Author: Novels

  • Arubuce Ta Ke 77

    Arubuce Ta Ke 77

    Page 77

    Bedroom slippers dinsa ya zura a hankali ya sauko daga gadon da nufin zuw kitchen ya samo lemon tsami ya matse yasha ko zai samu relief,ya isa bakin qofar ya dora hannunsa kenan da nufin bude qofar yaji an rigashi.

    Kamar wadda aka jefo haka ta fado jikinsa ta koma qanqameshi sosai tana sakin kuka.

    Cak komai na jikinsa ya tsaya ya daina aiki na wucin gadi kafin qwaqwalwarsa ta koma bakin aiki

    “Mage ce ta shig uncle,ni Allah a koreta daga gidan nan” ta fada cikin kukan shagwabar daya qarasa qwace dukka wani saiti da yayi saura tattare dashi,numfashinsa ya fara wani irin kai komo,babu abinda yake ji a tasa lallausar fatar sai tudun jikinta tako ina,tare da dumi da santsin tata fatar kasancewar jikinsa babu riga saboda wani mugun zafi da yake ji duk da akwai cikin dakin,hancinsa cike da wani tattausan qamshi mai tafi da hankali,irin scent din da bai taba jin irinsa ba,yayi mutuwar tsaye,ya zama kamar wani zane,hatta da gashin kanta daya maqale a habarsa yake isar da saqon qamshin hair mist dinta ya kasa cireshi.

    Shige masa ta sakeyi jin kukan kamar dakin yake matsowa,abinda ya sanya gaba daya jikinsa daukan rawa kamar wanda ake kadawa gangi,dukka wani sanin kamata nashi ya gushe,abu daya kwanyarsa ke karanta masa,ya kasance da ita,saiya zareta a hankali daga jikinsa ya sulale ya duqa saman gwiwoyinsa yana qare mata kallo.

    Komai na jikinta ya bayyana kansa,komai yana tsaye yadda zai dauki hankali fiye da kima,wata irin sura mai matuqar fusgar hankali da gusar da tunanin me tunani,wata irin halitta da idanuwansa basu taba ganin irinta ba.

    A lokacin gaba daha tsoron magen ya rufe mata ido,matsawar da yayi daga jikinta saita dinga jin she’s not secure,magen zata iya shigo ne kawai ta haye jikinta,don haka hawaye ya balle mata,tana ganin kamar guduwa yayi

    “Uncle” kafin ta qarasa fada ya bude hannayensa,bata bata lokaci ba ta isa jikinsa ta fada,yayi mata wata wawiyar runguma kamar zai maidata cikinsa,ya tattaro dukka qarfinsa ya miqe saman qafafunsa,ya dauketa cak cikin jikinsa ya azata saman gadon dakin.

    Ko ina na jikinsa rawa yakeyi,da qyar ya laluba makunnin ac dana fitilar dakin ya kashesu,duhu ya mamaye dakin,babu abinda yayi saura sai siririn hasken dake ratso labule daga wajen farfajiyar gidan,ya kuma sassauta kaifin duhun dake dakin.

    Cikin jikinsa yayi mata kyakkyawan masauki ya fara sansana kowanne loko da saqo na jikinta yana jin kamar ya zuqe dukka qamshin,duk inda yakai hancinsa scent na daban yake bayarwa,irin wannan yanayin……irin wannan abun ya jima yana mafarki yaji daga jikin hafsat,amma tun satin farko na amarci bai sake jin hakan ba.

    Sosai ya haukace ya hautsine,ya koma real abbas dinsa dake bawa hafsat tsoro especially a lokaci irin wannan,widad dake da qarancin shekaru kuma batasan komai ba sai abun ya girmi tunaninta da kuma iyawarta,tun tana daukae ya lullubeta ne yana rarrashinta har ta gane wani karatu na daban yake mata,tashin hankalin da bata taba jin kamarsa ba ya sauko mata,ta kasa koda motsi bare ta zare jikinta,saboda ya cukukikuyeta tako ina,ya mata wani irin namijin riqo mai wahalar qwacewa,kiran sunansa ta dinga ji a jejjere,amma ko alamun muryarta baiji ba bare ya fuskanci magana takeyi,kansa da jikinta da yake sarrafawa kawai yake iya fahimta cikin duniyar daya shiga.

    Tako ina yayi mata riqon tsaurin da ba zata iya qwacewa ba,yayin da shi kuma yake jinsa a wata duniyar da baisan yadda zai kirata ba.

    Kuka sosai widad din keyi,irin kukan da ake kira na neman agaji da ceton rai,ceton da babu mai iya yi mata shi,tun tana ihu da iya muryarta har sautinta ya fara dakushewa.

    Duk da yanayin da yake ciki hakan bai hanashi karanto addu’ar nan da ma’aiki ya hori ma’aurata da karantata ba,sai yaji wata nutsuwa tana saukarwa qwaqwalwarsa,ya riqe fuskarta cikin tafukan hannayensa yana duban qwayar idanunta da suka bayyana tsoro da tashin hankali

    “Am sorry…..i love you” ya fada da wata shaqaqqiyar murya,daga haka ya fara neman hanyarsa zuwa maida widad din cikakkiyar mace kuma mallakinsa tahar abada,kamar yadda ya jima yana buri.

    Batasan yadda zata musalta azabar data ziyarceta ba

    “Ummmuuuuuuu…….”ta kirayi sunanta da wata shaqaqqiyar murya,wanda daga sannan ta fara daina gane komai.

    Sanda yazo gangara kuka ne ya subuce masa,ya qanqameta sosai kamar zai tsagata gida biyu,tabbas banda hankalinta ya gushe sai tayi matuqar ji a jikinta,ya kifa fuskarsa cikin gashinta,idanuwansa na fitar da wani hawaye yana sake riqeta sosai cikin jikinsa,a lokacin wani abu mai girma da qarfi ya sake dasuwa a tsakaninsu,a lokacin ya dinga jin a shirye yake ya tunkari kowa da komai a kanta,ta wafce wani tsagi mai girma a rayuwarsa.

    Kusan mintuna hudu sannan ya dawo hayyacinsa ya fara qoqarin rabata jikinsa da ita,yadda jikinta ya saki gaba daya a hannunsa yasa ya fahimci babu numfashi a gangar jikinta.

    Sosai zuciyarsa ta kada ganin irin yadda wajen ya baci da jini,ya zare ido qirjinsa yana harbawa,kada dai ace ya kashe musu yarinya ne?,la haula wala quwwata illa billa.

    Cikin wani mugun kuzari da diro daga saman gadon ya doshi qaramin fridge dake dakin,hannunsa yana rawa ya dauko ruwa mai madaidaicin sanyi ya balle murfin har hannunsa yana jin ciwo ba tare daya lura ba,ya dawo ya zauna cikin jinin yana jawota jikinsa,ya bude ruwan ya soma shafa mata,amma harya kusa rabin robar bata motsa ba,wannan ya tashi hankalinsa,saiya sona tuttula yana zuba mata sosai har cikin gashinta.

    Doguwar ajiyar zuciya ta saki,suna hada ido ta maida idanun nata ta rufe tana sakin kuka wanda ko sautinsa ba’a ji saboda tuni muryarta ta dakushe,ko ina na jikinta wani azababben ciwo yake mata,ba zata iya tantancewa ba,amma daga can qasanta tana jin azabar data zarta tako ina.

    Saman qafarsa ta kifa fuskarta,sai ya rasa da wanne baki zai lallasheta,sai kawai ya cusa hannuwansa cikin sumarta yana shafawa a hankali

    “Am sorry…..kiyi haquri…..na tuba”shine abinda yaketa fadi,a qalla sun kusa mintuna talatin sannan wani baccin wahala yayi awon gaba da ita,kafin sannan wani zazzafan zazzabi ya rufeta ruf,tausayinta ya cikashi fal,shi kansa yasan yayi barna ba’yar qarama ba.

    A hankali yasamu yazameta cikin lallabawa kamar me riqe da sabon qwai ya kwantar da ita sannan ya tula mata duvet,don a yadda take cure waje daya ya tabbatar sanyi takeji,don ba qaramin zazzabi bane a jikinta.

    Qasan shower ya tsaya ya sakarwa kansa ruwa ba tare daya damu da rashin duminsa ba,don shi kansa wani zafi yakeji ta cikin qashinsa,kamar wanda zazzabin cikin qashi ke shirin kamashi.

    Kamar wani zautacce haka yabar ruwan yana sauka a jikinsa,yakai qololuwar tunani,sai furzar da duk ruwan daya shiga bakinsa da yakeyi,bai taba yarda da maganar nan da ake cewa mata suna suka tara ba sai a yau,iya yau kawai….iya yau kawai amma ta aje masa wani muhimmin tarihi cikin rayuwarsa.

    Tsaf ya gama wankansa sannan ya fito ya dawo dakin,ya tsane ruwan jikinsa,yana yi yana waiwayenta yaga ko ta motsa,amma har ya gama ya zame zanin gadon bata sani ba,bai damu ya maida wani ba,haka ya koma saman gadon tsurarsa babu shimfida.

    Sanda yake qoqarin sake maidata cikin jikinsa don ya rage mata sanyin zazzabin ta farka,kuka ta sakar masa sosai,don wannan karon muryarta ta bude ba kamar dazu ba,ido ya rintse yana jin sautin kukanta kamar saukar ruwan dalma a zuciyarsa,ya matso dab da ita,muryarsa tayi wani irin laushi,kamar ba abbas usman tafida ba(idan kunga sunan mahaifi ya banbanta kuyi haquri,na manta ainihin sunan mahaifinsa dana ambata a baya),jarumin kuma jajirtaccen dan sanda

    “Kina buqatar wani a kusa dake,let me help you please” qoqarin tureshi takeyi da hannu,don ko muryarsa batason ji

    “Banaso,ka qyaleni,ai ba sona kake ba,shi yasa kayimin haka,saboda ka ganni qarama ka girmeni” duk da yadda hankalinsa yake a kanta da damuwa da yanayin daya sanyata a ciki saida dariya taso kubce masa,har yanzu dai…..har yanzu dai ba zata bar wannan sakalcin nata ba

    “Naji… Kiyi haquri,ki bari na taimaka miki,idan kinji sauqi saiki rama”.

    Kanta ta mayar ta kwantar a hankali ba tare data sake cewa komai ba,sai qwallar azaba kawai da take fitarwa daga idanunta,cikin d’ari d’arin kada tace aah ya sake matsawa kusa da ita ya sanyata a faffadan qirjinsa yayi mata rumfa,sai ajiyar zuciya ta kubce masa mai nauyi,ya dora habarsa saman lallausar sumarta data hargitse,hankalinsa nakan dukkan wani fitar numfashinta.

    Yadda zazzabin jikinta ke sake qaruwa ya hana masa runtsawa,akwai paracetamol a gidan,amma ko yaya ya motsa saita saki wani marayan kuka saboda zafin da radadi da jikinta yake mata,a haka kusan suka kwana yana gadinta,tana baccin rabi da rabi,tayi ta farka,bakinsa ya kasa hutawa da yi mata sannu.

    Da dabara ya samu yayi alwalar sallar asuba,ya hau gadon ya isa inda take,sai ya ranqwafa yana kallon fuskarta wadda ta fada sosai,ta kuma qara haske tafi fayau.

    Murmushi ne ya kubce masa,wanda tun daga qasan zuciyarsa ya ratso,sai a lokacin ya dan dinga tuna sunayen data dinga kira saboda neman agaji,ummu ta kiranyu har babu adadi,uncle muhsin,alhaji,latifa anty deena anty madeena harda mommynta,yau kam ya tabbatar kashinsa ya bushe,tabara ma tayi ta banza bare an tabota,saiya duqa a hankali ya hade tsinin hancinsu waje daya,take suka fara musayar numfashi,hakan kuma ya bawa danshin fuskarsa dama sauka a fatarta mai sulbi da taushi.

    A hankali taji yanayin numfashin da take shaqa ya canza,wannan yayi sanadin katsewar numfashinta,ta soma bude idanunta a hankali har ta budesu tar,basu sauka kuma a ko ina ba sai a tashi fuskar dake dab da ita.

    Da sauri ta maida idanunta ta kulle,sai taga kamar a sannan komai yake faruwa tsakaninsu,duk yadda yaso ta waiwayo ta kalleshi taqi,daga qarshe sai hannunsa ya miqa mata

    “Oya…. shikenan na haqura,taso kiji” shuru tayi kamar ba zata motsa din ba,sai kuma ta motsa a hankali ta miqa.masa zara zaran yatsunta ya kama ya dagata a hankali tana cije lebe,kasa zama tayi sosai saida ta karkace,bata ankara ba taji ya nemi gefanta ya zauna

    “Komai ya faru unexpected,abubuwan daya kamata na tambayeki kafin faruwar komai ban tambayeki ba,but now i will ask you…..ya ake wankan ibada?” Ta fahimci sarai abinda yake nufi,don tsohon karatune da suka jima da yinsa a islamiyya,amma sai taji tambayar tayi nauyi fiye da yadda zata jita a bakin kowa,sai tayi qas da kanta hawaye yana son saukowa.

    Ya fahimci da gasken gaske ya tabota yau,kuma hatta da ‘yan muslikancinta sun motsa,ya saki qaramin murmushi na gefan baki,sannan ya zamo qasa ya tsaya kan gwiwoyinsa,yasa hannunsa masu taushi da sukayi wani sanyi da batasan na meye ba ya riqe dukka hannuwanta yana kallonta

    “Ayimin afuwa widad din ummu…..a gayamin naji,saboda wani nauyi ne da yake kaina da ya zama wajibi na saukeshi” a hankali ta motsa qafarta,saita cije lips dinta ta gefe saboda yadda taji ta kamar ba’a jikinta,saita motsa bakin nata ta fara yi masa bayani daki daki.

    Idanu ya zuba yana kallon yadda dan qaramin bakinta ke motsawa yana fidda sautin siriryar muryarta mai zaqi,duk bayanin da takai qarshensa sai ya gyada kai,ransa yana sakeyin fari tas,yana kuma sake godewa Allah

    “Ma sha Allah, alhamdulillah” ya furta murmushi yana subuce masa,ta fadi komai dai dai babu wani gyara a ciki,sai ya tuna wasu shekarun baya kamar haka shida hafsat din,gyara da yayi mata ya kusa na rabin bayaninta,amma yau sai gashi yarinya qarama tasan wajibin dake kanta.

    Miqewa yayi a hankali yana fadin

    “Get up dear” ta tattara dukka dauriyarta ta miqe din tana runtse idanunta,saidai taku daya tayi ta gagara yin na biyu kuka sosai ya qwace mata,dukka qafafunta suka dauki rawa da ilahirin jikinta,gumi kuma ya fara yanko mata,zata koma ta zauna ya tarota zuwa jikinsa da sauri ya riqeta da kyau

    “Is okay,ya isa….ya isa,you will be okay in sha Allah,am sorry,nasan duk nine na jawo” ya fadi abinda yake da tabbacin zaiyi wuya bata fadeshi ba,ya karanci komai tsaf cikin idanuwanta,haushinsa ne fal da kuma bacin rai,yanzun kuma zai qara mata wani fushin akan wanda takeyi,don kuwa daukarta yayi cak ya wuce bandaki da ita,ya kuma fara rabata da kayan jikinta.

    Gaban rigar da tuni ya tashi a aiki ta riqe sosai tana hawaye,kai ya girgiza mata alamar a’ah fuskarsa a hade ba alamun fara’a,dole ta saki rigar,yasa hannu yana qarasa zameta daga jikinta,ya kuma jefata gefe, don tuni ta tashi daga sunan riga zuwa tsumma,zamewa tayi kawai cikin bathtub din tana rufe idanuwanta dake fitar da qwalla,itakam ya gama da ita,tasan ya gama lalatata,iya zafin da takeji kadai ya isheta amsa.

    Tana ciki ya dinga tara ruwa me dumin gaske,tun bai cimmata ba har ya fara ratsata,a lokacin tayi yunqurin miqewa amma ina tuni ya rigata,da wani irin zafin nama ya xare rigar jikinsa ya shige cikin bathtub din,ya kamata zuwa jikinsa ya riqeta sosai saboda ruwan ya ratsata.

    Tana jin zafin tana jin komai amma ta kasa katabus,saboda dukka wani qarfi nata ya tafi, kukan ma ta kasa,saboda hatta bakinta tana jin kamar shima ciwon yakeyi,eh….batayi qarya ba, don idan ciwon ma yakeyi ba mamaki, tsahon lokacin da bakin shagwabar tata ya dauka yana tsone masa idanu,a jiya sai daya fanshe dukka wani haushinsa a kansa.[3/18, 3:05 PM] +234 903 685 1413: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)
    *Arewabooks:Huguma*

  • Arubuce Ta Ke 69

    Page 69

    A idanunta akayi sallar magariba bataga gilamawarsa ba,akayi isha’i ma haka,sai jikinta ya bata lallai ciwon cikinsa ya tashi ne,indai kuwa hakanne babu inda zai iya tafiya dauko yarinyar,hankalinta taji ya kwanta,ta kuma sake abinta,gwara yarinyar ta kwana a gidan hajiyan akan ta dawo cikin gidan yana cikin wannan yanayin,ta sanshi sarai,tamkar mayunwacin zaki yake,haram ce kadai baya iya dosa a irin wannan yanayin,saita koma ciki taci gaba da lissafin kudinta da kuma sabgoginta.

    Ta riga ta gama saddakarwa,wannan ya sanya shigowar umar da fita da motar duka bata jisu ba,ta gama abinda takeyi ta dawo falo ta kunna kallo abinta,saurana abincinsa da bai cinye ba shi ta zubawa yaran sukaci abincin dare dashi,hakanan suka tsakura,saboda sun gaji daci,shi sukaci tun rana sukaci da babansu yanzu ma kuma gashi shi dinne,sunata wasansu tana chart, hankalinta ma baikan tv din,tana bawa anty ummee labari ita kuma tana cin dariya

    _shegiya,wannan mafa hanyar samun kudi ce a wajen mace bana wasa ba_ anty ummee ta gaya mata

    _wallahi a wani group wata hamshaqiyar hajiya ta bamu sirrin,ina nan ina zuba ido,idan ya gaji ya kawo kansa ya kuma biya price sannan a bude masa gate_

    Daga can anty ummee tana ta dariya,cikin ranta kuma tana gulmar hafsat din,sai kace wata hamshaqiyar mace,banda ma abin namiji,ai ita qoqarin abbas take gani,duk da tsananin tsaftarsa amma yake iya tarayya da hafsat din,harda qulafucinta haka?,lallai abar rai da abinda yakeso kawai.

    Sun jima suna hirar anty ummee na sake dorata akan keken bera,don itama tanaso idan ta yagi kudin ta yagi nata kason itama,tanason canza kayan kwalliyar falonta, hankalinta ya dauku ga hirar ta wuce kitchen dauko lemo,tafison tana yi tana korawa dame sanyi,dai dai sannan motarsu widad din ta shigo,ya tsaidata a parking lot.

    “Matar yaaya,yace ki sameshi a bangarensa,ga key din motar,saiki tafi masa dashi”

    “To,sannu na gode” dariya ya danyi kadan,itakam halinta dabanne,duk da sun girmeta,bai taba jin hafsat ta aikesu tayi musu ko sannu ba bare godiya.

    Tare suka fita a motar,shi ya doshi gate ba tare da yayi tunanin zuwa su gaida da hafsat ba,don sai suyi zuwa dari ba wanda ya kalli sashenta,sai dai idan sunga idanun abbas din,ko shi yace su shiga su gaisheta.

    Kallon sashen hafsat din tayi,gabanta yadan fadi,ta tuna kiran data dinga mata bata dauka ba,wanda shine tun daga ranar bata sake kiranta ba,saita dauke kanta,ta doshi sashen abbas din da dan hanzari,tana Allah Allah ne ta shiga ta bashi ta fito ta wuce sassanta.

    Tayi mamakin ganin wutar falon gaba daya a kashe,babu hasken komai sai na wutar bedroom dinsa,sarkin tsoro tsoron nata ya motsa,duk da bawai duhu can can yayi ba,don hasken fitilun waje suna ratsowa ta labulayen falon,ta fidda wayarta ta kunna torche sannan ta doshi dakin.

    Da siririyar muryarta tayi sallama tana shiga dakin,bata lura dashi ba har sai daya dan motsa daga kwancen yana amsa mata sallamar,ta danja baya adan tsorace,sai ya koma rigingine yana kallonta da rinannu idanunsa

    “Uncle…. Lafiya?” Ido ya lumshe sannan yayi qoqarin miqewa yazauna yana cije bakinsa kadan

    “Lafiya lau,ina umar din?”

    “Ya wuce,ga key din yace na kawo maka” ta qaraso gefansa ta duqa ta ajjiye,qamshinta ya huro masa har inda yake,sai ya maida idanunsa ya rufe

    “Yunwa nakeji,zan samu abinci?” Da mamaki ta kalleshi

    “Mommy hafsa fa?”

    “Zan samu abinci?” Ya sake maimaita tambayar tasa ba tare da yabi takan maganarta ba,sai ta gyada kanta da sauri

    “Okay,dafamin wani abun mai sauqi mai ruwa ruwa” sai a yanzun ta lura da yanayin fuskarsa,gaba daya ta nuna bashi da lafiya,jikinta yayi sanyi,ta matso sosai kusa dashi,tasa hannu tana dan taba fuskar tasa

    “Uncle kamar baka da lafiya fa” ji yayi kamar ta zuba masa wani abu me sanyi a gangar jikinsa,ya rufe idanunsa ya budesu a kanta

    “Bani da lafiya weedad” sosai fuskarta ta nuna damuwa qwarai,ta tsugunna gabansa tana ajjiye jakarta

    “Amma uncle ne yasa ba zakasha magani ba?” Ido ya zuba mata sosai,yana ji a ransa inama zata iya dauke lalurarsa,inama tace zata zame masa maganin?,ya sani matarsa ce…..amma yasan halittar da Allah yayi masa a shekarunta yana ganin indai ya fuskanceta da wannan zai iya cutar da lafiyarta

    “Zansha weedad……bani wani abun tukunna” da saurinta ta miqe ta zame mayafinta da jakarta duka ta aje a wajen,suman zaune ya kusayi,dogon sassalkan gashinta na kwance a bayanta,tunda ta shigo daman dankwalinta yana jakarta,ba kasafai take daura dankwali ba don basa shiri, skert din ya fidda shape dinta sosai,ta baya zata dauka takai shekaru ashirin da wani abu,sai a lokacin yaga girman da yaji ‘yan uwansa na fadin tayi,ya koma da idanunsa luuuuu ya rufe yana kiran sunan Allah.

    Faten dankali ta shirya masa,duk da yadda yayi dadi amma gaba daya baya gane taste dinsa akan harshensa,zamanta kusa dashi yafi komai dagula masa lissafi,ita kuwa ta zauna ne bilhaqqi tana matsa masa yaci

    “ko baiyu dadi bane na sake maka wani uncle?” Ta fada a shagwabe saboda sam bata jin dadin yadda taga baya ci din sosai,kansa ya girgiza dankalin yana wuce masa wuya da qyar,sai ya aje plate din ya zuba mata idanunsa gaba daya yana mata wani mayunwacin kallo

    “Maganin zaki bani” ya furta da wata birkitacciyar murya,itama shi take kallo,karon farko da taji kallonsa ya saukar mata da wani abu mai nauyi a jikinta da zuciyarta

    “Ina maganin yake saina dauko maka” tayi masa tambayar tana janye qwayar idanunta daga kansa,saboda wani nauyi da taji ya saukar mata lokaci guda.

    Kanta ta daga sanda taga ya miqo mata hannunsa,ta kalli hannun ta kuma kalleshi,bata fahimci komai ba

    “Zo na gaya miki inda yake” a mamakance ta miqa masa hannunta,bata kai ga tuna komai ba ta samu kyakkyawan masauki a jikinsa daya dauki dumi,cikin qirjinsa ya lullubeta gaba daya yana sauke wani irin numfashi a jejjere,komai ya fara koma masa sabo,tunaninsa ya fara nisa ya fara daina gane komai.

    Yamutsa ta ya fara yi,abinda ya tsorata ta ta fara kiran sunanshi tare da qoqarin kama hannuwansa dake yawo a sassan jikinta,ko harafi daya bai gane ba cikin maganganunta,illa dai yana jin sautinta kamar mutumin daya sanya bakinsa cikin kofi yana magana(sama_sama),a yau ya ware dukka hannayensa a kanta,duk inda suka kai bai musu shamaki,haka nan bakinsa.

    Sanda ya hade fatar jikinsu waje daya daukewa numfashinsa yayi cak na wucin gadi sannan ya samu ya qwatoshi da qyar,qasan da suke yaji tayi masa kadan,ya dagata zuwa tafkeken gadonsa ya shimfidar da ita,zuwa sannan tsoro ya kusa halakata,abinda bata taba gani ba,bata kuma taba zata ko tsammani ba…..yayin da abbas yayi nisa a wata duniya, duniyar da tunda yake bai taba tunanin ana kaiwa har can ba,tun daga tsarin lallausar fatarta zuwa daddadan qamshin jiki dana sumar kanta komai ya sake kwance masa,ya rasa ta inda zai juyata,ko ina ya juyatan sai yaji yayi masa kadan.

    Kuka mai qarfi ta saki sanda taji ya soma rabata da sutturar jikinta,ta shiga roqonsa da kyau akan kada yayi mata komai……ummu ta hanata……idan yayi ummu zata kasheta,amma ina samm samm baiji ba,abu daya ne ya maidoshi duniyar sa,daukewar numfashi daga gangar jikinta bayan taja wani dogon numfashi sanda ya soma buda hanyarsa zuwa sabuwar rayuwa da sabuwar duniya…. dole ya zare jikinsa daga gareta ba tare da yakai ga cimma gaci ba,ya koma qoqarin ganin daidaituwar numfashinta.

    Tun da safe ta tashi da sha’awar cin awara,sai da yaran sukayi bacci sannan ta fita da 200 zuwa bakin gate dinsu,ta bawa yaron gidansu ya siyo mata

    “Ka riqemin kudi na da kyau,don idan ka yarmin sai ka biyani” kudin ya kalla sannan ya dubeta

    “Hajiya dari biyu ce fa” ya fada qasan ransa fal mamaki,kaf unguwar kowa yasan waye ASP abbas din,amma ita sam bata jin kunyar yin aike da qaramin kudi

    “Na sani,ko bani na baka ba?” Sai ya gyada kai

    “Hakane” daga haka ya juya yana fita daga gidan,cikin ransa yana tur da irin halinta.

    A hanyar dawowa ta kalli motarsa,har yanzu bataji motsinsa ba,wani sashen na zuciyarta yana mintsinarta kan ta shiga ta duboshi,wani sashen yana fadin ki shareshi,zai kawo kansa da kansa,kulawa ma yabawa ce ai.

    Kamar giftawar iska taji fitar sautin qaramin ihu,wanda banda hankalinta dama akan sashen yake babu lallai taji,birki taja ta tsaya,gabanta yayi wani mugun faduwa,ta tsaya cak tana duban sashen nasa,muryar tayi mata kama da muryar widad,to amma yaushe ta shigo gidan?,tunda dai ita bata ji shigowar kowa ba,hakanan bataji fitar kowa ba,ta zubawa sashen idanun sosai ko zata sake jin wani motsi amma bata ji komai ba,sai hankalinta ya rabu biyu,wani sashen na zuciyarta na bata shawarar ta shiga ta duba,wani sashen kuma yana cewa tsarguwa ce kawai tayi,duk da haka saita kasa gamsuwa,ta dawo farfajiyar gidan ta zauna saman fararen kujerun da abbas din ya zuba a wajen saboda baqi,idanunta nakan sashen tana nazartarsa.

    Babu ma alamun haske gaba daya,wanda wannan sign din da take gane abbas din yayi bacci,don baya kwanciya da haske a kanshi,sai taji zuciyar dake gaya mata tsarguwa ce tafi rinjaye,amma duk da haka zata jira dawowar yaron,tasan zaiyi wuya wani ya shigo ko ya fita baya wajen.

    Bai jima ba ya dawo da awarar a farar leda karrr kana hangota quru quru,tasa hannu ta karba tana dubansa

    “Babansu mimi ya fita ne dazu?” Kai ya girgiza

    “Anya?,tunda ya dawo dai banga ya fita ba”

    “Bayan shi fa ba wadda ta shigo gidan nan?” Kai ya jinjina

    “Babu gaskiya” saita gyada kai tana sauke ajiyar zuciya

    “Shikenan jeka” sai data qara wasu sakanni sannan ta miqe ta koma ciki,tana tafe tana waigen sashen, zuciyarta taqi gamsuwa,amma ranta ya aminta da abinda yaron ya fada,tsaki taja daga qarshe,ta maida qofa ta rufe sashenta.
    [3/15, 9:35 PM] +234 704 440 6400: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)
    *Arewabooks: Huguma*

  • Arubuce Ta Ke 73

    Arubuce Ta Ke 73

    Page 73

    A dan tsorace ta kalli matar,ganin kuma ita take kalla saita dake,don ita bata yarda ta fadi ba ako menene

    “Bazan bayar bafa,ladan wahalar aikin da mukayi mata,nima idan tawa haihuwar tazo duka biyun haka takeyimin” dubanta matar ta sakeyi sosai,cikin bacin rai da daga harshe tace

    “Haka ake taya aiki a kwashe maka abincin suna?,cooler guda saboda dan ke kafadai akayi girkin?,ku haka kukeyi?,don kun taya aiki sai kowa yace anan zaici abincin rana?”

    “Sai kuma kiyita yi,don Allah ki fita kiban waje,mijina ya dawo”

    “Au haka kika ce?,to wallahi saikin fito da abincin nan kuwa” nan sa’insa ta barke a tsakaninsu,tun sunayi iyasu har hayaniyarsu ta kaiwa abbas dake tsaye yana nazartar dakin hafsat din,yadda likkafara qazantarta taci gaba,ko ina pampers din nawwara da aka cire an kasa kirashi dust bin,ga zanin gadon dake saman gadonta a iya saninsa sanda ya siyoshi milk color ne mai kyau,amma yanzun ya tasamma zama ash color,naira dub ashirin da biyar ya siyeshi,kyansa da taushinsa ne ma ya burgeshi ya siya din,amma bazai iya tuna wani amfanarsa da yayi ba.

    Jin hayaniyar tana yawa ya sanya dole ya ajjiye bag din hannunsa dake dauke da sweet din,ya juya zai fita a dakin yaga me yake faruwa,sai cabal qafarsa ya taka wani abu,yaja baya da sauri tsigar jikinsa tana tashi ya duba meye a qasan, kashi ne harda fitsari,yaja tsaki yana girgiza kai,dole ya juya akalarsa zuwa vabdakinta saboda ya wanke qafar tasa.

    Da qyar ya samu ya hadiye yawu a bandakin,saboda urun bidirin daya gani,zarni tako ina,ga uban kashi cike cikin toilet din ba’ayi flushing ba, zuciyarsa ta fara tashi,yaji nadamae shiga bandakin,saboda qazantar bandaki tana daya daga cikin qazantar dake damunsa,baya qaunarta sam,haka ya wanke qafar ya fito yana qoqarin controlling kansa saboda sosai zuciyarsa take tashi.

    Dif hafsat din ta dauke wuta sanda suka hada idanu bayan ya fito,baibi ta kanta ba,ya maida dubansa ga matar

    “Me yake faruwa ne?”

    “Yallabai,shinkafar suna ce,bayan sun gama aiki ta kwasota da yawa ta taho da ita,mutane nata zuwa babu,shine na biyota nace tadan rage a samu a sallami wasu, shikenan fa…….”

    “Okay,shikenan” ya dakatar da matar daga rattabo masa bayanin da takeyi,shi kadai yasan abinda ya tsaye masa a wuya,bacin ran ya nuna har idanunsa

    “Ina abincin?” Ya jefa mata tambayar murya a kausashe cike fal da bacin rai,muryarta a cushe tana ayyana irin rashin mutuncin da zata yiwa maqociyar tata tace

    “Yana kitchen” baice komai ba ya juya akalarsa zuwa kitchen din.

    Nan ma uban wanke wanke ne jibge a sink dinta,har wani tsami sukeyi,ya laluba da qyar ya gano wata warmer,ya janyo ya budeta saiga qudundunanniyar shinkafar a cuccure irin ta gidan suna tayi fuska abinta,ya daga warmer din ya juyashi,nasa ne da ake zuba masa abinci,wato tana nufin shi ta dibarwa?,shi zaici?,abincin gidan wani?,abincin da wani ya nemo a gidansa?,ba zata iya zama ta girka masa ba kenan saboda tsabar qwarewa a qyuya da kuma iya cin fuska?,ransa ya baci sosai,waye yasan tun yaushe take haka?,waye yasan irin b’arar masa da mutuncin da tayi,haka maqota suke kallonsa kenan tsirara?,ya jawo warmer din ya fito da ita.

    A tsaye ya samesu matar na riqe da qugu,wani bacin rai ya sake tokareshi,shinkafar da ko masu aiki cikin gidansa sunfi qarfinta yau saboda ita aka shigo masa cikin gidan ake wanna tijarar

    “Gashi” ya miqa.mata gaba daya,ta karba tana qoqarin juyewa ya daga mata hannu

    “Jeki kawai”

    “Flask din naku ba”

    “Tafi dashi” sai ta saka flask din cikin robar ta juya tana bari wajen.

    Ganin da gaske tafi mata zatayi da warmer dinta me tsada saita yunqura zatayi mata magana kan ta dakata ta juye ta bata abarta,wani kallo ya watsa mata wanda ya sakata dawowa da baya,ta kuma yi laqwas babu shiri

    “Ina yarana?”

    “Naga fa warmer din nan me tsada ne,sai kacw tatafi da ita?,idan kuma taje ta bata fa,kasan gidan suna” ta shigar masa da qorafinta a maimakon amsa masa tambayarsa

    “Ina yarana nace?” Ya sake tambayarta wannan karon a kaurare

    “Suna……a gidan sunan sukace na barsu”

    “Kika barwa wa su?” Saita dan sosa kai

    “Mai aikin gidan maman husna,tace zata kawosu idan……”

    “Idan sun gama cin abincin gidan sunan suma?,saboda yunwacw fal a gidan ubansu?,maza maza kirata a dawomin da yara na,na baki minti biyar” yayi maganar yana murza yatsunsa,sannan ya juya yayi gaba yana barin mata sassan.

    Da harara ta bishi,ai kuma shikenan ya dawo babu zaman lafiya ba sakewa,dole ya suri wayarta ta laluba number talatu tace ta dawo dasu abbansu ya dawo,tace tahe bayan layinsu da yaran amma gata nan

    “Kiyi sauri don Allah”

    “To” ta amsa mata,saita cire wayar daga kunnenta tana jan tsaki sannan ta wuce dakinta.

    Sai data taka kashin daya taka ta tuna ma yadda dakin nata yake,ta dauki salati,tasan ya gani,kwata kwata ta manta a haka tabar dakin,harta fara gyarawa ta tuna qila da widad sukazo,sai ta yanke tayi kiranta

    “Tazo ta kama aikinta,nima na samu na tsugunna na huta” daga haka ta figi mayafinta ta nufi sashen widad din.

    Ta gama kintsa ko ina,sai fidda qamshi yakeyi,tsumman towel ne a hannunta tana goge nayan kallo da sauran glasses da abubuwan da suke. Daukan qura a falon,hafsat din ta turo qofar da dan qarfi,dama.ba kasafai ta fiya sallama ba har sai ta shigo falon, saboda tsabar zargi da ranta ke raya mata ko zata kama abbas a wajen(kamar wani kwarto ba matarsa ba).

    Kamshin data shaqa ya riqe maya maqoshi da irin kishi ta gaza sallamar,widad ta daga kai tana dubanta,karon farko da taji ranta ya baci na yadda ta shigo mata ba sallama,ta riga ta saba,duk yawansu a gidansu,duk kuma yadda suke da ummu bata isa ta shiga waje kai tsaye ba sallama ba.

    A yau itama saita riqe gaisuwarta,tana kallon yadda hafsat din kebin sassan da kallo kafin ta sauke dubanta ga widad,hatta sassan ya sauya mata,bare widad din dake qara wani irin girma da haske

    “Sannu isassa, shigowar da kike nasan kinzo yau ban isa ba kenan,shine kikazo nan kika kama.naki aikin ni kin barni da tulin aiki,to ki gayamin waye zaiyi miki aikin?” Maganar ta dan baiwa widad din haushi,sai kace ita ta hada mata dattin ko tace ta dinga barinsa,ci gaba tayi da goge gogenta sannan tace

    “Gani nan zuwa” tsaki hafsat din taja,ganin yadda taketa qalqale komai na wajen,ta danyi jim sai kuma ta juya ta fita,ta tsani ta shigo sassanta taga tana wannan qaqale qaqalen

    “Wannan dole na sake matsa miki lamba tare da sanya idanu sosai a kanki,idan ba haka ba fin qarfina gaba zakiyi” ta raya haka a ranta.

    Haka kawai yau saita samu kanta da jujjuya abinda mommy hafsat din tayi mata a rai,sai taji bataji dadin abinda tayi mata ba,amma sai ta danganta hakan da rashin sallamar da batayi mata bane yafi bata ranta.

    Koda ta gama saita wuce bedroom dinta,ta canza kayan jikinta zuwa wata smocked gown me skinny straight skert da yasha tsaga ta baya,ta daure sumarta mai tsaho da santsi cikin dankwalin kayan.

    Sassan abbas ta wuce,don bata manta ba sunyi dashi zata gyara masa,zuwa yanzun kuma tasan umarninsa da aikinsa sama yake dana hafsat din,kamar yadda ta taba yiwa anty madeena tambaya,ba kamar a baya ba,da takejin umarnin mummun hafsat din sama yake dana abbas dama kowa dake cikin rayuwarta.

    Sanda ta shiga yana zaune saman kujerar parlor yana amsa waya,ya kasa dauke idanunsa daga kanta,saboda taja hankalinsa sosai,ta sakar masa murmushi ganin waya yakeyi,ta kuma masa nuni da hannunta kamar maganar kurame akan ta ina zata fara?.

    Idonsa ya lumshe sannan ya budesu a kanta,ya mata nuni da falon,he wants to keep his eyes on her,saita tako zuwa ciki a hankali ta soma kintsa wajen.

    Duk inda ta motsa idanuwansa suka biye da ita,kamar yadda duk sanda ta gifta saita bar masa qamshinta,wani irin yanayi ya dinga sauka a jikinsa,da qyar ya samu ya kammala wayar,sai ya ajjiyeta daga gefansa yayi folding hannayensa a qirjinsa yana kallonta sanda mopping parlor din da mopping mist dinta data taho dashi,lallausan qamshin daya saba ji a sassanta ya fara game nasa falon,yana sin qamshi yana son qamshi har baisan iyaka ba,tsafta na daya daga cikin abubuwan dake bashi nutsuwa a rayuwarsa,sai ya samu kansa da miqewa a hankali,ya isa gareta,ya kama mop stick din ya riqe,hakan ya sanya hannayensu gamuwa waje daya,ta daga manyan fararen idanuwnata suka sarqe da nashi waje daya.

    Har cikin jikinta taji wani abu ya tsarga mata,sai ta sakar masa sandan taja da baya tana murmushi

    “So kake ka tsoratani?,banji tahowarka ba Allah” tayi maganar tana yarfe hannunta kamar wadda ta riqe wani abu me zafi

    “So nake na samu ladan sunnan taya matata aiki” kalmar tasa ta bata kunya,saita sunne kai cikin dankwalinta,ya daga kai yana murmushi,yana son yaha reaction na fuskarta da yadda ta karba maganar.

    Tana biye dashi yana mopping din,kuma shine yace ta dinga binsa din,wajen da bai gogu ba ta gaya masa,yayi hakanne kawai saboda nutsuwar da zuciyarsa ke samu kasancewarta a kusa dashi.

    Tare suka gama aikin,har cikin bedroom da toilet dinsa,ta kwashe zanin gadon kai ta sauya masa da wani bayan ta turarashi a kabbasa,ta maida komai muhallinsa,sai ya dinga jin zuciyarsa wasai,gyaran yayi masa fiye da yadda ma yake so.

    “Ga tukuici” ya fada yana miqa mata wani siririn agogon silver da aka masa ado da dan wani dige digen gold a jiki,yana da tsada sosai,hafsat ya taba siyawa gift dinsa,amma har yau ya kasa bata,saboda ta kasa bada kyakkyawan yanayin da zai gabatar mata da kyautarsa,duk sanda yazo da niyyar bata sai wani bacin rai ya gifta da zai sashi ma mantawa da hakan.

    Ido ta fidda sanda ta ciro agogon,yayi masifar burgeta

    “Uncle…..duka nawa ne?” Ta fada da wani irin accent dake nuni da zallar quruciya,kai ya jinjina yana murmushi

    “Yes,kin manta abincin da kikayimin last three days?,dama nace miki akwai gift,na hada miki harda na ranan” dan tsalle tayi,ta isa gabanshi ta riqeshi tana cewa

    “Thank you uncle,na gode sosai” ajiyar zuciya ya saki saboda riqon data yi masan yasan yanzun zai bada reaction a jikinsa

    “Is okay” yana kallonta tana ficewa a sassan riqe da agogon,fara’ar fuskarta ta gaza daukewa.

    Da baya ya koma ya zauna saman gadon,tana ci gaba da haifar da wani yanayi mai girma da nauyi a zuciyarsa,how can he continue looking at her a mazaunin matarsa?.

    Sai data koma sassanta ta ajiye agogon sanann ta wuce part din hafsat,tana hanya tana tunanin inasu mimin da bataji motsinsu cikin gidan ba.

    Dai dai lokacin da hafsat ta cika ta batse rashin zuwan widad din,zuciyarta ta fara mata saqe saqe,lallai tayi sake,har ankai matsayin da zata taka ta kirata ammaa ta bata kusan awa guda batazo ta fara mata aikin data sakata ba?,anya kuwa bai aikata wani abu da yarinyar ba wanda ya sanya ta fara rainata ko qoqarin yi mata gani gani?,baiko daidaita matsayinsu ba a shimfida?,amma tana tantamar hakan,tasan abbas tasan lalurarsa tass…..ko dai itace ta fara sanyi da saken daya fara kawo wannan canjin daga yarinyar?.[3/16, 10:18 PM] +234 704 440 6400: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)
    *Arewabooks: huguma*

  • Arubuce Ta Ke 64

    Arubuce Ta Ke 64

    Page 64

    Shi kadai yasan yadda yayi surviving wannan daren,ya azabtu da yawa,daga baya da yaga ba sarki sai Allah dole ya zareta daga jikinsa bayan yaji saukar numfashinta tayi bacci.

    Ya dade yana kai komo,zuciyarsa na gaya masa ya aika abinda zai samu sassauci,to amma yana tuna abinda zaije ya dawo,har yanzu ya tabbatar bata gama sanin meye aure ba,bugu da qari rainon zuciyarta yakeyi,baida tabbacin soyayyarsa a ranta,beside ma hajiya na gidan,bai kamata haka ta kasance ba a karon farko.

    Sai wajen biyu na dare ya samu kansa da qyar,da kansa ya zabi kwanciya a qasa,zuciya da ruhinsa cike fal da tunani,wannan din ba komai bane sai kasawa da gazawar hafsa,bai taba zuwa mata weekend ko tafiya irin wannan ya samu irin tarbar da yakeso ba,bai taba dawowa sun rabu lafiya lau da ita ba,duk yadda kuwa zaikai gakai zuciyarsa nesa da dauke kansa,ya tabbatar inda ya samu ko yana samun yadda yakeso daga gareta,duka hakan ba zata faru dashi ba,saidai kuma ajizanci irin na dan adam.

    Kusan tare suka tashi sallar asuba shi da ita,abu na farko data fara tambaya tun batayi alwala ba shine lafiyarsa,ya jikin nasa,ya saki murmushi yana jin dadi hat xikin ransa,saboda baisan da kalar wannan kulawar ba,yana iya yin ciwo har ya warke hafsat din bata sani ba saboda tsabar rashin kulawa irin nata

    “Na warware alhmdlh”

    “Sannu uncle,Allah ya sawwaqe”

    “Ameen” ya amsata yana murmushi,da gaske yarinyar ce,wadda aka raineta bisa tsaftataccen tarbiyyar da har batasan meye ainihin ma’anar aure ba,batasan sha’awa ko wani abu daya danganceta ba,abu kadan ta sani wanda baikai girman da zai shiga tunani ya lalata mata rayuwa ba, tashin farko da yaji rashin sanin meye aure da batayi ba bai wani dameshi sosai ba,saboda wannan shine yake basji guarantee na cewa ita din mai tsaftataccen tunani ce da batasan komai ba,zaiyi dashensa yayi shukarsa ya kuma yi girbinsa yadda yakeso kenan.

    Tana kan abun salla tana tunanin me zata dafa da safen,wayarta da tayi qara ta katse mata tunaninta,ta tashi ta dauko wayar tana duba me kiran

    “Mommy hafsa da safen nan?” Ta tambayi kanta gabanta yana faduwa,sai a sannan ta tuna a dakinshi fa ashe ta kwana,ko wani ya gaya mata ne?,wannan tunanin ya hanata daga wayar har ta katse.

    Iska mai zafi hafsa dake tsaye cikin dakinta ta furzar,ta daura alwalar amma ta gagara tayar da sallar,ta manta gaba daya gidan daki biyu gareshi,hakan yana nufin hajiya na daki daya,ita da abbas dinta zasu kwanta daki guda shimfida guda?.

    Ko yanzun data kiratata bata daga ba, zuciyarta na kissima mata qila a daren jiyan ya samu yadda yakeso ne,babu yadda take shi yasa ta gaza daukar wayarta,wannan tunanin ya tashi hankalinta,ta koma gefan gadon ta zauna ta shiga jera mata kira ba qaqqautawa.

    Abin da ya sake tsorata widad kenan ta kasa daga kiran,lallai tasan a dakinsa ta kwana,kuma tambayar da zata mata kenan tunda taketa kira,sai ta ajjiye wayar tana kallonta gabanta yana ci gaba da faduwa,har zuwa sa’ar da abbas ya dawo daga sallah,ya buda qofar dakin ya shigo.

    Idonsa akan wayar,don itama ita take kalla,hannunsa zube a aljihunsa ya qaraso,ya dauke idonsa daga kan wayar ya maida kan fuskarta,saita dan dauke kai tsoron kiran da ake mata,da kuma kunyarsa suka hadar mata

    “Ina kwana?”
    “Kin tashi lafiya?”
    “Lafiya lau ya jikin naka?” Idanunsa ya lumshe ya kuma budesu yana sakin murmushi, lallai quruciya na damunta da gaske

    “Da sauqi,na warke” kai ta jinjina masa,sai ya sake duban wayar

    “Ba kiranki akeyi ba ki daga” fuska ta kwabe sannan ta girgiza kanta,bai sake cewa komai ba ya matsa wajen kujerar da yakan zauna yayi karatu da asuba ya jawota ya zauna,sai widad din ta miqe a hankali ta nade abun sallar nata,ta nufi qofar fita a dakin

    “Ina zuwa?” Waiwayowa tayi

    “Xanje gaida hajiya” sai ya gyada mata kai kawai.

    Daga inda yake zaunen yana hangen hasken da wayar taketa yi,yadda aketa kira ba qaqqautawa ya bashi mamaki,ba tare daya shirya ba ya miqe,ya isa ga wayar ya dauko,sai yaga sunan mommy hafsat,abun ya daure masa kai,ya juya yana duba wayarsa waiko zaiga miscall dinta,may be ta kirashi ne baya kusa bai daga ba,wani abun kuma ya faru,amma sai yaga babu kiranta ko daya,ya daga wayar ya kara a kunnensa tare da yin sallama.

    Jin muryarsa ya qarasa fadar mata da gaba,jikinta gaba daya yayi laushi,ta saki abun sallar a qasa,da gaske suna tare,tare suka kwana,kasa motsawa bakinta yayi,ta riga data samu amsar abinda take nema,don haka ta kashe wayar tare da sulalewa a wajen ta saki wani irin kuka mai tsananin zafi da cin rai,shikenan,ta faru ts qare.

    Jin alamun an katse ya sashi daga wayar ya kalli screen din wayar,sai yadan tabe baki ya maida wayar ya ajjiye,har ya taka zai bar wajen sai hoton fuskar wayar ya dauki hankalinsa,ya koma ya sake dauka,ya koma saman kujerar ya zauna,ya buda gallery ya soma kallon pictures din a hankali har baisan sanda murmushi ya dinga kubcewa daga fuskarsa ba,kowanne hoto da kalar quruciyar da za’a nuna a jiki.

    Hannunsa ya miqa,ya dauki wayarsa ya buda,yayi marking wasu daga ciki ya tura.

    Ranar kaf qin yarda tayi ta sake komawa dakinsa,ko hanya qin yarda tayi su hada dashi,tana tsakanin dakin hajiya da kitchen,bayan sun hada breakfast ita da muneera suka shirya komai a falo,tare sukayi break din har hajiyan,sunayi ana taba hira,da suka gama suka sake gyare gidan tare,shi da hajiyan suna dai falo suna hira,a nan sukaci abincin ranar tare da hajiyan,sannan ya koma daki ya shirya ya fice.

    A daren ranar yana zaune daga bakin gadon sa,qaramin littafin addu’o’i ne a hannunsa yana karantawa,ya gama komai,kammala addu’arka ne kawai ya rage masa,amma sam baiji motsinta ba,lokaci lokaci yana daga kai ya kalli bakin qofar dakin nasa a haka har ya kammala addu’ar,ya aje littafin gefen bedside ya zuro qafafunsa ya zura bedroom slippers dinsa ya miqe a hankali ya fito daga dakin.

    Babu kowa a falon,amma yaga dakinta a bude,yasan suna ciki,yayi gaba zuwa dakin,ya tura qofar bakinsa dauke da sallama.

    Dukkansu suka amsa,hajiya na zaune gefan gado,muneera da widad na saman qaramin carpet din dake shimfide qasan dakin,muneeran na maidawa weedad kalbar kanta da santsin kan ya sanya ta ware kamar ba’a taba yinta ba,bataso a taba mata kai tana ta qorafi muneeran na fadin saita yi mata,hajiya na goyuwa da bayan weedad din.

    Kadan ya kalli sashen da suke,ya qaraso ciki,ya samu gefan hajiya ya zauna

    “Bakiyi bacci ba hajiya?” Sai tayi murmushi

    “Banyi ba,ina dai shiri”

    “to yayi kyau,kin hada komai naki waje daya ko?, saboda gobe sha biyu zamu fita”

    “Komai a kammale yake”

    “Ma sha Allah…..shikenan,dama zuwa nayi nai miki sallama,sai da safe”

    “To Allah ya bamu alkhairi ya tashemu lafiya” sai ya juya yana ficewa a dakin,minti biyu hajiyan ta kalli widad

    “Maza tashi ki tafi ki kwanta kin baro mijinki,nikam sai da safenku” dif widad tayi,don ita gaba daya ta gama tsarin kwana a nan din,ta dan dubi muneera taga itama ta fara shirin kwanciyar,dole ta miqe,ta dauki siririn gyalen abayarta ta dora saman kanta,ta bude closet dinta ta dauki rigar bacci tayi musu sai da safe ta fita.

    A sanyaye ta tura qofar dakin tashiga da sallama,yana zaune daga bakin gado yana amsa waya,haka kawai yaji sanyi har cikin ransa sanda yaga ta shigo din,bandaki ta wuce,ta fidda kayan jikinta tayi wanka,don zuwa yanzu tayi mugun sabo da wankan dare,ta shirya cikin kayan baccin ta fito.

    Dim light ne a dakin,yana iya hangen sanda ta fito da kuma hawanta saman gadon,taja duvet ta kwanta ba tare data ce komai ba,qaramin murmushi ya saki,abinda ya faru jiya yana dawo masa,sai ya samu kansa da janyo wayarsa,ya duba wajen music ya lalubo kukan magen jiya ya saka.

    Curewa tayi waje daya,tun tana iya ganin zata jure harta kasa,sannu sannu sai gata cikin jikinsa ta cukuikuye shi,ya saki murmushin nasara ya sanya hannunsa ya lullubeta cikin qirjinsa yana sakin murmushi,ita kuna tayi lamo tana sauraren bugun zuciyarsa da nata da kowannensu ke fita da sauri da sauri.
    [3/14, 7:17 PM] +234 816 133 8078: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)
    *Arewabooks:Huguma*

  • Arubuce Ta Ke 71

    Arubuce Ta Ke 71

    Page 71

    Har ta karbi kudin ta dawo da baya,tunda dama.ba karbar kudinne a zahiri ya shigo da ita ba

    “Wai niko latifa,akace widad tazo ita kadai da tsakar ranar nan,kuma na shigo banganta ba,ko tana bandaki?” Kallonta latifa tayi,banda tana ganin girmanta cewa zatayi tana cikin masai ba bandaki ba,amma saita dauke kai tana ci gaba da aikace aikacenta

    “Kinsan ni bana shiga hurumin wasu,iya matsayina nake tsayawa a gidan nan,inaga da kin koma wajen ummu da kika wuceta a falo,zakifi samun bayani” ta gane sarai magana takeson gaya mata,sai kawai tace mata

    “Eh,kuma haka ne” ta juya ta fita tana tabe baki a ranta tana fadin

    “Koma dai meye idan tayi wari maji,oh…..yau ga ‘yarso a gida,da alama ma dai auren ne ya balle,dama waye zai dauki wannan sakalcin nata,shafaffa da mai”.

    Tun tana kukan har bacci yayi awon gaba da ita ba tare data sani ba,bata farka ba sai wajen qarfe uku na rana,ta miqe ta zauna tana murza idanunta,ta manta shaf a dakin ummu take,komai ya dawo mata,tabi dakin da kallo,dai dai lokacin ummun ta buda qofar ta shigo,tazo ne dama fa dubata kota tashin.

    Qin yarda tayi su hada ido,sai ta kauda kanta tana kallon qasa

    “Ki tashi kiyi wanka kici abinci” kai ta gyada,sannan ta zuro qafafunta qasa ta miqe,har yanzu wajen tana jinsa wani dundurus,duk da zafin zuwa yanzu ya baje.

    Ruwa me zafi ta hada sosai tayi wankan,wajen yin tsarki taji ruwan dumin ya mata dadi a wajen,ta dinga kwararashi har sai data ji wajen ya saki gaba daya sannan ta fito,ta samu ummu ta aje mata doguwar riga cikin ire iren kayanta da bata gama kwashewa ba daga gidan,ta sakata tayi sallar la’asar da aka soma kira sannan ta daure ta fito falon ummun.

    Su biyu ta samu,ita da anty madina,madinan batasan da zuwanta ba,don bata gidan,yanzun ta dawo ta biyo kawowa ummu sallahu data bata,baki ta riqe cikin madaukakin mamaki da kuma farinciki

    “Widad din ummu….. innalillahi,yaushe kika zo,babu sanarwa bare nayi miki kyakkyawar sauka?,saida kika bari ranar da bana nan fisabilillahi” murmushi ya qwace mata,karon farko kenan tunda tazo gidan.

    Tabe baki ummu tayi tana duban anty madina

    “Waye ma yasan da zuwan nata?,koshi mijin nata ai baisan zata zo ba,muma ganinta kawai mukayi” gaban anty madina ya fadi

    “Kamar yaya?,widad me ya faru?” Tambayar dai dai take da sukar bulalai a jikinta,ta yaya zata iya ce musu ga abinda yayi mata?,sai kawai ta fara hawaye bayan ta zauna a wajen.

    “Kici gaba da kukan,karki bude baki ki fadi abinda ya kawoki,mahmudu kawai nake jira ya dawo,ai jibi yacemin zai dawo,yana hanya” cewar ummu bayan tayi qwafa,da alama ranta ya baci wannan karon akan widad din,a tausashe anty madina tace

    “A’ah,ai baza’ayi haka ba,ki bita a hankali ummu don Allah”

    “Yo madina meye ban mata ba?,indai ba so take na tsugunna tahau gadon bayana kuma na goyata ba,shine kawai abinda ya rage”.

    A nan suka sanyata gaba da tambaya harda latifa amma ta kasa cewa komai,har ummu ta qulu ta tashi ta barsu,daga baya suma hakanan kowa ya haqura ya qyaleta.

    A ranar duk wanda ya shigo gaida ummun cikin yaranta maza kawunnan widad din sai ya kirata ya tambayeta,amma ta kasa cewa komai sai kuka,haka washegari akayita fama taqi magana,tace duka su qyaleta, mahmudu ne dai dai da ita,a goben kuma ko jibi zai dawo,abinda ya sake ruda cikin widad din,amma batajin zata iya ce musu ga dalili.

    Yaran gidan nata shigowa murnar zuwanta amma ta kasa sakewa,haka su Aafiya,saidai suyita hirarsu tana kallonsu,don ita a cikin damuwa take,tana tsoron gamuwarta da babanta,amma kuma tayaya zatace musu ga abinda yayi mata daya sanyata guduwa?.

    Abbas kuwa umnu ce tasa muhsin ya gaya masa basai yazo ba,yayi zamansa,abinda ya bashi mamaki yadda yakejin damuwa sosai a ransa,har ya taba kuzarinsa,ya kira number dinta kuma sau babu adadi amma kullum wayartata a kashe take,inda don ta tashi ce da tuni ya tsufa a kano,kwana ukun kacal amma yana jin kamar wasu kwanaki ne masu dimbin yawa,hafsat ta lura da hakan,duk da kusan ba wani sabgar juna suke shiga ba,ta kuma ji qishi qishin zancan tafiyar widad din kano,duk da bata da tabbacin meye ya kaita,amma ko babu komai taji dadin hakan har qasan ranta,tunda dai tasan ba lafiya bace ta kawo hakan,fatanta ma ta tafi kenan,kada ta sake dawowa har abada.

    Abu daya ne ya tsaye mata a rai,damuwar data fuskanci abbas din kamar ya shiga,ta rasa gane ma’anar hakan,ya fara son yarinyar kenan?, tambayar data yiwa kanta kenan,sai kuma ta qaryata kanta da kanta,ta yaya abbas din zai fara son diyar cikinsa?,banda kyau babu wani abu data ga yarinyar tana dashi,samun kanta tayi da duqufa addu’ar kada Allah ya bata ikon dawowa.

    **********Dukkaninsu suna falon ummu,mahaifinta da ya kasance babba da kuma qannensa gaba daya,ummu da widad na gefe,yayin da widad din tayi kamar ta shige cikin ummun

    “Tunda taqi cewa komai yaaya,me zai hana a sake kiran abbas din aji” girgiza kai alhaji mahmud mahaifin widad yayi cikin takaici

    “Ya riga yace min babu komai,kuma tunda yace din babu,ita dai tana kwaso wadan nan siraran qafafuwan nata tazo,ita zata bude baki tayi mana bayani ko na tashi na babballata a wajen nan na zubar” ya fada cikin tsananin fushin da tun dazu idanun ummu yasa yake cinyewa.

    Duka kallo sai ya koma kanta,cikin hargagi kamar zai kai mata duka yace

    “Zaki bude baki kiyi magana ko saikin daku?” Kamar an rufto mata duniya haka taji,ga wani mugun tsoron yadda abban nata ya juye da yake ratsata,tayi qas da kanta tana hawaye, abinda ya tunzura alhj mahmud,ba wanda ya ankara sai gani sukayi ya isa kanta da wayar tv daya ciro ya fara sauke mata ita.

    Kuka ta saki sosai,don zata iya cewa wannan shine karon farko da aka taba mata irin wannan dukan kaf rayuwarta,kafin a samu a qwaceta kuwa ta daku yadda ya kamata,latifa ta karbota tana boyeta cikin hijabinta ta fice da ita daga sassan ummun cikin jimami da alhini.

    Kai tsaye sassan anty madina tayi da ita,tana kwance a falo ta miqe tana salati

    “Dukanta dama yaaya yakeyi dana jiyo muryarta daga nan?” Anty madina ta fada kamar zatayi kuka

    “Wallahi,taqi ta fadi komai ne,shi kuma ransa ya baci” rungumeta anty madina tayi tana lallashinta

    “Inda kin fada widad ai magani za’a yi miki na koma meye da yake damunki” a nan hannunta latifa ta barta

    “Kada kice musu tana wajena please” anty madina tace da latifa ta juya ta fice,ita kuma ta jata zuwa bedroom dinta.

    Shuru ne ya ratsa falon bayan fita da widad din,zuciyar ummu duka ba dadi,dukan da mahmud yayi mata saita dinga jin kamar ita aka daka,amma kuma babu wani sauran abinda za’a yiwa widad din

    “Inajin ruqiyya zan sanya azo gida ayi mata” ummu ta fada cikin karyewar murya,kai kawu maisara ya gyada

    “Eh to,ya kamata a bincika ta wannan fannin ma,saboda suna iya sakata yin hakan,kuma ba kasafai hankali yake kaiwa can din ba,sai abu ya ta’azzara sannan ba fata ake ba”

    Miqewa abban yayi

    “Ai magana ta qare,gobe in sha Allah zanzo na dauketa da kaina muje,idanma sune sayi bayani”

    “Da kanka yaaya,ka bari wasu cikinmu su kaita”

    “Gwara ayi komai a gabana sa’idu don qaniyarta” har dariya taso subucewa ummu,mahmud din badai zafi ba,duk cikin yaranta ya fisu zafi,musamman al’amarin aure,baya wasa dashi.

    A hankali anty madeena ta turo qofar dakin

    “Kinyi bacci ne widad?” Widad dake zaune qasan carfet tana duba wasu litattafai data gani a dakin anty madinan ta amsa

    “Ban kwanta ba maman walidi”

    “Au na dauka mai gidan ya koya miki baccin wuri” ta fada tana duban fuskarta

    “Uhmmm” kawai ta fada tana maida kallonta ga littafin,maganar da anty madinan tayi saita tuna da abbas din,yana da kirki matuqa,yana da tausayi,tanajin dadin hira dashi amma duka ya bata wannan ta sanadin abinda yayi mata.

    Kaya ta zuba cikin cupboard sannan ta dawo gefen widad din ta zauna tana kallonta

    “Ki shirya gobe inji yaaya abba(haka matan gidan suke kiran babanta),gobe da safe zaku gidan mai ruqiyyar cire aljanu” a tsorace ta kalli anty madina idanunta a waje

    “Aljanu kuma?” Kai ta gyada cikin nuna halin ko in kula

    “Eh,haka abbansu walid ya gaya min” tuni hawaye suka cika idanun widad,ta narke sosai tana kallon antyn

    “Don Allah anty kice kada su kaini wallahi ni ba aljanu bane dani”

    “To menene widad?,tundi kinqi gayawa kowa aka sani ko sune?,ai gwara aje can din,qila su zasuyi magana” yadda taga ta rude tana roqonta taji a ranta zasu samu bakin,sai ta gyara zamanta tana dubanta

    “Kinga daga ni sai ke,ki gayamin me yasa kika taho kinji”

    “Ni bana sonshi anty madina” baki anty madinan ta riqe tana kallonta cikin mamaki,lallai wani halin sai widad din,amma a yadda ta fadi maganar ta fuskanci akwai wani abu,don haka ta hadiye mamakinta tace da ita

    “Bakya sonshi?,to me yasa bakya sonshi?”

    “Dan iska ne” ta amsa mata kai tsaye hawaye na sauka a idonta.

    Dariya ce taso qwacewa anty madeena,to amma tanaso su qarqare qarshen zancan

    “Dan iska kamar yaya weedad?,me yayi miki na iskancin?” Kallon anty madeena tayi,idanunta kamar zasu fado,kunya da nauyinta takeji,amma.indai bataso a kaita wajen mai aljannu dole tayi bayani

    “Tattabani yakeyi” ta qarasa fada muryarta tana rawa.

    Zuwa wannan gabar dole dariya ta kufcewa anty madina,yayin da sautin dariyar ya sanya widad cikin rudu,ta dauka zataga ta saki salati tana tafa hannaye,kota rufeta da fada ko da duka ma akan ta bari ana tabata din,sai kawai taga tana dariya.

    Kusan minti biyu sannan anty madeena tayi shuru tana nazari,ba shakka kuskure nasu ne,duk yadda akayi ummu bata zaunar da widad ta gaya mata meye gundarin aure ba,suma kuma bata jin wata a cikinsu tayi hakan,duk da kusan abun ma qurarren lokaci yazo,amma duk da haka alhmdlh da aka gano bakin matsalar.

    A ranar dukka wata kunya anty madeena ta cire ta dinga gayawa widad komai gatso gatso,jikin widad har rawa ya dinga yi saboda mamaki,ta dinga kallon anty madeena tana mamakin haka take?

    “Eh kalleni da kyau,wannan abun da kika gudowa,kowa yana yi indai mata da miji ne an daura musu aure,harni kaina da kike gani” kunya ta sanyata cusa kanta a cinyoyinta ganin anty madeena din ta danganta abun da kanta,ta kasa daga kanta,sai kuma kwanyarta ta shiga mata research,me yasa mommy hafsa ta dinga jaddada mata kada ta yarda ya taba ko yatsarta yadda ummu take gaya mata sanda tana gida,meye dalili?,tambayar data rasa gano amsarta,sai kawai ta daga kai ta fuskanci anty madeena taga gwara ta tambayeta…….
    [3/16, 11:09 AM] +234 704 440 6400: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)
    *Arewabooks:Huguma*

  • Arubuce Ta Ke 72

    Arubuce Ta Ke 72

    Page 72

    “Umman walidi…..amma abinda mommy hafsat take fadamin ba gaskiya bane kenan?,naga itama babba ce kamar ku,amma bata taba gayan abinda kika gayamin yanzu ba”

    “Me take ce miki?” Anty madeena ta tambayi widad din tana kallonta,cikun fargabar kada ta koya mata dabi’ar banza

    “Ta gayamin abinda ummu ta jima tana gayamin har nabar gidan nan,tace idan ya kama hannuna Allah zai qona ni,idan na yarda ko kusa dani ya zauna sabon Allah ne,kuma Allah zai iya qonani,kuma koda wasa ya tabanin tana ganewa,har waya take tana tambayata”

    “Ke kuma idan ta tambayekin sai kike gaya mata?” Anty madina tayi hanzarim tambayar widad tana datsar numfashinta,kai widad din ta gyada,haushi da takaici ya saka anty madina sakin salati,sai yau ta yarda kaf gidan babu wanda yakai widad din rashin wayo,da gaske ne,ada da ake fada tana ganin ba haka bane,kawao miskilanci ne yayi mata yawa,ashe harda rashin wayon

    “Yaushe duka ta gaya miki hakan akan uncle din”

    “Kullum saita kirani,ta tambayeni dame dame nayi,dame dame yayimin” wanu malolo ya tsayawa anty madina,sai yanzu ta gane…..hafsat din tayi amfani da rashin wayon widad,da kuma tarbiyya me kyau data samu na girmama na gaba da kai da bin umarninsa ta kitsa mata wannaj baragurbin tunanin,tayi kuma sara akan gaba,suma sun manta basu fayyace mata irin rayuwar da ake nufi da rayuwar aure ba.

    Zama na dirshan anty madeena tayi ta fara dora mata bayani akan matsayin hafsat din a wajenta,ta fayyace mata wace kishiya fes,sannan ta rufe da cewa

    “Ba cewa akayi ki rainata ko kiqi yi mata biyayya ba,amma babu ruwanta da ko mene tsakaninki da uncle dinki,matsayinku daya a wajensa ke dashi,ki rufe sirrinki,karki yarda ki sake gaya mata komai dake tsakaninku”.

    Sai kusan sha biyu na dare sannan anty madeena tabar dakin ta wuce dakin mijinta,tabar widad a zaune tanata saqa da warwara,komai ya yiwa kanta girma,tana ta jujjuya maganganun da sukayi da anty madina,tun daga farko har zuwa qarshe, yanzun itama data tafi dakin kawu abinda sukeyi kenan?,abinda ya fado.mata a rai kenan,kunya ta kamata ita kadao cikin dakin,saita cusa kanta a cikin filo tana sake hasashen abubuwan da suka dinga faruwa tsakaninta da abbas din.

    Bayan sallar asuba anty madeena ta zayyanewa daddynsu walidi yadda sukayi da widad din,tana dariya dariya tace masa

    “Kaga babu sauran batun zuw wajen ruqiyya,a gayawa yaaya abba yayi haquri” kai ya jinjina yana murmushi

    “Na yarda widad din muguwar sakaliya ce,ku daman baku fada mata komai ba?”

    “Wallahi sam ban kawo haka a kaina ba,saboda naga yawanci yaran yanzun ma kafin a gaya musu sunsan komai,amma ita din shekarun nata sunyi qanana da yawa a sanda akayi auren,kuma dai dama widad din gaskiya ko cikin yaran gidan nan tana cikin ‘yan ba ruwa na,gatan da qaunar dake tsakaninta da ummu ne kadai yasa ake ganin ta sangarce da yawa,amma tana da dadin zama ainun”

    “Shikenan,bari gari ya qara haske,zan shiga na yiwa ummu bayani,sai a shaidawa yaayan kafin yakai.ga fitowa,don nasan da abun ya kwana,da wuri zaki ganshi ya shigo” anty madeena dai tana dariya ta fice daga dakin.

    Tare suka shiga kitchen da anty madeena din,saidai yadda taga widad din tana hada breakfast din cikin qwarewa yasa ta tsaya tana kallonta,sosai abun ya daure mata kai ya kuma bata mamaki,widad dince da iya sarrafa abinci haka?

    “Me ya faru anty naga kina kallona” murmushi tayi tana sakin habarta

    “Hmmmm,ba dole ba,irin wannan delicious haka da ake hada mana yau,lallai aure me gyara mutum,su Aafiya suzo suyi kallo,yau widad din da ummu ke hanawa dosar kitchen yau itace da hada breakfast tsaf mai rai da motsi” dariya tayi kawai,ita kanta a yanzun shiga kitchen na daya daga cikin hobbies dinta.

    Kamar yadda daddynsu walid ya fada kuwa da wuri abban nata ya shigo da shirinsa,yana parlor yana breakfast ummu na ciki tana gyara dakin alhaji da ya tafi umra daddyn walid din ya gayawa abban komai.

    Kofin hannunsa ya ajjiye yana girgiza kai

    “Ashsha…..ashsha” sai yaja tsaki

    “Zataci qaniyarta,wanne irin shirmen banza ne wannan?,dama wannan shirmen da shashancin tazo yi mana?”

    “Har yanzu quruciya ke damunta yaaya,sai anyi a hankali” abban bai tanka masa ba,illa wayarsa daya ciro yayi kiran uncle muhsin.

    Widad kuwa batasan me akeyi ba,tana can tare da anty madeena tanta karanta mata abubuwa,da azahar saiga anty deena,kamar tayi kuka haka ta dinga yiwa widad fada

    “Me yasa kika taho,bance komai ya shige miki duhu ki gayamin ba?” Haduwa sukayi suka dinga wayar mata da kai,anty deena bata bar gidan ba sai bayan sallar magariba.

    Washegari dai taga an hau mata shirye shirye,sai da azahar anty madeena ke gaya mata gobe zasu maidata kaduna,hawaye fal a idanunta take qorafi

    “Tunda na tafi fa anty banzo ba ba’a jemin ba,kuma yanzu kwana hudu kawai sai ace na koma?ko alhaji ban gani ba”

    “Eh ai wannan zuwan da kikayi mu ba irinsa mukeso ba,ki bari kizo cikin dadin rai da yardar mijinki,babu me cewa ki koma sai idan ranki yaso” dole tana ji tana gani taja bakinta tayi shuru,sai cika kawai da take tana batsewa.

    Washegari samuel ya iso,tana ta kukanta kamar ranar za’a fitar da ita zuwa gidan miji,ita umma batulu,anty halima da anty madeena,anty deena ma taso zuwa,amma kuma a ranar mai gidanta zai dawo daga tafiya.

    *_BAYAN WATANNI HUDU_*

    *********A nutse motar ta cusa kai cikin gidan,bata saurara ba har sai data dangane da muhallin da aka tanada saboda ajiyar motoci,ya dai daita tsaiwarta sosai sannan ya kasheta,ya zare key din daga jiki yana fadin
    “Alhamdulillah”.

    Waiwayawa yayi gefansa,tana kwance,ta lafe sosai cikin kujerar tana baccinta hankali kwance, murmushi ya subuce masa,bai dauka da tace baccin zatayi da gaske shi din zatayi ba,a hankali ya sanya hannu ya zare littafin dake kife saman cikinta wanda ya fadi bayan bacci ya dauketa,yadan duba page din da take ya saka mata alama sannan ya rufe ya dorashi a gaban motar.

    Idonsa ya sake mayarwa kanta,ya zubawa baby face dinta ido,baccin da alama yayi mata dadi,ya saki murmushi,koda yaushe idan ya kalleta saiya tunata da wata wauta da quruciya data tafka,kome tayi ganinta take dai dai ne,har suyita rikici idan yace ba haka bane.

    Hannu ya saka yadan bubbuga seat din,a hankali ta bude idanunta,ta zubesu fes cikin nasa,ta kafeshi dasu tana dubansa,he look gorgeous,kaftan din da ya saka sun bala’in amsarsa,ta gani tun daga gida kafin su fito,harma ta yaba,a yanzun kuma sai ta sake gani ya mata fresh sosai

    “Yadai….” Ya fada yana dage mata girarsa cikin salon tsokana,murmushi ya subuce mata, kunyarsa ta kamata wanda a ‘yan kwanakin nan haka take ji a kansa

    “Ba komai……”sai ta saka hannu ta bude murfin motar ta fito zuwa harabar gidan.

    Iska ta shaqa tana duban harabar gidan,daga tafiyarsu last two weeks harabar gidan har ta canza,akwai datti da qura sosai,ita ke sawa a gyara duk sanda sukazo din,bayan ta karba hidimar sassan hafsat data tabbatar ko a yanzun akwai aiki jingim yana jiranta,a yanzun zuwa bauchin ya fara fita mata a ka saboda wannan dan uban aikin bautar da hafsat ke hadata dashi.

    Waiwayawa tayi zuwa inda yake tsaye,ya fitar musu da kayansu daga booth

    “Shikenan?,i have done?” Ya fada yana dubanta,narke fuska tayi sannan ta marairaice masa

    “Uncle taimako please,ka qarasa min da luggage din mana” yadda tayi maganar a mugun shagwabe yayi masifar taba ransa,tun daga wancan ranar data dawo daga gudun hijirar da tayi,ba abinda ya sake bari ya hadasu,ko riqe hannunta,wannan yasa ta sake abinta sukaci gaba da mu’amalarsu,amma ya zuwa yanzun yadda kullum taketa canzawa da koyar abubuwa masu yawa ya sanya yaji ta fara taba zuciyarsa.

    Kansa ya gyada,ya kama hannun jakar zuwa sassanta tana biye dashi tana masa hira.

    Sai daya bude mata ya saka.mata jakar yana duban sashen nata da.har abada badai kaga datti ba saidai qura

    “Can you help me?”

    “Dame uncle?”

    “Idan kin gama gyara sassanki please” murmushi ta saki,ko bai qarasa ba tasan me.yake nufi,kuma tana da wannan nufin a wannan karon,saboda magana da hajjaaa tayi mata tun wancan zuwa sun tsaka da waya

    “Za’a yi in sha Allah uncle”

    “Thank you” murmushi ya subuce mata,komai.qanqantar abu idan kayi masa sai ya gode maka,tana kallonsa ya juya a hankali ya fice,yabar mata sauran qamshin turarensa data zuqa da kyau ta fesar tana sake sakin murmushi,sannan ta taka zuwa cikin falon nata tana kallon ko ina,tare da tsara yadda zata fara aikin.

    Sassan hafsat din ya wuce kai tsaye,yana son saur nauyin alqawarin sweet daya daukarma su mimi.

    Yana dosar sashen yana jin dan tashin hayaniya,sai abun ya daure masa kai,saboda iya saninsa ita din bamai sakewa mutane bace,bata da fuskar da za’a zo gidanta a zauna ana hira haka,suma mutanen kowa ya gane don haka zaiyi wuya kaga tayi baqo.

    Yana sake dosar sashen yana fahimtar tashin sautin maganganun ba na arziqi bane,yanayinsa yadan canza kadan da fargabar abinda yake faruwa,a haka ya isa qofar falon,ya tura ya shiga da sallama,dai dai lokacin da matar dake tsaye take cewa

    “Yanzu dai ki fito da shinkafa kawai,tunda ke waye yazo gidanki ma bare ya dauka” ta buda baki zata bata amsa maganar tata ta maqale a maqoshi,tana tsaye tsakar falon,fuskarta har maiqo takeyi,kayan jikinta wari da wari ne na rigar wani lace nata da har ya fara tashi tashi saboda dadewa,sai zanin atamfa,ta yane jikinta da wani tsohon mayafinta milk color

    “Sannu da zuwa” ta fada muryarta tana dan rawa,itama matar dake tsaye dauke da wata babbar roba blue ta miqa masa tata sannu da zuwan,duka ya hada ya amsa musu,sai ya wuce zuwa dakin hafsat din kai tsaye.
    [3/16, 11:09 AM] +234 704 440 6400: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)
    *Arewabooks:Huguma*

  • Arubuce Ta Ke 65

    Arubuce Ta Ke 65

    Page 65

    “Tom…..zamu tafi” abbas ya fada yana duban qwayar idanun widad din,hannunsa zube a aljihun wandon lallausan yadinsa da aka yiwa wani irin dinkin girma.

    Daga kai tayi da nufin kallonsa,duk yadda taso ya hadiye abinda takeji a qasan ranta amma ta kasa,dole haka ta saka qwayar idanunta a tasa,dai dai sanda hawayen da take riqewa ya sulmiyo daga idanunta,maganar da zatayi ta riqe mata a maqoshi,sai ta saki kuka sosai,abind aya tilasta mata saka tafukan hannayenta duka biyun ta lullube fuskarta dasu.

    Duka idanunsa ya fiddo,ya ciro hannayensa yana matsowa inda take tsaye

    “What’s happening weedad?” Kai ta girgiza masa,saidai kukan take har yanxu

    “Noo….noo,kada muyi haka dake mana uhnnn?” Ya fadi a tausashe,sai ya sake matsawa gabanta,ya saka duka hannuwansa ya zare nata tafukan hannayen daga fuskar tata yana kallonta

    “I will be back in sha Allah…..ki daina kukan nan,yana qona ni,zuciyata tana zafi…..ko kinaso nima nayi kukan?” Ya fadi yana jin wani irin rauni da bai taba jin kamarsa ba,kanta ta girgiza amma ta gaza tsaida hawayen

    “It’s okay,i promise you bazamu dade ba,shikenan?”saita sake jinjina masa kai,haka kawai takeji wani tashin hankali da rashin sukuni a tattare da ita,sai takejin kamar zai tafi ya barta,kamar bazai dawo ba,tana jin kamar an dauke wani muhimmin sashe ne a jikinta,batasan wanne irin feeling bane wannan,tsahon rayuwarta bata taba fuskantar irinsa ba.

    Tas yasa soft handkerchief dinsa ya goge mata hawayen,sannan ya bude tafin hannunta ya saka mata shi,ya maida ya dunqule hannun nata cikin nasa,sai yaja da baya kadan yana gyara zaman rigarsa data cukuikuye yana kallonta,cikin ransa yakejin wani shauqi yana saukar masa,ganin wani yana kewarka…..ya shiga damuwa saboda zaiyi rashinka a kusa dashi……wani irin dadi kima da daraja gareshi a zuciya,wani irin yanayi da bazaice ga lokaci na qarshe daya ganshi tattare da matarsa ba,sai ya buda dukkanin hannayensa yana kallonta da idanunsa masu girma da zuwa yanzu suka rusuna,girmansu ya ragu

    “Oya…. give me a hug” jiqaqqun idanunta ta daga ta kalleshi,qaramin miskilin murmushinta ya subuce zuwa saman labbanta,a yau din sai taji bata shakkar yin hakan,ta fara takawa a hankali kamar wadda aka sakawa wani kida na musamman,yayin da idanunsa yaji sun fara narkewa a kallonta,cat walking takeyi,irin tafiyar da sai wance da wance cikin isassun mata,bai taba lura da hakan ba sai yau,ya qaraso gareshi a hankali,ta shige jikinsa kuwa gaba daya,harda qoqarin saka hannuwanta ta zagayo dasu ta bayansa,sai ya tallafa mata,ya durquso ya sakata sosai a jikin nasa,yana jin kamar ya maidata cikinsa.

    Sun jima sosai a haka kafin ta fara janye jikinta,ya danyi baya jikinsa a mugun mace yana maida numfashi,kusan minti hudu kafin ya dai daita kansa

    “Ayimin rakiya mana” kai ta girgiza tana murmushi,duka idanunsa ya bude a kanta

    “Why?”

    “Hajiya fa…..so kake ta gane ka rungume ni,sannan tun dazu muka shigo daki ni dakai fa,nidai kunya nakeji” ta qarasa maganar tana turo baki,bai shirya ba bai kuma zata ba dariya ta kubce masa,yasa hannunsa saman bakinsa ya dara kadan sannan ya janye

    “Ok, come closer” ya fada yana daga mata hannu,bata musa ba tasake matsowa,ya sukuya a hankali ya bata wani irin hot and deep kisses saman goshi da kuncinta,sannan yaja baya yana cewa

    “Na bawa Allah amanarku,ki kula da kanki” ta gyada kai a hankali,sannan ta motsa bakinta

    “A dawo lafiya,Allah ya kiyaye yasa ku dawo lafiya” lumshe idanu yayi har ya fice,ji yayi a duniya kamar ba’a taba masa addu’a ba, siririyar muryarta ta dinga masa amsa kuwwa a kunne,har suka isa airport yana wassafa wasu abubuwa da yawa a kanta.

    Kafin jirginsu yakai ga tashi yayi kiran hafsat,ko ba komai yana son ya sauke nauyin dake kansa,yanason kuma yayi magana da yaranshi,sai daya kira sau uku,ana hudu yaci sa’a aka daga,saidai muryar yaran ce,ya biye musu sukayi surutu sosai har sai da yaji ya siqe

    “Ku bawa mommynku” ya fadawa mimi,shuru na sakanni ya ratsa,sannan yaji mimi tace

    “Tace bacci takeyi” idonsa ya rufe sannan ya budesu lokaci guda, irin yadda yakanyi wajen hadiya fushi idan ransa ya baci,baya so tana saka yaransa a ire iren wadan nan abubuwan nasu,yanzu ko ba komai ta koyawa yarinyar qarya

    “Alright….idan ta tashi kuce nace ta kula daku,daddynku zaiyi kewarku”

    “A dawo lafiya daddy,ka siyo mana jirgi” murmushi ya kufce masa,yana fatan wataran dukkansu ya kaisu umara ko aikin hajjin suma

    “In sha Allah mimi na,i love you”

    “I love you too daddy” ta amsa masa,dai dai lokacin hafsat da haushi ya cikata tayi fam ta warce wayar,ta jefi yarinyar da harara

    “Uwar kinibibin tsiya,i love you too daddy” tayi maganar tana kwata muryar yarinyar

    “Koni ban fada ba sai ke,saikibishi ai uwar son uba” taja tsaki tana jefa wayar gefe,harta koma zata kwanta sai kuma taji ta fasa,ta miqe ta fada bandaki ta watsa kwaskwarima,ta fito ta fara shirin fita,su mimi kuwa kaya kawai ta fidda musu tace su debo wasu ta saka musu,gida zasu,idan sun qarasa can a samu wani yayi musu wankan, yaro ba hankali,da murnarta ta shiga dakinsu ta debo musu kayan,uwar ba tare data tsaya wani dubawa ba ta karba ta saka musu,ta hado kansu ta sanyasu a motarta suka fice daga gidan,gidan kamar mazaunin bola,saidai hankalinta a kwance yake,tasan me sanya damuwar saita gyara din baya qasar ma gaba daya,duk sanda ta samu chance ta gyara din,hankalinta yayi gidan,tana son su hadu da anty ummee taji sabbin shawarwari,tana jin kamar tafiyar ta ta fara baudewa.

    A daren ranar daya sauka ya sake kiran hafsat din don ya gaya mata sun sauka lafiya,amma harta qaraci ringing dinta bata daga ba,har a lokacin ma tana gida bata koma ba,mamarta ta sake cewa da ita

    “Shareshi,wani abunma duk laifinki ne,ace mijinka baya shakkarka me akayi kenan” .

    Yasan dai ba yadda za’a yi ya mata irin wanna kiran tace bata gani ba,kuma koda a daxun baccin take da gaske ai yaci ace tayi kiransa bayan ta farka,ransa yakai qololuwar baci,yaji kuma a ransa bazai sake kiranta ba indai shine,sai ya maida akalar kiran nasa ga widad.

    Dukkaninsu wata irin sakewa sukayi shida ita,sunyi hira mai tsaho,duk abinda tayi a yau din sai data zayyane masa shi kuma yana kwance saman gadon hotel din da suka sauka yana biye mata,a nan take bashi labarin taga tallan wajen wani koyar da girki a kaduna tanaso

    “Iyeee …. dole wai so take ta fini iya girki…… alright,zansa Samuel ya yiwa rose magana” da murnarta sosai ta shiga masa godiya,har yaga godiyar kamar tayi yawa,ita kuwa a wajenta normal ne,kamar yadda aka horeta kenan a gida.

    Kwana daya da zancan kuwa saiga rose tazo har gida samuel ya kawota,haduwar farko jininsu ya hadu da rose din,saboda tana da matuqar kirki da kuma ban dariya,wannan ya sanya saurin sabo a tsakaninsu duk da rashin saurin sabon da widad ke dashi,shiryawa sukayi ita da muneera da aka bar mata suka wuce wajen sukayi register da komai da komai sannan suka dawo gida,tun daga ranar rose ce ke zuwa ta kaita ta kuma dawo da ita gida,cikin lokaci qalilan sukayi sabo,itama tana son widad saboda kirkinta,don idan sun dawo din sai ta tsare rose ta zauna taci abinci,harma suyi hira da ita,sau tari ma idan ta gwada abinda ta koya saita ajema rose din,komai tabgwada din kuwa sai yayi kyau exactly kamar yadda ta koyo,abun yayita bawa rose mamaki da sha’awa,wata irin gifted ce weedad din.

    Ganin yadda widad din keda sha’awa girke girke,sai rose din ta ware wasu ranaku take koya mata irin girkin nasu qabilar,idan sukayi wasu daga ciki takance

    “Oga yanaso wannan” tsaf widad ta dauke wadanda tace yafiso din,ta dinga practicing nasu da kyau,har suka zauna mata,ita a karan kanta dadi takeji,tana jin dadin yadda a yanzun ta fara iya kalolin girke girke da dama, yadda ta maida hankali a kitchen yanzun bata maida haka kan karatunta ba,gefe guda ta matsawa anty deena, kullum saita qara mata bayani akan abincin ainihin qasarsu,duk da wannan dama tana ganin ummu tana yinsu sosai,saidai bata taba cewa zatayi da kanta ba.

    Cikin wata daya ta koya abubuwa da yawa ta fannin girki,ansha barna,don kullum da abinda za’a girka,saidai ta samu experience sosai.

    Tun saura kwana uku su dawo take ta practicing abinda zata dafa musu shida hajiya,sunyi hira da anty deena da anty madeena sosai,sun kuma bata shawarwari cikin hikima,ana ya jibi zasu dawo muneera ta taimaka mata suka gyare gidan tas,sukayi goge goge sosai,washegari kuma rose tace mata

    “Madam ko za’a kaiki saloon?” Fadin da rose din tayi sai ya zama kamar tuni a wajenta,tace ta kaita.

    Waje ne mai kyau da zaka yiwa kallo daya kasan sun iya aikinsu,cikin yarensu sukayi magana da rose bayan sun gama gaisawa,mutum biyu aka gamawa sannan aka kama kanta.

    Sosai matar tayi mamakin yanayin kan widad din,da kanta matar mai suna ada tace bata buqatar relaxer.

    Wani irin gyaran kai akayi mata,wanda ita kanta widad din sai data tsaya ta kalla kanta da kyau a madubi bayan sun koma gida,muneera tace

    “Wallahi matar nan ta iya gyara matar uncle,inama idan bikina ya taso nan zanzo tayimin”

    “Kizo wallahi,saina rakaki” ta fada tana sake kallon kanta dadi yana cikata.

    Isowar yammaci sukayi a washegari,kafin isowar tasu komai ya kammala kamar wata babbar mace,cikin atamfa ta shirya dinkin riga da skert,saidai ta gaza daura dankwalin sai yafashi tayi saman kanta,tana maqale jikin window din falonta har zuwa sanda motar data daukosu ta sako kai harabar gidan.

    Bin motar tayi da kallo,tana zuciyarta na bugawa da sauri da sauri,farincikin da batasan dalilinsa ba takeji yana ratsa zuciyarta,taci gaba da kallon motar har ta shige parking lot

    “Sun iso,bakiji shigowar motarsu ba?,kizo muje mu taraso” muneera dake sanya hijab dinta ta fada tana kallon widad, waiwayo tayi tana duban muneera,sai takejin kamar qafafunta ba zasu iya kaita wajen ba,ta girgiza kai

    “Kije yanzu ai zasu shigo” kai ta kada tana dariya

    “Oh,wai kunyar hajiya kenan kikeyi,to nidai nayi nan” ta fadi tana yin gaba da sauri,ta bude qofaf ta fice.

    Sanda ya shigo ta dauka zata iya dakewa,sai tsintar kanta tayi a gabansa,shima yayi tsammanin zai iya jurewa amma sai ya kasa, hannuwansa gaba daya ya bude mata,batayi wata wata ba ta fada ciki,ya maida ya rufeta gam a cki yana sauke wata wawiyar ajiyar zuciya,yayin da ita kuma ta fashe da kuka sosai cike da wani tune na shagwaba,sai ya gaza jurewa tsaiwar,ya sulale ya zauna a wajen,hakan ya bata damar zama sosai a jikinsa.*H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)
    *Arewabooks: Huguma*

  • Arubuce Ta Ke 67

    Arubuce Ta Ke 67

    Page 67

    Kusan a manne fuskokinsu yake,yanajin saukar hawayenta,amma kuma bazai iya dakatawa ba,saboda wannan ce kadai hanya guda daya zata rage masa zafi,ya gwammace yayi duk wani kalar rarrashi da zaiyi daga baya.

    Ya kusa minti goma w offsha biyar a haka sannan jikinsa ya saki gaba daya har ta samu ta qwace kanta tana masa kuka sosai.

    Da qyar idanunsa ke buduwa,yana zube a wajen yana kallonta,ta koma gefe ta rakube tana kuka sosai,saboda qirjin nata dake mata zafi,haushinsa sosai ya cikata,taji kaman ta bude ido ya ganta a wani wajen ba a nan ba.

    Sai da energy dinsa ya dawo sannan ya tattara qarfin nasa ya miqe a hankali,ta runtse ido sanda yake gyara zaman daurin towel dinsa,ya tako qafafunsa a nutse ya iso gabanta ya tsugunna dab da ita,ta qurewa bango amma baya takeson ta sake ja

    “Relax…..am sorry kinji” harara takeson balla masa amma kuma yayi mata kwarjini da yawa, maimakon haka saita maida fuskarta tsakanin qafafunta ta boyeta,tun yana tsugunne sai daya zauna sosai yana lallashi,daqyar ya ciyo kanta,ya hada mata ruwan wankan ta shiga bandaki ta fara yi,data fito sanye da zumbulelen hijabinta tana ta qunci,tace ita ba’a nan zata shirya ba,salin alin ya bude mata qofar dakin ta fice dakinta.

    Da baya ya sake komawa ya zauna yana murmushi,wani nishadi ya samu kansa a ciki,ya yamutsa sumarsa sosai kwanyarsa na dawo masa da duk wani wani second daya daya shude sanda take cikin jikinsa

    “Oh my goodness” ya furta a hankali,ko a yanzun yana iya jin qamshinta cikin fatarsa,wani irin softness jikinta yake dashi irin wanda bai taba jin kamarsa ba,ya buda dukka tafukan hannayensa yana tuna santsi da laushin gashinta,saiya maidasu ya cure waje daya zuciyarsa tana jin inama zai sake samun wannan chance din.

    Kusan awa guda ya bata a zaune a wajen yana karanta tunanin baya,da qyar ya miqe yayi wanka,amma sai ya kasa fita,ya koma falo ya zauna ya tsiri hira da hajiya,hakan kuma ita sai ya takurata,saboda abinda ya faru a tsakaninsu ba mahalukin daya taba mata irinsa,duk giftawarta idanunsa a kanta,daga qarshe ta haqura tayi zamanta a kitchen tana tsara me zata dafa musu yau da abinda zasu tafi dashi hanyar bauchi gobe,bai fita daga gidan ba sai da akayi sallar azahar sannan ya wuce headquarter din tasu.

    Daren ranar qiri qiri taqi yarda ta kwana a dakin,hajiya nata mata hannunka mai sanda, har ta fahimci bata gane ba tayi mata quru quru

    “Zan tafi hajiya,bari mu gama hada kayan naku” haka ta yita cewa hajiyan,tun tana idanu biyu.har bacci ya dauke hajiya,hakan ya bata damar yin kwanciyar ta hankali kwance saman babban bargon data dauko ta shimfida a qasa,don sun barwa hajiya gadon.

    **********K’arfe tara na safe sun kammala shirinsu gaba daya,suja farfajiyar gidan ana shiga da kayansu booth din motar da zasuyi tafiyar,widad da muneera na tsaye daga gefe har aka gama,motar nada wajen zama biyu,sai wajen zaman driver,hajiya ce ta fara shiga seat din da yake da maqotaka dana driver

    “Bazan shige ciki ba abbas saboda qafata”

    “Ba matsala hajiya yayi hakan” yana shirin yima muneera magana kan ta shiga gefan hajiya sai weedad ta fara takowa,tsaf ya fahimci abinda take shirin yi,jiya kawai dama kawaici yayi mata,a yanzun sai yayi kamar bai ganta ba,sai da tazo daf dashi ya sanya hannunsa ya riqe hannunta da kyau,baiko waiwaya ba bare kayi zaton ya riqeta din,cikin sauri ta daga kai tana kallon fuskarsa,yasha muur da kyau,baiko kallon sashen da take kamar bashi bane ya riqeta.

    Gyaran murya kadan yayi sannan ya kira muneera yace ta shiga gefan hajiya

    “Saura ki saki baki kima mutane bacci ki barta da kallon hanya” murmushi ta danyi

    “Bazanyi ba uncle in sha Allah” hannu yasa ya rufe murfin motar,ya bude seat din baya sannan ya waiwaya ya kalleta.

    Cikin sa’a itama shidin take kalla, idanuwansu suka hadu waje daya,har cikin jininsa sai da yaji wani abu mai kaifi ya saukar masa,ya kuma baza saqonsa zuwa kowanne sashe na jikinsa,ya sake dawo masa da sweet memorie dinsu na shekaran jiya,wannan ya sake sanyawa gaba daya jikinsa ya amsa

    “Shiga” ya fada da mugun sanyi,narke fuska tayi sannan ta matsa ta shige yabi bayanta,ya maida murfin ya rufe sannan ya yiwa samuel da suka saba yin tafiyar dashi magana kan ya tashi motar suje.

    Gefe daya na motar ta rakube,gaba daya fuskarta a narke take,kamar wadda ke jiran qiris ta sanya masa kuka,yi yayi kaman bai fahimta ba,sunata hirarsu shi da hajiya,har taji shurun widad din yayi yawa

    “Widad ko.tayi bacci ne?” Hajiyan ta tambaya ba tare data waiwayosu ba,sai sannan ya juya inda take zaunen,tausayi ta bashi da kuma dariya amma ya danne,suna hada ido sai hawayen da take maqalewa ya sauko,ya miqa hannunsa ya lalubo tafin hannunta,duk da yadda take faman boyonsa ya sanya shi cikin nasa,sannan a hankali ya janyota zuwa kusa dashi ya hade duk wata tazarar dake tsakaninsu sannan ya amsawa hajiyan a ladabce

    “Idonta biyu hajiya”

    “Au to madalla”.

    Tun basuyi nisa da tafiyar ba bacci ya dauke hajiya,muneera ce kawai ta rage wadda taketa game da wayar hajiyan,har a sannan tafin hannunsa yana cikin nata yana yamutsawa,santsi da laushinsa ke haifar masa da wata kasala ta daban,maqoshinsa gaba daya ya bushe,ya kalleta ta gefe

    “Bani ruwa” ya fada a taqaice,kamar jira dama takeyi ta zame hannunta daga cikin nasa,saidai kafin ta gama zamewa ya maida hannun cikin nasa,ta juyo suka hada ido ya kada mata kai

    “Zan dinga hukuntaki fa” yayi maganar can qasa da wata irin gajiyayyar murya,sai tayi narai narai da ido tana kallonsa,ya girgiza mata kai da sauri

    “Kinayimin kuka zan cinye idanun” yadda yayi maganar with seriousness ya sanya mata dan jin tsoro,sai ta kifa kanta saman cinyarsa,abinda ya sanya numfashinsa yin qaura na wucin gadi,ita kuma ta tura kanta da kyau tana son goge hawayen daya fara fita kada ya gani.

    Da sauri ya saka hannunsa ya daga fuskartata,idanunsa suna rurrufewa,bugun zuciyarsa na fita da sauri

    “Ya isa….banaso…..idan nace ki bari ki dinga cewa to,understand?” Kai ta gyada masa

    “Good,bani ruwa” a hankali ta dauko masa ruwan,duk da yadda jikinta ke rawa,shima ya lura da hakan,sai ya sakar mata hannun ya karba ruwan,ya balle gorar ya sanya bakinsa bayan yayi bismillah ya soma sha.

    Tas ya shanyeta,ya maida numfashinsa,ya juya kadan suka hada ido,tunda ya fara shan ruwan ta zuba masa ido tana mamakin yadda yakeshan ruwan,kamar wanda ya jima baiga ruwa ba,suna hada idon ta dauke kanta,ya saki murmushi,ya gama karantar komai daga qwayar idonta

    “Zo kiji” ya kirata can qasa kamar yadda suke maganar tun daxu, saboda muneera da hajiya da suke cikin motar,bata musa ba ta matso dab dashi,sai yasake hade hannayensu waje daya yana kallonta

    “Menene auratayya?” yayi mata tambayar kai tsaye,tambayar da ya jima yanason mata ita,tambayar data sakata rufe idanunta gam lokaci guda,zuwa yanzu koda batasan ainihin me yake nufi ba,daga karance karancen data fara ta fuskanci wani abune mai girma,wani babban alaqa ce babban gini da kuma qatuwar dangantaka tsakanin namiji da mace,zuwa yanxu kuma tambayar ta girmi tunaninta,ta kuma haifar mata da wani jin nauyi da kuma kunya.

    Yadda ya rutsata da ido haka tabar idanun nata a kulle,wayyo Allah kawai take fada a ranta,itadai wannan iskancin ya fara isarta,inda ya barta kusa da hajiyar da duk haka bata faru ba,sai ya saki murmushi yana sakar mata hannyenta,bai sake cewa komai ba,haka itama,a haka har baccin ya soma fusgarta,sai yayi mata makari da manyan kafadunsa,sanda baccinta ya fara nisa kwance tayi bisa kafadun nasa ba tare data sani ba,wannan ya bashi wani irin yanayi mai dadi sanda suke keta dazuzzuka,yayin da tayi wani bacci mai dadin gaske bisa kafadun nasa.

    Cikin ikon Allah suka iso bauchi lafiya,yayi yayi da hajiya ta fara sauka gidansa amma tace sammm a gidanta zata sauka,dole haka ya wuce da ita gida,sanda suka isa gidan akwai mutane,yaranta matan su uku duka suna gidan su da yaransu,sun gyare gidan sunyi duk wani abu na tarbarta,kowa kallon widad yakeyi,cikin watannin ta sake girma da cika,tayi wani fresh,abinka da farra fata idan ya samu hutu,cikin girmamawa ta gaida kowannensu,tunda dui cikinsu babu sa’arta,sun haifeta ma,qaramar cikinsu ce take ganin zasuyi sa’anni da anty deena.

    Ina ka saka ina ka aje suka dinga yi da abbas din,shima da yake mai.kirki ne kuma na mutane sai yadan zauna shima a cikinsu kusan awa daya,lokacin har maqota da sauran matan kawunnansa sun fara shigowa yuwa hajiyan barka da zuwa,kusan kowa ya shigo idonsa akan widad

    “Amaryar abbas ce?” Haka suke tambaya,kowa da abinda ke cikin ransa,ya kusa shafe awa daya sannan ya miqe da zummar tafiya

    “Dauko mayafinki ku wuce widad kinji,sannunki kema da qoqari ansha hidima,Allah yayi albarka ya bada zuri’a ta gari” baki baba usaina ta tabe,matar daya daga cikin kawunnansa,wadda suna da ‘yar alaqa da hafsat din,fuska ta marairaice wa hajiyan,qasa qasa take gaya mata

    “Don Allah hajiya a barni a nan na kwana” can qasan ranta tana fargabar yadda yake liqe mata,a yanzun baya jin shakkar tabata,idan mommy hafsat ta gani tace mata meye?,gwara tana nan din,basu hadu ba bare ta gani.

    “Yaa abbas,ka barta zuwa anjima din kamar haka takeso tace ko?” Qanwarsa ta fada wadda ke kusa da hajiya,ta kuma ji abinda take fada din

    “Idan ka fito saika biyo ku tafi,idan ma baka zo din ba zan sanya a rakota” hajiya ta qara masa bayani.

    Idonsa ya maida kan widad din data wani lafe a gefan hajiyan,suka hada ido sai ya dauke kansa,itama janye nata idanun tayi cikin ranta tana jin kamar ta tsira,ya gyada kai

    “Shikenan hajiya,a huta lafiya”

    “To Allah yayi albarka,a gaida kishiyoyina” a hankali ya juya ya fice daga falon

    “Tirqashi” baaba usaina ta fada,yaaya bara’atu ta daga kai ta kalleta

    “Baaba usaina lafiya ko?” Baki ta tabe a fakaice,amma a zahiri sai tadan murmusa

    “Ina ganin rashin kunya irin ta yaran zamani,kema banda abinki hajiya kibar masa matarsa su wuce mana”

    “A’ah gwara ta zauna a gaisa sosai,aita kwan biyu dama bataxo ba” hajiya ta amsa mata cikin bagarar da zancan,don batason dogon zance.

    Sai da suka tsaya a hanya ya sake yin siyayya sannan suka wuce gidan,ba wani zumudi ko kadan a tattare dashi,abu daya ke sanyawa yaji dokin zuwa gidan,yaransa da yayi kewarsu.
    [3/15, 9:35 PM] +234 704 440 6400: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)
    *Arewabooks:Huguma*

  • Arubuce Ta Ke 75

    Arubuce Ta Ke 75

    Page 75

    Kamar yadda ya saba ko yaushe bayan sallar asuba yana shigowa ya tabbatar da lafiyarta yauma haka

    “Gidan hajiya nakeso naje yau” ta fadi masa bayan sun gama gaisawa

    “Ba damuwa,jiya ban samu zuwa ba,ki shirya na fita dake idan zan fita anjima kadan” saita gyada kai,tana maida idanuwanta ta lumshesu,kwata kwata daga jiya zuwa yau batason zaman gidan.

    Karfe goma na safe ta gama komai a bangarenta,ta gyarashi ta hada breakfast dan dai dai cikinta,ta kuma shirya cikin atamfa dinkin doguwar riga,tana zaune a falonta tana buga game a wayarta tana jiran fitowar abbas,hatta mayafinta yana gefe.

    A nutse ya tura qofar falon,yana sanye da shadda butter color da aka tsarama wani lafiyayyen dinki me aji,a kanta idanunsa suka fara sauka,sai yayi tsaye riqe da handle din qofar yana kallonta idanuwansa suna lumshewa,tayi masa kyau har baisan iya yadda zai musalta ba,atamfar ta karbeta ainun,har ya gaza gane doguwar riga da kuma atamfa wanne ne yafi mata kyau,ya dan rufe idonsa yana shafar qirjinsa da hannunsa,yana jin tana sake saka kai sosai cikin zuciyarsa tana samun kyakkyawan mazauni,illa take masa a kowacce rana,kullum yaqi yake da zuciyarsa,yana ganin kamar ya fiya zaqewa da yawa,yanason canzata,yana son sake kawo kusancin da yafi wannan a tsakaninsu,baisan ta yadda komai zai zo ya kuma kasance ba.

    Batasan da tsaiwarsa ba,saboda hankalinta yayi gaba a game din da takeyi,sai da qamshinsa ya fara kawowa hancinta ziyara,ta daga manyan idanuwanta a hankali,idanuwansu suka sarqe waje guda,siririn murmushi ya subuce mata,ta shagwabe fuska

    “Ka tsoratani uncle” ta fada tana tura baki gaba,yabi dan qaramin bakinta da kallo,wanda yau yasha jambaki pink,hakan ya qarawa lips dinta color akan ainihin color dinsa.

    Hannu ya saka ya yafitota yana jin jikinsa na mutuwa,ta miqe a hankali tana dubansa tare da takowa inda yake

    “Uncleee…….na gama fa na dauko.mayafina?” Kasa amsa mata yayi har ta iso gabansa,yasa hannu a tausashe ya kamo qugunta janyota gabansa,suka zama very close sosai a tsakaninsu.

    A tare suka lumshe idanu sannan suka bude,suka zubawa juna idanu kamar shiri,kowa da abinda jiki da zuciyarsa ke gaya masa,ya motsa labbansa da salon miskilancin nan nasa

    “Kinyi kyau baby doll” murmushi ya kubce mata tana kallon manyan idanunsa da suka qara masa kyau a idanunta,kafin tace komai sautin muryar hafsat ta tunkarosu,da alama sassan take nufowa,tana ta hayagaga da mimi da nawwara,sai ka dauka wasu manyan ‘yammata ne.

    Hannunta ta sanya da sauri ta zare hannayensa daga qugunta taja da baya,idamunsa a lumshe yana jinta,sai data matsa ta tsaya daga can baya sannan ya bude idon nasa fes a kanta yana kallonta

    “Meye hakan?”

    “Mommy” ta fada a tana yin narai narai da ido, kafin ya bata amsa hafsat din ta iso cikin saurinta kamar me shirin tashi sama,amma ganinsa a tsaye daga bakin qofa goye da hannayensa yana kallon ciki ya sauke mata duk wani fada da cin mutunci da tazo yiwa widad din nayin rana batazo tayi shara ba balle wanke wanke.

    Ta gefansa ta raba ta shiga ciki,da widad din ta fara cin karo,wanda ke tsaye rataye da qaramar jaka a kafadarta tana qoqarin yane kanta da kyakkyawan mayafin daya dace da kayan jikinta.

    Zuciyarta ce ta tsinke da irin kyan da yarinyar tayi,zuciyartata ta fara rawa,ta kuma fara ayyana mata tsaiwar da yayi widad din yake kallo,saita tsaya cak,ta fara raba kallonta tsakanin fuskokinsu su biyun,gabanta yana luguden faduwa.

    Fes yake kallon widad din kansa tsaye ba tare daya nuna kara ko alkunyar wanzuwarta a wajen ba,abinda ya sake dimautata kenan,bakinta har rawa yakeyi sanda jefa musu tambaya kamar wasu ‘ya’yan cikinta

    “Ina kuma zaku da safen nan…..naga har kun shirya” maganar ta ta tuna masa inda zasu,ya sauke hannayensa dake goye a qirjinsa yana daukar mimi da tafi kusa dashi ya juya zuwa waje yana cewa

    “Ki sameni a mota,rana tana yi” da kallo hafsat din ta bishi har ya fice,saita dawo da dubanta ga widad,kamae zatayi kuka saboda wani malolon kishi daya riqe mata wuya

    “Izinin wa kika nema da zaki shirya fita unguwa?kin fara rainani fa widad,ki shiga hankalinki” karon farko da taji maganar banbarakwai,tunda dai ita ce mata akayi ta tambayi abbas ne a duk sanda zata fita bawai hafsat ba,to amma tana jin shakkarta ba zata iya tsaiwa mata bayani ba,don batason fada ita sam a rayuwarta.

    Hon din motarsa ya hana kowa a cikinsu magana,da wannan yake maka sign idan yana jiranka,duk da haka sai hafsat din ta kalli widad a gaggauce

    “Ina zakuje?”

    “Gidan hajiya”

    “Shine kika saka wadan nan kayan?,bana gaya miki ki dinga killace kanki ba karki bari ya dinga ganin tsiraicinki?” Ta fafa gajiya da soki burutsun hafsat,ita kawai so take taga ta fita a gidan

    “Aiba haram bane,tunda miji da mata ne ni dashi” ta amsa mata ba tare da kawo komai a zuciyarta ba,tunda dai tasan da wannan salon anty madeena tayi mata bayani.

    Mummunar faduwar gaba ta saukar mata,yaushe yarinyar ta fara fahimtar kalmar MIJI da MATA?,lallai akwai qura,liqi yana shirin balle mata kenan,kasa ce mata komai tayi,saita juya kawai ya fita,widad din ta bita da kallo,akwai abubuwa da yawa.na mommy hafsat din dake bata mamaki,takowa tayi ta kulle sassan nata ta wuce zuwa motar tasa.

    Ranar wuni tayi ta kasa zaune ta kasa tsaye,daga qarshe ta dauka waya ta kira anty ummee don ta labarta mata,kiran duniya wayar taqi tafiya,sai taji tana ds buqatar fita taje gidanta zaifi mata sauqi,wannan ya sanya ta yita kiran abbas ta gaya masa zata fita amma bai dauka ba,ashe yabar wayar cikin mota.

    Ta kuwa cika tayi fam,zuciya ta dinga raya mata suna can suna holewarsa da yarinyar,lallai biri yayi kama da mutum,ba banza ba yarinyar ke iya kallon qwayar idanuwanta ba ta maida mata magana haka gatsal.

    Ji tayi kamar ta rataya mayafi ta fice abinta,to amma tana shakkarsa,tasan ko zai dauki komai banda wannan,bazai lamunta ba,haka tana ji tana gani ta haqura da fitar,taci gaba da kiransa amma saita daina shiga ma daga qarshe.

    Basu dawo ba sai dare,suna isowa kuma fa shige sassanta ta kulle abinta,abbas din ya bita da kallo, quruciya har yanzu taba dawainiya da ita ba ruwanta da zancan yau kwananta nw,baya mantawa akwai ranar da a gaban hafsat din ya zolayeta akan a sassansa zata kwana,kamar zata hadiyi zuciya haka hafsat taji amma ta dake tana tuna wasu daga cikin karatuttukan anty ummee,ta dake tana tayashi tsokanartata akan anan zata kwana, qarshe sulalewa tayi ya gudu abinta.

    °°°°°°°Tun daga wannan ranar ya zamana fiye da rabin weekend dinta agidan hajiya takeyi,wani lokacin tun a hanya taje cewa ya wuce da ita,sai ya wuce gida bayan ya ajjiyeta,baya musu, saboda hakan shi kansa yana faranta masa rai,saboda yadda take nunawa hajiyan qauna da kulawa,ita kanta hajiyan hakan yana mata dadi,don duk sanda widad din tazo saita gaji da kala kalar girki,saiya zamana shi kansa zaiyiwu wuya baka sameshi a gidan ba,a nan zaici abincin rana har na dare,kai wani binma da safe yake fitowa da jallabiya yazo yaci breakfast ya koma hafsat din na bacci,idan taga bai nema abinci ba saita share taci gaba da sabgarta tana ganin sauqi ta samu.

    Abu daya ke qonawa hafsan rai,yadda widad din ke guduwa tana barinta da tulin ayyukanta,tuni ungulu ta koma gidanta na gargajiya,qazanta sai wadda ta qaru,saboda gyaran weekend din data qwallafa rai akansa yanzu ba samuwa yake ba,idan widad ta shigo gidan sai daren da ana ya gobe zasu koma kaduna.

    *_MAFARI RAYUWA DA SOYAYYA_*

    Tun daga daren jiya daya daukota daga katsina gidan mahaifiyarta,har kawo yanzun da yake shigowa gidan jikinsa gaba daya baya jin dadinsa.

    Ya jima a parking space bayan dawowarsa daga aiki,yana zaune cikin mota,shi bai shiga ba shi bai fita a motar ba,daga nan inda yake yana iya jiyo daddadan qamshin turaren wutarta daya zama tambarinta,qamshin da duk sanda zasu bar kaduna zuwa bauchi yake kewarsa,haqurinsa ya fara gazawa,yana dab da hanata weekend gidan hajiyan,tunda ko ba komai idan tana gida,iya qamshinta kawai na saukar masa da nutsuwa.

    Cikin tattara qwarin gwiwar sa ya buda murfin motar ya fito,dai dai sanda ake qwala kiran sallar magariba a garin kadunan,sanye yake da uniform dinsa masu matuqar daraja da kuma qara masa kwarjini,yana iya hangen mai gadin gidan amma ya ratse yayi kaman bai ganshi ba,saboda yana jin kamae qafafuwansa ba zasu daukeshi ba.

    Da sallam ya shiga parlor din,dai dai sanda take fitowa daga kitchen dauke da wani tray data jera lemon zobo da abarba data koya ta gwada,ya kuma bata ma’ana sosai har fiye da yadda ta zata.

    Murmushi ne shimfide saman fuskartata,batasan dalilin da ya sanya kwata kwata batajin dadin gidan ba har sai sanda ya dawo,yayin da abbas din ya zube mata.manyan idanunsa yana kallonta,qafafunsa.na sakeyin laushi kamar bazasu iya daukarsa ba.

    Sanye take da wata baqa wul din gown wadda kwata kwata tsahonta iyakarsa qasan gwiwarta,hannunta gajere ne don kana iya hangen hammatarta da kuma tundun qirjinta da cikar da suka fara yasa suke bayyana kansu.

    Kanta babu komai sai lallausar sumarta baqa sidik mai laushi data yiwa kalba guda daya tak a kan nata,jelar ta sauka gadon bayanta taba reto,zata tsammaci relaxer ta sakawa kan nata.

    Tray din ta ajjiye,saita fara takowa gabansa tana juyawa gaba da baya

    “Uncle kalla ka gani,nayi kyau?,don Allah kwalliyata ba tayi kyau ba?” Ta fada bilhaqqi har cikin ranta tanason yace tayi kyau din,saboda ire iren kaya ne da mamarta mahaifiya ta hada mata su masu yawa da kyan gaske bayan ziyartarta da tayi,tsaraba tayi mata mara iyaka,don bata samu halartar bikinta ba,hasalima sai ana gobe daurin auren widad din ta sani,wannan yasa tayi fushi kwata kwata ta koma gefe,saidai zuwantan yasa tayi mata kyakkyawar tarba,ta kuma hada mata nau’in dukka wani kaya da tasan uwa zata yiwa diyarta,ta hada da nasiha mai kama da hannunka mai sanda

    “Kar na sake jin sirrinku ya fito keda mijinki,idan ba haka ba zamu bata dake,kome ya umarceki kiyi kiyishi indai kinaso muci gaba da shiri” a duniya idan akwai abinda ta tsana wani yace sun b’ata,waninma mahaifiyarta da take mata wata irin qauna take jinta har ranta.

    Bai ankara ba har ta iso gabansa,juyi daya tak tayi ta fada jikinsa,sai ta riqeshi tana dariya dariya

    “Uncle…..ba kace wannan rigar ba zata yimin kyau ba?,shi yasa itama na gwada maka ka gani…..bakace komai ba” ta furta tana tsareshi da ido.

    Tuni maqoshinsa ya bushe,ya tattaro yawu ya hadiye yana dan ja da baya

    “You look so good baby doll” dan tsalle ta saki a jikinsa tana cewa

    “Thank you uncle” cikin dabara yadan ja baya yana zare jikinsa saboda yadda yaji jikinsa ya fara dauka gaba daya,saita sake matsowa ba tare data lura da yanayin da gake ciki ba tana karbar jakar hannunsa

    “Sannu da zuwa,na manta” ta fadi tana dariya sannan tayi gaba tana cewa

    “Yau wani kalan abinci nayi maka,mommmy ce ta koyamin,tace irin abincinmu ne idan mun dawo nayi maka” duk maganar da takeyi yana tsaye cak yana kallon yadda qugunta yake juyawa ta cikin rigar,kusan rabin bayan rigar an debeshi,farar fata cikin baqar riga……abun ba qaramin qaawa yake bayarwa ba.

    Kasa riqe kansa yayi,har jikinsa yake jin bazai iya jurewa ba,saiya ja baya a hankali ya fice daga falon salin alin,sai waiwayowa tayi taga wayam,mamaki ya cikata,tahau kiran sunansa tana leqawa dakinsa,har nata dakin zuwa kitchen bashi anan,saita koma saman kujera ta zauna tana hawaye,me yasa zaiyi mata haka?,ta gama wahalar shirya masa abincin kuma kawai saiya fita bai gaya mata ba?.

    Tana qananun hawayenta ta miqe ta shiga daki itama ta daura alwalar sallar magariba ta tada sallar,tana sallar tana goge qwalla.
    [3/17, 1:28 PM] +234 813 343 4840: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)
    *Arewabooks:Huguma*

  • Arubuce Ta Ke 62

    Arubuce Ta Ke 62

    Page 62

    Tun jiya da ya kirata yace mata gobe zasu taho da hajiya,tayi murna sosai saboda zaman kadaicin ya isheta amma bata kawo wai ta tanadi komai ba,ta dauki littafinta taci gaba da karatunta,tana tsaka da karatun taga inda jarumar littafin ke shirye shiryen dawowar mijinta daga tafiya,abun sai ya burgeta sosai,ta idar da sallah azahar tana saman abun sallah abun ya sake fado mata,saita dauki wayarta ta kira anty deena tana labarta mata

    “Kema irin hakan zakiyi, bakiga abincin da aka kiya jiya ba a group?” Kai ta gyada

    “To haka zakiyi,ki shirya shi kamar yadda aka koyar ana shirya abincin mutum” daga kan abun sallar kuwa bata koma yin komai ba ta fara practicing abincin,datayi kuma yayi mata yadda takeso,suna da komai ba abinda zata buqata,saita fara shirya komai tun a ranar.

    Washegari gari yana yin haske ta gyara gidan,dama ta saba wannan ya fara zame mata jiki,saidai yau har dakinsa ta gyara kamar yadda anty deena tace mata,tana yi tana kiran anty deena ita kuma tana qara mata haske,tana aikin suna video call da anty deena ta watsapp,sannu sannan sai gashi har girkin ta gamashi tsaf,ta kuma zuba a warmer,ta jera,anty deena ta kalla ta cikin wayar,cikin farinciki tace

    “Well done qanwata,yanzu saura abu daya” langabe kai widad tayi

    “Allah anty na gaji sosai”

    “Aikin gama,sauranki wanka,ki dauko kayanki na zuwa gidan biki ki saka,yau duka kayan kwalliyarki ki juyesu a fuskarki” ido widad ta zaro tana dariya

    “Kai anty….suna da yawa fa” dariya itama tayi

    “Ai wai ina nufin ayi kwalliya da kyau,a saka turaren gida dana jiki ako ina” dan turbune fuska tayi

    “Wai anty duk uncle akewa haka?”

    “Kai,ai yafi gaban haka ma,ba kinje min litattafai kika samu kina karantawa ba?,bakiga yadda akeyi bane?” Batason tacewa anty deena din eh,saboda wasu guraren cikin litattafan kunya suke bata(tsarkakakkun litattafai wadanda babu batsa a ciki sai qaruwa),kai ta gyada mata a kunyace

    “Good,maza kije ki shirya to” cewar anty deena,daga haka suka katse kiran,ta dauki wayar ta wuce bedroom dinta,tana tafe tana hangen dining din kamar wani zai bata mata aikinta,saidai murmushi kawai takeyi najin dadin yau ta qure adaka tayi abinci,gidan kansa yadda yau ta gyarashi ita da kanta yana bata mamaki.

    Sai data bata lokaci a daki tana zaben kayan da zata saka,anty deena dai tace mata atamfa,ita kuma babu abinda tafiso irin doguwar riga abaya,don kusan kullum itace shigarta,kamar kuma sunsan zabinta sun sakota da yawa sosai a lefenta,tana kallon abayar ta haqura,ta ciro atamfa riga da skert,blue black mai adon maroon,sannan ta shige bandakin ta hada ruwan wanka ta fara wanke jikinta.

    Tana wankan tana ‘yan waqe waqenta qasa qasa,saboda yau din nishadi takeji cikin ranta,ta gama cuda jikinta ta shige asan shower ruwan yana ratsata,saita tuna gida,ummu na hanata shiga shower saboda wasa takeyi da ruwa, kuma tana jiqewa har kanta ne,sumarta nada tshao da yawa,yawancin lokaci saidai a saka hand Drayer a busar mata da ita,saita saki murmushi,tana jin ba dadi cikin ranta,ko sai yaushe zata ga ummu?,bata tabq zato a rayuwarta zatayi nesa da ummu har haka ba ta kuma haqura ba.

    °°°°”alhamdulillahi” hajiya ta fada tana fitowa daga motar bayan tsaiwar motar tasu a farfajiyar gidan,murmushi abbas yayi

    “Yau gaki a kaduna dai” sai tayi murmushi

    “Eh nufin Allah kenan” yana janye da trolly dinta, muneera na dauke da jakar hannunta suka doshi sashensu.

    “Assalamualaikum mutan gida” hajiya ta fada tana murmushi idanunta cikin falon,wani boyayyen ajiyar zuciya abbas din ya sauke,saboda hango warmers da yayi saman dining din,uwa uba yadda fakon yake a tsaftace ya qawatar dashi,duk da dama bai tana ganin wani abu na qazanta ko qanqani a tattare da ita ba,hasalima yana mamakin yadda bata son taji ta taka datti

    “Ki zauna hajiya,inajin tana daki” ya fada yana janye mata pillow din kujerar,tayi bismillah ta zauna,haka kawai taji ranta yana mata dadi,ya juya ya dubi muneera

    “Ki samo muku ruwa da lemo”

    “Aah,bari dai matar gidan ta fiti tukunna ta shaida xuwanmu ko?” Murmushi abbas yayi

    “Peace maker” shine sunan da sau tari yake kiran hajiyarsa,bata qaunar tashin hankali ko kuma husuma ko kadan.

    Kayan daya gani baje saman gado yasa hankalinsa yadan tashi,bai kuma ji motsinta ba,ba tare da tunanin komai ba ya murda handle na bandakin ya tura ya sanya kansa.

    Dai dai lokacin da take tsaye babu komai a jikinta,sai towel a hannunta tana tsane gashin kanta,mugun zabura tayi ta kuma tsorata matuqa,saidai data waiwayo suka hada ido sai taji kamar zata narke a wajen,saboda tsorata saita jefar da towel din,ta kuma sulale a wajen ta duqe tana cure jikinta waje daya,ko ina na jikinta rawa yakeyi,take ta fash da kuka.

    Shi din ma kamar an jona masa lantarki haka yaji,ganinta a hakan ba qaramin al’amari bane a zuciyarsa da kuma gangar jikinsa,ya rintae idanunsa ya koma baya days saut yana mayar da qofar yadda ya ganta,saidai ya kasa sakin hannun qofar,yayi tsaye riqe da handle din yana maida mumfashi.

    A hankali yaci gaba da sauke jumfashun nasa ta baki data hanci,ya bude idanunsa a hankali yana jiyo sautin kukanta,yasan yau kam ya taro match,sai ya matsa jikin qofar cikin kasala yace

    “Am sorry” shuru bata amsa masa ba,sai ya sake daga murya

    “Am very sorry” cakin muryar kuka tace

    “Kana sane ka budeni,ai kasan wanka nakeyi” murmushi ya saki tsigar jikinsa na sake zuba a,daga dawowarsa ta masa wani irin kunnawa da yasan bashi da maganinta

    “I swear bansan kina ciki ba…..am sorry…. please kiyi shuru mana”

    “Allah tunda ka ganni tsirara bazan yadda ba” ta fada bayan ta miqe tana daura towel dinta da sauri,tana tsoron kada ya dawo.

    Murmushi mai kama da dariya ne ya kubce masa,shagwabarta tana kasheshi ainun

    “To shikenan,let me come inside,sai na cire kayana kema ki rama,kinga shikenan anyi one one”

    “Wayyo ummuna….Allah karka shigo,idan ka shigo saina gayawa ummu” ta fada tana gunjin kuka jin yana taba qofar kama zai bude,dariya sosai ta kamashi har sai daya dan sunkuya

    “Alright…..alright,shikenan,khalas…..ya isa,am sorry,ki qarasa ki fito,hajiya na falo tana jiranki” ya danja da baya har yanzu fuskarsa murmushi ne kwance akai ya baro dakin,gaba daya bacin ran daya taho dashi babu kaso hamsin cikin dari.

    Da sauri ta miqe ta qarasa wankan jin cewa hajiya ta qaraso,ta shirya a gurguje,bata saka komai kan fuskarta ba,saisai jikinta ya wadata da turare,sanon turare ne ta bude cikin kayan lefenta.

    Rungume hajiyan tayi abinta tana jin dadi,sai take ganin kamar ummunta ce tazo,ta ma mance dashi a wajen,suna gama gaisawa ta gabatar mata da lemuka da ruwa

    “Hajiya na kawo miki abinci?,ni na girka da kaina” ta fadi tana murmushi,ta qagu taci taji me zata ce,dariya tayi

    “Bari nayi sallah tukunna widad,nunan bandaki”

    Dakinta ta kaita ita da muneera duka harda kayansu,sukayi sallah sannan suka dawo falon ta fara zuba musu abincin,a sannan abbas daya fita salla masallaci bai dawo ba.

    Hankali kwance suke cin abincin suna hira,duk yau sai widad takejinta free kamar a gida,babu wanna kadaicin ba komai,har suka gama bai dawo ba,sukaci gaba da hirarsu hajiya na jinsu,yanayin da taga widad yayi mata dadi sosai,saboda ta qara wani irin haske akan wanda take dashi,hakanan ta murje sosai,duk da ba qiba tayi ba,amma fatarta tayi kyau.

    Yamma liqis ta sake shiga kitchen ya gwada yin tuwo miyar kubewa,tanata taraddadi kada tayi kwaba,cikin ikon Allah sai gashi tayi shi fes,abinda ya faranta mata ranta,ta gama suka gyara kitchen din,muneera tayi mata wanke wanke sannan ta gabatarwa da hajiya bayan sunyi sallar magariba.

    Farincikin da hajiyar ta tsinci kanta a ciki ba dan kadan bane,zata iya cewa kaf rayuwarta bata taba cin.abincin gidan abbas din ba sai wannan karon,karamcin da yarinyar ta nuna mata ya qara dad’ad’a abincin a bakinta,ya kuma qara mata qaunar widad din a zuciyarta.

    Tana ta so tayi wanka amma kuma sai takejin nauyin hajiyan, saboda ba zata iya tube kayanya cikin dakin ta shirya ba,sai ta basar kawai sukaci gaba da hira abinsu.

    Ana idar da sallar isha’i dukka suna falo,a sannan yayi sallama ya shigo,hannunsa dauke da leda,dukkan alamun gajiya sun bayyana a tare dashi.

    Kusan a tare sukayi masa sannu da zuwa,ya amsa yana zubewa gaban hajiyan yana mata barka da dare

    “Ina ka shiga haka?,tun dazu nake taraddadi”

    “Wallahi na leqa office ne,akwai ayyukan da nakeso na rufe file dinsu kafin mu wuce,kuma zan dauki excuse ma.na tafiyar tamu”.kai ta jinjina

    “To Allah yayi.jagora ya dafa”

    “Ameen ameen hajiya,kunci abincin dare?” Sai da tayi murmushi sannan ta amsa

    “Munci abinci kuwa,tuwo ma,mun qoshi kuma alhmdlh”

    “To ma sha Allah” ya fada ransa na masa fari,bai taba zaton zai tadda hakan ba,ya saci.kallonta kanta yana a qasa tana wasa da zaren dankwalinta,har yanzu haushinsa takeji,kunyarsa kuwa kamar ta bace a wajen,musamman idan ta tuno a yadda ya ganta,ko ummu bata zaton ta taba ganinta a haka da wayonta.

    “Na gaji fa sosai,inajin kwanciya zan shiga nayi” hajiyan ta fada tana miqewa,sai muneera itama ta miqe,don itama a gajiyen take

    “Ya kamata”

    “To Allah ya bamu alkhairi,sai da safe” tayi musu sallama suka wuce dakin ita da muneera.

    A hankali ya tattaro dukka.hankalinsa a kanta,ya xuba mata idanuwansa yana kallon ta,da gaske ba zata kalleshi ba,har yanzu baku dankwalinta yana hannunta tana ta murzasu,cikin sakanni jikinta ya bata saqon cewa ana kallonta, tasan kuma shine,saboda rashin wanzuwar motsinsa kadai ya isa amsa.

    Dan daga kai tayi,sai suka hada idanu, karon farki taji ba zata iya jurewa ba,ta saki gefan mayafin ta yunqurq zata miqe

    “Ina zuwa?” Ya jefa mata tambayar,qeya ta juya masa,ya kuma tura baki gaba

    “Zanje na kwanta,nima baccin nakeji” yadda tayin ya bashi dariya,amma ya maze

    “Haka zaki tafi ki barni,ni baki bani abincin ba yuwa nakeji” ya fada yana karyar da wuya kamar qaramin yaro,shi kansa baisan yayi hakan ba.

    Dan jim tayi,sai maganar anty deena ta dawo mata

    “Idan ummu taga yayi miki ba dai dai ba ko nuna rashin kulawa,kinsan zataji babu dadi ko?,to kema idan kika masa hakan hajiyarsa ba zataji dadi ba” da wannan tunanin ta juya zuwa dining area don kwaso masa abincin,yabi bayanta da kallo,sosai skert din ya zauna mata das das,ya fidda qugunta dake juyawa sanda duk tayi taku,kamar da gayya takeyin hakan,ya janye gajiyayyun idanuwansa a hankali ya lumshesu yana furta kiran sunan Allah.
    [3/13, 12:54 PM] +234 813 343 4840: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)
    *Arewabooks:Huguma*