Category: Matar Makaho Hausa Novel

  • Matar Makaho 100

    Matar Makaho 100

    😥END😥

    Page1⃣0⃣0⃣
    Wani irin magana ne haka nabila?toh nidai baza’ayi wannan haukar dani ba, kinji na fad’a miki taya yaro da matarsa koh sanin dadin aure basuyi ba, gani tsohowar banza nazo nasa bakina a sha’aninsu salon nayi bakin jini a wajen baiwar Allah, yarinya na ganin girmana najawa kaina raini wallahi da sakel ki barni na mutu da mutunci na.

    Kuka nabila ta sake cikin maganar shagwaba tace, ni shikenan babu inda zanje naji dadi, dedena naje mata da zancen zagina tayi kema shine xaki mini haka?

    Jin abinda tace yasa mahmah kashe wayar ta aje ta fita a d’akin.

    Ammar yazo sun gaisa da khadija kuma ba laifi ta sake jiki dashi kad’an, kuma yana samun hankalinta, Amma ba karamin kunyar muhammad yake jiba duk lokacin da zaizo sai ya tambaye khadija a waya yayan ta na nan intace eh tofa ba zuwan zaiyi ba.

    Bayan sati uku Ayau ne dubun Al’umma suka shaida d’aurin auren sarki yusuf mutallaf tare da Amaryar sa zainab Rabi’u ubangari sai kuma Abdulsalam Abdul’Aziz shugaba da Amaryar sa Amina Ahmad Adara, d’auren auren da ya samu halaktan manyan mutane daga nijar har nigeri’a tabbas yan uwan zainab sun nuna mata gata a bikinta.

    Bayan d’auren Auren ne mahafin Ammar ke wa yusuf zancen khadija, wanda yace sai dai aje nijar ayi batun Auren tunda canne mahaifarsu kar yan uwa suga ana musu wariya.

    Su sumayya da muhammad harda khadija ayau sukabi gida gidan yan uwa domen musu sallama, washe gari taje abuja tama mahaifiyarta sallama zasu tafi nijar wajen dangin mijinta, kuma daga wajen zasu wuce America.

    Ayau ne sumayyya dasu khadija da mahmah tare da tawagar sarki da Amaryar sa,suka nufi nijar, sun samu kyakkyawar tarba, saidai fa sumayya ta fuskanci sauyi a wajen nabila wanda hakan yasata shawa nabila mur, ganin duk lokacin da taga Al’ameeen zatana wani kwarkwasa shikam baima nuna yasan tanayi ba, ga lawiza da kishi ke cinta, Amma dai ta kwantar da hankalinta ganin yanzun tana samun kulawa a wajen mijinta fiye da da.

    Nabila tayita nacewa mahmah akan zancen ta da muhammad, wanda abin yasa mahmah tarar yusuf da zancen, kai tsaye yace mata, mahmah banki bin umurnin kiba amma mama inkin duba duk abubuwan da suka faru Nine na fata ballo ruwan, da ace nayi biyayya ga mahaifina da duk abinnan bai faruwa ba, duk da bawa baya wuce kaddararsa mama bazan iyyama muhammad wannan zancen ba,A tausayawa yaron nan yasha wahala A rayuwar sa yanzun lokacine daya kamata Ya huta, duba da irin halakcin da yarinyar nan ta masa bata cancanci haka ba, in shine ya taso da zancen aure bazan hanasa ba, Amma mama bazan iyya tikasta masa ba kiyi hakuri bawai don yana d’ana ba, zaki iyya tuntubarsa duk Abinda ya yanke shikenan.

    Jikin mahmah yayi sanyi kuma taji shawaran da d’anta ya bata don/a dalilin Auren dole yusuf yasha wahala, hakan yasa bata ma tinkare muhammad da zancen ba.

    Gidado da badaru dayake ba boko sukayi ba, kuma yanzun sun wuce shiga makaranta, yasa sarki bada umurnin a sasu a islamiyya, da kuma yaki da jahilci koh karatun hausane da turanci su iyya,ya bude musu manyan shaguna a kasuwa,in sunje boko sun dawo sai kuma su tafi shago, asabar da lahadi suje islamiyya.

    A kasuwa gidado ya hadu da indo kanwarsa na bara, cikin wani irin yanayi ya tisata har inda suke da zama, aiko suna zuwa saida yayi hawaye ganin wani kazamin waje kusa da bola innarsa ke rayuwa gata a kwance ba lafiya ga yarsa cikin datti ,sai abinda indo tayi bara ta sama musu, d’aukar su yayi wanda a lokacin inna koh sanin wake kanta batayi ba.

    Sarki a washe garin ya tura su saudiya da inna,saboda ciwonta ya kazanta blood Cancer ne, yayinda indo ke zaune a gidan sarki tare da lantana karama.

    Muhammad da sumayya sun wuce America tare da yaransu suna mai kewar kasarsu da yan uwansu.

    Bayan tafiyar su akayi auren Gidado da nabila sai badaru da wata yarinya yar tsohowar unguwansu, sarkin shayi ma Yusuf ya had’asa da wata bazawara an had’asu aure.

    Jikin inna yayi sauki inda sarki yasai musu gida ita da indo da yar gidado , d’aya shashin kuma gidado ne da nabila, dataga ba sarki sai Allah ta aure sa abinta.

    Su sumayya basu dawo ba saida sukayi shekara d’aya, lokacin auren khadija da Ammar sukazo, khadija tayi weac dayake har lokacin tana Nigeria a abuja wajen hafsa, yayin da yaran sumayya suka cika shekara 1 da watanni a lokacin kowa yaga sumayya da muhammad sai sun basu sha’awa, gaskiya ne mahakurci mawadace, mai hakuri yana tare da riba, sannan duk mai biyayya ga iyaye zaiga Amfaninsa wata rana.

    Ana bikin Ammar da khadija suka koma wajen aikin Ammar a maiduguri bayan aure ya maidata makaranta, don result nata yayi kyau sosai, su sumayya sun koma America bayan biki.

    ***************
    Bayan wasu shekaru………
    Wani matashin magidanci ne tsaye a wani hadedden compound mai d’auke da shuke shuke mai ban sha’awa, sanye yake da kakin sojoji a jikinsa wandone da riga, kansa ba hula sai gashinsa dake kwance baki kirim yana sheki, yayi farine tas yayin da idanunsa ke d’auke da bakin glass, dukar da kansa yayi yana kallon agogon sa mai masifar tsada, dake hannunsa d’an yamutsa fuska yayi hade da dan sakin tsiririn tsaki,ganin 7:21pm Amma har yanzun gimbiyar tasa bata fitoh ba bare yaransa, jin karan bude kofar falonsu da akayi yasa sa saurin d’agowa.

    Sanye take da siket baki mai kauri yana nan kamar pencil Amma ba’a tsaga baya ba,sai takalmi mai tsini a kafarta dake d’auke da socks baki, shirt ne a jikinta white mai botur da dogon hannu, wanda tayi stokin dashi, Have sunnah ne a wuyanta baki, da agogo fari a d’aure a farin tsintsiyar hannunta, sai jakan office dake rataye a hannunta d’aya Tabar daya hannun na lilo, fuskar nan nata yayi fayau babu kwalliya alamu dai jin dadi ya samu waje, rike take da wani kyakkyawan yaro fari yana sanye da uniform na primary bazai wuce shekara 5 ba, ga wani yaron na binta a baya zaikai 7 shima yana sanye da uniform hannunsa d’auke da jaka d’aya hannun kuma lunch-box nasa.

    Da sauri ta kara hanzartawa ganin fuskar mijin nata a hade, don tasan tabbas sun sasa jira don yau dai sun makara.

    Yanzun ke kullum in zamu tafi aiki da safe sai kin sani lettin kike jin dadi, ki duba yanzun minutes 30 ina tsaye ina jiranku?

    “Don Allah kayi hakuri dear wallahi neman socks in na’ima nake wai bataga d’aya ba”

    Toh surutun ma ai ya cinye lokacin daya saura manan, yace yana kamo yaron dake hannunta ya bude seat back ya ajesa, kallon mai shekara bakwan yayi, Au kaima salim(takwaran salim marigayi, muhammad ya hana a masa inkiya yace a barsa da sunan sa)so kake na d’aga kane koh me? kana tsaye.

    Washe fararen hakoransa yayi cikin dariya ganin yau ran baban nasu a bace, yace, sorry Dady.

    Shiga gaba sumayya tayi ta aje jakanta akan cinyarta da mamaki Al’ameen yake kallonta, wai sumayya ina sauran yaran ne?

    “Au wai basu shiga bane tare fa muke futowa dasu”

    Kinsan Allah sumayya yau in kikayi tsiya sai kija mota da kanki tunda dai naga kowa nada shi, ya fad’a a hankali yanda yaran bazasu ji ba.

    “Kayi hakuri toh” kawai tace tana fita a motar daidai lokacin wasu yaran mata da zasukai shekara 10 masu tsananin kama da juna, gasu kyawawa sanye suke da uniform suna gudu da school back a hannu d’aya nabin d’ayar da gudu.

    Da sauri sumayya ta kalli wance ake binta da gudun, tazo ta makale a bayan Dadynsu,”Na’ima mekika mata”?

    Momy wallahi babu abinda na mata.

    Kallon na’ifa dake hawaye a gefenta tayi, tana tsaye batabi na’ima bayan dadyn sun ba” meta miki kika biyo ta”?

    Wallahi momy colour nata d’auka guda hudu, kum drewing zanyi dashi fa.

    Ke na’ima ina naki colour da zaki d’auka mata nata?

    Dady toh banga nawan bane bafa.

    Da sauri sumayya ta karbi maganan jin Amsar data bawa muhammad”Daman ke haka kike kome naki ba’a gani, kina ganin da safen nan harkin batar da socks naki daker na gane inda kika aje, kome naki baya lastic wannan biro in aka saima yar uwarki sai yayi 1 month tana amfani dashi, amma ke koh kwana bayayi sai kice ba pen ah ah pen ya bata, don haka oya bata colourn ta koh na saba miki”?

    Ba musu ta bude jakanta ta mikawa na’ifa abinta, sai kuma ta fashe da kuka.

    Muhammad dake tsaye ne ya dubeta, toh wai kukan na menene?

    Dady kuma fa bangama drewing ba gashi uncle yace duk wanda baida colour waje zai korasa bazai masa makin ba.

    Ina dai akan colour ne?muhammad ya tambaye ta.

    D’aga masa kai tayi alamun eh.

    Toh muje a hanya saina sai miki sabo koh?yanzun ku shiga mu wuce mun kusa makara.

    Dady nimafa bani da calculator?

    “Da sauri sumayya ta dubi yaron ta, kaji tsoron Allah khaleefa(yusuf) ba jiya naga calculator a jakan ka ba”

    Momy Abokina kullun sai uncle ya bugesa wai bayida calculator, shine na tambayesa mai yasa ba’a saya masa ba, wai Auntin sa(step mother)in dadynsa ya basa kudin saita kwace, shine na basa kyautan nawa jiya.

    “Masha Allah yaron kirki haka nakeso Allah ya muku Albarka”

    Gabaki d’ayansu suka Amsa da Ameeen .

    Jan motan muhammad yayi mai gadi ya walgale musu makeken get nasu suka fice.

    Sai da suka bi ta bookshop ya sai musu abinda suke bukata, yaran ya fara saukewa a school, kafun ya kama hanyar bank da sumayya, tun a hanya ta makala ID card nata a wuya, suna isa bank ta sabi jakanta sukayi sallama ya wuce wajen aikin sa.

    Misalin karfe 4:30 na yamma muhammad ne zaune a office yana aiki, yaji ring na wayan sa kamar bazai d’auka ba don aiki yake mai muhimmanci,d’auka yayi yana kallon mai kiran nasa da sauri yayi picking yasa a kunne,Assalamu Alaikum

    Ta d’aya bangaren Ammar ya Amsa wa’alaikumu salam, Captain muna fa Airport azo ya d’auke mu.

    Da sauri muhammad ya mike cikin mamaki yace What? kana nufin kun shigo Lagos koh note’s babu?

    Surprise muke son muku.

    Amma gaskiya ka kyauta gamunan zuwa, suna yanke wayar neman wayar sumayya yayi ya kirata

    sumayya dake zauce akan kantan customer care tana aiki taji wayanta na ringing d’agawa tayi tasa a kunne ganin sunan maikiran nata, “Hello Rabin Raina”

    Hello sweetheart kin koma gidane?

    “No Rabin Rai yanzun nake kokarin fita, musa driver na haraban bank yana jirana”

    Ok kice masa ya wuce dasu salim, ke ki jirani ina zuwa?

    “Lafiya dai naga kace mini yau sai 6 zaka dawo kana da aiki”?

    Lafiya yanzun Ammar yake sanar dani sun shigo lagos suna Airport.

    Ok saika zo tace tana yanke wayar, number musa driver ta kira ta shaida masa ya wuce kawai gida, sannan yacewa bahbah(tsohowar mai Aikinsu)ta kara wasu abubuwan cin zasuyi baki.

    Ba’a jima ba da wucewar musa saiga muhammad jakanta kawai ta d’auka ta shiga motarsa suka wuce Airport, suna isa Jakanta sumayya ta bude ta zaro Abayan ta sakawa tayi daman akwai have sunnah a jikinta dukansu suka sauka a motar waya Al’ameen ya d’aga ya kira Ammar.

    Tsaye suke suna duduba masu fitowa, daga nesa sumayya ta hango Khadija da katon cikinta a gaba tayi kyau kamar ba khadin goggo ba hutu dajin dadi sun ratsa ta, sai Ammar dake rike da hannun yaran su biyu mace da namiji,macen baka kamar babanta sabanin na mijin dayake fari, da sauri sumayya ta dagawa Khadija hannu da sauri suka karaso garesu da gudu, yaran suka rungumi muhammad suna masa oyoyo uncle da murna suka tattaru sai gida.

    Suna isa gida suka samu yaransu a tsakar gida, bahbah ta musu wanka, suna zazzaune a gaban malamin su dake can gefen flowern tsakar gidan, ai lokacin da suka gu momynsu ta sauko a mota da Ummi(khadija)gasu Amira(Aisha) da mukaddas yasasu rugawa da gudu suka nufesu da gudu, duk irin kwala musu kira da ustax keyi, ina sunyi gunsu da gudu da sauri suka rungume yaran suna murna.

    Koran su sumayya tayi hardasu Ameer suka wuce wajen karatu, tace sai ustax ya tadasu sai su shigo duka.

    Suna shiga cikin part daban sumayya ta sauke su khadija da mijinta, ta basu waje su kimtsa itama d’aki ta shiga ita da muhammad.

    Bayan mangariba zaune suke akan daining dukansu suna cin Abinci, Ga yaransu a zazzaune Suma ana ci dasu, hira ake na yaushe gamo, kallon sumayya khadija tayi.

    Aunty Gaskiya shagunan ki sun habbaka last months munje jalingo, nida maimuna mukaje shagon gaskiya nasha mamaki ganin harda saloon ga gyaran jiki duka?

    “Wallahi kuwa khadija kinsan yanzun shago hudu nake running Na make-up saloon gyaran jiki, lalle kuma gaskiya Alhamdulilh matar shagari na iyya kokarinta yarinyar ta burgeni akwai Amana”

    Gaskiya ne Aunty nima na yaba da nutsuwar Rufaida.

    “Ai shiyasa na bar mata kula da shagunan a hannunta sannan ita ke iban ma’aikata da masu training”.

    Toh Allah ya kara budi.

    “Ameen khadija waini ina labarin kamila ne”?

    wallahi aunty tadaiji sauki yanzun ba kadangarun sai daifa Abin ya taba kwakwalwanta.

    “Toh Allah ya sauwaka,Yajikan momy(safina)da rahama”

    Ameen suka amsa dukan su,bayan sun gama cin abinci Yaran suka wuce ciki yayinda su sumayya ke hira falo, sallan isha’i sukayi sukaci gaba da zaman falo ana hira.

    Da gudu Na’ifa take saukowa daga upstair hannunta d’auke da system in sumayya tana kwala mata kira ga sauran yaran na binsu baya.

    Da mamaki sumayya ta kalleta ganin vedio call suke da mutanen nijar, karban system in tayi ta aje musu akan center table dake falon, duk suna zazzauna akan kujeran da take gaisawa suke da su nabila indo Aunty zainab da nana(Aisha takwaran mamansu muhammad)sai muwaddat dake rike da sabuwar jaririya a hannunta, gaggaisawa suke tare da mata barkar haihuwa akan basu samu zuwa ba cikin khadija wata 8 amma insha Allah zasu zo auren muhibbat.

    Bawa su muhammad da Ammar system in sukayi suma suka gaisa da yusuf dake cikin iyalansa cikin farin ciki don yara biyu zainab ta haifa masa Aisha da muhin, sosai akayita hira harda mahmah data kara tsufa sosai ga lawiza duka don yau akayi sunan muwaddat duk suna hade.

    Sai kusan 9 sukayi sallama khadija da mijinta sukayi part da suke sauka in sunzo, dayake yaransu dasu Na’ima zasu kwana, had’a kansu sumayya tayi har bedroom na maza wanka ta musu dukansu tasa musu kayan bacci ta kwantar dasu, tufa masu Addu’a tayi taja musu kofa, d’akinsu na’ima ta shiga ta samu har suma sunyi wanka dasu Amira dayake duk zasu iyya ma kansu, Addu’a tasasu sukayi ta rufe musu kofa bayan ta tabbatar sun kwanta.

    D’akin ta ta shiga, wanka tayi ta sanya wani d’an iskan kayan bacci riga da wando jikinta sai kamshi yake ta wuce d’akin mijinta, tura kofar tayi da sallama ta shiga.

    Zaune yake akan gado yana aiki a laptop ganinta yasa sa kashewa ya aje akan drowern gado ya zuba mata ido ganin irin kyaun da ta masa.

    Da sauri sumayya ta karaso garesa faduwa tayi a kansa wanda yasa dole ya koma kan gadon suka kwanta, yayinda yake kasa tana samansa fuskar su ya hade waje d’aya Cikin kasa kasa da murya yake mata magana, wai Rabin Raina menene sirrin ne kullum dad’a kyau kike kamar yau Aka kawo mini ke?yana maganar yana mammatsa mata jiki.

    Murmushi sumayya tayi sai kuma ta tuno wani abu cikin dariya tace,kai menene haka?

    Dariya ya sake tuna masa da ranan su na farko, shima Amsa ya bata, yi hakuri gado nake nema zan kwanta ne?

    Itama ta sake basa Amsa, wallahi bazan kwanta dakai gado d’aya ba gadai kujera acan jeka kwanta.

    Gabaki d’ayansu dariya suka sake a tare cike da farin ciki suke romancing na juna, hannu muhammad yasa ya kamo blanket in ya lulubesu.

    *Alhamdulil!!!!!Alhamdulilah!!!!!!!! Alhamdulilh!!!!! nagode Allah daya nuna mini wannan rana cikin koshin lafiya, harna kawo karshen labarin matar makaho, duk wanda nama ba daidai ba ina neman afuwarsa*

    *MATAR MAKAHO FAN’S INA MATUKAR ALFAHARI DAKU, DON DA KARFAFAWARKU NA TAKA WANNAN STEPS DANAKE KAI AYAU, WA’INDA NAGA COMMENTS NAKU DA WA’INDA BANGANI BA WA’INDA NAMA REPLY DA WA’INDA BANMA WA BA, ALLAH YABAR KAUNA INA GODIYA*😃

    *SANNAN INA MAI MUKU ALBISHIR HADE DA SANAR DAKU SABON LABARI NA DAKE TAFE MAI SUNA*
    🏵 *ALKAWARIN MASOYA* 🏵
    *WANDA NAKE DA TABBACI HADE DA YAKININ ZAI MATUKAR KAYATAR DAKU INSHA ALLAH*😎

    ✨Ruqeenjalal ke muku sallama✨

  • Matar Makaho 84-85

    Matar Makaho 84-85

    Page8⃣4⃣&8⃣5⃣
    Mikewa Sukayi da sauri suka nufi kofar gidan, ba tare da wani tsoro ba suka zare sakatar, me zasu gani?bawan Allah nan ne aka d’ago rababe-rababe kamar kayan wanki, cikin hanzari suka bawa mutane biyu da suka d’agosa hanya suka shigo dashi cikin gidan, direct d’aki suka nufa dashi suka kwantar.

    Al’ameen dake binsu a bayane ya tambaye su meya faru dashi?

    Wani a cikin sune yake tsanar dashi wai ashe faduwa mutumin yayi a gidan da yake aiki, kafarsa ya karye shine aka kaisa asibiti aka d’aure kafar, amma yaki zaman asibiti wai sai dai a dawo dashi gida yayi jinya.

    Allah ya kiyaye na gaba Su Al’ameen sukace suna komawa d’akin mutumin.

    Kallon kafar da aka d’aure muhammad yayi, Sannu baba Allah ya kiyaye na gaba?

    Amsa masa yayi da, Ameen Al’ameen.

    Sannu baba, gidado da badaru sukace a tare, Amsa musu yayi a hankali, tashi Al’ameen yayi ya fita a d’akin, murhun inda ya gani na karfe d’an karami ga gaushi a ciki, nitsuwa yayi ya hura wutan ya d’aura butan shayi, atakaice dai shayi ya had’a a cikin butan ya had’a da kofi ya kaima mutumin, ba musu mutumin yasha kad’an, Al’ameen ya sake fita ya d’aura ruwan zafi, yana dumi ya d’auko a roba ya had’a da tsumma yazo ya gogewa mutumin jiki, ya shanja masa kaya, sosai mutumin yaji dadi yayita sama Muhammad Albarka.

    Da dadare ma su gidado sun koma dakin su, yayinda Al’ameen ya kwanta da mutumin a d’akinsa tare, tsakar dare mutumin ya farka da taimakon muhammad yayi fitsari ya sake dawo dashi ya kwantar, a hankali mutumin ya kalli muhammad sai kuma ya bude baki ya fara magana, Allah ya dubi halinda zan shiga ya aiko mini ku muhammad, da ace yau babuku a gidan nan bansan halinda zan tsinci kaina ba, bani da kowa gashi ba Aure nake dashi ba bare yara.

    Babu kome Baba fatan mudai Allah ya baka lafiya.

    Ameen muhammad, Akwai wani taimako da nakeso kamin, in babu damuwa d’an nan?

    Ba kome baba indai har baifi karfina ba, kuma bai sab’awa shariya ba, zan maka kome da kake bukata, kayi mana kome baba tunda ka bamu matsuguni a gidan ka.

    Muhammad a gidan da nake aiki tsawon shekararu a gidan, tun lokacin da mahaifina ke aikin a matsayin da nake yau, ina binsa muje tare har Allah ya d’auki Ransa, ni na cigaba da aikin kamar shi, a yanzun bani da kowa ba uwa ba uba ba yara ni kad’a nake rayuwa ta a gidan nan, sai yanzun da Allah ya turo mini ku, in ba damuwa so nake muhammad kaje a matsayina, kaci gaba da aikin da nake har Allah yasa na samu Lafiya, kaga bazanso ace aikin da nake tsawon shekaru, yau a samu wani ya karbe mini ba, tunda ciwon bana kwana biyu koh uku na warke bane?sai nayi jinya mai tsawo.

    Shuru muhammad yayi na d’an wani lokaci kafun yace, ba kome baba zanje nayi aikin har Allah ya baka lafiya, Amma wani irin aikine don ni baba banyi karatu mai zurfi ba?

    Murmushin karfin hali mutumin yayi, bafa aikin da ya shafi ilimi bane, aikin gidan sarauta ne, kuma nine sarkin shayi na gidan.

    Muhammad ne ya kalle sa da mamaki, Gidan sarauta kuma baba?

    Eh d’an nan zakaje ka zauna a matsayina tun jiya na sanar dasu zaka fara zuwa aiki gobe.

    Aini baba ban iyya dafa shayi irin naku ba, kadai ga yanda na had’a shayin d’azun baiyi irin wanda ka had’a mana ba.

    Karka damu muhammad akwai wa’inda zan turaka wajen su, ‘yan gida nane suna taimaka mini wajen raraba shayi a gidan, Na sarki ne kawai nake kaiwa da kaina, kaima yanzun kaine zakana kai masa,sannan shayi kala uku ake, akwai na sarki shinasa dabanne, akwai na family akwai na bayi.

    Baba anya zan iyya aikin nan kuwa, gidan sarauta fa kace?

    Zaka iyya muhammad ka taimaka kaje kaji?

    Shikenan Allah ya kaimu goben lafiya, Amma baba wazai nuna mini gidan, don ni bako ne , bansan ina ne gidan sarkin garin nan ba?

    Karka damu muhammad akwai yaron makwantan mu gobe zan turaka gidan su saiya kaika.

    Shuru muhammad yayi ya kwanta, Amma ya kasa bacci haka kawai yaji yana fargaban zuwa gidan kodon bai taba zuwa bane oho.

    Washe gari muhammad ne yayi wa mutumin Alwala da ruwan zafi ya saita sa gabas, sukuma suka wuce masallaci.

    Bayan sun dawo kamar jiya suka kimtsa gidan yau harda karyawa suka had’a mai kyau, bayan muhammad yayi wanka, baba kaya ya sakasa ya d’auka irin na buzaye, wando kato da rigansa mai aiki a gaba sai rawanin su, muhammad kasa nad’a rawanin yayi, Amma haka mutumin nan a bashi da lafiya saida ya nad’awa muhammad, rufe masa fuska yayi da rawanin babu abinda ake gani a fuskar sa sai kwayar idanunsa, sosai Al’ameen yayi mamaki harya kasa hakuri yayi magana, baba basai an rufe fuskar duka ba?

    Ah ah muhammad ina son koh kaje gidan karka bude fuskar ka, ka barsa a haka, kuma kayi taka tsamtsam da kowa na gidan, karka yarda da kowa kayi abinda ya kaika ka dawo, ga wannan in kaje get sai kanuna, kafun a barka ka wuce ciki.

    Karba muhammad yayi yana karanta abinda baba ya basa, get pass ne d’auke da rubutun larabci, a jiki saidai bai gane me aka rubuta ba, kasancewa yare aka rubuta da harufan Larabci sai hoton zaki a bayan get pass in, Muhammad fita yayi bayan yama su gidado bayanin inda zashi, sosai suke da Zuzuta karbar da kayan ta masa kamar buzun gaske, bayan ya fita a gidan, gidan makwancin su ya wuce ya masa bayani kamar yanda baban yace masa, had’asa da yaron sa mutumin yayi, ya rakasa gidan da baba ke aiki.

    Tunda suka sauko a machine yakejin wani irin masifeffen bugun zuciya, ga wani irin fargaba dake cikin ransa ya rasa dalilin da yasa? ya tsinci kansa da tsoron zuwa gidan, tun daga nesa ya hango wani irin gini mai d’aukar hankali gini ne irin dogin nan masu masifar tsaho, ga wani fankamemen get fari mai d’auke da hoton zaki babba a jiki, gidane na Alfarma koh ince unguwa guda tun daga nesa zaka tambatar gidane na sarauta, masuji da mulki,yanda suke matsowa gidan haka bugun zuciyar Al’ameen ke kara yawaita, karasowa sukayi bakin get in, masu tsarone sanye da bakaken kaya hannunsu d’auke da manya manyan bindigogi cikin tsawa d’aya daga cikin su ya dakawa su muhammad da karfi cikin yare yake musu magana.

    Daskarewa muhammad yayi jin yanda mutumin ya hayayyako musu kamar zaicisu d’anye, gashi sai yare yake shikuma baji yake ba, Allah yasa yaron da suka zo tare yana gun shiya musu bayanin zuwansu cikin yare tare da sanar dasu muhammad d’an uwan Sarkin shayi ne, zaizo ya karbe sa daidai yaji sauki.

    Basu barsu sun shiga ba har saida Al’ameen ya nuna musu get pass da baba ya basa kafun suka barsu suka shiga ciki, mutuwar tsaye muhammad yayi lokacin da idanunsa suka sauka a compound na gidan, duniyace babba gida mai matukar girma, a haka suke taka tsakar gidan daidai sun iso tsakiyar gidan muhammad yaga gunkin zaki babba mai matukar girman gaske, An kawatashi a tsakar gidan a zaune kamar mai rai, wucewa wani shashe sukayi da yaron sai gasu a wani kayatancen falo mai masifar kyau da d’aukar hankali, kujerune na Alfarma a cikin su, zarce wa sukayi cikin wani kofa dake gefen falon, shidai muhammad idone nasa yake bin koh ina da kallo, har suka shiga cikin d’akin, wow shine abinda ya fitoh a bakin sa ganin wani irin kitcheen na Alfarma mai dauke da kayan Alatu na zamani, sai samari guda biyu dake kitchen in a tsaye suna aiki,jin motsen su muhammad da sallamar suce yasasu juyowa.

    Amsa sallamar sukayi, bayan sun gaisa da yaron yake musu bayanin Al’ameen ne zai karbi, sarkin shayi harya warke, sannan sarkin shayi yace su koya masa had’a shayi, sannan shi zaina kaiwa sarki shayi kullum, duk da yare yaron ke musu bayani.

    Muhammad kamfa ya shiga tsaka mai wuya don shi dai ba yare yake jiba, tayaya zai iyya zama da wa’innan mutane wai daman babu hausawa ne a nijar koh dai wannan garine baida hausawan oho?kuma gashi baba ya iyya hausa?

    Yaron ne yajuya zai fita a kitchen in da sauri muhamamd ya bisa a baya, da mamaki yaron ya juyo ya kalli muhammad cikin mamaki yake tambayar sa yaya kuma zaina binsa?

    Gaskiya nifa ban gane ba kowa a gidan nan sai yare yake mini, nifa baji nake ba.

    Dariya yaron yayi karka damu kaji, wasu a cikin su suna ji sai dai in an ganka za’ayi tunanin koh kanajin yarene shiyasa wasu ke maka yare, Amma in suka maka magana kana musu hausa kaji zasu maka suma.

    Toh nagode kawai muhammad yace, ya koma kitchen in, sosai suka sakasa aiki goge kofuna d’aura shayi saka wanshan ganye ah ah yi kaza sai kusan azahar, bayan sunyi sallah aka fara rabon shayi a gidan, shima wasu kofuna da buta na Alfarma masu shegen kyau da sheki ruwan Gold suka zuba shayin a butan, aka jera a karamin tire da shukali sai bolw na zuma, shima Golden colour da shukali biyu, mikama Al’ameen sukayi Hade da had’asa da wani a cikin ma’aikatan ya nuna masa flat na sarki.

    Duk abinda Al’ameen kiyi tsananin bugun zuciyar sa nayi, har wa yanzun da suke nufar sashen sarki, hannunsa d’auke da tiren kayan shayin, suna isa kofar shiga falon, ma’aikacin ya koma ya bar muhammad tare da nuna masa kofar da hannu alamu dai nan zai shiga, yafi minutes 2 yana tsaye ya kasa shiga zuciyarsa na matukar buga wa da sauri-sauri, ganin wani bawa zai wuce yasa muhamamd saurin sa hannu ya murd’a kofar falon bakinsa d’auke da sallama, Amma bai shiga ciki ba a bakin kofar ya tsaya.

    Amsa masa sallamar akayi saiga wata mata ta fitoh, sanye da kayan da bayin gidan ke sanyawa, hade da masa iso zuwa cikin falon, shigowa Al’ameen yayi yana bin bayanta har suka karaso cikin falon, falone babba mai girman gaske da kawatuwa irin falon nan na sarakuna, masu ji da lokacin su, wuce falon sukayi suka nufi wani kofa daban, nan ma falone Amma baikai wanda suka wuce girma ba Da kayatuwa, kara nausawa sukayi cikin wani kofar, saigasu a wajen shakatawa mai d’auke da shuke shuke na flowers mai ban sha’awa da kamshi, jefa kafa kawai muhammad yake don yayi matukar gajiya da tafiyar nan, da yake daman bai gama sauke gudun hijiran da sukayi ba, ga matsanan cin bugun zuciyrsa kiyi da karfi, lokacin da idanunsa suka sauka akan mutanen dake zaune su biyu cikin shiga na Alfarma wanda koh ba’a fad’a ba kasan sarkine tare da matarsa dake sanye da Alkimba mai masifar kyau da d’aukar ido, farace tas kyakkyawa da ita, yayinda sarkin ke sanye da rawanin buzaye a kansa ya rufe fuskar sa luf banda idanunsa babu abinda mutun zai hanga don koh kafar sa da hannunsa boye yake a cikin suturansa, shuru sarauniyar tayi ganin su Al’ameen da Alamu dai magana take da mijinta Da sallama a bakin su Al’ameen suka karaso inda suke, da sauri sarkin ya dafe daidai saitin zuciyarsa yana Ambatun sunan Allah a zuciyar sa, yayin da muhamamd suka tsunguna a kan gwuwuwinsu A hankali ya d’aura tiren akan table inda ke gabansu, hannunsa sai rawa yake wanda baisan dalilin hakan ba, tsiyaye shayin ya fara a kofi yana had’awa da zuma.

    Sarauniya ita ta kula da halin da mijin ta ke ciki da sauri ta matso garesa Ranka ya dade lafiya meke faruwa zuciyar ce?

    Shuru ya mata, itama bata damu ba don tasan halin mijin ta zata masa magana sau dubu ba Samun Amsa zatayi ba, yasha yarfata a gaban bayinta Amma tun yana damunta yanzun koh a jikinta, kara tambayar sa tayi zuciyar sa na ciwo ne?

    Girgiza mata kai kawai yayi baiyi magana ba, jingina yayi da jikin kujeran da yake zaune akai ya lumshe ido yana maimaita innalilahi…..

    Al’ameen na gama had’a shayin ya mike abinsa ya fita a lambun, sai a lokacin sarkin ya zare hannunsa daga kan kirjinsa yayinda idanunsa sunyi matukar kaduwa zuwa ja, sosai jikinsa ke rawa, ganin hakan yasa sarauniya mikewa da sauri ta fita a lambun ba’a jima ba saiga ta, ta dawo da wata tsohowar mata cikin shiga ta Alfarma kyakkyawa da ita fara, ta karaso garesa hannunta d’auke da magani, da saurin ta balla hade da karban kofin ruwan dake hannun sarauniya ta kafa masa a baki, ba musu ya karba yasha maganin, ka tashi ka koma ciki kaji?tsohowar tace

    Girgiza mata kai kawai yayi vaiyi magana ba, Alamu dai yafison zaman nan in, ba musu daga matar tasa, har tsohowar suka basa waje don haka yake indai ta shine yafi kaunar a basa waje ya zauna shi kad’ai sau dubu akan ya zauna da mutane.

    Al’ameen kam yana komawa kitchen in abinci aka kawo musu na rana, mai rai da lafiya harda kaji sukaci, zama sukayi a falon da kitchen in ke cikinsa suka kwanta a kan kujerun dake wajen alamu dai daman falon donsu akama,(ma’aikatan shayi) sai la’asar suka sake dafa sabon shaye wannan karon Al’ameen ne ya d’auka shi kad’an sa, ba tare da rakiyar jakadiya ba ya shigo falon, yarane zaune a tsakar falo su uku, biyu suna zaune a kasan cafet dake shimfid’e a tsakiyar falon, suna rubutu a takarda dukansu mata ne d’ayan zata kai shekara goma sha biyar, d’ayan kuma zata kai shekara Goma, Lokacin da yaran suka d’ago suka kallesa baisan lokacin da tiren shayin dake hannun sa ya tsubuce a hannunsa ba, a take kome ya tarwatse a wajen, suma yaran zare ido sukayi ganin barnan da muhammad ya musu a falo, d’aya yarinya ta ukun dake zaune akan kujera tana danna waya bazata wuce shekara 20 ba, ta mike cikin masifa da izza, kai wani irin wawane koh ince dolo kana da hankali kuwa zaka shigo mana falo kazo ka zubar da abu, sannan ka tsaya kana kallon mu, jira kake mu kwashe maka koh me?

    Habba Nabila baikamata kima mutum babba kamar wannan irin zagin nan va, baikama taba gaskiya ki gyara halinki, d’aya daga cikin yaran da ke zaune a kasan cafet in tace ma nabilar.

    Kinga muhibbat babu ruwan ki dani ki daina mini irin wannan abin da kike mini, niba sa’arki bace Amma na fahimci kina mini shishigi a lamurana be careful, takarasa maganar da barin falon tana hararan sa.

    Muhibbat ce ta kallesa kaga malam tattara abinda ka fasan nan ka tafi store a baka wasu kayi sauri ka kawowa Abba shayi?duk da Turanci suke magana.

    Muhammad kam mutuwar tsaye yayi yana kallon yarinyar, koh dai mafarki yake ne yarinyar kamar khadijar sa haka yake jin muryar ta, yanda khadija ke magana ba R haka ita ke magana, kaman ninta kome nata yana masa irin na yar uwarsa,duk da khadija na yarinya ya makance amma hakan bazai hanasa gane taba, a gaskiya abinnan ya basa mamaki matuka da kuma tsoro gasu su biyu masu tsananin kama da juna, koh yace masu kama dasu, jin ta sake masa magana cikin yanayin mamaki ya tsunguna ya kwashe fashashun kofunan ya fita a falon da sauri.

    *****************
    Sumayya fa yanzun ci yafi nada ga bacci babu aikin da take yanzun kome khadija kiyi in taga aikin yama khadija yawa saita, sata ta musu take Away kawai, don khadija na kokari ga zuwa school har yamma take dawowa ga aikin gida ga masu kitso, amma Alhmdulilah baza’ace aikin mai yawa ba tunda sharane kawai sai girkin abinda zasuci don yanzun cin sumayya yafi nada gashi cikin yayi girma sosai ya kara hurata, jiki tayi bana wasa ba kafafunta haka suka cika tim,An hanata cin gishiri ma A hospital yanzun ganin irin huruwar da tayi.

    Yau weekend babu school khadija ce zaune a baranda tana ma mutane kitso, yayinda wasu ke zazzaune suna jiran layi yazo kansu, sumayya ce ta fito cikin shiga ta Alfarma zanine less da hijab nata mai hannu medium size, sai jakan sakalawa a kafad’a da waya a hannunta sosai tayi kyau, hannu tasa ta maida kofar falon ta rufe, “khadija lailar ta fitoh ne”?

    Ah ah Aunty bata fitoh ba koh na dubo miki itane?

    “Ah ah khadija ki bari kawai bara naje flat natan sai mu wuce”

    Toh Aunty saikun dawo

    Tana sauka a kan barandan tace”Yauwa khadija”

    au na manta me zan dafa ne na rana?

    “Kibari kawai khadija naga yau akwai layin kitso sosai in muka shiga kasuwa zanbi restaurant nai mana take Away”

    Ok toh Aunty adawo lafiya

    “Allah yasa khadija”wucewa compound in gidan tayi ta nufi sashen laila, harta haura dakalin d’akin ta saigata ta fitoh cikin shirin fita, ah ah sumayya harkin shiryane?

    “Bazan shirya ba laila so fa nake mu dawo kafun Azahar don wannan zafin ranan ba lafiya bane”

    Gaskiya kam bare ku masu ciki.

    “Kinga laila don Allah ki shige muje bana son yawan tsayuwar nan habba”

    Yi hakuri hajiya muje, kawai laila tace suka kama hanya da sumayya.

    Kasuwa laila da sumayya sukaje da taimakon laila sukayi sayayyan kayan baby, dana haihuwa kama daga baf gadon yara kayan sawa feda kome daya dangance baby da sumayya wanda zatayi Amfani dashi lokacin haihuwa da bayan haihuwa ita da babyn ta duk sumayya ta saya, kaya niki niki haka suka zuba a Texi, har sun shiga mota sumayya ta hangi mai mangoro, take tunanin mijin ta daya zamo mata jiki ya fado mata, sai kuma taji tanason sha, hakuri ta baiwa mai motar ta sauka, da sauri ta nufi wajen mai mongoron bata saurare maganar da laila kece mata ba,tana kokarin bude jakar hannunta, gabaki d’aya hankalin ta na kan jakan, bata koh ganin gabanta.

    Ji kawai tayi an bangajeta da karfi tayi baya tagal tagal zata fadi…………🍀🍀

    ✨Ruqeenjalal✨

    🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
    🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯
    ~ Na ~

    🍃 *Rukayya* *Ibrahim* 🍃

  • Matar Makaho 86-87

    Matar Makaho 86-87

    Page8⃣6⃣&8⃣7⃣
    Babane tsaye akan kafarsa yana gyara yayin dake kan bukkar sa, da mamaki Al’ameen yace ikon Allah baba menake ganin nan?

    Da sauri baba ya juya da mamakin ganin Muhammad ya dawo daidai lokacin nan, Alhalin ba lokacin ake tashi aiki ba, lafiya ka dawo yanzun?

    Kai zan tambaya dai baba, na ganka tsaye akan kafafunka, kaida ka karye?

    Zoka zauna muhammad muyi magana?yace yana zama akan taburma.

    Ba musu Al’ameen ya zauna a kusa da baban.

    Muhammad ina fatan kaga abinda nake so ka gani koh?

    Da sauri Al’ameen ya warware rawanin sa, kamar ya baba kuma me kakeso na gani?

    Muhammad Abinda yasani yin haka badon kome bane, illah don naga kaje da kanka gidan sarkin nan, tunda na ganka jikina ya bani wani abu, kamar dake tsakanin ka da muhibbat da muwaddat ya baci sosai, haka sarki ma duk da rabona dana ga fuskar sa, bazan iyya tuna ranan ba Saboda dadewar da nayi bana gani, Amma fa ka sani nasan sarki tunkan yahau mulki, yanda kaga fuskar ka, haka fuskar sa yake sai dai ka nuna masa yaranta?

    Me kake nufi baba bangane ba, wai sarkin da naga fuskar sa a rufe kana nufin yana kama da yara biyu dana gani innan?

    Kwarai muhammad duk da dai akan samu mutum, ya samu mai kamar sa a duniya Amma kaman ku dasu Akwai alamun jini.

    Baba ni bani da kowa a nijar fa bansan kowa a nan ba.

    Toh Amma kaman nin ku, ku hudun nan yayi yawa muhammad?

    Bamu hudu bane mu biyar ne, da kanwa ta.

    Muhammad niba yaro bane, Amma tunda kace haka shikenan, amma dai zaka cigaba da zuwa aiki har lokacin da na yanke akan zancen kafata, tunda ba kariyar gaske nayi ba baikamata na koma ba yanzun?

    Shikenan baba zan cigaba da zuwan,har randa zaka koma aikin, ina su gidado ne tunda na shigo ban gansu ba?

    Sunje kasuwa yi mana sayayyan kayan abinci.

    Tashi muhammad yayi ya ibi ruwa ya shiga band’aki wanka yayi ya shige d’aki ya kwanta, tunanin duniya ya dame sa, duk sanda ya lumshe idanunsa yaran nan yake gani wanda baba yace masa muwaddat da muhibbat wai suna kama da sarki, kenan suna kama dashi, kai shikam bai gane kan Al’amarin nan ba, wani zuciyar na kawo masa wani tunani, amma kokarin tunkude sa yake don yasan abune da kamar wuya.

    Yana kwance har gidado da badaru suka dawo kasuwa, yana jinsu suna ta girki da jido ruwa Amma bai koh fita ba.

    Har suka kammala aikin dare abinka da gidan gauraye, bayan sunci abinci suka wuce masallaci.

    Daren nan sukutum muhammad baiyi bacci ba, sai kusan asuba bacci ya d’auke sa.

    Washe gari muhammad yaje aiki kamar jiya bayan sun gama shayin safe, yaukam had’a masa akayi da yawa a tire, ya wuce dashi falon , da sallama ya tura kofar falon ba kowa a falon sai kamshin turare dake tashi aka tsakar falon, wucewa falon maimartaba yayi a hankali ya tura kofar da sallama.

    Sarauniya ce cikin Alkimba a zaune akan kujera hannunta dauke da kumshen lalle ja abinka da farar fata sosai yayi kyau, sai sarki dake kujeran sa na special kamar kullum fuskar sa a rufe, sai muwaddat da muhibbat dake zaune akasan kushin sai tsohowar nan dake zaune a kujera tana magana da nabila, ke nabila nafa fahimci babu wanda ya bata ku sai lawiza(sarauniya) ace mutum ya dage sai yayi turanci abinda bama amfani muke dashi anan ba?

    Kai mahmah karfa ki manta a abroad nake karatu kuma ashan basu san wani abu wai French koh buzanci ba, da turanci kawai ake Amfani kinga kuma nan gaba muwaddat da muhibbat suna gama secondary suma chan zasu, shiyasa nake saba musu tun a gida mahmah, nabila tace.

    Murmushi sarauniya lawiza tayi tana kallon mijinta da kwata kwata hankalinsa baya wajen su, hankinsa bama a wajen su yake ba, hawaye ne ya cika mata ido, ta rasa yaushe ne ita da yaranta zasu samu lokacin sa? abu tsawon shekaru abu d’aya, tun yaransa na kanana suke korafi har yanzun sun girma har yabi jikinsu, Abban muwaddat……bata karasa ba sukaji sallamar muhammad.

    Amsa masa mahmah tayi, ya karaso cikin falon yana gaidasu da turanci lawiza da su muwaddat ne suka amsa sarki kam koh d’ago kansa baiyi ba bare Amsa gaisuwa, mahmah kam baki ta kama sai kuma tayi shuru batace kome ba.

    a kan table ya aje shayin ya siyaye a kofuna yazo ya aje musu, yana kokarin tashi saiga wasu zaratan maza sun shigo falon cikin sallama, maza ne guda biyu d’ayan zaikai shekara 40 d’ayan kuma zaikai 33 zama sukayi akan kujerun falon suna gaida mah mah da buzanci bayan ta amsa suka juya wajen sarki sauka gaidashi hannu kawai ya d’aga musu.

    uncle Ango, nabila tace tana dariya

    Hararan ta mai shekara 33 yayi ke wallahi bana wasa dake? zan saba miki fa.

    Dariya muwaddat ta sake kai uncle jiya mafa aunty Amarya tazo school namu, ta kawo mana special Anko in mu na yaran Ango.

    Ganin bakin yasa muhammad siyaye musu shayi suma, don shidai duk hiran da suke baji yake ba, kasancewar da yare suke magana, yazo ya jera musu a gaba, har zai mike kawai kafarsa ya taka na nabila,

    ai da sauri ta mike cikin masifa, kai wallahi kaji na rantse maka ka fita idanuna, kai wani irin masifa ne,haka kawai kabi ka sani a gaba da fitina tunda ka fara aiki a gidan na kake takalata tun jiya?

    Kiyi hakuri don Allah bada sanina bane, muhammad yace da sauri yana matsawa gefe duk da sumayya ta masa rashin mutunci a farkon zamansu, Amma bata taba masa a cikin mutane ba, koh zata masa masifa sai insun kasance su biyu, amma wannan a gaban sarki take masa zagi haka bataji kunyar mulki ba? a take yaji wani irin tsanar yarinyar.

    Ke nabila matsalata dake kenan rashin hakuri da rashin kunya, d’aya daga cikin mazan ya fad’a yana mamakin rashin kunyar nabila

    Gaskiya nabila halinki sai Allah ace ke a rayuwar ki rashin kunya ne baya baki kunya a gaban Abba kike irin wannan tsewar kamar ba sarki bane a gaban ki?

    Kunya ne ya kamata da sauri ta sunkuyar da kanta kasa, cikin sanyin jiki ta fita a falon, muhammad ma hakuri ya kara basu ya fita, yana fita yaga nabila tsaye alamu dai shi take jira.

    Wallahi wallahi in baka fita idanuna ba zan maka rashin mutuncin da ba’a taba maka ba, matsiyaci kawai shashasha duk cikin turanci take maganar.

    Kala muhammad baice mata ba ya nufi kofa, sai masifa take Amma shi koh juyowa baiyi ya kara ganinta ba, yana gaba tana baya har suka fitoh a flat in sarki ta shiga nasu, muhammad kuma ya wuce sashen shayi.

    *****************
    Sumayya na bude kofar falon khadija ta gani tsaye da kaya a hannu, da mamaki tace”tsayuwar me kikayi a nan kuma, kika kasa shigowa koh rashin gaskiya ne”?

    Ah ah aunty yanzun nake kokarin shigowa.

    “Aiko kwara ki shigo inkam” tace tana koma ta zauna a kan katifa.

    A hankali khadija ta karaso falon kayan dake hannunta ta kai d’aki, sai kuma ta makale taki fitowa gabaki d’aya fargaba ne a Ranta, ganin fuskar sumayya a hade.

    “Khadija wai tsayuwar me kike a bakin kofar nan ne da bazaki shigo falon ba”?

    A hankali ta shigo falon tana rabe-rabe a jikin falo a nesa da sumayya ta tsaya.

    “Waike khadija meye haka? zama zakizo kiyi muyi magana”

    Kiyi hakuri Aunty wallahi ni bansan da maganar wayar nan ba, kawai sai naga ya bani shine fa danaki karba ya shigo falo.

    “Nidai bance kome ba nace kizo ki zauna muyi magana”

    A hankali ta matso ta zauna a bakin katifar.

    Kallonta sumayya tayi “menene tsakanin ki da kalamu-wahid”?

    Wallahi Aunty babu kome a tsakanin mu dashi kawai fa mutunci muke, kuma aunty koh soyayya zanyi sai nayi da d’an yaron nan?

    “Oh yaro koh lalle kam waya gaya miki ba’a auren yaro ai da ba’ayi da bazan aure yayanki ba”

    Kai Aunty yayana fa ya baki shekaru 4 rus fa, Amma kalamu bazai girmeni da 2 years bama.

    “Kwadaiji dashi wallahi ina nan ina zuba ido, kuma ga wayar taki saiki rike, tace tana mika mata kwalin wayar”

    Amsa khadija tayi da sauri ta ruga d’aki da gudu tana murmushi don wallahi ba karamin son waya take ba.

    “Khadija dawo nan”

    Jin abinda sumayya tace yasa khadija dawowa ta zauna.

    Kinga khadija waya a zamanin nan cikin kaso goma ya kwashe kaso 7 na hanyar lalacewar yara, sauran 3 nan sune ake amfanuwa, ki kula da wayar nan ban baki ita don kiyi abinda ranki yake so ba, kinga waya sirrin mutum ne wani bazaka taba tunanin koh yatsa aka saka masa a baki zai tauna ba, Amma in aka amshe wayarsa abinda za’a gani bamai kyau bane?na barki ki rike wayar nan ne saboda kalamu Amma ki rufamin asiri ki ji tsoron Allah ki kiyaye shiga inda bai dace ba”

    Insha Allah aunty zan kiyaye.

    “Yauwa sannan zaki iyya hawa online Amma ban yarda ki d’aura hoton ki ba sam banaso”

    in Allah ya yarda Aunty

    “Toh tashi ki tafi d’akin”

    D’akin khadija ta shiga ta had’a wayarta daman oready ya saka mata wayar a cherge, ya saka mata sim suka, tana kunna wayar aiko ta shiga latsawa, ya sauke mata facebook whatsApp da instagram harda telegram duk ya bubbude mata account, call ne ya shigo wayar da sauri tayi picking ganin rubuta daya bayyana Nurul-Qalbi a screen in, tana d’agawa taji yayi sallama hade da kiranta da kanwar sa.

    da masifa ta fara magana, Allah ya sauwaka ka zamo yayana wallahi wane kai kaji na fad’a maka.

    Shuru yayi bai mata magana ba, jin baiyi magana ba yasa ta dawowa hayyacinta cikin kunya ta Amsa sallamar, tana masa godiyan waya daya bata.

    baiyi magana ba har lokacin, ita ma shuru tayi kamar yanda yayi,sai da yayi minti biyu yace mata ta hau whatsApp ya mata messenge.

    Kashe call in tayi ta hau whatsApp ganin akwai enough card a wayar.

    Khadija kamfa gabaki d’aya yau waya ya d’auke mata hankali sosai, tana gama girkin ta, ta nuke a d’aki sai hira suke da kalamu, Abin har yaso bawa sumayya dariya daga zaran khadija taji motsen zata shigo d’akin saita kifa wayar ta kama baccin karya, Amma batace mata kome ba tunda yanzun hutun makaranta suke, sai kalamun yazo zata masa fad’a maganar karatunsa karya biye shashanci.

    Ranan fa khadija a d’aki tayi shimfida a kasan tiles ta kwanta da waya a hannu, sumayya ita kad’ai ta kwana a falo.

    ***************
    Yau kwanar muhammad 25 yana zuwa aiki gidan sarauta, zuwa yanzun ya fara fahimtar Halin mutanen gidan sosai, especially nabila ba karamin haushin yarinyar yake jib, bad’an kad’an ba, yau tun Asuba yayi wanka yabar gidansu, kasancewar yaune za’a fara bikin kanin sarki(Ramadan) kamar yanda yaji ana fad’a, shiyasa tun asuba zasu tafi aiki, don shirya shayi mai yawa da zai d’auke mutanen biki zasu wuni sha, duk lokacin da aka nemi shayi a samu kar ya kasance babu, aiko hakance tun safe da sukaje basu zauna ba daman har yanzun ba’a sakar ma muhammad hannu ya girka shayi shi kad’ai ba, anfi sashi ya rarrabawa mutane.

    yau haka ya wuni aiki saiya kaiwa flat innan yana dawowa a bugo telephone in kitchen ace yakai shayi, gabaki d’aya yayi mugun gajiya.

    Haka muhammad sukayi ta fama da aiki har na tsawon kwana 4, sai yau aka d’aura aure, da misalin karfe 4 na yamma liyafa aka had’a a tsakar farfajiyar gidan, manyan sarakuna da manyan kasa ne makil a ciki, masu kudi da shuni, tunda aka fara bikin sarki bai hallaci koh wani liyafa ba sai d’aurin aure da wanda yanzun ake, muhammad ne ya karaso filin yana raba shayi koh wani table yana aje musu nasu dayake taron na mazane da mata, kuma tarone na manya yasa Al’ameen yake bin kome sannu sannu karyayi kuskure koh laifi, kwala masa kira nabila tayi ganin ya wuce table nata da suke xaune da kawayen ta, bai aje musu shayi ba zai tafi next table, kai malam bazaka kawo mana namu shayin ba!!

    Cikin haushi yazo zai dongora mata shayin a gaban table inda suke, by mistake kafarsa ta harde da cafet inda aka shimfid’a a kasa, kawai shayin ya watsale sai jikin kawar nabila, ihu kawar ta saka wanda yaja hankalin jama’a, ai nabila na ganin haka batayi wata-wata ba ta tsinke muhammad da mari.

    Kafun ta sauke hannunta muhammad ya bata wasu tagwayen mari hagu da dama, masu masifar zafi ihu da sake cikin azaba don a tsawon rayuwar ta bazata iyya tuna lokacin da aka bugeta da wayon taba.

    Yayan nabila dake gefen su ne ya mike cikin zafin nama ya d’aga hannu zai wanke Al’ameen da mari, da sauri Al’ameen ya cafke hannunsa cikin matsanannin cin bacin rai ya nuna mustapha da yatsa, jikinsa har rawa yake cikin kakkauran murya yace karka kuskura ka tabani..

    Ai bai karasa maganar ba Ramadan(Ango)daya karaso wajen don abin sosai yajawo hankalin jama’a ganin mai aikin gidan sarauta ya mare yar gidan, cakumo kwalar muhammad yayi cikin zafin nama hade da kai masa naushe a fuska, da sauri Muhammad ya kauce a zafafe wanda yayi sanadin yagewar kwalar rigansa da ramadan yake rike dashi.

    A take Ramadan ya ja da bawa tare da kwalo ido waje, jikinsa har rawa yake yana nuna wuyan Al’ameen, sai kuma cikin sauri yasa hannu akan rawanin fuskar sa zai…………

    ✨Ruqeenjalal✨

    🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
    🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯
    ~ Na ~

    🍃 *Rukayya* *Ibrahim* 🍃

  • Matar Makaho 96-97

    Matar Makaho 96-97

    Page9⃣6⃣&9⃣7⃣
    Duk masu Aljanu sun zuzzube a kasa, muhammad da gudu yayi falon cikin gidan duk da yaga tashin hankali a cameroon Amma wannan tashin hankalin tabanne koh mutum baida Aljanu indai yaga kamila sai tsikar jikinsa ya mike, yana shiga falon yaga an watsar masa da jinjiraye akan kujera, kawayen dada tuni sun ruga daki da sauri ya ciccibi yaransa ya manna a kirjinsa yanemi gefen daining ya tsaya yana jijigasu.

    Ta gefen sumayya kam bayan d’akunan gidan suka nufa mahmah dake dana da jiki, gudu take kamar kazan Agric irin sunyi naman nan, kowa fa gudu yake abin dariya abin tausayi a take ramadan ya kira yusuf ya sanar dashi, Ammar ma abie ya kira don su harga Allah abin ya basu tsoro especially ganin yanda kadangarun makwanta ke biyowa ta gini da gudu suzo wajen kamila, gasu bataliya guda.

    Ba’a d’auki lokaci ba saiga Abie ya shigo shikaran kansa abin ya masa tsoro, Amma sai yayi ta maza ganin nafisa, babban get in ya wangale galala gabaki d’aya ana kallon cikin gidan, nuni yama nafisa dasu fita waje su tsaya, ba musu ganin get a bude ta kora mai kadangaru suka fitoh bakin get suka tsaya suna hangen cikin gidan.

    Daidai lokacin yusuf da mijin nafisa suka iso a tare, don shima wani abokinsa dake unguwan ne ya kirasa akan yaga kamila da nafisa sai gudunsu mutane kiyi.

    A get yusuf ya sauka suka nufo inda abie ke tsaye, yana ma nafisa masifa akan sun shigo sun dagawa jama’a hankali, ita kuma sai hakuri take basa akan tazo tana son ganin muhammadsumayya da hafsa taji labarin duk suna gidan nan.

    Daker aka shawo kan abie da wasu mazajen unguwan akan yayi hakuri aji meke tafe dasu, rukiya yusuf yayi ma masu Aljanun suka farfado, matan da suka gugudu ma duk aka tarkatosu, sumayya kam d’ankwali ya fadi koh takalmi babu, muhammad har lokacin yaransa na hannunsa,shimfid’a manyan taburmaye akayi a gefe guda hudu, gefen maza daban na mata daban kowa aka ajesa, wasu da dama kam sun gudu gida wasu kuma na cikin d’akuna, sun rantse bazasu kara yarda su kara kallon kamila ba, haka masu Aljanu duk an hanasu fita.

    Zama akayi sarki kam kujera aka kawo masa ya zauna, yasa aka shigo da nafisa kamila kam a wajen get akace ta zauna saboda kadangarun ta.

    Yusuf ne ya kalli nafisa, baiwar Allah lafiya kikazo kika d’agawa mutane hankali da wanshan abin?

    Kuka nafisa tasa a hankali ta kalli mijinta, sam bataso yau ta sanar da sirrin ta a gabansa ba tsoron kar auren ta ya mutu gashi batasan inda zata shiga ba.

    Wai ba magana ake miki bane kinsan waye a gabanki kuwa, sarkine da kansa ki kama kanki baya magana biyu?

    Kayi hakuri nasan yau koh naki koh naso sai gaskiya tayi halinta, shiyasa na gwammaci kunyar duniya data lahira, gwara na nemi yafiyar su koh Alhaki zai barni.

    Shuru kowa yayi ya zubawa nafisa ido don jin me tazo dashi.

    Abubuwan da suka faru a shekarun baya da suka wuce, nidai sunanan nafisa Abdullahi kamar yanda wasu suka sani macece maison abin duniya gabin bokaye, bayan nayi aure da mijina saboda halayena ya rabu dani, lokacin na haifi yarinyata kwalli d’aya da Allah ya bamu mai suna kamila, duk yanda naso na koma gidan mijina sam yaki amince wa hakan yasa na shiga islamiyya saboda a lokacin bana zuwa boko sam, mun hadu da safina ne A makarantar islamiyya muka kulla kawance, a lokacin don ance hali sai yazo d’aya ake abota, kawancen mu yayi karfi a lokacin safina ke sanar dani bata da buri saina auren Abdulsalam Amma goggon ta(dada) bata bata goyi baya ba.

    Ni kuma jin haka yasa na bata shawara muje gun wani malami danaji labarin sa, nima so nake na koma gidan mijina ba musu safina ta samo kudi muka kama hanya har Ardo-kwala wajen wani hanshakin boka.

    Bayan munje da bukatan mu yake sanar damu Auren safisa da Abdul bazai taba yuwa ba, mundin yana tare da hafsa don soyayyar su na daban ne kuma mai karfi, dole rabasu shine zai iyya taimakawa ta samu Abdul salam.

    Babu musu mukace mun Amince a rabasu, nima na shaida masa bukatana nason komawa gidan mijina aiko cikin sati d’aya baban kamila ya dawo yace shi kaf duniya saini, na koma gidan mijina aiki yayi kyau sai dai aikin safina shuru baici ba, haka muka koma wajen bokan nan yake sanar damu saimun kawo idanun jariri, kafun mu iyya dishar da soyayyar dake tsakanin su,yaji kwata-kwata baya ganin farin hafsa sai bakinta, sannan bazai iyya rabasu ba sai safina ta had’a da kirsa.

    Babu musu na samo wasu rikakakun yan daba muka biyasu suka sato mana jinjiri, haka ba tausayi aka kwakule idanunsa a take ya mutu koh shurawa baiyi ba, muka kaiwa boka ido yayi aiki aiko koh sati ba’ayi ba rashin zaman lafiya ya wanzu a tsakanin ma’auratan nan, yayinda na baiwa safina shawara ta shiga sacewa mutanen gidan Abubuwa daga karshe ta likawa hafsa.

    Aiko shawarata taci don cikin wata d’aya akayi hakan kuma aiki yayi Abdul ya sake hafsa.

    Bayan nan muka koma wajen boka ya mana wasu aikin gabaki d’aya ya rikitar da dada da yan uwanta akan sai Abdul ya Aure safina kuma duka aikin bokane.

    Bayan auren kuma safina tazo da bukata akan tanason a raba sumayya da Abdul don ta fahimci yana tsananin son yarsa, shawara na bata akan basai mun koma wajen boka ba ita ta d’auki mataki da kanta, amma abin mamaki har Kashe mata aure dukan sumayya yajawo wannan dalili yasata tayi sanyi ganin babu yanda ta iyya da sumayya.

    A lokacin da sumayya takai shekara 14 sai gabaki d’aya hankalin safina ya tashi ganin irin kyaun data tashi dashi, gashi koh a gidan su farin jinine da ita gashi kowa na dangi baida magana sai sumayya, kome sumayya hakan yasa safina fara kishi da sumayyar.

    Kasa hakuri tayi muka koma wajen boka akan a raba tsakanin sumayya da ubanta, dayan gidan su suji sun tsaneta yanda zatayi rayuwa cikin kaskanci, Amma boka yace hakan bazaiyu ba sai an diga magani a idanun yaro matashi mai tashen balaga kuma ya kasance tauraren sa nada karfi, wannan zance da mukaji yamatukar d’agawa safina hankali don ita tana da tsoro ba kamar ni ba.

    Nikam jin haka sai wani tunani ya fado mini na Al’ameen dake likewa yarinya ta, kwata kwata bana sonsa da yarinyana,gashi nayi iyya kokari na babanta ya rabasu yaki itama duk irin lallama da dabara da zan mata ta rabu dashi Amma taki, hakan yasa na kirawo wa’innan yan daban da suka taba sato mana jinjiri na basu hoton muhammad dake wajen kamila na d’auka, na musu kwatancen makarantan su a ranan suka kama muhammad bayan sun bugar dashi suka daukesa har Ardo-kwala wajen boka, sai da akayi sati baya cikin hayyacinsa, ana masa wankan magani da digawa a ido, kafun aka mayar dashi bayan gari aka jefar.

    Wannan shine dalilin makantan Al’ameee, ta karasa maganar tana kuka, jama’ar dake wajen salati suka buga, Muhammad kam gabaki d’aya jijiyoyin kansa su mike bacin raine karara a fuskarsa wanda kallo d’aya zaka masa kasan ran maza ya baci, mikewa dada tayi tsaye habba nafisa mai muka miki? yanzun da haden bakin safina aka aikata wannan mummunan aiki, Sai kuma ta fashe da kuka take surutai ya fara tashi kowa yana furta Albarkacin bakinsa.

    D’aga hannu sarki yayi tare da bada umurni kowa yayi shuru, aiko shurun akayi ya bawa nafisa dake kuka damar ci gaba da bayaninta.

    Bayan an gama aiki kuma yaci, sai dai sam bai kama Abdul ba iyya yan gidan ne sukaji basa kyaunar sumayya sam, sai kuma Abdul ya d’agata ya maidata hostel wanda hakan ya rage musguna mata da ake, kuma hakan baiwa safina Dadi ba, taso abar sumayya a gida taci kwakwa.

    Duk yanda mukayi babanta ya rabu da ita abin ya gagara karshe dai haka mukayi hakuri aka cigaba da rayuwa, kamila ma taki muhammad a lokacin ganin ya makance.

    Lokacin da sumayya ta zama cikekkeyar budurwa hankalin safina ya tashi hassada take da sumayya karta samu mijin dayafi ubanta kudi, koh wani mai mulki kwata kwata so take taga sumayya ta kaskanta a rayuwa wannan dalili yasa muka koma wajen boka daman sumayya nada wani hali na raina wa mutun ArZiki, aiko da halin nan nata aka samo mafita wajen mata magani yanda samari zasuji basa sonta kwata kwata wanda majority zasuce halinta ne ya ja mata.

    Bayan nan sumayya ta rasa manemi sai dai ba’anan gizo ke saka ba, sumayya na samun kudi sama da safina don tana aiki, ga kaunar da mahaifinta ke mata, shawara na bata muje wajen wani bokan aiko munsamu wannan aiki da wanshan ya kasa wannan yace zai mana amma da sharadi, shine sai an nemi makahon yaron da mukama asiri, mu had’asa aure da sumayya wannan ne zaisa ta fita a zuciyar Abie,yanda mukasa muhammad yana kallon baki, haka su dada ke kallon bakin sumayya, kuma duk adadin sex da zasuyi, haka aiki zai kara karfi tamkar muna bawa shuki ruw, tsanar ta a zukatansu zai karu, amma aiki zai lalace mundin aka rabasu misali d’aya na wani kasa d’ayan na wani kasa aiki zai karye.

    Ba musu muka abince daman safina ta shanye kowa a gidan, kowa tsoron ta yake sai abie kawai baya shayin ta, wannan dalili yasa ta samu su babuji da dada ta tilastasu akan aurar da sumayya kuma ita ta sama mata miji ba musu suka amince jiki na bari.

    Mu muka nemi mamman dayaje ya samu muhamamd akan shine uban sumayya, zai basa auren ta amma dayake Al’ameen nada tunani sai yaki Amince wa, karshe dai wajen Bappa suleman akaje don munji labarin yanada son kudi, mamman ya sake masa kudi masu yawa akan zance, wanda gaskiya lamari sharri muka ma suamyya akan tayi ciki saurayin da zata aura ya fasa, a taimaka a had’ata da muhamamd ba musu ya amince da zancen.

    Bayan auren sumayyya da muhammad magani yaci Abdul ya tsane yarsa, duniya kaf babu wanda yaki jini irinta, muma sosai muka sakawa rayuwar sumayya ido duk wani motsenta muna sane dashi.

    A lokacin An jima da sakar mini yata kamila wance ta koma makaranta tana ci gaba da karatunta da bata samu tayi ba, kusam ta dawo rayuwar muahmamd wanda bansan da labarin ba saida taje gidan Adara aka mata duka, a lokacin raina ya baci kuma na jama kamila kunne akan ta rabu da rayuwar yaron nan in tanason kanta da lafiya, amma bata daddara ba ita da kawarta suka je mutum biyu wajen boka………………………………………har sanadin haka ta samu wannan matsala na kadangaru wanda na tabbata Alhakine yake bibiyata.

    Munyi neman duniya wa bokan nan don mu biyasa koh mu basa hakuri ya rabu da ita, Amma ina bamu gansa ba duk malaman da muka kira shuru ba sauki, a lokacin na shiga tashin hankali ita kuma safina a lokacin take jin dadin ta, naje wajen ta akan ta taimaka mini akan zancen kamila koh da kudine don kaf abinda muka tara ya kare a wajen jinya amma haka safina ta murza ido bata tuna irin hallaci dana mata ba ta hanani koh biyar, ni kuma abin yayi matukar bata mini rai hakan ne yasa na d’auki kayan dakina na sayar na biya yan dabanda suke mini aiki tsawon shekaru, akan su kashe mini muhamamd yanda aikin safina zai lalace sannan nima na huce takaicina akansa, tunda ata dalilinsa rayuwar yata ya shiga garari, don haka kowa ma ya rasa.

    Aiko yan ta’andan nan sun bani tabbacin batar muhamamd wanda zancen yaje har kunnen safina, kuma ta zargi nice wanda har gida tazo mukayi fad’a kasha kasha, ta tafi ban sake bi takanta ba, sai kawai labarin rashin lafiyar safina ya riskeni, da kuma dawowar muhammad gida.

    Shine nazo neman yafiyar ku don Allah ku yafe mini sharrin shaid’an ne?

    Ai kece shaid’aniyar in kam, munafuka wallahi bazan taba yafe miki ba har abada kin cuceni kin rabani da matata kin muzguna ma rayuwar yata, Allah ya isa tsakanina daku kuma bala’i yanzun kika fara gani.

    Jin abinda abie yace yasa dada mikewa tsaye da hannu tayi pointing in mutanen gembu, maza maza su tashi su tafi gidan shugaba su tattari safina a yau innan su maidata wajen dangin uwarta babu ita babu safina har Abada, ita tana ta bauta mata ashe shaid’aniya ce.

    Baban kamila mikewa yayi yanzun nafisa har kisan kai kike? toh kiji daga yau bani bake kuma bara kiji na sakeki saki biyu daman babu igiya d’aya a tsakanin mu, ki tattara yarki ku kara gaba koh gidana karki koma don bakizo da kome ba, bazan iyya zama daku ba, kuka nafisa tasa da sauri ta rike kafar baban kamila tana neman yafiyar sa tunkudeta yayi ya kama gabansa.

    Duk yanda yusuf yaso wajen yayi shuru abu ya gagara ganin yan gidan Adara sun rufarwa nafina da duka, waya Ammar yayi wa ofishin yan sanda cikin kankanin lokaci sukazo daker aka kwace nafisa anso tafiya da ita, Amma yusuf ya hana yace a barta kodon Albarkacin kamila dake d’auke da wannan matsala taje duniyace, haka ta mike daker tana koran kamila suka bar unguwan gwanin tausayi.

    Hafsa a ranan kuka tasha bana wasa ba kuma itama ta basu labarin, bayan rabuwarsu akan cikin bai zube ba, jinine ya zuba kuma mahaifinta yace sai an zubar da cikin Abdul salam, baza’a haifa masa a gida ba ganin yanda ransa ya baci yasa kanwar mamarta d’aukar ta ashan ta haifi kalamu bayan haihuwar sa ne matar cousin nata kabeer ta rasu, bayan shekara d’aya da mutuwarta sai ya nemi ya auri hafsa kuma ba musu findon ta amince dayake kowa yasan halin ta macece mai nutsuwa, kuma bayan auren su ta rike yaran kabeer hannu bibbiyu, wannan dalili yasa sa rike d’anta itama kamar nasa hatta su babayo basa nuna wa kalamu ba yan uwansu bane harya girma, bayan kalamu ta haifi yara uku shamsiyya(tayi aure a maiduguri) falmata da musa (auta) duk yaran hafsa ne da suka haifa da kabeer.

    Sosai abie ya nuna nadamar sa kuma ya nemi yafiyarta tare da sanar da ita insha Allah gobe gobe xasu je maiduguri har wajen mahaifinta ya nemi yafiyarsa wannan umurnin yusuf ne kuma hardashi zasu.

    Washe gari haka aka tattaru duka aka wuce maiduguri duk yanda akayi sumayya ta zauna saboda yanayinta amma ina tace da ita za’aje taga kakan ninta da kanwarta shamsiyya, ba yanda aka iyya haka aka tattaru harda Ammar suka wuce maiduguri.

    Da isarsu suka sauka a gidan sarki yayinda Ammar ya nemi Alfarmar su muhammad su bisa gidan Uncle nasa su kwana, bazasuji dadi ba in sukasan yazo Maiduguri ya kwana a wani wajen, ba musu ramadan da muhamamd suka bisa jin yace musu babu kowa a gidan daga uncle nasa sai matarsa da yarsu babba.

    Unguwane mai kyau suka shiga cikin wani gida madaidaici mai kyau,sunyita sallama Amma shuru ba’a amsa ba, hakan yasa Ammar nufar kofar falon ganin kamar a bude, aiko yana turawa yaga kofar ta bude, bismillah yama su muhammad ba musu suka shiga da sallama, amma shuru.

    Macece zata kai shekara 44 zaune akan sallaya a falo ta fuskanci gabar rabin fuskar ta kawai suke iyya hanga zaune take tayi tagumi kana ganinta kasan tayi zurfi a tunani.

    Girgiza kai Ammar yyi saboda wannan abin ba sabo bane agunsa, abune da ya saba da ganinta a haka, da sauri ya nufi wajen da take ya tabata Aunty!!!!!

    Da sauri ta dawo hayyacinta, ta dubesa a dakile tace Ammar yaushe kazo?

    Yanzun nazo kina sana’ar taki ina zakisan na shigo?

    Shuru ta masa alamu dai batada yawan magana, koh ince damuwa ya maidata haka.

    Ganin ta masa shuru yasa sa tambayar ta, aunty ina mom?

    Basanan Ammar kai kad’aine?

    Ah ah Aunti babba nida abokai nane, yace yana nuna mata su Ramadan dake tsaye, yayinda shi kuma muhammad ya zuba ma fuskar matar ido yana kallonta, kallo irin na tsana, koh shekara dubune bazai manta da wannan fuskar ba.

    Ai tana kallonsa jikinta ya soma rawa da sauri ta mike tsaye sanye da hijab, tana nunasa da hannu sai kuma ta yanke jiki zata fad…………..

    ..
    ✨Ruqeenjalal✨🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
    🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯
    ~ Na ~

    🍃 *Rukayya* *Ibrahim* 🍃

  • Matar Makaho 88-89

    Matar Makaho 88-89

    Page8⃣8⃣&8⃣9⃣
    Da sauri muhammad ya damke rawanin sa, ya hana Ramadan bude masa fuska, menene haka? banaso karka kuskura ka bude mini fuska.

    Har lokacin jikin Ango rawa yake cikin mamaki yace a ina ka samu sarkan nan, waya baka wanene kai?da karfi yace security.

    Jama’an gurin duk sun mike banda sarki dake zaune akan kujera duk rikicin da ake baiko d’ago kansa ba bare yasan abinda ke faruwa.

    Mustapha ne yayi magana a rude wallahi sarkan ne, sarkan magadan masarauta ne, a ina ka samo sarkan nan?yana maganar yana kai hannunsa wuyan Al’ameen zai duba sarkan.

    Da sauri Al’ameen ya buge hannunsa, Shuru yayi yana kokarin barin filin, da sauri Ramadan ya jawo sa baya yana kwalawa Yayansa kira, da sauri sarki ya juyo yana kallon Ramadan da mamakin kiran gona da yake masa?

    Yaya sarkan magada ne a wuyan wannan me kawo shayin, kuma yaki bari aga fuskar sa, bamu yarda dashiba suspect ne?

    Ai kafun ma ya gama magana saiga sarki ya sauko a kujera da hanzari ya nufi inda suke tsaye, daga isarsa hannu yasa a kamo sarkan yana kallo sai kuma jikinsa ya fara rawa ya kamo rawanin fuskar muhammad.

    Da sauri muhammad ya dafe Hannun sarki dake kan fuskar sa yana girgiza masa kai, alamun rashin son hakan.

    Shima sarkin girgiza kai yayi, hakan yasa muhammad sauke Hannunsa akan na sarki.

    A Hankali yake warware Rawanin kansa, tsaf gashinsa ya bayyana mai masifar tsawo da sheki, a hankali ya warware na fuskar sa, da sauri ya dafe kirjinsa cikin tsananin mamaki da sauri yace muhammad!!!!!bai karasa ba kawai hancin sa ya fara tsiyayo da jini a hankali ya fara lumshe ido sai kuma ya yanke jiki zai fadi, da azama muhammad ya taro mahaifinsa da sauri ya rungumi abinsa cikin matsanan ciyar mamaki jin sarkin ya Ambace sunan sa.

    Zuwa fadawa sukayi aka kewaye sarki muhammad ne ya ciccibi sarki har cikin flat nasa, atake gida ya rude da koke koke, ga masu tsananin mamakin muhammad da abinda ya had’asu da sarki harya Ambace sunan sa?

    Bayan Ankai sarki d’aki likita da abokan aikinsa suka rufu a kansa, yayinda Ahlin gidan ke make a babban falon fada, daga maza har mata harda wa’inda muhammad bai taba ganinsu ba, mikewa yayi zai fita a falon da sauri Mahmah ta riko hannunsa, ina zaka yaron nan?

    Gidan mu mana ba aiki bane ya kawoni mama?yace yana kallon nabila dake rakube a jikin kujera fuska jajjawur ga jini ya taru a idanunta da gani dai ta maru.

    Wani irin ka tafi kuma kaje ina baka ga Halinda d’ana yake ciki ba? kuma na tabbata yana farfadowa kai zai nemi gani.da gorancen hausar ta take magana.

    Toh ni kuma so nake na tafi gida ranki ya dade, in Allah ya kaimu gobe ai zanzo aiki duk maganar da zamuyi sai muyishi?

    Ramadan ne ya mike,Hala nan dajine da bazaka iyya kwana a cikiba?

    Ban saba kwana gida irin wannan ba, kasa bacci zanyi, yace yana fita a falon babu wanda yayi yunkurin hanasa, sai rakasa da ido sukayi.

    Muhammad na zuwa gida gabaki d’aya abin duniya ya damesa, amma baicewa baba kome ba, shima baiyi magana ba duk da yaga sarkan wuyan Al’ameen Amma baice kala ba.

    Yau koh abincin dare kasa ci yayi, badaru da gidado ne sukaci gabaki d’aya jikinsa yau A sanyaye yaki kome yanayi a sake kamar mai ciwon fata.

    Har dare bai rumtsa ba, tunani kawai yake a ransa, donshi dai bai gane inda abinnan ya dosa ba, menene Alakansa da mutanen nan shi zaman kasar ma ya isheshi kuma ya rasa hanyar da zaibi yabar kasar gabaki d’aya, yau wani irin kewar iyalinsa yame dason jin duminta, ba irin tambayar duniya dasu gidado basu masa ba Amma bakome yake ce musu.

    Da misalin karfe 2:30 sukaji ana bugun kofar gidan, babane ya fita zai duba koh lafiya yayinda muhammad ke kwance duk da idanunsa biyu Amma bai mike ba.

    Baba bai jima da fita ba sai gasa ya shigo d’akin su muhammad, mikewa yayi yana kallon baba.

    Muhammad ka fitoh ana sallama dakai?

    Da mamaki yace dani kuma baba, sallamar ma tsakar dare?

    Ka tashi daga gidan sarautane.

    Gaskiya baba kace musu su bari sai gobe, koma menene in gari ya waye sai ayi bawai a tadani tsakar dare ba kamar tashin duniya.

    Muhammad yaushe ka koma mara kunya ban sani ba?

    Kayi hakuri baba

    Tashi kawai kaje kaji da wani sako aka turosa?

    Mikewa yayi kawai ya sanya kayansa ya fitoh a d’akin, kallon mutumin da aka aiko wajen sa yayi, lafiya malam?

    Lafiya muhammad ana neman ka a fada.

    Tsakani da Allah in Ana son ganin mutum sai azo tsakar dare ya kirasa ai naga gari zai waye?

    Babane ya kallesa, muhammad ka iyye bakinka banason irin wa’innan kalami, bai dace da kai ba, don haka ka bisa kuje bakasan menene dalilin kiranka ba, ya kamata kaje kaji.

    Baiyi magana ba kawai ya nufi hanyar kofar gidan, binsa a baya mutumin yayi daman da mota yazo ba musu muhammad ya shiga suka wuce.

    Daga isarsu masarauta gidan kaman rana koh ta ina fitilune haske kaman farin wata, ga mutane a tsatsaye kamar rana bakin dake gidan duk basu tafi ba, Al’ameen na fita a motar gabaki d’aya aka ringa binsa da ido har suka ratsa babban falon sarki, suna shiga mahmah da lawixa harda su ramadan muwaddat nabila duk suna cike a falon wasu kamma kuka suke fuskar lawiza da mahmah jazir alamu kuka sukasha, da sallama ya shigo falon amsa masa sukayi suna mikewa tsaye gabaki d’ayansu, binsu yayi da ido sai kuma ya nufi kofar d’aya falon, ya shiga yana shiga duka suka rufa masa baya zuwa ciki, tunda ya tinkare kofar bedroom yake jin salati ga sunan sa da ake kira da sauri ya cusa kansa adakin.

    Sarkine kwance akan gado yana tari jini na biyo bakinsa yana Ambatun sunan muhammad, ai Al’ameen baisan lokacin da yayi super ba ya isa garesa koh tsawon shekaru nawane bazai taba manta wannan fuska ba bare shekarun da baiwuce a kirgasu ba, hawaye ne ya cika masa ido ganin halinda mahaifinsa abin sonsa ke ciki, duk da ya rayu da takaicin gudunsu dayayi Ya kuma sha Alwashin duk randa ya gansa zai basa mamaki shima, amma bai d’auka zai gansa a irin wannan halin ba, karasawa yayi garesa a hankali ya kamo hannayensa dake dafe a kirjinsa cikin kuka yace Abbajoooo!!!me nake gani haka ka rufa mana asiri kar maraicin ya mana yawa?

    Ai jin muryar sa da sauri yusuf ya mike ya rungume d’ansa a zaune, tunda ya hau karagan mulki ba’a kara ganin hawayen saba sai yau, hawaye ne yake siyaya a idanunsa, ganin haka yasa muhammad fashewa da kuka mai matukar karfi yana banbare Abbajon sa a jikinsa, tare da kallon doctor dake gefe, habba bawan Allah jini nefa kebin bakinsa kun barsa haka?

    Kayi hakuri yallaboi wallahi tun da ya farfado anyi anyi ya tsaya a basa taimako yaki gashi ciwonsa baison damuwa Amma yaki ya saida hankalinsa.

    Jin haka yasa muhammad kokarin mikewa tsaye,Ai da sauri yusuf ya rikosa da karfi tamkar uwar da za’a rabata da jaririnta, fuskar muhammad ya rike sai kuma ya soma magana a hankali, tabbas jini yafi ruwa kauri, babu tantama wannan jini nane muhammad nane koh babu sarka a wuyanka akwai alamun jini muhammad ku yafe mini.

    Ah ah Abbajo ka rufa mini asiri karkace haka kayi hakuri ka rayu damu yana magana yana kuka.

    A hankali sarki yace muhammad dukkan mai Rai mamaci ne in lokaci yayi dole mu amsa kiran mahalincin mu.

    Don Allah Abbajo kabar irin wa’inan magana, likita kazo ka taimaka masa, da sauri likitan ya maso da taimakon muhammad suka gogi masa jinin dake bakinsa ya taimaka masa ya shiga toilet ya shanja kayan daya baci, daidai ya fitoh har muhammad ya sauya zanin gado.

    Yana fitowa ya kwanta likitan ya d’aura masa ruwa da Allurai ya fita, a hankali yusuf ya kama hannun d’ansa sosai ya zurawa muhammad ido yana kara tasbihi a zuciyar sa yaushe yabar muhammad yaro karami d’an shekara 13 Yau shine ya zama cikeken mutun tamkar shi a lokacin da ya barsu muhammad?badon shekaru ba koh yau duk wanda yaga muhammad zaice shine.

    Na’am Abbajo.

    Ya Aishan Adara?

    Jin tambayar da ya masa sai da gaban sa ya fadi, a halinda mahaifin sa yake cikin nan bai kamata ya kara d’aga masa hankali ba, cikin sanyin jiki yace, Tana Lafiya Abbajo.

    Murmushi yusuf yayi cikin karfin hali, nasan xuwa yanzun ta rage masifa koh? nama san itama ta tsufa kamar ni?

    Hhh bata tsufaba tana nan da kyawun ta daka sani, kuma yanzun sam bata fad’a da kowa.

    Ah ah muhammad fadi gaskiya dai nasan maman ku, saidai in ba’a bata mata rai ba?

    Dafa gaske nake.

    Ta yafe mini?

    Babu abinda ka mata abbajo asalima ita ke neman yafiyar ka, don gaskiya yayi halinsa bayan bakai, meyasa Abbajo kayi fushi ka tafi ka barmu, kana rayuwan ka cikin mulki da kudi mukuma baka damu da kalar rayuwar da muke ba?

    Girgiza kai kawai yusuf yayi baibawa muhammad Amsa ba, ya sake jefo masa wani tambayar, ya jikin salim nasan zuwa yanzun kam yagirma don zai fika jiki kasan jikin mamanku garesa?

    Kwarai ma kuwa abbajo salim ya warke sosai sai godiyan Allah.

    Su lawiza da suka jima a bakin kofa suna kallon ikon Allah wai me yusuf yake nufi da yaron nan ne basu gane ba, kasa magana sukayi ganin kamar ma basu san da zaman suba sai hira suke, hakan yasasu juyawa suka fita a d’akin ganin lokaci d’aya jikin yusuf yayi sauki gashi sam ba hausa suke ji sosai ba, duk da su mazan suna hausa tsabanin mata da kwata kwata bayi suke sosai ba sai jifa jifa,

    Haka yusuf da muhammad suka ringa hira na yaushe gamo, Amma sam muhammad bai fad’awa yusuf mutuwar Aisha ba koh salim, sai asuba da sukayi sallah doctor yazo ya cirewa yusuf laidan ruwan, suka kwanta tare a Royel bed na sarki bacci ya d’auke su.

    **************
    Sumayya ciki ya shiga wata bakwai yanzun sosai tayi wani irin kumbura, har yakai yanzun bata iyya tashi da kanta sai khadija ta kama hannunta ta jata da karfi saboda nauyin cikin, abincin ma yanzun bataci daga ruwan zafi sai tie koh nama.

    Kalamu-wahid da khadija yanzun kam an dinke sosai suka shaku kalamu na zuwa gidan sumayya akai-akai gashi yanzun har kwaryan tuwo yake dashi akofar sumayya na rana,kamar yau sumayya ta gaji da kwanciyar da khafija keyi a kasan tiles hakan yasa ta kiran ta hade da mika mata kudi taje ta sai karamin katifa, Amsan kudin tayi tace bari tayi wanka.

    Tana shiga d’aki messenge ta turawa kalamu akan zata fita, kafun ta shiga wanka.

    Tana fitowa shiryawa tayi ta fita da niyar tafiya kasuwa, tana nufar get ta bude da murmushi a fuskar ta ganin kalamu tsaye sanye da jamfa wando da riga yayi matukar masa kyau abinka da bakin mutun sanye da farin kaya, mota ya bude mata ta shiga shima ya zagaya ya shiga yaza suka cillah kasuwa.

    Duk yanda yaso ya saya mata katifa da kudinsa taki yarda, yace zai cikimata ta d’auki babba, amma taki tace aunty zatayi hulo itakam babu ruwan ta.

    Tare suka dawo kasuwa ya sauketa a get nasu, ta shiga da katifar ta da kanta don tace karya shigo kar aunty ta mata fad’a, sunje kasuwa dashi bada izininta ba, ba musu shima ya shige gidansu bai matsa mata ba.

    Bayan isha’i sumayya ne kwance a falo, yayinda khadija na cikin daki suna hira da kalamu a waya, kamar a mafarki taji sallamar sa a bakin kofar falon su, da sauri ta mike zaune tana mamakin sa na rashin fad’a mata yana zuwa Alhalin kuma waya suke da juna yanzun, kalamu!!!!

    Ta cikin wayar taji yace ke don Allah fitoh ki bude mini kofa.

    Ba musu ta fitoh a d’akin kallon sumayya dake falo a kwance, tana bude kofar ya shigo gaida sumayya yayi ta Amsa masa sama-sama don yanzun koh yawan magana bata so.

    Aunty daman wajen ki nazo?

    “Khadija basa wajen zama”

    Zama yayi akan kushin da khadija ta aje masa, itama ta koma gefe ta zauna.

    Aunty daman nace mezai hana khadija ta shiga islamiyyar mu ?nayi magana da ita tace nini tun saukar ta na farko bata kara komawa tushi ba.

    “Gaskiya ne kalamu koni ina son khadija ta koma islamiyya, nama laila magana akan koh akwai islamiyya a kusa, shine tacemin yaranta babansu ke koyar dasu, ni kuma bana son khadija taje wajen sa d’aukar karatu”

    Gaskiya ne Aunty kinga kuma zuwan weekend ne aje 3 adawo 5 ?

    “Shikenan kalamu sai Allah ya kaimu next week sai na had’aku ka kaita don ni ba iyya taka kafar nake sosai ba”

    Eh aunty daman na kammala mata kome yanzun ma uniform na kawo mata da form sai a cika mata sati mai zuwa ta fara zuwa.

    “Lallai ma kalamu toh Allah dai biya ka”

    Ameen ya Amsa yana kallon khadija dake murmushi a boye.

    “Yauwa kalamu daman akwai abinda nake son na fad’a muku kaida khadija”?

    Zuciyar suce a tare ya buga da sauri suka kalli juna sai kuma suka juya suka kalli sumayya har suna had’a baki, Aunty Allah dai yasa lafiya??

    “eh daman akan kune, ba kome bane illah abu d’aya zuwa biyu, ina so daga yau…………..

    ✨Ruqeenjalal✨

    🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
    🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯
    ~ Na ~

    🍃 *Rukayya* *Ibrahim* 🍃

  • Matar Makaho 90-91

    Matar Makaho 90-91

    Page9⃣0⃣&9⃣1⃣
    “Daga yau banason kara gani koh jin ka kira khadija a waya yafi sau biyu a rana, na gaji da halinku kunce ba soyayya kuke va ?sannan kai bakada aiki sai kiranta karfa ka manta kai d’alibin kiwon lafiya ne, bai kamata kana wasa da karatu ba”?

    Insha Allah Aunty za’a kiyaye.

    “Sannan ke kuma khadija kinga dai kokarin shiga ss 2 kike, kuma niyata in kika dage saina miki registration in waec next year, amma tunda wasa zaki saka a ranki bismillah zakiyita zama har 21 years a secondary”

    Shap wayaga maman aji, kalamu yace yana dariya.

    “Kaga banason shashanci kalamu, ina muku fad’a kana sako wasa”

    Sorry Aunty zamu kiyaye yace yana kallon khadija, ke akwai sauran shinkafa ki zubamin yau nanne na tuwo ta dafa?

    Babu kawai khadija tace tana mikewa ta shiga daki.

    “Kaga kalamu tashi akwai macaroni data dafa a tukunya kaje ka iba tunda kitchen in ba bakon ka bane, karku dameni da surutu kaina ciwo yake”.

    Mikewa yayi ya shiga kitchen in ya ibo makaroni da miyar kifin gesha, yana ci yana latsa wayarsa don yanzun sumayya bata surutu kamar da.

    *************
    Muhammad basu farka ba kuma ba’a tadasu ba sai kusan 10 na safe suka farka don kansu, wanka sarki yayi sosai yaji sauki jikinsa yayi karfi, kaya ya saka muhammad ma wanka yayi yasha jumfa da aka kawo masa mai masifar kyau da tsada, abincin karyawa aka jera musu a daining tare suka karya su biyu suna hira gwanin sha’awa, a hankali sarki yace muhammad wai nikam ban tambaye ka kaninku ba?

    Wanne kenan Abbajo?

    Kanin salim mana.

    Ai macece khadija tananan.

    Allah sarki yanzun fa shekarun ta 18 da wata 9 ta kusa 19?nasan itama yanzun ta kusa nabila koh?

    Eh Abbajo ta girma abinta.

    Allah ya raya mini ku ta farkin islama?

    Ameeen, haka suna ci suna hira har suka gama yusuf ya gyara rawanin sa yana rike da hannun muhammad sukayi fada.

    Ana bude musu kofa suna shiga saida gaban muhammad ya fad’i, ganin wasu jajayen buzaye, cikin su harda baba da gidado da badaru a zazzaune, sosai fadar ta cika makil da manya da yara alamu dai yusuf yasan da taron, sake hannun muhammad yayi ya zauna a kujeransa yama muhammad nuni da kasan cafen.

    Ba musu muhammad ya zauna a hankali, yayinda mutane kibinsa da kallo na mamaki sosai.

    a hankali yusuf yasa hannu ya ja rawanin fuskar sa, take fuskar nan mai kamala da dattako ya bayyana koh yaransa basu samun ganinta a araha irin na yau, kowa na kasa yusuf ne kawai a kujera.

    Gyaran murya yusuf yayi, Asslamu Alaikum warahamatullahi wabarkatuhu.

    Gabaki d’aya jama’an dake falon suka amsa masa sallamar.

    Na gode Allah daya nuna mini wannan rana, wanda ban taba tsammanin ganinsa nan kusa ba, koh ince ban taba sa ran ganinsa ba,Ayau xan sanar daku yan uwana don duk fadar nan yan uwana ne in aka cire mutane uku,ayau xan sanar daku abinda nasan dayawan cikin ku zasuyi mamaki, muhammad Al’ameen, d’aya daga cikin masu aikin gidan nan D’anane, kuma shine a gabana.

    Gabaki d’aya falon ya d’auki surutan mutane, daker aka samu ya lafa, yaci gaba da magana, nasan dole jama’a zasuyi mamaki Amma banda mahmah mahaifiyata, don ita tana d’aya daga cikin mutanen da suka san da wannan magana,mahmah ya kira sunan mahaifiyar sa dake xaune a gefe.

    Na’am .

    A taushashe yace, Mahmah ina son ki sanar dasu Asalin abinda ya faru shekarun baya da suka wuce, bani da koshin lafiya sosai kuma inbabu damuwa ina son kiyi da hausa wa’inda basa ji, Ramadan yana fassara musu.

    Gyara zama mahmah tayi ta fara magana kamar haka.

    *SHEKARUN BAYA DA SUKA WUCE*
    Masarautar karfe shine cikekken sunan masarautar gidan nan, wanda ke d’auke da tambarin zaki ya samo asaline tun bayan shekaru da suka shude, ka’idar masarautar ne duk yarima mai jiran gaso za’a makala masa sarka na magajin masarauta, sarkane daya samo asali daga makafan masarauta, duk wanda ya d’aura sarkan badai tsafi jifa koh tsibbo ya kamasa ba saida ikon Allah.

    mutallaf shine cikekken sunan mahaifin yusuf, a lokacin sarki ne yana da matarsa ta farko mai suna Hauwa-kulu sai dai Allah bai basu haihuwa ba har girma ya soma kama mutallaf don a lokacin harya haura shekara 50, hakan yasa kasa kara aure ya auro Hajara cikin ikon Allah shekara na zagayo wa hajara ta haifa masa yarinya mace, duk da yaso d’a namiji Amma hakan bai hanasa murnan samun mace ba, aka saka mata sunan hauwa-kulu yama uwar gidan sa takwara, haka hajara tayi ta haihuwar mata har hudu rus, sosai tsoro ya shiga zuciyar mutallaf, koh baida rabon d’a namjine kasancewar su a zuriyarsu ana yawan haihuwar mata, sama da maza gashi yana son magaji ga girma ya kamasa, Amma daga baya saiya maida lamuransa ga Allah, yaran nan kaf a wajen hauwa suke ita ke kula dasu kasancewar ta bata taba haihuwa ba kuma zaman lafiya suke da hajara.

    Hajara ta sake samun ciki sam wannan karon mutallaf bai kwallafawa ransa namiji zai haifa ba sam, cikin ikon Allah hajara ta haifi d’a namiji yaro yaci suna yusuf, tunda aka haifi yusuf mutallaf ya d’auki son duniya ya d’aura masa bama shi kad’ai ba duk wani masoyinsa nason yusuf, kuma aka d’aura masa sarkan magajin masarauta, saida hajara ta haifi yusuf daga shi bata kara haihuwa ba.

    Yar kaninta hauwa ta d’auko tana riko mai suna zahra, lokacin yusuf nada shekara goma sha biyar, sosai zarah keson yusuf ganin saukin kansa babu izzah koh nuna isa mutum ne na mutane, bai d’auki son mulki ya sakawa ransa ba wannan yasa zahra keson maganar sa.

    A lokacin da yusuf ya cika shekara 20 yayi haddan Alkur’ani mai girma da haddisai, yana cigaba da karatunsa na gaba da secondary, hauwa ta kwanta ciwo wanda kafun ta mutu saida ta nemi Alfarman mutallaf daya had’a aure tsakanin yar d’an uwanta zahra da yusuf, koh bayan ranta za’a tuna da ita a masarautan karfe, kuma zuriya vai kare tsakanin ta da mutallaf ba, babu wani shamaki mutallaf ya Amince mata.

    Bayan mutuwar hauwa mutallaf ya tada maganar auren yusuf da zahra, daman zahra nason yusuf wanda kowa ya sani sai dai shi yusuf inne bayayinta a lokacin, yaso gardama da nuna shifa Aure ba yanzun ba sai ya girma, Amma mahaifinsa ya murza ido akan lalle lalle auren Addanayen sa da za’ayi guda biyu Kafshatu da maisara tare za’a had’a da nasa, yusuf yayi iyya yinsa akan bayason zahra, abasa dama ya nemo wance zai aura Amma ina mutallaf yace bazai Aminta ba.

    Rana bata karya Saidai uwar deya taji kunya, a ranan da aka zartar amatsayin ranan d’auren auren yusuf da yan uwansa ya cika, Amma abin takaici an waye gari babu yusuf a gidan Sarauta.

    Sarki ya shiga tashin hankali Amma daga baya saiyayi zuciya akan duk inda yusuf yaje wata rana zai juyo gida, in ma bai dawo ba yama kansa, haka aka d’aura auren zahra da wani d’an uwanta.

    Tunda sarki ya rasa yusuf ya shiga wani irin matsanancin damuwa, ganin an share shekara goma babu yusuf babu a lamansa a lokacin hajara ta sake haihuwar na miji zulkiflu, sosai sarki yayi murna ya samu wani d’a na miji, sai dai ganin girma ya fara kamasa gashi shekaru naja yana sonyin murabas Amma babu magajiiiii.

    Shekaru sunja Amma shuru babu yusuf babu labarin sa, har hajara ta sake haihuwar wani d’a na mijin (Ramadan)dayake daman ita akwai kuruciya a tare da ita, Yusuf kam bai dawo ba shekaru sai tafiya suke har mahaifin sa ya kwanta ciwon ajali mai tsanani, a lokacin zulkiflu ya girma yakai saurayi, ga yan uwansa mata duk sunyi aure su hudu gashi mazajen su manya ne a kasa wasu kuma sarakuna.

    Hade Hannu sukayi aka bazama neman yusuf kasa da kasa Amma ina ba’aga yusuf ba gashi jikin mutallaf sai kara tsanani yake, baida magana saina d’ansa yusuf yana son ganin d’ansa kafun numfashinsa na karshe.

    Rana tsaka saiga shi an gano yusuf yana NIGERIA Kuma a ranan aka samu labarin An kaisa prison, bai kwana ba aka cirosa washe gari sai gasu a NIGER Har gaban mahafinsa dake kwance aka dukar dashi.

    Ganin halinda yusuf yaga mahaifinsa a take kuka ya kamasa tare da neman yafiyar mahaifinsa, sai a lokacin nadama tazo masa ganin yanda uban ya tsufa matuka, shekaru sunja, da ba’a d’aukosa ba da shikenan daker ya sake ganinsa sai wani ikon Allah.

    Mutallaf dake kwance cikin ciwo yace bazai taba yafe masa ba har sai ya masa Alkawari?

    Ba musu Yusuf yace ya Amince a take mutallaf yace koh bayan ransa bai yarda ya sake taka nigeria ba, koma menene zai kaisa baiyarda ba sannan ya masa Alkawarin zai auri lawiza(kanwar zahra) don cikawa hauwa burinta na had’a jini da zuriyar su.

    A take yusuf yasa kuka yana sanar da mahaifinsa cewa yana da mata da yara a nageria, a basa dama ya d’auko su kuma ya Amince da auren lawiza.

    Kin Yarda mutallaf yayi ganin haka yasa yusuf D’aukar wannan Alkawari, shi kuma mutallf ya yafe masa duniya da lahira tare da sakamasa Albarka, anyi haka washe gari aka d’aura auren yusuf da lawiza sati mai zuwa aka nad’a yusuf a matsayin sarkin masarautar karfe, a wannan rana mutallaf yabar duniya.

    Tunda yusuf ya zama sarki shikenan Rayuwar sa ta sauya bashida aiki sai tunani gabaki d’aya ya kwallafa ransa akan nigeria, yaso tura mutane aje a duba rayuwar da iyalansa keyi Amma hajara ta gargadesa akan rashin biyayya ga mahaifinsa da karya Alkawari, sannan tace bata son kowa yasan da maganar.

    Yusuf rayuwa suke da matar sa lawiza za’ace sai a hankali, batasan wan abu wai dadin aure ba, asalima yusuf ya samu ciwon zuciya wanda kullum gaba gaba yake duk wani abinda za’ayi don ganin yusuf ya dawo da walwalarsa anyi Amma abin yaci tura.

    Hatta yan uwansa da dangi ya shanja musu ba kamar yusuf da aka sani daba.

    Bayan wasu shekaru lawiza ta haifi yara biyu mata muwaddat da muhibbat, sai nabila yar kafshatu ce wance hajara ke riko a gidan sarauta.

    An dawo labari……….
    Tabbas yusuf nada yara ni shaidace mahmah tace tana hawaye.

    Jama’a da dama dake fadan sunsha mamakin abinda ya faru wai yusuf nada iyali, Amma ba’a sanar da kowa ba acikin zuriyar su, sannan wasu suna ganin rashin kyautawar abinda aka ma yusuf, lawiza kam kuka ta sake yanzun daman yusuf nada wasu yaran kamar muhammad, amma tana matsayin matarsa a kasa sanar da ita, mikewa tayi zata bar falon, alamu yusuf ya mata data koma ta zauna, ba musu ta koma ta zauna.

    Al’ameen ne ya dubi mahmah yanzun kina nufin kice mini kece mahaifiyar abbajo?

    Kwarai nice hajara kakar ka uwar yusuf…

    Yanzun kun kyauta kenan abinda kuka ma mahaifina ace mutum an yanke masa alaka da yaransa duk wani hakkin su daya rataya a wuyansa ? kai koh ashariya wannan ba daidai bane, mijinki bai kyauta wa mahaifina ba.

    Ya kyauta masa muhammad, nine ban kyauta ma mahaifinka ba, a Ranar da aka nad’a yusuf kafun mutallaf ya bar duniya munyi wani magana dashi akan yusuf……………

    ✨Ruqeenjalal✨

    🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
    🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯
    ~ Na ~

    🍃 *Rukayya* *Ibrahim* 🍃

    Page9⃣2⃣&9⃣3⃣

  • Matar Makaho 98-99

    Matar Makaho 98-99

    Page 9⃣8⃣&9⃣9⃣
    Zata fadi da sauri Ammar ya tarota cikin tashin hanki Ramadan ya bude firij inda ya gani a falon ya ibo ruwa watsa mata sukayi ta farfado cikin kidima take magana ina yake na tabbata d’an yusuf ne, don Allah ku taimaka ku kaini wajen sa na nemi yafiyarsa na tabbata muhammad ne, don salim baya kama da yusuf.

    Da mamaki suka juya baya don yima Muhammad magana, sai kawai sukaga wayam babu shi ga kuma mamakin ina matan nan ta sansu.

    Kuka take tana rokonsu su taimaka su kaita wajen muhammad, kwantar mata da hankali sukayi akan tayi hakuri ya koma inda suka sauka ne, kuma tare da yusuf suka zo, ai tana jin haka ta mike da sauri ta tsaya takalmi ta saka ta nufi kofar gida.

    Ganin haka yasa su Ammar binta suna tambayarta ina zata?

    Amsa ta basu akan gidan sarki zata wajen dasu yusuf suka sauka, jin haka yasa su binta a baya suna had’ata da Allah ta tsaya yanzun dai yana hutawa, amma ina bude get tayi zata fita daidai lokacin Alhaji suka dawo tsayawa yayi da motar sa yana tambyar zainab in zata? da mamaki don sam inba dalili mai karfi ba zainab sai tafi wata uku bata leka kofar gida ba.

    Tambayarta yayi ina zata Amma ina ta kasa basa Amsa shuru tayi ta tsunkuyar da kai, Ammar dake gefenta shiyake sanar da uncle insa ga inda zata, sata yayi ta koma amma kememmen Zainab taki komawa sai hawaye dayake bin fuskar ta, daka mata tsawa Alhaji yayi akan ta wuce ta koma ba musu ta juya tana kuka ta koma cikin gida, Ammar kam dariya abin ya basa watoh duk girman mace in batayi aure ba saikaga wani yaranta a tare da ita yanzun kamar Aunty zee ke kuka don ance bazata wani wajen ba.

    Komawa ciki sukayi dukansu harda uncle in Ammar da mom, shiga falon sukayi duka suka tsinci zainab na kuka a zaune zama sukayi baban ya fara rarrashinta don abin na zainab tsawa baya gyarasa.

    Tambayar Ammar yayi cikekken bayani, Ba musu Ammar ya zayyana masa kome dayafaru da labarin su yusuf kuka zainab tasa tana sambatu akan kome ya faru dasu yusuf itace ummulkaba’isin kome daya same su.

    Ajesu Alhaji yayi akan su zauna gobe daga shi harsu in saisu tafi wajen yusuf in tare.

    Aiko washe gari da sassafe suka wuce gidan sarki Amma basuyi sa’a ba duk basanan sunje gidan su hafsa, waya Ramadan ya d’auka ya kira zulkifilu akan ya tambaya musu sunan unguwan da suke.

    Bayan sun isa gidan da sallama suka shiga falon bayan an musu ido, zainab sai boye fuska take ganin sun had’a ido da yusuf dake mamakin ganinta da ubangari.

    Zama ubangari yayi suka gaggaisa da juna anan ne ubangari ke neman yafiyar yusuf tare da rokonsa daya yafe ma zainab, duniya ta koya mata Hankali, duk da sun dawo Maiduguri Amma har yanzun batayi aure ba, kowa yazo wajenta sai tace bata so gashi yau tana da shekara 44 harta fara tsufa Amma shuru kullum cikin istigifari dake da nadamar abinda ta Aikata, ga mutuwar khairat daya shiga jikinta sosai don Allah yusuf da muhammad su yafe musu.

    Daker aka samu muhammad ya yafe don yusuf kam a take ya yafe mata tare da neman izinin Aurenta, don zainab ta basa tausayi matuka tsawon shekara 44 ace batayi aure ba, yasan sonsa ke wahalar da ita duk da tsufa yaxo, Amma xuciyarta bai tsufa ba, ba musu Aka daidaita kome baban hafsa ma ya yafe ma abie, abin gwanin sha’awa su muhammad basu bar maiduguri ba saida aka saka sartin auren yusuf aka biya sadaki, Amma auren sai yusuf yaje nijar zasu dawo d’auren aure, duk wanda yaga fuskar zainab a lokacin zaisan lallai so ba karya bane don ta kasa boye farin cikinta.

    Daga maiduguri Hafsa da kalamu dasu falmata suka wuce Abuja,saboda karatunsu, muhammad da Sumayya suka wuce Taraba harda mahmah dasu dahdah, yusuf dasu ramadan sun wuce nijar daga Maiduguri.

    Bayan komawar sumayya dasu Abie jalingo sukaci gaba da kula da jariransu yayinda muhammad ya kai khadija wajen hafsa tacigaba da zuwa makaranta daidai su tashi tafiya nijar in sumayya ta gama jego.

    Kudi yusuf y sakarwa Al’ameeen a account ba kad’an ba, kamar yau suna zaune a falo su uku dashi da sumayya sai mahmah dake bawa na’ima madara gaggo na sallah a d’aki, hira suke anan ne muhammad ya kalli sumayya, ina so ki bani shawara matata cikin fulatanci yayi maganar sanin mahmah bataji.

    Murmushi sumayya tayi tana kallon mijinta sai kuma ta basa amsa da hausa gudun kar su ware mahmah, “ina jinka dear”
    Jin haka yasa mahmah mikewa ta basu waje.
    Yauwa don Allah ki tayani nazari in sama wa yan uwana mafita don nayi nazari Abinda ke damun Adara abu biyu ne, akwai jalinci akwai bin jini na gado, akan halinsu shiyasa nake son na shawo kan lamarin nan kuma na rasa mafita ta ina zan fara?

    “Gaskiya naji dadi daka ji a ranka Adara yan uwanka ne, baka kullace su a rai ba akan abinda suka maka ba, har kana nema musu tsira”?

    Taya zan gujesu sumayya bayan dangin mahaifiyata ne, da kinsu ake da Abbajo bai yarda ya auri mami ba.

    “Gaskiya ne ni a nawa shawaran abu na farko da zaka fara shine ka tarasu, kayi musu magana akan duk wanda yake da wance yake so koh wance take da saurayi tsayaye zaka aurar dasu, babu koh sisin iyayen su sannan ka gyara musu gidan tunda akwai fili saika ma samarukan d’akuna room and falo, suyi aure a ciki ka nema musu jari matan kuma asasu a islamiyya yara a had’a musu da boko, su kuma su inna ka basu jarin 50k ga kowance su kama san’a, sai maganar shagari kaje ka sanar dashi akan ka basa shagon halak malak kaga zaifi samun natsuwa akan ya zauna da tantama tunda Ammar yace ya baka kyautane”

    Gaskiya sumayya ngode matar Aljana Allah ya barmin ke baby, amma ya zanyi dasu bappa sulaiman?

    “Ameeen dear, ni a ganina kamar daman ai suna da sana’arsu kadai taimaka wa mata da yara matasan zaifi in yaso daga baya saika basu abinda kaga ya dace”

    Haka koh akayi washe gari muhammad yaje gidan adara kuma ya sanar da shagari ya barmasa shagon kyauta, yaron har kuka yayi gwanin tausayi, sannan yanzun yasan khadija tafi karfinsa shiyasa ya fara kula wata yarinyar school nasu dake matsa masa.

    Takardun makarantan sa muhammad kawai ya d’auka a dakinsu, sauran kayan d’akin ya baiwa matan gidan Adara kyauta harda na kitchen.

    Kafun wata d’aya duk samarin gidan adara da suka kai aure duk sun fitar da mata, haka ma matan don daman suna son auren, rashin kudine kawai, mazan ma wa’inda basu da budurwa jin auren bati da za’a musu yasa su neman yan mata cikin lokaci kankani, gashi ansa yara a boko ansa mata a islamiyya harda mazan ma.

    Anyi bikin gidan Adara na gani na fad’a wanda ya samu hallartar jama’a da yawa kowa na tofa Albarkacin bakinsa, akan muhammad da Halakcin daya musu.

    Sumayya ta kammala wankan jegon ta sati d’aya kenan, yau tun safe daga ita har muhammad in suna cikin farin ciki,adalilin khadija da kalamu da zasu zo yau don anyi hutun makaranta Khadija an kammala ss 1 zasu tafi 2, gashi yau daga ita har kalamu zasu zo Taraba tun asuba suke sanar dasu akan zasu bi fly, wanka sumayya tayi goggo tama yaranta wanka suka shirya cikin shiga ta Alfarma harda muhammad zasu je gaida maman Ammar, daga nan zasu bi Airport d’auko su Kalamu 4:00 na yamma.

    Dayake yanzun muhammad ya iyya tuki shiya d’aukesu a motar zuwa Gidan su Ammar, suna fita a motar dayake zuwan bazata sukayi basu sanar da Ammar zasuzo ba, tsayawa muhammad yayi a tsakar gidan yayinda sumayya ta wuce ciki rike da na’ima ta bar masa na’ifa da sallama ta shigo falon Amma babu kowa shuru kakeji,zama tayi koh masu gidan zasu fitoh Amma har minutes biyu bataga kowa ba, gashi Al’ameen sai kiranta yake akan yajita shuru saboda shi baya shiga gidan mutane ba tare da neman izini ba.

    Mikewa tayi ta nufi wani kofar dake gefen falon don a tunaninta koh dakin su maimuna ne a falon harta kama handle in kofar zata bude sai kuma ta dakata jin maganar dake tashi a d’akin.
    Muryar hajiyar Ammar ke magana, yanzun Ammar kanada wance ta fini ne ka zauna kana cutar da kanka ni bangane kanka ba gabaki d’aya ka chanja yau ciwo gobe lafiya?

    Ammar ne ya bata Amsa, Mom babu fa abinda ke damuwa kawai dai banajin dadi ne.

    Wani irin bakajin dadi, abinda ke damunka harda tunani da damuwa ba haka kake ba Ammar nice fa na haifeka?

    Mom daman wallahi na jima ina son khadija sai kuma yayi shuru bai karasa ba

    Wace khadijar?

    Kanwar Al’ameen

    Toh sai akayi yaya cewa tayi bata sonka?

    Ah ah mama ban fad’a mata ba,daman naso na sanar da sumayya maganar sai kuma bakina yayi nauyi kar tace daman da wani manufa nake taimakon su, gashi banason yarinyar ta rainani.

    Gyara zama mom tayi yana kara kallon Ammar tun ba yauba tasam d’an nata akwai son girma.

    Toh shine ita da Auntin nata suka gudu Abuja ba tare da na zayyana mata abinda ke raina ba, kuma yanzun kawai saina ganta da yaron nan kalamu kanin sumayya, kinga yanzun ai babu halin nace mata ina sonta tunda yanzun soyayya suke koma na fahimci tana son yaron.

    Ammar ka bani mamaki wallahi ita tace maka soyayya suke?

    Hamma mom kowa yagansu yasan masoya ne kuma nasan koh da ba sonsa khadija take ba Albarkacin sumayya zata yarda ta aure kalamun bare ma tana sonsa.

    Kaga Ammar kafito ka sanar da yarinyar nan kana sonta bakasan me Allah zaiyi a lamarin nan naku ba, ka kwantar da Hankalinka kaji inso samune ma ka shirya kaje abujan?

    Mom muhammad ya sanar dani khadija na zuwa.

    Toh maza ka tashi ka shirya samun ta ganka tsaf dakai kabi yayanta Airport gobe kuma sai kaje gidan su ku gaisa kaga saika sanar da ita Amma ka dubi yanda duk kabi ka rame……..

    Jin abinda suke cewa yasa sumayya sauri tabar bakin kofar, jin alamun mom zata iyya fitowa da sauri ta bude kofar falo ta fita waje, muhammad dake tsaye a rumfa har yanzun rike da babyn sa, dan yanzun sunyi wayo sosai,ya tambaye ta Lafiya tun d’azun Ammar bai fito ba?

    “Muje kawai ba kowa a gidan”

    Da gaske?

    “Don Allah ka shiga mu tafi gidan mu pls nace maka basa nan”

    Ba musu muhammamd ya shiga motar yaja suka wuce gidan su sumayya.

    Yad’an jima a gidan kafun kiran Ammar ya shigo wayarsa, sallama yama su dada ya wuce, bayan fitar Muhamamd ne dada ke sanar da sumayya akan ta kara ma abie magana akan Amina(goggo)ya aureta don ita hankalin matar ya burge ta, Amma duk yanda dada tayi akan ya yarda Ya nemi Amina tunda dai bata tsufa ba, da yarantanta Amma yaki Amince wa.

    Sumayya karan kanta taji dadin Abin don babu shakka goggo macece ta gari duba da zaman da suke da ita yanzun a gida d’aya sam bata da dumuwa.

    Sumayya ta samu Abie akan maganar daker saida takai ruwa rana kafun ya Amince da zancen, A ranan dada ta sasa dole sai ya wuce gidan su Al’ameen sun daidaita da goggo tunda yanzun yaran basa gida sai mahmah ne kawai.

    Muhammad da Ammar su sukaje suka d’auko su khadija a Airport gidan su Abie suka sauka daman sumayya na gidan sosai suka musu tarba ta musamman, Sannan a nan suke xancen Abie ya tafi zance gun goggo, aiko muhamamd yaji dadi don daman tunanin da yake kenan in ya tafi karatu abroad kamar yanda uncle zulkiflu yace masa next month zasu tafi America an sama masa gurbin karatu harda sumayya da yaransu don gida yusuf ya kama musu ashan haya, yanzun ma bikin Abbajo suke jira.

    Lokacin da abie ya dawo sosai yayi farin cikin isowar d’an nasa hira ne ya kara barkewa a tsakaninsu sai dare su sumayya suka tashi tafiya, kiran kalamu tayi da Khadija a compound ta tambayesu shin soyayya suke kuma su fad’a mata tsakanin su da Allah?

    Dariya suka sake a tare sannan khadija tace wa sumayya ai tsakaninta da kalamu babu zancen soyayya asali ma Abota ce kawai da shakuwa don kalamu kamma yana da budurwa yar school nasu sunsha gaisawa da khadija a wayar Kalamu.

    Hakan sosai yama sumayya dadi sallama sukayi da yan uwanta.

    Sun isa gida muhammad kam kwanciya yayi ya barsu da khadija anan sumayya ke sanar da ita Zancen sonda Ammar ke mata, da kuma bata shawarwari da tuna mata irin Alkharin Ammar a karesu ya cancanci ta sosa koh Albarkacin Halakcin sa, saida ta tabbatar jikin khadija ya mutu murus kafun ta mata sallama ta wuce d’akin mijinta khadija kam tare da mahmah zasu kwanta.

    Washe gari da safe bayan sun karya Al’ameen ke tambayar ta dalilin sasa su bar gidan su Ammar bayan kuma Ammar yace masa suna nan,sumayya ke sanar da muhammad zancen Ammar da abinda ta jiyo suna tattaunawa sosai muhammad yayi murna ba d’an kadan ba, haka mahmah khadija kam kunyane kamar zai kasheta, especially jin muhamamd ya shirya ya fita wai kar Ammar yazo ya samesa a gidan tunda wajen khadija zaizo.

    Sumayya da khadija kitchen suka shiga bayan matsawa khadija datayi kafun ta yarda, suna aikin girki yayinda mahmah da goggo ke falo suna rirrike da yaran sumayya.

    Wayar mahmah ne yayi kara a d’aki mikewa tayi da na’ima a hannunta ta shiga dakin ta d’auko wayar, ganin nabila ne yasata d’auka da sauri.

    Ta bangaren nabila jin mahmah ta dauka jiki a sanyaye tace hello

    Kedai nabila anyi yar banza, sallamar ma bazakiyi ba sai wani d’an banzan hello wai gaki baturiya koh?

    Yi hakuri mahmah Assalamu alaikum

    Amsawa mahmah tayi tana tambayar nabila lafiya?jin muryarta cike da damuwa

    Dada kewarku nake yaushe akki (muhammada)zai dawo?

    Toh watoh shi kike kewa kenan banda ni?

    Yi hakuri harda kene mahmah

    Toh make damunki nabila in baki fad’amin ba wa zaki fadawa?

    Mahmah wallahi nifa son Akki nake don Allah kisa baki a maganar nan ki sanar da abba kice ke kikeso a had’amu ki taimaka mini mahmah………

    ✨Ruqeenjalal✨🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
    🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯
    ~ Na ~

    🍃 *Rukayya* *Ibrahim* 🍃

    ✨Tsokaci A ranan 30/8/2021 na fara rubuta Wannan novel na matar makaho, gashi A yau 28/10/2021 na kammala cikin Yardan Allah kuskuren danayi a ciki Ubangaji ka yafe mini🤲🤲🤲🤲🤲🤲🤲🤲🤲🤲🤲

    Free book🤧

  • Matar Makaho 72-73

    Matar Makaho 72-73

    Page7⃣2⃣&7⃣3⃣
    Fita yayi a d’akin da gudu yayi waje, jikinsa rawa ya soma ganin An cinnawa gidan bappa wuta, ga sauran gidaje duk wuta ke tashi da karan mutane da guje guje.

    Gidado ne ya fitoh d’aki rike da matar sa, da tashin hankali yasa ta nakuda, ya kalli bappa dake xaune shuru, babu alamun tashin hankali a fuskar sa hakama babu alamun kwanciyar hankali.

    Inna ce ta mike da sauri ta isa garesa, hannun lantana ta kama wance ke kokarin faduwa,gaskiya haihuwace gadan gadan fa bappan gidado musan abinyi.

    Hanyar wajen gidado ya nufa hannunsa d’auke da wuka sharbebiya.

    Kai gidado ina zaka?koh bakajin abinda ke gudana a waje ne?muhammad yace cikin tsananin tashin hankali.

    Kaga ku zauna a ciki bara na fita, mu munfi karfin ana kashemu, muna buya sai dai a fito a gwabza, yana magana yana kokarin barin gidan.

    Kaiiii gidado, fitar da zakayi ba shine mafita ba, kanada tabbacin inka fita zaka dawo ka samemu a raye?wuta fa aka kunna wa gidan nan, mafita zamu nemawa kan mu, na fita a garin gabaki d’aya.

    Allah ya sauwaka, mugudu mubar mahaifan mu, da Arzikin mu.

    Gidado kabi abinda yaron nan ya fad’a, don yafika gaskiya nakuda matar ka take, kamata yayi ka fitar da ita, ga indo can sumar ta biyu,inna tace tana nuna indo dake zaune a gefe kamar ruwa ya cita.

    Shuru gidado yayi ya tsaya sosai jikinsa ke rawa , kowa yasan yanda ran fulani yake baci in an tabo musu dukiya ba sauki, gaskiya inna saidai kuzo kutafi da ita kaima muhammad ka bisu, mukam zamu kare shanukan mu, yayi maganar yana tsinka zanar bayan gidansu wanda wuta bai iso gunba.

    Soyayyar da ka iyya jure shadi akanta, da soyayyar tsakanin uwa da d’a, bazaka iyya sadaukar da arzkinka ba, gidado ku rayu tare?

    Mikewa inne tayi, gidado ya ciccibi matarsa da tiyo ya fashe ruwa yana zuba, da gudu indo ta rike hannun inna, muhammad ma binsu yayi a baya, har sun shiga bandaki kafun suka tuna da bappa yana bayansu, juyawa dukansu sukayi suna kallon sa har lokacin bai motsa ba.

    Inna ce ta dubesa, Bappan gidado yakana zaune kazo mu tafi baka ga halin da yarinyar nan take ciki bane?

    Kuje kawai Allah ya tsare hanya, ni bazan iyya gudu a rugan mu ba.

    Habba bappa yanzun kafison ka zauna azo a kashe ka, hakan bai dace ba koh a addinan ce, kana da damar kare kanka, ka bari a kashika, muhammad ya karasa maganar yana karasowa kusa da bappa.

    Don Allah bappa y’an dillo, indo tace tana kuka.

    Girgiza kai bappa yayi, kuyi hakuri bazan iyya zuwa ba.

    Muhammad ne ya dube gidado, kaga gidado ku tafi da inna, lantana da indo , ka fara fitar dasu, muna zuwa da bappa.

    Sanin taurin kai da kafiya irin na bappa, yasa gidado da inna suka fita ta zanan bayan gida, harda lantana data gama galabaita da indo.

    Zama muhammad yayi kusa da bappa sosai zuciyar sa ta tsinke, ganin yanda wuta yaci rabin gidan yanzun ma wani irin turiri da rad’adi yakeji a jikinsa ga hayaki, bappa don Allah badon niba kazo mu tafi a rugan nan, rayuwar ka tana da matukar Amfani wa Ahlinka, kasan wani irin hali zasu shiga in aka waye gari baka?akan iyya rasa dukiya, wata rana su dawo, Amma ba’a taba rasa uba wani ya maye gurbinsa har Abada, kama iyalinka adalci ka rayu dasu koh ba kome zasu walwala koh ba shanukai, akansu rayu bakai ba dukiya.

    Kuka bappa ya fashe dashi, babana bazaka gane bane yanda abin yake, akwai zafi azo a same ka har gidan ka a kwace maka dukiya, a kwace maka muhammali, asaka gudu kamar barawo ina sukeso muje, irin wa’innan mutane, sune sukayi sanadin iyaye na, shekara talatin baya, mu kullun cikin zulumi muke bamuda sakat?

    Kayi hakuri bappa, rayuwa tafi kome muhimmanci ita d’ayace, kayi hakuri mu fita anan, yana maganar yana kama hannun bappa ganin jikinsa yayi sanyi, kamasa yayi suka nufi bayan gidan, suka fita ta zanan gidan.

    Da ido bappa yake bin rugansu dashi, ganin gawawwakin fulani cikin jini manya da yara, kota ina hayaki ne.

    Tafiya suke kamar wasu barayi a hankali a hankali, suna bin ciyaye kamar a mafarki muhammad yaga yan ta’adan nan sanye da kakin sojoji ga bindigogi manya manya a hannunsu, kafun ma su buya tuni sun gansu, ai da gudu muhammad ya kama hannun bappa suka nausa daji, da gudun tsiya, suma suka rufa musu baya.

    Gudu muhammad yake da bappa suma suna binsu a baya, bappa ne yayi tuntube ya fadi tim, da sauri muhammad ya dakata kokarin tayar da bappa yake, Amma bappa ya kasa saboda ya buga kafarsa mai ciwo a dutse, ka tafi kawai yaron nan ni inaji lokacina yayi, Allah yamaka Albarka ya sadaka da ahlinka lafiya, sai wata rana.bappa yace.

    A karon farko muhammad ya sake kuka mai karfi, harga Allah a d’an zamansu da bappa jinsa yake kamar mahaifinsa, don Allah bappa karkace haka, bara na d’agaka, ciccibar bappa yayi, yana gudu kamar kiftawar walkiya yajisa a kasa dagashi har bappa, mummunan buguwa sukayi muhammad saida tsakiyar giransa ya tsage, saiga jini bappa ma gwuwarsa ta kwarzane sosai.

    Kafun ma ya mike tuni yan ta’adan nan sun kewaye su, d’aya daga cikin sune ya taka kafar muhammad saida yaci ta baki, jini ya balle masa, bindiga d’ayan yasa ya buga a kan bappa, kara bappa ya sake yana dukawa hade da rike kansa da karfi yana salati, jin wani irin azaba mai tarin yawa na bazata.

    Don Allah kuyi hakuri, karku cutar dashi don Allah, muhammad yana magana yana kuka.

    Kai ragon maza kaika san Allah ne?wani a cikinsu yace.

    Kuyi hakuri…

    Bamuda imani bare hakuri.

    Bappa dake duke har lokacin jikinsa sai rawa yake tsabar azaba, kamasa d’ayan yayi ya kwantar kaman rago yasa masa wuka a wuya.

    Ai muhammad na ganin haka yayi wani irin mikewa da karfi, ya bangaje mutumin da ya takasa, duk wani tsoro ya fitar masa a rai ganin tabbas abu biyune zai faru rayuwa koh mutuwa, rugawa yayi da gudu ya nufi bappa, kafun ma ya iso garesa tuni mutumin ya dirza wukar jini ya fantsama.

    Zuciyar muhammad ta riga ta kikashe yanzun, yaga mutuwar mahaifiyarsa, kaninsa, amma bai taba ganin mutuwar da ta mugu-mugun ratsasa ba irin wannan, sharbeben Adda dake rataye a jikin d’aya daga cikin yan Ta’adan ya zare da karfe, kafun giftawa da bismillah tuni muhammad ya shiga fad’a da mutanen nan, cikin bazata da rashin tsammani,Allah kad’ai yake kira, yakini kawai yasa a ransa koh yakashe koh a kashesa, suna da bindiga shikam wukane kawai, sosai suke..zuba alburusai yana kaucewa, cikin rashin sa’a wani yasake bullet, ya kuskure sa a hannun hagunsa, ihu yasa da karfi yayi kan mutumin, wukar hannunsa yasa ya fille masa kai,sosai jikin muhammad yake bari ganin yau da kansa ya kashe mutum shi muhammad, mutum hudu ya kwantar, daman su hudun suka bisu.

    Mikewa yayi ya sabe gawan bappa, sai kuma ya rasa ina zai nufa dashi, tunda fa ya fitoh baiga su inna ba, wani shawara ne ya fado masa, aje bappa yayi ya sabi bindiga da wuka ya koma cikin rugan su gidado.

    Tun daga nesa ya hango fulani da aka tara waje d’aya, cikinsu harda su gidado da wasu kattai suka danne sa, sai lantana dake kwance bata motse, sai jinjira a gefe tana cillara kara cikin jini koh cibi ba’a yanke mata ba, Alamu dai daga haihuwarta ta riski wannan masifa.

    Bin jikin ciyayi muhammad yayi ya saita mutanen da suka danne gidado, su biyar gabaki d’aya ya sakar musu bullet one by one, ai take yan ta’adan nan suka fusata suna sake ruwan harsashi ta saitin muhammad, da sauri ya kwanta a kasa.

    Wanna daman gidado ya samu da wasu matasan fulani suka d’auke wukake da adda aka fara aran gama.

    Inna dake gefe da sauri ta rarrafa zuwa wajen jaririyar, wuka ta karba a hannun wani ta yanke mata cibi, nadeta tayi a d’an kwallinta ta kama hannun indo, tare da wasu matan suka ruga a guje, sukayi daji kowa yayi takai takai, aka bar gawan lantana a wajen, don ta rai ake.

    Muhammad yau an zama zaratan maza sosai ake gomxa fad’a, duk wani tsoro nasa yau ya kau, yakini d’aya a ransa zaiyi rai koh ah ah, ganin yanda wasu dakarun barayin nan suka fara shigowa rugan, suna karuwa har sun fara ninkesu, gashi mata da yara da suka rage a raye sun dade da gudu, yasa muhammad d’aga murya da karfi, kowa yayi ta kansa karuwa suke aje-aje zasufi karfin mu.

    Ai yana maganar nan da gudu ya kama hannun gidado da wani saurayi zaiyi sa’an sa suka nausa daji da gudu, haka ma sauran mazan ana harbinsu suna gudu wasu na faduwa matantu, barayin suka mara musu baya, yayinda su kuma suka raba kawunan su, kashi-kashi.

    Muhammad gudu suke a daji koh gabansu basa gani, gudune irin na bakin Rai bakin fama, nausawa daji suke yan ta’andan nan na binsu, a hakan suka ringa gudu, (wani abu sai tashin Hankali kayi abinda koh da kudi aka had’aka bazaka iyya ba, sai kaga masifa)sosai sukayi nisan kiwo, gudu suke mutanen na binsu suna sake bullet, Allah ya tsare su, har suka isa wani baban ruwa fad’awa sukayi ciki, yaufa muhammad da kansa ya tsallake ruwa, suna tsallaka kogin har lokacin mutanen na binsu, sosai suka kara azama basu jima da gudu bayan tsallake kogi na biyu, suka hango wani kauyen, ganin Hakan ne yasa mutanen juyawa suka barsu.

    Faduwa muhammad yayi dasu gidado a kasa, ganin sun shigo cikin mutane, A raye basu mutu ba, karasawa sukayi cikin gari.

    Sun ma rasa ta ina zasu fara, fahimtar da sukayi garin kamar babu alamun musulunci, ganin yanda mutanen garin suke, buya Al’ameen sukayi basu bari hankalin yan kauyen ya dawo kansu ba, a hankali suke bin cikin gonaki har suka tsallake kauyen lokacin dare yayi sosai, don akiyasce zaikai 10:00 na dare, gindin wata bishiya suka samu suka zauna, kowa na maida numfashi koh bacci basuji yau, muhammad kam jingina yayi da jikin bishiyar ya lumshe idanunsa yana tunanin rayuwa, tunda ya tashi yake ganin jarabawa iri iri, Amma baitaba zata zaiga irin nayau ba, ace tun 2 na dare yana cikin tashin hankali har dare war haka, ada yayi tunanin zuwan sumayya da farin cikin da ya samu, baitaba tunanin akwai sauran wani damuwa ba, ya zauna da sumayya da zuciya d’aya, duk da an sanar dashi ita ba mutuniyar arziki bace, auren jingina za’a basa, hakan yaji A Ransa zai iyya zama da ita cikin aminci, baitaba sawa ransa, don sumayya tayi ciki zai gujeta ba.

    A Ranar daya samu tabbacin farin cikin sa, sumayyar sa budurwa ce, yaji dukkan wani damuwa kunci ya yaye, a lokacin rayuwa yake tuna musu mai dadi nan gaba,don ya tabbatar auren sa da sumayya akwai dalili, bai d’auka zaiga irin masifar yau ba, shine yayi kisa?kisan ma mutum d’aya ba, ba biyu ba, atake yaji aransa tabbas yanason zama SOJA don ya bawa kasarsa gudumawa, da maganin ire iren mutanen nan, indai da rai da lafiya koh kurtune inya koma gida zai nema, tunda ba ilimi mai zurfine dashi ba, insha Allah sumayyar sa sai tabar Amsa sunan MATAR MAKAHO zuwa MATAR SOJA……..

     

    *******************
    Bazaki cigaba da zama da miskini ba yanzun sumayya, mahaifin kima yace gobe in Allah ya kaimu zaku wuce garin su mahaifiyar ki.

    “Kin gama, koh baki gama ba”?

    Na gama sumayya.

    “Toh bara kiji, ni a haka naga mijina kuma nake son zama dashi a miskinin, banga wanda ya’inda suka isa su rabani dashi ba, wallahi sai mutuwa karyar mutum”

    Sumayya Rashin kunyar da kika koya harya kai haka, bansani ba shige toh muje, su Abie na waje saikije ki kare musu tanadi bamu ba, aikoh me muka miki bamu shanshanci wannan iskancin ba.

    “Inje ina? mijina bayanan kuma baibani izinin fita waje inga kowa ba” sumayya tayi maganar tana tura kosanta a baki bibbiyu ma, take turawa irin na huce haushin nan.

    Innalilahi wa’inna’ilaihi raji’un na shiga uku ni sumayya,na lalace da’aka had’a baki dani aka aurar wa yan iskan Adarawan nan, yarinyar yarona ni sumayya na bonu, wi.. wi. wi dada ke kuka tana maganar nan gwanin tausayi

    Mimi ce ta mike tayi waje, wajen su Abie dake zaune a cikin manyan mototi a waje na Alfarma, gabaki daya yan unguwan sun maida hankalinsu kan mototin, atunanin su koh wani masifar yan gidan suka jajibo.

    Miemie na isa kuka ta fashe dashe a bakin motar da abie ke ciki.

    Da sauri dukansu suka fitoh a motar , magidanta ne sun d’an manyanta, su biyar harda abie sai samari hudu da masu aure biyu, abie da sauri ya fara tambayar mimi abinda yake faruwa, ina sumayyar?gabaki d’aya inka gansa sai ya baka tausayi.

    Tas mimi ta zayyana musu kwandon masifar da sumayya ta juye musu, kuma tace bazata fitoh ba mijinta bainan.

    Ita sumayyar ce ta fad’a miki haka?babuji yace yana rike baki.

    Eh babuji….

    Ke kije cikin gidan kice ana sallama damai gidan, babuji yace wa mimi.

    Juyawa tayi ta shiga gidan, daidai lokacin Ammar ma yayi packing in motarsa, suka fitoh shida khadija a ciki, rage mata hanya yayi a bakin kasuwa.

    Karasowa yayi da sauri kusa da dasu, cikin sallama ganin su mutane ne ba raini, gaisawa sukayi, khadija ma ta gaidasu, tana mamakin meya kawos, don bata mantasu ba, sune iyayen sumayya, cikin gida ta shiga ta barsu a waje harda Ammar.

    Bayan d’aya daga cikin mazajen gidan adara ya fitoh, gaisawa sukayi dasu babuji, sannan suka nemi izinin shiga cikin gidan zasuyi magana da yarsu in ba damuwa.

    da mamaki mijin inno ke kallon su izini shi ai harma ya manta ana neman izini, kafun a shiga gidan wasu, suda gidansu ina yaga izinin shiga, amma dai ya maze yace su shigo.

    Ammar fa zare ido yake, wai meke faruwa ne haka, yasa sa binsu a baya suka shiga ciki.

    Sumayya na tsaka da cimar ta, taga shigowar Familin su maza, kwarjinin da suka mata yasata mikewa tsaye, haka kawai taji gwuwarta yayi sanyi, had’a ido da tayi da abienta dake binta da kallo, baitaba tsammanin xaiganta haka ba, daren jiya koh bacci baiyi ba, yana zullumin halinda xaizo ya risketa yau.

    Sannu sumayya tunda baxaki fita ba, mu munshigo munsame ki, uncle gaddafi yace.

    Tsunkuyar da kai, kawai sumayya tayi batace kala ba.

    Shige mu tafi, in mijin naki ya dawo saiya zo muna da magana dashi, wannan auren bamu yarda dashi ba, daman kudi muka biya sulaiman akan auren.

    “Kamar ya uncle bangane baku yarda da auren ba? Kuma ba wanda ya baiwa muhammad kudi, asalima cemai akai ciki ne dani”

    Eh Momcy gida zamu koma gaskiya bazaki cigaba da xama a gidan nan ba,ai daman mu muka sakaki auren sa, yanzun kuma munce bazaki zauna dashi ba, uncle nata d’aya yace.

    Hajjo ce ta kalli sumayya, kuma kaf mu innan babu wanda ya miki kazafin zina in karya muke a kira sulaiman in, don mu sulaiman in ma bamu sansa ba jinsa kawai muke a waliyin mijin da muka baki.

    “Ai uncle bakin Alkalami ya bushe, a da kunada iko dani Amma banda yanzun, ban shirya xama karamar baxawara ba, ina son mijina.

    Sumayya!! abie ya kirata da dukkan yakininsa, yau koh momcy baice ba sunan Dadansa guda ya Ambata, sumayya yau nayi miki Alkawarin cika miki burinki, zan kaiki kiga mahaifiyarki kiga danginta, zan dawo miki da aikin ki, ki Amince mu koma gida tare.

    Kara khadija ta sake da karfi, hade da kuka wayyo na shiga uku don Allah kuyi hakuri, wallahi yayana na sonta babu abinda baya mata, kuma ba mutumin banza bane, don Allah karku rabasu da Aunty, wallahi nima ina son zama da ita.

    “Kiyi shuru khadija koda Al’ameen bazai dawo ba, ni bazan taba barin gidan nan ba, koda na bari toh ba gidan shugaba zan koma ba, ku fita ku barmin gida banason ganin ku, nace ku fita”tayi maganar cikin karfi sai kuma ta sulale ta zube a kasa sumemmeya.

    After 6 hour’s sumayya ce kwance a gado an d’aura mata ruwa a hannu, sai khadija dake gefen ta a zaune idanu jahur, sai Ammar dake gefe shima a zaune, cikin tashin hankali.

    A hankali sumayya takalli ammar ” sun tafi”?

    Ah ah sumayya basu tafi ba tunda aka kawoki suke zaune a asibitin nan, yanzun ma sunso shiga likitane ya hana, kamar yanda kikace saboda yanayin bp ki, sumayya duk da bansan meke faruwa ba, nasan tabbas iyayen kine su, kuma iyaye darajane dasu baikama ta ki musu abinda kikayin nan ba, sannan abinda ya tsayamin a wuya, abin mamaki daman ba auren soyayya kukayi da Al’ameen ba? Don nasan sone kawai zaisa ke dashi ku kasance a karkashin inuwa d’aya, duba da duniyar mu ayau mai kudi sai mai kudi miskini sai miskini, talaka sai talaka Amma ke kullun sai na kwana da lamarin ku keda muhammad A raina, a yanda na ganku naga tsantsan kula da juna da soyayya, gaki kyakkyawa ruwan manya, kullun saina tambaye kaina taya kika aure muhammad?Amma Amsa d’aya nake samu soyayyace , don Allah yau ki fad’amin wani abu game dake koh muhammad, koh nima zansamu na kunce kullin dake damuna akanki.

    Hmm Ajiyar zuciya sumayya tayi, sannan a hankali ta bude baki”yau zan sanar dakai wacece sumayya Abdusalam Shugaba, ada kafun ta zamo MATAR MAKAHO………..🍀🍀🍀🍀

    🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
    🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯
    ~ Na ~

  • Matar Makaho 76-77

    Matar Makaho 76-77

    Page7⃣6⃣&7⃣7⃣
    Bayan Auren abie da safina, a lokacin safina tafito da duk wani mugun halinta a gidan, ta buwayi kowa, har dada bata ragarwa ba, shikuma abie daman ba sonta yake ba, shiyasa sam koh ana meeting, safina naci musu mutunci baya saka bakinsa a maganar, tunda su suka kakkaba masa ita, badason rasa ba.

    A lokacin safina tasaka sumayya a gaba da duka zagi, sai da dada ta sanar da abie, ranan da yasan abinda safina ke aikata wa yarinyar sa in baya nan, baraxanan sakin ta yayi ya zazzage ta, kai ranan anyi kwanan bacin rai a gidan.

    safina ganin auren ta zai iyya mutuwa yasa ta shafawa kanta lafiya, bata koh ga maciji da sumayya, daman ba’a hannunta take ba, a hannun Dada ne.

    Lokacin da sumayya takai shekara 12, har lokacin safina(momy)bata haihuba, kuma abie bai wani damuba, tunda yana da sumayya, duk wani soyayya da kulawa sumayya na samu a gidan, baga bappanayen taba, ba dada ba ga abien ta, momy ce kawai bata kaunar ta, har lokacin safina na tare da nafisa, duk da nafisar ta koma gidan tsohon mijinta, lokacin.

    Haka kawai sumayya ta waye gari duk yan gidansu basa kaunar ta, daga su babuji har matan su, dada karan kanta bata shiga tsabgarta sai in babu mutane a wajen, ga tsoron momy da suke, da bin umurnin ta kome tace jiki na bari zasuyi inka cire abie, sosai sumayya ta shiga wani irin mawuyacin hali, abie inta ne kawai ke tsaya mata akan kome, baya taba yarda a cutar da ita, kuma duk wanda yama yarsa abu a ranan zaiga bacin ransa, ana hakan ne fa momy rana tsaka ta dake sumayya, wai ta b’ata mata labulen d’aki da lalle, a ranan abie saki d’aya ya mata ya korata.

    Amma safina taki tafiya, dada tace sayya maidata d’akin ta, ganin matsaloli da sumayya keta fuskarta a lokacin, ga kananun shekaru, abin harya fara tayar mata da kewar mahaifiyarta, yasa abie saka a FGGC boarding school, ta cigaba da rayuwan ta a hostel, shikad’ai ne gatan ta, sai wata rana Dada tana zuwa mata visiting a boye, kuma tace mata karta fad’awa kowa tazo wajen ta, sumayya koh marmarin komawa gidansu hutu batayi, amma hakan take komawa in anyi hutu tana Allah Allah a dawo hutu.

     

    Sumayya lokacin da ta cika budurwa, ta tashi da wani irin hali, akwai jijida kai da ganin tafi kowa, kasancewar ta mai kyau, ga Arzikin gidan su, ga rashin sabo da mutanen gidan, ga rashin mafadi don har lokacin xaman hostel take.

    Sumayya inta dawo hutu duk yanda saurayi zai biyota, saita raina masa arziki gani take kamar tafi karfin sa, in kuma yakasan ce mai kudi sosai, sai taga kamar zata samu wanda ya fisa, in mai kyaune sai taga kamar nan gaba zata samu wanda ya fisa kyau, sumayya nada kawaye, koh saurayin kawarta ta gani ta ringa dariya kenan, tana kushe sa mummuna talaka kaza kazan, wasu Friends inta da dama in auren su ya tashi basa gayyatanta, saboda rainin wayo da take zuwa ta musu a wajen biki.

    Lokacin da sumayya tayi candy, taci jamb A lokacin tana da shekara 18, aka shiga university sai abin ya d’ara na da, ganin yanda ake tururin sonta, babu ranan da zata fita ba’a biyo taba, hatta cikin gidan su Abdul(wanda lokacin da sukaje gida, bayan aure aka mata wulakanci, yace zai rage musu hanya ita da khadija)da kaninsa sunsha dambe akanta, Amma haka ta murza ido tace basu mata ba, karshe dai Abdul aure yayi, harda yaransa biyu ya fita harkar sumayya.

    Sumayya bata gane kuranta ba, sai lokacin da takai shekara 23 lokacin ta kammala digree inta har tayi service, zuwa lokacin duk samarin ta sunja jiki da ita, kowa yana baya baya koh hira suke ta sako musu zancen aure, sai su kama kaucewa wasu kamma gudu suke, rabin kawayen ta duk sunyi aure, sai d’aid’aikune suka rage.

    Bayan dawowar ta gida lokacin yaran gidansu sun d’ara nada, a yawa wasu sunyi aure wasu na aiki, itama rashin miji yasa abie nema mata aiki a bank nasu dayake aiki , dayake statistic ta karanta, tana aikinta tana samun Albashin ta, Amma maganar samari fa babu yanzun, ita karan kanta aure take so Amma babu mazan, ga kyau ga aiki ga kudi, mijine kawai matsalar ta.

    Shekara 2 sumayya tana aiki a bank lokacin tana da shekara 25 a duniya, ganin haka yasa dada nema mata maganin farin jini, amma ina tayi tayi abin shuru, karshe dai dada ta nemi kanin abdul ya dawo su daidaita da sumayya, amma ba kunya a idon abie yace shi bazai aure sumayya ba, yarinya yar 15 xai nema ya aura ba rikekkeyaba abinnan yama abie zafi matuka, hakan yasa sa zagin kanin Abdul sosai abin ya zama babban magana.

    Wannan dalili yasa babuji rantsuwa sai sumayya ta fitoh da mijin aure nan da wata uku, tunda dai zaman ta a gida fad’a zata had’a a tsakanin su, kamar yanda momy ta kitsa musu, don Abie indai akan sumayya ne baya ganin kowa da gashi, jin abinda akace ma sumayya yace sam bai yarda ba, ga yaransu su kubra da miemie sun girmi sumayya ba’a saka musu ka’ida ba sai yarsa.

    Kuka dada tasa akan abie zai nuna musu iko da sumayya, abinda ya sa abie yarda kenan, sumayya har wata uku ya shige bata samu miji ba, su babuji sukace aikin da take shiya hanata aure, hakan yasa sukasa abie dakatar da aikinta.

    Sumayya kam ganin an rabata da aikin ta da tafi so, don lagon sumayya kenan, kace zaka kaita garin su mamanta, koh kace makaranta, hakan yasata d’aukar takardun ta, ta tafi asibiti neman aiki babu wanda ya sani.

    Dayake result nata nada kyau, yasata samun aiki a pharmacy tana musu lissafin kudin magani.

    Kullum take fita aiki, ba tare da aisan ina take zuwa ba, abie bincike yayi ya gano aiki take zuwa, wannan ne dalilin kwace mata ducument da yan uwan mahaifinta sukayi, sannan suka rabata da aikin ta.

    Ta dawo zaman gida, daga baya taga bazata iyya ba, tanemi shagon make-up tana zuwa training, daman ta iyya lalle, da sukaga ba sarki sai Allah, yasasu barinta tana zuwa koyon make-up in, basu hanata ba.

    Sumayya ta cigaba da koyon make-up, har ta iyya aka sallame ta, taso abie ya bude mata nata shagon, Amma yaki karshe dai kawaye da yan gidansu, in sun tashi aure koh yan unguwansu take ma, ana hakan ne lokacin Aikin hajji yayi, kamar koda yaushe daman duka gidan ake tafiya hajji koh wani shekara, amma bana sunce baxasu ba, sumayya da abie suje.

    Ba musu sumayya suka tafi aikin hajji, wanda zuwa lokacin bazata iyya kirga sau nawa taje ziyaran d’akin kaba ba, bayan sallah abie ya dawo, sumayyya kam daman akwai yar babuji dake aure a saudi, kin dawowa tayi ta zauna agunta har sai da tayi wata 7,lokacin ta cika shekara 26 ta dawo, kamar wasa tana dawowa yan gidan sukace sun mata miji, akwai wanda ya ganta yana so, hankalin sumayya ya tashi a lokacin, amma abie ya kwantar mata da hankali, akan zaiyi bincike akan mijin.

    Duk yanda abie yaso yan uwansa su sanar dashi waye ne mijin, sunki Amsa d’aya suke basa, shine sun isa da yarsa, haka ba yanda ya iyya dagashi har sumayya suka zubawa sarautan Allah ido, sumayya duk azanta wani shararen mai kudi za’a aura mata, koh d’aya daga cikin samarin gidan.

    Abu kamar da wasa, ya zama gaske don maganar auren sumayya babu inda baije ba, sai shirye shirye ake duk da ba auren soyayya bane, sumayya ta kwantar da hankalin ta koh banza tasan mijin classic za’a bata koh ajeboter.

    RANAR D’AURIN AURE
    Sai da sumayya ta tuno da mahaifiyar ta, haka kawai ranan tunda ta tashi sai kuka take, shi karan kansa abie a zullumin rabuwa da yarsa yake, yasan ba’a kyauta mata ba sam.

    A waje kofar gidan shugaba, ake shirye shiryen d’aurin aure, sumayya dake d’aki da kawayen ta Ansha kwalliya kamar me, za’a aure classic kanta sai wani kara fashewa yake yanzun kam koh kukan ta daina, ji kawai sukayi Ana Alhamdulilahi An d’aura auren sumayya Abdulsalam shugaba, tare da Angon ta Muhammad Al’ameen yusuf, akan sadaki naira dubu 20, da mamaki sumayya tace “dubu ishirin kuma?wani irin mijine haka dubu ishiri ai mu tunda muke aure a gidan nan ba’a taba biyan sadaki haka ba”

    Kawarta ce ta kalleta, kai sumayya sadaki fa Albarkansa ake nema, ba yawa ba kika sani koh mijin Alu-sunnah ne, irin samarin nan ne ustaxai, ga gemu ga d’angalalen wando kinsan fa irin su sunfi dadi love.

    Gabaki d’aya kawayen dake d’akin dariya suka saka da shewa, don harga Allah sun d’auka mai zafi sumayya zata aura, sanin da suka ma halinta na rainako, ke ina ga fa irin samarin nan ne yan 20 something zuwa 30.

    “Allah ya sauka bakin ki ya sare guntun kashi, habba 30 ai nima na fara jin kamshin, 30 ina laifin 35 irin ya bani shekara 9 nan” sumayya ta bata amsa

    Duka suka kwashe da dariya, ana ta nishadi, kamar daga sama suka fara jin hayani yana tashi a babban falon gidan, muryar abie ne yake cewa bai yarda da auren nan ba, bazai yafe ba arasa wa za’a aurawa yarsa sai miskini, saboda babuji yaga ba yar gaddafi bane koh Abubakar shiyasa har ya iyya had’ata da yaron nan, yau sai an raba auren bai yarda ba, jin haka yasa sumayya da kawayen ta rugawa da gudu suka shigo falon don jin ba’asi.

    MAKAHO ne ya ganta yana so, ba sai a basa ba tunda ba manemi bane da ita, babuji yace.

    Kafun abie yayi magana sukaji timmmm sumayya ta yanke jiki ta fad’i jin wai MAKAHO aka aura mata ita sumayya.

    ***********
    Bayan sumayya ta farfado duk borinta da masifar abie, dada tace a yau innan sai ankai sumayya gidan mijin ta, koh ta d’aga masa nono, ba yanda abie ya iyya yana ji yana gani aka sabi yarsa a mota, tare da babban mota na kayan d’akin ta, dana gara wanda kome set uku aka mata gado uku kujeru uku firij uku kome uku uku aka mata hada kayan kitchen, kawayen ta fa sun samu abin yi, sai dariya suke suna yad’a mata bakar magana, especially wa’inda sukayi aure, sumayya a ranan tayi kuka har saida tayi Addu’a Allah ya d’auki ranta,saida wata yar uwar su na gembu ta mata wa’azi kar bacin rai yasa tayi sabo.

    Ai bata tashi ganin bacin rai ba, saida motar su tayi fakin a kofar gidan Adara, wani gidane irin na talakawa mai jan kasa sai kofar gidan da babu kofa, lulubi aka mata suka shiga gidan, amma kamar ba gidan da za’a kawowa amarya ba, babu wanda ya tarbesu asalima kowa harkar gabansa yake kamar ba’aga zuwansu ba, tambayar kofar amarya sukayi aka nuna musu, wani samurmurin d’aki koh kewaye sa ba’ayi ba, d’akine d’aya kankani wani rubebe dashi, ihu sumayya tasa ta tsunguna agun tana sakin kuka itakam tata ta sameta.

    Ga auren MAKAHO ga talauci dame zataji, Allah ya isa ta farama su babuji, tana sun cuceta, a hakan dai aka wuce d’akin, yar uwar dada ce ta tura rubebben kofar da koh sakata bazai zauna ba tsaban rubewarsa, suna bude dakin ba laifi a wanke yake sai dai babu kome sai cinyayen taburma da ghana must go na kaya kad’ai a d’akin, su karan kansu masu jeren ma sun rasa ta ina zasu fara, wanda aka kawowa set uku shine aka samu d’aki d’aya karami.

    Da gudu sumayya ta b’anbara ta bar gidan, kawai su dada na zaune sukaga amarya ta faso da gudu ta dawo gida”wallahi bazan xauna agidan shan ba”wannan shine abinda sumayya tace, kuma ba wanda yayi maagana.

    Wannan hajiya yar uwar dada ita tayi waya aka kira mata kafinta, a take yaxo shida abokan aikinsa uku,suka buga musu kofar daki, a ka cire tsohon dayake yammane, wasu daga cikin yan uwan, kwana sukayi washe gari kafintoti suka gama aikinsu, sun kewaye kofar da falange an mata band”aki a kofarta, an saka silif da kitchen da baranda, Amma fa kaya bai d’auka ba koh set d’aya basu samu shigaba, haka aka juya da sauran kayan.

    Abie da kansa a ranan da , dadare ya dawo da sumayya bisa umurnin dada,haka aka watse aka bar sumayya da halinta, wasu sun mata wa’azi wasu kam magana suka gaggaya mata.

    Sumayya tunda suka watse aka barta kuka take, gashi dare ne tana zaune akan gadon tana kuka cikin bakin cikin wannan al’amari, sai a ranan wani irin kewar mahaifiyarta ya kamata da ace mamarta na tare da ita da abubuwa zasu mata sauki.

    Duke take tana kuka baji ba gani wai itace da aure a irin wannan gida……………..

    Tas sumayya ta sanar da Ammar duk irin wahalar da tasha, da burinda taci na ganin tayi wa muhammad wulakanci, harsai yaji a jikinsa kafun tanemi sakin ta, amma saboda kyawawan halinsa da hakurinsa don babu abinda sumayya bata masa ba, amma bai taba nunawa koh a fuska ba, bai taba riketa , da wani manufa a ransa ba, kullum kokarin faranta mata yake, wannan sune makamin da yayi tasiri wajen mallakar zuciyar sumayya, taji zata rayu dashi a haka, sannan ta d’auki auren su da Al’ameeen isharane Allah ya nuna mata, akan halinta, kuma ta karbe kaddarar ta, tazauna da mijinta….

    cigaban labari………
    “Sannan yau suce wai na rabu dashi akan me”?

    D’aga ido Ammar yayi ya kalli sumayya da khadija dake kuka, lokaci guda, sumayya!!ya kira sunan ta.

    “Na’am”

    Kukan ya isa haka abinda nakeso dake shine ki d’auki duk abinda ya faru a matsayin jarabawa, kamar yanda kikace, naji duk abinda iyayen ki suka miki, Amma ke me kika fahimta akan auren ku da muhammad, da gaske bashi yace yana sonki ba?

    Gyara xama sumayya tayi ta zayyana masa labarin muhammad, da irin wahalhalun da yasha.

    Tabbas Ammar ya tausayawa rayuwar su muhammad, kuma a cikin labarin sa da sumayya ya auna wasu abubuwa da dama akai, sai kuma abu na biyu, sumayya kina nufin mamar ki sunan ta hafsa sannan yar maiduguri ce?

    “Eh Amma bansan a ina take a maidugurin ba”

    Amma naji mahaifin ki yace zai kaiki wannan karon.

    “Ni yanzun bata maiduguri nake ba, ta mijina nake”

    Sumayya kiyi hakuri ki koma gidan naku, tunda naga iyayenki zama a gidan Adara ne basaso kiyi, in Allah yasa Al’ameen ya dawo, kinga shikenan sai ki dawo d’akinki, in ma basason zaman gidan ne, nizan nema muku wani gidan saiku koma, amma a halinda kike cikin nan ya kamata ki kula da kanki, juna biyu ne dake ga dp ki na hawa, koh kinaso ki rasa babyn nakune?

    “Ah ah yaya Ammar”sumayya ta amsa masa.

    Yauwa koh kefa kiyi hakuri ki koma gidan kinji?insha Allah auren ki da muhammad bazai mutu ba.

    Kuka sukaji da karfi a gefen su, khadija ce ke kuka.

    Kee lafiya menene haka?

    Kallonsa khadija tayi da haushi jin tambayar da ya mata, toh ba kai bane kake cewa Aunty ta tafi, toh ni kuma in zauna dawa?

    Da goggo mana zaki zauna, ba za’a bude makaranta gobe monday ba?saiki cigaba da zuwa kafun yayan ki ya dawo.

    Kuka khadija ta sake, shikenan aunty yanzun tafiya zakiyi ki barni.

    Toh koh zaki bita ne gidan nasu?koh taki bin umurnin iyayen ta akanki?khadija iyaye fa ba wasa bane?ammar yace cikin haushi

    Shuru ta masa, sai ga likita yazo ya basu sallama, don sumayyar ba wani jin jiki tayi ba, ruwan da aka saka mata ya kare.

    Suna Fitowa taga Ahlin gidansu tim a cike a haraban asibitin, kala batace musu ba Tana bin Ammar a baya, ga khadija a gefe.

    Tashi sukayi suka bisu a baya har packing space, sumayya motar Ammar tayi niyar shiga Amma dada tayi tsalle ta dire akan ba inda sumayya zata shiga, sai motar gidansu.

    “Kinsan Allah dada in kika matsamin saina fasa bin naku naga ta tsiya” sumayya tace.

    Yi hakuri kawalli jeki shiga na Abokin mijin naki.

    Shiga motar sumayya tayi ta kalli khadija dake tafiya a hankali kamar kwai ya fashe mata a ciki, daga ka ganta kasan tana cikin matsanan cin damuwa, “ya Ammar ka fad’a musu bazan koma yau ba sai gobe, sutura driver yazo ya d’auke ni inna shirya kayana”

    ba musu Ammar ya fita a motar daidai lokacin khadija ke kokarin shiga, yaje ya sanar dasu basu wani d’aga hankalisu ba sukace goben insha Allah abie da kansa zaizo d’aukar ta, in kayan sawane ma?ta bari kawai za’a saya mata sabbi.

    Amma sumayya tace ita sai ta kwana washe gari zata koma gidan su.

    Bayan isar su sumayya gida, Ammar tafiya yayi, khadija ta kalli Auntin ta, yanzun Aunty da gaske zaki tafi ki barni?shikenan ni babu yaya babu ke banida kowa yanzun sai goggo?

    “Khadija baxan barki ba koh babu yayan ki Zan kula dake, guduwa zamuyi daga jalingo, gobe goben nan da asuba zamu bar gari…………..🍀🍀🍀

    ✨Ruqeenjalal✨

    🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
    🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯
    ~ Na ~

    🍃 *Rukayya* *Ibrahim* 🍃

  • Matar Makaho 92-93

    Matar Makaho 92-93

    A ranan da aka nad’a yusuf a ranan mahaifinsa yake sanar dani, akan na fad’awa yusuf ya d’auko iyalansa, ya masa hakan ne don yaga zai masa biyayya koh zai bijire masa, Amma tunda ya yarda da auren lawiza kuma ya hau karagan mulki ya yafe masa duniya da lahira.

    A hankali yusuf ya kalli mahaifiyarsa, mahmah meyasa kika hanani?

    Kayi hakuri yusuf nayi hakan ne don banason kayi nisa dani, nayi tunanin koh inna sanar dakai hakan zaka iyya bijire wa mulki.

    Ramadan ne ya kalleta Amma wallahi mama baki kyauta ba, duk irin ciwon da yaya yake Amma mahmah baki tausaya ma d’anki ba?kowa yasan dalilin ciwon yaya yusuf Amma ga magani a hannunki mahmah kika kasa basa habba mama mulki yafi lafiya ne?

    Kuka mahmah ta sake tana nuna Alhininta.

    Kaga ramadan ya isa haka mahmah uwatace har abada babu wanda yakai uwa son d’anta don haka ni mama bata mini kome ba.

    Jin abinda yusuf yace sosai jikin wasu yayi sanyi, Al’ameen hannu yasa a wuyansa ya zaro sarkan tare da mikawa mahaifinsa, Abbajo ga sarkanku a sawa wanda ya dace?

    Kallonsa zulkiflu yayi, akan me zaka cire, wayace maka baka dace da magaji ba?

    Ah ah uncle kai ya dace kasa koh uncle Ramadan nikam banida sha’awar sarauta so nake nayi karatu mai zurfi na zama soja mai mukami.

    Kowa dake wajen da kallo yabi muhammad jin abinda ya fad’a, murmushi sarki yayi hade da cewa yan uwansa, bazan tilasta muhammad ba daman na basa sarkane badon na shaida shine magaji ba, na basane don na gane sa aduk shekaru da zai gabato duk da Akwai kamar jini, Amma zan aje shaida don haka Za’a d’aurawa zulkiflu.

    Da sauri zulkiflu yace Ah ah wallahi yaya nikam banaso gaskiya, amini afuwa adai bawa Ramadan.

    Ba musu aka d’aura wa Ramadan sarkan magajin masarauta, sannan a mana booking in fly next week zamu shige nageria.

    Jin Abinda sarki yace yasa zuciyar muhamamd rawa, ganin wani rawan jiki da mahaifinsa keyi zashi nageria duk zatonsa matarsa na raye, Abbajo nace dukan mu zamu wuce ne?

    Ah ah muhamamd bazamu wuce mu biyar ba, tunda in muka d’auko su dawowa zamuyi nan?

    Shuru muhammad yayi yana kallon Mahaifinsa, ya sake juyawa ya kalli mama kamar hadin baki suka had’a ido da nabila kauda fuskar sa yayi.

    Waini muhammad baka bamu labarin abubuwan da suka shafeka ba, da Alakar ka da sarkin shayi da yaran nan?, zulkiflu yace yana nuna su gidado.

    Da sauri muwaddat tace eh hakane Akki.

    Kasa magana yayi yana kallon yusuf, gyad’a masa kai yusuf yayi Alamun yayi maganar sa, A hankali ya fara basu labarin abubuwan da suka faru bayan tafiyar yusuf da wahalar da suka sha da abubuwan da suka faru da ubangari da zainab, da mutuwar Maminsa da kaninsa harda Aurensa da sumayya, sai dai bai fad’a musu dalilin da yasa aka aura masa ita ba, don baidace yace dangin ta sunyi mata kazafi ba, har kawo zuwansa cameroon.

    Muhammad na bayani mutane wasu na kuka wasu na salati wasu najin haushin zainab da mahmah data hana a d’auko yaran yusuf, kuka itama mahmah ta sake tana cewa su muhammad su yafeta ta cutar dasu.

    Yusuf kam zaune yake akan karagan mulkinsa sosai fuska tayi zahur, jijiyoyin fuskarsa ya mike alamu dai ran maza ya baci, gashi a fada yake dole ya matse irin na sarakun, abin tsoro koh bacin rai da tausayi baya bayyana a fuskarsu mundin suma gaban jama’arsu.

    A take aka matso da tafiya zuwa jibi in Allah ya kaimu da rai da lafiya sai NIGERIA!!!!!!

    Mikewa yusuf yayi ya koma falonsa kafun kowa ya mike ya fita, nabila kam jiki yayi sanyi saibin mahmah take a baya, yayinda muwaddat da muhibbat suka likewa d’an uwansu sai hira suke masa da tambayarsa labarin khadija, sosai yaji wani irin farin ciki ganin yan kannensa, lawiza ma tashi tayi batama kowa magana ba tayi flat nata, da fari tad’au abin da zafi Amma jin irin wahalar da su muhamamd sukasha da mutuwar Aisha sai taji jikinta yayi sanyi.

    ***************
    Sumayya ce zaune a kitchen tana girka pepper chicken zallah, don ita yanzun nama kawai takeci sai shayi, yanzun ma khdija taje islamiyya ne shiyasa ta shiga kitchen da rarrafe zata girka abinci.

    Sai karfe 5:21 khadija ta shigo falon da sallama, sanye take da riga da wando sai hijab babba na islamiyya, hannunta d’auke da jaka.

    Amsa mata sumayya tayi tana binta da kallo ta rasa meke damun khadija a kwana biyun nan, gabaki d’aya ta shanja bata da nutsuwa sam, kullum ta zauna shuru koh aiki ta sata bata gamawa akan lokaci, shiyasa wasu aikin take lallabawa tayi duk da nauyin cikinta, don yanzun saidai ta ja ta shiga d’aki indai khadija bata nan”khadija zonan”?

    Ba musu ta kwabe hijab nata tazo ta zauna kusa da sumayya, Aunty gani.

    “Khadija meke damunki”?

    Babu Aunty

    “Wani irin babu kome, ki dubi halinda kike ciki duk kinsa rayuwar ki a garari, sai kinzo kin samu ciwone a koma ana sayan magani koh yaya”?

    Babu kome fa Aunty

    “Bankai ki fad’amin damuwarki ba koh”?

    Sunkuyar da kai khadina tayi bata iyya cewa sumayya kome ba, tana wasa da yatsarta.

    “kunyi fad’a da kalamu ne kwana uku yau baizo ba”

    Wallahi Aunty bansan meke faruwa ba yau kwana uku bai kirani ba, inna kirasa wayar sa a kashe.

    “Ok abinda ke damunki kenan?amma meyasa baki tambaye kannensa ba tunda islamiyyar ku d’aya kuma boko ma d’aya”

    Wallahi Aunty kunya nake ji, karsuce da wani abu.

    “Kunya?lallai khadija bakisan inda ke miki ciwo ba, yaro kullum sai yazo wajen ki kwana uku bakisa sa a idanunki ba, bazaki iyya shigiyarsa ba?

    Sai gobe innaje school saina tambaye falmata(kanwarsa)

    ” ohon miki”

    Tashi khadija tayi jin amsar da Auntin ta ta bata.

    Washe gari bayan khadija ta dawo gida take sanar da sumayya ai kalamu ba lafiya yana hospital, kasancewar sumayya tayi nauyi, khadija ce tayi girki mai rai da lafiya, kawarta ta rakata suka je asibiti wajen kalamu, sosai suka samu jikin nasa yad’anyi sauki, kuma taji dadin tarbar da aka mata maman sa nada kirki sosai, haka ma babansa, wanda ke d’auke da zanen kanuri a fuska, amma mamansa bata dashi, haka kannensa sukayita tsokanarta wai budurwan kalamu ne, sosai tayita jin kunya.

    ************
    Kwana biyu da muhammad yayi a gidan sarauta, da ace zasu hadu da wanda yasansa a baya indai ba farin sani ba, bazai ganesa ba, ya samu gata kota ina bana wasa ba yayi kyau ya kara fresh yana cin mai kyau yana shan mai kyau, ya kwanta a maikyau baida buri daya wuce yadawo yaga matarsa abar sonsa, sannan yana iyya bakin kokarinsa wajen ganin mahaifinsa bai saka damuwar rashin Aisha da salim ba, sosai yake kula dashi baya barinsa shi kad’ai mundin yabar fada, toh zasu kasance tare haka yan uwan babansa na sonsa, kannensa ma duk ya shaku dasu, nabila ce kawai bata samu fuska a wajen saba duk da mahmah tasata ta basa hakuri kome ya wuce, kuma ya nuna ya hakura Amma bata ganin fuska koh hira yake tazo wajen sai yayi shuru abinsa koh ya tashi.

    Su gidado da sarkin shayi duk sun dawo gidan da zama.

    Waya mai tsada zulkiflu ya saya masa da kayayyakin sawa masu yawa, wanda zaina sawa.

    Kamar yanda Aka saka rana yaune za’a diro nigeria, maimartaba ne da mahmah sai muhamamd da zulkiflu Adda maisara, dayake su muwaddat na jarabawa an barsu da lawiza a gida, karfe 2 na rana jirginsu ya d’aga zuwa Kasarmu ta gado!!!!!

    Sun sauka lafiya, suna fita a jirgi dayake sarki yasan da zuwansu yasa suka samu tarba na musamman direct gidan sarki suka nufa, duk da muhammad yaso ya fara zarcewa sintali sai dai ba dama.

    Bayan sunyi wanka sunci abinci,kasa hakuri yayi ya ce zaije sintali ramadan ya rakasa a mota tare da driver.

    Tunda suka shigo sintali yake bin koh ina da kallo yana tuna abubuwan da suka shude watan nin baya, har kofar gidan Adara akayi packing in motar,jikinsa har rawa yake yana Allah Allah ya fitoh, saura kad’an ya buge kafarsa saban sauri ya bude motar ya fita, gashi daman yammane ana shirye shiryen kiran mangariba, abin mamaki yana fita babu wanda ma ya zaci shine, harya ratsa mutane sai binsa ake da kallo ganin babbar motar da ya sauka a ciki.

    Shiga gidan adara yayi kamar yanda ya tsammani hakan ce ta faru, wato jama’ar gidan na tsakar gida, duk juyawa sukayi suna kallonsa harya karaso tsakar gidan, gaidasu yayi da sauri gabaki d’ayansu suka Amsa hade da shiga shock, indai ba gizau ba Al’ameen ne, duk gatan da ya samu bazai hana su kasa gane saba.

    Da sauri iro ya mike bura uba wanake ganin nan kamar muhammad ina ka shiga?

    Bai samu daman basu amsa ba, kofar su kawai ya nufa cikin sauri ya bude kofar shashen, da mamaki yakebin kofar ganin duk datti, Alamu dai an dade ba’a share ba da sauri ya karaso kofar, yana bin koh ina da kallo,da sauri ya shiga kitchen insu ga mamakinsa kome a zaune yayi kura, da sauri ya fitoh a kofar, daidai lokacin Ramadan ya shigo gidan, da sauri muhammad ke tambayar yan gidan da har yanzun suke a tsaye sun maidashi madubi,tambayar su yayi ya yaga kofar sumayya a kulle?

    Inna asabe ce take sanar dashi ai ba’aga sumayya ba, kama kai kawai yayi yana salati, da sauri ya fita a gidan da kafa ya taka har gidan goggo, yayinda su iro ke mara masa baya, duk inda suka wuce saisu cewa mutane ga MAKAHO ya dawo ga makaho, har gidan goggo va tare da wani neman izini ba ya shiga gidan.

    Goggo dake zaune a gindin bishiya, gabaki d’aya ta rame ta zama abin tausayi zaune take tayi tagumi, jin sallamar muhammad yasa ta mike da sauri, wanake ganin nan kaman muhamamd?Allahu Akbar Allah mungode maka sai kuma ta fashe da kuka tana rungumar Al’ameen.

    Saida tayi kukanta mai isarta kafun Suka gaisa na yaushe rabo, hade da karama mujammad karin bayani akan batan su sumayya, wanda shagari ya sanar dasu guduwa sukayi bawai sacesu akayi ba, sosai muhammad yaji wani irin ciwo na abinda dangin sumayya sukayi bayan rabuwar su, taya zasuce ya rabu da matarsa akan wani dalili, anan yake sanar da goggo abubuwan da suka faru sannan yace mata yana son zuwa gidan su sumayya don ganawa da iyayenta, koh Allah yasa sunsan inda sumayya zata iyya zuwa.

    Ba karamin mamaki Goggo tasha ba jin wai yusuf sarkine yanzun, Allah sarki duniya, mikewa gogho tayi tad’au hijabinta suka fita gidan da Al’ameen, ai suna fita kofar gida, me zasu gani mutane ne makil a kofar gidan, sunzo kallon Al’ameen don lokaci d’aya labari ya samesu makaho ya dawo yayi kudi, goggo ma a take ta kara musu da wani ai yanzun d’an sarki ne babansa yana mulkin wani gari, a nijar, muhamamd in ma kudi ya ciro a Aljuhunsa ya rarraba musu dubu bibbiyu.

    Yana gama raba musu kowa ya watse yana saka masa Albarka, harya juya zasu shiga mota,don driver yajawo ramadan dake ciki har kofar gidan goggo, yana shiga tun daga nesa ya fara jin ana kwala masa kira oga oga oga!!!!

    Shagari ne ya iso wajen da gudu, da ido muhammad ke binsa koh ba’a fad’a ba yasan shagari ne daga muryarsa ya gane sa.

    Oga sannu da dawowa ka dawo lafiya, yanzun Abdu ra’uf kece mini wai ka dawo.

    Murmushi muhammad yayi, lafiya Alhamdulilah shagari.

    Da sauri shagari yace munyi kewarka oga shagon mu ya bunkasa nima, yanzun ina makaranta bara na kira Ammar na sanar dashi daman ina da number sa?

    Ah ah basai ka kiraba ka bani number sa zan kirasa.

    Kallon ramadan da goggo dake mota shagari yayi sai kuma ahankali yace oga tafiya zakayi ne?

    Ah ah shagari ina Taraba har sai anga sumayya.

    Number Ammar ya basa sukayi sallama suka tafi, dayake shugaba family house sanannen gidane kuma driven dan garine, yasa da kwatance suka gane gidan, goggo ramadan da muhamamd suka shiga gidan,ganin zubinsu yasa mai gadin basu hanya suka wuce cikin compound, ya shiga gidan don musu sallama da mai gidan, ba’a jima ba saiga Uncle Abubakar ya fitoh suka gaisawa, sannan suka gabatar masa da kansu, kuma suna son magana da mahaifin sumayya, da rawan jiki Abubakar ya musu iso zuwa cikin gidan, da gaggawa ya hado kan mutanen gidan a falo, kowa na zazzaune don su daman ba farin sani sukayiwa muhammad sosai ba, a d’auren aure suka fara ganinsa hakan yasa basu wani ganesa ba, gashi ba’a makaho yake ba yau.

    Bayan sun zazzauna wannan zaman ma ba momy a ciki, a nitse goggo ta musu bayanin ga mijin sumayya ga kuma bappansa ta nuna Ramadan, da mamaki suke tambayarta ba’ance mijin sumayya makaho bane kuma ya bata.

    Ramadan ne ya musu bayanin kome a take jikinsu yayi mugun sanyi, sannan suke sanar dashi rashin ganin sumayya anyi iyya bincike Amma shuru, duk inda ake tsammanin zataje ba’a ganta ba, abie har wani ya samu ya tura unguwan su Hafsa a maiduguri a dubo masa koh sumayya ta gane gidan kakan ninta shan taje, amma an samu tabbacin banan sumayya taje ba, Asali ma hafsa tayi aure bata maiduguri yanzun.

    Hankalin muhammad ba karamin tashi yayi ba, fiye da hankalin yan gidan duk da abie ya shiga damuwa don har rama yayi mai tsanani, suna tsaka da maida zancen sukaji an turo kofar falon koh sallama babu.

    Gabaki d’aya suka juyo suna duban falon, safina ce ta shigo Alamu dai daga unguwa take, duk suka bita da kallo itama, d’aga ido tayi ta kalli jama’an falon da karfi ta kwala kara ta zube a kasa sumammeya..

    Da sauri dada tayi kanta, sabanin Abie da sauran yan gidan dako a jikinsu alamu dai ba karamin tsanarta sukayi ba, muhammad ma mikewa yayi shida ramadan suka nufi kan momy, da taimakon su aka kaita asibiti don anyita watsa ruwa bata farfado ba, gashi yan gidan koh a jikinsu, sune suka d’auketa har asibiti suka biya kudin kome suka tafi suka barta da dada, gida suka koma bayan isha’i suke sanar dasu yusuf abubuwan da ya faru da batar da sumayya tayi,sosai suka nuna Alhininsu da damuwa sosai muhamamd ya basu tausayi yaro tun yana karami yasan wahalan duniya, har tashinsa ma yayi gwagwarmaya.

    Washe gari da sassafe saiga Ammar a gidan sarauta, daya samu aka barsa ya shiga ya tura wani dogari yace ana sallama da muhamamd bakin Niger, ba’a jima ba sai ga muhammad ya fitoh, tun daga nesa yake kallon muhamamd kamar bashi ba gabaki d’aya rayuwa ta sauya, sanye yake da jallabiya yar saudi sai hula taba kaji hadisi, sosai yayi kyau saidai fuskar sa a tamke take alamu baya cikin walwalarsa, yana karasowa da sallama a bakinsa, amsa masa Ammar yayi ai yana jim muryar Ammar da sauri ya rungume sa, cikin farin ciki suka hau hira har cikin gida muhammad ya shigar da Ammar suka gaisa da yan uwansa da mahaifinsa, sai a lokacin yake sanar dashi ai shagarine ya kirasa yake sanar sashi muhamamd ya dawo, yana gidan sarki kuma ya basa number Amma shuru Al’ameen bai kirasa ba shiyasa yabuga sammako yazo ya gansa.

    Abinci aka kawowa Ammar, suna zaune a d’akin da aka sauke muhammad ana hira da labarun abubuwan da suka faru a baya harda Ramadan, kawai saijin muryar jama’a sukayi a sashen sarki, dayake window d’akin da aka sauke muhammad yana saitin sashen.

    Mikewa sukayi gabaki d’ayansu suka zagaya zuwa falon sarki,family shugaba ne, suka gaishe dasu abie, aka daura zancen batan sumayya kowa na kawo shawaran sa, karshe dai akace za’a dage da rokon Allah da sadaka sannan za’a zuba jami’an tsaro a bincike su, kafun kowa ya watse, daman yan gidan su sumayya gaida yusuf sukazo da mahaifiyar sa tare da bada hakuri akan abinda ya faru kuma ba laifi sun nuna musu bakome, kome ya wuce Allah ya kiyaye na gaba.

    Satin yan nijar biyu a taraba ba’aga sumayya ba, gashi kaf gidan su an duba hotonan ta duka ba’a gani ba, hatta dakin su muhammad ya koma yayi bincike sap baiga wani hoto ba, don sumayya ta tafi da hotunan su, gashi na wayar maimuna kanwar Ammar ma, wayar ta lalace harma ta saida ta, bare su samu hotunan su, da yake yanzun zamani ya sauya ba kamar daba, mutun ya bata a gari ma ba’a ganesa sai da rabo bare a kasa sukutum, dole tasa Yusuf komawa dasu ramadan aka bar mahmah da muhammad, kafun su tafi saida aka sai musu gida mai shegen kyau a Amazon suka koma ciki su uku harda goggo, kasancewar mijinta ya rasu bayan tafiyar sumayya hakan yasa muhammad d’aukar ta suka koma gidan su suna zaune tare da mahmah.

    Wasa wasa saida muhamamd suka share wata biyu a jalingo Ana kan bincike har yanzun shuru ba’aji duriyar sumayya ba, koh khadija sosai abin ya dame muhammad koh abinci baya iyyaci sosai, ba irin tunanin da baiyi ba don shi gani yake saceta akayi tunda makiyansa suka iyya saka a kashesa, Amma ammar na yawan kwantar masa da hankali ba kad’an ba.

    Ta bangaren safina dai tunda ta farfado a gadon asibiti ta makance bata gani kwata kwata haka magana ma bata iyyawa saboda bakinta daya koma gefe, fuska ya karkace ya murd’u ya wainu wanda likitoti sun tabbatar hawan jinine daya hau lokaci d’aya, daya bugar da ita ta fadin nan, shine ya kaushar mata da fuska, sai dai makantar ne basu gano sila ba, kuma kaf gidan babu wanda ya damu da lamuranta sai dada ita ke jinya amma hatta abie yaji ya tsaneta hakama y’an gidan wanda basu san dalili ba, dada ma daurewa take Amma ba kaunar safinan take ba yanzun.

    Ammar ne zaune a falon gidan su shida kannen sa, abinci yake ci gabaki d’aya hankalin sa nakan TV, yayinda iyayen sa ke hiran batar sumayya da dawowar Al’ameen wanda Ammar ke kawo musu zancen, don iyayen sama sunje har gidan muhammad, suka masa jaje, kaninsa ne kawai baya falon.

    Kwala masa kira yaji kaninsa yayi daga d’aki sai gasa ya fitoh da gudu hannunsa d’auke da waya yana zuwa baiyi magana ba, kawai ya mikawa Ammar wayan.

    Kallon wayan yayi hotunane akayi posted nasu a instagram guda uku, Khadija ce sanye da uniform ita da wani bakin yaro wanda zaiyi sa’ar ta koh ya fita da kad’an shima da uniform in nurse suka d’auki hoto a unguwa mai kyau, sai na biyun tana sanye da uniform in islamilayya nan ma su biyu sai na ukun ita da yaron suna sanye da kayan hausa atamfa da shadda.

    Jikin Ammar na rawa yake tambayar Abdul wanene yaron nan?

    Aboki nane kalamu-wahid, school namu d’aya dashi a abuja naga yayi post kuma naga kamar khadija?

    Ba kama bane Abdul itace, yanzun kasan inda yaron yake takamamme a Abuja?

    Eh na sani yaya don inban manta ba kafun mu dawo hutu yayi ciwo danaje asibiti dubasa na samu an sallamo sa, so yamin kwatancen gidan su naje.

    Waya kawai Ammar ya fitar a Aljuhunsa yana lalubar numban muhammad gabaki d’aya yabi ya gigice.

    *******************
    Kalamu yaji sauki har ya dawo da normal life nasa, a haka sukaci gaba da rayuwa abinsu cikin farin ciki duk da basa rasa kalubalen rayuwa.

    Sumayya ciki ya shiga wata tara duk rashin tausayin mutun inya ganta sayya tausaya mata, cikine yayi kato matuka yayi tsayi ga nauyi don yanzun koh tafiya bata iyyawa sai dai rarrafe abin tausayi bata fita koh ina daga falo sai toilet khadija ke kome wani sa’in kalamu zaizo ya tattara wankin ta ya kai mata dana khadija, wani sa’in har girki yake zuwa ya taya khadija in ayyuka sun mata yawa, sumayya kam yanzun sai a hankali, koh riga bata iyya sawa sai wasu manya manyan vest na gwanjo da zani shine kayanta, sosai laila ke tausaya mata.

    Yau laila da mijinta harda yaranta sunyi tafiya zuwa Adamawa wajen dangin mijinta, bayan isha’i kalamu yazo ya kawowa sumayya balankun nama, amma ta kasa ci saboda ciwon kanda ke damunta, suka sha hira da khadija suna cin nama, bai koma gida ba sai kusan 9 ya ma khadija sallama ya wuce, don zuwa lokacin sumayya ta dade da kwanciya.

    Da misalin karfe 1 na dare sumayya ta farka jin wani irin matsetsen fitsari daya kamata, mikewa tayi zaune a hankali jin fitsari ya cika mata mara, gashi dare ne batason shiga hakkin khadija, yasa ta rarrafawa ta shiga bedroom da rarrafe har cikin bandaki, tsungunawa tayi, tayi fitsari ai tana gamawa taji bayan ta ya kama ga wani irin c…………….

    ✨Ruqeenjalal✨
    🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
    🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯
    ~ Na ~

    🍃 *Rukayya* *Ibrahim* 🍃