Hausa NovelsNoor Al Hayat Hausa Novel

Noor Al Hayat 19

Sponsored Links

NOOR-AL-HAYAT*

Khadijah ta xauna kan kujera tana kalle kallen parlorn tace “Umma nan ne gidan ku koh?” Umma ta bude fridge xata dauko mata ruwa tace “Ehh” Karban ruwan tayi tace “Umma yunwa nake ji ban ci komai ba” Umma tace “Toh me xa ki ci yanxu?” Murmushi tayi da ya bayyana fararen hakoranta ta langwabar da kai tace “Indomie Ummata” Umma ma ta yi murmushin ta juya ta fita, Khadijah ta dinga bin madaidaicin parlon da kallo kai kana ganinta kasan she is just happy, muryar Umma taji tana kiranta daga waje ta fita da sauri ta sa takalminta tace “Gani Umma” Umma ta mika mata ruwa a buta tace “Gashi ki fara yin alwala kiyi sallah” tace “Toh” sannan ta durkusa tana alwala tana yi tana kallon yaran dake ta kallonta har da matar dake girki a kitchen, Umma ta shiga kitchen din ta dauko indomie daya ta fito ta kai parlorn ta sannan ta dawo rike da naira dari tana mika ma wani yaro da baxai wuce shekara biyar ba tace “Mudassir je kanti ka amso min kwai biyu” yaron ya karba ya wuce waje da gudu, Karamin tukunya Umma ta daura kan electric madaidaici dake parlorn ta bayan ta shimfida ma Khadijah darduma, khadijah na idar da sallahn Umma tace “Kin fara xuwa school a can gidan” girgixa kai tayi tace “A’a, kin san me Umma ta” Umma tace “Bari ki ci abinci” soya mata kwan da yaron ya kawo Umma tayi sannan ta ajiye mata a gabanta da ruwa a cup ta mayar da wani tukunyar ta sa mata ruwan wanka, Umma tayi tagumi tana kallon yanda take cin abincin, kana ganinta kasan yunwa kawai take ji, kafin ta gama Umma ta juye mata ruwa ta kai bayi da sabulu, ita ta rakata bayin sannan ta koma parlorn, khadijah na gama wankan ta fito daure da xanin da Umma ta bata, Shafah dake girki daga cikin kitchen ta bi ta da wani kallo hakan yasa tace “Ina yini” dauke kai tayi kamar bata ji ba, khadijah ta wuce cikin parlorn Umma tace “Wannan matar dake girki na gaisheta bata amsa ba” Umma tace “Kar ki sake gaisheta” daga haka ta cire hular kanta bayan ta kawo mata man shafawa, sakin baki tayi tana kallon gashin don tun kalaba shidda da ta yi mata kafin kawu ya tafi da ita kasancewar gashinta na da tsayin bala’i kuma bata son ana taba shi, Umma bata dai ce komai ba, ta dau gyalenta tace “Ban ce ki fito ba ki jira ni har in dawo” khadijah tace “Toh” daga haka Umma ta fita, bayan kusan minti ashirin ta dawo rike da Leda ta sake labulen parlorn ta bude ledan ta fiddo wasu dinkakkun riga da skirt kana ganinsu dai kasan taje ta karbo su ne tace “Tashi ki sa, gobe xan je kasuwa in siyo maki kaya kinji” khadijah ta sa kayan tace “Umma in kunna TV?” Umma tace “Ban ce ba” kwanciya tayi kan kujera bbu bata lkci bacci ya dauketa, Umma ta xuba ma jikinta ido ganin shattin duka, tagumi tayi tana kallonta tana tausaya ma marainiyar. Khadijah na tsugunne tana alwala tsakar gida da magrib bayan Umma ta tasheta tayi sllh taji an fixge butar daga hannunta ta daga kai tana kallon yarinyar da baxata wuce ta ba, Yarinyar ta murguda baki ta tafi ta kara ruwan ta fara alwala, mikewa khadijah tayi tace “Are you okay?” Yarinyar ta balla mata harara tace “Ki fadi wanda xan ji mana” khadijah bata sake cewa komai ba har yarinyar ta gama sannan ta wuce da butar parlornsu, khadijah ta xaro ido sai kuma ta juya ra wuce gun Umma dake parlor ta tsaya bakin kofa a hankali tace “Umma wata yarinya ta karbe butan ta tafi da shi” Umma ta fito tace “Wace yarinya?” Nuna mata parlorn da yarinyar ta shiga tayi, Umma ta kama hannun ta suka je har kofar parlorn ta bude labule tace “Wacece a ciki” Khadijah ta dinga bin yara kusan biyar dake parlorn da kallo sannan ta nuna mata yarinyar, Umma tace “Rahmah dalilin me kika karbe buta tana alwala?” Yarinyar da ta tsuke baki tace “Toh Anty namu ne ai” Umma tace “Kar ki sake, idan ko ba haka ba sai na bata maki rai” daga haka ta ja hannun Khadijah suka bar wajen ba tare da ta bi ta kan Uwarsu Hasana dake xaune parlorn ba, Umma ta dauko buta parlorn ta ta bata, Wata yarinyar ce ta shigo parlorn da abinci a er warmer ta ajiye ta juya ta fita, Umma ta daga kan khadijah dake kafarta a kwance tana bata labarin abubuwan da aka dinga yi mata gidan Kawu sannan ta mike ta jawo warmer din, shinkafa ce da miya sai nama biyu da salad a gefe, iya cin ta ne abincin, ta daura dankwali ta fita xuwa kitchen din ta dau wani plate ta bude tukunkya xata debi abinci sai ga Shafah da sauri tace “Amma dai Amina kinsan ba ke ce da kitchen ba, don haka baki da hurumin shigar min kitchen” Umma ta kalleta tace “Ae kin gan ni da bakuwa kika yarfo min er shinkafa a cooler kamar mayunwaci, don haka ke ma baki da hurumin hana ni debar mata abinci” Shafah tace “Bakuwa? Kin gaya min xaki yi Bakuwa in sa girki da ita ne, to wllh kin yi kadan ki kara diban wani abincin don na almajirai ne” Umma ta Debi shinkafar kusan cikin plate ta xuba miya kai da nama biyu tana kallonta tace “In ji duka” daga haka ta fice daga kitchen din Shafah tace “Ai kuwa ni da ke shege ka fasa Amina, mu xuba” tsaye Umma ta ga Hasana bakin nata parlorn tana lekosu tana ganinta ta shige ciki da sauri Umma tayi tsaki ta shiga ciki ta ba Khadijah abincin hannunta. Da yake khadijah tayi baccin rana har karfe goma idonta biyu tana ta ba Umma da tayi tagumi tana saurarenta labarai iri iri, Yar Shafa ta farko fadila ta bude kofa tace “Abba yana kiran ki” daga haka ta juya ta bar gun, mikewa Umma tayi ta fita tare da Khadijah tana rike da hannunta suka tafi turakar mai gidan, ba wani babba bane mai gidan don baxai wuce 48 ba, Shafah na xaune kan kujera da Hasana a gefenta, Umma ta xauna ta nuna ma khadijah k’asa ta xauna ita na, Gaishe da shi tayi, khadijah na kallonsa tace “Good evening Sir” idonsa a kanta yace “How are you” tace “I am fine” Shafah da Hasana aka kyabe baki, mai gidan da suke kira da Abban Fadila yace “Wacece wannan Amina?” Umma tace “Kayi hakuri na so kiran ka tun kafin in iso kano daxu sai da bani da charge, duk da mun yi da kai gobe xan dawo kawai kuma na fasa, wannan ‘er marigayin tsohon mijina ce Khadijah, na taho da ita ba tare da ixinin ka ba, kayi hakuri ban ji dadin yanayin da na same ta bane shi yasa na daukota bbu shawara da kai” shiru yyi bai ce komai ba, can ya jinjina kai yace “Toh Allah ya kyauta” Su shafa aka kwalalo ido ana kallon khadijah jin wai er kishiyarta ce da ta rasu, Abban fadila yace “Dalilin ki na shiga kitchen ba ke ce da girki ba daxu nake son ji? Shi yasa ma na aika a kira ki” Umma tace “Ehh toh, sun ganni da yarinya mun dawo Abban fadila, sai da aka tashi xubo min abinci da magrib sai aka xubo dai dai wanda ni xan ci a yar cooler” yace “Shine aka ce ko shiga ki diba? me yasa baxa ki nemi izini gun mai girki ba ko kuma kice ta k’ara maki kina da bakuwa, ke ce kadai me karya min doka a gidana fa Amina” Umma tace “Watana kusan uku gidan nan yaushe da yaushe na karya maka doka Alhaji?” Hasana sai wani blushing ake Shafa na taya ta, Abban fadila yace “Toh tashi ki je” mikewa tayi ta daga khadijah da su Hasana aka bi da harara ta fice parlorn ta koma nata, daki ta nuna ma khadijah ta tafi ta hau saman gado ta kwanta, khadijah tace “Toh Ummata” sannan ta shiga dakin ta kwanta hade da lumshe ido don har ta mance Rabon da ta hau gado har tayi bacci a kai. Washegari da asuba Umma ta tada Khadijah taje tayi sallah bayan ita ta idar, khadijah ta fita tsakar gidan rike da buta tana mitsika ido, yara ne kusan biyar ko wanne na alwala tana kokarin shiga bayi tayi fitsari taji an fixgota ta juyo da sauri a tsorace, yarinyar da ta kawo ma umma abinci jiya ce, tana kallo yarinyar ta shiga bayin, ta ja gefe a hankali ta tsaya tana jiranta, bata gaya ma Umma abinda ta sake yi mata ba, bayan ta idar da sallah ta koma daki ta kwanta ta ci gaba da baccinta. Gari na fara wayewa Umma ta kuma tashinta daga baccin ta kai mata ruwan xafi bayi da sabulu da soso, ba a dau lkci ba khadijah ta dawo tana wasa da yatsunta a hankali tace “Umma wata yarinya ta fitar min da ruwan ta sa nata ta rufe bathroom din” fita umma tayi ta tafi kofar bayin da sauri tana kallon xanin waye kafin tayi kwafa ta nuna ma Khadijah kujera tace “Xauna nan ki kyaleta kawai, idan ta fito ki shiga” khadijah ta xauna tace “Toh” umma ta koma ta ci gaba da sharanta, yarinyar na fitowa khadijah ta mike ta shiga da ruwan da kyar ta juyo xata dau sponge case wata ta sake fitar da ruwan nata ta hankadota waje ta shiga ta rufe kofa, tsaye khadijah tayi baki bude tana kallon bayin, dai dai fitowar Umma da abun kwashe shara da tsintsiya, karasawa tayi da sauri ta tura kofar ta janyo ruwan waje ta fiddo sabulun yarinyar sannan ta dau na Khadijah ta saka tana kallonta tace “Xo ki shiga” yarinyar ta fashe da ihu tana buga kafa, khadijah dake kallonta baki bude a hankali tace “Why are they behaving like this” Umma ta shigar da ita bayin tace “Maxa ki fara wanka” Hasana ce ta fito da sauri jin ihu da kukan yarta, tana kallonta a gigice tace “Walida ya aka yi, me ya faru” cikin kuka walidar tace “Xan shiga inyi wanka shine Anti ta fiddo min ruwana ta fito da ni ta saka yarinyar da ta kawo cikin bayin” Hasana da tayi mitsi mitsi da ido tace “Toh Allah ya isan ki, kuma mu xuba da su a gidan nan xan ga ko agolarta xata samu gun xama, ita ma da take a dosane ta ji da kanta mana, tsabar munafurci da neman kugun xama taje ta jajibo yar kishiyar da kilan ma ita ta kasheta ta kashe ubanta, shege ya fasa mu da ita a gidan nan” Umma bata ko kalleta ba ta shiga share kofar parlorn ta, Shafa ta fito tace “Ya aka yi ke kuma da sassafe, ke da wa?” A fusace Hasana tace “Ki rabu da yar kaxa kaza, wai Walida ce xata shiga wanka shine ta fiddo mata da ruwan ta ta saka na shegiyar da ta kawo mana mai kama da aljanu” Shafah ta rike ha6a tace “Ikon Allah Walida da xata makaranta? Ita kuma agolar da take gida, Mutum dai bashi da aiki sai neman fitina, banda jakanci ma ina aka taba dauko agola ace xa a takura ma masu gida dominta” Hasana tace “Ke fa kika san jakanta, amma ni nasan maganinsu wllh, kuma xa mu sa kafar wando guda da su” daga haka ta kalli yar ta tace “In ta fito ki kwara ruwa bayin ka fin ki shiga, Allah dai ya tsine duk mai son takura ku gidan ubanku ehe” daki ta shiga tana ci gaba da kumfar baki, Shafa ta bi bayan ta tana cewa “Amin dai, Allah kuma ya kawo mana karshen bala’in nan, muna xaman xamanmu dai” Khadijah bata fito ba duk da ta gama wankan, sai leken tsakar gidan ta kofar bayin take taga ko sun tafi, ganin Walida ce kadai xaune tsakar gida ta fito tana gyara daurin da tayi ma Xanin jikinta ta ta nufi dakin Umma da sauri, taji Walida tace “Shegiya kawai” kallonta khadijah tayi tace “Back to sender” sannan tayi saurin shigewa dakin ummanta. Kafin karfe bakwai da rabi duk yaran gidan an shirya wucewa makaranta, jin muryar Abban fadila a waje, Umma ta kalli khadijah tace “Go outside and greet him. Come back immediately after that” khadijah ta fita waje ta gansa tsaye ya shirya alamar xai fita kasuwa yana sauraren yaransa mata biyu da suke requesting kudin wani littafi da xa su siya a boko ga iyayensu tsaye bakin kofa, Khadijah ta karasa kusa da shi ta durkusa a hankali tace “Good morning sir” ya kalleta yace “Morning yar turawa, how was ur nyt?” Ta washe hakora tace “It was splendid” yace “Good, ina mamar taki?” Ta kalli kofa tace “Tana ciki” yace “Kira min ita” Shafa da Hasana da lkci daya mood dinsu ya canxa suka kalli juna, juyawa khadijah tayi taje kiran Umma suka fito a tare, Yace “Naga baki shigo gaisheni ba” Umma tace “Bayan nayi sallah I just slept off” yace “Ohk, anjima sai ki je ki mata registern islamiyya ko xuwa next week sai a samu boko a sata” Umma tace “Toh nagode, Allah ya kai mu” Naira Dari ya Ciro ya mika ma khadijah yace “Gashi ki siya biscuit” xaro ido tayi ta kalli Umma, Umma tace “Amsa” ta karba da hannu biyu tana murmushi tace “Nagode uncle” daga haka Umma ta ja ta suka shiga ciki ba tare da ta yarda ta kalli inda kishiyoyinta dake cika suna batsewa suke ba, Shafa tace “Toh Abban Fadila kudin kitso da na tambaye ka tun jiya fa?” Hasana tace “Ni tun shekaranjiya nake ta bi ya sa min kati amma kinga wani gwaninta a nan” Tuni ya isa kofa bayan ya sallami yaransa mata dake turo baki kudin bai ishesu ba, sai da ya fita gidan, Hasana tace “Toh wllh abinda baxai yiwu ba kenan, ya gama ji da nasa yaran mana, har xa a kara daura masa nauyi bayan wanda ke kansa, ko ita yarinyar bata da dangin uba ko uwa ne sai karere??” Shafah tace “Ke fa kika San karere, ita nan gwaninta take a idon duniya ko, toh kuwa xata sha kunya in har bata mayar da yarinyar nan gun dangin ubanta ba, sai yarinyar nan ta ja mata masifa da bala’i sai kuma ta dauko mata abun kunya muna nan dake, sai dai idan ba ni ce nan Shafa’atu yar gidan Sanusi jikar Yakubu na bude baki na yi magana ba” Hasana tayi shewa tace “In sha Allahu kuwa” Umma dake ta jin su ta girgixa kai tana murmushi a ranta tana masu addu’ar samun sauki, sai bayan da duk suka gaji suka shiga ciki ta dauko kibiya da comb xata tsefe ma khadijah gashinta, Tuni khadijah ta fara matsar kwalla tun kan ta kama kan din right from Beginning idan ana son tashin hankali toh a taba gashinta, sosai ta ba Umma wahala ta dinga rusa kuka tana ihu, har dai aka gama tsefewa ta bata Hijab ta sa suka fito don xuwa saloon a wanke mata gashin, da ido su Hasana suka bi su har suka fita.

Sai kusan azahar suka dawo gida, Idon khadijah ya kumbura don kuka, Hasana na xaune tsakar gida tana jajjagen tafasasshen nama da alama dai dambunsa xata yi, Shafah kuma na daga xaune bakin kofa suna ganin shigowarsu suka yi shiru daga xancen da suke ko wacce ta hade rai, Umma ta bude kofar ta ta ja khadijah suka shiga ciki, xaunawa khadijah tayi kan kujera Umma na harararta tace “Duk kika tsefe kan nan ke kadai xaki saloon din baxan iya wahala ba, dubi idanuwanki kamar warce aka yi ma duka, ke ba yarinya ba ki dinga ma mutane ihun kitso” Khadijah ta kwanta kan kujera bata ce komai ba, Umma ta fita ta shiga kitchen ta dau indomie biyu ta fito, Hasana ce tace “Gaskiya Abban fadila ya dawo ya kasa ma kowa indomie ya ajiye a dakinsa tun jiya ake ta shiga ana daukar indomie abinda yaran gidan ma sai su yi sati basu ci ba, wnn ai mugunta ce” Umma tayi yar dariya bata ce komai ba ta shiga ciki, dama da kwai hudu ta dawo gidan, don haka ta girka indomien a daki ta dafa kwan ta tada khadijah da ta fara bacci ta bata nata sannan ta fita yin alwala, Da daddare yau ma kamar jiya a karamar cooler shafah ta aiko ma Umma abinci, Tea ta hada da yake tana da kayan shayin a daki ta fita da kanta ta siyo bread ta ba khadijah ta ci ba tare da ta bi kan yan gidan ba. A can katsina kuwa neman duniya kawu da matansa sun ma khadijah amma bbu ita babu labarinta, gidan da suka fara xuwa kuwa gidansu sadeeq ne, nan mahaifiyarsa ta nuna masu the other side of her don har sai da suka tsorata kuma tace kada warce ta sake shigo mata gida, har station kawu yaje da gidan radio, bai taba kawo wa cewa Umma ta san gidansa ba balle ta xo ta dauke khadijah, Duk da ba wai abun ya wani dame su Hajiya salaha da Hajiya maimuna ba amma ganin yanda mai gidan nasu ya dage yana nemanta yasa su ma suka xage, har shawara Hajiya salaha ta bada su kai karar Hajiya Amina da d’anta, kawu ya gwaleta cike da masifa yace “Kinsan waye uban yaron?” Hajiya Maimuna tace “Alkali” Kawu yace “Shine xata dinga magana kamar mahaukaciya?” Ita dai Hajiya Salaha bata ce komai ba. Washegari da safe Umma ta fita tare da Khadijah don sama mata islamiyyan da xata fara xuwa, bata yrda ta kai ta wanda yan gidan ke xuwa ba ta kai ta wani dake gaba da shi sosai, bayan ta biya komai ta wuce kasuwa tare da ita don yankar mata uniform daga can tayi mata siyayya kananun kaya. Da yammacin ranan Umma ta amshi girki, tuwon shinkafa da miyar vegetable take girkawa, Khadijah na xaune kan tabarma bakin kofar Umma tana cin gyadar da Umma ta siya mata a hanyarsu ta dawowa, da ta bare sai ta jefa ma wani kadangare dake tsakar gidan yana yawo bawon gyadar, tsawa taji an mata ta waiga da sauri Hasana da fitowarta kenan tace “maxa tashi ki tsince su don baki da bawa mai shara a gidan nan” Umma kallo waje tayi daga kitchen din bata dai ce komai ba ta ci gaba da girkinta, mikewa khadijah tayi ta isa gun da ta ke ta jefa bawon ta shiga tsince su tana xubasu a shara har ta gama, Hasana ta nuna mata wasu bola dake kusa da kofar Shafah wai taje ta tsince, Umma ta fito tace “Wannan kuma ne baki isa ba” kujerar da ke kusa da kofar kitchen ta nuna ma khadijah tace “Sit here” khadijah ta karasa da sauri ta xauna, Hasana ta rike ha6a tana kallon Umma bata dai ce komai ba. Umma bata bar khadijah ba sai da ta tabbatar ta yi bacci sannan ta tafi bangaren Abban Fadila, bata yi mamakin ganin kishiyoyinta ba a xaune parlorn, da kuma alamar yana shigowa suka bi sa don bai jima da dawowa ba, har Umma ta ajiye tray din abincin hannunta kallonta yake, ta xauna ta gaishesa, bai amsa ba yace “Dama kin taho da yarinyar nan ne don ki ci xarafin mutane Amina?” Umma ta kallonsa tace “Ban gane ba” yace “Toh daga yau kar ki sake nuna iko a kan ta Idan ba haka ba ki mayar da ita dangin ubanta, banda janyo yaro ya raina babba don me Hasana zata sa ta aiki ki hanata, akan me? Meye amfanin xamanta gidan idan baxa a ci moriyarta ba!” Umma dake saurarensa tayi murmushi tace “Tun da na shigo gidan nan cikin yaransu akwai warce na taba sa aiki ta min? Babu…. domin kuwa duk sun hanasu amma na taba kai maka kara? Ni wllh matan ka basu isheni kishi ba Alhaji, banda kaddara ba lallai su gan ni cikinsu ba balle su sa ni gaba, ina ce ni ka fara sani ma kafin su? Wllh basa gabana balle inyi kishi da su, marainiya ce dai na daukota sae dai bakin ciki ya kashe su tunda ba a kansu xata xauna ba” Tana kai wa nan ta fice daga parlon idan sun fita sai ta dawo. Ka’ida ce duk safiya a gidan su Fadila ne ke yin wanke wanken safe da sharan tsakar gida ko ma wacece ke girki kafin su tafi makaranta, yau kam suna tashi da safe wanka suka yi ko wanne ta tafi ta saka uniform, Umma bata ce masu komai ba tana ta soya dankalin irish da xa ayi breakfast da shi a gidan, Khadijah na durkushe kitchen din sai dai ta bude babban cooler a Umma ta xuba wanda ta soya, Umma ta gama soya Irish din da ta fere gaba daya ta soya kwai, kananun yaran gidan ne suka dinga tahowa karban nasu duk ta basu ko wanne sa cup din shayi da ta hada, Khadijah dake ta kallonsu tace “Umma why are they so plenty?” murmushi umma tayi tace “Just as the one ur uncles home” Khadijah ta langwabar da kai tace “Noo, they are nt as much as this” Fadila ce ta taho kitchen din tace “Anty ina kwana, ina dankalina” Umma ba tare da ta kalleta ba tace “Idan kin gama wanke wanken can xan xuba maki” juyawa tayi ta wuce sai ga Shafah ta fito, “Amina ban gane baxa ki ba Fadila kalachi ba, meye dalili” Ko tanka ta Umma bata yi ba, ta hau masifa tayi mai isarta daga karshe tace “Bar ta ita ce mayunwaciya Fadila, ta hada da Wanda ta ajiye ma kanta da agolar da ta kawo su cinye, mu je in baki kudi ki siya kosai da bredi a hanya, wanke wanken su shekara nan, in dai baxa ta ba ma agolarta tayi ba” daga haka ta wuce ciki Fadila na biye da ita a baya, daga Hasana har Shafah bbu warce tayi kalaci da girkin da Umma tayi, duk wainar shinkafa suka aiki almajiri ya siyo masu a makwabta, Umma kam ko a gyalenta, wanda ya rage ra kira almajirai ta basu ta hada kayan wanke wanke xata yi, Khadijah tace “Umma na iya wanke wanke fa yanxu xan yi” da kyar ta amince ta bar ta, Ganin yanda ta fara jika kayan jikinta Umma ta karbi kayanta ta shiga yi tace mata ta tafi daki ta kwanta. Da rana cous cous umma ta girka gidan d’an dai dai, daga ita sai khadijah a gidan don tun misalin goma su Shafah da Hasana suka fita basu dawo ba, ta dibar ma kananun yaran gidan a warmer ta kai can dakinta da miyar ta ajiye bayan ta xuba ma Khadijah, ta dawo ta tsaftace kitchen din ta wanke tukwanen da tayi amfani da su da utensils sannan ta koma ciki. Sai kusan karfe Uku su Shafa suka shigo gidan Hasana na cewa “Wash wajen nan ba dai nisa ba Maman fadila, na xata bai fi tafiyar minti talatin ba fa” Shafa tace “Nima farkon xuwa na na sha wahala sosai, ga hanyar bbu kyau mutum na mota kamar ya hau jaki duk jikina ciwo yake…” Shiru Umma taji sun yi suna kallon kofar ta, ita ke ganin su ta labule amma su basa ganinta, suka kalli juna basu dai ce komai ba, kitchen Shafah ta wuce, can sai ga ta ta fito tana kallon Maman walida tace “Ke kamar fa bata yi girki ba” Maman Fadila tace “Bata yi girki ba kuma? Kin ga uban yunwar da nake ji ga shi bani da kosisi kudin sun kare a kudin motar” Daga labulen Umma Maman walida tayi suka yi ido hudu, d’an kame kame ta fara da farko, sai kuma tace “Ba a da niyyar yin girkin rana ne yau a gidan nan ga yara su kusa dawowa” Umma tace “Ehh” sake labulen tayi ta bar wajen Maman fadila ta bi bayan ta, tana jin Shafah na jajjage a kitchen xa su dafa indomie, ita dai tana xaune inda take. Uku da rabi yaran suka dawo kuwa, nan Umma ta xuba ma kowa abincinsa ta ajiye masu tsakar gida, Shafah dake kan tabarma ta kalli kishiyarta dake bakin kofar ta ita ma a xaune, yaran suna gama ci suka fara shirin tafiya islamiyya, Umma ta sa Khadijah ta shirya cikin dinkekken uniform din da tela ta kawo mata daxu, sai murna take har ta gama shiryawa, har bakin makarantar umma ta rakata na ranan kadai sannan ta dawo gida. Umma na kitchen tana girkin dinner ta dinga jin kamar kukan khadijah, ta mike da sauri ta nufi kofar fita, su Shafah da Hasana dake xaune kusa da juna suka bi Umma da ido, a bakin kofa ta kusa cin karo da Khadijah ta riko hannunta tana kkrin cire Hijab din da ta rufe fuskarta tace “Me ya faru?” Cikin kuka tace “Umma wannan yarinyar dake gidan nan ne ban mata komai ba na gansu a hanya, she just slapped my eyes and pushed me na fadi a kan wani dutse” Umma da ranta ya gama baci tace “Wace yarinya kenan?” Dai dai nan walida ta shigo fuskarta tsuke, Khadijah ta nuna mata ita tana shessheka, fixota Umma tayi ta wanka mata mari ta ja kunnenta tace “Don uwarki kika sake taba min ‘ya sai na cire maki hakori wallahi, muguwa kawai mai halin banxa” daga haka Umma ta hankadata, walida ta fasa wani ihu kamar xata tsaga gida tana kiran uwarta. Mikewa Hasana tayi baki bude tace “Amina??? Ita walidar kika mara??” Umma ta juya tana facing dinta tace “An mareta, ki taho ki rama mata, d’a ya fi d’a ne, ai wllh duk shegiyar da tace ‘ya ta baxa ta xauna lafiya ba gidan nan sai dai ita ta rasa xaman lafiya, me marainiyar ta maku? Ko ba a cin arxiki dama a duniya, kishin naku ya tsaya iya kai na mana, toh wllh duk ku ja ma ‘ya yan ku kunne, duk wanda ya sake ko da yi ma khadijah kallon banxa ne, sai nayi masa abinda bai yi xato ba” tana kai wa nan ta tafi daki da Khadijah ta tura ta ciki tace “Maxa ki canxa kaya” daga nan kuma ta dawo kitchen ta ci gaba da abinda take rai bace, daga Hasana har Shafah haka suka bude baki suna kallonta bbu wanda ya iya cewa komai cikinsu. Da daddare Abban Fadila ya dinga kwalo ma Umma dake xaune kan darduma kira, ta mike ta fita don bata ma ji shigowarsa ba amma tuni har ya shiga parlon sa, bin bayansa tayi ta shiga parlon tana masa sannu da xuwa, bai amsa ba ta xauna ba tare da ta yarda ta kalli kishiyoyinta dake xaune parlorn ga Walida a durkushe a kasa, Abban Fadila yace “Amina, so nake xuwa gobe ki mayar da yarinyar nan dangin ubanta da kika daukota, I agree zan yi sponsoring dinta ko tana can din, idan ya so duk bayan watanni uku ko hudu sai ki je ki dinga dubata, I think that will better, I didn’t buy d idea of her staying here anymore….” Tun da ya fara Umma ke kallonsa a sanyaye, Hasana da Shafah da aka wani hakikance kan kujera kamar wasu Hajiyoyi xa a iya ganin murnar dake shimfide fuskarsu, trying hard to control her tears Umma tace “Saboda me kace haka Alhaji? Kada ka mance yarinyar nan marainiya ce ba ta da kowa, tun tana yar shekara biyu mahaifiyarta ta rasu, mahaifinta kuma bai mata gatan nuna mata dangin mahaifiyarta ta ba, da na sansu da can xan kai masu ita baxan kawo ta ba gidan ka Alhaji” Abban fadila yace “Kiyi hakuri iyakar taimakon da xan ma yarinyar kenan, ko nawa ne kudin karatunta xan biya idan ya kama ma da feeding expenses duk xan ba da, kawai dai gidana ne baxata xauna ba, kuma baki min kara ba da har xaki daga hannu ki mari diyata a ido don abun su can ya hada su, so tafiyarta xai fi, I think that’s all… Gobe ki hada kayanta ki maida ta inda kika dauko ta” Umma da hawaye ke xuba idonta a hankali tace “Ina jin da ka sauwake min kawai in tafi da ita xai fi don ni baxan mayar da ita dangin mahaifinta ba” yana gyada kai yace “Kema xa ki iya sauwake ma kanki ai Amina ba sai na sauwake maki ba” mikewa Umma tayi ta fita ta koma bangarenta, ta shiga daki tayi kukanta mai isarta, duk tausayin khadijah ya cika xuciyarta, to yanxu ina xata kai marainiyar nan, ita ba ta da kowa mahaifiyarta ta rasu da sai ta kai ta gun ta tasan xata rike mata ita, bata da wani abun hannu don duk cutar ta yayyin mahaifin khadijah suka yi a rabon gado bayan ya rasu, domin kuwa kafin a ankare sun boye abubuwa da dama cikin dukiyarsa, banda haka da ko boarding sai ta kai khadijah, har gari ya waye Umma bata ritsa ba tana ta tunanin inda xata kai khadijah domin ta ma kanta alkawari first thing da safe xata fitar da ita da gidan, yayarta warce suke uba daya dake Kaduna ta fado mata ta yi shiru tana naxari.

Daukar waya Umma tayi ta shiga kiran layin step sister dinta Yakumbo amma baya shiga alamar dai wayar a kashe yake, da safe bbu abinda ta girka ma mutan gidan a madadin breakfast, ta dai hada ma Khadijah tea ta siyo mata bread ta bata, Karfe takwas ta shiga bangaren mai gidan nasu ta sanar da shi xata mayar da Khadijah gida, ya kirgo dubu biyar ya mika mata yace “Gashi ku yi kudin mota, idan kin dawo sai a san yanda xa ayi batun makarantar nata in ji ko nawa ake biya” Umma ta girgixa kai tace “A’a ka bar shi mun gode Alhaji, muna da kudin mota” Yace “Shi kenan, Allah ya tsare” mikewa tayi ta fita dakin, a cikin wata karamar jaka Umma ta hada ma Khadijah d’an kayan da ta fara siyo mata, suka fito parlor ta sa ma kofar kwado bayan ta rufe, khadijah dake sanye cikin doguwar riga da karamin Hijab tace “Umma ina xa mu?” Umma ta kasa kallonta tace “Xa mu d’an yi tafiya ne khadijah” daga haka ta kama hannunta suka nufi kofa, tana jin su Shafah da Hasana na dariya suna cewa “Toh a sauka lafiya, sai a kara gaba can da ita” ita dai bata tanka su ba har ta fita. Tasha suka tafi cikin a dai dai ta, can suka samu motar Kaduna, bayan wani lokaci motar ta cika suka yi set off xuwa Kaduna garin gwamna… Ko barin kano basu yi ba khadijah tayi bacci jikin Ummanta, har suka isa Kaduna bata tashi ba, suna isa kawo bayan driver yyi parking kowa ya fara alighting daga cikin motar, Umma ta tada khadijah suka sauka su ma, sai kalle kalle khadijah take tace “Umma where is this?” umma tace “Kaduna” Khadijah tace “Wow I’ve heard of Kaduna in school” Umma ta samar masu napep suka yi ciniki sannan suka shiga xuwa hayin rigasa Unguwar da yakumbo take, tafiya ce mai nisa kafin su iso rigasa, da yake Umma sunan layin kadai ta sani ba wai ta wani san gidan yakumbo bane a bakin layin tasa mai napep din ya sauke su ta basa kudinsa tana rike da hannun khadijah suka shiga layin umma na bin ko wani gida suka xo wucewa da kallo don ta haka kadai xata gane gidan yayarta kasancewar ta jima bata xo wajenta ba, sun fi minti talatin suna bulayi a layin, Khadijah sai tambayarta take “Umma where is this, everyway is dirty, they are smelly gutters everywhere” Umma tace “look I don’t want to here ur mouth again” shiru khadijah tayi, daga karshe dai wata mata da ta gansu suna ta yawo ce ta tambayesu gidan da suke nema, Umma tayi shiru tana tuna sunan da aka fi sanin yakumbo da shi, can tace “Kulu mai waina” Matar tace “Ikon Allah, yo ai ga gidan can kun wuce” Umma ta juya tana kallon gidan da matar ke nuna mata, matar tace “Wancan gidan mai keke a gaban sa” Umma tayi murmushi tace “Kin ga kuwa sai yanxu na gane, gaskiya na nagode sosai” daga haka suka juya khadijah na biye da ita a baya, tsallake gutter din dake kofar shiga gidan Umma tayi Khadijah ma ta yi haka sannan suka shiga xauren gidan, gida ne ginin kasa duk ya kwarabe, Khadijah ta xaro ido tana bin gidan da kallo, Yakumbo ce xaune tsakar gida tana hura icce duk hayaki ya cika ko ina, Umma tace “Yaya” dagowa yakumbo tayi ta xaro ido tace “Aminatu” karasawa Umma tayi ta rungumeta tace “Rai kan ga rai yaya” cike da farin ciki Yakumbo tace “Sannu da xuwa Amina, daga ina haka? ya mai gidan naki?” Umma tace “Wllh daga kano Yaya, yana nan lafiya yace duk a gaida ku” Yakumbo tace “Maa sha Allah sai dai kin rame kan lokacin bikin, wacece wancan” Yakumbo ta fada tana nuna Khadijah, A hankali Umma tace “Yar marigayin mijina ce Alhaji Muhammad” Yakumbo ta rike haba tace “Ikon Allah gashi ta kusa xama budurwa, sun hakura sun baki ita kenan?” Umma tace “uhn, labari ne me yawa yaya bari dai mu yi sallah” Yakumbo tace “Gaskiya ne bari in kawo maku ruwa” tabarma ta fara shimfida masu kafin ta tafi debo ruwan alwala, Umma ta xauna ta nuna ma khadijah dake tsaye gefenta, khadijah ta karaso tana tsattsallake bololin dake watse tsakar gidan, Umma tace “yaya ina mutan gidan?” Yakumbo tace “Toh jikokin nawa sun fita wasa, tun safe rabona da su, yaran makwabtana kuma duk sun tafi talla, iyayensu kuma aikatau suke na yini, Ladi ce kadai ta shiga makwabta daxu, nima anjima xan fita suyan wara da dankali a bakin titi” shiru Umma tayi jikinta yayi mugun sanyi, yakumbo ta kara da cewa “Ai Allah ma yyi ban tashi a gidan nan ba kika xo, don duk mai gidan ya ba mu notice xai rushe gidan wai, to gida ne duk ya rube” Umma ta kalleta da sauri tace “Ina xa ku koma yaya?” Yakumbo tace “Oho dai har yanxu ina lalube ne, kudin kama wani gidan ma ai xaune yake da kugunsa, talauci yyi yawa ta ko ina, ko daxu na fita duba gida don sati daya ya ba mu xai watsar mana da kaya waje” Umma tace “Ikon Allah” Yakumbo tace “Ai ke dai kawai sai du’a’i duniyar ta xama abinda ta xama” Yakumbo ta kalli khadijah da ta takure gu daya tace “ke yar nan tashi ki fita waje gun mai kanti ki siyo min farin maggi” Umma tace “Yaya ai bata san ko ina ba” Yakumbo tace “Ka ji ki, nan nan ga masu kanti kamar jampa a jos ta ko ina a anguwar nan, tana fita duk inda ta bi akwai mai kanti” daga haka Yakumbo ta kunce kullin xaninta ta fiddo wani naira ashirin dake a dunkule ta jefa ma khadijah, mikewa khadijah tayi ta karasa ta duka ta dau kudin tana kallon Yakumbo tace “How much own” yakumbo ta d’an bude ido tace “Eh??’ Umma tace ” twenty naira” khadijah ta juya ta fita, yakumbo tace “Sai na ji kamar yare tayi” Umma tayi murmushi tace “Turanci tayi” Yakumbo tace “Au tohhh abun na manya ne Ashe” ita dai Umma bata ce komai ba ta mike taje tayi alwala ta dawo tayi hau kan tabarman ta tada sallah, jin shiru shiru Umma na idarwa ta bi bayan khadijah, a bakin xaure suka kusa cin karo Umma tace “Ina magin kuma me ya sa kika dade?” Khadijah tace “Umma I’ve forgotten the one she mentioned” Umma ta hade rai tace “Bani kudin” mika mata khadijah tayi ta umma ta koma ta dau dari a Jakarta ta fita, farin magin hamsin ta siyo mata da maggi star saba’in sannan ta dawo gida, garau garau na dafaduka Yakumbo ta girka masu, ta xubo a faranti. Umma kadai ce ke cin abincin a sanyaye tana tausayin khadijah dake tsintar shinkafar, yakumbo kuwa na ta yankan warar da xata fita soyawa kamar yanda tace suna yi suna hirar xumunci da yar uwarta, la’asar nayi Yakumbo ta kira almajiri ya kai mata kayan bakin titi gun da take suyar, Tana kokarin saka Hijab dinta da yyi dukun dukun tace “Toh Amina xan fita kasuwa, idan kun ji yunwa ku kara deban abincin, sai ki d’an taimaka ki share min daki ki fiddo kayan wanke wanken ki ajiye su bakin kwararon can ko yarinyar nan ki sa tayi” Umma tace “Toh yaya, amma fa har yanxu yaran basu dawo ba” Yakumbo tace “Rabu da gantalallu suna makwabta na sani, idan yunwa ta kwakulesu xa ki ga sun dawo da daddaya da daddaya” daga haka yakumbo ta fita rike da roban dake dauke da dankali a ruwa, Umma ta bi ta da kallo, Khadijah ta yatsine fuska tace “Umma the food is somehow” Umma ta hade rai tace “Haka nan xa ki ci, ko ni ma baki ga hakan na ci ba” Khadijah bata ce komai ba, Umma ta mike ta shiga d’an karamin dakin yakumbo, har wani wari dakin yake gashi bbu ventilation don windown dan karami ne, ga kaya ta ko ina, plastern dakin duk ya faffashe gashi ko leda babu, jikin umma yyi sanyi ta daga dan karamin katifar da tayi bakikirin ta shiga gyaran dakin ta fidda duk kwanukan da har da funfuna jikinsu sannan ta fara sharan dakin. Ko da ta fito bayan ta gama bacci ta tarda khadijah na yi, ga shinkafar ta bar sa, Umma ta tada ta ta bata Dari biyu tace “Kije kantin da kika je daxu ki karbo Nutri milk da biscuit din hamsin ki xo ki ci” Karba khadijah tayi ta fita. Sai kusan karfe biyar jikokin yakumbo uku suka dawo gidan sun yi dukun dukun da dirty, duk kanana ne yaran, Umma ta masu wanka da sabulun wankin da ta gani, ta xuba masu abinci, Khadijah dai na xaune sai kallonsu take da wani expression, nama Umma ta fita ta nemo a anguwar ta xuba masu kan abincin ko khadijah xata ci, nan ta tsince naman ta bar mata shinkafar wai ta koshi, sai dab da Isha yakumbo ta shigo gidan tare da Almajiri da ya dauko kayan suyanta, Sannu ta dinga ma su Umma, Umma ta mike ta taya ta karban kayan…. sha dayan dare bayan su khadijah sun yi bacci Umma ta shiga yi ma Yakumbo bayanin abinda ya kawo ta da Khadijah, bayan yakumbo ta gama saurarenta tace “Ikon Allah, mugunta fa yyi yawa a duniyar nn yanxu ki kuluwa” Umma tayi shiru bata ce komai ba, Yakumbo ta kyabe baki tace “Toh ni wannan ai ba matsala bace, don dai in rike marainiya, bakomai wllh” Dubu 30 Umma ta kirgo ta ba yakumbo tace “Wannan sai ki siya kayan abinci da indomie ki ajiye yaya” makaranta kuma ayi mata Register da ta gwamnati idan Allah ya hore min sai in canxa mata, dubu ashirin ta kuma bata tayi ma khadijah siyayyar makaranta, yakumbo ta dinga godiya kamar ita ta ba kudin, sai kusan karfe daya suka kwanta bayan yakumbo ta gama tsine ma matan mijin Umma, da su kawu. Washegari da safe Umma ta dau hanyar kano bayan ta rubuta ma Yakumbo lambarta kan cewa duk inda suka koma ta sanar da ita in case xata dawo duba khadijah, dubara aka ma khadijah aka aiketa daga nan Umma ta samu ta bar gidan duk jikinta a sanyaye, da Khadijah ta dawo ta kyallara ido taga ba umma ta dinga ihu tana kuka a gidan tana cewa a kai ta gun ta, Bakin yakumbo a leko ta dauko muciya tace “Kin ga wannan abun hannu na? To wllh da shi xan fasa maki kai idan kika ci gaba da tona min asiri a anguwa, kaji min katuwar banxa, maxa ki tafi tare da Fauxiyya ku siyo min ice da xan yi tuyan awara anjima” Jikin khadijah na bari suka fita, matan gidan dake ta kallon ikon Allah suka ce “Yo ke kulu da kike jiran fauxiyya ta kara wayo ki kai ta aikatu kina samun kudi don me baxa ki kai wnn budurwar da aka kawo maki ba? Ai wannan da ganinta bbu aikin da baxata iya ba har wanki” Yakumbo tayi shiru tana kallonsu.

Ko da suka dawo gidan firewood kwara biyu kadai khadijah ta riko a hannu, fauziyya kuma ta rike ya kusa shidda, daga matan gidan har Yakumbo sakin baki suka yi suna kallon Khadijah da ta ajiye tana haki, yakumbo tace “Meye wannan din kika dauko?” Da kyar khadijah tace “Firewood, it’s too heavy, and it’s pricking me all over” a fusace Yakumbo tace “Kin ma uwar ki Amina turanci ba ni ba, kuma ke kadai xaki koma ki kwaso duk wanda ga rage fauziyya baxa ta je ba tunda ba ki da mutunci” korata Yakumbo tayi ta fita ta na share hawayen dake sakko mata, mai firewood din ganin yanda take hawaye kuma kana ganinta kasan baxata iya dauka ba ta dauko wani rabanta ta xuba mata su a ciki ta daura mata a kai tace “Kina kai wa ki dawo min da roba na kin ji” a hankali khadijah tace “Toh nagode” A haka ta isa gida tayi ta tsayuwa da roba a kai wai bbu ke sauke mata inji Yakumbo, daga karshe ladi ta kike ta sauke mata tana cewa “Idan ka xa ki kama jiki ki kama jiki ki daina ma mutane kamar mara laka a jiki” Khadijah dai bata ce komai ba, bayan ta juye iccen tace ma yakumbo xata mayar da roban, ko kallonta yakumbo bata yi ba ta juya ta fita kai ma mai iccen robar ta. Yakumbo ce tsaye tsakar gida bayan kwana uku da xuwan su Umma, tafi minti talatin banda kumfar baki da masifa bbu abinda take, ga matan gidan da yaransu a xaune babu mai bata hakuri sai ma xugata da suke, khadijah kuma na tsaye bakin xaure duk tayi wani duhu ta rame sosai, idonta duk ya kumbura don kuka ga shatin bulala a jikinta, Ladi tace “Yo da kinsan haka ne tun farko kema ai baxa ki fara daukarta ba, meye amfanin yaron da baxa ka amfana da shi ba sai shegen son jiki da iyayi, ai kadan ma kika mata da kin hada kin fasa shegen bakin turancin da take xagin mutane da shi a gidan nan” Yakumbo na huci tace “Ai Amina ta cuce ni, ta yaudare ni… Tasan haka shegiyar yar take xata kawo min ita tun farko, gode gode da yarinya bata iya komai ba wanke wanke duk ta jika kayan jikinta tayi awa da awanni a bakin kwararo, shara duk a gantale, gyaran daki gwara ka da fauziyya mai shekara biyar, aike sai kayi yyi sau uku, har yau ta kasa iya hura icce, girki dama ba a maganar sa, wa ennan yan mitsimitsi yaran idan na sa ta tayi masu wanka ta shaka masu sabulu a hanci ko a ido, ni dama tun farko abinda ya sa na karbeta na yi xatan xan amfana da ita ne, banda haka me xai kai ni kowa na ta kansa a rayuwar nan gashi gobe ko jibi xa a xo a fitar mana da kaya har ynxu ban kama wani gidan ba, ni wllh wllh da nasan gidan Amina sai in yi kudin mota in mayar da ita ta bani kudi na don baxan iya kayan tsiya ba, dama can Aminar ma ba wani kyautata min take ba uba ne kadai ya hada mu” Salamatu tace “Ai irin yaran nan kyansu aikatu wllh, a can xa a horasu su ladabtu….” Katse ta yakumbo tayi tace “Yar da har yanxu bata iya shara ba xan kai aikatau, ai koramu xa ayi daga ni har ita” Ladi tace “Yo ke nuna masu xa ki yi bbu abinda bata iya ba ai, a can xa su gyara mata xama ta iya komai, mutanen da basu san darajar d’an Adam ba, ai tuni wahalar da xa su dinga mata xai sa ta xage a nan kuma xata koyi komai, wannan d’an abincin da kike bata ma take kin ci take yawo da yunwa can nema xata yi ta rasa, hakan xai ladabtar da ita wllh” Yakumbo ta ja kujerar tsugunno ta xauna tace “Kai amma fa kun kawo shawara, amma….” Sai kuma tayi shiru ta kalli khadijah dake kallonsu, tsawa tayi mata ta ce “Fita ki ban waje kije gun mai kanti da hamsin di ta dake gunsa ki amso min barkonu” juyawa khadijah tayi da sauri ta fita gidan, Yakumbo ta mayar da dubanta gun su Ladi tace “Toh Amina fa? Kunsan baxa ta yarda ba” dariya Ladi tayi tace “Ka ji ki, sai ki gaya mata, barin ma yanxu tashi xa ku yi Ku bar anguwar, shawara a nan shine kada ki kuskura ki gaya ma ko inda kika koma a anguwar nan, kawai cewa xa ki yi ba ki ma samu gidan ba gidan wata yar uwarki xa ki kafin ki samu, ke kuwa kije shanono abun ki ki kama ko daki daya ne bbu wanda yasan inda kike, dama ba waya gare ki ba, har ki tara kudin da xa ki tara da yarinyar daga nan idan ma mayar da ita gun Aminan xa ki yi sai ki ja mata kunne ki mayar da ita” Yakumbo tayi murmushi tace “Dadina da ku akwai shawara mai ma’ana, amma fa har da kudin da xan sa yarinyar a makarantar gwamnati ta bani, yanxu haka ma da kudin xan je kama haya a shanonon, dubu hamsin kuma jari xan ja na su omo da sabulu ina siyarwa, ita can na kai ta gun aiki ana biyanta dubu uku misali, kun ga ni ban ma kai da nisa ba….” Ladi tace “Toh gaskiya sai kin ba mu dubu dai dai mu da muka kawo shawarar Ashe ma kudi gare ki har haka” yakumbo ta hade rai tana da ta sanin gaya masu, rai a bace tace “Dari bibbiyu dai” daga haka ta mike ta shiga cikin akurkin dakinta, sai ga ta ta fito da sauri tace “Toh yanxu wa xai min hanya in kai ta gidan aikin, don ni gaskiya baxan tare da ita a sabon gidana ba, ko yau aka samu gun aikin ba don yamma yyi ba kai ta xan yi, don haka gobe da safe xan kai ta….” Ladi tace “Akwai wata kawata Habiba dillaliyarsu ce, xan baki lambarta… Ko kuma ki sa katin dari a wayata mu kirata, in sha Allah nasan baxata rasa inda xata kai maki ita ba” hakan ko aka yi Yakumbo ta sa kati ladi ta kira Habiba, suka ci sa’a number ya shiga, bayan ladi ta gaisa da kawartata tace “Bibalo dama wata yarinya ce da ake son kai ta gidan aiki to shine muke son ki yi taimako” Bibalo tace “Kai yanxu haka Ina hanyar dawowa daga kauye na mayar da wasu yara, amma gobe da safe xa ki gan ni duk da bani da wa enda ke son masu aiki yanxu, amma nasan kawata Abu baxata rasa ba don ta ma fi ni sanin gidajen manya” daga haka suka yi sallama ladi ta katse wayar tana kallon Yakumbo don ba sai ta mata bayani ba tunda a handsfree tasa ita ma ta ji komai, Yakumbo tace “Toh Allah ya sa a dace, ni wllh ko dubu biyu ma xa a dinga biyanta na yarda” tagumi tayi tace “Allah gani gare ka, kasa a karbi yarinyar nan ni kuluwa” Washegari da safe kuwa sai ga Bibalo tare da kawarta da ta fada Abu, Yakumbo dake ta washe hakora ta gaishesu suka amsa aka xaxxauna kan tabarma ladi ma ta fito akurkin ta tana masu sannu da xuwa, bayan sun gaisa Bibalo tace “Toh kinga ni bni da inda xan kai ta amma Abu tace kawarta ta taba hadata da wata Hajiya mai neman mai aiki, da xata dinga share share da goge goge sannan wanke wanke, akwai ma wata babbar mai aiki dake girki a gidan, to Abu taje gidan ya fi sau uku ba a bude mata gate, yanxu ma gwada sa’a xa ayi kuje har da ke kika wajen, idan sun dauketa to, idan kuma sun ce A’a sai ki jira har a bukaci mai aiki a wani gidan sai in kai ta” Yakumbo tace “A’a mu je kawai mu gwada sa’ar mu” Bibalo tace “Toh ki sallame ni ni xan wuce” Yakumbo ta hade rai tace “In sallame ki? Me kika min da xan sallame ki” Bibalo ta bude baki tace “Au haka ma xa ki ce, shi kudin motar da nayi da kuma bata lokacina da na yi na xo nan tare da kawata har xa ki ce min me na maki” mikewa Yakumbo tayi rai a bace ta shiga ciki ta fito da dari biyu tana cewa “Ko daukar yarinya ba ayi ba xaki wani ce in sallame ki idan ba hadama ba” dungura mata dari biyun tayi a gabanta rai a bace, Bibalo ta dauka ta mike tace “Ya fi babu ai” daga haka ta yi ma Ladi sallama da Abu tayi ficewarta, Abu tace “Toh inji kinsan mu dubu daya ce sallamar mu?” Yakumbo ta hade rai tace “Idan an dauki yarinya ba” Abu tace “Toh gwara da kika san haka don ni baxan tsaya cacar baki ba, yanxu Ina yarinyar take?” Yakumbo ta nuna mata khadijah dake ta fama da wanke wanke, kwalalo ido tayi tace “Warcen da ta fi minti ashirin tana d’an wanke wanken can, tun shigowar mu fa take wanke wanken kamar ayi kamar baxa ayi ba” yakumbo ta marairaice tace “Haka take Abu, akwai iya aiki amma ba sauri ne kawai, amma tana xuwa can nasan xa su gyara mata xama ta xama mai hanxari” Abu ta tabe baki tace “Toh unguwar da nisa, don can Gra ne, kuma wllh gidan babban mutane ne, ni dai Allah ya sa su dauketa, yanxu sai ki tashi ku shirya ta hada kayanta ina jiran ku mu kama hanya” Yakumbo ta mike da sauri ta shiga ciki tana cewa “Toh bamu minti biyar kacal” tana shiga dakin ta kwalo ma khadijah kira, khadijah ta mike ta shiga da sauri. Yakumbo ta jawota tayi kasa da murya tace “Dijangala ta mai gari, ba auren talaka ba” tana washe hakora ta fadi haka, ita dai khadijah kallon ta kawai take, Yakumbo tace “Kinsan inda xa mu yanxu kuwa?” Girgixa kai khadijah tayi, Yakumbo tace “Gidan da xa a dinga biyanki kudi mai yawa in tara maki in sa ki a boko, kai har in maki aure ma” khadijah tayi shiru bata ce komai ba, yakumbo ta marairaice tace “Don haka muna xuwa kice kin iya aikin komai, sai ki bada himma idan an saki aiki ki yi da sauri da sauri, sannan don Allah Idan mun je gidan khadijah kar ki masu wannan yaran naki na turanci kin ji koh? Kawai Hausa xa ki masu, idan kuma baki san Kalmar da xa ki fada da hausa ba sai kiyi shiru abun ki ba sai kin yi turancin ba” yanxu maxa canxa kayan Ki bari in tusa maki wa encan a jaka tunda basu samu wanki ba idan kin je can ko ba ki iya wankin ba ki tsoma su a ruwa ki xuba omo ki shanya” daga haka Yakumbo ta shiga tusa kayanta a wani karamin Ghana must go, don har ta siyar da jakar da Umma ta kawo mata kayanta ciki, karfe tara da kusan rabi su yakumbo suka bar gidan tare da Abu bayan ta yi ma yan gidan sallama suka dinga yi mata Allah ya bada sa’a, tana rike da hannun khadijah suka isa bakin titi, Abu tace “Amma kinsan ke xa ki biya kudin abun hawa dai koh?” Yakumbo ta tsuke fuska tace “A kan me?” Abu tace “A’a mayar da wukar ae dai naga ba xuwan kai na xan yi ba gidan don hka idan kinsan gidan ke sai ki kai ta, yakumbo ta rikota da sauri tace “Naji, mu je ya na iya, daga yau ai babu wanda xai xo yace in biya masa kudin napep dai koh?” Ko tanka ta Abu bata yi ba ta shiga napep din da ta tsayar, Yakumbo ta shiga ta daura khadijah a cinya. Tafiya ce mai nisa kamar yanda Abu tace masu, tun da suka bar hayi dama Yakumbo ke addu’ar Allah ya sa a dau khadijah gidan aikin idan ba haka ba asirinta ya tonu don ta sa rai da kudin da xa a dinga biyan khadijah, tun da suka shigo anguwan Yakumbo ta saki baki kamar yawu xai dalalo tana kallon gidaje na alfarma, Abu ta dinga nuna ma Mai napep din inda xai bai, har suka iso wani cool silent anguwa mai cike da shuke shuke a ko wani gate, ga bakin kwalta a shimfide daga farkon layin har inda yakumbo ke tunani karshe ne, bakin wani gate Abu ta sa mai napep din ya tsaya, yakumbo ta wage baki tana kallon jibgegen gidan da aka yi ma ginin xamani kamar ta sure ta gudu, gidan ya hadu ne kawai don ita a ganinta duk ya fi sauran gidajen dake layin haduwa, suka sauka sai kuma Yakumbo aka tsuke fuska da ta tuna kudi xata bada yanxu, ta dungura ma mai napep din kudin da yace lkci daya kuma tana hararan Abu, Abu da ko lura da ita bata yi ba tace “Toh Allah ka bamu sa’a don kwanaki da na xo haka na sha xamana bakin gate rana yayi maganina ban samu shiga gidan ba… Yakumbo tace “Yana da kyau mutum ya dinga fadin alkhairi ko yayi shiru, yanxu me ya kawo wannan xancen, in sha Allahu ma sai mun shiga don haka ki mana shiru” daga haka Yakumbo bta kwankwasa gate din a hankali kamar me tsoron kada ya fashe don ita fa gani take kamar glass ne a kauyancinta, ta kwankwasa ya kai sau hudu kafin wani da alamar mai gadi ne ya bude yana kallonsu, Yakumbo ta durkusa har kasa ta gaishesa, yace “Wa ku ke nema?” Yakumbo ta mike tace “Matar gidan muke nema ce mana tayi mu samo mata mai aiki yarinya karama, to cikin ikon Allah gashi mun samo mai haxaka, shine muke hadaka da Allah yaro ka bar mu mu shiga, mu gabatar mata da aiken da ta mana” ya girgixa kai yace “Ai akwai mai aiki yanxu haka a gidan don haka ban ji xa a bukaci warce xa ku kawo” Bakin yakumbo ya fara rawa tace “Wllh xa su bukata dubeta fa kaga bbu abinda bata iya ba, sannan Hajiyar da kanta ta sa mu ko daxu mun yi waya da ita tace sai mun xo, haba yarona ka duba tsufana mana gashi daga hayin rigasa muke wllh” Mai gadin yace “Toh yanxu ma ku kirata idan tace ku shiga toh shkkn” daga yakumbo har Abu aka hadiye yawu da kyar don babu mai waya cikinsu, Yakumbo tayi karfin halin cewa “Wallahi wallahi na mance wayar a gida kaji rantsuwar musulmi” Abu ta saki baki jin rantsuwar da Yakumbo tayi alhalin taji Bibalo tace bata da waya.

Back to top button