Auren Shehu Book 1Hausa NovelsHausa Novels

Auren Shehu Book 1 Page 2

Sponsored Links

AUREN SHEHU

Biyu

***

Kamar ta san abin da ta ke ayyanawa cikin ran ta, ta na mai duban idanun ta ta ce

“Falmat na yarda da ke, Amma ki sani matukar na ji wannan maganar ta zaga wajan Ammy ke zan tuhama..”

Cike da nuna rashin gaskiya Falmat ta shiga girgiza kai tare da fadin

“Kin san dai ni mai rufa mi ki asiri ce Halitta, amma wannan abun da ki ke shirin yi ba daidai ba ne, ki tuna fa Dady ya ce ko saurayi bai yarda mu kula a waje ba ko mu kawo masa gida ba tare da yana da masaniya akai ba, Amma yanzu kin shirya dan baya nan ki ce mu yi karya ki ga namiji Halitta?”

Hannun Falmat ta saki, ta na mai dafe kai ta furta

“Ya Ilahi! Ya iIlahi! Ya Allah ga Falmat! Dalla wa ya ce ma ki zance zan yi da shi? Kawai fa yi za mu yi kamar za mu fita ne idan Allah ya sa yana waje sai na ?an gan shi…”

Cike da mamaki gami da tausayin halin da yar uwar ta ke ciki Falmat ta zura mata idanu. Ganin haka Halitta ta kara da

“Haba mana yar ?anwa ta, in ba ki taimaka min ba wazai taimake ni? Kin san dai Yakura is a snob, ji da kanta ba zai bari ma ta saurare ni ba balle ma taimaka min sai dai ma ta tona min asiri idan dai wannan ce, please Falmat! Zan baki wannan abayar tawa da ki ke so”

Jin batun abaya sai ga Falmat ta mike tsaye, ta ce

“Da ga yau shikenan gaskiya ba zan kara yin karya dan kawai ki ga Usman Mai gadi ba Halitta…”

“Usman! Sunan shi Usman ba Usman Mai gadi ba”

Halitta ta gyara mata cikin jaddadawa. Fita Falmat ta yi tana mitar kar Halitta ta takura mata wallahi sai ta fasa raka ta. Haka ta lallaba ta, bayan ta ?auko mayafin ta, su ka yiwa Ammy karyar za su je gidan wata kawar Falmat, dan kuwa cikin su Falmat ce kadai mai kawa a cikin unguwar. Sai da Ammy ta yi mitar dama jira su ke Malam ya tafi su sami kafar yawo, tare da kashedin kar su dade sannan su ka kama hanya.

Tun da su ka kama hanyar fita gaban Halitta ke faduwa, fatan ta Allah ya cika mata buri ya sa Usman na nan farfajiyar gidan. Ai kuwa su ka ci sa’a can kusa da gate ta hango shi tare da abokin gadin shi. Zaune su ke bisa teburi ga ledar dafaffiyar gyada gaban su, suna afawa a baki su na hirar duniya.

Tun da ya hangi fitowar su idanun sa ke kan su, kokari ya ke ko zai iya gano wacce ta diro daren jiya cikin su. Sam Halitta ba ta lura da yanda ya saka mu su Ido ba domin kuwa ta yi kasa da na ta idanun tun fitowar su, Falmat ce dai ta ke kokarin kare masa kallo tun daga nesa ta na mai mamakin yanda yayarta ta fada ma san dankauye irin shi. Ganin yanda ya tsura musu ido Falmat ta ja tsaki

“Mtsw ashe ma mayen kallo ne! Ji fa yanda ya tsura ma mutane idanu sai ka ce mujiya! Wallahi ya ci sa’ar ki da sai na tsawatar masa!”

“Kai Falmat ke da wani ido ki ka san ya na kallan ki? Bare kuma ai ban da burin da ya wuce ya lura da ni nima………..”

“Hajiyoyi za a fita ne?”

Cewar abokin gadin Usman yayin da ya tashi ya nufi gate din gidan domin bude musu kofa.

“Eh sannun ku da aiki”

Falmat ta furta ta na mai kai kallon ta ga Usman wanda fuskar sa ke ?auke da fara’a, haka ma Halitta wacce tunda ta sauke idanun ta bisa fuskarsa mai kwarjini da dumbun annuri gaban ta ya shiga faduwa.

“Toh Allah ya dawo da ku lafiya”

Ya fada sa’ad da ya bude kofar ya na jira su fita ya kulle. Ganin yanda Halitta ta yi kasake ta na duban shi ya sanya shi fadada fara’ar shi, cike da girmamawa ya sunkuyar da kai alamar gaisuwa, ba Halitta ba hatta Falmat sai da hakan ya burge ta, ganin Halitta na shirin ba da su ya sanya ta jan hannun ta su ka yi waje ta na fadin

“Amen Isa, godiya mu ke”

Isa na mayar da kofar gate ya koma wajan zaman shi ya zauna, tare da fadin

“Ina ruwan Falmat, ‘ya’yan Malam ne ai, kila ba za ka san su sosai ba saboda ba sa fita, in za su fita kuma fuskarsu kullum a rufe, na yi mamaki ma yau ka ga ba su rufe ba”

Kai Usman ya gyada masa da ke mutum ne da be fiya magana ba, tunanin Falmat ya ke dan ko shakka babu ita ma ta yi kama da wacce ta diro daren jiya, sai dai kuma yanayin kibar Falmat ce ke karyata ita ce din. Duk da waccar hijabi ne jikin ta har kasa, Amma ba ya Jin ta kai Falmat kiba. Nisawa yayi kafin ya furta

“Isa ina da wata tambaya domin Allah”

“Ina jin ka”

Cewar Isa ya yayinda ya bare gyada ya afa a baki.

“Shin Malam ya na da ‘ya’ya mata da yawa ne,?”

“‘ya’yan sa uku ne, wannan biyun da ka gani, sai guda, ita ba ta fiye zama a gida ba, jami’ar kwana ta ke ai”

Isa ya amsa masa zuciya daya ba tare da ya kawo wani abu cikin ran sa ba. Shiru ne ya biyo baya, Isa bai fasa cin gyadar sa ba, shi kuwa Usman zaton shi ne ya tabbata, Zainab ita ce diyar Malam da ya gani jiya ta hauro kan katanga.

‘ita ko wannan Bingel me zai sa ta haura katangar gidan su tsakar dare haka?’

Tambayar da yayiwa kan sa kenan, ji yayi duk duniya be da muradin da ya wuce ya san musabbabin wannan lamari na diyar Malam.

Halitta kuwa tun bayan fitar su take washe baki kamar wacce aka ma bushara da gidan aljanna. Ba ta bari sun dade gidan da su ka je ba ta ringa azalzalal Falmat su tafi gida, dan kawai su dawo ta kara ganin shi. Su ka yi rashin sa’a kafin su dawo Usman ya tashi sai Isa kawai su ka tadda. Haka ba yanda ta so ba su ka wuce ciki.

Dakin ta tayi kwance, bayan ta sallami Falmat da abayar da ta yi mata alkawari. Da kwanciyar ta ishe ta ne ta leka account din ta na Instagram, nan ta ci karo da hotunan Zainab na club, tun tana dauke kai har ta kai hotan da tayi tsakiyar maza ta na busa hayakin shisha, ka na gani ka san sababbiya ce a harkar. kasa zama ta yi, zuciya na zafi ta tashi ta nufi dakin ta.

Kai tsaye ta bude kofar dakin ta shiga batare da ta buga mata ba. Bisa gadon ta tarar da ita ta yi kwanciyar rub da ciki, sanye cikin wando “bump short”, da yar riga wacce ko cibiya bai rufe mata ba. Ba komai ya dauki hankalin Halitta ba face wata yar zanen fulawa da ta gani kugun Zainab, dab da mazaunan ta, ta na mai tafa hannu ta furta

“Innalillahi wainnailaihi ilaihi rajiun Mai Zan gani jikin ki Yakura kamar Tattoo?”

Jin maganar kamar daga sama ya sanya ta sakin wayar hannun ta ta tashi zaune da sauri ta na duban Halitta.

“Haba Halitta! Ya za ki shigo min daki haka ba sallama! In aka yi magana you claimed Ustaziya ke diyar Dady! Yes Tattoo ne jiki na so what?”

“Tattoo fa Yakura? Ki na diyar musulmai ki yi tattoo? Ba ki ji tsoran tsinuwar Allah? Yanzu dan Allah idan Dady ya gani ya ki ke tunani zai ji….?”

“It’s not meant for Daddy’s view shi ya sa na yi shi kusa da ass dina ok?”

Cewar Zainab ta na mai sake nunawa Halitta inda zanen tattoo din ya ke. Halitta kamar za ta yi kuka dan takaici. Zainab kuwa ko a jikin ta, sai ma ta kara mata da yi da

“Toh dan ma na yi tattoo na kafirta ne? Tsinuwar Allah kuma ai tsakani na da Allah na ne, bare ke da ki ke claiming ki na tsoran tsinuwar Allah na ga ai kina make up once in a while, kuma in za a zana mi ki gira sai an aske….”

“Auzubillallah! Allah ya tsare ni da aske gira, ban taba ba, kuma ba zan taba ba in Sha Allah”

Halitta ta katse ta. Komawa ta yi, ta yi irin wannan kwanciyar ta rigingine, ta na duban Halitta ta ce

“An yi rashin sa’a ban sami wanda su ka iya permanent one ba ne, wannan iyakan sa shekara daya, Amma ya na gogewa zan fita US a yi min permanent, after all jiki na ne ba naki ba, oya me ma ya kawo ki daki na?”

Shanye bakin cikin da ya taso mata cikin ranta ta yi, wayyar ta ta daga mata, nan hotan nan ya bayyana a idanun Zainab, Halitta ta ce

“Wannan wani irin shiga ne Yakura? Yanzu har kya iya zama cikin maza da wannan shigar ta ki? Har ki dauka ki sa a social media? Kuma ki na busa hayaki Yakura! You smoke? You are smoking in the picture! Me mutane za su yi tunani akan Dady muddun su ka san ke diyar shi ce?”

Zainab na kallan ta irin kallan nan na hadarin kaji ta ce

“Wai ke Haliita ba za ki fita harka ta ba? It’s my life, my personal life! Ko kin ga na sa sunan Dady jikin sunana? Ina ruwan Dady da rayuwa ta a waje? Cikin gida na ke diyar sa, ina shiga irin wanda ya ke so a cikin gida in da ya ke gani na, ina masa ladabi da biyayya and he is satisfied! a school da social media I’m the person I chose to be, I don’t use his name! mahaifina kenan bare ke da kike kanwa ta! Dan Allah ki fita harka ta Halitta!!”

Ta dan tsagaita ta na mai jan wayar ta, Instagram ta shiga ta dubo sunan Halitta, ta ce

“Alright ga shi nan na yi unfollowing din ki, I expect you to do the same in dai ke ba mayya ba ce! Wannan masifar har ina!”

Ran Halitta idan yayi dubu ya baci, cikin zafin rai take kallan Zainab, ta ce

“Ki tuba Yakura! Ko dan darajar mahaifin mu ki tuba, kuma ki sani idan babu mutuwa akwai tsufa, ke mace ce, Rayuwar diya mace kalilan ce, Me za ki ce da ‘ya’ya duk randa su ka wayi gari aka yi musu nuni da wannan hoto aka ce ke mahaifiyar su ce? Da wani ido za ki kalle su?……”

“Get out of my room! Ba na bukatar wa’azin ki, ki bari sai Dady ya hau mambari ki ja masa baki! Nonsense!”

Ta katse ta cike da masifa. Jiki sanyaye Halitta ta juya, ko da ta kai kofa sai ta sake juyowa ta da dubi Zainab da ke kallan ta kamar zakanya, ta ce

“Ba zan fasa mi ki wa’azi ba Yakura, ba zan fasa mi ki addua ba, Allah ya shirye ki”

“Mtswww”

Amsar Zainab kenan, yayin da ta tashi ta rufe kofarta da key bayan fitar Halitta. Idan ran ta yayi dubu ya baci dan kuwa a rayuwar ta ta tsani sa ido, gani ta ke duk duniya babu wanda ya sa mata ido kamar Halitta, shi ya sa ma sam ba sa shiri.

 

Back to top button