Blog

  • Arubuce Ta Ke 11

    Arubuce Ta Ke 11

    Iska mai zafi ya furzar daga bakinsa yana miqewa tsaye,kafin yakai ga aiwatar da komai mimi ta kama cikinta

    “Abba……yunwa nakeji,tun dazu mommy tace zata dafa mana indomie……bata gama bane har yanzu?” Idanunsa ya zubawa yarinyar,a nutse yace

    “Bakuci abinci bane yau?” Kai ta gyada masa

    “Eh,momy tace tana jin bacci,kada mu dameta,musha tea,idan ta tashi zata dafa mana,har nawwara ma ta zuba ruwan tea din a qafarta,tayita kuka” lumshe idanunsa yayi,wani abu ya taba ransa,sai ya duqa a hankali tana laluben qafan yarinyar yana son ganin wajen,dai dai sanda yaji an murda qofar an kuma budeta,sanin waye ya sanyashi qin waiwayo yaci gaba da duba qafar nawwaran.

    Matashiyar macace,wadda a qalla zata doshi shekara ashirin da takwas ko kuma da tara,wankan tarwada ce wadda kalar fatarta ta kusa juyewa ta baqaqe,banda hutu da jin dadin data samu,mai matsakaicin tsaho ce,tana da ‘yar qiba kadan da tudun hanci,idanuwanta basu fiya girma ba,saidai tana da ‘yar cikar gira da kuma fararen haqora da suka sake bayyana duhun fatarta.

    Sanye take da kayan bacci a jikinta,kanta saye cikin wata hular zaren lilo da qabilu sukafi amfani da ita,zaka tsammaci qarfe bakwai ne na safiya a lokacin,saboda yadda fuskarta ke nuna alamu na bacci,uwa uba kuma sleeping dress din da take sanye dashi.

    Tsaye tayi daga bakin qofar tana qare masa kallo,fushi takeyi dashi sanda ya tafi,ta kuma ci alwashin sai yaga fushin nata,saidai tun bai jima da tafiyar ba kewarsa ta dameta,idanuwanta kuma suka damu da son ganinsa,ta ajeshi qololuwar matsayi a rayuwa da kuma zuciyarta,shi din na musamman ne,tunda har yana da qarfin ikon juyata da sauya mata ra’ayinta zuwa wadanda yakeso,abu mafi girma kenan dake haddasa sabaninsu,kowa da alqiblar da yake kalla tsakanin shi da ita,hakanan kowa yana ganin akan dai dai yake.

    Ci gaba tayi da kallonsa har ya gama duba qafar yarinyarshi,ya kuma tofa mata addu’o’i,tayi tsammanin zai waiwayo gareta ne tunda yaji shigowarta,amma sai taga yana yunqurin miqewa hadi da sake baiwa qofar baya,don haka ta saki hannayenta data rungume tana qarasowa cikin dakin,bayan ta dan bata fuska

    “Dama kuna nan kuka sanyani inata bulayin nemanku cikin gida?,sai dana fita gate sule yacemin ya ganku tare?” Maganarta ta qarshe ta sanyashi waiwayowa,idan ba gizo idanunsa yayi masa ba yaga shacin kayan bacci a jikinta,tana nufin haka ta tafi wajen sulen nemansu,mutum ne shi mai tsananin kishi,ko kusa ko alama baya daukan sakaci ko ganganci akan iyalinshi

    “A hakan kike tafi cigiyarsu har waje?” Ya jefa mata tambayar a nutse,saidai kuma wani bacin rai na daban bayan wanda yake ciki ke bijiro masa.

    Sai a sannan kwanyarta ta ankarar da ita zallar wautar data tafka,duk yadda taso taja zarenta itama har sai ya gane yayi mata laifi ya bata haquri take komai ya rushe mata,saidai cikin sa’a ta kama zaren qaryar da takejin zata qwaceta

    “Ta yaya zan fita a haka?,na cire hijab dina a falo” tana gama fada ta kauda qwayar idanunta daga cikin nasa,tana jin yadda yaketa kokawar ganin sun hada idanun,hanya guda daya da yake iya karanto qarya ko gaskiyarta,ta saara masa ta wannan fannin,kuma tasan ba banza ba,tunda aikinsa ne.

    Bayason ya sake dagula al’amuran,dole shima ya janye nasa idanun

    “Koda wasa,koda ganganci kada ki sake hakan ta faru” ranta ya baci,ta zumbura baki gaba,daqyar kamar wadda aka yiwa dole tace

    “Tom” saita maida dubanta ga yaran ba tare data wani damu da yi masa sannu da zuwa ba ko tambayarsa hanya

    “Kuka sani dafa muku indomie ashe ma ba yunwa kukeji ba kuka katsemin bacci na” sai taja dan siririn tsaki

    “Saiku tashi muje kuci,idan kuma bakwaci a bayar da ita” mimi ce ta maqale kafada

    “Nidai mommy banason indomie” ta hasala sosai,dama ga fadan da yayi mata

    “Baki isa ba tunda na dafa sai kunci”

    “Ji mana” ya dakatar da ita,saita waiwaya tana dubansa,ya ritsata da idanun nan nasa dake kassarata,bata buqatar ta sauko don haka ta kauda kanta

    “Babu lallai yaro sai yaci abincin da ya riga ya ginsheshi,ki deba musu cikin abinda kika dafa min,sauran ki kawomin shi falo na” fuska ta bata,cikin jin shakka murya ciki ciki tace

    “Ni ban dafa maka komai ba” ya zuwa yanzu mamakin hafsat ne ya kamashi,cikin son danne bacin ransa yace

    “Saboda me?”

    “To ai bakacemin ka taho ba”

    “Bakisan yau zan dawo bane?”ya jefa mata tambayar cikin salo na tsitsiye,saita rasa amsar bashi,saboda wayar qarshe da sukayi bayan sun gama ya tura mata tex na date da time na dawowar tashi,kawai ta share ne saboda tana jin haushinsa,tazo kuma ta raba dare tana kallo,shi yasa da safen ta dinga barci kamar matacciya,sai da yaran suka dameta da kukan yunwa sannan ta rarrafa ta dora musu indomie,ta rage wutar ta koma baccinta bayan ta zuba komai da komai,da nufin ta sake matsewa kafin ta dahu,a wannan tsukin ya shigo,kuma har ya kwashe yaran bata snai ba,uwa uba ma kuma manta shaf da batun dawowar tashi.

    Idanunsa ya lumshe yana jinjina kai,ya taka zuwa gaba kamar bazaice komai ba,sai kuma ya dakata ba tare da waiwayo ba yace

    “Ki gyaran sashe na,sannan ki dafa min abinda zanci kafin na gama” daga wannan ya wuce bandaki.

    Da kallo ta bishi har ya kammala wucewar ya rufe qofa,janye idanunta tayi tana sauke gauron numfashi,sai kuma tsaki ya biyo baya,bata dauka zai dauki abun da sauqi haka ba,duk da tasan halinsa,yakan iya share laifi yayi kaman ba’ayi masa ba,amma horonsa kuma sai yafi miki ciwo fiye da komai,a duniya babu namijin da ya taba yi mata abinda abbas din yake mata,batasan wanne irin so take masa ba daya samu dama da yawa yake juyata har haka ba,saita dakata da tunanin ganin bata da isashen lokaci,ta tarkata kan yaran ta sauka dasu zuwa sashenta,ta juye musu indomie din duk da sunce ba zasu ci,ta kunna musu kallo ta wuce kitchen tana tunani me zata dafa wanda bazai jaa mata lokaci ba.

    Sai data kwashe mintuna kusan biyar tana dawurwurar abinda zata dafa masa cikin kitchen din,daga bisani ta yanke dafa masa jallop din taliya,duk da tasan cewa kwata kwata bata cikin lissafin abincinsa,hasalima saboda ita da yara yake ajjiyeta,banda haka tasha zamanta,to amma kuma bata da wani sauran option,hakanan bata da idea din wani abu me sauqi da sauri baya ga taliyar,kuma koma meye dai oho,indai ta dafa ta bashi ai ta fita ko babu sabulu.

    Sai data wanke tukunyar da zata dafa abincin a ciki,saboda tun jiya datayi baqi qawayenta ta bata su gaba daya,ta kuma jiqasu sa zummar yau idan ta tashi aiki ta tsaftacesu,sai gashi kuma yayi mata dawowar ba zata.

    Tana hada girkin tana mita cikin ranta,taja tsaki yafi a qirga

    “Dole ne ma na samo ‘yar aiki gaskiya,haba dame zaka ji?,kashe kanka zakayi?” Ta dinga gunaguni ita daya,tuntuni takeson daukar mai aiki,amma saboda wani banzan ra’ayi nashi da kuma kafiyarsa yaqi aminta,alhali kuma aiki yayi mata yawa,ga yara gashi karan kansa.

    Sanda ta gama ta juye masa a plate ta sanya wani ta rufe ta fito,a falon ta samu su mimi duka sun sheme barci ya daukesu,bacci dama sukeji,amma yunwa da rashin kyawun tsaftar jikinsu ya hanasu yin baccin,ga indomie dinta nan sunci wadda zasuci sauran sunyi wasa da ita sun sake d’aid’aita falon,sai a sannan ta lura da wankan da yayi musu,baki ta tabe

    “Kwado sarkin tsafta,ni wallahi bazan kashe kaina da wannan shegen son tsaftar taka ba” daga haka ta sanya kai tana ficewa zuwa sassansa.

    Zaune ta sameshi saman kujera riqe da remote yana kallon labarai,armless white shirt ce a jikinsa da three quarter wine color,ya miqa dogayen qafafunsa saman center table din yana kadasu a hankali.

    Kallo daya yayi mata ya amsa sallamarta yana maida dubansa ga tv,ta qaraso dab dashi ta janyo daya table din ta dora plate din abincin ta matso masa dashi,a gajiye take jinta tubus don bata sanyawa ranta wannan aikin ba,don haka ta koma kan daya daga cikin kujerun ta zauna
    “Sannu da zuwa” hankalinta ya bata tayi masa a sannan,sai daya sauke qafafunsa qasa ya zauna sosai sannan ya isa amsa mata,ya bude abincin yana kallonsa yayin da ita kuma take kallonsa tana jiran me zaice,kamar bazaici ba,sai kuma ya sanya fork a ciki ya debo yakai bakinsa.

    Idanunsa ya ragewa girma yana tauna taliyar cikin bakinsa,kamar mai tauna mutuwa haka yaji,baisan ya zaima hafsat ba,baisan sai yaushe zata nutsu ta gyara tukunyarta ba,kudade da yawa ya kashe wajen ganin ta iya abubuwa da dama saboda inganta rayuwar aurensu amma har yau babu riba,tana sane?,mugunta ce ko kuma meye?,idan kishi ne da nuna masa zallar soyayya a baki ita din tana kan gaba,amma ya rasa abinda yake damunta.

    Salin alin ya maida murfin ya rufe sannan ya miqe ya wuce bedroom dinsa,binsa tayi da kallo tana jiran taji me ya faru?,ba jimawa ya fito sanye da jallabiyya mai santsi dinkin qasar morocco mai gajeran hannu

    “Ina key din mota ta?” Ya tambayeta yana sanya qaramar hula saman kansa,maimakon ta amsa masa saita miqe ta wuce gaba zuwa dakin nasa,ta jawo locker inda ta zuba muqullan ta dauko ts miqa masa,saiya karba

    “Banaso na dawo na samu wajen nan a haka” ya fadi yana yin gab,tana son tambayarsa ina zashi amma bai bata damar wannan ba,tun daga fuskarsa har yanayin yadda yayi mata ya fice ba tare daya bata hanzari ba.

    *_ASSALAMU ALAIKUM_*

    _Barkanmu da dare da fatan kowa yana cikin qoshin lafiya_

    _Akwai abinda muka turo tallansa na WOMEN EMPOWERMENT PROGRAM(KUDI KE KIRA),so please duk wadda batayi pyment ba ta jira tukunna kada tayi,akwai wani CONFIRMATION da mukeso mu samu a kansu_

    *Idan komai ya daidaita zamu sanar muku*

    *_idan kikaci gaba da pyment kuma bada yawunmu ba_*

    *Muna godiya sosai**H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • Arubuce Ta Ke 14

    Arubuce Ta Ke 14

    Page 14

    Ta tsakiyar mutane da suka cika a wajen ‘yan kallo ya samu ya ratsa ya koma motarsa,yabar mutane suna ta tattauna maganar,da yawansu hakan da yayi ya sake burgesu saboda diban albarkar yaron tayi yawa,yan bani na iya kuma na ganin baiken hakan,suna ganin kamar yayi amfani da qarfin ikonsa ne.

    Abinda ya faru akan hanyar ya qarawa kansa zafi,ransa ya dinga sosuwa duk sanda ya tuna girman shekarun mutumin da abinda qaramin yaro yayi masa,a nutse yaci gaba da tuqinsa har ya shiga unguwar tasu,qofar gidansu yayi parking,yana shirin fita a motar sukaci kacibus da qanin mahaifinsa suka tsaya suna gaisawa,wannan yaja masa jinkirin shiga gidan,sai bayan la’asar sa wasu ‘yan mintuna bayan sunyi sallar la’asar a masallacin qasan layinsu sannan suka taho tare da kawu hassan din,yanata masa godiyar uban gudunmawar daya bayar na auren diyar kawu hassan din,har suka iso gida,kawun ya shige gidansa dake jikin gidansu abbas din.

    Tun a harabar gidan ya fuskanci kamar gidan yau ba iya mutanen gidan bane kawai a cikinsa,muneera dake wanke alayyahu cikin famfon dake baiwa shukokin da suka qawata harabar gidan ruwa ta amsa sallamar tasa gami da gaidashi ya amsa mata,har yaa taka zuwa gaba sai ya tsaya cak ya waiwayo ga muneera

    “Hajiya na ciki ne?”
    “Eh sallah takeyi” fasa shigar yayi,saboda hayaniyar daya danji,a yanzun kuma ba abinda yake buqata sai zaman shuru,don haka ya juya akalarsa zuwa sitting room din baqi dake harabar gidan daga gefe

    “Idan ta idar ki gaya mata na shigo,amma zan dan kwanta kadan”

    “To uncle” ta amsa masa tana daukan kwandon alayyahunta tayi ciki,shi kuma ya murza key din daya gani a jiki ya bude falon ya shiga.

    Yasan tsaf falon yake,duk da ba shigarsa akeyi akai akai ba,babu inda hajiyarsa ke bari da qazanta cikin gidanta,koda kuwa ba’a amfani da wajen,bata lamutar datti ko qura,wannan yasa babu haufi ya nufi daya daga cikin kujerun Three sitter ake falon yayi kwanciyarsa,ya miqe bayansa sosai saman kujerar yana lumshe idanunsa hadi da sakin ajiyar zuciya,yanason baiwa kwanyarsu hutu,bayason tuna komai da zai dameshi.

    Minti kusan goma yana a haka,yanata kokawa da tunane tunanen dake kwanyarsa,saidai surutai da ‘yan iface ifacen dake gilamawa kadan kadan ta wajen nadan damunsa lokaci bayan lokaci,bai wani dameshi da yawa ba,wannan ya sanya yaci gaba da barin idanuwansa a rufe.

    Gigitaccciyar qarar data cika harabar gidan ta sanyashi durowa daga saman kujerar ba tare daya shirya ba,muryar nada matuqar kaifi da zaqin da zata iya huda kunnuwan duk wanda ke wajen,zaman dirshan yayi saman kujerar yana rufe idanunsa jin yadda qarar taqi tsagaitawa,ya rintse idanunsa yana jin yadda kansa ke sara masa sanadiyyar qarar,tsaki yaja dabmugun qarfi ya kuma miqe a fusace ya nufi qofa yaje yaga wanda ke qarar kamar wanda ake cirewa rai.

    A hankali ya yaye labulen ranshi a bace idanuwansa a farfajiyar gidan yana son ganin wanne tashin hankalin ne haka yake faruwa,idanunsa suka sauka a kanta,a lokacin ta jima da fara tsalle tana runtuma ihu hadi hadi da hawaye face face saman fuskarta,tuni ‘yar hular dake saman kanta tayi nata waje,gashinta da koda lafiya lau yake sabulewa daga jikin ribbom ya baje abinsa iska tana daukarsa.

    Idanunsa ya zube mata,yana qare mata kallo,me ya sanyata wannan tsallen a gigice?,kunama ce ta harbeta ko maciji ta gani?,saidai kunamar,don ya tabbatar cikin gidan nasu ba za’a samu maciji ba,sai ya rasa me ya kamata yayi,ihunta yana sake cika masa kunne,baikai qarshen tunaninsa ba hajiya ta iso wajen da hanzarinta ita da muneera,a rude take qoqarin kama widad tana tambayarsu nujood me ya sameta?,sai ya harde hannayensa a qirji,ya zauna a hankali saman hannun kujerar dake daura da qofar yana kallo da sauraren abinda yake faruwa

    “Kyankyaso ne ya shigar mata riga” idanunsa ya lumshe yana jin wani haushinta yana cikashi,kyankyason takema wannan kamar wadda taga mutuwa?,bai bude idanun nasa ba yayi shuru yana sauraren muryar hajiya tana cewa

    “Kyankyaso?,riga kuma?,garin yaya?”

    “Musaddiq ne ya saka mata(qanin nujood dake binta)”

    “Ashsha musaddiq baka kyauta ba” hajiya ta fada tana qoqarin kakkabe mata rigar.

    Hannu daya ya sanya ya sauke labulen,ya kuma tura qofar da qafa sannan ya koma saman kujerar ya kwanta kamar dazun yana sake jan tsaki,ko a ina hajiya ta samo su suka cikawa mutane gida da hayaniya?. Still idanuwansa suna rufe,yana jinta cikin sheshsheqar kuka tana gayama hajiyan yadda abun ya faru,ta yima musaddiq fada sosai sannan ta hada kansu suka wuce cikin gidan.

    Ana kiran sallar magariba ya wuce masallaci yayi sallah sannan ya shiga cikin gidan,zuwa sannan babu kowa daga hajiyan sai muneera

    “A’ah,shigowar magariba kuma yau kayi abbas?”

    “Ina nan tun sanda wannan tsanyar ke ihu” dan shuru tayi na sakanni,sai kuma ta saki murmushi

    “Wai widad?,aikin musaddiq ne wallahi”

    “Musaddiq din muhsin wai?,dama sune?”

    “Sune,a nan hajjaa ke barinsu,idan ta taso daga makaranta take daukansu,widad kam ai bata da hayaniya ko kwaramniya,shaqiyancin musaddiq dinne,yasan yadda take tsoron kyankyason ya saka mata shi” kai ya jinjina kawai ba tare da yace komai ba,sai a sannan hankalin hajiya kuma ya dauku ga fuskarsa,ya akayi har ya shigo gidan tun yamma bai nemeta ba,fuskarsa ta nuna akwai damuwa tattare dashi

    “Allah dai yasa lafiya” ta fada bayan sun gaisa,furzar da iska yayi daga bakinsa,ya motsa baki zaiyi magana ta datsi numfashinsa

    “Kada kacemin babu komai” shuru ya ratsa falon na wasu sakanni,sai ya buda baki a hankali yana gayama hajiyan zancan tafiyarsa kaduna da hafsat tayi tutsun ba zata je ba.

    Ran hajiyan ya dan tabu,tun ba yau ba tasan matsalar dake cikin gidanshi,ba yau ta fara gani da fuskanta ba,saidai batason shiga lamuran gidansa sam,hakanan a matsayinta na uwa bata da abinda zata masa illa addu’a da kuma bashi shawara na gari

    “Kayi haquri ka tafin,kada ka matsa mata,duk sanda ka samu sarari ka dinga zuwa kana ganinsu,ta wani fannin tana da hanzarinta daya kamata a duba,ko don karatun mariya(mimi) da yanzu ta farashi kada ya samu tangarda,zama da iyali dan haquri ne,mahaifanku dukka haquri sukayi damu har zuwa sanda Allah ya rabamu,komai yayi farko kuma yana da qarshe” ajiyar zuciya ya saki,maganganun hajiyan sai suka sake kwantar masa da hankali da sanya masa nutsuwa,kalmominta masu tsada ne da baiwa zuciya da kuma ruhi nutsuwa,take yaji gaba daya dukka wani kwadayinsa na tafiya kaduna da hafsat din yakau a take

    “Na gode hajiya” ya fada yana bude abincin data saka aka kawo masa,ya fara ci a hankali suna hira da hajiya,hirar da ako yaushe ita ke debe masa damuwa.

    Basu jima suna hirar ba babban yayansa ya shigo,wannan yaja hirar tasu,har yakai qarfe tara na dare,sai da zai tafi yace ya saukeshi a hanya,ya ajjiyeshin sannan ya wuce gida shima.

    Tun k’arfe takwas da rabi duka yaran sukayi bacci,ta kwashesu ta kaisu dakinsu ta kwantar dasu,ranta a jagule,kishi fal ranta,zuciya nata mata saqe kala daban daban kan inda ya tsaya din,don ba kasafai yake kaiwa dare haka a waje ba,koda zaikai din yana kiranta ya gaya mata zai kai dare din,tunda babu ta yadda aikinsu baya kamawa.

    Dakinta ta wuce bayan ta rage hasken falon,tanaso qwarai tayi wanka amma kuma tana gandar zuba ruwa a jikinta,saita zarme da zama gefan gadonta kawai taja wayarta ta fara chart.

    Batasan lokaci ya ja haka ba sai data ji qarar shigowar motarsa,ta sauke wayar tana duba lokaci,sai taci gaba da chart dinta,don tasan yawanci bai fiya dawowa shi kadai ba,kuma idan hakan ta kasance sai ya sallamesu kafin ya shigo cikin gidan.

    Duk da yasan babu lallai ya samu kowa a falon amma bai fasa yin sallama ba,ya dan bi falon da kallo,babu laifi,bai wani kacame can da yawa ba,duk da bai masa tsari yadda rai da zuciyarsa sukeso ba,kai tsaye dakin yaran ya wuce,ya tura qofa ya shiga,wutar dakin tana kunne,yabi yaran da kallo,ba alamun an musu wanka da zasu kwanta bare ayi maganar brush,kowanne cikinsu yana da kayan bacci qasa da kala goma goma,amma bazaice ya gansu dasu sau biyar ba,baima san inda take kaisu ba.

    Yadan jima a kansu yana musu addu’ar daya tabbatar bata musu ba,ya shafesu da ita,ya sake gyara musu kwanciyar ya lullubesu sannan ya kashe wutar dakin ya fito yaja musu qofar.

    Yana fitowa tana fitowa a nata dakin,kallon kallo sukayi a tsakaninsu,tanason ta karanci har yanzu ranshi na abace ne ko ya haqura?,duk da ba yau suka saba irin wannan ba,yayin da shi kuma yake kallon dressing din jikinta,kayan daya fita ya barta ne dasu,wanda tun safe suke jikinta,duk da yalwar suturu da take dasu masu tsada da kyan gaske,to amma fa idan ka gansu a jikinta wani babban sha’ani ya tashi da zata shiga dangi ko qawaye tayi bajinta

    “Sannu da zuwa” ta fada tana dan basarwa”

    “Yauwa,ya gida ya yaran?”

    “Alhmdlh” ta amsa masa tana mamaki,a yadda ya fita bata taba kawo saukarsa a nan kusa ba,amma sai taga kamar babu abinda ya faru

    “Anan zaka ci abincin naka?” Ta tambayeshi sanda taga yana takawa yana barin wajen

    “Zan danyi wanka,kamar nan da minti goma ki kawomin sashena” dan yatsina fuska tayi can qasan ranta tana mita,bayan wahalar girkin da tasha kuma sai ya sanyata wahalar diban cooler din abinci ta bishi dasu?,me yasa bazai zauna a nan yaci ba?,bata amsa masa ba har ya fice,sai ta juya ta koma daki abinta taci gaba da charting dinta.

    Da sauri ta miqe sanda taji agogi ya buga,minti goma sai data ninkasu wajen sau hudu,ta qara ya zama minti arba’in da kusan biyar ba tare data ankara ba,ta jefa wayar gefe ta miqe tana gyara daurin dankwalin atamfar dake kanta sannan ta fito tana gyara daurin zaninta daya dangale tana qoqarin daidaita tsahonsa.

    Har ya gama shirinsa tsaf ba ita ba alamunta,ba wani yunwa yake ji ba ya riga da ya take cikinsa wajen hajiyarsa,don haka bai wani damu ba can,dama kuma idan da sabo ya riga ya saba,sai ya dauko luggage dinsa ya fara shirya kayan da zai tafi kaduna dasu.

    Ya gama hadasu tsaf ya debo wasu takardu nasa yana dubawa,sai ya koma kan sofa dake dakin ya zauna yana dubawa cikin nutsuwar nan tasa.

    *_RIGIJI GABJI!_*🔥🔥

    *_WANI KAYA SAI AMALE_*🔥🔥🔥

    *FITATTUN ZAFAFAN DA BABU NA BIYUNSU*🔥🔥

    *JERIN GWANON LITATTAFAI ABOKAN TAFIYAR JUNA MASU MABANBANTAN LABARAI DA FASAHA*

    *_’YAN BIYAR DIN NAN NE FA_*

    *_SARAKAN LABARUN_*

    *NISHADI*
    *CAKWAKIYA*
    *GWAGWARMAYA*
    *BARKWANCI*
    *TSANTSAR DARASIN RAYUWA*

    *TARE DA*

    *ZAZZAFAN SALO NA SOYAYYA MAI RIKITA TUNANI DA TSUNDUMA MAI KARATU CIKIN TAFKIN SHAUQI*

    *SUN SAKE SHIRYAWA TSAF,DAUKE DA WANI TARAGO MAI CIKE DA LABARAI MASU ZAZZAFAN ZAFI!!!*

    *KIN SHIRYA MADAM?*

    *MAZA ANTAYA NAKI KUDADEN KIBI SAHUN AYARIN MATA MASU AJI TA HANYAR BIYAN KUDIN NAKI KARATUN WADAN NAN LITTAFAI KAMAR HAKA*

    *DAUD’AR GORA* Billynabdul

    *KI KULANI* Missxoxo

    *IDON NERA* Mamuhghee

    *RUMBUN K’AYA* hafsat rano

    *A RUBUCE TAKE* Huguma

    *ZAKI IYA BIYA KAI TSAYE TA WANNAN ACCOUNT DIN*

    0022419171
    Maryam sani
    Access bank

    Saiki tura shaidar biyanki ta wannan number

    09033181070

    *MASU TURA KATIN MTN KO VTU KUMA ZASU TURA WA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANSU*

    09166221261

    *Muna godiya da ci gaba da zabin zafafa biyar a koda yaushe*🙏🏾🙏🏾
    [2/13, 5:29 PM] +234 903 685 1413: *Arewabooks:huguma*
    *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • Arubuce Ta Ke 8

    Arubuce Ta Ke 8

    Page 08

    Cikin dakinta take tsaye,sanye da uniform na islamiyya,farin riga da wando da kuma hijab ne,sai baqar abaya da suke dorawa a sama,idan ta saka kayan sai ka dauka ita daya aka kebe aka yi uniform din don ita,tana da wani irin kyau da yasha banban da na yaran gidan dukkansu,innocent face ne da ita,duk da cewar a zahirance din ma bata fiya hayaniya ko rigima ba,bata da abokin fada idan bawai taso ba ko quruciyar ta motsa.

    Dukka jakar tata ta zazzage saman gadon tana kwashe tarkacen dake ciki gami da kauda su gefe daya,ta maida alqur’aninta ciki,tana shirin rataya jakar ummu ta leqo

    “Kin fasa zuwa islamiyyar ne?” Da fuskarta dake da qarancin walwala ta waiwayo tana dubanta,ssnnan ta buda baki a nutse

    “Zani”

    “To ai gwara ki hanzarta kada ki makara” ummu ta fada tana sakin labulen gami da juyawa,har cikin ranta bata jin dadin rashin walwalar widad din sam,gaba daya tun ranar ta koma wata sukuku.

    Plate takalmanta masu igiya ta daura,baqaqe da suka zauna suka yiwa fararen qafafuwanta kyau,saita fito a dakin,ta yiwa ummu dake zaune a falon sallama sannan ta fito farfajiyar gidan.

    Tana tsaka da tunanin ta tsayawa koda Aafiya ne su wuce tare ko kuma tayi tafiyarta hon din mota daga waje ya cika harabar gidan,ba tare da jinkiri ba baba awwa ya miqe ya bude gate din,baqar motar dake daukan idanu da sheqi ta sako kanta zuwa cikin gidan,hankalin widad ya dauku kan motar,kamar taso ta gane motar waye?,tunaninta yazo dai dai sanda baba awwa ya qarasa ga motar bayan ya rufe gate din yana fadin

    “Barka dai da sauka,barka da sauka mai gida muhsin” wani murmushi ne ya qwace mata,uncle muhsin?,uncle muhsin ne yazo?,mutumin dake cikin jerin sahun mutanen dake da girma da matsayi a rayuwarta,mutumin dake nuna mata kulawa kamar yadda yaga ummu nayi mata,gaba daya ta sha’afa ma da batun makaranta ta fito,gaba daya hankalinta ya tattara ga uncle muhsin din,wanda ko second daya bata qara a tsaye ba ta nufi inda ya faka motar tasa harda sassarfarta.

    Suna tsaka da gaisawa da baaba awwa din ya tsinceta a wajen,bakinta har kunne

    “A’ah,yammata sai ina?, islamiyya za’a je?” Farincikinta ya gaza boyuwa,ta gyada kai tana dariya gami da fadin

    “Uncle muhsin ka shammaceni,dama zaka zo?”

    “Gani kuwa widad,bakiji wajen alhaji ko ummu ba?” Kai ta girgiza still dai tana dariyar.

    Kafarta kafarsa suka shige gidan,sai daya fara shiga sassan ‘yan uwan nasa suka gaisa,tana biye dashi qafa da qafa,duk da hararar da take samu daga wajensu amma bata damu ba,anty madina ce ma ta tsokaneta

    “Batun tafiya makaranta ya tashi kenan?”. Dariya widad din tayi,sai uncle muhsin din ya juya ya kalleta

    “A’ah,ai ba za’a fasa zuwa makaranta ba saboda zuwa ne,kije ki dawo,ina nan ai” cikin shagwaba ta narke fuska

    “Don Allah uncle,yau kadai…..kuma ma lokaci ya wuce,na makara,idan ma naje bulala zaayimin Allah” kai ya jinjina kawai,widad din ta daukeshi da wani matsayi sosai,haka suka wuce sassan ummun tare.

    Ina ka saka ina ka ajjiye ummu keyi da dan autan nata,wanda take lelensa kamar kowanne auta a wajen iyayensa,duka su ukun suna falon suna hira,ita widad da kuma uncle muhsin din,sai da ummu ta korata tace ta fidda uniform din daga jikinta tunda taqi makarantar sannan ta miqe da jakarta a hanzarce ta wuce daki.

    Dauke dubansa muhsin yayi daga dubanta sanda ta bacewa ganinsa ya maido ga ummu

    “Me ya samu widad ne?,ko tayi ciwo baya bayan nan?”

    “Me ka gani?” Ummun ta tambayeshi itama

    “Ramewa naga tayi,ko girma ne ya kawo hakan?” Kai ummun ta girgiza tana tabe baki

    “Batun aurenta ne yaketa zuwa da mishkiloli kawai”

    “Aure fa ummu?,widad din?”

    “Eh baqon abu ne?,naga kusan duka ‘yan bayanta ma haka aka musu” zamansa ya gyara,har cikin ransa bayaso a aikata wannan dabi’a ga widad din,yana jin yarinyar har ransa,saboda baya mancewa da yadda mamarta ta daukeshi a sanda take auren dan uwansa,saboda da shaquwa ne sosai tsakaninsu da ita,ta daukeshi kamar qaramin qaninta

    “Amma ummu sunfi widad datawa ai,duka duka ita din shekararta nawa ne?,sha hudu fa?”

    “To mahaifinta dai ya tasamma aurar da diyarshi,mahfood ne akayita gwagwarmaya akan lamarinsa tace bataso,muka saka baki ni da alhaji aka ajiye zancansa,ya dauko ma’aruf to yanzu akan batunsa ake,shima din kuma ba so take ba” sosai fuskar uncle muhsin ta sauya

    “Amma ummu shikam yaaya meye haka?,tunda bataso duka basai a qyaleta ba?,nawa widad din take?,naga batayi girman da zai daga hankalin kowa ba saboda batayi aure ba ko?”

    “Duk yadda nake da iko dashi da ita dole akwai huruminsa na uba daya zama dole na bashi,nidai abu daya na sani bazan bari ayi mata auren dole ba” dan qaramin tsaki yaja abun yana bashi haushi,ko da shi dabi’arsa ta daban ce,bare a yanzun da ya zama riqaqqen dan boko

    “Wannan maganar a barta kawai,indan tace taji ta gani tana so ne ma shikenan sai ayi zancan aure,amma ni sha’awar karatu nake mata,karatu nakeso tayi,bari zamu hadu da yayan,ya bani ita kawai mu wuce gida tare”

    “Bazan iya baka widad ba,zan maka lamuni dai taje zuwa sanda komai zai lafa” murmushi yayi

    “Zahra ta dade tana nacin a bata widad ummu,su kansu su nujood zancansu yaushe zatazo,tunda anyi haka kawai ki haqura ku barmin ita”

    “Banyi alqawari ba” ummu ta shaida masa kai tsaye.

    Sanda widad din ta dawo falon bayan ta sauya kaya ummu ta shiga ciki ta duba dashishin da za’a girkawa alhajin,har yau har kwanan gobe tsufa jin dadi ko wadata bai hana dattijuwar matar aikin abincin mijinta ba.

    Cikin hikima uncle muhsin yake bugun cikin widad kan batun,tuni ta fara share qwalla,sai ya ajjiye spoon din hannunsa

    “Kinga share hawayenki,ba wanda zai miki auren dole,dake zan koma ma na kaiki wajensu nujood,ai zaki je ko?” Duk da nisa da ummu shine abu da tafi tsana,amma a yanzun sai takejin shine mafi dacewa,kawai tabi uncle muhsin din,tayi nisa da garin ko abbanta zai haqura da qudurinsa,bata da zabin da ya wuce wannan,don haka ta gyada kai hadi da cewa

    “Zanje uncle”

    “To shikenan,share hawayen ki bani labarin izifinku nawa yanzu a islamiyya” hira ce ta barke tsakaninsu,harma ta manta da fargabar tafiya tabar ummu,saima zumudin matsawa daga garin,ko banza ta gujewa wani ma’aruf abbanta dama auren da ake shirin qaqaba mata.

    Uncle muhsin shine auta ga ummu a maza,daga shi sai halimatu kenan,kuma qani ga abbanta da suke uwa daya uba daya,shi din ba mazaunin kano bane,yanayin aiki ne ya kaishi bauchi,da farko ma kamar bazaije ba,saida ummu ta qarfafa masa gwiwa,ta kuma nuna masa aiki ba inda baya kai mutum,yanzu haka shekararsa kusan goma sha uku da aure,yana da yara hudu,diyarsa ta farko widad ta girmeta da shekara kusan daya,dan boko ne sosai,yana da sauqin kai som mutane da kuma kirki,widad na ji dashi cikin dukka tulin qannen da mahaifinta ke dasu,saboda yadda yake nuna mata kulawa da kuma janta a jiki.

    Da kansa uncle muhsin din ya zauna da yayan masa mahmudu,ya sha fama sosai kafin ya gane abinda yake kwatanta masa,don daga bisani dole ummu da alhaji suka sake shiga maganar sannan ya janye qudurin nasa,ba kuma wai don ya haqura da maganar bane gaba daya,wannan ya sake qarfafawa uncle muhsin gwiwar tafiya da widad din

    “Taje dai ta huta,amma ban bar muku ita ba,kada ma kazo kace min ga zance ga magana”.

    Kamar wasa sai ga widad tana murnar tafiya,har ta fara hada kayanta da kanta ma,latifa ita da anty madina sunata dariya

    “Ba cinya ba qafar baya,Allah dai yasa a qarke qalau kada ku dawo ranar da kukaje” suke tsokanar uncle muhsin sanda sukaga widad din nata shiri.

    Kwana uku kacal ya qara suka tattara sai bauchi,ranar da zata tafin gaba daya ‘yan rakiyarsu har bakin motar uncle muhsin din,latifa ke riqon jakarta,tana ta tsokanarta

    “Uwar dakina kada dai zama yayi dadi a manta dani” widad dake sanye da atamfarta dinkin doguwar riga tayi dariya tana qwamewa gaban motar uncle din

    “Bazan manta dake ba inna latifa,kedai ki zuba ido zakisha tsaraba” dariya ta saki

    “To Allah yasa” itama ta amsa tana dariyar,suna dakon uncle muhsin ne,yana rabawa yaran gidan da sukayo masa rakiya kudi,’yan dari dari ne sababbi qar,baya rabo dasu,ya kammala ya dawo cikin motar ya zauna yana sake waina injin motar sosai,ummu ta zagayo ta durqusa tana musu addu’ar sauka lafiya,sannan ta zura hannu saman cinyar widad ta ajjiye mata kudi

    “Gashinan,kada kije baqon guri hannunki babu komai” murmushi uncle muhsin yayi bayan ya kalli kudin

    “Banda abinki ummu me zatayi da kudi?”

    “Ina ruwanka kai dai?” Ta amsa shi,tana gyara yafen mayafin dake saman kanta

    “Nidai bance a riqemin yarinya acan ba,aro na baku” ta sake jaddada masa abinda yake ranta,sai yayi dariya kawai yana tayar da motar,dai dai sanda widad kema ummun godiya,duk da itama din batasan amfanin me kudin zasuyi mata ba.

    Har motar ta fice daga harabar gidan suna waigen juna ita da ummun

    “Zauna sosai kada ki baro kan naki a gida kije bauchi da iya gangar jiki” uncle muhsin ya tsokaneta,sai tayi dariya tana zama sosai din,saidai tun a lokacin taji ta fara kewar gida,taji kamar ta koma,to amma idan ta tuna abinda ta gujewan sai taji dadi,hankalinta kuma yadan kwanta,ko ba komai za’a daina zancan,tana saka ran maganar ma tabi ruwa ta huta.

    Suma shirin ficewa a unguwar motar ma’aruf din ta sako kai,uncle muhsin yadan dakata kadan,sai ta lafe sosai ta kwantar da kanta saman cinyoyinta ta yadda bazaya ganta ba,ma’aruf din ya gaidashi sukayi sallama,uncle muhsin yaja motar sukayi gaba yana dariyar widad din cikin ransa,quruciya sai abarta.

    *ZAFAFA BIYAR 2023*

    IDON NERA Mamuhghee

    KI KULANI miss xoxo

    A RUBUCE TAKE Huguma

    RUMBUN K’AYA Hafsat rano

    DAUDAR GORA Billynabdul

    Account number

    0022419171
    Maryam sani
    Access bank

    Saiki tura shaidar biyanki ga
    09033181070

    VTU OR MTN RECHARGE CARD
    09166221261

    AL’UMMAR NIJER SU TUNTUBI WANNAN NUMBER

    +227 90 16 59 91

    Thanks for choosing us
    [2/3, 4:25 PM] +234 813 343 4840: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • Arubuce Ta Ke 4

    Arubuce Ta Ke 4

    *Widad*

    Alhaji salim musayyib mai fata shine cikakken sunan,mazaunin maiduguri da wanda aka haifa a can,ya taso ya girma ya kuma yi gwagwarmayar karatunsa dukka acan din,nau’in jinsin nan da mutane ke kira da suna SHUWA_ARAB,saboda asalin iyayensu da kuma kakanninsu dukka ba’a maiduguri aka haifesu ba,ba kuma anan sukayi rayuwarsu ba,rayuwar da sukayi a maidugurin duka duka ‘yar taqaitacciya ce,sanadin kasuwanci,asalin tushensu sun fito ne daga qasar mali zuwa yemen,kuma har yanzu danginsa da tushensa suna can gaba daya ko nace mafi yawa daga cikinsu,iyali ga mahaifinsa musayyib suke ta yado a nan,da kuma nashi ahalin shima daya tara.

    Matan aurensa biyu dukka ‘yan asalin qasarsa wadanda suka hada masa tarin zuri’a da kuma yara masu yawa,dansa na farko da matarsa ta fari wadda ta kasance balarabiyar qasar yemen shine mahmud,wanda yake mahaifi ne ga widad data kasance ruwa biyu,balarabiyar mali kuma bafulatanar usul daga katsina ta gefen mahaifiya,wannan shi ya taru ya bata wani irin sassanyan kyau daya banbanta da kyawun dukka cousin dinta da kuma sauran ‘yan uwanta,domin ita daya mahaifiyarta ta haifa ta barta a gidan,sai tarin ‘yan uba da kuma cousins da take dasu.

    Yanayi na rayuwa da kuma kasuwanci ya maido alhaji salim qasar kano da zama,ya fara tara iyalinsa shima,bayan ya aurar da mahmud arziqinsa ya qara ninkuwa fiye dana da,wanann ya siya manya manyan filaye ya hadesu waje guda,ya kuma yanki wani sashe na gidan ya fara ginin matsugunnin da zai zauna da matansa da kuma yaransa,bayan ya kammala suna gab da tarewa matarsa ta biyu ta rasu,sai mahaifiyar mahmud ce kawai Allah ya qaddara mata zama a gidan.

    Mahmud ne kawai ke rayuwa a wajen gidan,girman gidan ya sanya duk yaronsa daya tashi yin aure,za’a fitar masa da tsarin ginin da zai dace da gidan a gina masa ya tare a ciki,wannan yasa sannu a hankali gidan ya zama babban family house dake dauke da sassa sassa guda biyar,kuma kowanne sashe cike yake da albarkar zuri’a wadata da kuma kwanciyar hankali.

    Widad ta kasance ta musamman a wajen ummu,saboda ummun ta bude idanu ta gani a matsayin uwa kuma mahaifiya a wajenta,don itace ta raineta tun tana tsumman goyonta har kawo yanzu da shekarunta suke goma sha daya da watanni a duniya.

    Soyayyar da ummun itama kewa widad din ta banbamta data kowa,saboda itama tana jinta da matsayi biyu ne a wajenta,d’iya kuma jika,ta manta da raino sanda ta amshi widad da nufin rainonta,don a sannan ta aurar da autarta ma anty halima tuni,kasancewar su din basa zurfafawa karatun boko,kina gama primary ma kika samu miji to tabbas alhaji salim zai bada aurenki ne, matuqar ya yarda da addinin mutum da kuma mutuncinsa,ruwan miji ya barki kici gaba,ruwansa yace a’ah.

    Ko kadan rashin uwa bai wani taba widad ba,saboda ta samu dukka kulawa da ‘ya ke samu ga mahaifiyarta daga wajen ummu.

    Mahfood d’a ne ga baaba maisara,wanda suke ‘ya’yan wa da ‘ya’yan qani da mahaifin widad,tun kafin ta kawo haka yake nuna yana da interest a kanta,amma ko daya widad din taqi sake masa balle ya samu fuskar da ko hira ta zauna tayi dashi,saboda ita din wata irin mutum ce,tana da wahalar sabo,hakanan idan kanason ganin kazar kazar dinta da hirarta to cikin gidansu ne,musamman sassan ummu ko na anty madina,indai akace maka baqon guri ne zaka tsammaci cikakkiyar magana ma bata iya ta ba.

    Abu na biyu tana da masifar tsoron maza,saboda kullum hudubar ummu shine,idan ta sake ta yarda ko hannunta namiji ya kama zatayi ciki,idan kuma ta samu ciki mutuwa zatayi,wannan yasa sam sam bata yarda ko inuwa su hada,bama shi ba,dukka samarin gidan da suke a matsayin yayye a wajenta haka dabi’ar ta take.

    _wannan kenan_

    *Bayan shekara uku*

    Tun daga daren juma’ar da ya kama gobe sallah gaba daya yanayin gari ya canza daga yanayin azumi zuwa yanayin daren sallah,ko ta ina al’ummar musulmi sai hada hada ake,tituna zuwa layuka,gidajen kitso qunshi zuwa shagunan masu dinki ko ina cike yake danqam da jama’a kamar rana.

    Haka ce ta kasance gidan alhaji salim musayyib,babban gidan dake dauke da family masu yawa,a dabi’ar gidan babu tsawwalawa,koda salla ce kowanne sashe yana yin kalar girkin da mace ko matan sashen suka tsara yi,saboda kowanne part akwai store da kuma kitchen din su tare da me aikinsu,saidai idan an gama ranar sallah dukka suna zubawa abincin mai dan dama su aike sashen surukarsu hajiya ummu,duk da ita dinma ba zama take ba, takanyi abinci har kusan kala biyu,sabida karbar baquncin jikokinta dama surukanta matan ‘ya’yanta maza guda biyar da Allah ya bata,su da ‘ya’yansu da kuma ‘ya’yan wajen diyarta halimatu,hakanan su kansu jikokin dake cikin gidan suma kusan a nan suke zuwa su karba nata,sukance yafi dadi.

    Dai dai lokacin da sassan anty madina yake a cike da yara yaran matan gidan,wanda ake ta faman saka musu qunshin salla daga mai qunshin da ummu da kanta ke daukowa ayi musu,sannan kuma ga me kitso itama tanata kitse musu kansu duk da baiwar suma da yalwar gashi da suke dashi tubarkalla,babban falon da anty madinan ta ware musu saboda irin wannan hidimar a kacame yake.

    Daga gefe daya widad ce zaune,tsahon shekaru ukun data qara kyawunta ya sake bayyana muraran,hakanan alamun girma sun fara bayyanar mata,duk da cewa har yanzu gabunta sakarci da kuma wautarta tana nan,cikakkiyar GOYON KAKA,Qunshinta yafi na kowa jan lokaci,saboda ummun tace na musamman za’ayi mata kamar yadda aka saba,masu zumbura baki nayi masu qorafi nayi,to amma kusan idan da sabo an riga an saba,haka sukayi suka gama suka kuma haqura.

    “Aafiya ciremin lallen nan” widad ta fada tana yamutsa fuska saboda jimawar da tayi a zaune

    “ke kam kin huta,sauranki kitso” afiya ta fada tana matsowa hadi da fara sabule ledar da aka rufa hannun,harara widad ta jefa mata

    “Tabdijan,wa za’ayi wa kitson?,Allah ya kiyaye” ta fada tana bata fuska,kitso babban abokin gabarta ne,sam bata qaunarsa,tun daga quruciyarta kawo yau tsaf zata iya irga adadin sau nawa aka taba yi mata kitso,mutane kance saboda tana da suma me kyau ne da tsaho,kusan sumarta ta zarta dukka ta yaran gidan,tamkar zabarta akayi,hakan kuma baya rasa nasaba da gado da tayi ta wajen uwa da uba,don idan ta ware sumarta tana iya saukar mata har tsakiyar gadon bayanta.

    Dariya afiya ta saki tana ci gaba da tsokanarta

    “Nikam naga lokacin da zaki daina gudun kitso”

    “Babu rana”ta amsa mata tana Allah Allah a gama cire mata ta tsallake ta gudu ma daga falon.

    “Tubarkalla ma sha Allah ‘yammatan ummu,lallai dole mu caji ‘yan samari kudi,irin wannan kyau haka?” Anty madina dake shigowa dauke da babban farantin data yanka musu fruit ta fada tana murmushi,cikin yanayi na nuna jin kunya abinda ke nuni da soma girman widad dim ta boye fuskarta tana dariya

    “Bafa wasu samari anty Allah”

    “Aah fada kike wallahi,kowa fa ya sani” wuf tayi ta tashi saboda yadda sauran ‘yan uwanta ke juyowa suna kallonta,wasunsu suna mata dariya ne da gaske har zuciyarsu,yayin da wasunsu kallon hassada qyashi da baqinciki ne suke.jifanta dashi,abu guda daya da bai taba dadata da qasa ba,itakam indai zata jita wajen ummunta to komai lafiya lau,takan manta da dukka wasu qananun abubuwa dake tasowa ko kuma faruwa cikin gidan.

    “Ina zaki sauranki kitso ai” anty madina ta fada,sai ta tsaya tana duban anty madina,fuskarta dauke da zallar quruciya ta narke fuska,abinda ke nuna gab take da fara tara hawaye

    “Don Allah anty a barshi,nayi bayan sallah” haba ta kama tana kallonta

    “Anya widad?,ke wannan sumar bata damunki ne?” Dariyar yadda anty madinan ta saki baki ya kamata

    “Ai shikenan,ki biya ta kitchen,ki cewa yalwa ta baki abincin ki kaiwa ma’aruf” sunan da anty madinan ta ambata sai taji kamar tace mata ba zata aiken ba,amma anty madina tafi gaban haka a wajensu,dukkaninsu suna mata kallon babbar yaya, kasancewar dukka manyan yayyansu mata suna gidajen aurensu,a kaf surukan gidan kuma ita dince mai qananun shekarun da suke iya sakewa suke komai tare da ita,itama kuma ta riqesu tamkar qannen nata.

    Ba’a son ranta ba ta biya kitchen din ta dauki abincin,ta fito tana dariyar yadda yalwa keta koda kyan qunshin nata,tsakaninta da dukka ma’aikatan gidan qauna ce da soyayya,koda kuwa ba masu aikin sassan nasu ba,idan ka ture wautarta da quruciya da tabara ta goyon kaka,ita din yarinya ce mai matuqar girmama wanda ya girmeta,zaiyi wuya ka sameta da laifin rashin kunya,kai koda laifi akayi cikin gidan da wahala ka samu sunanta a ciki,idan kaji an ambaci sunanta to wata wautar aka tafka,ko kuma ta taba sakalcin nata data saba,wannan ya sanya ummu bata ragawa duk wanda ya tabata,takan ce

    “Nasa halin kayata fes,duk wanda yace tayi wani abu idan ma sharri ne zan gane ato,nasan me zata aikata,hakanan kuma nasan abinda ba zata aikata ba”.

    Har ta isa qofar dakunansu taji hayaniyar mutane a dakin nasa,da alama baqi yayi abokansa,tsaki taja,ta koma da baya cikin takun da basu fi goma ba,ta tsaya dab da motarsa.

    Sai data qarewa motar kallo sannan ta matsa kusa da boot din motar ta dora masa abincin a nan,ta kama gabanta hankali kwance ta wuce sassan ummu.

    Saidai tana sallama a sassan taji nadamar dawowa sassan ta kamata,babu wanda ya gaya mata yazo gidan,da babu abinda zai sanyata dawowa yanzu,sun riga da sun ganta gaba dayansu,harda na’eema diyar anty halimatu da tazo gidan sallah,saboda haka duk wata dama ta komawa ta qwace mata babu ita,sai taci gaba da takawa cikin falon tana tsuke fuska,hadi da sake gayyato bacin rai saman fuskarta,uwa uba dama ga yunwa dake cin hanjinta,taqi abincin wajen anty madina saboda ba cimarta ta dafa ba,tace sai ta dawo wajen ummunta.

    *_RIGIJI GABJI!_*🔥🔥

    *_WANI KAYA SAI AMALE_*🔥🔥🔥

    *FITATTUN ZAFAFAN DA BABU NA BIYUNSU*🔥🔥

    *JERIN GWANON LITATTAFAI ABOKAN TAFIYAR JUNA MASU MABANBANTAN LABARAI DA FASAHA*

    *_’YAN BIYAR DIN NAN NE FA_*

    *_SARAKAN LABARUN_*

    *NISHADI*
    *CAKWAKIYA*
    *GWAGWARMAYA*
    *BARKWANCI*
    *TSANTSAR DARASIN RAYUWA*

    *TARE DA*

    *ZAZZAFAN SALO NA SOYAYYA MAI RIKITA TUNANI DA TSUNDUMA MAI KARATU CIKIN TAFKIN SHAUQI*

    *SUN SAKE SHIRYAWA TSAF,DAUKE DA WANI TARAGO MAI CIKE DA LABARAI MASU ZAZZAFAN ZAFI!!!*

    *KIN SHIRYA MADAM?*

    *MAZA ANTAYA NAKI KUDADEN KIBI SAHUN AYARIN MATA MASU AJI TA HANYAR BIYAN KUDIN NAKI KARATUN WADAN NAN LITTAFAI KAMAR HAKA*

    *DAUD’AR GORA* Billynabdul

    *KI KULANI* Missxoxo

    *IDON NERA* Mamuhghee

    *RUMBUN K’AYA* hafsat rano

    *A RUBUCE TAKE* Huguma

    *ZAKI IYA BIYA KAI TSAYE TA WANNAN ACCOUNT DIN*

    0022419171
    Maryam
    Access bank

    Saiki tura shaidar biyanki ta wannan number

    09033181070

    *MASU TURA KATIN MTN KO VTU KUMA ZASU TURA WA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANSU*

    09166221261

    *Yan nijer 🇳🇪🇳🇪kuma zasu tuntubi wannan number*

    +227 90 16 59 91

    *Muna godiya da ci gaba da zabin zafafa biyar a koda yaushe*🙏🏾🙏🏾*H U G U M A*
    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

    Page 05

    *MAAB LUXURY HOME*

    *_idan kaji gangami akwai labari_*
    *_SABUWAR DUNIYA CE_*
    *ALFAHARIN UWAR GIDA*
    *FARINCIKIN AMARYA*
    *MAIDA TSOHON GIDA SABO*
    *DUNIYAR QYALE QYALE*
    *KAYA NA ALFAHARI DA TAQAMA*

    *_Ba iya kyawun idanu suka tsaya ba,harma da ingancinsu da kuma qwarkonsu,ka dade kana mora kana kece tsara a tsakanin tsararraku da sauran mutane_*

    *nasan zaku tambaya ina ne nan?*

    *MAAB LUXURY HOME*

    😊 *Kai daga jin sunan ma babu tambaya*

    *_duniyar qawata muku gidajenku ku ganku kamar a wata nahiya ko wata duniyar_*

    *Suna kawo kayan kitchen rankatakaf manya da qananu*

    *Kayan gado dana parlor*

    *Kai…suna kawo kowanne nau’in kayan ado na cikin gida*

    *Karkiyi qasa a gwiwa kuma kada kiyi sake ma dafe,maza garzaya ki nemesu a*

    _adress dinsu dake No 22 Ahmadu bello way,kano state_

    *Ko kuma kuyi order din kayanku kuna daga gida ta shafinsu na instagram*

    @maabluxuryhome

    *Facebook*
    @maabluxuryhome

    *Ko ku nemesu ta lambar wayarsu kamar haka*
    08034631010

    *Kyau inganci da rahusa shine takenmu*😊😊🤝🤝🤝🤝
    ____________________________

  • Arubuce Ta Ke 25

    Arubuce Ta Ke 25

    Page 25

    Murmushi kadan ummu tayi,qarara ta hango kishin widad a idanun halima,ta rasa me yasa haliman ta kasa sabawa da hakan,sai ta gyara zama

    “Mu dinma uwayenku da sanda aka aurar damu banajin munkai ya widad din,a gidan muka iya abubuwa,tun mun kwamacala har muka qware,yanzu gashi ba’a ce mune muka haifeku ba” kauda kanta anty halima tayi,tasan dama duk yadda takai bakai isa ka fadi wallen widad ko ka kusheta ga ummun ba.

    Yau din tun qarfe takwas ta qudunduna a bargo cikin dakin ummu,bayan ta gama qarewa kayan data gani jibge a dakin ummun kallo,tun shekaran jiya taga ummun nata jibge kaya a dakin nata,itadai bata ce ga dalili ba,ta dan tura baki taja bargo abinta,bacci yau takeji da gaske,don ko sassan anty madina da aka cika ana hira yadda aka saba taqi zama,bugu da qari kuma yadda suketa faman kiranta da sunan amarya,wanda ta dauka duka tsokana ce irin tasu yau ta sauka a kanta suka tasota gaba,ita kuma bataso.

    Fakare tayi tana jiran bacci ya iso,gefe daya tsoro tsoro takeji saboda ummun tana wajen dattijon mijinta,buda qofar dakin akayi a hankali,sai ta tada idonta tana kallon me shigowar ba tare data tashi ba,ummun ce,hannunta dauke da babbar baqar leda

    “Yauwwa,gwara ma da bakiyi baccin ba,tashi” kai tsaye ta miqe din,don itama tanason yiwa.ummu tambayar

    “Ummu…wai wannan kayan,na wanene duk sun cika miki daki?”

    “Kayan aurenki ne” ta amsa mata gaba gadi tana kallon fuskar widad din,cike da fargabar yadda zata kalli zancan,kada ta watsa musu qasa a ido.

    Idanun ta fitar,fuskarta babu wani emotion saina mamakin

    “Aurena ummu?,duka wadan nan kayan?” Kai ta gyada mata

    “Eh,harda wasu ma” ta fada tana bude mata ledar

    “Wannan babanku yace ki zaba iya wadanda kikeso za’a dinka miki” da mamaki ta sake duban ummu

    “Wai duka nawa ne?”

    “Kadanma kika gani shalele ta,za’a kawo lefe a kawatuna duka naki” murmushi ya subucewa widad,kawai taji farincikin na kamata

    “Harda kayan kwalliya ma irin nasu anty ramziyya?”

    “Sosai,inajinma yafi nasu” ta fada tana murmushi ganin bata dauki zancan da zafi yadda ta saba ba,da wannan hirar ummun ta dinga hilatarta tana jaddada mata zancan auren,quruciya ta sanya widad din bata wani damu ba,saima cika da tayi da zumudin zuwan ranar da za’a kawo mata kayanta,wanda ummun tace mata sai ranar daurin aurenta.

    ********Wasa gaske saiga shirin biki nata kankama daga bangarensu widad,sam bata wani damu ko daga hankalinta ba,abinda ya baiwa kowa mamaki,yayin da wasu kuma hankalinsu ya kwanta ganin bata qi yadda ta saba ba,’yan adawa kuma fadi suke

    “Shegiya dama da guntun wayonta,gashi tayi luff kamar ba ita taqi ‘yan uwanta har mutum biyu ba” oho,ita dai sabgar gabanta takeyi kawai,tana lissafin ranar da za’a kawo mata kayan kwalliya.

    Daga bangaren su abbas kuwa maganar ta fara yawo,da yawa daga cikin dangi wadanda sukaci burin zuwan wannan rana,ranar da abbas zai qara aure labarin baije musu a dadi ba,wadanda suka jima suna addu’ar hajiyan ta sanyashi qara aure saboda halayen hafsa,duk sai gwiwarsu tayi sanyi,hajiyan ta musu ba zata,irin abbas din shi kowa ke kwadayin samu,saboda alamun wadata da aziqi dukka sun fara bayyana a tattare dashi.

    Tabbas hajiyan tasan da wannan,shi yasa tayi musu wannan ba zatar,ta kuma zartar da wannan hukuncin,fatanta daya abbas din ya samu inuwar da zai huta,ya kuma samu sanyin idaniyarsa.

    Har a sannan hafsat din bata da labari,gidanta ba gidan zuwan ‘yan uwan abbas bane,bama su kadai ba,hatta da nata dangin,saboda wata iriyar jarrababbiyar rowa da take da ita,muguwar sa’a ka taka idan kaje gidan ka samu tarbar pure water bare abinci,kusan anty ummee ce kawai ke samun wannan daga gareta,shi kuwa abbas,bayan ya ajjiye wa hajiya dukkan wani abu da yasan zata iya nema daga gareshi,komawa yayi kaduna,amma yace mata cikin satin daurin auren zaiyi qoqarin zuwa da wuri,da fatan alkhairi ta bishi,domin kuwa ita ya gama mata komai,sai fatan dacewa bisa niyyar alkhairin data nufaci rayuwarsa dashi.

    ************

    Daga can tsakiyar ‘yan jaridar dake dauke da nau’ikan kayan aiki daban daban,ASP ABBAS SARKI ne tsaye,sanye da uniform din ‘yan sanda daga dace da structure na jikinsa,ya kuma yi masa kyau ainun,iya yadda yake tsayen kadai ya isa ya gaya maka cewa jajirtaccen police ne,wanda ya qware a aikinsa

    “Wannan shine abinda ya faru a taqaice,we will let you know when the investigation is completed”. Sai ya zare hannunsa daga aljihu yana shirin wucewa,amma suka sake yunquro masa da tarin tulin tambayoyinsu,rasa wacce zai amsa yayi,saidai akwai wani cikinsu da yafi kowa matsa masa da tambayar

    “Amma yallabai,labari ya iskemu cewa kai da kanka ka gudanar da wannan aikin,kuma kaine ka samu nasara cafko su,shin meye gaskiyar wannan al’amari?,don dama jama’a sun dade da saninka da kuma ficenka wajen gudanar da aiki?”

    Wani miskilin murmushi yayi wanda yake cike da tarin gajiya,murmushin da har yau hafsa ta gaza gane irinsa har sai ya buda baki ya magantu,yasa hannu ya cire hular police din dake kansa mai zubin P-cap,cikin muryarsa mai zurfi da kwarjini ya fara amsa tambayar tasa,bayan tarin jama’ar dake wajen sunyi shuru suna jiran amsa

    “Ko ni nayi wannan aiki,ko bani nayi ba nasara ce,nasarata kuwa nasarar dukka jami’an tsaro musamman na ‘yan sanda dake wannan qasar ne,muhimmin abu aci gaba da yi mana addu’a,fatan nasara” ya fada yana saluting nasu,sannan ya juya sa sassarfa ya shige ciki gudun kada su sake tsaidashi,sai wajen ya rude da muryoyinsu cikin farinciki kowanne na bawa kafar yada labaran nashi cikakken jawabi.

    Tsaye yayi gaban table din office dinsa bayan ya ajjiye hular hannunsa a kai,saiya zare agogonsa ma ya dorashi saman hular,ya furzar da iska yana duba lokaci,ya riga yayi alqawarin barin Kaduna a yau zuwa bauchi,lokaci yanata quracewa ba tare da ya shaidawa hafsa komai ba,yanason ta fara ji daga bakinsa shi yasa ya hana kowa ya gaya masa,duk haukar da zatayi ta yita ta gama,yasan tabbas akwai case babba

    Uwa uba kuma mai girma gwamnan bauchin yanason ganinsa,ya bashi appointment gobe da yammaci,zai sameshi gidan gonarsa,to dole tafiya ta kamashi a yau,saidai yana jin komai ma zaizo masa da sauqi da yardar Allah,tunda aikin da yake kwana ya kuma tashi dashi ya kammalashi,duka suspect dinsu suna hannu.

    Wayarsa ya ciro da sirritaccen layinsa da ba kowa ya sanshi ba,ya kira wata number yayi confirming samun flight daga kaduna zuwa bauchi sannan ya aje wayar,ba kasafai ya fiya zirga zirga a jirgi ba,yafi ganewa yayi driving da kansa wani lokaci,yana tafe yana karantar hanya da inda tsaro yayi qaranci ko kuma inda komai yake tafiya dai dai,amma a yau din bashi da zabi illa yabi jirgin.

    Taku biyu ya qara kamar zai fita,sai kuma ya fasa,ya sake daukar wayar yayi kira na sakanni ya ajjiye,ya shiga toilet ya kama ruwa sannan ya fito,ya duba dukka wani abu da yake da buqata cikin office din ya hada waje guda,bayan yayi wasu rubuce rubuce a wasu files sannan ya fito.

    Daya daga cikin juniors dinsa ne yake driving nasa zuwa gida,yana a motar ya kira hafsat din don ya shaida mata tahowarsa,mimi ce ta fara daga wayar,sai data gama shirmenta sannan uwar ta karba wayar

    “Kuna lafiya keda yaran?” Ya fadi don yasan zaiyi wuya ta fara tambayarsa lafiyarsa kota gaisheshi

    “Lafiya qalau muke” ta amsa masa cikin ranta tana mamakin yadda ya sauko daga laifin data masa haka da wurwuri,duk da dama shi din bai cika riqo ba,amma a yadda taga ransa ya baci jikinta yayi sanyi,ta kuma aza zai mata hukunci mafi tsauri ne

    “Am on my way to bauchi in sha Allah,two to three hours”

    “Tooo….basai Friday ko Saturday ba?” Goshinsa ya murza kadan,ya salam,a nashi zaton tayi murna da yace zai dawo din ko?,amma saita buge da tuna masa ranar dawowarsa batayi ba?

    “Na sani,inda muhimmin abu ne da zanyi a nan”

    “Okay to,a taho mana da tsaraba”

    “Yayi…..me zan samu?” Ta fahimci sarai me yake nufi,amma sai tayi kamar bata gane din ba

    “Kamar me kenan?” Ta fada tana dan bata fuska,duk da ba ganinta yakeyi ba,zai dawo yanzu zai fara damunta da tsarabe tsarabensa.

    “In so samu ne tuwo nakeso” tanason musa masa amma kuma batason bata saukowa da yayi daga fushin da yayi da ita ba tare data bashi haquri ba

    “Xan qoqarta” ta fada cikin ranta tana jin ba zata iya yi ba

    “Alright,saina qaraso” ya amsa ta ba tare da yaja doguwar hira da ita ba.

    Bai wuce hutun awa yayi cikin gidan nasa ba,ya shirya ya wuce airport,gab da sallar isha’i cikin gidansa tayi masa, samuel ne yaje ya daukoshi ya ajeshi,ya shiga gidan nasa dauke da jakarsa,wata a hannu wata a kafada,sabida baya barin kowa da kowa ya shiga masa gida.

    Yana shiga falon yanayinsa ya canza gaba daya,saboda qarancin tsafta da falon yake da,babu wani alamun qamshi ko qanqani da zaka iya ji daga falon,wala’alla ma idan ka taki mummunar sa’a hancinka ya iya shaqo maka qauri mara dadi dake ratsowa tun daga kitchen din dake falon zuwa hancinka.

    Wannan ba baqon abu bane a wajensa,yayi fada yayi nasiha amma jiya iyau babu wani ci gaba,saidai yaci gaba da haquri kau da kai da nusashe ta,duk da hakan tana ganin kamar gazawarta yake gani,tunda dai tana iya nata bakin qoqarin a ganinta.

    Yaran da suka garzayo suna masa oyoyo ya daure ya duqa ya rungumesu cikin jikinsa,ko daya babu wani kyakkyawan yanayi a tattare dasu suma,ita kuwa saita aje wayar hannunta tana dan sosa kai irin na marasa gaskiya,tare da qoqarin yi masa sannu da zuwa.

    Amsawa yayi yana kallonta,wani hargitsatsen kaya ne a jikinta,atamfar dake jikinta ya soma gajiya da ganinta,idan zai iya tunawa da ita tazo gidan,kuma har yau ta gaza bada ita kyauta saboda tsabar baqar rowa,sau tari yakan tambayi kansa menene amfanin karatun da hafsa tayi?,tabbas da yasan haka zata ci gaba da kasancewa,baiga abinda zai sanya ya barta ci gaba da karatun ba,don wadan nan dabi’un nata babu wanda zai gani ya dauka yasan bihim a boko.

    “Muje ku rakani na shirya” ya fada yana kada kan yaransa,saita bi bayansu da harara

    “Agwagwa sarkin wanka” tafada,don tasan zuwa zaiyi ya hada ruwa ya musu wanka,ita duka ba wannan bane ya dameta,yadda dafa dukan shinkafar da tayi masa ta kama ta kuma yi qauri da kyau,ta yadda zata masa bayani take tunani,tasan halinsa,sarai baya wasa da cikinsa,ya baiwa abincinsa muhimmanci sosai.

    KI KULANI miss xoxo

    DAUDAR GORA Billynabdul

    RUMBUN K’AYA hafsat rano

    IDON NERA Mamuhghee

    A RUBUCE TAKE huguma

    _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_

    _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

    0022419171
    Maryam sani
    Access bank

    Saiku tura shaidar biya ga
    +234 903 318 1070

    *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
    09166221261

    *Al’ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
    +227 96 09 67 63

    *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥

     

    [2/21, 4:17 PM] It’s Queen Meenali👸🏻: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • Arubuce Ta Ke 10

    Arubuce Ta Ke 10

    Page 10

    K’ofar wani madaidaicin gida mai fenti ruwan toka da qaramin gate ruwan madara motar ta tsaya,ya sanya hannunsa cike da nutsuwar nan tasa dake zmaa mabudin nasara ga dukka aikin da ya sanya a gaba zai buda motar,saidai kafin yakai ga aiwatar da hakan Samuel ya rigashi,ya kalleshi yadan kau da kai sannan yace

    “Thank you Samuel,you can go,zan koma gida da kaina” kai ya girgiza

    “No oga,zamu jiraka,daga nan station zamu koma,babu wani aiki da zamuyi kuma”. Baice masa komai ba ya sauka daga motar ya nufi gidan yana takawa cikin tafiya ta tsayayyun maza.

    Da sallama ya tura qofar ya shiga,yar farfajiyar gidan babu kowa saidai qal take,fes kamar babu wanda ke rayuwa cikin gidan bare ya bata ba,yana hango takalma daga qofar falon,wanda zaka fara taka wata qaramae baranda kafin ka cimma falon,sai yaci gaba da takawa har ya isa baranda yana maimaita sallamar sa,hadi da yunqurin zame takalman qafarsa kafin yakai ga shiga falon

    “A’ah qaraso da takalmanka abinka” daga can cikin falon aka fadi,sai ya miqe murmushi daga qasan zuciyarsa na kubce masa,har ta hangoshi kenan,duk da shi bai hangota ba,ya yaye labulen yana sanya kansa ciki tare da jaddada sallamarsa.

    Daga can saman kujera mai cin mutum biyu take a zaune,babbar macace wadda aqalla ta doshi shekara sittin,zaune sanye da atamfa dinkin riga da zani,kanta lullube da kallabi mai santsi irin na asalin tsaffi a qasar hausa.kyakkyawae bafulatanar bauchi,wadda bata qi dibar komai nasu ba,illa hasken fata,bata cika fari sosai ba irin wanda akasan fulani dashi ba,fuskarta na nuna zallar kamala da nutsuwa da kuma mutuntaka irin ta cikakken dan adam.

    “Wa’alaikumus salam,maraba…yanzu kake tafe?”tayi tambayar tana gyara zamanta cikin kujerun

    “Eh hajiya” ya amsa mata dai dai sanda take duban ‘yar budurwar dake kwance cikin kujera

    “Tashi ki bashi waje” tun kafin ma hajiyar takai qarshen maganarta ta soma yunqurin tashi tana lalubar dan kwalinta daya fita,cikin sauri ta fara gaidashi

    “Ina yini uncle”

    “Lafiya lau” ya amsa mata yana zama cikin wata kujerar ta daban,bayan ya dan ture kayan da suke kai

    “Shiga kitchen ki samo masa ruwa”

    “Tom” ta amsa tana ficewa daga falon.

    Sai a sannan ta tattara hankalinta a kansa,cike da girmamawa ya zamo qasa yana gaidata,ta amsa masa cikin kulawa da kuma qauna

    “Alhmdlh…..ashe kun dawo”

    “Shigowata bauchi kenan nace bari na fara zuwa na gaidaki” ya amsa mata yana komawa mazauninsa

    “Ma sha Allah,Allah yayi jagora”

    “Yayi hajiya,saidai fatan Allah ya dada yi mana,duk abinda akaje yi din Allah ya dafa mana an samu nasara” murmushi ya wadaci fuskarta,duk sanda zaiyi tafiya irin wannan sai ya shaida mata abinda zaije yi din,duk da cewa kusan komai din da zaiyi ma cikin rayuwarsa ita yake fara sanarwa,ita yake fara shawarta,takan tsaya tuquru da addu’a koda bai nema addu’arta ba,domin kuwa shi din na dabanne a zuciyarta,yana da wata irin tarin biyyaya me wahalar samuwa ga yaran yanzu.

    “alhamdulillah, alhamdulillah,Allah abun godiya,to Allah yaci gaba da kula mana da rayuwarku”

    “Ameeen ya hayyu ya qayyumu hajiya” ya amsata yana sake cire hular kansa kamar tana damunsa ne ya ajjiye a gefansa yana duban tarin kayanta dake ajjiye

    “Ya akayi maisara ya kawo miki kayanki haka babu guga?” Dan duban kayan tayi

    “To wallahi dai bana ce ba,kamar dai kallon qwallo suka tafi” fuska yadan tsuke

    “Qwallon me?,idan bazaya iya aikinsa yadda ya kamata ba sai yayi magana” murmushi hajiya ta saki,shikam akan dukkan abinda ya shafeta baya wasa dashi,baya bada uzuri,hakanan baya daga qafa

    “Yana qoqari ai,kasan su da son qwallo,kuma yau da gobe ma sai Allah” shuru yayi ya sanya hannu yana karbar cup din da muneera take miqo masa mai cike da ruwa.

    Sai da ya shanye ruwan sannan ya dubi hajiyan

    “Saura kwana nawa ne bikin gidan kawu hassan?”

    “Na zaci zaka leqa ma,yana gida kamar bai fita ba yau”

    “Sai idan na dawo,na yiwa auwal magana zai fidda kudin gudunmawar nan,zai kawo miki sai a bashi”

    “To to madallah,Allah yayi albarka,ya qara budi”

    “Ameen ameen” ya amsa mata yana sanya hannunsa a aljihun uniform dinsa ya fiddo kudi ya ajjiye mata yana cewa

    “Zan dan huta gobe,may be bazan fito ba”

    “Baka gajiya abbas?” Murmushi kawai ya saki ba tare da yace komai ba,baijin zai gaji da yiwa hajiyan tashi hidima bakin ransa,domin baya da kamarta a fadin duniya

    “Allah yayi albarka”

    “Ameen ameeen”

    “A gaida gida,a gaidamin kishiyoyin nawa” kamar tace kwana biyu sunqi gidan sai kuma ta fasa fadin hakan,ita din mutum ce mai son zaman lafiya,batason rigima sam,saidai a duk sanda ka qureta bata da dadi.

    A bakin mota ya samu su Samuel sunata hirarrakinsu,kafin ya iso ya bude masa qofar motar ya shiga,sannan suka zagaya suka shiga suma ya tada motar suka bar layin.

    Duka duka tafiyar minti talatin da ‘yan kai motar ta sake sanya signal sannan suka shiga wani madaidaicin titi mai burji,wanda zai sakada da ainihin unguwar da suka nufi shiga.

    Basuyi tafiya me yawa ba motar ta fara slow,da alama sun cimma inda suka nufa,ba jimawa ta faka qofar wani madaidaicin gida.

    Daga girman gate din gidan zaka fahimci girman gidan,idan nace girma bawai ina nufin girma na sosai ba,saidai kana gani kasan yalwataccen gini ne daga ciki,hakanan ya qawatu ga idanun me kallo,yana dauke da tsayayyun katanku masu tsaho da qarko,wadanda ke dauke da fenti ruwan madara har jikin gate din,wanda aka yiwa ratsin zaiba(gold) a jiki.

    Wannan karon kafin su bude masa ya rigasu budewar,ya zuro qafafunsa dake saye cikin baqin boot zuwa waje yana duban gaban gidan sannan ya sanyo gangar jikinsa zuwa waje

    “Thanks Samuel” yace dasu bayan yadan waiwaya da kyau

    “You deserve it sir”ya fada yana saluting nashi cikin girmamawa,jinjina kansa kawai yayi yana nan tsaye har suka tada motar suka fara barin gaban gidan,sannan ya qarasa a hankali yasa hannu yana knocking.

    Daga ciki wata kakkaurar murya ta bayyana ana tambayar waye,bai bada amsa ba har zuwa sanda mai tsaron gidan ya bude qofar,da sauri yaja da baya cikin matuqar girmamawa yana masa sannu da zuwa

    “Yauwa sule,mun sameku lafiya?”

    “Lafiya lau oga”

    “Ma sha Allah” ya furta yana takawa zuwa cikin gidan,hannunsa guda daya saye a aljihun wandon uniform dinsa,daya hannun kuma riqe da hular tasa.

    A hankali yake takawa zuwa cikin gidan yana nazartar yanayin gidan,daga farfajiyar gidan ko ina fes yake cikin hankali da nutsuwarsa,duk da bashi da tabbacin abinda zai tarar a ciki amma hankalinsa ya dan kwanta kadan,yaci gaba da takawa cikin taku na qaqqarfan namiji wanda horon aikin damara ke yawo cikin jiki da kuma jininsa.

    Qofar falon ya murza,yayi sa’a ya sameta a bude,sai ya tura yana sanya kai ciki,bakinsa dauke da sallama.

    Kamar jira akeyi,yara biyun dake wasa a falon saman dan keken wasan yara suka waiwayo zuwa gareshi,babbar me wayon wadda ke tura qanwarta ta saki keken da mugun gudu ta nufeshi

    “Abba….abba!” Take fada cikin daga murya dake cakude da sautin zallar farinciki,yayin da daya yarinyar keta kiciniyar saukowa daga kan keken itama don ta iso gareshi.

    Wani qawataccen murmushi ne ya subuce masa,ya duqa a hankali yana jiran isowar yarinyar,tana qarasowa ya dauketa caraf yana sanyata cikin jikinsa,saidai kuma me?….. janyeta yayi da sauri yana duban kayan jikinta sakamakon qarnin da baisan na meye ba daya daki hancinsa,ya sauke idanunsa kan gaban rigar yarinyar,rigar da idan bai manta ba naira dubu shida ya sanya ya siyeta kafin tafiyarsa wannan aikin,kwanaki goma baya da suke wuce kenan.

    Jirwaye ne na abubuwa kala daban daban a gaban rigar,wanda shi kansa bazai tantance na meye ba,ya dauke idanunsa ya maida kan fuskar yarinyar dake dauke da jirwayen busassun hawaye,kafin yayi magana yaji ana jan hannunsa hade da gwaranci,sai ya mayar da kallonsa kanta,tana tsaye a gabansa tana ta babbaka masa dariya,da alama akwai abinda takeson gaya masa cikin gwarancin nata,sai ya miqa hannu daga tsugunen da yake ya dauketa cak yana azata saman cinyarsa,saidai ita din ma babu sauqi,tsami ko kuma warin pampers dinta ne ya kaima hancinsa ziyara,ya miqa hannu yana taba pampers din,sai ya jishi a cike,tausayin yarinyar ya kamashi,take kuma ranshi ya baci

    “Abba,ka siyo man teddy din?” Kumatunta ya kama yana qoqarin hadiye fushinsa,abinda kusan ya zame masa jiki koda yaushe

    “Mimi teddy,bari na huta tukunna” bai sake jiran komai ba ya sanya hannu ya sunkuci yaran duka su biyun,sunata zuba masa shirmensu yana biye musu ya doshi sassanshi dasu,don bazai iya sake zama a wannan sashen ba a yadda idanuwansa suka ganshi a hargitse kamar an shekara ba’ayi masa shara ba.

    Sashe ne daya tsaru matuqa cikin kalolin light blue da fari,tun daga babban falonsa dake manne da window size da hotunansa da yawancinsu cikin uniform dinsa ne na police zuwa bedroom dinsa wanda aka zubawa kayan gado masu matuqar kyau da tsari.

    Yayi zaton zai samu sassauci a sashen nasa,tunda yabar key ya kuma buqaci a gyara masa,amma sai ya samu waje shima sammakal,sauqin daya ne baikai jagalewar can ba,ya hadiye wani abu mai tauri yana sauke yaran gefan gadonsa,sannan ya fara cire uniform din nasa,ya rage daga shi sai wata farar shirt mara nauyi ko kadan mai gajeran hannu,wanda hakan ya bayyana cikar zati da siffar jikinsa,muscles tako ina dake nuni da siffar qarfi da kuma yanayi na motsa jiki da daga qarfe da yakeyi a kowanne lokaci,wandon jikinsa ya fidda ya rage iya boxer,sannan ya shige toilet dinsa ya hada ruwa mai dumi sosai ya dawo dakin ya fidda musu kayan jikinsu ya wuce toilet din dasu ya sanyasu a bathtub.

    Fes yayi musu wanka dukka su biyun har gashin kansu,sunata qyalqyala dariya hadi da cikashi da duminsu,shi kuma yana ta biye musu,dukka a qoqarinsu na hadiye damuwa da kuma bacin ransa,bayan ya gama ya sanya kayan daya cire musun a leda ya jefa a dustbin,duk da kudin da ya sanya ya siyesu,mutum ne shi mai tsananin tsafta hadi da tsantsami,don hakan baima san ta ina zai fara tsaftace kayan ba,don haka ya gwammace yayi musu hakan.

    Anan dakin ya shafa musu mai ya gyara musu gashinsu,sannan ya buda jakar da yazo da ita,a duk sanda yayi wata tafiya indai dama ta samu baya gajiya da yiwa iyalinsa tsaraba,ya fidda wasu gown na wani cotton material iri daya guda biyu ya sanya musu,sannan ya feshe jikinsu da turare.

    Murna suke abinsu kawai,walwalarsu ta dadu saboda yadda sukaji jikinsu yayi musu dadi,ransa a bace ya daga kai yana duban agogon bango,a qalla ya kusa minti talatin da shigowa,amma batasan ya dawo din ba,abar ta tashi ma,yaran data bari a parlor fa?,haka take tafiya ta qyale yaran qofa a bude kusan awa guda ba tare data leqa su ko ta bibiyi halin da suke ciki ba?.

    *RUMBUN K’AYA*🔥

    *DAUDAR GORA*🔥

    *IDON NERA*🔥

    *A RUBUCE TAKE*🔥

    *KI KULANI*🔥

    *_uhmmmm_*😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊

    *Nasan zakuce ya da murmushi haka?*

    *Wanda bai shigo ba bazai gane ba*

    *Sai kin shigo daga ciki zaki gane me nake nufi*☺️☺️

    *KE DAGA JIN SUNAYEN LITATTAFAN MA KADAI KASAN CEWA AKWAI WANI BABBAN ABU MAI MATUQAR JAN HAKALI TATTARE DASU*

    *KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?*

    *KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?*

    Littafi daya—400
    Biyu—600
    Uku—-800
    Hudu—–1k
    Biyar din duka—-1200

    *ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥

    0022419171
    Maryam sani
    Access bank.

    Shaidar biya tanan👇🏻
    09033181070

    *MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN*

    09166221261

    🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
    *Ina yan uwa ‘yan nijer?*
    *Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

    +227 90 16 59 91

    Littafi daya—450CFA
    biyu—650CFA
    uku—-850CFA
    hudu—-1050 CFA
    Biyar—-1250CFA

    *A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*

    *SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!*

    *Thanks for choosing us*🔥*H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

    Page 11

  • Arubuce Ta Ke 16

    Arubuce Ta Ke 16

    Page 16

    Tunda ya fita yaso miqa mimi wajen hajiya sai ya wuce,idan ya dawo ya dauketa su wuce gida,amma tun baiyi nisa ba ogansa yayi kiransa,yayi shigowar ba zata yankinsu,don haka ya wuce da ita,sai ya ajjiyeta wajen rose abokiyar aikinsu ce,babbar macace haka,tana da matuqar kirki da son yara,sai yamma sosai sannan suka gama,ya dauketa suka yo gidan hajiyan.

    A qofar gida yayi parking,ya buda murfin motar ya fita ya zagaya ya fiddo mimi,yana riqe da hannunta suna shiga cikin gidan,tana basu labarin rose da irin abubuwan data siya mata,yana saurarenta yana murmushi,yaransa sune ke debe masa mafi yawa daga damuwae hafsat.

    Dai dai lokacin da widad ke daura alwala bakin famfon dake farfajiyar gidan,ta gama wanke qafafuwanta kenan tana gyara daurin dankwalinta gizo gizo ya taho,fallatsin ruwa yasa ya qara gudu,take ta rude,sai taga kamar kanta zaiyo,wannan yasa ta saki qara sannan kuma ta buga tsalle tana komawa gefe,bata dora ko ina ba sai a gabansa ba tare data lura da waye ke tsaye a wajen ba,saboda hankalinta gaba daya yana kan gizo gizon.

    Baya yaja yana bata fuska gami da dubanta,baya iya ganin fuskarta,sai sassalkar sumarta data yiwa kanta rumfa,sanadin dankwalinta da ya zame yake kuma riqe a hannunta tana ci gaba da kallon gizo gizon

    “Allah yasa bai tabani ba” yaji ta fadi tana ci gaba da maida daurin dankwalinta,wannan ya alamta masa ma batasan me tayi ba,sai ya kama hannun mimi suka shige cikin falo.

    “Yau kice a gidan kishiyata,ko batan kai kikayi?” Hajiya ta fada cikin dariya,yayin da su nujood dake falon suka fara gaidashi,yana amsa musu wayarsa ta dauki tsuwwa,sai ya fidda wayar yana dubawa,kawun sa ne,wanda shima gidansa ke jikin gidan kawu hassan,gida daya ne daa gaba daya,bayan rasuwar mahaifinsu aka raba gado aka fitarwa da kowa shiyyarsa ya gyara ya maidata gida me zaman kansa.

    Hajiya dake faman tsokanar mimi ya kalla

    “Hajiya bari naje,kawu imrana ke nemana,yace yaga motata a waje”

    “To ba laifi saika dawo” sai ya juya ya fice.

    A harabar gidan ya hangeta waje daya ta shimfida dankwalinta tana sallah,ya dauke kansa a hankali ya doshi gate din,ina hajiya ta samo wannan?,duka sauran yaran muhsin ne ya sani,amma wannan mai tsalle tsallen fa?. Dan tsaki yaja yana ture tunanin gefe guda ya doshi qofar gidan kawu imrana.

    Koda ta gama sallarta tattarawa tayi ta shige ciki,don ita ko sau daya ba wanda ta gani,tun daga shigowar tasa har fitarsa ta yanzun,bata jima da shiga ba hajjaa ta iso ta hada kansu suka wuce gida tana sake yima hajiya godiya da ban gajiya.

    Sai bayan magariba ya dawo,yaci abincinsa sukayi hira da hajiyan,sanda ya tasamma tafiya mimi tayi bacci,don haka ya barta a gidan

    “Babu matsala abbas kuwa idan ka barta?” Hajiyan ta tambaya a fakaice,saboda tasan halin hafsat,tana da tsananin nuna son ‘ya’ya,bata iya boyewa gaban kowa,idan ka gansu sun kwana wani guri to tare da ita ne.

    Wani abu yaji ya tsaya mas a wuya,jikinsa yayi sanyi,mahaifiyarsa ke shakku da kokwanton kwanan diyar da shi ua haifeta a hannunta?,tabbas da saake,akwai kuma gyara

    “Ba komai hajiya,idanma kina buqatar wasu qarin kwanakin sai na debo miki kayanta” murmushi ta saki tana shafa kan mimin

    “A’ah,kwana dayan ma yayi alhmdlh” boyayyar ajiyar zuciya ya sauke,sukayi sallama ya fita.

    Yana tuqi a hanya amma tunani ne fal kwanyarsa,qarar wayarsa ce ta taimaka masa ta katse masa tunanin,ya duba mai kiran,sai ya dan saki miskilin murmushin nan nasa,ya miqa hannu ya daga

    “Allah ya taimakeka ranka ya dade,tuba nake,kwana biyu an zubda ni,naji tsoron kada hakan ya zama silar watsewar zumunci nace bari na kiraka”

    “Wallahi ko yau naso shiga na gaida umma,kawu ma’aruf ne ya tsaidani,sai kuma na sha’afa,ta yaya zan manta da kai,ayyuka ne suka taru sukayimin yawa,that’s why na ajjiyema governor ADC dinsa saboda na ragewa kaina wasun sabgogin,so kuma maimakon su barni na huta,wallahi kaga sun sake cillani KD”

    “Naji labari,ina nan ina tunanin me yasa ka ajjiye appointment din?,bayan kana da sauran lokaci?” Kansa ya shafa da hannunsa

    “Mu hadu kawai gobe idan kana gari”

    “Ina nan,babu damuwa zan sameka gida”

    “To sai na ganka” sukayi sallama ya ajjiye wayar yana furzar da iska me zafi daga bakinsa,hadi da sanya idanunsa kan hanya yana duba shagon dake masa aski,ya samu suna nan don haka ya gangara yayi parking ya kashe motar ya fito.

    Babban kanti ne na matasa masu aji,masu j da jini a jika wadanda duniyar ke garawa,suna qaruwa ga jikinsa sosai,sun kuma san matsayinsa,don haka tarbar musamman sukayi masa,ya zauna yana duba jaridar da suke ajewa kafin a gamawa wanda ka samu.

    Goma na dare ya baro wajen,ya tsaya ya siya fruit ya wuce gida,don yaga kaman nasun ya qare,to amma babu lallai ta gaya masa babu ya sanya a kawo kamar yadda aka saba,qila sai ya tashi amfani dashi sannan tace masa babun.

    Kulle ko ina yayi sannan ya wuce sashenta don ya duba lafiyarsu kamar yadda ya saba,ko me sukayi da ita baya fasa wannan,ko bai shiga don ita ba zai shiga don yaransa.

    Abun mamaki yau zaune ya sameta a falon,saidai fuskarta gana daya babu annuri,yau din ba laifi,wani lace ne a jikinta peach color dinkin riga da zani,fuskarta tas babu digon komai,sai daurin ture kaga tsiya da tayi.

    Tana daga zaunen tayi masa sannu da zuwa,ya amsa mata yana wucewa dakinsu mimi,yaga nawwara sannan ya fito,sai ta miqe tana cewa

    “Ina kaje wai?,sanda ka shigo gidan nan fa goma ta wuce” hannayensa zube a aljihun wandonsa ya waiwayo ya zube mata manyan idanunsa yana kallonta,a nutse ya buda baki

    “Ina wajen hajiya,daga nan na wuce aski” ya bata amsa yana kafeta da kallo me alamta sai kuma me?,kasa jurar idanuwan nasa tayi,sai ta kauda kanta,cikin salo na mita tace

    “Amma yanzu dai tsakani da Allah duk inda kaga dama kake zuwa,kama daina gayamin kana waje kaza” hannunsa ya fidda daga aljihunsa ya juya kawai yaci gaba da tafiya ba tare daya tanka mata ba

    “Ina mimi?” Ta fada tans leqe leqe,don sai a sannan hankalinta ya bata ba tare suka shigo ba

    “Tana wajen hajiya,zata kwana can” wani abune yayi mata tsaye a maqoshi,har ta bude baki zatayi magana sai kuma ta hadiye data tuna da maganganun anty ummee,ranta a bace amma tayi qoqarin rage kaifin bacin ran nata daga samsn fuskarta ta sake cewa dashi

    “Ga abincinka” ya riga ya qoshi sosai,amma yana cewa bazaici din ba sabuwar magana zata balle da ita,abinda bai buqata

    “Me kika dafa?”
    “Tuwon shinkafa ne” kai ya jinjina,ba kasafai tuwon shinkafarta ke shiga ba,koda bata jima da gamashi ba kana gutsura yana wargajewa,ga uban gaari da zaka yita cin karo dashi a ciki wanda ta d’aure tuwon

    “Babu wani abun sai shi?” Sai a sannan ta tuna ta yiwa anty ummee dafadukan taliya,wadda har shi ta dafa amma anty ummee din tace ta daure ta canza masa abincin da tasan yafi so,hakan zai sake sassauto dashi

    “Sai jallop din taliya” kai ya jinjina,duka babu wanda zai iya ci,sai yace da ita

    “Hadomin black tea kawai,ki saka kayan qamshi please sosai a ciki”

    “Tom” ta amsa takaici na cikata,baisan tana yi ba ya sanya kai ya fice,saita daga kai tana kallon agogo,takaici goma da shirin,ta zauna ta wahala tayi masa tuwon amma ya watsa mata qasa a ido,ita anty ummee idan tana bata wasu shawarwarin rashun sanin halin abbas dinne yasa take gaya matan,sannan yanzun qarfe goma harda kusan rabi a sanya mutum wani shig kitchen,ko uwarta bata taba bata wannan aikin ba,tana qananun motoci haka ta shige kitchen din,rabi da rabin hankalinta yana kan mimi dake wajen hajiyar,taja tsaki yafi a qirga,wai duka duka nawa mimin take da tsohuwar zata nace sai ta kwana wajenta(ni kuwa nace uhmmm,sai kace ke din wata uwar kike iya musu).

    Saman tray ta kammala komai ta wuce sassanshi dashi,sanda ta shiga bedroom din taji motsin ruwa a toilet,da alama wanka yakeyi kenan,sai ta dora masa saman madubi tana tabe baki,shi mutum Allahn da yayishi bashi da wani aiki saina wanka kamar kwado?,da wannan tunanin ta koma nata sassan don ta kashe wutar ta kuma dauko nawwara,don a nan yau tayi niyyar kwana.

    Nawwaran kawai ta dauko,wata zuciyar na cewa ta dauko turare da night gown amma taji ba zata iya ba,ta rufe sassan ta koma nashi. Har sanda ta koma din bai fito ba,sai ta kwantar da yarinyar saman gadon,ta zauna saman sofa bed tana danna wayar ta.

    Ringing wayarsa dake saman madubi ta fara,saita miqe da hanzari kai kace ita ake kira,haka dabi’arta take,duk wanda zai kira saita duba waye idan baya kusa da wayar,idan kuwa yana kusa kunnuwanta gaba daya tafiya suke ga wayar,sai ta tantance me yakeyi kafin taci gaba da harkarta,ta nufi wayar tana duba me kiran kamar yadda ta saba,sai taga sunan rose.

    *RUMBUN K’AYA*🔥

    *DAUDAR GORA*🔥

    *IDON NERA*🔥

    *A RUBUCE TAKE*🔥

    *KI KULANI*🔥

    *_uhmmmm_*😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊

    *Nasan zakuce ya da murmushi haka?*

    *Wanda bai shigo ba bazai gane ba*

    *Sai kin shigo daga ciki zaki gane me nake nufi*☺️☺️

    *KE DAGA JIN SUNAYEN LITATTAFAN MA KADAI KASAN CEWA AKWAI WANI BABBAN ABU MAI MATUQAR JAN HAKALI TATTARE DASU*

    *KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?*

    *KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?*

    Littafi daya—400
    Biyu—600
    Uku—-800
    Hudu—–1k
    Biyar din duka—-1200

    *ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥

    0022419171
    Maryam sani
    Access bank.

    Shaidar biya tanan👇🏻
    09033181070

    *MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN*

    09166221261

    🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
    *Ina yan uwa ‘yan nijer?*
    *Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

    +227 90 16 59 91

    Littafi daya—450CFA
    biyu—650CFA
    uku—-850CFA
    hudu—-1050 CFA
    Biyar—-1250CFA

    *A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*

    *SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!*

    *Thanks for choosing us*🔥[2/16, 10:43 AM] Sweet sis: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • Duk Karfin Izzata Book 2 Page 32

    Duk Karfin Izzata Book 2 Page 32

    Page 32

    …..Gudu Bgs ke shararawa da motar sa har Hiyana ta fara tsorata. chikin kanƙanin lokacin suka isa wajen su Aryan Shahram na isa ba daɗewa bgs ya iso tun bai karisa kashe motar ba ya fito cikin sauri ya kariso wajen da Aryan ke tsugunne kaban yarinyar da suka buge “me ma ya fito da kai Aryan?” Sai lokacin Aryan ya ɗago kai a hanzarce ya mike cike da damuwa yace “mu karisa hospital daga baya mayi magana” mai da kallon sa Bgs yayi kan yarinyar da suka buge kallo ɗaya ya mata ya kawar da kansa yana faɗin “Aryan me ya ruɗa ka haka da ka kasa gane yarinyar bata mutuba wai meke faruwa ne?” Wucewa Aryan yayi ba tare da yayi Magana ba ya karisa wajen motar sa ya buɗe ya ɗauko diyana dake sume ya nufi motar Bgs da sauri Shahram ya buɗe masa kofar mota a razane Hiyana ta buɗe motar ta fito ganin diyana a hannun yaya Aryan kamar ta mutu dai dai lokacin Bgs ma ya iso wajen tana kokarin karisawa wajen Aryan bgs ya rikota chikin ruɗu tace “sake Ni” waro ido waje yayi yana kallon ta ganin bai sake ta bane ya sa ta ɗago ido dan taga wanenen kallo ɗaya ta masa taji ta dawo cikin hayyacin ta kasa tayi da kai sai kuma hawaye ya fara bin kuncin ta jawota jikin sa yayi dan ba zai iya barin ta ta nufi Aryan ba kallon ɗaya yayiwa diyana ya gane matsalar. “yaya Prince me ya samu diyana? Naga bata numfashi” tayi maganar cikin shesshekar kuka,hannun ta ya kama ba tare da yayi magana ba ya shiga gidan gaba na motar tare da ɗaurata kan cinyar sa umarni Aryan ya bawa Shahram akan ya ɗauko yarinyar da suka buge ɗin nan ya sata a motar sa. Ɗauko ta Shahram yayi ya sanya ta motar sa “Aryan ka dawo nan bari na jamu” chewar Bgs shiru Aryan yayi bai yi magana ba ya tada motar da gudun gaske suka bar wajen Shahram ya rufa musu baya.

    Chikin kanƙanin lokacin suka isa PRINCE SAFRAS HOSPITAL hannu bibbiyu aka karɓesu chikin sauri akayi A&E da su aka fara basu taimakon gaggawa shiru hiyana ta tsaya kusa da bgs tana addu’ar Allah ya sa diyana bata ji wani ciwo sosai ba zubawa Aryan dake kai kawo a bakin kofar accident and emergency ido bgs yayi ya ma rasa me zai ce masa. Tsawon 30mins suna tsaye ba wanda yace da wani ko uppan. suna tsaye mai sai da face mask yazo wucewa kiran sa bgs yayi ya ansa biyu ya sanya ɗaya ya miƙa wa hiyana ɗaya kallon mai sai da face mark ɗin yayi kallo ɗaya ya kawar da kansa kafin yace “ka bamu sa daka ne? dan bamu fito da kuɗi ba” murmushi ɗan yaron yayi kafin yace “ba komai oga,ae sadakar face mark kamar haka kam ba yau na fara ba Allah ya bawa mara lfy ku lfy” yana kai karshen maganar ya wuce chikin sanyin murya bgs yace “zo ɗan yaro” juyowa yayi ya dawo kusa da su “what is your name? da murmushi a kan face nashi yace “my name is Sadiq” hannu bgs ya miƙa masa da mamaki hiyana ke kallon su daman bgs yana kula talakawa kamar haka ne yanzu duk kyankyanin san nan zai haɗa hannu da wanna yaro ɗan dattin nan lallai ma tab. zazzakar voice nashi ne ya katse mata tunani yace “ina iyayen ka? Lokaci guda fiskar yaron ya sauya murya kamar zai fashe da kuka yace “ni bani da mama kuma bani da baba a hannun yayata wadda nake bi nake ita kaɗai ta rage min a duniya” kallon yaron da kyau bgs yayi kwata kwata yaron nan ba zai wuchi 13 years ba amma wai a hannun yayar sa wadda yake bi to ko itama ba zata 15 to 16 years ba kenan ina yan uwan maman sa da baban sa yayi nisa chikin tunani yaron ya katse shi da cewa “oga zan iya tafiya? Kallon Shahram bgs yayi chike da kaunar yaron ya fara magana “Shahram kuje ka tawomin da yar uwar tasa” waro ido waje yaron yayi chikin tsoro yace “dan Allah karka cutar da mu wlh bamu da kowa bamu da komai daga ni sai ita iya face mark ɗin nan nake sayar wa na kai mana kuɗi muci abin ci dan Allah idan ma face mark ɗin kake so tom gashi amma mu dai ka kyale mu” ganin yaron ya tsorata sosai ya sanya bgs ya shafa kan sa chikin kulawa yace “mai sunan Abba ka kwantar da hankalin ni soja ne ba zan cutar da kai ba sai dai ma na yaki masu cutar da mutane ina son akawomin yar uwar kane dan naji ina yan uwan ku suke da har suka barku kuke yawo haka” girgiza kai yaron yayi alamar shikenan ita dai hiyana ta zuba musu ido tana ganin ikon Allah bin yaron tayi da kallo har suka wuce da Shahram. dai dai lokacin Dr ya fito daga A&E chikin sauri Aryan ya tare sa yana faɗin “Dr ya jikin nasu” chike da rashin mutunci Dr yace “kubar yara suna yawo a gari sai abu ya same su kuzo ku dame mu a asibiti yanzu ka duba irin fyaɗen da aka yiwa yarinyar nan lokacin da aka mata ina k…bai kai karshen maganar ba Aryan ya ɗauke sa da wata mahaukaciyar mari wadda ya sa shi yin tangal tangal kamar zai faɗin lokacin guda yaji duniya ta tsaya chak chikin zafin nama ya danko wuyar rigar sa yana kokarin kara masa mari bgs ya kariso wajen tare da rike hannun sa ta baya dai dai lokacin Doctor Peter and doctor John suka fito da sauri suka kariso wajen ganin abun da ke faruwa,rai a matukar ɓace Aryan ya dubi dr John ya fara magana “kai John wanene wanna? yaushe kuka kawo shi aiki a hospital nan? “I’m sorry sir bai daɗe da fara aikk bane shi ya sanya bai san ka ba kuma ina ganin bai lura da face naka da kyau bane shi ya sa har yake kokarin ja da kai amma amasa afuwa” Aryan zai yi magana bga ya rufe masa baki chikin nitsuwa ya dubi dr Peter ya fara magana “dr ya jikin nasu?” ɗan murmushin dr Peter yayi kafin ya fara magana “jiki da sauki sai dai dukkan su basu farfaɗo ba mun dai yi nasarar shawo kan matsalar su yanzu zamu chanja musu ɗaki zuwa ɗaki na musamman” shiru Aryan yayi ya kasa magana, wucewa dr Peter da dr John sukayi juyawa bgs yayi ya nufi wajen motar su har ya ɗan yi nisa ya juyo yace “ke mutafi” tana tsaye kusa da Aryan kamar bata ji me yace ba kallon ta Aryan yayi “sister yaya Prince na kiran ki” dogon numfashi taja tare da sauke nauyayyar ajiyar zuchiya kafin tace “yaya Aryan menenen ya samu diyana? Satar kallon bgs yayi ta kasan ido yayin da shima bgs ɗin ya tsare sa da ido kasa magana yayi bashi da amsar da zai bata “yaya Aryan dan Allah ka faɗa min me ya same ta idan ba haka ba zuciya ta zata iya bugawa ka….bata kai karshen maganar ba aka fito da diyana a saman gado tana kwance,chikin sauri ta nufesu;tana kiran sunan ta “diyana!!diyana!!” bata kai ga karisawa wajen ba ya hamko hannun ta tare da jawo ta ta faɗa saman faffaɗar kirjin sa hannu ya sanya ya kwantar da kanta a kirjin sa “yaya Prince dan Allah ka sake ni inje in ga meke damun diyana,ɗazun fa muna tare da ita lfy ta kalau kuma accident da suka yi yaya Aryan yace basu ji ciwo ba iya yarinyar chan suka buge” hannu ya ɗaura mata a saman bakin ta yana faɗin “shiiiiiii” buɗe baki tayi zata sake magana yayi sauri sanya mata manuniyar yatsar sa a baki ya danne harshen ta chizon yatsan nashi tayi har sai da yace “wash” sai da ya ga an wuce da su diyana sanna ya zame hannun sa daga bakin ta tare da raba jikin su ya kama hannun ta suka koma wajen mota sai magiya take masa akan ya kai ta taga diyana amma yaki kula ta

    chikin motar su Aryan ya dawo ya zauna tare da chiro wayar sa ya fara kiran layin Ammi.
    “Yaya Prince inje? Zanyi magana kenan wayar sa ta fara kara satar kallon ta yayi ta kasan ido kafin yayi picking call ɗin ya koma daga ɗan nesa da su gyara tsayuwan ta tayi a jikin motar ta harɗe hannu a kirji tana tunanin ko me ya sanya diyana rashin lfy lokacin guda har da suma bata, murnushin tayi lokacin da wani tunani ya faɗo mata a rai ko dai yaya Aryan ne yayi maganin ta tab lallai in dai ko haka ne yau akoi dirama dan idan diyana ta farka sai yaya Aryan ya gwammaci da bai taɓa ta ba. tayi nisa chikin tunanin kamar daga sama taga mutun a gaban ta yana magana “sannun ki yanmata” kasa kasa tace “yauwa sannu” duk tunanin ta tambayar ta wani abu zai yi sai ta ga akasin haka,sai washe baki yake yana surutu “amma gaskiya yammata ke kyakkyawa ce duk da kin sanya face mark hakan bai hana kyanki bayyana ba ban taɓa ganin masu blue eyes a zahiri ba sai a film yau kam gashi na gani dan Allah idan ba damuwa ki tai makamin da phone number,dan mu rinƙa gaisawa,kuma ni sunana tarif,a nan kano nake babana mai kuɗi ne sosai kinga baki da matsala in dai akan kuɗi ne” tsaki taja kafin tace “malam ni matar Aure ce ka kama kan ka” murnushin yayi yana faɗin “haka kuke kyawawan matan nan idan mutun yace yana son ku sai ku fara cewa kuna da Aure to nima ai mijin Aure ne” shiru tayi bata yi magana ba lokacin guda ta birkice ta rasa ina zata sa ranta,ganin ta birkice hankali ta baya kan sa yana bayan sa ne ya sanya yace “yammata menene naga kin birkice haka yana maganar yana juyowa karaf idon sa ya sauka kan bgs dake tsaye a bayan sa fuska a ɗaure kamar an aiko masa da sakon mutuwa

    murmushi ya saki yana faɗin “au chemin zakiyi yayan ki kika gani to ba sai na gabatar da kai na ba tun da da aure nake son ki amma gaskiya duk da kunsa face mark kuna kama sosai da yayan nan naki kamar wasu larabawa, to babban yaya sunana dai tarif kuma son kanwar ka da Aure nake” ya kai karshen maganar tare da miƙawa bgs hannu akan suyi musabaha ba musu bgs ya miƙa masa hannu da ido yayi wa hiyana alama akan ta tashe a awajen. hannun sa tarif ya kama ta nufin su gaisa chikin kwanchiyar hankali bgs ya muɗe hannun tarif baya jikake kas kashin ya karye,ihun azaba tarif ya saki wadda ya sanya Aryan fitowa daga chikin motar ba shiri a tsorace yake kallon yadda bgs ya sauya lokaci guda idon sa sun sauya sunyi jaa sosai kamar garwashin wuta sai wani hukuci yake tarif sai ihu yake bgs yaki sakin hannun nashi duk da ya karya masa hannu,a zafafe Aryan yace “bgs lfy? Meke faruwa? Me ya haɗa ku?” ko kallon in da Aryan yake bgs bai yi ba
    kallon hiyana dake tsaye a gefe ta takure jikin ta waje guda Aryan yayi “sister meke faruwa?” Lokaci guda taji kwarin guiwa ya zo mata tuna abun da ya faru yau da safe tayi chike da dakiyar zuciya ta fara magana “yaya Aryan wai dan yazo yace yana sona ne shine yaya Prince yake bugun sa bayan kuma shine yace ina da damar da zanyi soyayya da kowa in na samu wanda nake so zai aura min shi da kansa amma shine kuma yake dukan mutumin nan dan yace yana sona” bakaramin daɗi Aryan ya ji ba lokacin da zasu gwada bgs yayi chike da tsoron abun da bgs zai iya aikata wa ya dube shi ya fara magana “to in dai haka ne ai bai kamata ka buge sa ba ko ka manta yadda mukayi da kai da safe? Ton ida…..bai kai karshen maganar ba ya ja birki ba shiri saka makon wurgi da bgs yayi da tarif gefe ihun azaba tarif ya saki lokacin guda ya ɗauke kamar an ɗauke wutan nefa a fusace yayi kan Aryan ya dunkule hannu zai kai masa bugu hiyana ta kwasa a guje ta shiga tsakiyar su ta gefen ido ya gan ta da hannu ɗaya ya damko ta ya fisgo ta ta faɗa saman kirjin sa fasa kai wa Aryan bugun yayi zullewa Aryan yayi ya juya yana dariya kasa kasa sai da ya ɗanyi nisa ya juyo yace “wlh bgs baka da kirki yanzu ka sumar wa sister saurayin ta har da karaya fa yanzu idan sister na son shi fa? kaga kai da zaka haɗa aure kai zakayi jinyar sa sai ya warke sai ka haɗa Aure tun da kaine yaya babba” yana kai karshen maganar ya wuce ya nufi cikin A&E dan nemo nurse suzo su ɗauki tarif su bashi tai makon gaggawa

    damkar wuyar hiyana yayi chikin fushi yaja ta ya turata cikin mota a fusace ya shiga motar ya tayar sai huci yake kamar wani zaki da gudu ya figi motar ya nufi gate ɗin hospital ɗin dai dai zai fita motocin su Ammi su danno kai cikin asibitin ajere motocin suke na sojoji ɗaya a gaba sai wadda Ammi da Ummi ke ciki a tsakiya sai na sojoji ɗaya a hayan su kallo ɗaya ya musu ya kau da kai ya kara gudun motar sa suka bar asibitin

    Chikin kanƙanin lokacin suka isa gida tun bai gama kashe motar ba hiyana ta buɗe motar ta fita da gudu gaske dan ta lura baya cikin hayyacin sa kai tsaye fada ta nufa dan tasan idan ba Abba ko Ammi ba bawan da zai iya tare mata faɗan nan. Tana shiga fada bayan Abba ta nufa ta ɓuya tana mai da numfashi da kyar da kyar “hiyana meke faruwa? kasa maga tayi dan gudun da tayi juyowa Abba yayi yana kallon ta yana kokarin sake magana yaji takun jarumin maza ya tinkaro su ko bai juya ba yasan bgs ne dan takun sa da ban ne dana kowa,tun da yaji irin takun da bgs keyi yasan ba lfy ba chikin sauri ya miƙe tare da juyowa bai kai ga buɗe baki ba bgs ya damko gashin kanta a fusace ya jata suka nufi hanyar fita “Safras menene ta maka? Ko kallon Abba bai yi ba bare yayi magana chi gaba da tafiya yayi
    da sauri Abba ya sha gaban su tare da ɗaure fuska sosai yace “me ta maka?” ya kai karshen maganar tare da sanya hannu ya jawo hiyana daga hannun sa,shiru bgs ya tsaya dan bai da niyar yin magana da Abba “Safras nace me ta maka!? A fusace yace “Abba pls ka kyale ni na hukun ta yarinyar nan” yayi maganar cukin nitsuwa da girmamawa “ban ce bazaka hukunta taba amma me tamaka?” Kara ɗaure fuska sosai bgs yayi yace “Abba wai yarinyar nan tayi girman da ina magana zata bani amsa” juyowa Abba yayi yana kallon hiyana “hiyana me ya haɗaki da yayan ki?” Murya ta har kerma yake tace “Abba wani ne yazo yace yana sona kuma….bata karisa maganar ba bgs ya wanka wa bakin ta mari ihu ta fasa ta kara kankame Abba shiru Abba yayi a ransa yana faɗin lallai hiyana kin kira ruwa duk ƴaƴana ba wan da ya kai Safras kishin bala’i bana jin yau wanna rigima zata kare da wuri,ganin Abba yayi shiru ne ya sai bgs ya sanya hannu ya damko ta cikin sauri Abba ya rike ta yana faɗin “tsaya mana ai ban yanke nawa hukunci ba tunun nan”kallon hiyana yayi ya cigaba da cewa “ki bawa yayan ki hakuri ki tafi ɗaki ta gama tsorata da lamarin Bgs jikin ta har rawa yake ta tsuggunna kasa a nitse tace “yaya Prince dan Allah kayi hakuri ba zan sake ba” kara ɗaure fuska yayi chike da bada umarni yace “ki tashi kije part na ki fara frog jump ina zuwa” ɗago ido tayi tana kalli Abba kawar da kai gefe Abba yayi dan ba zai iya cewa bgs ya kyaleta a gaban ta ba idan yayi hakan gobe ma zata sake yiwa mijin ta raini jiki ba kwari ta miƙe ta fice daga fadan ta nufi part nashi.

    A fusace shima ya juya zai bi bayan ta Abba yayi saurin damko hannun sa yana faɗin “zo mana ai bamu gama ba” shiru yayi bayyi magana ba zaunar da shi Abba yayi ya fara magana “pls Safras ka rinƙa sawa zuciyar ka ruwan sanyi karin ƙa tausayin yarinyar nan kaji? Shiru yayi bai yi magana ba,dafa kafaɗar sa Abba yayi cikin rarrashi ya cigaba da magana “my son ina son in ga kana tausayawa yarinyar nan kana bata kulawa pls kamin haka ko dan farincikina” shiru nan ma yayi bai yi magana ba “my son ina Aryan? da sauri yace “na aike sa yamin wani aiki” murmushi Abba yayi kafin yace “yaushe ka fara karya my son?” juyo da idon sa yayi kan face ɗin Abba ya mai mai ta maganar “karya kuma Abba!?” hararar wasa Abba ya jefa masa kafin yace “kwarai ba gaskiya ka faɗa ba tun ɗazun nake maka magana baka amsa min ba amma daga yin maganar Aryan kayi saurin bani amsa hakan ya tabbatar min da wani abu ya saɓa akoi abun da kuke ɓoye min” “Abba babu wani abu da muke ɓoye ma” yana kai karshen maganar ya miƙe ya fice da sauri, aniyar zuciya Abba ya sauke yana addu’ar Allah ya sauwakawa Safras zafin zuciyar sa.

    Yana fita fada yaci karo da Shahram da Sadiq tare da yar uwar sa tsayuwa yayi suka kariso wajen har kasa yarinyar ta tsugunna cikin girmamawa tace “ina wuni” bai amsa gaisuwar nata ba kallo ɗaya ya mata ya kawar da kan sa shiru yayi na yan mintoci kafin yace “ina son sanin ina iyayen ku?” “Baban mu ya rasu maman mu kuma tun muna yara ta tafi aiki a makka har yau bata sake dawowa ba” shiru ya sake yi na yan mintoci kafin yace “ina yan uwan maman ku da baban ku?” “maman mu yar kaduna ce yan uwan ta basu nan kano suna chan kaduna bamu san in da suke ba a kaduna su kuma yan uwan baban mu basa son mu ko munje gidan su korin mu suke” kallon Shahram yayi yace “ka kai mace part ɗin Ammi kace Auta ta mata abun da ya dace shi kuma namijin ka kai shi part ɗin su Omar zan yi magana da Ammi zan wai wai ye su” yana karshen maganar ya juya ya nufi part na shi yana jiyo muryan su suna masa godiya.

    Tun daga palo yake jiyo kukan ta har ya kai cikin bedroom ɗin frog jump take tana kuka da hawaye sharɓa sharɓa lokacin guda yaji ta bashi tausayi, wucewa yayi ya zauna a bakin gado yana kallon yadda take frog jump da kyar da kyar,kewaye ɗakin take da frog jump har ta kariso ta gaban sa kama dogayen kafofin sa tayi chikin shasshekar kuka ta fara magana “yaya Prince dan Allah kayi hakuri wlh ba zan sake ba na tuba wanna frog jump ɗin akoi wahala na gaji bazan iya ba dan Allah kayafe min” hannu ya sanya ya ɗagota amma ta kasa miƙewa tashi yayi ya ɗaga ta chak ya ɗaura ta saman gadon tare da zama gefen ta yana kallon face nata “yau na miki afuwa ne saboda dalili ɗaya idan kika sake yimin abun da kika min yau sai na lahira ya fi jin daɗi” faɗowa tayi saman faffaɗar kirjin sa tana shasshekar kuka tana faɗin “amma yaya Prince ba kai kace idan na samu miji zaka min aure ba?” ɗago haɓar ta yayi yace “eh ni nace haka amma ai ba mijin kan hanya nace ki samo ba ko?” hannunta ta zuro ta bayan sa ta kewaye sa da shi tana faɗin “to ai ba zan samu wani mijin ba idan a gida ne” yatsa ya ɗaura mata a saman bakin ta yana faɗin “shiiiii ya isa maganar” “yaya Prince dan Allah…..ba ta kai ga karisa maganar ba ya ɗaura hannu sa saman bakin ta yana girgiza mata kai, shiru tayi ta kwantar da kan ta saman kirjin sa. Zame hijabin kan ta yayi ya mai da shi wuyar ta ya fara shafa lallausan bakin gashin kanta shafa bayan sa ta fara yi itama, lokaci guda yayi saurin raba ta da jikin sa yana mamakin how comes yake ji feeling da ta taɓa shi? runtse ido yayi na yan mintoci kafin ya sake buɗe wa miƙewa yayi a zafafe ya nufi wajen mirror da sauri ta riko hannun sa ta marairaice murya tace “yaya Prince dan Allah ka mai da ni asibiti ina son ganin diyana” kwace hannun sa yayi ya wuce gaban mirror yana faɗin “an jima da yanma zamu koma” ya kai karshen maganar dai dai lokacin da ya buɗe drawer mirror ya fito da kwalin alluran yana dubawa

    To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu akoi fa chakwakiya

    To yan Duk Karfin Izzata comments section group Brigadier general Safras ne ke magana sako ya iso kunnena irin zagin da kuke min a group ya iso ni to ina son ku buɗe kunnenku ku saurare ni idan kuka bari rai na ya ɓaci zan wurgo muku bom ya tarwatse ku 😡😎😹😹😹

    💖The talent troupe writer’s 💖

     

    💋Duk Karfin Izzata 💋

    By Star Lady

  • Duk Karfin Izzata Book 2 Page 34

    Duk Karfin Izzata Book 2 Page 34

    Page 34

    Barci mai daɗi ne ya kwashe su dukkan su biyu suna manne da juna ya ƙanƙame ta kamar wani yace zai kwace masa ita.

    3am dai dai ya farka tare da waro idon sa waje juyawa gefen sa yayi bata awajen cikin kasala ya miƙe zaune chan ya hangota saman dadduma ta idar da sallah tana karatun al Qur’ani mai girma,zuro kafafunsa kasa yayi kafin ya miƙe tsaye ya nufi toilet.

    A gurguje yayi wanka tare da ɗauro alwala kafin ya fito ya wuce dressing room jim kaɗan ya fito sanye da jallabiya fara tas ganin ya nufo wajen tane ya sanya ta miƙe ta bashi daddumar ta koma saman sofa ta zauna tare da ɗan kwantar da kan ta jikin sofar tana karatu kasa kasa.

    Nafila raka’a 4 yayi sanna yayi shafae da witiri yayi sallama tare da gyara zaman sa yana jero addu’oe.
    Almost 30mins ya ɗauka yana addu’a kafin ya miƙe ya nufi saman sofar da take zaune,a nitse ya ansa Al Qur’ani hannun ta kasan cewar tayi barci zaune a wajen bayan ya mai da Al Qur’ani ma zaunin sa ne ya dawo ya ɗauke ta chak suka koma saman gado,kwanciya yayi tare da ita a jikin sa yana ɗan shafa bayan ta
    Kasa kasa cikin muryan barci tace “yaya Prince addu’ar me kamin? Ko dai baka sani cikin addu’ar kane? kallon face nata yayi kafin ya ɗan kawar da kan sa gefe “ina saki mana duk wanda ma yake gidan nan ina sa shi a addu’a ta” “to amma yaya Prince wani irin addu’a kake min? Shiru yayi bai tanka taba hannu ta sanya saman dogon hancin sa tana faɗin “yaya Prince me ya sa baka son yi mini magana sosai? Bayan kuma kai kace na koya maka magana” shiru nan ma yayi kamar bai ji taɓa “yaya Prince dan Allah…bai bari ta karisa maganar ba ya ɗaura hannun sa saman lallausan lips nata yana faɗin “sarkin magana kiyi barci” kukan shagwaɓa ta saka masa tana faɗin “ni dai yaya Prince hira nake son muyi gaskiya” zuba mata ido yayi yana mamakinta idan tana irin wanna shagwaɓan ba karamin burge sa take ba “uhm uhm yaya Prince wai ba zaka yi magana bane?” da wata daddaɗar voice da bai san yana da ita ba ya fara magana sak yadda take “to me kike so ince miki?” mamaki ne ya sanya ta waro manya manyan ido ta wajen daman yaya Prince ma ya iya shagwaɓa ba karamin burge ta abun yayi ba,ganin ta tsare sa da ido takasa magana ne ya sanya ya hura mata iska mai sanyi a face nata tare da ɗaga mata gera ɗaya alamar yane, cool murmushi ta saki kafin tace “yaya Prince Allah kai ɗin kyakkyawa ne sosai” kallon gefen ido ya mata da sexy voice yace “ba za dai kiyi barci ba kuma ba zaki kyale ni nayi ba ko?” Turo ɗan karamin bakin ta tayi cikin shagwaɓa ta fara magana “uhm uhm ni bana jin barcin ne ai kuma ban son kayi barci ka kyleni ni kaɗai” hannu ya ɗaura saman ɗan karamin bakin ta yana kewaye ɗan bakin yana faɗin “ba zaka ga baki ba sai magana at the first time idan mutun ya kalle ki zai ganki like you’re not talk” ya tsan nasa ta tura cikin bakin ta tana tsotsa kamar sweet,wani zirr zirr yake ji a jikin sa kamar ana masa allura cikin sauri ya zame yatsan nashi daga bakin nata dan bai san wata fitina yanzun nan “uhm uhm yaya Prince ni ka bani sweet na” girgiza kai yayi kafin yace “uhm uhm hannu nane sweet nakin? Baki ɓuɗe take kallon sa yadda ya kwaikwayi maganar nata ba karamin bata mamaki yayi ba amma yadda yayi maganar ya burgeta sosai da sosai,ganin alamar kamar ta tafi duniyar tunani ne ya sanya ya shafa fuskar ta da sauri ta ɗago ido ta ɗan kalle san kasa kasa tace “yaya Prince ai ya tsanka yafi sweet daɗi ni dai ka bani na cigaba da sha” “waya koya miki magana haka? turo baki ta daɗa yi tana faɗin “ni yaya Prince ba wanda ya koyamin ni da kai na na iya” “to why ban ta ɓa jin kinyi magana haka ba sai yau? gyara kwanciyar ta tayi da kyau a jikin sa kafin tace “ai daman mijina ne kawai yakamata na rinƙa yiwa magana haka ba wasu ba bai ma kamata wasu maza suji voice na ba idan ba miji na ba shi ya sanya bana magana sosai da wasu koda su diyana ne,voice na dan miji na kawai akayi shi” bakaramin daɗin kalaman ta yaji ba har ran shi lallai yarinyar nan tana da hankali da ilimi da sanin yakamata sosai kuma tana aiki da ilimin da take da shi ɗin
    ganin alamar ya ji daɗin maganar tane ya sanya tace “yaya Prince amma in tambaye ka mana? zuba mata ido yayi ba tare da yayi magana ba cigaba da magana tayi “yaya Prince me ya sa baka so na? Shiru yayi na yan mintoci kafin yace “ni nace miki bana son ki? girza masa kai tayi alamar a’a “kafin kuzo gidan nan sister mace ɗaya nake da shi Auta ina matikar kaunar ta fiye da kai na daga baya kukazo kamar yadda na ɗauki auta a raina haka kuma na ɗauke ku so dukkan ku ina kaunar ku” ajiyar zuciya ta sauke ba tare da tayi magana ba “lfy? Kike sauke ajiyar zuciya haka?” “Yaya Prince ban taɓa tunanin akoi kaunar mu ni da yan uwana a ranka ko kaɗan ba shi ya sanya da naji kace kana kaunar mu kamar yadda kake son Aunty Zahra sai naji daɗi sosai har rai na” shiru yayi tare da lunshe ido bai sake magana ba kankame sa tayi tana jin farinciki har ran ta da haka barci ya ɗauke su manne da juna.

    Washe gari misalin 7 suka gama shirin su na zuwa Maiduguri a tare suka jera zuwa part ɗin Ammi zaune suka same Ammi da yanmatan ta a palo har da diyana da ko tafiya bata iya yi sai dai a ɗaga ta.
    Tana ganin yaya Aryan ta sunkuyar da kan ta kasa dan bata son haɗa ido ta shi
    Gefe da gefen Ammi suka zauna suka sata a tsakiya kasan cewar tana zaune ne a saman sofa mai mazaunin mutun 3 cikin girmamawa su Zahra suka fara ɗaga musu gaisuwa Aryan ne kawai ya ansa gaisuwar bayan su Zahra sun gama gai da su su kuma suka gaida Ammi

    “Ina zaku je naga kunyi shiri haka?” basu bawa Ammi amsa ba dan basu so su faɗa wa koma batun rashin lfy Aunty farida dan kar su ɗagawa kowa hankali
    bgs ne yayi saurin cewe “Ammi na gama bincike na akan yaran nan dana sa aka kawo jiya,zasu zauna a gidan nan kafin mu koma Abdol zai je ya musu komai na school su fara karatu” waro ido waje Aryan yayi kafin yace “wasu yara kuma? Aina suke? Aina kuma ka samo su? Ammi ce tace “yarinyar ma tana ɗaki har yanzu bata saki jiki da muba bata son shiga cikin su Zahra da alama tsoron su take ji” “amma Ammi me ya sanya za’a kawo wasu kuma gidan nan wayan da bamu san su ba ko dai yan uwan mune? Chewar Aryan hararar wasa bgs ya wurga masa kafin yace “nayi binchike akan yaran suna da zuciya mai kyau wadda idan aka taimake su suma zasu iya taimaka wa wata al’umma nan gaba duk da sun taso cikin tsanani da wahala hakan baya hana su bautar Allah da dagewa wajen ganin sunci halak nasu duk da cewa iya face mark suke sayarwa suci abinci danace yaron ya bamu kyauta ya banu bai damu da cewa iya kan jarin su kenan ba bai damu da cewa idan ya bada sadaka shi zai rasa ba,duk ta laucin da suke ciki hakan baya hana su sadaka shiya sanya idan zakayi kyauta kar ka duba abun da zaka bayar ka duba ladar da zaka samu hakanne zai baka kwarin guiwar cigaba da kyautatawa na kasa da kai kullun ku kasan ce masu hangen ladan ku kar ku duba idan kun baya kazan ku zai ragu” murmushi Aryan yayi yana mamaki wai waya koyawa bgs magana mai tsawo haka mutumin da cewa okey ma wahala take masa ko da yake yanzu wa’azi yake wa su auta dan su rinƙa taimako.

    Ajiyar zuciya Ammi ta sauke kafin tace “gaskiya ne nima ɗan zaman da nayi da yarinyar na fahimci tana da hankali da son taimakon mutane yanzu dai ina zaku je kukayi wanna shiri haka? Miƙewa bgs yayi ya dubi hiyana dake zaune ta sunkuyar da kai kasa yace “ke ki same ni a part na” yana kai karshen maganar ya fice daga palon
    kallon diyana dake ta faman kunbure kumbure Aryan yayi cikin sanyi murya yace “my jidda ba gaisuwa? To ni bari na gaishe ki ya jiki? Kin rashi lfy?” Miƙewa Ammi tayi ta basu wajen a tare su Zahra suka miƙe hiyana ta fice daga palon ta nufi part ɗin bgs su kuma su Zahra suka wuce ɗakin su.

    Kamar jira Aryan yake Ammi ta fice tana fita ya dawo kusa da jiddan sa tare da riko hannun ta duka biyu cikin muryan rarrashi ya fara magana “I’m so so sorry my jidda kin ji ko? Ayiwa yaya Aryan afuwa da ran gwami ba zan kara ba” hararar sa tayi ta kasar ido ba tare da ta ɗago ta kalle sa ba kasa kasa ta fara magana “ni ai nace na yafa maka tun da Ammi ta sa baki amma ni bana son ka ba zan zauna da kai ba amayar dani gidan Aunty farida na” shafa kansa yayi tare da kara matsowa kusa da ita yace “ok ɗago idonki ki kalli cikin ido na kice bakya so na idan kikayi hakan i promise u that zan mai daki wajen Aunty farida” “ni ba sai na kalle ka ba kawai ka mai da ni can dan ni ba zan zauna da kai ba” dukar da kan sa yayi ya leko fuskar ta yana faɗin “eyaeeee my jidda da kan ta kefa tawace ba mai rabani da ke mrs Aryan” duka ta kai masa a baya tana faɗin “Allah yaya Aryan kabari bana so ni da gaske nake bana son ka”dariya yayi tare da jawota jikin sa yana faɗin “eyeeeee mrs Aryan yanzu kam kin tuna sunana kenan ba a hospital kin manta sunana ɗin ba har da cewa ban son kallon wanna mutumin” ya kai karshen yana kwaikwayar yadda tayi maganar,kokarin kwace jikin ta tayi daga nashi tana faɗin “ni ka kyale ni ba wasa nake maka ba Allah ba…bai bari ta idasa maganar ba ya rufe mata baki tare da raba jikin su dan bai san ya jata da magana ta cigaba da cewa bata son shi yasan wacece diyana ita mutunce da idan ka ja magana ta kafe akan abu tofa ko mai wuya bata sauyawa.

    Miƙewa tsaye yayi cikin sanyi murya yace “my jidda zan tafi Maiduguri amin addu’a” sai lokacin ta ɗago da sauri karaf suka haɗa ido kawar da idon ta tayi gefe kafin ta fara magana “dan Allah yaya Aryan ka tafi da ni sai ka barni wajen Aunty farida” dukowa yayi ba tare da yayi magana ba yayi kissing na goshin ta ya juya ya nufi kofar fita yana faɗin “ina kewar lallausan lips ɗin my jidda ta Allah ya baki lfy idan kin samu sauki zamuje tare” cikin sauri ya fice dan bai san jin kukan ta kuma yasan ba makawa sai tayi kuka haka ko akayi yana fita tasa kuka kamar wata yar baby ita ala dole sai an tafi da ita

    A ɓangaren hiyana kuwa tana shiga bedroom nashi zaune ta samesa a bakin gado da alama ita yake jira gaban sa tazo tana kokarin tsugunnawa ya jawota jikin sa cikin kunnen ta ya raɗa mata “waye ce ki gudu ɗazun?” Murmushin tayi tana mai jin daɗin sauyawar da yaya Prince yayi daga jiya zuwa yau abun ba karamin kayatar da ita yake ba duk da cewa yace shi ba son ta yake ba har da wani cewa ta samo miji ya mata aure to da alama dai maganar yaya Aryan ne gaskiya

    Hannu ya ɗaura saman wuyar ta yana shafawa “zanyi tafiya zuwa Maiduguri yanzu i need your prayer” buɗe baki tayi tana kokarin yin magana yayi sauri rufe mata baki yana faɗin “ni ba a nan nace ki min addu’a ba time ya tafi kamata yayi mu isa Maiduguri tun 7 amma yanzu almost 8:5 bamuma tafiba yanzu dai tashi min ajiki na bari mu wuce shagwaɓe fuska tayi kamar zatayi kuka tace “yaya Prince ayya zan bika” girgiza mata kai yayi tare da miƙa wa da ita tsaye ya nufi hanyar fita.

    Sai da suka fita palo ya sauke ta a tsakiyar palon ya manna mata kiss a goshi sannan ya wuce ya fice daga palon,zuba masa ido tayi har ya fice sanna ta koma ɗakin sa tafara gyara masa,bayan ta kammala ta cire kayan jikin ta tare da cire ɗan karamin nauran da ya bata ta ɗaura saman mirror ta shiga wanka.

    45mins ta ɗauka kafin ta fito ɗaure da towel a kirji ta ɗauki hijabin ta ta sanya ta fice daga ɗakin ta nufi part ɗin Ammi
    har zata shiga part ɗin Ammi sai ta tuna ta bar na’uran da ya bata a saman mirror sa girgiza kai kawai ta wuce cikin part ɗin Ammi tana faɗin “zan dawo na ɗauka anjima”

    tana shiga palon Ammi ta samu yaya Khalid yaya Fahad yaya Yusuf suna zaune ga matan su zaune kusa da su suna hira
    har kasa ta tsugunna ta gaida su cikin girmamawa sanna ta wuce ɗaki ta shirya cikin doguwar riga pink colour ta sanya hijabi har kasa sanna ta fito palo ta zauna kusa da diyana sai hira su Zahra suke

    “Yaya Khalid dan Allah ka kai ni gyaran gashi pls”chewar Zahra tayi maganar a shagwaɓe Khalid ya buɗe baki zai yi magana hiyana ta rigasa da cewa “Ni ma yaya Khalid muje tare dan nima gashi na yana son gyara” murmushi Khalid yayi kafin yace “ok to ku shirya muje” kallon su amrat Zahra tayi tace “amrat lamrat ku fa zaku je ne? Har suna haɗa baki wajen cewa “aa ba zamu je ba” yar dariya Khalid yayi kafin yace “oh sister’s hadda saurin haɗa baki haka to shikenan yanzu dai auta dake da sister ku shirya muje” da sauri diyana tace “nima ina son zuwa” girgiza kai Khalid yayi yana faɗin “aa jidda ki bari sai kin samu sauki sai na kai ki ko kuma Aryan ya kai ki” shiru tayi bata sake magana ba dan bata son yawan magana da su Khalid,mikewa Zahra tayi ta kama hannun hiyana tana faɗin “muje mu shirya idan munyi sallar azahar sai yaya Khalid ya kai mu,tana kai karshen maganar suka wuce ɗaki.

    Miƙewa Yusuf yay ya riko hannun lamrat yana faɗin “muje mu gaida Ummi” “to” kawai tace kafin ta miƙe su fice daga ɗakin miƙewa Khalid ma yayi ya fice
    satar kallon diyana ta kasan ido Fahad yayi kafin ya dawo da kallon sa kan amrat dake kusa da shi “amri tashi muje ko” kallon diyana tayi itama kafin tace “yaya Fahad zan zauna a nan nayi hira da Aunty diyana” tun bata gama rufe baki ba diyana tace “ni ban ce ki zauna ki dame ni ba ato kiyi tafiyar ki ban son surutu” murmushi Fahad yayi a ransa yace diyana uwar rigima ita dai idan bata son abu bata jin kunyan faɗin bata so haka kuma idan tana so abu a gaban kowa take faɗin abun da ke ranta. sunkuyar da kai kasa amrat tayi dan har ga Allah bata son bin yaya Fahad gashi diyana ta sa dole ta bishi,kumbura kumatu tayi a ranta tana faɗin “shi yaya Fahad ɗin nan sai yayi ta matse mutun baya gajiya ko kaɗan” ta shagala da tunanin sai jin sa tayi ya sureta sama ya saɓa ta a kafaɗa ya fice da ita
    suna fita diyana ta gyara kwanciyar ta saman kujera tana faɗin “haka kawai zaki dameni ni kam Allah ma ya sa yaya Fahad ɗin nan ya miki abun da yaya Aryan yamin kila kyayi hankali, rumtse idon tayi kamar mai barci.

    To masu karatu sai muleka yola muga me suke ai katawa

    Yola

    Yaya bello kamar zai yi kuka haka suka fito shi da hasana riƙe da bakkon kayan su su inna suna biye da su a baya har wajen motar da Ammi ta aiko akan a ɗauko su sukaje gaba ɗaya jama’ar kauye sun fito yimusu sallama kuka hasana take sosai dan ita gani take kamar idan taje birni ba zata dawo ba.

    gidan baya na motar yaya bello ya shiga hasana kuwa tana tsaye tana kuka,dafa kafaɗar ta innar bello tayi tana faɗin “ba komai In Sha Allah ki shiga ku tafi” juyowa tayi ta rungumi inna cikin shesshekar kuka tace “inna dan Allah ki sa baki a bani hajjo mu tafi da ita” kallon maman hasana dake tsaye rike da hannun hajjo innar bello tayi kafin tace “inna wuro dan Allah ki bata kanwar tan nan mana tun jiya aketa ta rokon ki amma kinki ba abun da zai faru tun da kika iya barin hasana ta tafi itama hajjo zaki iya bada ita” shiru maman hasana ta ɗanyi kafin ta saki hannun hajjo tana faɗin “to kije Allah ya tsare min ku” da murna hasana ta rungumi hajjo yarinya yar shekara 14 suna ta farinciki suka shiga mota. gaba ɗaya jama’ar kauye sai addu’a da fatan alkhari suke musu,sai da motar ta kurewa ganin su sanna su inna suka koma cikin gida.

    Maiduguri

    Koda suka isa gidan Aunty farida kwance suka sameta saman katafaren gadon ta idon ta buɗe tana kallon sama ko motsi bata yi kallo ɗaya bgs ya mata ya fahimci irin ciwon Ahmad ne kallon dadyn Junior dake zaune gefenta yayi calmly ya fara magana “Aryan zai cire mata ruwan nan da aka sa mata zamu wuce da ita kano anjima yanzu dai ina zuwa”yana kai karshen maganar ya fice da ga ɗakin
    miƙewa Aryan yayi ya cire mata ruwan dake jikinta suka fito palo shi da dadyn Junior.

    To kunji halin da Aunty farida ke ciki mu waiya kano kuma muga wani waina su hiyana ke toyawa

    Kano

    Zahra hiyan Sun gama shirin su tsab yaya Khalid da kan sa ya ja su a cikin motar sa suna tafiya suna yar hira Zahra a gaba mota hiyana a baya “yaya Khalid ayya zaka kai mu wajen lallema idan mun gama gyaran gashin?” chewar hiyana kallon ta yayi ta cikin mirror motar kafin yace “yanzu haka addu’a nake Allah ya sanya kar bgs ya nemiki har muje mu dawo nayi gangancin fita da ke ba tare da izinin sa ba sai yanzu ma nake nadamar yin hakan” “to ai yaya Prince bay…bata karisa maganar ba tayi shiru kasan cewar ta tuna tun da yaya Prince bai sanar da yaya Khalid akan tafiyar su ba to tafiyar sirri ce bai kamata ta sanar wa kowa ba amma ta sha ruwan mamaki ya akayi yaya Prince bai sanar da yaya Khalid ba ya sanar min?
    tayi nisa cikin tunani Khalid ya taka wata wawan birki wadda ya sanya sai da kanta ya bugu da jikin kujerar gabar motar.
    A zafafe ta ɗago kai dan taga me ya sanya yaya Khalid taka irin wanna birki haka,wata mota ta gani kirar siyasa baka mai bakin glass ne ta sha gabar su kan kace me jibga jibgan bakaken mutane sanye da bakin kaya sun rufe fuskar su baka iya ganin komai sai ido ne suka fito daga cikin motar
    Khalid na kokarin ɗaukan wayar sa babban cikin su ya buɗe kofar motar nasu ya damko Khalid ya fitar waje ba tare da ɓata lokaci ba suka tura Khalid cikin motar su sanna suka fito da hiyana da Zahra nan fa suka ruɗe sun rasa wacece ogan su yace su kawo dan Zahra da hiyana da bgs duk kamannin su ɗaya sak kamannin Ammi suka ɗauko. Fito da wani hoton ogan nasu yayi da wata murya mara daɗin ji ya dubi su Zahra ya nuna musu hoton yana faɗin “wacece wanna a cikin ku? Murya na rawa hiyana tace “ni ce” da sauri Zahra tace “ba ita bace ni ce” tsawa ya daka musu tare da fito da bindiga ya saita su yace “idan baku faɗa min wacece ba sai na harbe ku dukkan ku biyu!!” “wlh karya Aunty Zahra take ni ce ba ita bace” chewar hiyana damko wuyar hiyana yayi ya turata cikin mota suka shiga suka tada motar da gudun gaske suka bar wajen

    durkushewa kasa Zahra tayi ta saki kuka mai ban tausayi tana faɗin “me yasa zaki ce kece Aunty Hiyana? why ba zaki bari su tafi da ni ba tun da yaya Khalid na hannun su ni nasan yaya Prince ya fara son ki yanzu idan suka kashe ki shike nan ba zai sake son wata mace ba” tana kuka tana surutai kamar mahaukaciya.

    Sai da tayi kukan ta mai isar ta san nan ta miƙe ta koma cikin motar su cikin sauri ta ɗauko wayar ta tafara kiran layin Bgs sau uku tana kiran sa bai ɗaga ba kiran layin Aryan tayi shima har sau uku bai ɗaga ba juyawa tayi gabas da yamma hanyar shiru babu motsin kowa lokacin guda mugun tsoro ya dira a ranta gashi ita bata san haryan komawa gida ba dan ba fita take ba ko school kai ta ake kuma a ɗauko ta chan wani dabara ya faɗo mata akan ta kira layin Abba
    cikin sauri ta fara kiran layin Abba shima bai ɗaga ba ihu ta saki tare da yin wurgi da wayar gefen titi dan bakin ciki
    tarwatsewa kaca kaxa wayar yayi,sai bayan da ta fasa wayar ne kuma ta fara nadama yanzu dame zata nemo gida akan azo a ɗauke ta fita tayi daga cikin motar ta fara tafiya da kafa tana tafiya bata ma san in da ta nufa ba tanayi tana kuka kamar zararriya.

    To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu to masoyan yaya Khalid masoyiyan hiyana masoyan Zahra aikin tsayuwar dare ya ganku fa amusu addu’a gashi zaku nan gidan Abba basanan suna Maiduguri akoi chakwakiya fa hmmmm

     

  • Arubuce Ta Ke 5

    Idanu ya zuba mata yana kallonta,kullum sake canza masa takeyi,tana dada girma tana kuma sauyawa,yana kuma sake jinta a ransa,a haka ta qaraso wajen,amma ko sau daya taqi kallon sashen da yake zaune ma.

    “Ina yini?” Ta gaidashi tana rusunawa kadan,saidai bashi take fuskanta ba,wani sashe na daban take fuskanta

    “Lafiya lau widad,ya shirye shiryen sallah?”

    “Lafiya” ta amsa masa a cunkushe tana duban ummu

    “Ummu yunwa nakeji,me aka dafa?” Abinda ta tsana ummun ta fara yi wato miqewa,da alama zata basu waje kenan,gamin haka sai tayi wuf ta riga ummun miqewa,daga kai tayi ta kalleta

    “Ki zauna, na’eema zata kawo miki abincin yanzu” yadda ummu tayi maganar babu wasa saman fuskarta ya sanya ta koma jiki a mace ta zauna tana tara hawaye a idanunta,tana kallonsu suka fice daga falon.

    Ajiyar zuciya ummun ta sauke bayan barinta wajen,wanan wanne irin abune haka?,me yake faruwa ne?,har yanzu komai yaqi ya canza tsakaninta da mahfood din?’.

    Cikinsu shi da ita ba wanda ya iya cewa komai,har na’eema ta kawo abincin ta ajjiye ta juya ta fice,a hankali yasa hannu ya jawo abincin gabansa sannan yace

    “Kamar yunwa naji kince kina ji ko?,matso kici abincin kada ya huce” ko kallonsa batayi ba bare yasa ran zata cin,yayita fama amma qememe tayi biris,dole yaja ledar da yazo da ita zuwa gabansa

    “Ga kayan sallah nan,da fatan za’ayi kwalliya me kyau” sosai ya sake quleta,don tana da son kwalliya da gayu sai ya maidata wata qwalamammiya?,bashi da aiki sai kawo mata kayayyaki,yadda taji haushinsa sosai a yau din har taji tana qwarin gwiwar gaya masa abinda bata taba gaya masan ba,daga fararen manyan idanuwanta tayi ta azasu a kansa

    “Nifa bana so,banason komai naka,sannan ma ni ba wani auren dangi da zanyi,ni ba yanzu ma zanyi aure ba,don Allah ka rabu dani,ni…..bana sonka” dai dai lokacin da alhaji mahmud salim mahaifinta yayi sallama cikin falon ya kuma sanyo qafafuwansa.

    Idanu yake bin widad din dashi,yaji kalamanta guda biyu na qarshe,zallar bacin rai ne kwance akan fuskarsa,ita kanta suna hada ido da abban nata ta sadda kanta qasa gabanta yana tsananta faduwa,mahfood kuwa miqewa yayi yana masa sannu da zuwa

    “Zauna mahfood……me naji kina fada widad?” Tsoro da firgici suka hanata yin koda qwaqwqwaran motsi bare ta amsa shi,cikin tsawa ya sake maimaita mata tambayar,saita ida rikicewa gaba daya,ta kuma saki kuka a lokaci guda,saboda sam sam bata saba da irin wannan tsawar ba.

    “Dan uwanki kike gayawa bakiso saboda baki da kunya?,wato kin fara girma kenan widad?” Ya fada cikin mugun fada da kuma daga murya,sautin muryar tasa da ya isarwa da ummu saqon akwai abinda ke faruwa a falon,taji kuma ta kasa nutsuwa saboda kama sunan shalelenta da taji anyi,saita yunqura ta miqe tana duban na’eema

    “Ki qarasa hada muku kayan waje guda ki maida daya dakin kafin gobe gidan ya sake cika,ina zuwa” ta fada tana takawa a hankali saboda dan ciwon qasa da take fama dashi lokaci lokaci.

    Isowarta wajen kadai tafahimci abinda ya faru,fada sosai abban yake zuba mata,da alama ransa ya baci sosai

    “Mahfood dan uwanki ne,da kike cewa kuma bakya sonshi gwara ki koya tun wuri,don baki da miji sai shi,shi zaki aura ki jini da kyau” ya fada yana kama kunnensa da hannunsa guda daya

    “Tashi ki bani waje” ya fada a tsawace,ta gudu ta miqe tayi hanyar dakinsu fuskarta jiqe da hawaye,saman gadonta ta fada wanda ba kasafai ma take kwana a dakin ba,koda yaushe tana maqale da ummu,a dakinta take kwana,koda tana wajen alhajin to itakam tana dakin nata,haka zata hada duka filallukan dake saman gadon ta qudundune a ciki saboda shegen tsoron da take dashi,bare ma ba kasafai ummun ke barinta ba,wani lokaci ma bata sanin bata dakin idan baccinta yayi nisa ko kuma nauyi.

    Kan mahfood a qasa sanda abba ke bashi haquri

    “Nasan harda quruciya abba,har yanzu shekararta sha hudu”

    “Da kuma sakarci ba”

    “Ayi haquri” ya sake fada kansa a qasa,sannan ya miqe yayi musu sallama ya fice daga sassan ummun yace zai shiga cikin gidan su gaisa da sauran mutane.

    “Ka dinga bin al’amarin nan a hankali mahmudu,wannan fadan duka ba shine ba” ummu ta fada bayan dukkaninsu sun zauna

    “Ummu abunne yake dauren kai,anata cewa quruciya ce,to amma tana sake girma tana sake qinsa?” Kai ummun ta jinjina,ita kanta bataga na meye abba din sai ya matsa har haka ba,shi zumuncin da yakeson a qarfafa a kuma sake qullawar ai ba dole sai ta hanyar hada aure ba,inda akwai wata diyar gareshi wadda tadan tasa kamae widad din ma ita zaifi mata sauqi ya maida alqawarin kanta,bata qaunar wannan rikicin da aketa yi da widad din

    “Kasan haduwar jini ne,idan kuma Allah bai sanyata tsakanin bayinsa ba babu yadda za’ayi”

    “Haka ne,Allah yayi mana mafita”

    “Ameen ya hayyu ya qayyumu” ummun ta amsa masa,sai ya miqa mata babbar jakar da yasa aka shigo da ita,wadda ke shaqe da kayan sallah na mutanen da ya saba yiwa duk shekara,wanda yaran gidanne ‘ya’yan qannensa da suke sa’annin widad,wasu kuma qasanta a shekaru,ga kuma nata na musamman ita da widad din da alhaji

    “Alhajin baya gida ne?”

    “Kasan yau daren sallah,suna can fadar mai martaba,har sai an sanar da ganin wata sannan” kai ya jinjina,don kusan al’adar sa ce duk shekara

    “To Allah ya dafa mana” ya amsawa ummun.

    Kuka take sosai da hawayen daya fara jiqa pillow din da take kwnace akai,juyin duniya na’eema tayi ta tashi tayi haquri ta dauki abincinta taci amma ko kulata batayi ba,sosai take jin qin mahfood din cikin ranta,ko sau daya bata taba jin tana sonshi ko yana burgeta ba,yana da kirki ta sani,amma ita ba wani magana datayi kama data aure a tsakaninsu da take jin zata yiwu.

    Har abbanta ya tafi tana kwance tana kuka,ummu na falon bata motsa ba,duk da na’eema ta gaya mata,bataso taje taga yanayin da take ciki zuciyarta ta karye ta gaza bata qwarin gwiwar yiwa mahaifinta biyayya,wannan yasa tayi zamanta a falo,duk da zuciyar da hankalinta na kanta.

    Duk wanda ya shigo nemanta sai tace masa kawai tayi bacci,wasu su zauna suyi hirarrakinsu wasu kuma su wuce,tana nan zaune har qarfe goma na dare,zuwa sannan juriyarta ta qare,sai ta miqe ta shiga dakin da kanta.

    Tana kwance rub da ciki har yanzu,saidai ba zaka iya tantance bacci take ko idanuwanta biyu ba,ta qarasa a hankali tasa hannu tana taba kanta gami da kiran sunanta,sheshsheqar data sauke hadi da ajiyar zuciya ya tabbatar mata idanuwanta biyu

    “Meye haka wai widad?,tashi mana” ta fadi tana qoqarin dagota ta zaunar da ita,sanda ta kalli fuskarta sai zuciyar ummun tayi rauni,kallon marainiya takewa widad shine dadin abinda yasa batason komai ya sameta mara dadi,yarinyar da batasan dumin uwarta ba?,gaba daya fuskar tata ta tashi ta kuma yi jazur da ita abinka da farar fata

    “Kukan kike har yanzu kamar wadda akace mata zata mutu?,tashi ki wanke fuskarki kici abincin naki”

    “Ni banaci” ta fada muryarta na rawa hawaye yana sake barke mata,sai kawai ta fada jikin ummun tana sakin sabon kuka,har cikin ranta ummu takejin kukan,sai ta fara lallashinta,da qyar ta ciyo kanta taje ta wanke fuskar ta sanyata a gaba taci abincin,da qyar tayi cokali biyar tace ta qoshi,ummun taso sanyata a gaba su wuce dakinta ta kwana kamar yadda ta saba amma tace anan zata kwana,tunda ga na’eema,sannan Aafiya ma yau a nan zata kwana,dole ta rabu da ita tabar musu dakin bayan ta ja mata kunnen kada ta sake irin wannan kukan,ta kwantar da hankalinta kuma.

    *_W A S H E G A R I_*

    Kamar yadda suka saba kusan kowa da kowa ake tafiya sallar idi a gidan,akwai wadatar ababen hawa,kowa zai diba iya mutanen da motarsa zata iya dauka,tun sassafe kowanne sashe suke tashi yaran suyita shiri,iyayen kuma suna qoqarin qarasa abincin sallah wanda idan an dawo saga udi za’a dira akai a fara ci da kuma rabo,to hakanma wannan karon ta kasance,har sassan ummun hayaniya ce ke tashi,saidai banda widad dake nannade a bargo,ko motsawa batayi ba bare ta shirya,sunyi sunyi ta tashin amma taqi kula kowa,ummu kuma tunda ta fito da asuba ta tadasu sallah bata kuma fitowa ba,sai alhaji ya gama shirin idinsa.

    Karo na biyu latifa fa dawo,wadda itama ta shirya fes da ita cikin dinkin sallarta,duk sallah sai an mata dinki kamar kowanne yaro ko jika dake gidan,dinkinta masu kyau da tsada har kala hudu ko uku

    “Widad din ummu,kiyi haquri ki tashi ki shirya,kinga kowa ya gama shiryawa,yanzun nan zakiji an fara tafiya”ta fada cikin lallabawa,bakam tayi kamar bata a wajen,duk iya dabara da hila ta latifa haka tayi ta haqura,daga qarshe dai haka suka tattara suka tafi sallar suka barta.

    Bayan ficewarsu ummu ta fito

    “Ja’irai,tunda naji shuru nasan sun tafi,kafin su dawo su hana mutun sakat” tayi maganar tana tura qofar dakin,sai idanunta ya sauka kan tudun bargon dake kan gado,cikin ranta zuciyarta ta bata mutum ne,sai ta qarasa tana yaye bargon.

    Salati ta saka ganin widad din kwance tana sharbar kuka

    “Na shiga uku ni laila?,wai dama baki haqura ba widad?” Hankalin ummun ya tashi sosai,haka ta sanyata a gaba sai data tashi tayi wanka ta kuma zuba mata abincin safe taci,tana gama cin ta koma ta kwanta

    “Falo zaki fito ki kwanta,bazan barki ki sake kwanciya ba”

    “Ki qyaleni kawai ummu,tunda abba baya sona” ta fada da yanayi na quruciya tana kuma sake sakin kuka,baki ummun ta saki,tana magana kamar wata babba?,duk yadda taso ta fiddota amma taqi sai kwanciya.

    Koda aka fara dawowa daga idi tuni gidan ya fara cika da jama’a kamar yadda aka saba duk shekara,jikoki sun fara hallara,kowa fuskarsa da zuciyarsa cike da walwala da kuma farinciki,lokacin sallah lokacine na farinciki,amma wannan shekarar banda widad din,don kuwa duk budurin da akeyi tana kwance a qule a daki,da yake tana da kirki qwarai da son yara qananu,kowa yazo sai yace ina widad,saidai ummun tace bata da lafiya tana daki tana bacci.

    Duk yadda jikokinta ke karakaina a falon amma rashin walwala da fitowar widad din sai taji komai ma baya tafiya dai dai,maganar mahfood din taji itama ta soma fita mata a kai,gwara abar zancan,idan yaso a gwada bata wani,duk da abban nata ya gaya mata ita din bata son auren zumunci,to amma maiyuwuwa ta haqura idan aka gwada mata wani indai jininsu yazo daya,da wannan maganar a ranta tayita dakon shigowar alhaji don suyi maganar ita dashi.

    Bai samu shigowa gidan ba sai yamma liqis,zuwa lokacin manyan yayyensu maza dake sa mota sun debi yaran gidan da yawa zuwa guraren wasannin sallah da shaqatawa,gidan sai yayi shuru,sai dai daikun yara dake shigowa su fita,har sannan widad din tana daki a kwance,duk da tulin kayan sallar da take dashi bata sanya ko guda daya ba bare ta fito.

    Sai data gabatar masa da abinci yaci ya qoshi sannan ta fara magana dashi,yayi shuru yana sauraren ta har ta gama bayananta gaba daya,sannan yayi gyaran murya yana dubanta…….

    *_TOFA,TAFIYAR BA’A FARA BA,KO SHIMFIDA BAMU GAMA BA_*

    *_INA SAKE TUNA MUKU,IDAN KIN KARANTA HANGEN DALA,TO TABBAS SHAFAR MAI NE,WANNAN TAFIYAR TA FISHI ZAFI AMFANI DA KUMA DARUSSA_*

    *_LABARI NE DAYA QUNSHI TSANTSAR KISHI,KAIDI MUGUNTA DA KUMA SIHIRI_*

    *_MUGUN TAKU IRIN NA BAQAR KISHIYA_*

    *ZALLAR RAYUWAR GIDAJENMU TA GASKE*

    *MADARAR SOYAYYA MAI TSUMA ZUCIYA BURGEWA DA BARWA RAYUWA DARASI*

    *GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN TA WANNAN ACCOUNT NUMBER DIN*

    0022419171
    Maryam sani
    ACCESS bank

    *Saiku tura shaidar biya ta nan*

    +234 903 318 1070

    *Masu tura katin waya kuma zasu tuntubi wannan number*

    09166221261

    *Yan nijer zaku tuntubi wannan number*🇳🇪🇳🇪

    +227 90 16 59 91

    *Thanks for choosing us**H U G U M A*
    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)