Hausa NovelsNoor Al Hayat Hausa Novel

Noor Al Hayat 18

Sponsored Links

A hankali khadijah dake kallonsa tace “please” ya dago ya kalleta kafin yace “Sai in gan ki a ina in baki abincin?” Shiru ta yi kamar me naxari, can tace “Ohk, ae akwai flowers a kusa da gate din, to ka dinga ajiye min a wajen idan na fito sai in dauka” murmushi yyi yace “Koh?” Ta gyada masa kai, yace “Ohk” ta kara matsowa gaban sa tace “Promise u will do that plss” yace “I will” ta wara idonta ta hade hannayenta tace “Thank you very much, may Allah reward you, byeee” daga haka ta juya da sauri ta bar wajen ta nufi gida ya bi ta da ido, bbu wanda ya bi ta kanta ta ajiye sakon a kan kujera ta fito ta ci gaba da wanke wankenta Happily, sai kusan karfe biyar ta gama ta shigo ciki, Hajiya Maimuna ta hada ta da uban kayan yaranta ta linke su ta xuba a cupboard, sai kusan magrib ta fito ganin kowa na alwala ita ma taje bakin tap tayi alwala ta dawo tayi sllh, tana rakube jikin kujera aka fara kiran kowa ya je kitchen ya karba abinci, ita ma ta tashi sanin Hajiya Maimuna na iya kunduma mata xagi idan taga bata shigo ba, tuwo ne da miyar karkashi aka yi ranan, ta fito bayan an dungura mata nata tana kallon cikin tuwon, xaunawa tayi ta kai hannu cikin miyar dake turiri ta dangwala ta kai baki, ta kasa hadiyewa ta shiga satan kallon mutanen parlorn trying very hard to keep her face normal, kowa hankalinsa na gun kallon Hausa film da ake yi a TV, ita da yake can gida basa kallon Hausa film ko bin ta kan kallon bata yi ba, sulalewa tayi ta fita waje rike da kwanon tuwon ta ajiye nan verenda ta nufi gate da sauri, a hankali ta durkusa gun flowers din bakin gate tana addu’ar Allah yasa ya ajiye mata abincin, ta bude flower din a hankali tana dubawa ai kuwa ta ga leda fari, ta dauka da sauri ta bude taga takeaway ne da goran five alive, ajiye ledan tayi ta doka uban tsallen murna sannan ta dau ledan har tana tuntube ta shiga cikin gida, backyard ta nufa da sauri ta nemi wani lungu ta xauna ta bude abincin taga jollof rice ne da naman kaza da plantains sai sauce a gefe, Cike da murna ta fara cin abincin tana ci tana gyada kai har da lumshe ido, sauri sauri ta cinye abincin ta bude drink din ta sha kusan rabi sauran ta kasa shanyewa, ta mike ta boye goran drink din sannan ta dau takeaway din ta fita gate ta jefar cikin katon abinda ake xuba shara ta dawo ciki tana goge bakinta, sai da ta tsorata ganin tuwon da ta ajiye ta kauda kai da sauri kamar ta ga mugun abu ta daukesa kamar wani shara tana yamutse fuska ta fita waje, almajiri ta samu ta juye ma sannan ta dawo gidan ta tafi gun tap tana wanke kwanon sajidah ta leko da alamar sai lkcn aka lura bata parlorn, yarinyar ta juya ta koma Khadijah ta bi bayan ta da sauri rike da kwanon da ta wanke, Hajiya salaha tace “Daga ina kike?” Ta nuna mata kwanon tace “Naje wanke wa ne” salati ta saki tana tafe hannu tace “Yanxu abincin kika je kika xubar khadijah?” A tsorace tace “Wllh mama ban xubar ba” Hajiya Maimuna tace “Karya kike, kece xa ki ci tuwon nan har ki cinye?” Ta marairaice tace “Amma ban xubar ba wllh” Hajiya salaha tace “Toh ya kika yi da shi?” A hankali tace “Na ba almajiri” cup Hajiya Maimuna ta dauka ta jefeta da shi tace “Allah ya isa” Khadijah tayi kofa da gudu ta fita ganin Hajiya salaha ta mike, can bakin gate ta tafi ta tsaya a tsorace, yau ma dai kamar jiya kawu ne ya shiga da ita parlor, bayan ya duddungureta yyi gorin iya son ransa sannan ya juya kan iyalansa cike da fada yana nanata masu indai suka janyo ma khadijah malaria sisin sa baxai yi ciwon kai ba sai in su xa su kai ta asibiiti, bbu warce ta tanka sa cikinsu, ya gama bambamin sa ya shiga ciki. Washegari sai da kowa ya tafi makaranta khadijah ta fara wanke wanken kwanukan jiya, kamar xata yi kuka take yi don duk sun bubbushe, tayi kusan awa daya bakin tap din ta bar sauran kwanukan ta shiga ciki, Hajiya tace “Kin gama ne munafuka” ta girgixa kai tace “Na kai halve” koranta tayi taje maxa ta gama, khadijah ta fito tana kallon agogo ta ga karfe tara ya wuce har da rabi, cikin sanda ta nufi gate ta bi anguwar da kallo ta ga ba kowa da yake silent anguwa ce, bude flower tayi dai dai wajen jiya taga farin Leda, ta washe hakora ta dauka da sauri ta shiga ciki, backyard ta nufa tana waige waige kamar munafuka, ta samu inda ta xauna jiya ta xauna ta bude ledan ta fiddo takeaway din, fried potato ne na turawa da uban kwai a ciki, ta lumshe ido tana murmushi, ta fito da wani water bottle karami da ke ledan ta bude tana kallon ciki taga shayi ne yaji madara da Milo, ta wara ido tace “Wowwww” har wani rawa hannunta yake ta kai bakinta tana yi a hankali kar ya konata taji bbu xafi sosai, tun da ta kafa baki bata ajiye ba sai da ta ga bayan shayin, ta ajiye bottle din ta rufe tana lullumshe ido ta dau fork din cikin ledan ta soma cin dankali da kwan, da kyar ta gama cinyewa don ta koshi kuma bata son xubar da abincin, ta tashi a hankali tana leke leke ta fita da gudu ta jefar da takeaway din a bola, ta dawo bakin tap ta wanke bottle din ta sa a Leda ta koma jikin flower ta bude ta ajiye sannan ta shigo ciki ta ci gaba da wanke wanken, bayan ta gama ta shiga ciki Hajiya Maimuna ta nuna mata kunu a cup da aka rufe a walakanci da wani bushashen bread a leda tace “Idan kin ga dama gasu can, don bawa baxae biye ta halin ki ba tunda yana da baya” Khadijah ta girgixa kai ba tare da ta sake kallon direction din kunun ba tace “Ni na koshi mama” sakin baki Hajiya Maimuna tayi can tayi murmushin mugunta tana gyada kai tace “Toh maa sha Allah” xaunawa khadijah tayi a favourite position dinta, daga karshe Hajiya Maimuna ta mike ta wuce ciki, kwanciya khadijah tayi don ji tayi cikinta ya mata nauyi nan da nan kuwa bacci ya dauketa. Yau ma dai da rana shinkafa da mai da yaji aka girka, tana gani suka xubo ma baki da suka yi ita ko oho sai ma wankin socks da panties din yara da aka tula mata bakin tap abinda bata taba ba, sai shafa socks din take tana turo baki gashi ta fara jin yunwa da wajajen karfe uku ne, kalle kalle ta fara yi kafin ta mike kamar mara gaskiya ta fita wajen gate, bude gun flower tayi a hankali taga farin leda sabo, ta wara ido ta dauke ledan taga bbu na bottle din da tasha daxu, ta shiga ciki da sauri ta wuce backyard, snack ne a ledan da roban five alive. Nan da nan ta ci da sauri ta sha drink din sannan ta fita ta xubar da ledan a shara taje ta ci gaba da wankin ta. Sai kusan la’asar bakin suka tafi, Hajiya salaha ta fito ganin wankin da Khadijah tayi, kuka ne kawai bata yi ba, amma har kumfa bakinta yake don fada da xage xage ita dai Khadijah na tsaye jikin bango tana kallonta tana wasa da flower din gown din jikinta, sai da Hajiya salaha ta mayar da gaba daya kayan cikin bucket ta xuba omo xata sake wankewa, Allah ya isa kam Khadijah ta sha sa na barnar omon da tayi mata, daga karshe Hajiya Maimuna ta kirata kamar ta ji shawarar da mai kanti ya ba khadijahr ta dungura mata takarda dauke da abubuwan da xata siyo mata ta bata kudin ta je kanti, Khadijah na isa kantin bayan ta basa takarda ta sa ya bata fallen takarda da Biro, yana mika mata ta xauna shi kuma ya ci gaba da hada mata kayan Aiken da aka yi mata a Leda, rubutu tayi kamar haka “Assalam, I am soo happy you fulfilled ur promise, I am no longer hungry anymore, I love the foods, may Allah reward u abundantly, I like you.” Ta tsura ma neat writing dinta mai kyau ido tana murmushi, can ta linke takardar ta mayar ma mai kanti biron sannan ta karbi kayan ta ta wuce da sauri, cikin flowers ta bar takardan yanda xa a gani sannan ta shiga gida, Hajiya Salaha dake ta wanke ta jefa mata kallon tsana tace “Shi yasa fa kayan ki can a kwandon kayan wanki har sun fara tsutsa maga uban da xai wanke maki, ba dai duk kin saye kayan ba” Ita dai bata ce komai ba ta shiga ciki ta kai ma Hajiya Maimuna sakonta. Karfe biyar da rabi yara suka dawo gaba daya, aka xuba ma kowa abinci amma banda ita, ko kallon inda abincin su yake bata yi ba banda kallon da take har kowa ya gama cin abincin ya kai kwanuka waje, Hajiya salaha ta shiga kitchen gun kishiyarta dake girki tace “Maman Hafsa kinsan yarinyar can daxu bata karya ba gashi yanxu ma ko damuwa bata yi tace ina abincin ta ba?” Hajiya Maimuna tace “Wallahi ina lura da ita, ke dai na mu ido, ranan yanke jikinta ta fadi ya kusa xuwa, ni dai baxan roketa ta xo ga abinci ba idan ma ba ta ci ba auki xai ma yaran mu” Hajiya Salaha ta fita tana cewa “Toh ni kinga ina bi ta kanta” Da daddare yau dai macaroni dafaduka aka yi ta manja, Khadijah ta ki xuwa kitchen ta karbi abincin sai kallo take, Tsawa Hajiya Salaha ta mata tace “Toh maxa tashi ki fita ki wanke kwanukan daxu da aka 6ata, ba dai kina xaune kina jiran a kawo maki abinci ba…” Khadijah ta mike ta fita da sauri daga parlorn Hajiya ta bi ta da kallon mamaki don a tunaninta xata shiga kitchen ne, wanke wanken taje ta d’an yi kafin ta fita gate da sauri ta bude flower sai ga wani ledan, tayi murmushi ta dauka ta dawo ciki ta wuce favourite position din da take xama ta bude take away din taga shinkafa ce da miya sai nama kusan yanka biyar ta wara ido cike da jin dadi ta fiddo goron five alive ta ajiye sannan ta fara ci, cikin few minutes ta gama saboda saurin da take ta koshi ba kadan ba don har ta kasa shan drink din gaba daya, ta boye a inda ta saba boyewa sannan taje ta jefar da ledan ta dawo ta ci gaba da wanke wanken tana gyangyadi tsabar koshin da tayi, da kyar ta karasa ta shiga ciki wajen karfe tara tana shiga kuwa isha tayi suna ta kallonta su ji ta ce ina abincinta amma sai ji suka yi tace xata je kwanta daga haka kuma ta tafi tayi kwanciyarta. Haka nan Khadijah ta ci gaba da rayuwa gidan har na kusan wata biyu bbu ranan da ya taba fashin ajiye mata abinci gashi tun haduwar da suka yi a kanti ta bukaci ya dinga ajiye mata abincin basu sake haduwa ba, duk kwana biyu sai ta ajiye masa note din godiya cikin flowers, Bbu abinda ke daure ma Hajiya Maimuna da Hajiya salaha kai irin yanda suka ga Khadijah ke ta kiba tana kyau gashi fa sai ta kai har washegari wani lkcn bata ko bi ta kan abinda suka girka ba, ga uban aikin xa take narka kullum a gidan, ranan dai abun ya ishi Hajiya Maimuna tace “Ni kam yarinyar nan ko dai akwai gun da take xuwa cin abinci ne ba mu sani ba, dubi fa ko bin ta kan abincin gidan nan bata yi ko da an xuba mata sai ta ki ci, gashi lafiya lau sai ma kiba da na ga ta yi kamar” Hajiya Salaha tace “Nima abun na daure min kai kuma kema kinsan bbu inda take xuwa sai gun mai kanti kuma bata dadewa take dawowa gida” Hajiya Maimuna tace “Yanxu dai kawai mu sa ma duk movement dinta ido sosai” Da rana Khadijah na ta xaune parlorn tana jiran su tafi su kwanta taje ta dau abincin ta a flowers, kallon wani Hausa film suke, taga basu da niyyar shiga ciki, ta mike ta dauke few plates dake parlorn duk da tayi wanke wanken safe tace “Mama in je in wanke” Hajiya Salaha tace “Toh sai kin tambaya, ko ba aikin ki bane” fita tayi da sauri don dama abinda take nema kenan, tana ajiye plates din ta fita gate, tuni su Hajiya suka fito suna lekan compound suka ga bbu ita, hakan yasa Hajiya Salaha xata nufi gate Hajiya Maimuna ta rike tace “Jira kamar ga kafafuwanta can a tsaye” ko rufe baki basu yi ba sai gata ta shigo da leda suka yi saurin makalewa da bango, ko lura da su bata yi ba ta wuce inda ta saba xama da sauri, ta bude soyayyen kwai da indomien dake turiri kenan ta ajiye five alive a gefe, sai ga su a kan ta, tsuru tsuru tayi tana kallonsa kamar yanda su ma suka saki baki suna kallon abincin, salati suka saki a tare, Hajiya Maimuna tace “Uban wa ta baki wannan abincin Khadijah” Khadijah da tayi mugun tsorata xata mike ta gudu Hajiya Maimuna ta cafketa tace “Gun ubanwa kika karbo?” Jikinta na rawa tace “Ku yi hakuri” Mari Hajiya Maimuna ta xabga mata tace “Dama shi yasa kika daina bi ta kan girkinmu a gidan nan, karuwanci kika fara ba mu sani ba? To yau sai kin fiddo wanda ke baki abincin nn” cikin kuka tace “Gidansu yana can mama” janta suka yi suka fita ko warce ta yafe dankwalinta a kai ana huci suka ce “Mu je gidan”

Kuka kawai Khadijah take a tsorace tana biye da su Hajiya Maimuna na janta har suka isa kofar gidan, Cikin rawar murya tace “Nan ne gidan….” Hajiya Maimuna ta xaro ido tace “Nan kike xuwa?” Ta girgixa kai da sauri tace “Mama sau daya na xo, mutumin ne ke kawo min abincin ya ajiye cikin flower, ku yi hakuri don Allah” kwankwasa gate Hajiya salaha ta dinga yi da karfi mai gadi ya bude, tace “Ina masu gidan nan” Mai gadin yace “Daga ina?” Bin gefensa tayi a fusace ta shiga tace “Xaka ji da munafurcin ka, ni din ce xaka ce baka taba gani ba” Hajiya Maimuna ta bi bayan ta tana jaye da Khadijah suka isa parlorn gidan suka bude, Hajiya Maimuna ta rafka sallama kamar tashin duniya, Wata yar budurwar ce ta fara fitowa tana kallonsu ta gaishesu, a takaice suka amsa suka tambayi uwarta, ta juya kenan xata je kiranta sai ga ta ta shigo parlor, har ta karaso kallonsu take da mamaki, Hajiya Maimuna ta hade rai tace “Hajiya Amina mun wuni lafiya?” Hajiya Aminar tace “Alhmdllh, in ji lafiya” Hajiya Salaha tace “Ba lafiya ba, ina d’an ki yake?” Da mamaki tace “Da na kuma?” Cike da jaraba Hajiya Salaha tace “Kwarai, ya fito ya gaya mana menene tsakaninsa da yarinyar nan, ya fito yanxun nan” Hajiya Amina tace “Kar ku min hayaniya a gida don Allah, ku gaya min meye ya faru?” Hajiya Maimuna tace “Hayaniya kam dole, don wannan case din sai ya iya kai mu har kotu, tunda batanci yake yi da ‘yar mu” bude baki Hajiya Amina tayi tana kallonsu, haka ma ‘yar ta… Khadijah dai sai matsar kwalla take jiki na rawa, Dai dai nan kuwa sai ga shi ya fito parlor, tsaye shi ma yyi yana kallonsu da mamaki, Mahaifiyarsa da ranta ya gama baci tace “Sadeeq, what’s between you two” ta fadi haka tana nuna masa khadijah, kafin yace komai Khadijah tayi saurin cewa “Nothing ma, kawai yana kawo min abinci yana ajiyewa cikin flowers ne in dauka in ci…” Buge mata baki Hajiya Maimuna tayi ta kunduma mata xagi tace “Kece sadeeq? Makira yar iska? Ke ta tambaya?” Sadeeq dai na tsaye yana kallon ikon Allah ya kasa cewa komai, mahaifiyarsa tace “Magana nake maka malam” ya juya ya kalleta yace “Mum I don’t think I have time explaining my self to any of this women, ni dai nasan the girl told me about how hungry she was ba’a a bata abinci a gidan, and I volunteered….” Uwarsa ta xaro ido tace “Volunteered what Sadeeq?” Ya d’an hade rai yace “She requested in dinga ajiye mata abinci a flowers din kofar gidansu thats all, sannan tun ranan bamu sake haduwa da ita ba cox dama gun wancen mai kantin muka hadu, sai kuma yanxu da take tsaye a nan, ashe dama taimako na xama laifi, kuma da ba su barta da yunwa ba har xata ce in dinga ajiye mata abinci she’s always hungry? Ba komai kuma yasa nake ajiye mata abincin ba sai don nasan bbu illar da ya kai barin ‘ya mace da yunwa, bana son ta shiga wani hali shi yasa, if not what’s my connection with her da har xan dinga bata 3 daily meals?” Tunda ya fara magana su Hajiya suka saki baki suna kallon Khadijah da ta sunkuyar da kai, Hajiya Maimuna tace “Toh kayi na farko kayi na karshe, dauki 3 daily meals din naka ka kai gidan almajirai ko marayu, kada ka sake xuwa mana kofar gida da abinci, ita kuma yanxu xa mu koma gida mu ji wanda yake barin ta da yunwa da tace she’s always hungry” Hajiya Salaha tace “Sai ma kin fada, kuma wllh Allah ya isa tsakaninmu da ita tunda mu ta ke bi gida gida a anguwar nan tana cewa muna barin ta da yunwa, bbu abinda xai hanani yi mata jina jina yau” Daga haka ta ja ta xasu fita, khadijah ta hade hannunta tana kallon sadeeq cikin rawar murya tace “I am very sorry” Rankwashi Hajiya Salaha ta kai mata da karfi ta ja ta suka fice gidan, Hajiya Amina ta kalli d’anta tace “Daga this very moment na raba ka da abinda kake yi” Hajiya Maimuna tace “Da dai ya fi maku” daga haka ta bi bayan su. Duka da xagi kam khadijah ta sha shi ranan, duk ta fita hayyacinta sai kiran Ummarte take, don Kansu suka kyaleta daga karshe, indomie da kwan kuma suka dauke suka juye a plate suka cinye. Tun daga ranan sadeeq bai sake ajiye mata abinci ba, kafin kwana biyu ta rama duk ta xama wata iri har lkcn ta ki kwantar da hankali ta ci abinci da suke girkawa, sai taji yunwar xae sumar da ita take tura abincin ko yaya shi ma wani lkcn har da amai sai tayi, tafe take kamar iska xai kadeta tsabar weakness dake tartare da ita, ta isa gun mai kanti ta basa takardar da aka aiketa ya karba yana tsokanarta kamar yanda ya saba, ita dai bata ce komai ba unlike before da xata fara masa turanci, kiranta taji anyi ta juya da sauri jin muryar, ta ga Sadeeq tsaye bayan ta, ta yi murmushi tace “Good evening” a hankali yace “How you?” Tace “Fyn” kallonta ya dinga yi ganin yanda ta rame, ta juya ta karbi sakonta tace “Bye” yace “Khadijah” ta juya da sauri tana kallonsa, yace “You are always hungry koh?” Shiru ta yi hawaye ya cika mata ido, yace “I am sorry I cant help it” ta ce “Don’t worry, I appreciate the one you did before…..” Hannu ya sa a aljihu ya Ciro kudi ya kirga dubu biyar ya mika mata yace “Toh gashi ki boye wannan ko biscuits da doughnut sai ki dinga siya kina ci a nan kinji?” Shiru ta yi ya kamo hannunta ya sa mata yana murmushi ya gyada kai yace “Yeah” rike kudin tayi ya sake hannunta yace “See you some other time” ta daga masa hannu hawaye cike idonta tace “Thank you” hanya daban daban suka bi tana isa gida ta boye kudin, tana son fita ta siyo abinda yace da daddare ta kwanta amma tana tsoro, hakan yasa ta sha ruwa kawai ta kwanta cikinta na kugi don wake da taliya aka yi daren ranan. Bayan kwana biyu tana xaune ita kadai tsakar gida tana tankaden uban garin masaran da Hajiya salaha ta hada ta shi, duk kayan jikinta ya koma fari kamar warce ta yini a kusa da injin nikan, ga hawaye da ya bubbushe fuskarta, a kan tankaden nn tun safe Hajiya Salaha ke dukanta da tayi sai tace bai yi ba, hakan yasa take yi a hankli ynxu bayan ta ci kukanta ta koshi, bude gate aka yi ta daga kai ta ga Ummarta, still tayi rike da rariyar, kamar yanda ita ma Umma ta tsaya kallonta ko kiftawa bbu, hawaye ya cika idon khadijah ta mike da gudu ta nufeta ta rungumeta tace “Ummata” sosai Umma ma ta rungumeta duk jikinta yyi sanyi, can ta janyeta jikinta tana kallonta daga sama har kasa, hawaye ne ya cika idonta ta mata alamar ta dauko takalmarta, khadijah ta koma ta dauko takalman da duk sun tsinke ta sa su haka, Umma ta ja ta suka fice daga gidan, Khadijah dake ta bin ta tace “Ummata tafiya xa kiyi da ni?” Hawaye na sakkowa idonta tayi tambayar, Umma ta gyada mata kai kawai don ta kasa cewa komai, suna isa dai dai gidansu Sadeeq khadijah dake murmushin farin ciki tana rike da hannun Umma gam tace “Umma I have a frnd here, can I just go and bid him goodbye, he is more than kind” Umma ta kalleta for d 1st time ta bude baki cikin sanyin murya ganin hawayen dake ta sauka idon khadijar, tace Some other time dear, khadijah ta gyada mata kai har suka wuce kofar gidan, da sauri Umma ke janta har suka isa main road ta tsayar da adai daita, direct sai motor park, ta biya masu kudin mota bayan yan mintuna motarsu ya tashi xuwa garin kano, bacci Khadijah ta dinga yi jikin Umma don tun asuban fari aka tasheta a can gidan, har suka isa kano bacci take yi, Umma ta tasheta, ta bude ido a hankali, suka sauka cikin motar Umma na rike da ita suka fito bakin titi ta dau adai daitan da xae kai su har gidan da take aure. Ba laifi babban tsakar gida ne compound din mai dauke da small building har hudu, ko wani building na da parlor da daki a cikinsa, sai babban kitchen dake tsakar gidan, da kuma bayin wanka biyu da toilet ma biyu, a gefen kitchen kuwa ga rijiya a rufe, gidan da Umma ke aure kenan, tana kuma auren d’an kasuwa ne mai mata biyu, yara ne su kusan biyar ke ta wasa tsakar gidan da yake da yamma ne kuma ranan alhamis ba islamiyya, da wasu yan mata uku dake xaune kan tabarma suna danne dannen waya, umma ta amsa gaisuwar da yara kananan ke mata ba tare da ta sake kallon gun da yan matan suke va ta fiddo key ta bude part dinta, khadijah dai na tsaye sai kallon yaran take kamar yanda su ma ke kallonta, can ta kalli yan matan taga su ma kallonta suke, Umma ta kalli direction din kitchen jin kamshin girki suka yi ido hudu da Shafa kishiyarta dake lekosu ta cikin kitchen din, suna hada ido kuwa tayi saurin dauke kanta, Umma ma ta dauke nata kan, can ta hango uwar gidan mai gidan nata ita ma tana lekota ta windown parlornta ita ma suna hada ido tayi saurin dauke kai, Umma ta bude kofar ta ta ja hannun Khadijah suka shiga ciki ta dage labule ta daura kan kofar kasancewar parlorn ya dau xafi.

Back to top button