A Rubuce Take Book 2Hausa Novels

A Rubuce Take Book 2 Page 29

Sponsored Links

Part 2
Page 29

A nutse ta bude k’ofar toilet din ta fito daure da babban towel fari sol,lallausar farar fatarta mai santsi da sheqi tana ta daukan idanu.

Gaban dressing mirror din dake dakin ta isa,ta ja kujera ta zauna tana kallon fuskarta a ciki,gaba daya jin ranta da jikinta takeyi babu dadi,fuskarsa ke gilma mata cikin idanuwanta,sam jikinta bai bata ba,ta kasa nutsuwa gami da gamsuwa da wannan tafiyar da ya qirqirar mata bagtatan lokaci guda,tana tsaka da hidindimunta,tun daga yanayi fuskarsa da kuma yadda ya dinga tuqi daga bauchi zuwa katsina takejin kamar ba abbas dinta ba,tabbas akwai abinda ke faruwa,akwai wani muhimmin abu dake gudana,tayi tunani har babu iyaka,ta laluba dalilin tas tun daga randa ya sanya qafa ya fita daga gidan zuwa dawowarsa da kuma isowarsu katsina……tayi zagaye cikin tunani da abubuwan da suka wanzu kaf! Ta kasa gano abu guda daya farun.

A iya saninta sun rabu suna masu kewa da kuma shauqin juna kamar ko yaushe,hakanan koda safiyar ranar sun jima ita dashi akan waya suna hira,wata irin hira irin wadda ke fallasa sirrin zuciyar masoyi zuwa ga dan uwansa,yana ta mata qorafin a takure yake acan din tare da mita tana lallabashi tana kuma masa dariya,har suka rabu kyawawan kalamai ne bisa fatar baki da zuciyar kowannensu,to amma me ya canza hakan?

“AKWAI WANI ABU” ta fada murya qasa qasa tana motsa tausasan lips din bakinta tare da zare idanunta daga kallon da take qarewa fuskartata,ta dauki lotion dinta mai taushi da qamshi ta fara shafawa fatarta cikin kasala taraddadi da kuma damuwa.

Duk bayan wasu mintuna saita kalli wayarta dake gefe tana tsammanin kiransa,saboda ta sani haka suka sabarwa juna,duk inda zashi cikin nigeria….. matuqar tafiyar mota zaiyi itace abokiyar hirarsa har ya isa inda zashi,idan kuma hakan bata kasance ba…..zaiyita kiranta har ya isa din,amma wannan karon ko gilmawar miscall dinsa bata gani ba bare kiransa,a qididdigen da tayi a yanzun kuma, tabbas koda baije gida ba yana gab da isa

“Waishin meke faruwa?” Ta sake jefawa kanta tambayar wata irin damuwa tana tabata tun daga qasan zuciyarta.

Cikin dauriya ta shirya kanta cikin doguwar rigar atamfa,ta fidda ainihin kyanta da surarta sosai,duk da yanayin da take ciki sai data tsaya gaban mudubi ta kalli kanta,lokutta da dama takan dubi kanta da kanta tana tuna WACECE ITA A SHEKARUN DA SUKA SHUDE,a yanzun sai taga kamar ba ita ba…..komai yana zuwa yana shudewa da wani irin sauyi mai ban mamaki.

Lausasan slippers ta zurawa qafarta,sannan ta isa bakin qofa ta kama handle din ta bude tabi siririn corridor din da zai sadaka da ainihin falon gidan.

Tun bata qarasa ba ta hangeta zaune cikin falon,halittace mai girman matsayi a wajenta,halitta dake sahun farko cikin halittu mafi soyuwa a wajenta,a duk lokaci irin wannan da zatayi balaguro ta taho takanas saboda kasancewa da ita…..duniyarta kan cika da farinciki,takanji a duniya yanayi irin wannan bashi da tsaara a wajenta.

A jikinta taji tahowarta,saita dauke idanunta daga kan tv din da take kalla ta maida kanta,kusan lokaci daya suka sakarwa juna murmushi,ta kuma rigata magana

“Wannan nauyin wankan naki dai yana nan,affan ya fara kuka har sai da aka fitar dashi” cikin karaya da rauni da takeji cikin gangar jikinta da zuciyarta ta qaraso dab da ita ta zauna,tana shirin amsa mata…..kamar me kiran yana jiran dai dai lokacinne kira ya shigo wayarta,a hanzarce ta daga wayar tana duba me kiran, zuciyarta cike da fata da burin ganin wanda ranta ke darsa mata.

Batasan sanda murmushi ya subuce mata ba hadi da fitar siririyar ajiyar zuciya ba

“Ina zuwa” tace da mommie,ba zata iya amsa wayarshi a gabanta ba,ita kadai tasan hottest words da suke gayama junansu,kuma muddin aka samu mishkila mommie taji daga ita har shi sun gama tafka abun kunya.

Kai tsaye dakin ta koma,ta samu gaban madubin data tashi dazu ta zauna tana yunqurin daga wayar

“Assalamualaikum” ta fada a shagwabe tana karyar da wuyanta gefe,abu mafi soyuwa kenan da tasan yana so tattare da ita,har yau kallonta yake cikin madubin da yake kallonta shekarun baya da suka shude,bata canza a idanunsa ba

“Wa’alaikumus salam” mummunar faduwa gabanta yayi daka jin sautin muryarsa me taushi da sanyi da yake mata magana da ita koda yaushe ta juye zuwa wata iriyar murya,irin muryar da yake magana da cirminals a yayin da aikinsa ya biyo ta kansu…..irin muryar da yake magana da juniors dinsa a yayin da suke hurumin aiki……irin muryar da yake magana da ita a duk sanda ya shiga qololuwar bacin rai da fushi,muryar da bata taba jin yayi mata magana da ita ba.

Kowacce gaba ta jikinta tayi sanyi,tayi namijin qoqarin tattaro nutsuwarta da juriyarta tace masa

“Ka sauka lafiya?,ya kaje gida”

“Me yasa zaki aikata min haka?” Ya fada muryarsa tana ninka ta da kaushi da ban tsoro,daga cikin wayar tana iya jin hucinsa,da alama a matuqar bacin rai da kuma fusata yake, tambayar tasa kuma ta dilmiyar da ita kogin tunanin ina ya nufa ne?,kafin ta lalubo amsa kunnuwanta sun fara isar mata da saqo mafi muni cikin rayuwarta,daga bakin halitta mafi soyuwa a gareta

“Ashe haka kike?,ina miki kallon saliha ashe mayaudariya ce ke?,maciyar amana ce?,macuciya ce ke?,na baki dukkan yarda,na damqi miki rayuwata ashe zaki wasa da rai na da lafiyata?” Wani irin tashin hankali ne ya sauko mata,me abbas ke fada ne

“Me nayi maka?,abban affan me ya faru?,kasan me kake fada kuwa?”

“Na sani!,nace miki na sani, tsahon yaushe tsahon kuma wanne lokaci kika dauka kina cin amanata kina kuma ha’intata WIDAD?” Kasa zama tayi,ilahirin jikinta ya dauki tsuma,sai ta miqe tsaye qafafuwanta suna rawa

“Kana cikin hankalinka kuwa abban affan?,a ins kake yanzu?” Ta tambayeshi don ta tabbatar da cewa he’s safe,ba gusar masa da hankali akayi ba yake gaya mata hakan

“Har kinyi wayon fara bin maza?,ki kwana a hotel?,hakan bai isheki ba har sai kin dauko gardi kin kawomin gidana?,kin kuma kaishi har gadona na sunna widad?,wane laifi na aikata miki haka dana cancanci irin wannan hukuncin?” Yayi maganar ta qarshe muryarsa a wani mugun karye,saidai zafi da kaushin nan suna nan taf a muryarsa

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” ta fada a bayyane,qafafuwanta suka hau rawa,gabanta yayi wani irin bugawa da zuciyarta ta hasko mata abinda yake magana a kai.

“Hotel kuma?” Ta tambayeshi muryarta na wata mugun rawa,irin rawar dake bayyanar da zallar daburce wa a sanda aka ritsaka bisa wani abu na rashin gaskiya

“Bakije bane?,ko zaki shiryamin irin qaryar da kika saba?”

“Naje,tabbas naje….amm……”

“Ya isa!!!!” Abinda ya fada kenan a tsawace

“Abinda nakeson ji kenan kuma naji,kije ke da Allah,bazan taba yafe miki ba,amanata da kikaci ubangiji ne kawai zaiyimin sakayya,Allah ya isa ban yafe miki ba!!!” Kit! Wayar ta katse

“Abban affan,daddy!!!” Ta fada a gigice,saidai tuni ya katse layin

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” ta sake maimaitawa jikinta na wani irin kyarma tana yunqurin binsa,saidai a take kamfanin sadarwa suka gaya mata is switched off,saita saki wayar ta sulale a wajen tana sakin wani azababben kuka,wani abu mai tauri da zafi yana tokare mata qirji.

“Waye ya ganta?,waye ya gaya masa?,waye???” Ta soma nacin gano daga inda maganar ta fita

“Hafsah” taji an bata amsa daga can tsakiyar zuciyarta,kukanta ya tsaya cak na wasu sakanni,sai ta sake rushewa da kukan tana jin kanta yana sara mata,tana son miqewa amma ta kasa,idan tayi kamar zata tashi sai jiri ya maidata ya kayar,a haka aka turo qofar dakin,ta daga idanunta da taji kamar basa dauko.mata hoton komai da kyau ta tsurawa qofar idanu tanason tantance mai shigowar.
[20/05, 8:46 am] +234 810 324 4136: *H U G U M A*
*Arewabooks:Huguma*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)

Back to top button