A Rubuce Take Book 2Hausa Novels

A Rubuce Take Book 2 Page 39

Sponsored Links

Part 02

Page 39

Duk da kayanta ne na wancan gidan nasu amma gidan yayi bala’in burgeta,komai ya tsaru,an kuma shirya mata shi dai dai da ra’ayinta da kuma yadda takeson gida ya kasance,ta dinga satar kallon abbas tana mamakin yadda ya karanci komai nata,me takeso,meye bataso,walwala da damuwarta,sai taji zuciyarta ta karaya,ta samu kanta da addu’ar kada Allah ya kawo abinda zai sake rabasu ko ya saka shakka ko rudani a tsakaninsu har qarewar numfashinsu.

Widad din mutum ce mai matuqar qoqari,a tsaye take kan hidimar gidanta,duk da komai a gyare yake amma sai da tayi goge goge,ta kuma samar musu da abinci duk da akwai taimakon abbas din yana kama mata,sannan suka sake wanka gaba dayansu suka shirya don wucewa gidan saukar yaaya bara’atu.

Yana riqe da hannunta suka shiga motar tata

“Inajin aminatu zanje na roqa abarmiki,wannan aikin yana miki yawa” dadi sosai ya kamata,ta murmusa tana cewa

“Amma da ka kyautamin qwarai,inason yarinyar,tana da hankali,amma kuma ranka ya dade,naga kaman baka da ra’ayin daukan mai aiki” kallonta yayi sannan yayi murmushi

“Wayon tsiya gareki,nasan me kikeso kice,na farko amintu ai bame aiki bace,qaramin qarfi garesu,daukotan zai zama kamar taimako,kamar yadda tasa aka dauko lawan yaso ya zame mana wani abu daban,na biyu kuma ina da tabbacin ko ire iren aminatu dubu zan cika miki gidanki dasu,ba zaki bari kowacce tayi hidimar mijinki ba,ba kuma zaki sakar musu hidimar gidanki gaba daya sai yadda sukaso suyi ba,munsan aminatu muna da tabbaci akan tarbiyyarta,ba zata batamin yara ba,kuma na tabbatar baki da sakaci da zaki kasa sanya ido a kanta,ko yaya motsinta ya canza nasan in sha Allah zaki kula,zaki kuma tsawatar” shuru tayi tana dan gyada kai,komai yayi wato yana sane,yana kuma da hujja akai

“To Allah ya zaba abinda yafi zama alkhairi”

“Ameen ya hayyu ya qayyumu” ya fada cikin nuna kulawa.

Sai da ya ajjiyeta a qofar gidan sannan ya miqa mata key dinta yana jifanta da wani kallo,saika dauka sabon saurayi da budurwa ne

“Drivernki ya gama aikinsa ranki ya dade” dariya ta tsuntsire da ita

“Godiya nake,zan ninka maka salary dinka”

“Da kuwa kin kyautawa dan marayan Allah” ta girgiza kai tausayinsa yana dan tabata

“Allah ya jiqansu ya kyauta makwancinsu ya kyauta namu zuwan”

“Ameen ya Allah,Allah yayi albarka” ta amsa da ameen ya fita a motar yana gaya mata zai qarasa gidan suraj da yake basu da nisa,idan sun shiga wata sabgar yasan zata iya maida kanta gida,idan kuma ya dawo da wuri sai ya maidata

“Koka maidani dawowa zakayi,kasan dai kwanan waye ai” harara ya balla mata,tayi kamar bata gani ba ta wuce ciki tana qunshe dariya tana riqe da hannun affan da ya fara koyon tafiya,wannan yasa ta dinga takawa a hankali cikin kula da takatsantsan.

Tun daga qofar gidan jama’a ne,ta dinga gaisawa da mutane sunayi mata sannu saboda ganin yadda tayi nauyi sosai da uban ciki a gaba,yan mata matan suka daukar mata affan din suka kutsa cikin gidan dashi ita kuma ta tsaya tana ci gaba da gaisawa da mutane.

Hafsat din na tsakar gida anata rabon tuwon sauka,gaba daya ba cikin sukuninta take ba ganin yadda su mimi suka shiga sabgarsu cikin mutane,ko ta kanta basayi,yaran sunyi fes dasu sunyi haske sunyi qiba

“La la la,da gani babu tambaya wannan yaron sir abbas ne” wata qanwar mijin yaaya bara’atu ta fada bayan an shigo da affan ciki

“Tubarkalla ma sha Allah,yaro ya debo ruwa biyu,miqomin shi na ganshi” ta miqa hannu tana karbar affan dake fidda qamshi cikin navy blue din jeans da shirt dinsa.

Sosai maganar taja hankalin hafsat,gabanta ya fadi ta waiwaya tana kallon yaron dake da yawan fara’a,abinda ya qara masa farinjini kenan,saita dauke kanta wani abu yana tsaya mata a wuya,shi da babansa sukazo lo shi kadai?, indai kuwa shi da babansa ne lallai abun abbas qara ta’azzara yakeyi,har yazo bauchi amma bata da mutuncin da zai gaya mata yazo din?.

Bata gama wanann taraddadin ba widad ta danno kai,kamar kunna fitila cikin duhu haka ta haska gurin,da kyakkyawar shigarta me aji,dama tunda can din ita gwanar iya dressing ce,tunda quruciya ballantana yanzu data mallaki hankalin kanta,wata lafiyayyar atamfa ce a jikinta wadda tafi kama da material.

Suna hada ido gaban hafsat din yayi Wani mummunar faduwa,faduwar da sai data rufe idanunta don tanajin sautin bugun zuciyarta har kunnenta,kamar ciki fa take gani a jikin widad din,ciki fa,cikin ma tsoho?,saita miqe tana laluben hanya,wanda banda Allah ya kare tayi hanzarin dafa bango da tuni ta timu a gurin ta fadi.

Ba wanda ma ya kula da ita suna yiwa widad din maraba,kowa na qoqarin mata godiyar alkhairin da ya samu wannan karon daga wajen abbas din,wanda da yawansu sun tabbatar widad din ce sila,hakan yake kuwa,a wannan karon tayi shirin karbar soyayyarsu ne gaba daya,ribar kasuwancinta ta raba biyu,rabi ta dinga qarawa kowa akan abinda abbas ya saba bayarwar,har sai da suka qare,ita da fahad sukayi,batasan bakinsa bai iya shuru ba sai daya gaya musu,saboda shidai abun mamaki ya bashi,don koda wasa bai taba ganin hafsat din tayi musu haka ba,saidai tayi qoqarin ragewa ma.

Mayafi da takalminta ta dauka ta sulale sai gidansu,tsananin bacin rai yasa da tashin hankali yasa ta manta da batun daukansu mimi da jiran zuwan abbas tayi masa kwance kwance ya bata yaranta.

Tana shiga gidan ta dora hannu aka ta sakama maman nasu kuka,tayo wajenta hankali tashe

“Wani cikinne da ita umma na shiga uku,ta kusa haihuwa fa?”

“Ina fatan bakiyi wannan haukar a gabansu ba ko?” Ta fada cikin taraddadi,ta jinjina kai kawai don ta kasa cewa komai

“Shikenan tashi muje ciki” yunqurin miqewa tayi amma sai jini ya soma bin qafafunta,ta fidda idanu waje ta qwala qara tana fadin

“Wayyo Allah!…..cikina umma” sai kuma tayi baya luuuu ta sume umman tata ta tareta cikin tashin hankali.

Kai tsaye asibiti suka wuce da ita,bayan an basu gado anyi gwaje gwaje aka tabbatar da zubewar cikin jikinta,kamar zatayi dan qaramin hauka koma ace qaramin haukan ta dinga yi a asibitin,har sai da haushi ya kama ‘yan uwanta.

Ta ciwa cikin jikinta buri sosai,tasan abbas din da matuqar son yara,ta gama tsara yadda zai zame mata makamin da zata yaqi abbas ta kuma dawo dashi tsundum cikin rayuwarta.

Ba abinda abbas din baiyi ba na hidimar asibitin,hatta da ruwan da yan dubiya zasu sha bai bari kowa ya siya masa ba,ko dama can shi din tsayayye ne,baya dorawa kowa lalurar iyalinsa.

Ranar da aka sallameta ranar suke komawa bauchi,don haka duk wani plan dinta ya gama rushewa,umman nata tace kada ta damu,ta bari ta gama jinin biqin nan,sai su shirya ma komai da kyau.

********Shirin haihuwa sosai abbas yake yiwa widad din,siyayya yakema twince din da basuzo duniya ba kamar ba gobe,abun yazo masa akan gaba,saboda wani irin budi yake samu sosai,harkokin kasuwancinsa da yake gudanarwa a gefe kamar ana musu yayyafin alkhairi,haka ta fannin aikinsa,ya tsare gaskiya da amana,hakanan koda cikin yaransa ya kamaka da laifin karbar cin hanci ko rashawa to ka kade,dukkansu sun sani kuma suna kiyayewa dokokinsa.

Already likita ya gaya mata,tana cika watanni takwas to zata iya haihuwa daga sannan,kasancewar cikin twince,kuma ba haihuwar fari bace,don haka kullum abbas din cikin shiri yake,tayita dariya saboda yadda yakeyi din,kamar lokacin za’a fara yi masa haihuwa.

Ranar da zaije bauchi weekend kamar kada ya tafi,tace sam sai yaje,watansa guda kenan baije ba saboda cunkoson aiki anan katsinan,hakadai ya tattara ya tafin ya barta da aminatu da yasa akaje aka dauko mata ita kafin ya wuce,sai da ya dawo sannan hankalinsa ya kwanta.

********Tun kafin su gama cin abincin dare bayanta da mararta ke ciwo,amma take daurewa tana cijewa,suna gama cin abincin tasa aminatu ta dauki affan suka wuce dakinsu,sai itama tace kwanciya zatayi,don bayan sun gama cin abincin fita ta kama abbas din ta gaggawa,don haka suka rufe ko ina,yana da key din kowacce qofa tasan idan ya dawo zai bude.

Tashinta uku xuwa wani irin fitsari da yake takura mata,a zuwa na hudunne ta durqushe a bakin toilet din tana riqe da mararta da bayanta saboda wani mugun murdawa da tayi

“Ya hayyu ya qayyumu bi rahmatika astagis” ta dinga maimaitawa,sai ta koma ta zauna sosai a wajen.

Tun a can yaji jikinsa bai bashi ba,don haka ya katse meeting din,yabar mataimakinsa yace su qarasa,kome ake ciki su gaya masa.

Yana buda qofar nishinta ya fara ji,a rude ya qaraso inda take yana tambayarta,amma babu baki,sai kawai ya fara sauko da kayan haihuwar data hadasu jiya jiya ya fidda cikin mota,ya kamata ya kaita mota,ya qwanqwasa dakinsu aminatu ta bude,ya gaya mata su kulle ko ina su kwanta,ya bata dukka keys din na gidan yace zasu asibiti,hankalin aminatun a tashe tayi musu addu’a ya fice.

Kafin su isa ya kira daya daga cikin juniors dinsa,suka sameta a asibitin,bayan an dubata aka wuce labor room da ita.

Addu’ar data dinga yi ba kadan bace,a wannan karon duk yadda ta zata ba haka bane,ana kiraye kirayen sallar asuba lokacin da abbas ya wuce masallaci cikin hukuncin ubangiji ta haife kyawawan twins dinta dukka maza.

Yana kuma idar da sallar kira na shigowa wayarsa,ya daga yana sauraren bayanin da ake masa,tafiyar gaggawa ce ta taso musu shida matimakinsa da wanda abbas din ke bi,shine matsayar tattaunawarsu ta jiya,qarfe shida na safe,don dole ba yadda zaiyi haka ya amsa,don a qa’idar aikinsu ba sabawa umarni,ya baro masallacin yazo ya tarar da alkhairin da Allah ya saukar masa a wannan sassanyar asubar,baki da dukka zuciyarsa sun gaza daina furta godiya ga Allah,yaran kawai ya samu gani suma a gaggauce,haka yabar asibitin cike da kewar yaran da kuma mamarsu.

Tun a hanya ya buga waya ya gayawa dukkan wanda ya dace ace ya sani,daga danginsa zuwa nata,gab da zai shiga gida ya kashe wayar don ya samu ya shirya,bai kunna wayar ba sai da suka dauki hanya.

Yana kunnawa hafsat ya fara kira don ya fita hakkinta,ko basa tare indai zaiyi tafiya ya saba yana sanar da kowaccensu,bayan ya gama gaya mata tafiyar ya dora mata da batun haihuwar.

Uffan kasa cewa tayi,saboda wani qaton abu da ya toshe mata qofofin maganarta,twince?,to maza ko mata?,ko Mace da namiji?,kai koma meye yarinyar ta haifa itakam ta shiga uku.

Shurun da yaji yayi yawa sai ya mata sallama kawai ya katse wayar,ya amsa kiran yaaya bara’atu daya shigo masa.
[25/05, 1:45 pm] +234 810 324 4136: *H U G U M A*
*Arewabooks:Huguma*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)

Back to top button