa,

    hannu yasa ya ansa cup ɗin ya ajiye gefen sa,kan shi na kan system chike da izza ya fara magana “idan kika sake tambaya ta ki kawomin abun da bance ba sai na ballaki”

    “kayi hakuri ba zan sake ba”

    shiru yayi bai sake magana ba, itama shiru tayi tana son tashi ta koma palo ta kwanta dan barchi take ji amma tana tsoron yin hakan

    zaman 30mins tayi awajen, tana jiran taji me zai sake che mata ko zai bukachi wani abun
    shiko aikin sa kawai yake yama manta da mutun a wajen chikin tsoron amsar da zai bata tace

    “yaya prince zan iya tafiya?

    Kai kawai ya ɗaga mata alamar eh ba tare da yayi Magana ba,

    chikin sauri ta miƙe ta koma palo ta kwanta, tana ta murmushi jin daɗin yadda yaya prince yayi mata magana chikin sanyin murya da haka har barchi ya ɗauke ta.

    1:30am ya fito daga betroom nashi sherye chikin kayan barchi masu bala’i kyau da tsada ya shigo chikin palon,

    palon duhu baka iya ganin komai,

    a duhun ya taka har zuwa wajen kujerar da take Kwanche kunna harshen screen ɗin wayar sa yayi a kan face nata, guntun tsaki yaja tare da kawar da kanshi jefe chikin zuchiyar sa yana faɗin “U kill me Ammi U already kill me,yanzu ki rasa wani hukunci zaki min sai kiche idan na sake kwana gado daban daban da yarinyar nan baki yafe ba, why zaki min haka, ni da wanan hukunci wlh gwara ki sanya bindiga ki harbeni ai. Dojon tsaki ya kuma ja kafin ya mai da wayar sa aljihu ya duka ya dauke ta chak tare da saɓata a kafadar sa yayi chikin betroom da ita .

    Saman katafaren gadon sa ya kwantar da ita, sai kwaɓe fuska yake ya koma ta ɗayan gefen ya kwanta tare da jawo blanket,zuwa kirjin sa, ya lumshe green eyes nashi yana karanto Addu’ar barchi, yana gama addu’ar ya shafa tare da juyawa yana kallon gefe ba jimawa barchi ya ɗauke sa

    4:50am dai dai ya farka slowly ya waro green eyes nashi akan face nata, ta shige chikin jikin sa yayin da shi kuma ya ɗora hannun sa ɗaya saman bayan ta suna fiskantar juna,

    barchi yayi daɗi basu san lokacin da suka manne da juna ba, kawar da kansa gefe yayi chike da ɓachin rai ya furta

    “U kill me Ammi kin gama dani wlh ni gaskiya ba zai yuwu ba, dole yarinyar nan ta bar gidan nan kwata kwata ma ban son sake ganin ta.

    A hankali hankali take jiyo voice nashi a chikin barchi da kyar ta iya waro blue eyes nata a kan face nashi

    Chikin sauri ya juyo yana kallon ta, ba karamin mamaki ya shaba ganin yadda idon nata ke kyallin, saboda ta waro su waje sosai dan tsoron ganin ta ajikin sa da tayi, kallon chikin idon nata yake sosai, ganin hakan yasa ta runtse idon ta dan ba za ta iya kallon chikin idon sa lokachi da yake kallon taba, hukunci kawai take jira ya yanke mata dan tasan yau ta shiga uku.

    cool voice nashi ne ya daki dodon kunnen ta wadda ya sanyata buɗe ido ba shiri

    “me ya kawoki jiki na? Yayi maganar yana kokarin raba jikin sa da nata

    kasa magana tayi dan gaba ɗaya yadda yayi magana da sanyayyar voice yasa taji harshen ta ya mata nauyi,

    Kokarin mekewa yake ba tare da ya ankara ba ya dora hannun sa saman breast nata, wani laushi da yajine yasa shi waigowa da sauri yana bin hannun nashi da kallon,

    Da sauri ta runtse ido tana jin zafi,dan ya danne mata su sosai ga shi hannun sa da nauyi sosai, kai kallon sa yayi kan face nata yaga yadda ta tsuke fuska alamar tana jin zafi, shiru yayi yana tunani yana kallon yadda take tsuke ɗan bakin nata alamar tanajin zafi sosai.

    muryan tane ya katse masa tunanin da cewa
    “dan Allah yaya prince kayi hakuri zafi sosai wajen yake min ta karisa maganar tare da sakin wani marayar kuka, t

    saki ya ja tare da ɗauke hannun sa, daga wajen ya miƙe ya nufi toilet dan yayi wanka ya shirya zuwa masallaci

    Kasa kasa take kuka har da shessheƙa, dan ba karamin zafi wajen yake nata ba, yaya prince ya danne mata da karfi domin kusan gaba ɗaya nauyin sa ya saki a kan hannun nasa dafa wajen yayi zai miƙe, ba karamin dauriya tayi ba ma lokachin da ya ɗaura hannun sa awajen, ji take kamar zata fasa ihu.

    Har ya fito daga toilet ɗaure da towel tana kwance tana kuka kasa kasa, ko kallon in da take bai yi ba, ya shirya ya fice daga ɗakin ya nufi masallaci.

    kasa tashi tayi dan raɗaɗin da wajen ke mata haka ta kwanta tana ta kuka mai tsuma zuchiyar mai sauraro, tana son taje tayi wanka tayi sallah amma ta kasa mikewa ji take kamar idan ta tashi breast natan zai faɗi kasa, dan azaban chiwo

    FAHAD AMRAT

    “Yaya Fahad dan Allah ka bari mana” kara matsowa yayi kusa da ita kasa kasa yace

    “naki bari wai ma shin jikin kine ko nawa?
    Chikin sauri Amrat ta buɗe baki zata yi magana ya chapko lip nata na kasa ya shiga tsotsa kamar sweet, hannun sa ɗaya ya ɗora saman kirjin ta, ya shiga murza yan kananan breast nata, a hankali ya zame bakin sa daga nata chike da so da kauna yace

    “my,wayan nan abubuwan wai sai yaushe zasu girma sosai ne, dan na kosa naga kin fara bawa baby na yana sha”

    chike da yaran ta tace
    “yaya Fahad to ai baka sayo mana babyn ba

    “eh zan sayo amma sai breast naki sun girma sosai kin ga wanan ai baby ba zai iya sha ya koshi bako? Hannu ta sanya ta rufe idon ta

    kasa kasa tace
    “yaya Fahad ai zai girma baza’a daɗe ba domin haka na Aunty hiyana da kuma Aunty diyana ma….. Bata karisa maganar ba ta fashe da kuka saka makon tunu da diyana da tayi

    Chikin sauri ya zame hannun sa daga kan yan breast nata ya rungumota sosai chike da rarrashi yace

    “kukan me kike? Chikin kuka take faɗin

    “yaya Fahad wai taushe Aunty diyana zata dawo ne?

    “Aunty diyanar ki ai ta dawo yau da safe”

    zubur ta miƙe daga jikin sa tana zaro ido da mamaki ta kasa magana,

    hannu ya sanya ya jawota ta faɗa saman kirjinsa ya rungume ta sosai a kunne ya raɗa mata

    “karki yi magana kiyi shiru kinji Allah yaji kukan mu ya dawo mana da yar uwar mu anjima da safe zan haɗaku video call yanzu dai kin ga anfara kiran sallan asuba bari naje na shirya zuwa masallaci sai na dawo” ya karisa maganar ya manna mata kiss a kumatu,
    Ya zareta daga jikin sa ya kwantar da ita ya miƙe chikin sauri dan lokaci ya tafi, almost 5:15am sauri sauri ya watsa ruwa ya shirya chikin jallabiya ya fito Lokacin har an fara Sallah, kallon in da take kwance yayi chikin sauri yace

    “lokacin Sallah yayi ki tashi kiyi alwala kiyi sallah, yana gama faɗin hakan ya wuche ba sauri ya nufi masallaci.

    BGS HIYANA

    6am dai dai ya dawo💖The Talent Troupe Writer’s 💖

    Wannan page ɗin sadaukar wane gareki masoyiya Gidan Aunty ya Allah ya baki lfy Allah yasa kaffara ce

    💖Story And Written💖
    ⬇️
    *Star lady*

    Duk mai buƙatar littafin bDuk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

  • Duk Karfin Izzata Book 2 Page 23

    Book 2

    Page 23

    Uk

    4:40am ya farka daga barci slowly ya waro idon sa waje kyakkyawar face nata ya fara chin karo da shi ba karamin kyau hasken blue light na ɗakin ya ma face nata ba, barcin ta take chikin kwanciyar hankali ya ɗan ɗauki mintoci yana kallon face nata kafin ya miƙe zaune tare da zuro kafafun sa kasan kagon gently ya miƙe ya fara tafiya toilet ya nufa brush yayi sannan yayi wanka ya fito ya shirya chikin fara jallabiya ya fice daga ɗakin ya nufi masallaci

    Yana fita ba jimawa ta farka da kyar ta iya buɗe idon ta dan barci bai ishe taba kiran Sallah ne ya tashe ta mikewa tayi ta nufi toilet jim kaɗan ta fito ɗaure da towel jallabiyar sa ta sanya ta sanya karamin hijabi tayi sallah zama tayi saman dadduma bayan ta idar da sallan ta fara yiwa diyana addu’ar Allah ya bata lfy sai karfe 6am dai dai ta tashi daga kan daddumar ta naɗe ta mai da mazaunin sa

    Toilet ta fara wanke wa kafin ta fito ta gyara masa ɗakin tsab ta sanya wani daddaɗar turare ɗaki mai bala’i kamshi sai da ta gama komai sanna ta wuce dressing nashi ta chire masa jallabiyar sa ta ɗaura towel ta dawo ta tsaya a gaban mirrow kallon kan ta tayi sosai kafin tace “Allah sarki yaya Prince wlh yanzu zan ɗaura ɗamarar ya kar ka a gidan nan domin son ka yana neman halakani dole nayi amfani da shawarar Aunty farida, da wanna tunani ta fara shafa body lotion nashi masu kamshi da tsada bayan ta gama ta nufi trolley ɗin ta sosai ta shiga wargaza kayan nata tana neman kayan da sukafi lallacewa wadda idan ka sanya zatayi kama da karuwar gaske koma abun da ya fi karuwa chan kasan babban trolley ta samu wasu wanduna da ba zasu wuchi chinyar taba da yan rigunan su masu kama da singlet ɗaga rigar tayi tana kallon rigar ba zata wuci chibiyar taba murmushi tayi ta mai da ta ajiye tana faɗin “wanna sai da daddare” kara watsa kayan tayi sosai wani shegen wando ta sake chin karo da shi shima ba zai wuchi guiwar ta ba sai dai shi rigar sa zata saukar mata zuwa marar ta da rigar da wandon duk jikin su robane, miƙewa tayi da su a hannun ta tana murmushin chikin sauri ta sanya su tanayi tana sanyawa Zahra albarka da addu’ar Allah ya bata baby mai kyau kamar yaya Khalid ɗin ta, sai yau taji daɗin kayan da Zahra ta zaɓa mata, sosai kayan suka kamata sunfitar mata da ainihin surar jikin ta ba karamin kyau tayi ba ta zama kamar waruwar gaske

    bayan ta gama sanya kayan ta kwashe wayan da ta fitar ta mai da chikin trolley ɗin sanna ta nufi gaban mirrow wow ita da kanta tasan tayi kyau sai dai mugun kunya take ji yayay Prince yazo ya ganta a haka tara gashin kanta tayi ta ɗaure a tsakiya da gangan ta ɗauki perfume nashi ta sanya a jikin ta dan ta lura idan ta taɓa wani abu nasa hakan yana sa yazo jikin ta da niyar hukun tata saman gado ta koma ta kwanta tana tunanin ya kamata a che ya yaya Prince ya dawo yanzu, bata kai ga rufe tunanin nata ba sai gashi ya shigo kallon ɗaya ya mata ya kau da kai ya wuce ya nufi toilet har ya kai bakin kofar toilet ɗin ba tare da ya juyo ya kalleta ba kasa kasa yace “ki fitar min da kayan sawa da suka dace da ni” yana kai karshen maganar ya shege toilet ɗin tunani Hiyana ta farayi ki fitomin da kayan sawa da suka dace da ni kenan yana nufi wanda na fitar masa jiya basu dace da shi ba kenan? to ni ya za’ayi in san wan da suka dace da shi kai dole na tambayi Aunty farida ta faraɗamin wasu kayane sukafi dacewa in rinƙa fitar masa idan ya buƙaci dana fitar masan da wanna tunani ta miƙe ta shiga dressing room ɗin,wandon jeans baki da t-shirt ash ta fiddo masa da shi ta ɗaura saman gado ta wuce kitchen dan ɗauko masa breakfast

    lokacin da ta dawo ɗakin har ya fito yana shiryawa godiya tayiwa Allah da ya sanya tafita kafin ya fito ba dan haka ba da zata iya sumewa dan shi yaya Prince ba ruwan shi bai san kunya ba zai iya shiryawa ma a gaban ta,bakaramin daɗi taji ba ganin yau ya sanya kayan da ta zaɓa masa

    saman table ta ajiye masa trey mai ɗauke da kayan breakfast ɗin,tana kokarin zama saman sofa sai ta tuna massage ɗin yaya Khalid in da yake chewa ta rinƙa taya bgs sanya kaya da sauri ta fasa zamar ta miƙe ta karisa wajen sa dai dai lokacin yana sanya buttin ɗin rigar, ba tare da tayi magana ba ta sanya hannu chike da tsoro kirjin ta na dukan uku uku ta fara tayashi sanya wa, kasa kasa yake satar kallon ta mamaki ne ya kama shi wato yarinyar nan ta dai na tsoron sa kenan,amma duk da hakan ya ji daɗi sosai har chikin zuciyar sa da ta taya shi sanya buttin ɗin afili kuwa ɗaure fuska yayi chikin tsawa yace “ke me haka!? Chikin sauri ta chire hannun ta daga saman rigar nashi da cool voice tace “kayi hakuri ba zan sake ba” ko kallon ta bai sake ba ya chi gaba da sanya buttin ɗin sa bayan ya kammala ne ya wuce saman sofa mai zaman mutun uku ya zauna da sauri ta karisa wajen ta fara sarving na shi sai da ta gama komai ta tura masa gaban sa sanna ta tsugunna chikin girmamawa tace “yaya Prince dan Allah ka kiramin Aunty farida” da hannu ya mata nuni da wayar sa dake saman bedside drawer ba tare da yayi magana ba miƙewa tayi ta ɗauko wayar ta dawo ta miƙa masa tare da ɗan tsayawa daga gefe layin Aunty farida ya kira wayar na fara ringing ya miƙa mata

    Ansar wayar tayi ta nufi kofar fita dan ta koma palo bata son yaji me zatace tsawa ya daga mata wadda ya sanya ta juyowa ba shiri “in zaki je!? “Palo zanje” ta bashi amsa chikin tsoro batare da ya kalli in da take ba ya mata nuni da hannun sa akan ta wuce wajen hutawar sa tayi wayar achan,ba musu ta wuce ta nufi wajen already Aunty farida tayi picking call ɗin tun ringing na farko duk abun da ya faru a kunnen ta ya faru tana jin su, zaman saman sofan dake wajen hiyana tayi kafin ta manna wayar a kunnen ta ta fara magana

    “Hello Aunty farida in kwana” “my Hiyana kina ji yanzu ba gaisuwa zamuyi ba kin ga wayar sa ne kuma lokacin tafiyar sa wajen Aiki yayi kawai muyi abun da ke gaban mu yanzu wani chi gaba aka samu”shiru hiyana tayi tana ɗan muku muku bazata iya faɗaqa Aunty farida chewar Bgs yayi kissed nata ba,jin tayi shirune ya sanya Aunty farida tace “my hiyana karki ɓoyemin komai ki faɗa min da wuri kinga bamu da time ko, sunkuyar da kanta kasa kayi tamkar Aunty farida na gaban ta chike da jin kunya ta fara bata lbr duk abun da ya faru tsakanin ta da bgs,murna sosai Aunty farida tayi kafin tace “yanzu bari na faɗa miki kayan da ya dace kirin ka bashi da lokacin da suka dace idan ya dawo aiki kinga yana bukatar ya huta ya sha iska to wannan lokaci kananan kaya zaki fitar masa dan su yake buƙata idan ya shiga wanka da daddare kiyi sauri fitar masa da kayan barci masu laushi kuma Prince ya fison abu fari komai nashi farine yana son kalan fari sosai sai ki kula da wanna ma idan da safene to kayan Aiki zaki fitar masa idan kuma ranar weekend ne to ki karanche sa shin yana fita weekend ne idan yana fita to kaya masu kyau da tsada zaki fitar masa irin jeans da t-shirt ba manyan kaya ba aikema ranar kinyi wauta Prince baya sanya kayan hausawa idan ba dole ba, abu na gaba idan kuma baya fita weekend to jallabiya zaki fitar masa sanan ki rinƙa rigasa tashi sallar asuba dan idan ya shiga wanka ki fiddo masa da jallabiya da zai sanye yaje masallaci,yanzu dai sai mu bari haka sai anjima zan kira ku ta wayar Auta akoi wani shirin da zamuyi kuma ki dage akan shawarar Khalid da Aryan yanzu ki mai da masa da wayar sa dan naga lokacin ya tafi zaije wajen aikin sa kar kije kiyi laifi rike masa waya da kikayi” miƙewa tsaye tayi kafin tace “to Aunty farida na gode sosai” “ba sai kin min godiya ba ke dai ki chigaba da yin abun da na faɗa miki In Sha Allah mun kusa nasara” a chikin zuchiya ta amsa da amin tare da chiro wayar daga kunnenta bata iya komai a wayar san nan ba dan haka bata katse kiran ba ta mai da masa da wayar yana zaume saman sofa kamar yadda ta bashi haka ta dawo ta same sa kusa da shi ta zauna tare da miƙa masa wayar tana faɗin “gashi yaya Prince Nagode” an sar wayar yayi tare da miƙewa ya fice daga ɗakin,bin bayar sa da kallo tayi har ya fice, tana kokarin miƙewa sai gashi ya dawo ɗakin a tsakiyar ɗakin ya tsaya tare da miƙa mata hannu sa alamar tazo ta ansa miƙewa tayi chikin sauri ta kariso wajen sa sim card nata ya miƙa mata tare da faɗin “now zaki iya kiran kowa sister ki ta dawo dai dai” yana kai karshen maganar ya juya chikin sauri tace “yaya Prince to dan Allah kasamin kati awayar” ba tare da ya juyo ba yace “akoi card a chiki” “to yaya Prince dan Allah ina neman wata alfarma ma” sai lokacin ya juyo yana kallon ta tare da dakatawa da tafiyar da yake takowa tayi a hankali tazo kusa da shi chikin sanyi murya tace “yaya Prince ina son abubuwa da ɗan dama ina son perfume ina son kayan sawa ina son…sai kuma tayi shiru ta fasa faɗe, kallon ta yayi from head to toe kafin yace “wayace ki sanya min perfume na? Waro ido waje tayi tana nadamar tambayar sa da tayi yanzu gashi ta tonawa kanta asiri, harara ya wurga mata kafin ya sake chewa “ki shirya muje” yana kai karshen ya juya “yaya Prince bani da kayan masu hankali a chikin akwatin wanda zan sanya na fita” “ki sanya jallabiya ta” ya kai karshen maganar tare da ficewa tsalle ta buga tana dariya da sauri ta wuche dressing room nashi ta ɗauko jallabiyar sa ta sanya jallabiyar ya fi karfin ta har jaa yake a kasa sosai itakam bata damu da yawan da jallabiyar ya mata ba sai murna take ta fito daga ɗakin baya palo dan haka sai ta wuche ta nufi harabar gidan

    Yana zaune chikin motar sa sunyi reading tafiya da alama ita suke jira tsayuwa tayi ta rasa wani mota zata shiga chikin sauri Abdol ya buɗe motar ya fito ya buɗe mata gidan baya in da Bgs ke zaune,satar kallon sa tayi ta kasan ido taga ko ya kalli abun da Abdol yayi kuwa ganin ko kallon in da suke bai yi bane hankali sa na kan system dake saman chinyar sa, hakan ya sanya ta tako jiki ba kwari ta shiga kusa da shi ta zauna tana jiran taji me zai che rufe motar Abdol yayi ya buɗe gidan gaba ya shiga mazaunin driver ya tayar da motar da matsanancin gudu suka bar gidan

    wani katafaren shopping mall suka shiga bayan sunyi parking Abdol ya fito ya buɗewa Bgs ɓangaren sa sanan ya buɗe wa hiyana,kusan a tare suka fito sai kallon wajen take tana satar kallon sa gaba yayi ta bi bayan sa Abdol ya rufa musu baya tun kafin su shiga chikin wajen ya sanya face mark a face na shi

    Suna shiga chikin shopping ɗin Abdol yayi saurin ɗauko masa kujera ya zauna tsayuwa hiyana tayi kusa da shi dan ita gaba ɗaya wajen ma tsoro yake bata da ɗan tsawa Bgs yace “ki wuce kije ki ɗauki abubuwan da kike bukata mana kina ɓatamin lokaci!” Tsuke fuska tayi kafin tace “ni wlh yaya Prince tsoron wajen nake ji ba zan iya zuwa ni kaɗai ba sai dai ka rakani” a sukwane ya ɗago kai yana kallon ta lokacin guda taji numfashi ta ya tsaya dan irin kallon da ya mata tsoro take kar yace an fasa sayan komai su koma gida,kallon ficekar hiyana Abdol yayi kafin ya juyo ya kalli Bgs chikin girmamawa yace “sir let me escort her tun da tana tsoro” wani mugun kallo Bgs ya wurga masa wadda ya sanya shi juyawa ba shiri ya ɗauke kansa daga garesu ya mayar yana kallon kofar shigowa,miƙewa bgs yayi yana faɗin “wuce a mai daki gida tun da ba sayyayyar zaki yi ba” yayi maganar tare da kama hanyar fita chikin sauri ta riko hannun sa tana faɗin “dan Allah yaya Prince kayi hakuri ka rakani karkace mu koma wlh ina bukatar kayan ne” ta karisa maganar kamar zatayi kuka juyowa yayi ya kalleta kafin ya saukar da kallon sa kan hannun sa da ta riƙe ganin hakan ya sanya ta sake masa hannun sa da sauri chigaba yayi da tafiya har ya fice daga wajen,tsayuwa tayi a ranta tana faɗin “yau zan gani rashin imanin ka ya kai ka iya tafiya ka bar ni a nan ne ko kuma akoi sauran imani a zuciyar ka kuma wlh ko kasheni zakayi bazan fita shopping ɗin nan ba har sai mun yi sayayyan nan bare ma ba abun da ka isa kamin yanzu dan Ammi ta sanar dani bazaka kara buguna ba wlh yau sai nayi maganin ka sai ka sauke girman kan nan naka yau” tana tsaye tana kallon su ta chikin glass har suka tada motocin su suka fice daga shopping ɗin waro ido waje tayi tana kallon su har suka kurewa ganin ta hawaye ne ya fara gangarowa a kan kuncin ta nan take tafara na damar dama bata biyewa zuchiyar taba da ta bishi sun tafi ta hakura da sayayyar yanzu ya zatayi tayiwa mijin ta laifi yayi magana ta ki bin maganar sa wai menene ya shiga kanta wayyo Allah” chikin kuka ta sanya hannu a aljihun jallabiyar jikin ta ta chiro wayar ta ta kira layin yaya Khalid bugu ɗaya ya ɗaga chikin kuka ta sanar da shi abun da yake faruwa dariya Khalid yayi kafin yace “kiyi sauri fitowa daga wajen ki ɓuya ta inda ba wan da zai ganki ganinan zuwa dan ina da tabbacin zai aiko a ɗauke ki amma bari muyi wasa da hankalin sa kaɗan” haka ko akayi chikin sauri ta fito daga wajen kamar yadda Khalid ya umarce ta ta boye ta bayan wani hospital dake kusa da wajen, bata fi 10mins da tsayuwa a wajen ba sai ga motar yaya Khalid,kiranta yayi awaya akan ta fito su tafi da sauri ta fito har tana haɗawa da gudu ta shiga motar Khalid suka bar wajen suna tafi ba jimawa sai ga Abdol ya dawo shi kaɗai a chikin mota yazo ɗaukan ta chikin shopping ɗin ya shiga batanan tambayar mutanen wajen yayi suka sanar da shi ta fita tun ɗazun juyawa yayi ya koma wajen motar sa ya ɗauko waya ya fara kiran layin Bgs sau biyu yana kira Bgs bai ɗaga ba sai a na uku ne ya ɗaga murya har rawa yake Abdol yace “sir madam fa bata wajen ta fita ta tafi” daga tsayan ɓangaren Bgs ya ja tsaki kafin yace “to ina ruwa na ka dawo ka chigaba da aikin gaban ka” yana gama magana ya katse kiran,shiru Abdol yayi yana tunanin hali irin na ogan sa wani lokaci abun ma mamaki yake bashi mutun ne kamar ba mutun ba bazaka gane me yake so me baya so ba yanzu fa shi yache nazo na ɗauko yarinyar nan amma danache bata nan ya nuna halin ko in kula bayan kuma kallo ɗaya zaka masa kasan ya ɗauki yarinyar da mahimmanci kai Allah dai ya shiryamin oga na amma gaskiya zan so ganin ya wanna wasan nasu zai kare shida sister nan tasa Allah ya sama kar a ganta har dare muga ya zaiyi dolene ma yaje neman ta ko dan iyayen su, da wanna tunani Abdol ya shiga motar sa ya bar wajen

    to masu karatu mu koma Nigeria muga me sukeyi kafin mudawo kila yaya Khalid ya dawo mana da hiyanar mu

    Kano

    Zaune take saman sofa a palon habibin ta tana buga game da wayar sa ta sha kwalliya sosai jikin ta na sanye da dogiwar riga abaya pink color kanta babu ɗan kwali ta saki gashi har gadon baya tana taunar chewing gum tayi nisa chikin game da take bugawa kamar daga sama aka fisge wayar daga hannun ta a zafafe ta ɗago kai ganin yaya Aryan ne ya sanya ta turo ɗan karamin bakin ta tana faɗin “kai yaya Aryan me haka ne dan Allah” hararar wasa ya wurga mata kafin yace “wai ke baki da Aiki sai buga game to ki tashi kije ki ɗauki Kur’ani ki fara karatu zanje na duba wata criminal ina dawowa ba jimawa” miƙewa tayi tsaye chikin jin haushi tace “daman kana da wata budurwace zakache kana sona? Kallon ta yake da mamaki ya mai mai ta kalmar nata “budurwa” “eh mana budurwa ba yanzu kache zakaje ka duba ta ba to idan ma bata da lfy ne Allah ya sa ta mutu” dariya abun ma yaso bashi wai yar karamar yarinya da kishi to ko me takewa kishi yanzu oho ita da bata san menene Auren bama tukun nan,ganin yayi shiru ne ya san ta fasa ihu tana faɗin “to ni wlh babu in da zakaje sai dai muje tare kuma wlh in dai mukaje sai na kashe ta” Aryan dai yau yaga ikon Allah yama rasa mai zaiche shi da zaije hukunta zulaihat me ya haɗa shi da budurwa wani tunanine ya faɗo masa shin ko dai diyana bata san ma’anar criminal bane tuna hakan ya sanya yayi kasa da murya yace “my jidda nifa mai laifi zanje hukun tawa ni da nake dake ina ruwa na da wata ko kin taɓa kallona ina magana da wata mace ne, ina chewa wayata awajen ki take zama kin taɓa kallon hoto ko number mace? Idan ba su Aunty farida ba” jin haka ya sanya tayi shiru ta sa hannu ta rufe fuska ita adole taji kunya murmushi ya saki tare da chire hannun da ta rufe fuska da shi yana faɗin “my jidda sarkin rigima wato har yanzu baki dai na ba ko? Faɗowa jikin sa tayi tana dariya “ni dai ban taɓa kallon mutun mai kuka da dariya lokacin guda ba sai ke my jidda kuka baya miki wuya kamar yadda dariya ma bata miki wuya” ɗan karamin bakin ta ta kafa a sai yin kirjin sa ta gabza masa chizo har sai da yace “wash my jidda to laifin me kuma nayi? da akamin hukunci haka”chikin shagwaɓa tace “Allah yaya Aryan ka chika neman magana to ni gaskiya ko ina ma zakaje sai dai mutafi tare dan naji kace wadda zakaje hukun tawa macece kar ina zaune a gida kai kuma kaje daga hukunci ku fara soyayya” rungumeta yayi sosai yana shafa lallausan gashin kan ta yace “my jidda nifa ke kaɗai kin ishe ni bana son ƙari ki kwantar da hankalin” ɗago kan ta tayi daga kirjin sa tana kallon face nashi tace “yaya Aryan to yanzu dai ka askemin gashin nan dan wlh yana damuna” juyawa yayi ya kamo hannun ta ta baya ya haurar da ita bayan sa ya goyata ya nufi hanyar fita yana faɗin “muje ki rakani wajen mota kuma idan kika kuskura kika taɓa min wanna kyakkyawar bakin gashin nawa sai na miki hukunci gaba ɗaya jikin ki wanna kyakkyawar gashin naki yafi komai burgeni” “kai yaya Aryan Allah ni kuma ban son gashi ni gaskiya askewa zanyi” tayi maganar dai dai lokacin da suka fito harabar gidan “to shikenan kina aske gashin naki ni kuma zan Aure mace mai gashi domin ni inason mace mai gashi sosai” hannu ta sanya da karfi ta za gashin kansa har sai da yace “wash haba my jidda” yayi maganar tare da sauke ta ɗaure fusaka tayi sosai tana faɗin “yanzu duk dogon gashin kan nan naka bai ishe kaba sai….ba ta karisa magana ba tayi shiru tare da juyawa ta bashi baya, murmushi yayi kafin yace “oh my goodness my jidda wai fushi kikayi kenan? to shikenan yanzu dai muje ki rakani wajen mota idan na dawo sai na rarrasheki sauri nake yanzu” make kafaɗa tayi tana faɗin “aa ni ba zan je ba na fasa rakiyar kayi tafiyar ka” juyawa yayi ya nufi parking space yana faɗin “Allah ya sa na haɗu da wata baby kyakkyawa a hanya nayi wuff da ita” jin abun da yace ya sanya ta juyo da gudu tayi tsalle ta haye saman bayan sa tana dariya,buɗe baki yayi zai yi magana wayar sa ta fara ringing,chikin sauri ya fito da wayar daga aljihun sa dan ya san call ɗin Bgs kawai yake expecting chikin sauri yayi picking call ɗin tare da manna wayar a kunne yana faɗin “hello my blood” daga ɗayan ɓangaren Bgs yace “ba sai kaje ba na sa an saki yarinyar” “What!!! Aryan ya furta azafafe tare da sauke diyana kasa daga bayan sa ya jingina da jikin motar sa “akan me zaka sanya a sake ta!? “Akoi dalili idan na gama da case ɗin zakaji” yana kai karshen maganar ya katse kiran juyowa Aryan yayi yana kallon diyana, gaba ɗaya yama manta bata da ɗankwali a kanta, “my jidda jeki ɗauko hijabi kizo mu tafi” “to” kawai tace ta wuce ta koma part nasu,binta yayi da kallo har ta shige ajiyar zuchiya ya sauƙe tare da ɗaga kai yana kallon sama jim kaɗan ta fito sanye da hijabi ɗan karami zuwa kirji,kallon ɗaya ya mata ya kawar da kansa tun bata kariso ba ya shiga motar gidan gaba mazaunin driver shiga ɗayan gefen tayi tana faɗin “yaya Aryan daman ka iya tuka motane? Yau kenan bazaka tafi da wayanchan masu mummunar fuskan ba” girgiza kai kawai yayi ya tada motar yaja suka nufi gate dan ya lura idan ya biyewa diyana sai su kwana a nan, a bakin gate na gidan ya tsai da mota tare da sauke glass ɗin motar ya dubi Shahram yace “ni kaɗai nake son fita kuma ba lallai mu dawo yau ba” yana kai karshen maganar ya ja motar da gudu suka fice daga gidan

    Gudu yake shararawa sosai kamar zasu tashi sama chikin kankanin lokaci suka fita garin kano dai dai kafin su isa kwanan ɗan gora dake hanyar Zaria a wani ɗan karamin daji kusa da checkpoint na sojoji ya tsai da motar sa kusa da wata itacen mango dake fuskantar checkpoint ɗin, juyowa yayi yana kallon ta sai fakan kumbure kumbure kumatu take, murnushi ya ɗan yi kafin yace “my jidda sarkin shagwaɓa to yanzu kuma me nayi?ake fushi da ni” kara turu ɗan karamin bakin ta tayi tana wasa da ɗan yatsan hannun ta bata che da shi komai ba, jawota yayi ta faɗa saman faffaɗar kirjin sa ya fara shafa bayan ta yana ɗan bubbuga ta a hankali kamar yar baby “my jidda wai me nayi ne? Kasa kasa tace “ba kai ne ka rinƙa gudu sosai da motar ba da yanzu mum mutu fa? ni fa bana son na mutu ban sa kayan sojoji na riƙe bindiga kamin hoto ba” ɗago habar ta yayi suna kallon juna kafin yace “In Sha Allah babu abun da zai faru ba zaki mutu ba har sai kin haifa min baby’s dozin uku,dariya tayi sosai ta sanya hannu ta tana wasa da jikin rigar sa tace “yaya Aryan dozin uku fa kace kowani dozin guda goma sha biyu ne fa,tab ai ni ko baby uku ba zan haifa ba baby’s biyu nake so ɗaya takwarar Ammi ɗaya takwarar Abba shike nan sun ishe ni” haɗe fuskokin su yayi chikin tsananin kaunar ta ya fara magana “gaskiya my jidda ina son baby’s dayawa kuma ni bana son mata dayawa mace ɗaya ta ishe ni dan haka ki shirya ansan baby’s koda 12 ne kin ji? Ɗago ido tayi suna kallon chikin idon juna yayin ta shi kuma yake goggoga mata karan hanchin sa a saman nata yana shafa ta da hannu ɗaya “Yaya Aryan…bai bari ta yi maganar da take son yi ba ya haɗe bakin su waje guda waro ido tayi waje tana kallon sa ɗayan hannu sa ya sanya ya rufe mata ido chikin dabara ya kwantar da kujerar motar da suke kai kwanchiya yayi da ita a jikin sa bakin su manne da na juna zuro ɗayan hannun sa yayi ta saman rigar ta tare da kara matse ta a jikin sa sosai wani daddaɗar ajiyar zuchiya ya sauke lokacin da hannun sa ya sauka saman lallausan tula tulan breast nata chikin sauri diyana ta kwache bakin ta daga nashi tana kokarin miƙewa daga jikin sa ya sake jawota a kule tace “yaya Aryan ni ka sake ni akan me zaka taɓa min nono?” mamaki ne ya kamashi ji yadda ta kira sunan su ko ajikin ta wanna dole ya mai data makaran ta da islamiya dan ba abun da ta sani jawo ta yayi ta faɗa jikin sa ya kankanme ta da kyau ya fara yi mata raɗa a kunne “my jidda wanna fa kayanane pls karki hana ni wasa da su namiki alkawari iya wasa kawai zanyi da su ko ganin su ba zan yi ba” shiru ta masa kamar bata ji me yace ba ta fara kuka kasa kasa,ba tare da ya lura da kukan nata ba ya fara kokarin zuge mata zip ɗin gaban rigar ta ji yayi ana knocking na glass ɗin motar ba tare da ya miƙe ba ya sanya hannun sa ya sauƙe glass na motar kasa, kamar daga sama yaji anja kofar motar da karfi an buɗe ana faɗin “fito munafiki ka sato yar mutane zaka mata fyaɗe ko? daman tun da naga kayi parking na motar ka a nan na fara zargin motar irin wanna shirgegiyar motar awan nan dajin dole ayi zargin ta ashe ashe zargina gaskiya ne maza ka fito yau taka ta kare!!” ɗan ɗago kan sa yayi yana kallon masu maganar wasu sojoji ne su uku a tsaye suna riƙe da gun tsaki yaja tare da mai da kansa ya kwantar dan gaba ɗaya jikin sa a mace kokarin miƙewa diyana take dan ta tsorata ganin sojojin nan jikin ta har kerma yake kara sautin kukan nata tayi sosai, hannun ta ya kama ya sake jawota jikin sa

    chikin tsawa ɗaya daga cikin sojojin yace “lallai wanan ka chika marakunya bar gani ka fito daga babban gida kana yawo da wanna shirgegiyar motar yau zaka gane kuren ka ko uban ka bai isa ya fidda kai ba yau!!” shi dai Aryan ko kallon in da suke bai sake yi ba gashi yama kasa tashi gaba ɗaya jikin sa a mace, damkar kafar sa ɗayan sojan yayi yana jansa yana faɗin “ka fito daga chikin motar nan munafiki yau asirin ka ya tonu zaka gane kuren ka, ganin sojan nan ya damki kafar yaya Aryan yana jan sa ne ya sanya diyana ta fasa ihu tare da kara kankame Aryan ɗin ta
    waro idon sa waje yayi tare da yunkurawa zai miƙe zaune jan kafar sa da sojan chan ya riƙe yayi yana kokarin zama tafiya sojan yayi luuuu ya buga kansa da jikin stearin motar da kyar sojan ya ja kan sa ya fitar ya tsaya a gefe tsaki Aryan yaja tare da mayar da diyana saman nata kujerar ya zaunar da ita chikin dashewar murya ya bawa diyana umarni akan ta zauna a mota karta fito, kafafunsa ya zuro waje kafin ya fito gaba ɗaya chike da jin haushi ɓata masa farincikin sa da sojojin nan sukayi ya ɗauke babban su da wani gigitatchiyar mari wadda sai da sanya shi tangal tangal kamar zai faɗi lokacin guda yaji duniya ta tsaya masa chak gaba ɗaya kunnen sa ta dai na jin sautin komai marin Aryan fa ba wasa ba, a zafafe sauran sojoji biyun suka ɗaga gun suka sai ta Aryan da shi suna faɗin “kneel down”

    To masu karatu sai mun haɗu ranar Monday idan mai dukka ya kai mu ku bini bashin 2 page love u all

    💋Duk Karfin Izzata 💋

     

    💖The Talent Troupe Writer’s 💖

    💖Story And Written💖
    ⬇️
    *Star lady*