Arubuce Ta Ke Hausa NovelHausa Novels

Arubuce Ta Ke 51

Sponsored Links

Page 51

Tun tana wanke wanken na marmari har ta soma ji gaba daya hannayenta sun fara mata zafi,sannu a hankali gajiya gaba daya ta saukar mata,hannunta yayi jazur saboda wankin kwanukan da kuma zafin detergent,tunda tunda uwarta ta haifeta bata taba wanke wanke mai yawan haka ba,da qyar ta samu ta kammala,ta gyara daurin dankwalinta daya sabule ta baro wajen.

Babu kowa a falon,bama alamar suna nan,hakan yasa ta wuce zuwa sashenta kai tsaye,bayan ta ciro key din da ya bata a qaramar purse dinta.

Idanu a narke ta shiga sashen nata,sai zuciyarta ta karaya,taga kamar zataga latifa,ta tuna wayon data yi mata ranar da zasu bar bauchi,komai yana nan a killace yadda latifa ta barshi,ba wani datti sai ‘yan qananun qura dake shiga wajen sanadin babu giftawar kowa,ta zube saman kujera tana share qananun qwalla,itakam tana jin kamar tsanarta akayi,kowa yana gida banda ita?,hakanan ta gaji da zaman,ba motsin kowa cikin gidan,ba alamun kuma zata samu wani abun da zata ci,ta miqe cike da shegen tsoron nan nata cikin sanda ta isa kitchen,ta duba store dinta ta fidda indomie,cikin tsoro da fargabar kada ta cabe irin ta rannan ta kunna wuta ta dora.

A kitchen din ta zauna harta dahu,ta juye a plate,tasa fork ta debo ta dandana,sai murmushi ya subuce mata,tayi dadi fiye da yadda ta zata,har abun ya burgeta ita kanta,ta dauki plate din da hanzarin tayo hanyar falo,tana fitowa sai tayi turus da plate din a hannunta,ta manta ba’a kaduna suke ba,ta yaya zata wuce momy hafsat dake gargadinta koda yaushe ta tafi dakinsa?,saita koma ta zauna jiki a salube,ta sanya cokalin ta fara diban taliyar tana ci,ko TV ta kasa kunnawa saboda tsoro,sai taji kamar ana tafiya daga bayanta.

Duk da ba’a nutse take ba amma hakan bai hanata jin dadin taliyar ba da gaske,tana ci idanuwanta suna mata nauyi,don haka kafin ma ta kammala bacci ya kwasheta a wajen,ko hannu bata samu wankewa ba.

Daga yanayin da ya samu gidan yasan cewa babu wani abinci da zaya samu,don haka koda aka idar da sallar magariba bai shigo gidan ba sai da akayi isha’i,daga nan kuma ya dauki motarsa ya wuce yayi musu takeaway,bai bi ta halin hafsat din ba,don ko kaffara bazaiyi ba yasan ba wanda ya qoshi a gidan ciki harda yaranta,don haka ya hado dasu.

Afalo ya sameta ta kammala mopping,tana ta fada dasu nawwara,fadan da bashi da dalili,yasan dai duka bazai wuce akan aikin sharar daya sanyata ba,yaran suka masa oyoyo ya daukesu yayi hugging dinsu,sanna ya ajjiyesu hade da ledar hannunsa yana cewa

“Bari naje na dawo muyi dinner ko?” Suka daga kai cikin zumudi da jin dadi.

“Ina kuma zaka je?” Ta tambayeshi cikin d’ar d’ar ganin ya kama hanyar fita da leda daya,waiwayowa yayi ya dubeta,bai bata amsa ba yaci gaba da takawa

“Kawo nakai mata ka zauna kai kaci naka abincin” ta furta tana matsowa,saidai kafin ta iso ma ya fice abinsa,baisan me yake damun kanta ba,ita idan tayi laifi ma bata yarda tayi bare ta kamo hanyar gyarawa.

Sau hudu yana knocking yaji shuru,sai kawai yayi amfani da spare key dinsa ya bude ya shiga.

Sassanyan qamshin turarukan da latifa ta tsuma sassan dashi har yanxu yana nan,kamar ma a yanxun ake turara wajen,turaruka masu tsada da kama jiki na asalin shuwa.

A yashe ya hangeta saman carfet ta cure waje daya,ya taka a hankali zuwa cikin falon,ya dauki remote ya sanyin ac din,ya ajiye remote din ya maida dubansa gareta,ko pillow babu a kanta,ya ajjiye ledar a hankali a gabanta,sannan ya durqusa yana tunanin yadda zai gyara mata kwanciya.

Pillow din ya miqa hannu ya dauko,sannan ya zauna sosai,ya sanya hannuwansa duka biyu ya dagota,sumar kanta data baje ta watsu saman baby face dinta,sosai pink lips dinta suka dauki hankalinsa,bai taba kallonsu da kyau irin yau ba,wani irin sexy lips masu daukan hankali,girarta da suka kusa hadewa da juna ta sake qawata fuskarta da kyau.

Ji yayi sunyi mugun kusanci da juna,kamar wanda aka sawa electric shock ya saketa da sauri,ta farka a firgice sanadin sakinta da yayi,jinta kusa da mutum kuma ya sake sakawa ta tsorata da gaske,saboda tasan dai already kafin ta kwanta ta rufe qofarta.

Ihu ta sanya sosai a tsorace,yasa hannunsa da sauri ya rufe mata bakinta yana cewa

“Ke….meye haka,it’s me” jin muryarsa ya sake kad’a mata cikinta,ta tattara qarfinta tana tureshi,dai dai lokacin da hafsa wadda ta saka zama ta biyo bayansa ta turo qofar falon da sauri ta shigo.

Da yadda za’a fadi yadda taji a lokacin ya wuce haka,gaba daya ji tayi wani tashin hankali ya rufto mata,widad din a jikin abbas dinta?,sam batasan gabansu take nufa ba,har sai data isa,gaba daya zuciya ta gama gaya mata ta fincikota daga jikinsa ta rufeta da mugun duka ne,saidai tana isa din abbas din yana buda hannayensa widad din ta fice tana sakin dan qaramin kuka,gaba daya a tsorace take, jikinta sai rawa yakeyi tana kallon fuskar hafsat wadda ta ritsata da idanu,hantar cikinta ta gama kadawa kamar wadda aka kamata da kwarto,yanxun me zata cewa mummy?,duk yadda take kiyayewa da yin takatsantsan yau ta kamata a jikin wani.

Mugun kallon data watsawa widad din ya sanyata cikin sauri da kuma rawar murya tace

“Wallahi mummy ina cikin bacci,bansan ya shigo ba….” A nutse abbas dake tsaye ya waiwaya ya kalli hafsat din,da sauri ta dauke rikitaccen kallon da takewa widad ta maida ga abbas din cikin rudewa,yarinyar tana son balle mata liqin da tayi,sukayi kallon kallo na sakanni,kallon data hangi ayoyin tambaya masu yawa a idanun abbas din,ta hadiye wani yawu mai tauri,cikin qasa da second goma dabara ta fado mata,ta maida dubanta ga widad din

“Ni Matsalata dake shegen tsoro,kinsan dai gidan nan babu wanda zai shigo,dagamu sai mu,ki dinga addu’a idan zaki kwanta kinji” tayi maganar cikin karyar da harshe,saita matsa tana zaunar da widad din sosai,amma qasan zuciyarta a mugun matse yake,kada fa ya zamana abbas ya fara latse d’iyar mutane,ta miqe sosai ta tsaya tana dubansa

“Abban mimi…..ka dinga haquri,kaga dole ayi mata uzuri,akwai quruciya sosai a tare da ita” lumshe idanunsa yayi bisa fuskar hafsan,shi baima gane abinda take fada ba,gaba daya bugun zuciyarsa ne yake neman sauyawa,saiya maida dubansa ga hafsat din dake matsar qwalla

“Ga dinner dinki nan,ki taso ki rufe qofar” ya furta yana juyawa cikin mutuwar jiki,sai hafsat ta biyo bayansa tana cewa

“Kisa key ki rufe qofan falon kinji,saiki rufe ta bedroom din ma,sai da safe”

“To Mommy” ta fada,cikin ranta tana jin tazarar son da hafsat din ke mata abbas din bai kama koda kwatarsa ba,haka tasa muqulli ta rufe qofar sannan ta dawo falon,tsoro ne fal ranta da zuciyarta,tana jin kamar ta bisu,amma kuma haushinsa takeji,don me zai dinga taba mata jikinta,a gurguje ta tattare komai ta wuce bedroom dinta,shima sai data saka key ta rufe da kyau sannan ta canza kayanta zuwa na barci ta haye gado,yau ko.wankan ma bata tsaya yi ba.

Ta jima tana juyi ciie da tsoro, duqunqune cikin duvet,wannan gidan yafi na kaduna girma,hakanan gidan kaduna dakunan kusan a kusa da juna suke,tana jin kusancin abbas dake dakinsa a jikinta,sabanin wannan da kowa bangarensa daban,cusa kanta ta sakeyi cikin duvet din,hancinta na zuqo mata qamshin turarensa,wanda ya kama rigar jikinta radam,sai taja tsaki,haushi na cika mata zuciya

“Dan iska” ta fada tana murguda baki.

**********washegari bata bude qofarta ba har sai dasu mimi sukazo suna buga mata,taji dadin ganinsu,suka dinga wasansu a falonta,ita kuma ta shiga kitchen ta dafa musu jallop din taliya.

Da dan gyare gyare cikin girkin,to amma da yake ba wani cimar kirki yaran suke ba sai abincin ya musu dadi sosai,suka zauna sukaci kaman ba gobe,itama cikinsu ta zauna,sunaci suna surutu tana tayasu,sai da suka qoshi sannan mimi tace

“Mummy ce ta aikomu,tace kiyi mana wanka,bacci suke wai basu tashi ba” bata ji komai ba,don zamanta da yaran ita dadi yake mata,sannan ita kallon hafsat din take kamar anty deena,don haka ta kunna heater,ta tara ruwa mai dumi sosai,tayi musu wanka kuwa fes,ta shafa musu manta sannan ta dubesu

“Ku karbo kaya wajen mommy din a saka muku” da gudu suka fella suka fita,saidai basu jima ba sai gasu sun dawo da kayansu a jikinsu

“Mommy tace kizo” jikinta ta kalla,da da hali wanka zatayi kafin ta fita din,don gaba daya bata jin dadin jikin nata,saboda bata samu yin wanka jiya ba,amma kafin ta gama tunanin maganar mimi ta katse mata

“Yanzu yanzu wai tace” mayafin doguwar rigarta ta zura tabi bayansu suka fice.

Sallamar widad din ta sanyata ninke kudin da take irgawa ta daga bayan pillow dinta ta xubasu tana amsa sallamar,kudin da abbas din ya bata ne ta bawa widad din,anyi rasuwa yana sauri ya fita bai samu leqata ba.

Sanda ta karba kudin kamar zuciyarta tayi tsalle ta fito,ita din gotai gotai da ita zai raba musu kudi dai dai da yarinyar da ta haifeta kota kusa haifar ta?

“Badai ya fita din ba,meye abun damuwa” zuciyarta ta gaya mata,wannan ya sassauta fushinta,don tayi imanin sisin kwabo ba zata bata ba a cikin kudin.

Har qasa ta tsugunna ta gaidata kamar yadda ta saba,saita koma gefe tayi tsaye a darare,ba tare data kalleta ba tace

“Kitchen zaki shiga ki gyaramin,idan kin fito saiki fara da falo, bedroom dina kuma idan na gama abinda nakeyi zan miki magana saiki gyarashi,zan gyara dakin yaran da kaina” ta qarashe maganar tana debe kudinta,sannan ta wuce dakinta abinta.

Hakanan widad ta zage ta cashi aikin da zata iya cewa bata taba kamarsa ba,ta gyara kitchen tayi wanke wanke,ta dawo falon ta gyarashi tsaf,sannan tayi knocking qofar bedroom din.

Tana kwance abinta daga saman gado ta amsa da

“Shigo” a darare ta shigo da sallama,a kashingide take tana chart

“Mommy na gama”

“Gyara abinda ya samu,idan na tashi kya gyara gadon,ko na gyara da kaina” cikin d’ararewa ta fara kwashe tarkacen dake zube a qasan dakin tana hadesu waje guda.

KI KULANI miss xoxo

DAUDAR GORA Billynabdul

RUMBUN K’AYA hafsat rano

IDON NERA Mamuhghee

A RUBUCE TAKE huguma

_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_

_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

0022419171
Maryam sani
Access bank

Saiku tura shaidar biya ga
+234 903 318 1070

*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
09166221261

*Al’ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
+227 96 09 67 63

*Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)

Leave a Reply

Back to top button