Category: A Rubuce Take Book 2

  • A Rubuce Take Book 2 Page 41

    A Rubuce Take Book 2 Page 41

    Part 02

    Page 41

    Saita sake fashewa da kuka,tana jin kamar ranta zai fita,kamar alqiyamarta aka tsayar mata ita kadai.

    “Ikon rabbi sai kallo,wannan wanne irin musiba ce?,saki haka bagtatan?,wannan abu nu hassana yafi qarfina” gwaggwo hassana ta fada tana kama hafsat daketa zamewa tana tumuwa a qasa

    “Kiyi haquri tunda aikin gama ya riga ya gama” amma inaaaaa…..sai hafsat din ta hau zage zage,ta dinga debo ashar tana qundumawa widad

    “Sai naga bayanki,yadda kika hanani zaman lafiya saida kika cisgeni daga gidana wallahi tallahi kema ba zaki sake jin dadin abbas ba…..na rantse kinci bashi bazan qyaleki ba” gwaggwo mero ce ranta yayi mugun baci,ta sanya widad ta koma dakinta abinta ta dubi hafsat

    “Sakin nan dai ba ita tayi miki shi ba,hasalima batasan me ya hadaku ba,kuma zaman gidan aure dama kowa ya iya allonsa ya wanke ne,halinka kuma shike sai daka,indai bazakiyi haquri kija bakinki ki karbi qaddaraki ba har zuwa wayewar gari,to don Allah bamason hayaniya da tashin hankali ki wuce kitafi,mu taron farinciki ne ya hadamu” gwaggwo mero ta fada wadda ta jima dama tana juya maganganun da sukayi da ‘yar uwarta hajiya na qarshe kan yadda take gasa abbas.

    Banda tsoron fita da takeyi da daddaren ba shakka saita yayyabawa gwaggwo mero maganganu,don tana ganin a yanzun ta zama munafuka ne, goyon bayan widad takeyi.

    Ranar wani irin dare mai mugun tsaho da baqinciki hafsat ta gani,ta dinga kuka kamar idanunta zai fado,idan ta tuna wai a yau ta rabu da abbas uban yaranta rabuwa ta har abada?,sai taji kamar mafarki takeyi,lallai namiji qanin ajali ne,namiji tabarmar qashi,namiji bashi da tabbas yau ita ta gani zahiran!!! (To masu karatu kunji fa,nidai nace uhmmmm).

    Ita kanta widad batayi cikakken bacci ba,idan ta kalli su mimi sai tausayinsu ya kamata,ta dinga kiran wayarsa yaqi dagawa,sai daga qarshe ya daga a dake yace da ita

    “Meye kike ta kirana?,idan zaki samu guri ki kwanta saboda baqinki na gobe gwara ki kwanta” kit ya kashe wayar,yasan magana zata masa akan abinda bakin alqalaminsa ya riga ya bushe,a daren yau sakayau ya dinga jin kansa,zuciyarsa tayi wani irin fes kamar an fito masa da ita an wanke,hankalinsa kwance yayi baccinsa,irin baccin ma da shi ya jima baiyi ba.

    Washegari kowa da harkokinsa na bikin suna ya tashi,sai hafsat da jama’arta dake qule a daki,wanda kowa ke mamakin abinda ya hanata tafiya tun sassafe,yadda ta dinga yi a daren jiyan basu zaci hantsi zai daga basu tafi ba.

    Widad na kitchen tana hada ruwan zafi suna magana ita dasu marwa dasu muneera gwaggwo hassana ta shigo,suka hada ido da widad din ta jefa mata Wani munafukin kallo,widad din ta basar ta gaidata a matsayin matar kawun abbas din,ta amsa mata kadaran kadaham,sai tahau neman abinci,sai data gama diban komai sannan tace

    “Mudai wannan bikin sunan ba damu za’ayi ba,dole muje mu raka diyarmu da aka kora……yarinya kin samu duniya,ku dama sadakar yalla wuyarta ku shiga gida,saikun fidda kowa,da biye biyen malamai duk sai kunbi kun ishi kowa”.

    Ran widad ya baci da kalaman gwaggwo hassana,itadai tasan ba wani abu daya taba hadasu ballantana tace,akan hafsat din?,ita meye nata a ciki?,ita tayi sakin?.

    “Gwaggwo ni bansan meye sadakar yalla ba kwata kwata,saboda tsatsona ni balarabiya ce,kuma duk wanda ya kalleni ya kalli ahalina ya sani,malamai kuwa isa ce,kuma na gode da kika shaidamin aikina yayi,zanje na qarawa malamina kudi yaci gaba da aiki kada ya daga qafa”

    Kuka gwaggwo hassana ta saki tana jan salati wai widad tayi mata rashin kunya,duka kitchen din sai akahau kallon kallo,kowa yaqi tanka mata,don duk sunsan itace bata da gaskiya,haka ta fita tana fatar majina tana kaiwa gwaggwo mero qararta,a cewarta yanzu ita daya takejin maganarta.

    Suna tsaka da maganar abbas ya shigo gidan cikin wata danyar gezna fara qal,sai maiqo takeyi,ta fidda zatinsa da kwarjininsa gami da kyansa da wani irin kamala.

    Gwaggo hassanar tana ganinsa sai tayi shuru,ta wuce dakinsu sumi sumi,ya tsugunna yana gaida gwaggwo mero tare da tambayarta me ya faru

    “Fitina ce kawai sukeson ja kafin hafsatu ta fita a gidan nan”

    “Bata tafi ba?,zaman me takeyi?” Ya fada fuskarsa a hade,sai ya miqe ya nufi dakin, gwaggwo mero ce ta dakatar dashi

    “Ka barsu muga iya gudun ruwansu,neman wanda zai tayasu dama sukeyi” .

    Dole ya haqura da shiga dakin,amma ya kasa ya tsare yaqi barin gidan,daga qarshe ya zauna daga bakin gate yana amsa waya.

    Abinda baiyi zato bane ya sameshi,wato qarin matsayin da yaketa addu’ar tabbatuwarsa idan da alkhairi,hadi da tafiya course na watanni shida america.

    Dai dai sanda hafsatu ke fitowa da jakarta fuska qozai qozai ita gwaggwo mero,don gwaggwo fanteka tace ita fa babu inda zata sai an gama suna taci abinda tazo ci,idan sun koma dai tazo gida ta sameta ta sake jajanta mata,bayan sun fita taja tsaki tana gunguni

    “Yarinyar da ba mutuncin kowa take gani ba, zamanta da yaron nan har yai alkhairin da ita qanwar cikinta ya samemu ta sanadinta,ita da ya shekara kusan takwas da ita har ta gama zamanta bamu sameshi ba,yo na meye zan damu kaina?,saina gamacin qwai kaji da nama,ina gani an tirke sa za’a kayar kawai sai na yiwa kaina na tafi rakiyar sakakkiya?,da yake nice maqunshin gishiri”(????,niko nace gaskiyar ki hajiua fanteka,shi mutum mai yawan alkhairi dama maqiyinsa ma wataran masoyinsa yake komawa,Allah kada ka jarrabemu da hannun ‘yan dambe).

    “Alhamdulillah, Alhamdulillah,Allah ya tayaka riqo,kai nayi farinciki,inama ace yar uwata tana raye taga wannan rana da taketa roqa maka ita” gwaggwo mero ta fada zuciyarta a karye,abinda kuma ya shiga kunnen hafsat kenan wanda ya sakata tsananin rudewa,ko ba’a fada ba tasan wani promotion dinne ya samu,dai dai sanda take fita a rayuwarsa?,wannan wacce irin hasara ce ta tafka.

    Ko gwaggwo mero dake ban baki tare da musu fatan sauka lafiya basu kalla ba,suna fita wajen gidan ta damqi hannun gwaggwo mero

    “Na shiga uku mero,ya samu promotion,kuma wallahi babban matsayi ne ya samu wannan karon” ta fada qwalla na zubo mata

    “Eh to dai hakanan zakiyi haquri,duk wani abun rashin haqurinki ne sila,yqnzu gashi kin bar mata gidan kin bar mata mijin,kin bar mata yaran” maganar gwaggwo hassana saita zama kamar kamar wani fami ta yiwa hafsat din,taji kamar itama tana layin maqiyanta ne,amma dole haka ta danne don tana buqatar dan rakiya,bazaiyiwu ta tafi ziqau ba abun sai yayi mata yawa.

    Abinka da ba ‘yan halak ba,isarsu keda wuya laifin yaso ya koma kamar na gwaggwo hassana ne ma,ummanta tana salati tana komai amma tana fadin su gwaggwon basu kyauta mata ba,ta yaya suna wajen zasu bari ya qarasa tsinke ragowar igiyar da tayi saura?.

    Abun duniya ya taru ya ishi gwaggwo hassana,ta kama baki kawai tana kallon qarfin halin umman hafsatun,wato shi dai abun arziqi bai karbi kare ba wato,hakanan matsiyaci ko a tandun mai aka sakashi haka za’a fiddashi qamas,haka ta karkade zaninta ta tashi ta wuce gida cikin takaici,abun arziqin da tasoyi ya koma na tsiya,can kuma ga daula da gagarumin bikin sunan da za’a yi ta yiwa kanta rasa rasa,sai ta yiwa gwaggwo fanteka barka da batayi biyu babu ba.

    ******Kwananta biyu cikin matsanancin hali na kuka da damuwa,har daga qarshe umman nata ta gaji da ji ta zaunar da ita

    “Nifa wannan koke koken naki ya fara isata,wai shin abbas shine autan maza koko ya aka fara?,kinga fa babu ta inda Allah ya rageki in gaya miki,kin samu a jikinsa kin tara abinda kika tara,ki gama iddarki ki gyagije ki fara zawarci me lasisi,wallahi da gudu zaki samu manema,ai sai wani ya yar wani yake dauka,abu daya zaki.masa ki rama,kema da zarar kin gama iddarki ki rattaba aurenki kawai,shine qarshen baqincikin da zaki cusa masa,yara kuma ya baki abinki,ta nan ma kadai zamu sake samun wasu kudin shigar”.

    Da wannan shawarar suka dinga shige da fice saida aka saka baki aka bata su mimi,kallonsu kawai yakeyi,yasan manufarsu,don haka dukkan abinda ya tashi bayarwa na amfanin yaran qeqe da qeqe yayi musu,na watanni uku cas ba qari babu dadi,haka umman da hafsat din sukayita zaginsa sunayi dashi a gaban yaran,mimi da nawwara saidai su bata rai,babu damar yin magana,don tun randa nawwara tayi magana da yake ta danfi mimi tsiwa uwar ta gwabje mata baki basu sake cewa komai ba,saidai suyita bata fuska,takaici da baqinciki ya ishi hafsa,don ko widad aka zaga a gabansu sai fuskarsu ta canza

    “Shegu an goga musu baqin hali” haka hafsat din ke fada.

    Watanni uku aka bawa abbas din kafin tafiyar da zaiyi america, office zasu gama masa dukkan shirye shiryen tafiyar,sun bashi damar tafiya da mata daya da yara uku zasu dauki nauyinsu,idan yana buqatar qarawa kuma wannan saidai yayi a aljihunsa.

    Hankali kwance cikin wata irin nutsuwa yake dukka shirinsa,yanason tafiya da widad amma baisan ya zata kasance ba,saidai yana mata shirin ba tare data sani ba incase koda zai buqaci hakan,don bayajin zai iya nesa da ita na wadan nan watannin.

    Gefe guda kuwa widad din ta gaya ma kanta aikine sosai ya sameta,idan a baya su biyu ne yanzun ita daya ce dashi,uwa uba kuma riqe namijin da a baya yake da mata biyu yanzu ke daya ce dole saikin zage damtse kin ninka shirinki,duk da hafsat din akwai ya babu ce,amma dai duk tsiya macace itama.

    Ta tsaya ta gyara kanta da kyau,ciki da waje ta fara canzawa tana komawa yarinyarta danya shakaf,ta sake shiga classes kala kala da groups groups ‘yan gaske na manyan matan da suka fita gogewa a komai, groups na hajiyoyi masu mutunci da tarbiyya da ake mugun qaruwa,ta shiga ne ta sanadiyyar su anty fanna da a yanzu suka zame mata madubi kuma makaranta,gefe guda kuma ga su anty madeena da anty deena da sauran yayyenta da kowannensu yanzu zaman lafiya sukeyi sosai,dama can widad din akwai sauqin kai da bin na gaba da ita koda tazarar shekarunku babu yawa,to har kawo aure bai canzata ba,saima sake riqe yayyenta da kyau datayi.

    Ga mummynta itama da bata jin kunyar yi mata bayanin komai,widad din kawai gareta diya mace,sauran dukka maza ne,don haka ta sake zage damtse tana gyare yarta tsaf,kama daga tarbiyyar jiki data zamantakewarta da mijinta.

    Cikin lokaci kadan ta sake gigita abbas din,idan sun zauna bashi da zance sai yace

    “Kina haihuwa kina sake zama mace,kina kuma sake dada wayo,kina kuma mallakeni wuudd” dariya yake bata

    “Allah ka daina fadan mallakar nan,banason jinta,kada wataran kayi subutar baki a dauka da gaske mallakar nayi maka”.

    Murmushi kawai yake binta dashi,ta shiga kowanne lungu da saqo na rayuwarsa ta tsaye masa cakkk,yasha rayawa a ransa zama da hafsat da rabon haihuwar su mimi ne qaddararsa,bansa haka,inda ace widad din ya fara samu babu abinda zai sanyashi sake wani aure anan dai gidan duniya,saidai hurul’een na aljanna.

    Wata biyu kacal ta gama gyaran kanta,idan ka ganta ita da yaranta ko ke mace saita baki sha’awa ta burgeki,yaran su dukka ukun affan da sajid da sajjad (twince dinta)dukansu masu kyau ma sha Allah,sun debo kyau wani daga na widad wani daga na abbas,sai kyansu ya zama wani kala daban me ban sha’awa,bul bul dasu dukansu,idan ka gansu su ukun ba zakace ita ta haifa yara ukun nan ba(daya daga cikin sirrin auren wuri kenan,zaki tara yaranki tunda quruciyarki,baki san dadin jikinki ba,sanda zaki gama haihuwa da sauran qarfinki,sai ayita mamakin wadannan duka yaranki ne,ayita sha’awarku,Allah ya bamu haihuwa me albarka,ya albarkaci wadanda muke dasu).

    Sai da suka cika cika watanni uku sannan sukayi shirin shiga garin bauchi,suka shirya tsaf da tsarabar da widad din tayi da kudinta,ita da yaran da aminatu da fahad wanda a yanzun yake tare dasu,sun fara gaba ne,abbas din yace washegari zai biyosu,akwai wani case da zai rufe ne a ranar.

    Zuwa tayi ta tarar an yiwa gidanta sabon gyara,wancan gidan nasu kuma da hafsat ta kwashe kayanta duka anata masa aiki,an canza masa fasali da tsari gaba daya,wani irin gini ake masa na tashin kai.

    Washegari da azahar ya iso, yaran duka suna wajen aminatu ita kuma tana wajen mai gayya mai aiki tana kula dashi,sai da yayi wanka yaci ya qoshi sannan yace mata su shirya suje suyi gaishe gaishe,ta shirya yaran duk da dama ko yaushe tsaf suke,suka fita gaba daya a sabuwar dalleliyar motarsa daya canza,ita kuma yabar mata waccar.

    Sun zaga dangi sosai,widad kuma tasha sanya albarka sosai ita da yaranta,bayan sun taho hanya abbas ya kalleta

    “Waini hajjaju,jarin naki duka kike kwashewa kike kyauta dasu?” Murmushi tayi masa tana narkar da wuyanta,ta masa wani kallo na qasan ido

    “To yallabai ko me zan basu ai ban fadi ba,danginka ne fa?,abun tutiya wa yarana,kuma ka manta ribar da na samu a wannan shekarar?,ko ka manta ina shirin bude shago?”

    “Tuba nake,na manta fa da hajjajun gaske nake magana ba da jabun ba” sai suka saka dariya a tare tana dora kanta a kafadarsa bayan ta kaiwa bayan hannunsa duka.

    “Mu samu wani eatery din muci abinci,banason mu koma gida kice zaki shiga kitchen din nan girki,nidai yau na sauke miki”

    “Godiya nake” ya fada tana hade hannayenta guri guda,ya sakar mata murmushi,yasan duk da yayi hakan tabbas saifa ta shiga kitchen ba fashi,ko Black tea saita dafa masa hankalinta zai kwanta,dun rintsi duk tsanani bata taba bari rana ta fito ta fadi baici komai daga hannunta ba.

    Gaba daya ta tattara hankalinta akan baqin mutumin da za’a iya kiransa matashi,don bai qarasa shekarun abbas ba,aqalla abbas din yana iya bashi shekara biyar,tun wancan sati biyun da ta kammala idda ya fara zuwa wajenta,amma tun lokacin taji sam baiyi mata ba,a tsukin maza kusan uku sunzo mata,amma duk wanda ta daga kai ta kalla sai taga baikai mata zatin abbas ba,tana da buri…..tanason bawa mara da kunya,tanason tayi auren huce takaici,tanason tayi auren da za’a san bataci baya ba,zatayi auren da abbas zai ciji yatsa,widad kuma tasan cewa tayi mata nisa,ta kuma yi mata tazara da ratar da bazata taba iya kamota ba.

    [26/05, 2:43 pm] +234 903 583 2936: *H U G U M A*
    *Arewabooks:Huguma*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • A Rubuce Take Book 2 Page 40

    A Rubuce Take Book 2 Page 40

    Part 02

    Page 40

    Jikinta yana rawa ta lalubi layin muneera don jin me widad ta haifa

    “innalillahi,na shiga uku” shine abinda hafsat ta samu kanta da fada bayan muneera ta tabbatar mata twins ta haifa kuma dukka maza,ta dinga safa da marwa cikin falonta kamar wata zautacciya,kamar kuma wadda ciwon naquda ya sameta,kuka takeyi wurjanjan,tana tsinewa widad a zuciyarta,yarinyar ta gama cutarta,cuta tahar abada,ta gama da rayuwarta gaba daya,haihuwa?,haihuwa tayi?,haihuwar kuma ta yara maza ma?,sai yaushe zata iya ruguza dukkan wannan ginin da widad tayi?,yaushe haqarta zai cimma ruwa?,rayuwa na qara tafiya,tana saqa widad din tana warware mata tana dawo da komai baya,ta gaji da wannan jiran gawon shanun,sai ta kira habiba ta fashe mata da kuka me cin rai ta fara gaya mata.

    Ajiyar zuciya ta sauke

    “Abinda nakeso dake kiyi haquri kawai,ko kowa ya kasa yi miki komai boka bagwaare ina mai imanin zai miki komai(wa’iyazubillah),saura wata daya kacal aikinka ya kammala,wallahi kinji na rantse miki,ko hajiya dake kabari inda zata dawo duniya tace masa yayi kaza wallahi wallahi naki zai dauka,kudade kika kashe bana wasa ba kin manta?, fiye da rabin jarinki kika bayar,ta yaya zan bari asara ta hauki?” Bayanan habiba sun sanyaya mata rai qwarai sun bata kuma qwarin gwiwa

    “Kedai abinda nakeso dake,kici gaba da lallabawa,ki sake ayi komai dake,yadda kome zaizo zaizo da sauqi”

    “Anya zan iya kuwa habiba?, zuciyata bata da wannan qwarin gwiwar”

    “Ke matsalata dake kenan, kwata kwata baki iya cinye jarabarki ba,wannan karon kuwa dole kiyi haka ko don amfanin kanki”

    “Zan jarraba in sha Allah”.

    Wunin ranar haka ya yishi babu wata walwala ko jin dadi,ranta a mugun quntace,a zuciyarta tanata fatan taji wani mummunan abu ya samu yaran kowa ya huta,duk bayan mintuna saita tsine musu su da uwarsu,amma cikin ikon Allah lafiya sumul widad ita da jariranta.

    Wannan karon ummu ce ta kashe kunya da kanta ta yiwo tattaki katsina,gidan widad din sai ya kasance kullum cikin jama’a yake abokan aikin abbas na nan katsinan,gashi kuma a gida take,garin ummanta,dangi tako ina barkowa suke barka ,haka daga kanon ma,wasu na zuwa barka,wasu kuma sai ranar suna sannan zasu iso,yara dai sunyo goshi sosai kamar affan,kowa yasan yadda twins suke da farinjini daman,widad din taga gata tako ina.

    Ko yaushe suna waya da abbas din da yakejin kamar yayi tsuntsuwa ya dawo,an katse masa hanzarinsa sosai,don bai gama kallon yaransa,iya kallo guda dayan da yayi musu qaunarsu sosai yakeji cikin rayuwarsa da ruhinsa.

    Komai ya sakar musu dai dai bakin samunsa,don yanzu babu abinda zaice da Allah sai godiya,hatta da hafsat da yara bai barta ba,sai daya gwangwajesu da dinkunan fitar suna na alfarma har kala uku,ta kalli kayan taja mugun tsaki ta nadesu a waje daya,wannan karon kam koda ba’a ce mata ba tabbas zataje suna,zataje kallon sunan widad na qarshe a gidan abbas din,zata je kuma ko don ta sake ganin yadda zata qara sawa bokanta ya qara tsanantawa da aikinsa.

    _batasan tuni qaddara tayi mata nata tanadin ba,tanadin da tabbas da tana da masaniya a kansa……da babu abinda zai kaita garin katsina_

    _hukuncin Allah,da kaf dube duben bokayen nata basu iso suka gano shi ba,hukuncin Allah TALALA mai kamar sake,lallai qaddarar kowanne nawa A RUBUCE TAKE_

    Ana ya gobe suna gidan widad din ya qara cika sosai da jama’a,ba laifi gidan yana da nashi girman,don haka kowa ya samu masauki da wajen zama,duk da dakuna biyu ne,nata dana baqi wanda aminatu ke ciki don na abbas a rufe yake,sai wasu dakunan guda biyu da toilet ta baya.

    A ranar widad ta gama komai,gyaran kai kawai ya rage mata,tayi wani mugun kyau na fitar hankali saboda yadda jegon ya fara karbarta tun a sannan,da safiyar ranar sukayi waya da abbas din yace ta bari sai azahar taje gyaran gashin,abun mamaki zuwa azahar din taji wayarsa,yace ta fito qofar gida ya miqata.

    Na’eema da marwa ta dauka, kowacce ta dauki baby daya suka fito,tayi kyau cikin maroon din abaya, fuskarta tamkar madubi.

    Tunda ta fito ya zuba mata ido yana kallonta ta madubi,ya lunshe ido sannan ya bude,yana tuna muryarta lokacin da take naquda,addu’o’i da salati kadai ke fita a bakinta cikin wani hali,ya sake gasgata lallai haihuwa ba wasa bace,duk dan a baibi uwarsa ba ba shakka ya tabe,hakanan duk namijin da bai girmama matarsa ba kodon darajar yaransu lallai ya cika abun zargi.

    Buda motar tayi ta shigo,suka hada ido ta saki murmushi

    “Amma fa ka shammaceni,shine baka gayamin zaka dawo yau ba?”

    “Bakiji dadi ba da kika ganni kenan?” Shagwabe masa tayi

    “Sosai ma uncle, Surprise fa kayimin”

    “Good me jego” a ladabce ta gaidashi,sannan suka gaisa dasu marwa da suka zama ‘yammata suma,ya tayar da motar yana tambayarta

    “To yaya?,meye labari?, Ya akaji da jama’a yan suna?,hope komai dai lafiya ko?”.

    Qasa qasa suke hirarsu cike da wani irin kulawa da juna,kosu marwa dake baya basajin me suke fada kamar masu rada,abinda yayi matuqat burgesu ya kuma tafi dasu,don basu taba ganin irin wannan soyayyar tsakanin miji da mata ba,sunfi ganinta ga saurayi da budurwa,amma yau anty widad da uncle abbas din sun karya musu record.

    A saloon din ya ajjiyeta sannan yace

    “Zanje na karbo dinkina gaba da nan,idan na tashi dawowa sai na daukeku mu wuce”

    “Tom,godiya nake sosai,Allah ya qara girma” ta fada tana dunqule hannu cikin salon jinjina da kuma rusunawa, murmushi ya balle masa,tana bala’in respect dinsa,ko meye zai hadasu bata kasa ganin wannan girman nasa.

    Yana ci gaba da tuqi yana murmushi,halaye da dabi’un widad din yaketa tariyowa,tun daga aurensu kawo yau,tana da sauqin kai da dadin mu’amala over,bata da fushi ko tsaurara abu indai ba bango taje ba.

    Ya isa ya samu tailor din ya masa halinsu,don a sannan yake qarashe hade dinkin,yana ganinsa ya rude

    “Sir…..ayimin afuwa yallabai,tuba nake” sai ya jawo stool ya bashi

    “Yanzun nan za’a kammala sir” bai zauna ba,yadai harde hannayensa a qirji yana dubansa

    “Kome zakayi ka dinga qoqarin cika alqawari,shine cikar kamalar mutum,sannan sana’arka,duk yadda ka riqeta haka take zamar maka”

    “In sha Allah sir” yaci gaba da qoqarin hada masa kayan

    “Ka zauna mana sir” ya sake masa tayin zama

    “Karka damu,qarasa aikinka” ya fada a nutse,don shi bayajin tsaiwa duba da yanayin aikinsa.

    Wayarsa ce dake aljihun trouser dinsa ta dauki ruri,ya saka hannu a hankali yana qoqarin cirota,yana duba me kiran kiran ya katse,saiya fara qoqarin kira sai gashi an sake kiransa.

    Hafsat ce,ya daga wayar a nutse ya kara a kunnensa

    “Kana ta wajen ina?,gamu a park kazo ka daukemu” ta fadi kanta tsaye cikin son nunawa wadanda take tare dasu lallai har yanzu itace da gwamnati,fiye da rabinsu jama’ar widad ne ta fahimci haka ta yadda suketa hirarta da fadan alkhairinta tun a mota,hakan ya sake hassala zuciyarta da wani mugun bacin rai.

    Cikin mamaki yace

    “Me ya biyo dake titi bayan na tura kudin ticket a siya muku keda yara,yanzun haka fahad inajin yana airport yana jiran saukarkuya dauko ku” baki ta tura gaba hadi da tura dankwalinta ma,haka kawai ga mota tana gani sai ta bari ayi asarar kudin a wani siya musu ticket,kudi ba dubu biyar ba ba goma ba

    “Kawai haka nafiso,na karba kudin ticket din nayi saving mayi wani abun dashi” yadda take masa magana a tsaitsaye yadan bashi mamaki,don tunda tayi kome ta danyi laushi

    “Okay,to yanzu haka ina cikin wani uzuri,ki kira fahad din ki kwatanta masa inda kuke sai ya daukoku” daga haka ya datse wayarsa shima.

    Sai yaushe zata bar son kudi?,yaushe zai saka doka ta daina karya masa kanta tsaye?.

    Sakato tayi da wayar a hannu,ranta yana mugun baci,batakai yabar duk abinda yakeyi ba kenan saboda ita yazo ya daukesu?,cikin wannan bacin ran ta kira fahad ta gaya masa inda suke din,wanda saboda dan nisan dake tsakanin airport din da station din sai daya dan dauki lokaci,sauran wadanda basuga amfanin abinda tayi din ba sukace tunda ba abun hawa na haya available na zasu tsaya wani jira ba sai kawai suka dauki taxi drop suka wuce suka barta ita da su baaba hassana ‘yan kanzaginta,sai da suka jima da wucewa sannan fahad ya iso,tayita masa bala’i amma yayi biris da ita bai kulata ba tunda ya riga yasan hali.

    Sai da aka gama hada masa dinkin sannan ya dawo ya dauki su widad,tuntuni an gama suna zaman jiransa ne ma

    “Ba komai,tunda dai ya gama alhmdlh” abinda tace dashi kenan sanda yake bata labarin abinda ya tsaidashi,shi kansa baiji dadi ba,don shima yana da baqi daga wasu garuruwan da sukazo masa saboda yana sanya ran zaiyi walima a goben kamar yadda ya saba kowacce haihuwa,haihuwar affan ce kawai bai samu yayi ba.

    Tunda suka isa gidan tana farfajiyar gidan a zaune ta kasa shiga ciki,kowa saidai yazo ya wuceta,tun a sannan hidimar da akeyi da yadda taga gidan ya fara tara jama’a ya tsaya mata a rai,kowa yana ciki yana huce gajiya harda su mimi,amma baqin kishi ya hanata sakat.

    Sanda motar abbas din ta shigo harabar gidan idanunta akai,baqin glass ne,bata lura da waye da waye a wajen a ciki ba sai da suka bude,su marwa suka fara fitowa sabe da yaran dake cikin wani lallausan blue din abun daukan yaran suka nufi cikin gidan,ta qurawa motar ido tanason ganin wadda zata fito,sai bayan kusan minti uku sannan widad din ta fito tana murmushi,da alama wata maganar sukayi da abbas din data bata dariya.

    “Kan abu ta kazar uba” hafsat ta fada cikin ranta,zuciya tayi mugun dibarta,batasan sanda ta isa gaban motar ba side din da abbas din ke zaune cikin wani mugun fushi

    “Ai dama odan bakayi haka ba ba kaine abbas ba,idan bakayi haka kai din ba namiji bane,dan kunama…..tabarmar qashi RIGAR K’AYA” ta da cikin madaukakin sautin da yaja hankalin mutanen cikin gida da sauran na farfajiyar wajen,ganin yadda hankula ke dawowa kansu bai saka ta fasa magana ba

    “Ni dana taho daga wata uwa duniya ka zubeni a station ka kasa zuwa daukata,amma ka dauki ‘yar gwal da danyen jego a gaban mota kana yawo da ita,kabi ka tattare a gindinta ita da danginta,kana musu wahala kana musu bauta……wallahi sai Allah yayi mana hisabi ni da…….”.

    Tsawar daya daka mata ta yanke sauran maganar,yayi wata irin fitowa daga cikin motar,Allah ya kissimawa widad ba za’a kwasheta da kyau ba,cikin gaggawa ta shiga tsakani ta dora hannayenta kan qirjinsa tanason yaja baya,ta tabbatar gamuwarsu da hafsat din ba zata taba kyau ba,batason kuma zuciyar nan data taso masa ta sanya ya biye mata ga mutane a wajen.

    ‘yan uwan abbas dake kusa ne suketa yima hafsat fada suna janyeta,ana tsaka da haka kiran dan auta a dakinsu baban abbas din ya shigo yana shaida masa sun bata kwatancen masaukinsu,sai ya kashe wayar yana huci ya juya ya koma cikin motar ya figeta ya fice daga gidan.

    Iska me zafi widad ta furzar,tabi hafsat da kallo wadda aka janyeta can bayan gidan

    “Barin hali sai mutuwa”ta fada tana mamakin halin halin tantagaryar hauka irin na hafsat din.

    Ranar gaba daya a birkice hafsat din ta yini,donma ‘yan kanzaginta suna dannarta,da qyar takai ga shigowa falon,saidai gaba daya a hargitse take.

    A yanzun widad din tafi qarfin raini,kuma tafi qarfin ta keta idanunta ta gaya mata maganar banza,uwa uba kuma tana tsakiyar danginta da hafsat din bataga alamun daukan raini ko wargi daga wajensu ba,haka ta yini har dare a falon tana qunsar takaici,saidai idan abun ya qume mata da yawa ta fita ta matse hawaye ta dawo.

    Har tayi shirin kwanciya abbas din ya shigo,har yanzu fuskarsa babu walwala,ta kalleshi cikin langabar da kai a shagwabe tace

    “Angon qarni babu fara’a, gaskiya ba kanta,abunma ko kyau baiyi maka ba” dole ta sakashi dariya,sannan ta gyara zamanta

    “Kaci gaba da haquri uncle don Allah”

    “Wanne haqurin?,haqurina ai ya gama qarewa……akwai abinda kuke buqata?,zan tafi masauki wajen baqi na” kai ta girgiza,don babu ce kawai basu da ita,ya tsugunna yayi kissing yaransa duka,harsu mimi da tasa aka debo mata suka kwanta gaba daya su bakwai kenan harda ita,da yake gadon babba ne ba wanda ya matsi wani.

    Har ya fita tana juya abun a ranta, zuciyarta duka ba dadi,batason bacin ran nan nasa,fatanta ko yaushe mummyn mimi ta gyara halinta ko zai samu nutsuwa.

    Dakin da su gwaggwo mero suka sauka ya leqa don ya musu sallama,baima san hafsat din tana cikinsu ba sai daya shiga,ya gama yi musu sallama ya miqe ya fice,sai hafsat din tayi zumbur ta dauki jakarta ta biyo bayansa.

    A tsakiyar falon ta cimmasa,tana riqe da qugunta,zuciya kuma na ingizata tace

    “Muje masaukin tare,acan nima zan kwana” wani banzan kallo ya watsa mata,yaja mata tsaki yayi gaba,saita sha gabansa cikin kuka

    “Wallahi na gaji da wanna wulaqancin da kakemin,kamar nima ba matarka bace,yau saidai duk abinda zaka yimin ka yimin,na gaji da wannan rashin adalcin” sosai zuciya ya ciyoshi,ya finciki jakar hannunta yayi wurgi da ita sai gata a bakin qofa

    “Na fiki gajiya,na gaji dake gaba dayanki,kije na sakeki saki daya,badai shikenan ba?” Wutace ta kawo mata ta kuma dauke mata a take,saita aza hannu aka ta kurma wata uwar kururuwa data zama tamkar shele ga dukkan wani me rai da yake gidan,shelar tata kuwa ta iske kowa,take falon ya fara karbar jama’a dake cikin gidan banda na harabar gidan da kunnuwansu baije wajen ba,a lokacin abbas ya jima da ficewa daga gidan yana jin kamar an zare masa qaya.

    Faduwa tayi tahau tirje tirje a wajen, gwaggwo hassana ce ta riqeta tana kiran sunan Allah kafin sauran su tayata riqe hafsat,tanata abu kamar wadda ke shirin hawa bori ko kuma tayar da iskoki

    “Ku cikani,ai kuna gani,a gabanku ya sakeni,saki uku kenan yayimin,saki uku kenan fa”.
    *H U G U M A*
    *Arewabooks:Huguma*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • A Rubuce Take Book 2 Page 42

    A Rubuce Take Book 2 Page 42

    Part 02

    Page 42

    Matashin ya sake gyara zamansa yana gyaran murya

    “Sunana AVM mu’awiya mani adam” da hanzari hafsat ta daga kai tana dubansa

    “AVM kuma?,air vice marshall kenan fa?,dama babban mutum ne shi din haka me muqami yaketa binta tana wulaqanta shi?,wato Allah yayi tana da rabo,da tayi wasa da damarta,saita gyara zama tana sakin masa fuska sosai harda murmushi

    “Ayyah,afwa yallabai,inata bata maka lokaci ko?,kasan komai sai Allah yayi” shima murmushin ya saki,da alama tarkon da ya dana yayi kamu

    “Ba komai,yau ai gashi zamu tattauna sosai” sakewa yayi yana bayyana mata waye shi da irin abinda yake dashi,cikin mintunan da basu gaza talatin ba taji ta gamsu ta kuma amince dashi,kuma lallai ta samu mijin auren da take fata wanda yafi abbas matsayi da dukiya,saidai ya nuna masa kyau,take ta bashi damar turo magabatansa,sukayi dan ciye ciye suka kuma sake tattaunawa,ganin shima din mawadaci ne sai bata boye masa komai ba ta gaya masa irin business din da takeyi,da kuma abinda ta mallaka yanzu haka,don ma tanata fama da ummanta dakeson ta hau kan kudin a dinga murqushewa,banda ta bade idanunta da toka zuwa yanzu Allah ne kadai yasan nawa za’a rugurguza,bayan kudaden abincinsu mimi da ake kawowa suke kashe mu raba,shi yasa taji ta matsu tayi aurenta ta samu inda zata sauke dawainiyarta ta daina facaka da kudinta.

    Sosai take kashewa kanta kudi,ita ala dole bataso aga ta canza bare ayi tunanin baqincikin barin gidan abbas ne yake damunta,idan tayi aure kuwa tunda ta samu mai farcen susa,zata tsula tsiyarta yadda taga dama,sai tasa widad taji ta muzanta.

    Ya jima wajen masu biyan kudi sannan ya qaraso wajen motarsa yana mita

    “Sai suce su basuson Dollar dole saida naira za’a biyasu,bayan ribarsu ne idan aka basu dollar din”.

    Kanta ya sake fashewa ta saki murmushi

    “Rashin wayewa ne kawai yake damunsu”

    “Wallahi kuwa,duk da haka saida suka riqe canji na wajen 5k” kamar ta juya taje ta karbo,amma sai taga kamar ajinta zai zuba,haka ta kanne sukaci gaba da tafiya.

    Tana tsaye tana jiran ya bude mata ta ciki motarsu abbas ta faka daga gefansu,tunda motar ta tsaya hankalinta ya dauku a kanta,don ba qaramin burgeta motar tayi baba jimawa ya bude ya fito cikin wani lallausan yadi da aka yiwa dinkin zamani.

    Mummunar faduwa gabanta yayi,abbas din ya canza yayi mugun fresh,ga qiba mai kyau daya hada,fatarsa ta qara haske,gaba daya qamshinsa ya cika wajen.

    Sanda madam widad kuma ta fito cikin wani fitinannen dinkin bubu sai yawun bakinta ya ida qafewa,abbas din ya sunkuya ya karbi sajjad daga hannunta,sajid yana wajen aminatu shida affan,sannan ya karba hand bag dinta ya riqe suka jera zuwa ciki.

    “Ina zuwa” tace da AVM mu’awiya tana komawa ciki da sauri saurinta kamar wadda tayi mantuwa,so take ta tabbatar da abinda idanunta ke gane mata,widad dince ta koma kamar wata basarakiya a fadar masarautun larabawa.

    Can ta gansu suna magana da receptionist din,tana dan jifan abbas din da harara,gurin zaben abinci ne,sun saba kuma irin haka,akwai saboda da fahimtar juna sosai tsakaninsu da ma’aikatan wajen,wani abu ya tsaye nata a wuya, tsabar hassada da baqinciki ya rufe mata ido,ta nufi gurin dason nuna musu itama cikin wadata take,kuma tare take da mijin zata aura

    “Hello” ta fada tana wani yatsina,tunda abbas ya waiwaya sau daya ya kalleta bai qara ba,a yadda yayi zaka tsammaci ranar farko ne daya taba ganin halitta me kama da ita,kuma basu da wata alaqa ko kusa ko alama,sai ya dauke kansa yanaci gaba da miqa musu atm dinsa kan su cira kudin

    “Takeaway zaku hada mana kawai,basai mun zauna ci a nan ba” abbas ya fada yana duban ma’aikacin,widad da ta yiwa hafsat din kallo biyu cike da mamakin yadda ta tsomale kamar dattijuwar kaza ta maida dubanta ga abbas tana mamaki,yace anan zasuci amma yanzu ya canza,batadai ce komai ba,dukkansu sukayi shuru sai.muryar hafsat daketa qoqarin mata kwaskwarima,ita ala dole ga ajebo.

    “Nice wadda muka zauna a wancan table din ni da AVM mu’awiya”

    “AVM mu’awiya kuma?” Ma’aikacin ya tambayeta cikin mamaki

    “Yes…..mijina da zan aura,akwai sauran 5k canjinsa dake wajenku…..idan ba damuwa zaku iya riqewa” junansu suka kalla cikin mamaki,saboda sudai sunsan indai wanda take magana akai ne da qyar ya cike musu balance dinsu ma,daya daga cikinsu ne ya girgiza kai

    “Aah,muba wanda muke riqewa canji,saidai idan bai fada miki dai dai ba,ko bakiji dai dai ba” fuska ta bata ganin suna niyyar yarfata

    “Me kake fada?,ya anyi muku alkhairi zaku saka ma mutane da sharri?”

    “hajiya wai me kike fada?,mufa ba wani canji a wajenmu,kije ki sake tambayarsa dai”

    “Okay,indai kuka sakani zuwa na dawo zaku gane kurenku,zaku gane da matar waye kuke musu” ta fada tana murza hannu,saita juya tayi hanyar fita tana taku dai dai,tanason murza power dinga a gabansu ko don yau ta hanasu barci.

    Jajantawa suke a tsakaninsu na abinda tayin,abbas dake tsaye yana jinsu yace

    “Inajin bata da hankali,ko damuwa ce tayi mata yawa” ya fada da salon shaqiyanci dariya tana cinsa yana dannewa,dubansa widad tayi da sauri ta galla masa harara

    “Hafsat dince bata da hankali?”

    “Oh…..wai dama kinsanta ne?” Yayi tambayar yana dubanta gami da dage dukka girarsa sama,sakato tayi tana kallon abbas din,sai kuma ta girgiza kai kawai,dai dai sanda suka juya suna barin wajen zuwa inda su aminatu ke zaman jiransu

    “Dama ai dole kace baka santa ba,kana kishi” wata dariya ce ta qwace masa sosai,ya dinga dariya yana duban widad din,bai tsagaita ba har suka shiga mota ya tayar da ita sannan yace

    “Bakisan tausayin wanda zai dauketa nakeyi ba?,niko a lahira horon da za’a yimin shine na sake zama da ita inuwa daya bare nan gidan duniya?,sam,haihata haihata,idan taso ta auri sarkin makka ma,ina mata murna,amma nikam abbas turaki har abada,ni kadai nasan me naji me na gani” shuru tayi tana girgiza kai cikin mamaki,wato mace na iya fidda kanta fit daga zuciyar namiji kenan,kamar yadda take iya kafa kanta kwatankwacin yadda ita tayi

    “Su mimi ne a raina,banajin zan iya ci gaba da bar musu yarana gaskiya,kullum haqurina sake qarewa yakeyi a kansu”

    “Yaushe zamuje ganinsu?”

    “Gobe……in sha Allah”

    “Yayi,Allah ya nuna mana” ta fada itama can qasan ranta da damuwa,Allah ya sani tana son yaran sosai,bataqi kuma a dawo dasu a mallaka mata su ba.

    Daren ranar kasa bacci gaba daya hafsat tayi,ta dinga zarya tana hango abbas da widad a idanunta,happy family,me zatayi wanda zai bata wannan jin dadin nasu?,bata samu hutu ba saida zuciyarta ta yanke mata abinda zata aikata musu,ta san yadda mata suka tsani riqo,musamman ma riqon dan kishiya,ba abinda zata cusgunawa widad din dashi saidai takai mata yaran,ta qara mata yawan aiki ta hanata hutu,wannan kuma tasan zaiyita hadata fada da abbas din,shikenan hankalinta ya kwanta.

    Da wannan shawarar ta kwanta, washegari kuwa tunda safe ta soma hada musu kayansu,har sun sanya uniform tace su cire,ummansu nata fada da mita

    “Dan hanyar samun alkhairin zaki toshe mana?”

    “Nifa aure zanyi umma,don haka yaci gaba da riqe yaransa,babu me masa wahala,yanacan yana holewa da matarsa mu ya barmu da raino” hakanan badon umman taso ba ta tasasu a gaba,ta sakasu a napep sai gidan abbas din kanta tsaye.

    Kusan kowacce safiya zaka samu gidan neat dashi,bama gidansu na katsina ba har na nan din,saboda basa kwanciya dama abar gidan da datti,har aminatu ta saba,ya zame mata jiki,duk inda takwas tayi ta gama komai,ta yi wanka ta yiwa affan din kansa wanka,saidai suyi wani abun daban kuma,kosu sake kwanciya bayan sunci abinci,ko suyi game na alphabet din arabic ko na english da dai sauran abubuwa masu amfani.

    Tsaye tayi a tsakiyar falon tana qare masa kallo,an tsara komai na falon daki daki bisa sha’awa da burgewa,hakanan ya samu cikakkiyar tsafta da kulawa,ba abinda yake fitarwa sai wani irin sassanyan qamshi da ya hade da sanyin ac din dake Parlor din.

    Muryarta ta ware cikin baqinciki ta kwarara sallama,aminatu dake daki ta jiyota,ta miqe ta fito tana riqe da hannu affan,hannunta daya kuma dauke da sajjad dake cikin wasu fafaren overall,ya cikata fam ma sha Allah,idan ka kalli yaran ba zakace twins bane ba.

    Tsaiwa tayi tana kallon hafsat din cike da mamakin ganinta a gidan,saita kalleta da harara harara

    “Ina mutan gidan?”

    “Antyn tana wajen daddynsu…..”

    “Na sani,dalla malama kiramin shi mai gidan” ido aminatu ta fiddo,tunda take dasu bata taba buga musu qofa ba ai,ba zata iya ba,barema dokar widad dince,indai ba wani babban abu bane ya faru basa kiranta idan tana tare da daddyn

    “Ba’a kiranta idan tana wajen daddy,kiyi haquri ki zauna ki jirasu,bari na kawo miki ruwa” ta fada cikin nutsuwa irin ta yarinyar tana sakin hannun affan,wanda mimi tayi caraf ta kamoshi

    “Qani…..ka manta ni ko?,ya naga kana kumatu,muji ko bread ka boye” ta fada tana dariya gami da fara lallatsa masa kumatun,yaron bashi da saurin mantuwa,ya tunata sarai,sai kuwa yahau bagala mata dariya,dukkansu sai suka matso kuwa,abinda ya qarawa hafsat takaici ganin yadda suka yanyame yaron dukansu cike da qauna suna masa wasa,ta daka musu tsawa,duk sai suka koma suka lafe.

    Sosai aminatu ta cika plate da kayan kaiwa baka ta ajjiye gaban hafsat dake tsaye,tabi kayan da kallo,rai naso amma kuma zuciyar ta hana,baqinciki qyashi da kishi mara amfani ya rufe mata ido,taso ta basar amma ta kasa,saita faki ido ta dauki lemo ta jefa a jaka,ta dan rarraba ido taga hankalinsu bai kanta,ta sake zarar wani abun ta jefa,tana kan jefa na uku ne qofar bedroom din abbas ya bude suka fito shi da ita,sai tayi sauri ta saki abunda ta dauka,saidai tuni sun gani,amma sai sukayi kamar basu gani ba.

    Riqe suke da hannun juna,perfect match couples da kowa ya kallesu sai sun bashi sha’awa,sanye take da wata rigar wani material da aka yiwa wani kyakkyawan dinki da ya zauna mata sosai a jiki,kanta ba dankwali sai sassalkan baqin gashinta me yauqi wanda kullum bata gajiya da gyaransa da yi masa style kala kala harda nasu bead,yau matseshi tayi cikin band ta kuma yiwa jelar kitso guda daya ta barshi yana yawo a bayanta,jikinta ba abinda yake sai fidda sassanyan qamshin turarukan jiki dana hayaqi data tsuma kanta dasu.

    Shima abbas din shirye yake tsaf cikin qananun kaya wadanda suka sake qara masa kyau da quruciya, hannuwansu cikin na juna,tana riqe da wayarsa da kuma takalmansa da baikai ga sakawa ba da alama wata magana suke me muhimmanci,don kowannensu fuskarsa dauke take da walwala,duk da kusan ko yaushe haka suke su din,zaiyi wuya kaga sabani a tsakaninsu.

    Kanta ta dauke kamar zatayi aman zuciyarta,saidai a fuska kuma bata nuna hakan ba,amma wannan yanayin ya bayyana har saman fuskar tata

    “Oyoyo mimin daddy,oyoyo nawwaraty…..a’ah ga baby yusra” widad din ta fada cikin farincikin ganin yaran,suka taho da saurinsu suka rungumesu duka har uban,sai ta sanyasu cikin jikinta sosai,tausayinsu yana ratsata,inama ace abban nasu zai bar mata su.

    Yana zaune yana gaisawa da yaran nasa daya bayan daya yana bincikar lafiyarsu ba tare daya dubi ko sashen da hafsatun take zaune ba,widad kuma na tsugunne gabansa tana sanya masa takalmi a qafafunsa,sun share hafsat din kamar ba ita a falon,tun bayan sannunku da zuwa da widad tace mata ta amsa da qyar sai itama ta watsar da ita,don a yanzun kuma bataga wani alaqa tsakaninsu ba bare ta dameta.

    “Yaranka na kawo maka,don nima aure zanyi” maganar data fada kenan cikin gadara,dai dai sanda widad ta gama saka masa takalman,sai ya miqe tsam ba tare da yabi takan maganarta ba yana fadin

    “Allah yayi miki albarka,zan fita amma idan na taho zan kiraki,karkiyi nesa da wayarki” ido ta lumshe tana gyada kai

    “In sha Allah daddy” har ya daga qafa saita tsaidashi

    “Kamar kai mummynsu mimi keson gani”

    “Ohhhh…..” Ya fada yana dan sosa girarsa

    “Yara ta kawo,kuma tayi abinda ya dace,shikenan ta ajjiyesu ta tafi,idan kuma akwai sauran wani damuwan ki wakilceni kawai dear,nasan zaki iya komai…..i trust you” ya fada yana jinjina kai fuskarsa kwance da murmushi.
    [26/05, 2:43 pm] +234 903 583 2936: *H U G U M A*
    *Arewabooks:Huguma*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • A Rubuce Take Book 2 Page 37

    A Rubuce Take Book 2 Page 37

    Part 02

    Page 37

    Tun bakwai na safe ya gama shirin barin bauchi ya wuce katsina,sai daya tabbatar yabar gidan hannun umar,yace ya kula da kowanne sashe na gidan,idan ya gama ya rufe gidan,ya kaiwa yaaya bara’atu key din,sannan ya dauki dukka wani abu me muhimmanci ya zuba a motarsa ya fice a gidan.

    Gidan yaaya bara’atun ya fara isa,tasa aka kawo masa breakfast ya taba sama sama,don shi yanzu kowanne abinci kallon hadarin kaji yake masa indai ba abincin widad ba,bayan ta sallami mai gidanta dake sammakon fita tazo suka zauna,a sannan su mimi na tare dashi,yaran duka babu wata damuwa a tattare dasu,ita mimi ma nata murnar

    “Daddy har anyi kana wanka munci abinci,daddy aiba yanzu zamu koma gida ba ko?” Sai ya gyada kai yana shafa kanta,tausayin yaran kawai yake damunsa,banda mutuwa babu abinda zai raba uwa da danta,amma da yake Allah ya jarabcesu da shashashar uwa bata wani shiga jikinsu da zasu damu can da ita ba,kawai yana baqincikin su girma su tuhumeshi da rashin samar musu da uwa ta gari,saidai yayi imanin Allah bazai taba tozartar dashi ba,tunda yayi dukkan iya bakin qoqarinsa bisa kyautatawa hafsat din zato ya zabeta a matsayin uwar ‘ya’yansa.

    Duk da yaaya bara’atu tana dojewa amma bai bar mata wahalar yaran ta sisin kwabo ba,komai sai daya ajjiye musu kama daga na islamiyya har zuwa na boko,sannan ya bada wasu kudaden yace a canza musu suturar sanyawa,saboda ya lura da yadda kaf kayansu suka qarasa macewa,harda tsadaddun laces din da ya dinka musu,wanda ko shekara basu rufa ba,don shi baya jiran sai wani lokaci na daban zaiyiwa iyalinsa dinki,kusan ko yaushe cikin yi musu suttura yake.

    A nan ne tace ba zata karba sisinsa ba, dole ya maida kudin dinkinsu,ya mata sallama ya wuce.

    Tunaninsa a hanya kaf ya qare kan yadda zai doshi widad da yadda zai hukuntata,don ya gaji da maganar da take yaba masa a fakaice,yanaji a jikinsa muddin taci gaba da haka wataran za’a wayi gari ya samu matsalar hawan jini ko zuciyarsa ta tabu,ta shiga rayuwarsa da yawa,a yanzun kuma ta sake kutsawa nisan inda baiyi zato ba,wannana abun da ya faru sai sake qara mata kima da daraja a idanunsa,ya sake qaunar iyayenta tare da ganin zallar dattakonsu.

    Tun tana bagarar da batunsa daga ranta har tadan soma jin damuwar rashin jin wayarsa da kuma dawowarsa,amma hakanan dai taci gaba da daurewar tana yakicewa.

    Ko a yau data tashi duk jikinta babu kuzari sosai,ta gama komanta da wuri wajejen azahar,saita zauna shuru,sai kallo da kuma duba littafi zuwa waya da ta dinga yi,affan baya nan,wata maqociyarta ta daukeshi tun azahar din,babbar macace,dukka yaranta sun girma,shi yasa suke da son qananun yara.

    Karfe uku da kusan minti talatin da tara ya sauka a cikin gidan,ya sanya motarsa cikin parking lot ya kasheta,ya fito yana yiwa yaron gidan magana ya bude booth na motar ya fidda tsarabar da yayo a hanya ya aje masa qofar falon sannan ya wuce.

    Knocking yayi,ta dauke fuskarta daga kan littafin dake hannunta,sai ta aje littafin ta miqe a zatonta affan aka dawo dashi,tana gyara wuyan rigar wata bubu ta net da aka yiwa shafin wani irin yadi me kyau daga qasanta,rigar tayi mata kyau sosai,saboda ko ina na jikinta ya a cike yake,babu wani rami loko ko lobawa sai inda yake dama a halittar diya mace haka yake,fatarta lumui lumui,wiyanta ta saka wani ziririn zaren sarqa me qyalli da ya ake qawata wuyan nata,ta riga data saba,ya kuma zame mata jiki,ko yaushe a haka zaka sameta fes tana fidda qamshinta me laushi.

    A nutse ta bude qofar,ta buda siraran labbanta zatayi magana sai maganar tata ta maqale,yana tsaye gaban qofar falon hannunsa harde a qirjinsa,idanunsu suka gauraya waje daya,sai wani abu ya tsarga ma kowannensu,wani abu ya tasowa widad mai matuqar qarfi da tasiri.

    Ashe dai qarya ne idan kace ka daina son mutum?,ashe dai qarya ne kace baka damu da masoyinka ba saboda wani sabani ko bacin rai,saita juya da hanzari zuwa ciki,batason ta bada kanta.

    Baice mata komai ba ya dauki kayan duka ya shiga dasu ciki,ya maida qofar ya rufe,ya tsaya tsakiyar falon yana sauke ajiyar zuciya hancinsa yana zuqar lallausan qamshin da yake bayarwa,qirjinsa yana masa wani irin wasai,duk uban nauyin nan da yakeji cikin qirjinsa a yanzu babu shi,yana jin kamar ya sauke wani uban dutse daya danne masa zuciya.

    Ya wuwwulga idanunsa bata cikin falon,yasan ba zata wuce bedroom dinta ba,don haka ya wuce kai tsaye.

    Gaban madubi ta wuce kai tsaye, tayi tsaye kawai tana kallon fuskarta da qirjinta dake motsawa saboda bugun da zuciyarta ke mata,ta lumshe ido tana tuhumar kanta akan yadda take samun sauyi akan abbas din,duk wani alwashinta yana sulalewa yana yin nasa waje.

    Sam bataji shigowarsa ba,sai sautin muryarsa daga bayanta

    “Me bakin tsiwa,ina tsiwar taki ta tafi?,kin iya gasama mutum magana ko?,ki barshi da ciwon zuciya kiqi nemansa” ya fada yana kafeta da ido,gami da hukuntata da kallon nan nasa,haka kawai batasan ya akayi ta juye masa kalar shagwabarta data saba ba,saita tura baki gaba taja baya tana qara kusancin dake tsakaninsu

    “Qarya nayi?,ai banyi qarya ba k…….” Kasa qarasawa tayi saboda yadda taku biyu kacal ya hade ratar dake tsakaninsu,yaci gaba da ritsata da kaifaffen kallon nan nasa

    “Uhmmm……qarasa mana” ya fada yana matsota.

    Ta hangi fitintinu bama fitina ba fal idanunsa,ta kuma tabbatar yau idan ya kamata zata ji jiki da kyau,don haka ta kulle bakinta taqi tanka masa,saidai duk da hakan bai fasa matsota ba,har ya danga da bangon dakin

    “Tunda kinji tsoro zan qarasa cire wannan rashin kunyar taki,kin dauka ni age mate dinki ne ko?” Kai ya shiga girgiza masa,saidai kafin tace wani abu yakai mata cafka,yayi mata wata wawuyar runguma har yana takure abinda ke kwance a cikinta,baiyi wata waya ba ya hade bakinsu waje daya,ya fara aika mata da wani zazzafan kiss,wanda ko sau daya ya gaza dauke bakinsa daga cikin nata.

    Cikin mintunan da ba masu yawa ba ya zare mata dukka wata laka ta jikinta,ya cire dukkan wani zafin rai taurin kai da kuma qwafar data yi masa,cikin qalilan din mintuna ya zautata,ya jefata wata duniya wadda ta mantar da ita wacece ita,ta sukurkuce gaba daya,ta kuma miqa masa kanta,irin miqawar da bata tashi gane cewa ta tafka abun kunya ba sai bayan da komai ya kammala,tana kwance a qirjinsa tana kukan da dai dai yake da nade tabarmar kunya.

    Tabbas taji jiki a hannunsa,ta kuma biya dukkan bashin soyayya da kewa da suka cima juna,yana maqale da ita tsam a jikinsa yana aikin lallashinta,hannunsa daya kan sumarta yana shafawa a hankali,zuciyarsa fes,nutsuwa tana saukar masa

    “Ka daina tabamin kai,bayan tunda na dawo baka nema komai a gurina ba,har dai kaje bauchi ka gama bincikenka” ta fada cikin kukan shagwaba tana turo baki gaba.

    Don dole dariya ta kubce masa,ya rungumeta da kyau jikinsa

    “Am sorry madam,bansan a matse kike ba ai…..”kuka ta fashe masa dashi,ta dunqule hannunta tana dan dukan qirjinsa

    “To na daina,na fasa fada,nine a matse” ya fada yana kare dukan da take kai masa da hannayensa shima.

    Sai da ya tsagaita dariyar sannan ya sake gyara mata kwanciya sosai a jikinsa,ya kira sunanta cikin sautin muryar data sanyata daga kai ta kalleshi

    “Banqi neman komai a wajenki da gangan kodon saboda wata mafita ba,a lokacin kina cikin zafi da radadin abinda na aikata miki,na tabbatar idan na nemi wani abu a wajenki a sannan,abinda zaizo kanki shine jikinki kawai nakeso,ban fara sonki saboda jikinki ba ke shaida ce akan hakan,kuma bazan fara saboda hakan ba in sha Allah,koda baki da komai tattare da ke banajin zan daina sonki har gaban abada” sosai kalamansa suka kashe mata jiki,tayi shuru tana saurarensa,tana kuma sake gasgata zancan nujood da tace mata,abinda uncle abbas yayi din tabbas ba halinsa bane,tafi gasgata asiri ne yake dawainiya dashi,a lokacin tace mata hafsat,saidai ita din har yau bata kawota cikin ranta ba.

    Sake kiran sunanta yayi bayan ya hade hannayensu guri guda cikin wani irin taushi da sanyi,sai data sake shigewa jikinsa da kyau saboda yadda sautin muryar yaratsa kowacce gaba ta jikinta

    “Don girman Allah ki yafemin,yafiya irin ta har abada,banason ki sake tuna wani abu makamancin wannan ya taba faruwa a rayuwar aurenmu” Abbas ya cancanci yafiyarta,koba komai uban danta ne wanda ta haifa da wanda zata haifa ma a gaba,ba zata taba mancewa kuma da yadda ya tsayawa rayuwarta ba,ya dauki wautarta da shirmenta,ya raineta har ta zama abun kallo ga kowa ba

    “Na yafe maka har abada” wani farinciki yaji yana ratsa zuciyarsa,har baisan adadin godiyar daya dinga jera mata ba.

    Cikin kwanakin komai ya wuce ya kuma zama tarihi a rayuwarsu,ba wanda ya sake tada zance makamancin wannan a tsakaninsu,ta koma masa widad din nan dake rikita duniyarsa,ta sake shigewa rayuwarsa da zafafan sirrikan mallakar zuciyar miji tsaftatacciyar hanya babu boka ba malam,sai addu’a data duqufa da ita haiqan a kowacce sujjadarta akan Allah yaci gaba da mallaka mata abbas din.

    Da yake zuciyarta akwai haske da tsarki,sai komai yake zuwa mata yadda takeso,abbas din ya samu a gareta har fiye da yadda ta zata,ta sake gasgata cewa addu’a ba qarya bace,hakanan duk macen data sadaukarwa kanta wa mijinta,tabbas zai zama bawa a gareta ba tare daya ankara da hakan ba.

    Samun nutsuwa da kwanciyar hankalin da yayi daga widad yasa yake aiki tuquru cikin garin katsina,aikin da ya sake tamfatsa sunansa,ya kuma sake sanya sunansa a bakunan manyansa,suka kuma ji tabbas hazaqarsa da qoqarinsa sun girmi wannan matsayin da yake kai a yanzu.

    Budi sosai ya dinga shigo masa,hatta da kasuwancinsa kamar an qara masa albarka,cikin lokacin ya rasa wanne tukuici ya kamata ya bawa widad din,ba tare da saninta ko shawara da ita ba ya dallo mata sabuwar mota,ya kuma siya wani babban gida daban acan qasan layinsu dake garin bauchi ya ajjiyeshi reserve.

    Randa ya danqa mata motar tsananin murna ya sanyata kasa runtsawa,kyau da tsadar motar sai takejin kamae tafi qarfinta kamar ba tata bace

    “Madam,azo a kwanta hakanan murnar ya isa,ko kin manta bake kadai bace?,anya bazan fasa wannan kyautar ba?” Da sauri ta qaraso ta haye gadon tana dariya

    “Afwan yallabai,suma babies din naka taya ummarsu murna sukeyi” ya saki murmushi ya yaye rigar baccin jikinta yayi kissing cikinta sannan yaja mata duvets ya rufeta.
    [24/05, 2:59 pm] Mimah Yusuf: *H U G U M A*
    *Arewabooks:Huguma*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • A Rubuce Take Book 2 Page 34

    A Rubuce Take Book 2 Page 34

    Part 02

    Page 34

    Tana kwancen saman gadon tana chart affan yana kwance a gefanta yayi bacci abinsa kira ya shigo wayartata,tadan saki murmushi ganin suna uncle muhsin ta zauna sosai ta daga wayar suka gaisa,cikin hikima ya sako mata zancan abbas din,yadda yaga tana kame kame ya fahimtar dashi gaskiyar zancan,sai ya fara yi mata fada cikin nasiha,nasihar data sanyata zubda qwalla,ya kuma umarceta ta buda qofarta,tabar uba da da suyi harkarsu,shi yaron ba ruwansa a fadansu,wannan tsakaninsu ne,bazai hanata hukunta abbas ba muddin zata huce,amma kada ta sako affan a ciki.

    Cikin share qwalla ta bawa uncle muhsin haquri tare da bashi tabbacin ba zata qara ba,ta ajjiye wayar tana sake jin zafin abbas a ranta,a daketa a hanata kuka?,har yana da qwarin gwiwar kaita qara?,saita gyada kai tana cije lebe,ya kirawa kansa ruwa kuwa,lallai ba shakka zata hukuntashi har sai ya gwammace kida da karatu,saita sake daukan wayarta taci gaba da abinda takeyi.

    Yayi aikin da yakeson yi sosai,ya kuma hada information masu yawa,wannan yaja masa lokaci,bai fita a office din ba sai da yayi sallar magariba,ko kafin yaje gida ana dab da kiran isha’i.

    Komai data saba yi a gidanta na kaduna ta miqe tayi,ta tsaftace gidan saboda ita kanta jurewa take,duk da bata rayuwa a falon amma tana jin ya dameta har ranta,sabo da qazanta masifa ne,kamar yadda sabo da tsafta yakebin jini shima,tayi girkinta amma iya cikinta dana affan,ta gama ta kwashe musu,ta gyara kanta da yaronta,saboda batason abbas din ya shigar mata daki saita dawo falon tana jiran shigowarsa ta bashi affan din ta wuce dakinta abinta,aqalla ai tayi qoqari,ta kuma bi umarnin kawun nata,bata watsa masa qasa a ido ba.

    Ya jima zaune cikin motar bayan ya shigo gidan,murfin motar a bude qafarsa daya a waje yana shaqar daddadan qamshin da tun daga harabar gdan kana jiyoshi, qamshin da gaba daya ya gama kashe masa jiki,bai fito ba sai da yaji ana kiran sallar isha’i sannan ya fita,ya daura alwala a famfon harabar gidan ya wuce masallaci.

    Rigima yaron yaketa mata,saita sakashi a kafada ta soma zarya dashi,sanye take da doguwar rigar wata atmafa mara nauyi,an mata budadden dinki daga qasa,saman kuma yasha tattara ya zauna dai dai qirjinta.

    Tana kawowa bakin qofar zata juya yana buda qofar,suka hada ido ita dashi,yayi wani irin kwarjini na musamman cikin uniform din, hular kayan na riqe a hannunsa,saita janye idanun nata ta juya zuwa ciki affan na qijrinta,yabi bayanta da kallo,ya tako a hankali zuwa cikin falon bakinsa dauke da sallama,ta duqa tana ajjiye yaron gami da amsa sallamar tasa muryarta can qasan maqoshinta,saita juya ta nufi dakinta ba tare da ta sake kallonsa ba,tana shiga ta tura qofar,ta koma saman gadon tayi kwanciyar ta gami da jan wayarta ta fara dubawa,saidai zuciyarta adan hargitse take kadan,don bugunta ma ya sauya ba kamar yadda yake a qa’ida ba,kuma ita kanta batasan dalili ba.

    Tsaye yayi kawai a wajen kusan minti biyu yana duban hanyar,sai ya dauke idonsa yana sauke ajiyar zuciya,gaba daya a wannan lokacin bazaice yana jin dadin duniyarsa ba,duk yadda yaso ga qaryata hakan da gayawa kansa komai dai dai yake,amma yasan ya fada dinne kawai bawai don dai dai din yake ba.

    Gurin affan ya qarasa,ya dauki yaron yayi masa wasa sosai sanann ya wuce dashi dakinsa,ya cikashi da kayan wasa ya shiga bandaki ya sake wanka, sanda ya fito harya bingire saman gadonsa yayi bacci,da alama dazun dama kukan rigimar baccin yakeyi,ya saki murmushi yayi kissing goshinsa a hankali ya gyara masa kwanciya yana jin qaunar yaron har cikin jininsa,sai ya tsaya gaban madubi ya shirya cikin qananun kaya,ya shafe jikinsa da turare sanna ya fito.

    A falo ya fara zama,amma kamar wanda magnet ke jan hankalinsa zuwa ga dakinta saiya kasa samun sukuni,bayason shurunta,kasheshi yakeyi,a qalla ko fada yana da buqatar su dinga yi,duk sanda tayi masa shariya irin wannan baya iya jurewa,bashi da juriya akan abinda yakeso,sai ya taka a hankali ya saka kai zuwa cikin dakin.

    Tana tsaye gaban wardrobe tana fidda wasu kaya,sau daya ta waiwayo ta kalleshi ta mayar da kanta kamar batasan da wanzuwarsa ba,ya tsaya daga bayanta yana dubanta

    “Ina abinci na?” Kamar ba zata amsa masa ba,saita zuqi numfashi ta fitar ta bakinta a hankali, zuciyarta tafasa kawai takeyi amma batason tayi wani abu da zai nuna bata ganin qimar uncle muhsin,ta saki kayan hannunta ta juya ta fice ba tare data tanka masa ba,yabi bayanta sai ya sameta saman dining tana serving dinsa.

    Kujera yaja ya zauna yana bin dukka motsinta da kallo,ko sau daya taqi duban inda yake,kamar ma ita daya ne cikin falon,wani irin fushi ne kwance saman fuskarta ba tare da ita kanta tasan da hakan ba,yaja ajiyar zuciya me nauyi ya sauke a hankali,dai dai sanda ta gama zuba abincin ta motsa da niyyar miqewa tabar wajen

    “Dawo ki zauna” ya fada a tausashe cikin muryar bada umarni,bata musa masa ba,kamar yadda bata kalleshi ba,ta kauda kanta zuwa wani sashen daban,yaja abincin gabansa ya fara ci,saidai gaba daya girkin kamar ba nata ba,ta cika masa yaji sosai,abinda tasan yafi tsana kenan,ya lumshe ido yana jin yadda yajin ke ratsa harshensa har kwanyarsa,ya sakeyin loma ya biyu ba tare da ya bari ta gane tsananin yaji da yakeji ba,saidai idanunsa suna kanta,ya tsatstsareta dasu ya hanata sakewa gaba daya,cikin jikinta takejin laifin data masa,amma zuciyarta taqi amsar haka.

    “Karomin” ya fada yana tura mata plate din,sai ta daga kanta da sauri cike da zallar mamaki ta kalli plate din ta kuma maida dubanta gareshi suka hada ido,idanun nasa da suka dan canza launi saboda tsananin zafin yaji,sai kuma ta janye idon nata ta basar,tasa hannu ta dauki plate din ta qara masa ta tura masa hadi da bashi qeya.

    Spoon ya sake sakawa ya kuma cinyewa,sanda ya sake cewa ta qara masa sai data zauna sosai ta dubeshi da kyau,bakinta yadan motsa kamar zatace wani abun sai kuma ta fasa,ta sake janyo plate din ta fara zuba masa

    “Wannan karon ki zuba yafi sauran yawa,muddin ta wannan hanyar zuciyarki zatayi sanyi……zan jurewa ci har sai kince na barshi haka”

    “Kayita ci,bazance ka barshi ba” ta gayawa zuciyarta hakan.

    Ta gefan ido ta dinga satar kallonsa ganin yana hanyar cinye uban abincin data sake loda masan,tun tana satar kallonsa harta koma kallonsa kai tsaye,ko sau daya bai kalleta ba yaci gaba da ci,ta kalli idanunsa zuwa sannan sun canza launi sosai,tasan yadda yajin abinci ke masa illa,musamman ulcer da yake da ita wadda idan ta tashi ba qaramar wahala take bashi ba,batasan lokacin data riqe hannunsa ba

    “Ka barshi haka” ta fada da sauri muryarta tana rawa.

    Jajayen idanunsa Ya daga ya kalleta dasu,sai ta gaza jurewa kuka ya qwace mata,ta saka dukka hannuwanta biyu ya rufe fuskarta dasu tana sakin siririn kuka.

    Tsam ya miqe daga inda yake zaune ya iso gabanta ya tsaya yana dubanta zuciyarsa na wani irin tafasa,kafin yace komai tayi hanzarin bude fuskar saboda wani irin amai mai zafi daya danno mata,yana qoqarin riqeta tana qoqarin zamewa,saboda tasan muddin yaci gaba da riqeta zata wankeshi da aman.

    Bata iya riqeshi ba kuwa ta fara kwararashi,bai damu da yadda ta batashi ba saboda gaba daya hankalinsa a tashe yake,dama bata da lafiya?,tun yaushe?,duka bashi da wannan amsar,ya riqe hannuwanta sosai daya hannun nasa ya dafe mata bayanta yana jera mata sannu kamar zai ari baki.

    Shi ya gyara wajen,ya hada mata ruwan dumi ta gyara jikinta da ta bata shima ya gyara nasa jikin,tana kwance tana maida numfashi idanunta a kulle ya qaraso dakin,ya canza kayan jikinsa, boxer ne kawai a jikinsa,qaqqarfar kuma lafiyayyar surarsa ta fita sosai,ya dawo gaban gadon ya durqusa dab da ita ya kama lallausan hannunta ya riqe cikin nasa

    “Tun yaushe ne baki da lafiya?”

    “Kada ka tambayeni” ta fada muryarta tana rawa

    “Why?” Ya tambayeta a mamakance,sai data zame hannunta daga nashi sannan tace

    “Saboda baka damu dani bama gaba daya bare lafiyata”

    Tashi yayi ya haye gadon gaba daya,ya jawota cikin jikinsa dukkaninta ya rungumeta tsam,bata da qarfin da zata qwace a jikinsa dole haka ta zauna,a hankali sai taji yadda zuciyarsa ke bugawa da Wani irin qarfi n da ya wuce qa’ida

    “Tun daga wancan lokacin da abun ya faru haka kullum zuciyata take bugawa,ban taba zaton zankai wannan lokacin ban kamu da ciwon zuciya ba,komai nina aikata miki shi,amma bisa wani umarni da bansan daga inda zuciyata take karboshi ba…….kiyi haquri da dukkan abinda ya faru,ki kuma yafemin,amma nayiwa zuciyata alqawarin bazan bar wannan abun ya wuce a haka ba, kowanne irin tunani nasan zaki iyayi a kaina,dai dai ne bazan hanaki ba,amma ki bani dama……i need a chance don Allah don kuma affan bawai don ni ba” daga wannan maganar ya zame jikinsa daga gareta,ya barta da tunani.

    Hijab ya dauko mata sannan ya dauko affan

    “Muje kiga likita,bai kamata ki kwana hakanan ba” shi ya taimaka mata har zuwa bakin mota,sai data shiga ya kwantar da affan a baya sannan ya shiga ya tayar da motar suka fice daga gidan,dukkaninsu zuciyoyinsu babu dadi.

    Idanunsa qyar akan allon computer din sanda likita yake mata scanning,yara biyu ne gasunan kwance a mahaifarta har zuciyoyinsu sun fara bugawa.

    Da sauri ta dauke kanta gefe hawaye yana sauko mata,ta yaya zata iya rainon cikin ‘yan biyu?,bayan ko yaye affan batayi ba,a wannan yanayin da take ciki bata jin tana da qwarin gwiwar da zata iya rainon cikin ma gaba daya

    “Satin cikin sha biyu gashinan,congratulations” Dr anwar likitan mai matuqar kirki da barkwanci ya fada.

    Abbas dake jinsa kamar a duniyar mafarki ya miqa masa nasa hannun,Allah me yadda yaso a lokacin da yaso,cikin yanayin da yake na daukewar dukkan wani farinciki daga rayuwarsa sai ga hasken farinciki ya ratso daga ubangiji,ya maida dubansa ga widad hankalinsa ya tashi da ganin hawayen da take zubarwa,ya matsa saman kanta yana jera mata tambayoyin akwai abinda ke mata ciwo ne?,saita gyada kai

    “Bari ina zuwa” Dr anwar ya fada yana fita a office din,hakan ya bawa abbas damar dagata,ta zauna sosai yana riqe da hannunta,saidai ya kasa zama,yana tsaye ne tsakiyar qafafunta yana kallonta

    “Bani da qwarin gwiwar rainonsu da haifarsu” ta fada tana zubda sabbin qwalla,sai ya dora yatsantsa saman labbansa

    “Zan baki duk wani qwarin gwiwa da kika rasa,zan baki dukan hope,zamu rainesu tare na kuma tayaki naqudarsu,don Allah ki kwantar da hankalinki na roqeki,ina da buqatarsu,burin kuma hajiya kenan kullum taga tarin jikoki daga wajenki” furta sunan hajiya da yayi ya sake sanya damuwa da karyewar zuciya a zukatansu su duka biyun,sai ya matso ya sanyata cikin qirjinsa yanason saukar mata da nutsuwa.

    Tun daga wanna lokaci gaba daya ya maido hankalinsa akan widad din,ya bata dukkan lokacinsa ya rage ranakun fita aikinsa,ya hanata yin komai,komai shi yake mata,yayi nata yayi nasa yayi na affan,sai daya gama karantar komai da takeso naci sha da sauransu,wani lokacin har tausayi yake bata,duk da har yanzu ta kasa warewa yadda suke a baya,abinda yake qara masa damuwa cikin qirjinsa kenan,yake ganin kamar komai bai wuce a wajenta ba.

    Tun randa yaci wannan abincin qirjinsa yake yawan riqe masa da ciwo,amma sam bai nuna mata ba,don so yake ya dawo da dukkan farinciki da walwalarta.
    [22/05, 12:28 pm] +234 810 324 4136: *H U G U M A*
    *Arewabooks:Huguma*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • A Rubuce Take Book 2 Page 33

    A Rubuce Take Book 2 Page 33

    Part 02

    Page 33

     

    Ido suka kuma hadawa,ta sake janye nata idanun tana kuma hade fuskarta tsaf tamkar bata taba dariya ba,sai shima ya basar,yakai hannu kan kafadarta zai karba affan.

    Ji tayi sam ba zata iya bashi shi ba,don haka ta goce ta hanyar ja da baya,ya kalleta cikin tsantsar mamaki,ya sake takowa ya matso ta sake matsawa baya,sukayi haka har sau uku sai ya gaza daurewa,ya motsa labbansa da dan bacin rai a muryarsa

    “Yarona nakeson ki bani”

    “Sai yanzu ka tuna yaronka ne?,aina dauka shima a hotel nayo cikinsa” gam ya runtse idonsa yana jin saukar maganar kan qahon zuciyarsa kamar saukar mashi,karo na farko tsahon tarayyarsa da ita data taba gaya masa wata magana mai gautsi,ko kafin ya bude idanun nasa yaji giftawarta ta gefansa,ya waiwaya ya bita da kallo,ta doshi dakin data gani a bude ba tare data tsaya tambayarsa bedroom dinta ba.

    Tanata addu’a Allah yasa nata dakin kenan,ta kuwa dace don duka kayanta da aka shigo mata dasu suna ciki,wadataccen bedroom da aka saka komai na buqata daya dace da dakin kwana,ta qarasa a hankali ta kwantar da affan dake bacci saman gado,sannan ta jawo jakarta zuwa tsakiyar dakin,ta budeta ta fidda abubuwan da take buqatar cirewa,ta jefata dukanta cikin wardrobe na dakin,cikin ranta tana jin kamar ba wani zama zatayi ba,kamar na dan lokaci ne zata koma inda ta fito.

    Agogon hannunta ta cire ta ajiye saman madubi ta shiga bandaki tayi fitsari sannan ta daura alwala,tana fitowa ta hangeshi,tsugunne gaban gadon, hannunsa riqe da hannun affan dake bacci,ya sunkuya a hankali yayi kissing dinsa sannan ya miqe,suka sake hada ido ta kuma kau da kanta tana tabe baki,shima sai ya dauke kansa,amma duk da haka idanunsa na fusgo masa yadda ta wani murje,sai kishinta ya sake motsawa a zuciyarsa,yadan cije lips dinsa kadan,har yanzu zuciyarsa ta gaza samun nutsuwa akan abinda ya farun,kuma bayajin zata samu nutsuwar har sai ya sakeyin binciken qwaqwaf akai.

    Kamar yasan me take shirin aikatawa,har yasa qafarsa waje sai ya fasa ya dawo yana dubanta tana rolling mayafinta saman kanta tana jira ya gama ficewa ta saka sakata

    “Karki kuskura kice zaki kulle qofa,ki barmin yarona ya sake a gidan babanshi yadda yaso,inda ke daya ce sai nace bismillah,kiyita rufe qofar har Allah ya gajisheki” tabe masa baki tayi ta kauda kai ba tare da tako tanka masa ba,sai yaji haushi ya kamashi,yaso ko yaya ne tace wani abun,yaso ta magantu ko baqar magana ta gaya masa amma sai ta qiya,haka ya qarasa ficewa yana wani tsatstsare gida,yana jin Wani abu mai nauyi yana taba zuciyarsa.

    Bata kuwa fasa kulle qofarta ba,don batason ma ya wani shigo mata daki,don bata da buqatar ganinsa sam sam,zuciyarta wani irin zafi take mata idan ta ganshi,ta idar da sallar la’asar,zuwa sannan jikinta har yadan fara rawa,don bata jure yunwa kwata kwata,don dole ta fita ta laluba kitchen.

    Akwai komai a ciki,harda ruwan zafi a flask,ta shiga tunanin sassauqan abinda zata dafa kafin ya dawo gidan,sai kawai tayi amfani da ruwan zafin flask din ta tsaida ruwa,ta bare noodles ta zuba,ta kunna daya side na gas din ta soya qwai,cikin minti talatin kacal ta hada komai ta dauko ta wuce dakinta abinta.

    Tana murza key din yana shigowa,yaji qarar key din,yabi qofar da kallo,ransa ya baci,bata ji abinda ya fada kenan ba?,sai ya taka zuwa qofar dakin,ya daga hannu kamar zaiyi knocking me ya tuna kuma sai ya fasa Ya juya ya wuce kitchen.

    Wayam ya samu kitchen din,sai tukunyar data dafa noodles wadda ta cika da ruwa ta ajjeta a wajen,da spoon din da tayi amfani dashi wajen juyawa,bawon maggi dana vegetables din data zuba,sai yaji abun yayi masa banbarakwai,tsahon zamansu bai taba ganin tayi girki tabar gurin haka ba.

    Ci gaba yayi da duba kwanukan kitchen din,ko noodles din bata ajjiye masa ba,ransa ya sosu,haka ya jawo wata qaramar tukunya ya dora baqin shayi,don bashi da kuzari da kuma qarfin jikin dora komai a yanzu,girkinta yake marmari,ya kuma sanya ran ci,sai gashi ko ruwa bata dafa ta ajjiye masa ba.

    Jikin kitchen cabinet ya tsaya yana shan tea din,sau biyu ya kurba ya furzar,babu dadi sam bakinsa,sai a sannan ya ankara ashe ya cika komai yayi yawa,baisan kuma ya akayi hakan ta faru ba,haka ya kwarar da tea din ya fito yabar kitchen din.

    Parlor ya dawo ya zauna yana sauke numfashi saboda qirjinsa da yaji ya fara riqewa

    “Hasbunallahu wani’imal wakil” ya soma maimaitawa a hankali yana qoqarin cooling down kansa,likita ya gargadeshi game da dorawa kansa stress da damuwa mai yawa,jininsa ya hau an samu kuma ya sauka da qyar,idan kuma bai kiyaye ba zai iya dawowa.

    Yana tunanin akwai yunwa tattare dashi,ya manta rabonsa da cin abinci cikakke,ta riga ta batashi da taste din abincinta mai dadi,damuwa da rashin samun kalar taste dinta yasa ya watsar da lamarin abinci,dole ya cire waya ya kira daya daga cikin yaransa ya gaya musu irin abincin da yakeso.

    Ko da aka kawo din ba wani mai yawa yaci ba,cikinsa gaba daya a cushe yake,sai ya ture abincin ya koma ya kwanta kan doguwar kujerar falon,tunani ya masa yawa,a yanzun yake jinsa cikakken maraya gaba da baya.

    Sau kusan biyar yana ganin kiran hafsat,saidai yabi wayar da kallo,harta gama ringing dinta ta katse,bayason damuwa a yanzu,don haka bashi sa buqatar daga wayarta.

    Daga bangaren hafsat din sai ta dinga jin fargaba da dar dar,amma indai abinda malam ya gaya mata haka yake,me zai hana abbas din daga wayarta,tunda dai lokaci irin wannan da baya da lafiya ta tabbatar yana gida bare tace ya fita Wani aiki na musamman

    “Basa qarya a zancensu,tunda ta gayamin hakanne,kawai ki shareshi” zuciyarta ta bata shawara,saita aje wayar taci gaba da sabgarta.

    Washegari kafin ya fito ta gama duk abinda zatayi a kitchen din ta dawo daki ta rufe abinta,bata kuma sake fitowa ba sai bayan isha’i data tabbatar ya tafi masallaci sallah,ta zube kwanukan ta debi wasu ta koma.

    Cikin kwanaki uku abinda da dawowarta abinda ya dinga faruwa kenan,wani irin zama sukeyi na shariya da fita sabgar juna,saidai widad din ta fishi daukan zafi sosai,don bata fita a dakin sai idan ya fita sallah,da yake har yanzun bai gama warwarewa ba,yana gida yana sake hutawa,ko aiki bai fara fita ba,da zarar ya fita zata fita ta dafa musu abinda zasuci ita da affan ta zuba a cooler ta koma daki,ko wanke wanke taqiyi,haka ta dinga tarawa kitchen din kwanuka itama.

    Sau daya da wasa bata taba saka tsintsiyarta ta share falon ba tunda tazo cikin gidan,iya dakin da take ciki kawai take tsaftacewa,tun bai lura ba har ya lura da abinda takeyi shigen na hafsat,don kitchen din ya fara canza launi,haka qura ta fara yiwa gidan yawa,hakanan duk da baida lafiya ya zage ya gyara kitchen din da gidan,yayi tsammanin zata dauki haske ta gyara amma a banza,don ci gaba tayi da batawa tana jibge masa kayan a kitchen din,tun yana ganin zai jure har haqurinsa ya gaza,ya dinga fakonta ta fito amma ko sau daya bata bari hakan ta kasance ba,har ya gama murmurewa ya koma bakin aikinsa.

    Randa zai soma fita din haka ya hadawa kansa baqin ruwan shayi a tsaitsaye,yana tsaye a falon yana kurba,gaba daya sai yakejin bashi da sukuni,idanunsa qyar bisa qofar dakin,yana jiyo hayaniyar yaron,bama rashin isashen abinci da baya samu ne damuwarsa ba,wata kewarsu da yaji ta fara shigarsa da gasken gaske,tun bayan da ya duqufa da addu’o’in da aminin mahaifinsa ya bashi bayan zuwansa dubashi,ya kasa jurewa ya ajjiye cup din ya taka zuwa dakin.

    Sai da yayi knocking kusan sau biyar sannan aka tambayi waye a daqile

    “Kinsan ko waye ai ko ban fada ba” ya amsa mata adan kaurare,sai tayi banza dashi kamar bataji abinda ya fada ba,har sai da ya qosa da tsaiwar ya sake bugawa,amma sai tayi biris dashi

    “Open the door malama” ya fada da dan hargagi

    “Dakin ‘yar kwanan hotel din zaka shiga?,me zakayi da ita kai da kake da kamilar mace a bauchi?” Runtse idanunsa yayi yana jin zafin sunan data kira kanta dashi sannan ya bude a hankali yana aje numfashi

    “Stop it……ki budemin qofa kiban affan”

    “Affan kuma?,ai yarona ne ni kadai”

    “Widad!” Ya kirata da qarfi,sai taqi amsa masa

    “Ki budemin qofa nace” nan ma tayi masa shuru,har gwarancin da yaron yakeyi,da alama har yazo bakin qofar ne shima yaji.muryarsa,sai ya zame ya duqa a bakin qofar,yana jin kamar yayi zaana ya tsaga qofar ya shige,ba yaron kadai yayi missing ba,harda mamansa,yana son kallon wannan fuskar tata da ya jima bai gani ba,ya tabbatar ba zata sake ce masa komai ba,haka ya gama tsaiwarsa a wajen,ya juya a hankali ya dauki brief case dinsa ya fita a gidan.

    Rana ta farko a office dinsa amma bai iya wanzar da komai ba,shi kansa yasan baiyi tabuka komai ba,tunani fal kwanyarsa,gaba daya yana jin kamar an canzashi ne,kamar ba ainihin abbas ba,yaja tsaki yafi sau dubu,ya yarfa hannuwansa har baisan adadi ba,har cikin zuciyarsa yaji bazai iya jura ba,kawai sai ya dauki wayarsa yayi qundumbala ya kira muhsin.

    Kamar komai bai faru ba suka gaisa,sai abbas din ya samu kansa da bawa muhsin haquri

    “Ya wuce,amma tabbas saika dage da addu’a abbas,idan ba haka ba mata basu da kirki,zasuyita saka ka kana abu kamar Wani zautacce ko qaramin yaro” ajiyar zuciya ya sauke

    “Na gode” ya gaya masa

    “Alfarma nake nema don Allah idan zan samu”

    “Ba ‘yar wannan a tsakaninmu,fadi kawai”

    “Maman affan nakeson ka yiwa magana,ta hanani ganin yaron gaba daya,ta takureshi a daki, at least ta sakeshi ya dinga fitowa yana samun wadatacciyar iska” ya fada a mugun karye,karayar da shi kansa baisan ya nunata ba,sai dariya taso kubcewa muhsin,ya fahimci wani abu a cikin muryarsa wanda shi kansa baisan yana bada wannan amon ba,ba affan bane,maman affan din yake kewa gami da qishirwar gani

    “Kada ka damu,zan mata magana in sha Allah” yayi masa kuwa godiya sosai sannan sukayi sallama,ya ajjiye wayar yana sauke ajiyar zuciya,sai yake jin wani sassauci cikin ransa,ya jawo system dinsa zai fara rage wasu abubuwan saboda wani dan karsashi yanzun da ya samu,sai kira ya shigo wayarsa,daya duba sai yaga number hafsat ce.

    Da kallo yabi wayar yana jin wani abu yana yawo a ransa kafin daga bisani ya daga wayar,cikin salo da kisisinar jin cewa a yanzun ita daya ce a duniyarsa tace

    “Barka da yamma,ya gida ya jikin?”

    “Alhmdlh,ya yaran?”

    “Lafiya lau suke,yaushe zaka shigo?, inaga ya kamata ka taho gida don nafijin dadin kula da kai,ga rashin lafiya sannan kuma kai daya kake zaune ai baiyi ba abun” inda ace yau ya fara sanin halaye da dabi’unta sai yace ta bashi mamaki,wato ita ba zata iya takowa ta iskeshi a inda yake ba inda ace cikin buqatar hakan yake,saidai shi ya dawo ya sameta kenan,bai shirya gaya mata komai a kansa a sannan ba,saboda zuciyarsa ta fara tsara masa wasu abubuwa a kanta,shi yasa ya hana a sanar da ita komai game da abinda yake faruwa,har kuma dawowar widad din

    “Bazan iya tahowa yanzu ba,sai na warke sosai sannan”

    “K’nnnnn,ai shikenan,nace pampers din nawwara,kudin makarantar yara duka sun qare fa,naji Shuru”

    “Zan miki transfer ki siya” ya fada a gajarce,dama abinda takeson ji kenan

    “To yayi,sai anjima” ta fadi a gaggauce kamar wadda ake jira.

    Wayar yabi da kallo na wasu daqiqu,sai ya tafi contact nasa ya fara lalubar number wayar umar qaninsa.

    A ladabce ya gaida yayan nasa yakuma yi masa sannu da jiki

    “Kana ina?”

    “Ina kasuwa,muna lissafin qarshen shekara zamu danje hutu”

    “To yayi,idan kun gama ka ajjiye lissafin a wajenka,zan karba idan na nutsu na duba”

    “To yaya”

    “Aiki nakeson na baka,amma banason kowa ya sani,inason ya zama sirri tsakanina dakai”

    “To yaaya in sha Allah”

    “Ka hada kayanka ka koma gida na,karka taho har sai ranar da na umarceka,anjima idan na koma gida zan kiraka nayi maka bayanin abinda nakeso kayimin”

    “To shikenan,in sha Allah” yayi masa sallama,ya ajjiye wayar,saiya sake komawa kan system din,maimakon yayi aikin dake kai,sai kawai ya fita,ya saka sunan FAAZ HOTELS ya fara wani sirrintaccen bincike a kansa.

    [22/05, 12:28 pm] +234 810 324 4136: *H U G U M A*
    *Arewabooks:Huguma*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • A Rubuce Take Book 2 Page 38

    A Rubuce Take Book 2 Page 38

    Part 02

    Page 38

    Duk wajen wanda hafsat tasan zata ya yiwa abbas magana ya maidata taje amma abbas yayi biris,yaqi bawa kowa fuska yayi masa zancan hafsat din,suma din kuma suna kunya da nauyin yi masa maganar,saboda kowa yasan irin haquri da wahalar da yasha da ita,a yanzun sai yakejin ya samu wata irin nutsuwa da kwanciyar hankali da ya jima baiji irinta a rayuwarsa ba.

    Duk yadda takai ga bugawa bataga alamun samun nasarar komawarta gidan abbas ba,cikin qasqanci mugun bacin rai da baqinciki mai tsanani ta dauki shawarar da ummanta ta bata

    “Tunda yanzun itace ke fada masa yaji,babu wata hanya data rage illa mu wanke qafarmu muje kanon,mu samu kakanta shi kadai nakejin yayi saura da zai gaya masa yaji,karkiyi baqinciki,idan kika samu nasarar dawowarki gidan,wannan karon ko komai nawa da naki zai qare saimun salwantar da ita,ko ta fita daga gidan d qafafunta,koshi ya koreta,ko kuma tabar duniyar gaba daya”.

    Washegari suka shirya suka nufi kano ita da ummanta,ummu ta ganesu,ta kuma tarbesu kadaran kadaham,basu gaya mata abinda ya kawosu ba amma sun nemi ganin alhaji tsoho,ta sanar masa tayi musu iso ta kuma basu guri.

    Yadda ta dinga kuka tana gaya masa qaramin ciki ne a jikinta tana roqon alhaji ya sanya baki ya karyar masa da zuciya,duk da yana sane da komai da yake faruwa,ba kuma wai bayajin ciwo ba,to amma hausawa sunce d’a na kowa ne,kuma har yanzu shi akwai wannan jinin na karamci cikin jikinsa,wannan ya sanya ya tabbatar mata da cewa zata koma dakinta in sha Allah ta riqe yaranta.

    Murna kamar ta taka rawa ita da umman nata,ta yamutsa fuska bayan sun fito ta goge sauran ruwan hawayen dake fuskarta

    “Yadda kika qasqantar dani kika sanya na nemi alfarma daga wajen iyayenki,na zubda ruwan hawaye na duk ta dalilinki wallahi bazan qyaleki ba” hafsat ta fada cikin cin alwashi da buri.

    Sanda alhaji yayi kiran abbas din yana office,yabar dukka aikin dake gabansa ya saurari alhajin.

    Yayi mamakin jin ta inda hafsat ta bullo,bazai iya musu da tsohon ba koda wuqa ya dora masa a maqoshi,saidai yasan maganin hafsat,idan tasan wata batasan wata ba,don haka bai musa din ba yace ya karbi komen ya maidata,amma alhajin yayi masa alfarmar sanar da ita cewa,daga rana irin ta yau,duk randa ta sake yunquri ko ta daga masa hankali to a bakin aurenta.

    Alhajin baiso yayi wanna furucin ba,to amma kuma mai daki shi yasan inda yake masa yoyo,duk mutumin da ya iya irin wannan hukuncin akan uwargidansa duk da zuri’ar dake tsakaninsu……shi kadai yasan irin abinda yake fuskanta.

    Saida alhaji ya nemi magabatan hafsa sukayi magana ta waya,ya kuma shaida musu sharadin abbas sannan yace musu ya maidata.

    “Alhmdlh,Allah ya qara girma,ya saka maka da alkhairi yasa a gama lafiya” kawunta da ya cire hannunsa daga lamarin saboda baqincikin hafsat da uwarta ya fada,yanason ‘ya’yan yan uwansa,amma hafsat ta fita zakka ko a cikin marasa mutuncin gidan,dukka qoqarin da yakewa rayuwarta yana yine kawai don girman zatin Allah da kuma hakkin zumunta.

    A washegari ta tattara kayanta ta koma gidan,gidan da har ta debe haso da tsammani daga zamanta a cikinsa.

    Ranar data koma ta tsammaci zai maido mata dasu mimi,saidai har washegari shuru,washegarin ma data saka rai shima dai shuru,haka ta wuni gidan ita daya kamar mayya,zuwa dare ta kasa haquri,ta daga waya ta kirashi.

    Dai dai sanda suke zaune a falonshi shida widad da tsohon cikinta da take gab da shiga watan haihuwarta,tana saman kujera yana zaune a qasa,ya dora qafafunta saman cinyarsa yana matsa mata saboda yadda suke yawan kumburar mata,iya girman cikin kawai ya isa ya gaya maka cewa lallai twince dinne da gaske,labari yake bata kan gagarumin promotion din da yake sanya rai za’a yi masa koda wanne lokaci,muqamin CP wato commissioner of police,saidai akwai masu so da yawa,amma yana fatan indai zai zame masa rayuwarsa data iyalinsa alkhairi Allah ya tabbatar masa.

    A yanzun widad din itace abokiyar shawararsa da baya iya boye mata kowanne sirri nasa,duk abinda ya taso masa zai zaunar da ita yayi shawara da ita,Allah ya hore mata wani irin kaifin qwaqwalwa da basirar da muddin ta bashi shawara yana ganin haskenta.

    “Waye yake kira?” Ya tambayeta saboda tafi kusa da wayar,ta kalli screen na wayar sannan ta amsa masa tana miqa masa wayar

    “Mummyn mimi ce” qaramin tsakin da baisan ya fito ba yaja

    “Ki daga kice mata hutawa nakeyi” kai ta girgiza

    “A’ah fa,ba ruwana,kayi mata dai bayani”

    “Bazanyi ba,ke nace ki daga,idan kuma ba zaki daga ba ki gayamin kanki tsaye”

    “Allah ya baka haquri” ta fada tana girgiza kai,sannan ta daga wayar takai kunnenta

    Cikin kwantar da murya da kuma laushi tayi sallama ta dora da

    “Daddyn Mimi yanzu ba yafiya tsakanina da kai kenan”

    “Sorry,yana hutawa ne yanzun haka,saidai ki sake kira anjima” wata ashar ce ta tasowa hafsat din amma ta haqura ta danneta, zuciyarta kamar zata fito ta bakinta,saboda tsabar wulaqanci ita zai bawa wata ta daga mata waya?,a duniya yanzu cikin wadanda ta tsana babu sama da widad,sai taja mugun tsaki ta dauke wayar daga kunnenta,saidai ashe widad din ta rigata gimtse kiran.

    Safa da marwa kawai ta dinga yi a falon,da qyar ta taushi zuciyarta da dare ta sake kiransa amma bata sameshi bama kwata kwata,haka ta kwana biyar cikin gidan,ga kayan amfaninta duka sunyi qasa,sai takejin gidan gaba daya ya sauya mata tunda ba haka ta saba rayuwa a cikinsa ba.

    Tasan yaran suna gidan yaaya bara’atu,koda ta kira tace don Allah tasa a kawo mata su sai tace

    “Babansu yace zai kirani ya gayan duk sanda za’a kaisu din” kan bala’in ubancan,ita da yaranta ma sai an shata mata layin sanda zata gansu?,me abbas ke nufi da ita ne?,anya zata iya jura kuwa?.

    “Dole ki jure muddin kinason zama cikin gidan” haka anty ummee tace da ita,haka taci gaba da hadiyar baqinciki,cikin lokaci kadan ta fara rama.

    Sai da tayi sati uku da dawowa sannan umar ya shigo mata da kayan abinci zallarsu,bata ga alamun nama kifi fruits ko drinks da ya saba hadawa dasu ba,babu kuma kudin da yake dora mata akai,wannan karon ta kasa daurewa ta kirashi

    “Iya abinda zan iya kenan,idan zaki zauna ki zauna,idan ba zaki zauna ba qofa a bude take” amsar da ya bata kenan ya kashe wayarsa.

    Tana kuka sosai ta kira anty ummee tana gaya mata,don ta kasa samun ummanta

    “Ke kin cika gajen haquri,tunda bada yunwa ya barki ba saikiyi haquri ai” ta fada a mugun gajiye,saboda itama yanzun ta kanta takeyi,nata ballin kissar ya fara tashi,miji da sauran danginsa sun fara ramfota.

    Cikin aljannar kare abbas din ya sakata,dukkan wani abu da bai zama dole a addini ba ya janye mata shi,kudi da yake bata na kashewa da qari da yake mata da sauran wasu kayan alatu da basu zama tabbas ba gaba daya ya janye,yanason ya gani shin da gaske ta rusuna?,saidai a yadda ta fara rawa da kiraye kiraye zuciyarsa ta gaya masa

    “Mai hali fa baya fasa halinsa”.

    Sai da tayi wata guda da komawa sannan ya shirya zuwa bauchi,wannan karon da widad din za’a je,abinda ta manta rabonta dashi,ta jima sosai rabonta da bauchin,gaba daya ma garin ya fita a ranta tun wancan lokacin,yanzun ma tsaowar bikin nujood ne zai kaita garin,don dole taje tayi kara duk da nauyin da tayi,abun kuma yazo dai dai da saukar ‘yar yaaya bara’atu.

    Ya zame mata dabi’a,a duk sanda zaiyi tafiya bata qasa a gwiwa ita ka shirya masa komai,koda weekend din kuwa zaije bauchi,duk dadai ya jima rabonsa da bauchin,tun bayan kammala bincikensa da sallamar hafsat da yayi.

    Koda ta gama da qyar ta iya miqewa da taimakonsa hannunta riqe da bayanta tana cije lebe

    “Anya madam,kodai triples ne computer bai gano dayan ba?” Ya fada cikin sigar tsokana yana boye dariyarsa,harara ta balla masa

    “Ta ina zasu fito?,yallabai ka barni ma naji da wadan nan guda biyun,bansan ina zaka kai son yara ba”

    “Yaya ai rahama ne,banqi kowacce shekara na dauki sabon baby cikin gidan nan ba” kukan shagwaba ta sake masa tana yarfa hannu,tayi tayi qafa ta taku takai gareshi ya rufeshi da duka kamar yadda ranta keso amma ta kasa,wannan ya sake hasalata ta sakar masa kuka sosai.

    Shi da affan suka dinga mata dariya,duk da yaran baisan me akewa dariyar ba amma ya taya babansa,sai daga bisani daya fuskanci da gaske take sannan ya aje affan din yana cewa

    “Baka kyauta ba affan,kawo hannun taho ki rabu dashi” data samu kanta tana isowa kuwa abbas din ranqwasa saman kansa,ya dafe wajen yana shafawa a hankali,sai tasa hannu ta tureshi gaba daya yayi baya ya fadi.

    Motarsa ya ajjiye ya dauki tata motar,a ciki suka tsara tafiya bauchin dama,tunda already yana da wata motar a gida,idan sunje sai ya bata abarta tayi ziyarce ziyarce itama.

    Tunda suka idar da sallar asuba basu koma ba,sun gama shiri tsaf sai suka dauki hanya,sammakon da sukayi ya basu damar isa da wuri,taso ta masa magana kan ya sauketa a gidan uncle muhsin amma sai tayi Shuru gudun ta zama mai yawan qorafi,tasan dai yana sane da sharadin raba musu muhalli.

    Sun shiga layin sai taga yana fakawa qofar wani gidan na daban,tabi gidan da kallo,yakai girman nasu gidan,a tsare yake kamar dai nasun,ya fita ya bude qofar sannan ya tura gate din,ya dawo cikin motar ya jata zuwa ciki.

    A parking lot ya tsaya ya kashe motar ya waiwaya yana kallon widad din,ya sakar mata murmushi sannan ya fita a motar,ya zagayo side din da take zaune ya bude mata sannan yace

    “Welcome to your new home” kallonsa tayi da alamun son qarin bayani,sai ya dage mata dukka girarsa

    “Eh ga naki gidan…..kin dauka mance?,ni na isa nayi saken mantawa da sharadin abba?,ban shirya rasaki bafa kwata kwata koda kuwa da wasa” yayi furucin yana miqa mata hannunsa,saita dora nata akai murmushi yana qwace mata,ya taimaka mata fita a motar,ya fidda affan ya aza a kafadarsa suka wuce cikin gidan.

    [25/05, 1:45 pm] +234 810 324 4136: *H U G U M A*
    *Arewabooks:Huguma*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • A Rubuce Take Book 2 Page 36

    A Rubuce Take Book 2 Page 36

    Part 02

    Page 36

    Har sun dauki hanyar gida ya cewa umar ya kaishi gidan hajiya,ya sakashi ya shiga da motar ciki ya karbi key din gidan ya bude ya shiga.

    Komai na gidan yana nan tsaf tamkar tana raye,ba qazanta ba komai,su umar suna kula da gidan yadda ya kamata,har ya bude parlor dinta zai shiga sai ya kasa daurewa,ya fito ya bude dakinsu umar din.

    Wanka yayi ya sanya boxer da farar riga armless,ya rage hasken dake shigowa dakin ya kwanta,a maimakon bacci sai tunani suka cika kwanyarsa fal,ya dinga bitar halaye da dabi’un hafsat din,yana kuma irgen shekarun da suka dauka a haka ba tare da wani sauyi daga gareta ba,har cikin zuciyarsa yana jin ya fara qosawa,haqurinsa kuma yana dab da qarewa,abu daya yake tunawa yake kuma tausayawa,mimi nawwara da yusra,bayason su girma su kalleshi a matsayin wanda ya gaza wajen samar musu da nagartacciyar uwa.

    Haka yayita saqe saqe,kansa kamar tsage saboda rashin bacci da tunani,dole ya jawo wayarsa yana dubawa,ya cika da mamaki fal na rashin ganin kiran widad ko sau daya daga jiya zuwa yau,wani abune da bai taba faruwa ba a tsakaninsu saida wannan ibtila’in ya fadowa rayuwarsu,ya gama lalubensa sai ya kirata kai tsaye.

    Tana zaune riqe da wani qaramin littafin addu’o’i da anty madeena ta hadota dashi tana dubawa tare da qoqarin haddace wadanda suke na ko yaushe suke fi kuma muhimmanci,tun jiyan yana ranta,amma kuma batason bada kanta ta kirashi,tanason ta auna yadda take da matsayinta a yanzu a zuciyarsa,akwai abinda ya sauya ne ko har yanzun tana nan dai a yadda take a wajensa bata motsa ba.

    Qarar wayar yaja hankalinta,koda ta duba taga sunan data saka masa akan wayar sai ajiyar zuciya ta qwace mata,ta kife littafin ta dauki wayar ta kara a kunnenta.

    Sassanyar muryarta ta sauka a kunnensa, abinda ya sakashi sakin ajiyar zuciya da sautinta ya shiga kunnuwan widad

    “Kina azabtar dani da yawa maman affan,na dahu haka na dahu,wallahi nayi laushi over,don Allah kiyi haquri ki sassautawa dan marayan da baida uwa baida uba……sai Allah saike……”

    “Sai kuma uwar gidansa,sarautar mata” ta tari numfashinsa tana qarasa maganar da ba ita ta daukota ba.

    Dif sukayi gaba dayansu shida ita,ita tana sauraren amsar da zai bata,shi kuma yana fama da wasu abubuwa data saukarwa zuciyarsa,sai yaji harshensa yayi nauyi,duk wani abu da yayi shirin fada ya kama gabansa,bashi da sauran zabi illa zame wayar daga kunnensa ya kuma kasheta gaba daya ya koma yayi rub da ciki yana sauke numfashi da qarfi.

    Taji lokacin da wayar ta tsinke,don haka ta cireta daga kunnenta tana kallon wayar,tausayinsa ya darsu a ranta,amma ya zatayi,ta kasa daina jin zafin wai hafsta ce zata hadasu?,har ta isa ta zama silar girgizar yadda tsaftatacciyar qauna shaquwa da soyayyar da suka ginata ita dashi?,wata zuciyar na raya mata ta kirashi,wata tana hanata tare da gaya mata ki barshi ya sake dandanar irin abinda kika dandana,duk da ranta ba dadi hakanan ta shareshi,ta dauki littafin addu’o’inta taci gaba da dubawa.

    Da qyar ya samu bacci ya daukeshi,saboda maganar data gaya masa tayi masa nauyi da yawa a qirji,ya samu baccin nasa yayi nisan zango,don har missing salloli biyu yayi,ya tashi da hanzari ya daura alwala ya bada su, kafin ya kammala wayarsa ta fara tsuwwa alamun shigowar kira.

    Miscall uku ne na ezekiel,kafin ya gama dubawa tex ya shigo masa akan idan ya samu miscall dinsa ya kirashi.

    Sai da ya gama ‘yan addu’o’insa sannan ya zauna sosai gefan katifa ya kira Ezekiel din,bugu daya ya daga,ya gaidashi cikin girmamawa,sannan ya fara bashi feedback akan aikin da ya basu.

    Tunda ezekiel ya fara bayanin idanunsa a kulle suke yana saurarensa,babu abinda zuciyarsa keyi illa bugawa

    “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” kawai yake maimaitawa a hankali bakinsa yana motsawa,sai da ya gama bayanin tas abbas yayi saluting nasa,ya kuma tattara komai kama daga recording na muryarsa da video ya turawa abbas din ta email dinsa sannan sukayi sallama bayan ya gaya masa kwana biyu yakeso lawan yayi a cell,zaizo da kansa ya fiddashi.

    Duk da jikinsa yayita bashi hakan,duba da sanya idanun da yasa umar yayi masa kan yanayin mu’amalar dake tsakanin hafsat da lawan din,amma kuma ya girgiza matuqa,yadda har lawan ya iya aminta suka hada baki suka shiryawa widad din wannan tuggun,wanda kai tsaye zai iya cewa shi suka cutar bawai widad ba,duk abinda zai cutar da iyalinsa kai tsaye za’a iya cewa shi ya cutar,bare mummunan al’amari irin wannan,ya jima yana juya dalilin da yasa hafsat din ta sadaukar da lokacinta da kudinta ta sanya akabi widad din har hotel din akayi mata hotunan,me hakan ke nufi?,me takeson ta cimma,tace gyara,amma ta haka ake bin hanyar gyara?.

    Bai dauki komai ba illa key din motarsa ya fita a gidan ya nufi gida,yana tuqi cikin qarfin hali ne kawai,babu wani karsashi a tuqin nasa,har ya isa gidan,ya wuce parking lot ya ajjiye motarsa.

    Sashensa kawai ya nufa,don sai yaji gaba daya ya tsani kallon fuskar hafsat,mutum ne tsayayye ma’abocin gaskiya da kuma son aiwatar da ita,wannan ya sanya ya tsani qarya da maqaryacin mutum qwarai da gaske,ya buda sashen nasa ya shige ya maida muqullin ya rufe,sannan ya wuce bedroom dinsa kawai ya fada saman gadonsa qwaqwalwarsa na zayyano masa kalolin hukuncin da zai dace za hafsat,don ta lawan ya tabbatar ko iya haka ya barshi ya zuwa yanzu ya gane Allah daya ne,bare shi dinma bazai qyaleshi haka ba,yabar masa gidansa bari na har abada.

    *H A F S A T*

    Tun da rana data aiki lawan take jiran dawowarsa amma shuru wai malam yaci shirwa,tun tana bashi uzuri harta tunzura ta fara fada,ta kuma fara neman layinsa amma anata gaya mata a kashe layin yake,ta zauna tayita masifa tana kumfar baki,ragowar lace din da aka siya na anko ne a wajenta guda daya bai cika ba,ta bashi kudin kan yaje kasuwa ya cikaso mata dayan,gashi sun gaya mata suna hanya amma shuru babu shi ba dalilinsa.

    Sai data gama fadan ta godewa Allah ta koma taraddadi kuma saiga kiransa,sanda ta daga da niyyar yin sababi sai maganarta ta tsinke sanda taji muryarsa a shaqe kuma cikin tashin hankali yana magana da ita

    “Ina hannun police,sun kamani ne akan batun maman affan, wallahi bakiga mugun dukan da nakesha a hannunsu ba,yanzu haka basusan da wannan wayar a hannuna ba,sun gama dukana sun fita su hutane na kiraki,don Allah kizo kiyi beli na,ki fitar dani daga wannan masifar da kika jefani a ciki”. Wata hajijiya ce ta kwasheta ta jefar,dama da gaske ne kenan?,ashe dai zancen bai mutu ba?,wannan wacce irin masifa ce,tana zaton komai ya lafa,tana zaton ta samu nasara ashe qura tana baya

    “Idan na sake nazo wannan wajen lawan na zama nama na tabbatar,ka jirani zan nemi abban mimi na gaya masa qarya da gaskiya,zaiyi magana kosu waye na tabbatar zaka fito” saita yanke kiran tabar lawan da waya a hannu cikin matuqar mamakin yadda takeso ta barshi shi kadai a masifar,bayan ita ya yiwa aikin.

    Sanda taketa yunqurin kiran wayar abbas din a kashe take,dai dai sanda ya kashe wayarsa bayan widad ta yaba masa maganar data masa zafi matuqa,tayita kira a jere amma amsar daya ce,haka ta fito wajen baqinta tana rarraba idanu,fuskarta a yamutse,gumi yana tsattsafo mata ta kowacce kafa ta jikinta

    “Don Allah ina zuwa” ta fada tana yin waje da hanzari zani a hannu kamar zata ci da baka ta fara kiran wayar habiba tana dosar sassan abbas da nufin fakewa a can tayi wayar,don can dinne bata da haufi dashi,tana da tabbacin babu kowa a ciki bare tayi shakka ko taji dar dar din wani zai iya jinta.

    Koda ta bude sashen abban din sai data tabbatar ta qule har cikin bedroom dinsa,tsabar hankalinta a tashe yake bata ma yi tunanin yadda akayi qofar bedroom din yake a bude ba,burinta kawai ta isa dakin habiba kuma ta daga wayarta.

    Sama sama ya dinga jin magana yana tsaye gaban madubin bandakin yana kallon fuskarsa,ya matsawa kansa da tambaya da kuma tunanin son sanin yadda akayi ya yankewa widad wannan hukuncin,ya akayi ya aminta da zancan hafsat,a irin baiwa da Allah yayi masa,a irin matsayi da yake dashi da rank a wajen aiki?, tabbas wannan babbar jarrabawa ce,kuma qaddara ce mai girma,wadda ya godewa Allah da ya taqaita masa komai,bai jarrabeshi da sakin widad ba.

    Sautin muryar hafsat da ya fara ji yasa ya tako a hankali zuwa gaban qofar,har ya sanya hannu zai bude qofar sai ya fasa,kalamanta cikin rudani da tashin hankali suka fara shiga kunnuwansa

    “Ina cikin tashin hankali habiba,komai yana iya faruwa dani,wannan maganar dai bata mutu ba yadda malam yace,yanzu haka lawan yana hannun ‘yan sanda ba,na tabbatar zuwa yanzu indai sun gama bincikarsa to asirina ya gama tonuwa,don ba lallai ya iya iurewa dukansu wallahi sunana zai fadi,ki taimakamin habiba a sake danne maganar nan,dama hankalina tun ranar da sukayi maganar zuwa kotu ba’a kwance yake ba,ko baccin kirki bana iyayi wallahi,idan har abbas yaji maganar nan bani da sauran dabara kuma sai abinda y……..” Gaba daya ya rasa karsashi da qwarin gwiwar tsaiwa yaji qarshen maganganunta,hankalinsa yayi mummunar tashi,bayan sharri makirci da qazafi harda bin malamai hafsat din ta hada dashi?,a yaushe?,kuma yana me?,sai kawai ya buda qofar da wani irin qarfi,qarar qofar taja hankalin hafsat har sauran maganar ta maqale mata a maqoshi.

    Batasan wanne yanayi ta shiga ba,suma tayi a tsaye ko mutuwa tayi ta dawo?,itadai ta bude idanunta taga abbas a gaban mudubi riqe da biro yana rubutu,ta dinga qoqarin zaqulo kalamai daga qasan maqoshinta amma kalma daya ta gaza fita daga bakinta,har ya kammala rubutun ya iso inda take ya ajjiye takardar a gefanta

    “Daraja daya zuwa biyu kawai zakici yau a hannuna,na farko iyayen widad tun sunan zallar tauhidinsu,sun miqa ki kotun ubangiji wadda babu wata kotu a gaba da ita,babu wani adalin alqali da yakai ubangiji iya hukunci,to kije ni dasu suka mun barki da wannan,na biyu kuma kinci darajar mimi nawwara da yusra,banason na fito na qara ganin fuskarki cikin dakin nan,idan kuma baki yarda ba……” Sai ya murza yatsunsa kawai ya gewayeta ya fice ya barta a wajen a tsugunne.

    Dukka hannuwanta ta saka ta kama kanta da kyau ta riqe,sai kuma ta saki kuka mai qarfi kamar wata zautacciya

    “Haba abbas……daddyn ya zakayimin haka?,ko meye nayi nayi ne saboda kai” sake rushewa tayi da kuka,tana jin abun tamkar a mafarki,yau ita abbas ya saka?,abinda bai taba giftawa ba tsahon zamansu sai a yanzu?,a dalilin wata?,wai shin saki nawa ma yayi mata?,sai ta zabura ta dauko takardar ta warware jikinta yana rawa kamar wadda zazzabi ya yiwa mugun kamu.

    Saki biyu ta gani a rubuce fes,ta saki takardar tana sake rushewa da kuka,duk da ta samu sassauci ganin akwai sauran igiya daya da tayi saura, saita miqe da sassarfa ta fita daga dakin nasa ta doshi sashenta.

    Wayam ta tarar babu kowa,ba yaran babu baqinta,ta shiga nemansu kamar zautacciya lungu da saqo na gidan amma babu su,a bakin gate shazali ya gaya mata yaga mai gida ya fita shi da yaran duka a mota,batasan sadda ta sulale a wajen ba ta sake fashewa da kuka,tsoro ya kama shazali ganin yadda take sheqa kuka yau a gabansa,gashi babu damar ya tambayeta ko kuma ya bata haquri saboda yasan cin mutunci irin nata,haka ya koma gefe yana satar kallonta,har ta gama me isarta taja qafafunta tayi cikin gida bayan tayi futu futu da jikinta a wajen.

    Baifi minti talatin ba sai gata da jakarta tana janta,ta buda motarta ta jefa jakar ta shige itama,ta dannewa shazali wani mugun hon,tuni ya durfafi gate din ya bude mata da hanzari gudun kada ta huce haushinta a kansa.

    Gidan yaaya bara’atu yakai yaran wadda ta cika da mamakin ganinsa,diyarta budurwa ta kira ta dauki yaran,tace ta hada musu abinci,tuni sukabi bayan mariya ta zuba musu abincin suka sake abinsu sunaci,don dama yunwa ce fal cikinsu,tunda tun rana rabonta da basu abinci,tana ta business dinta,sai kuma wannan tashin hankalin yazo ya ratso na kama lawan,hatta da yusra abinci taci sosai,suna gama ci ba dadewa dukkansu bacci ya kwashesu a wajen.

    A can falo kuwa Shuru yaaya bara’atu tayi kamar ruwa ya cita,jikinta gaba daya ya gama mutuwa murus,tausayi da kuma namijin qoqarin da abbas yayi na zama da ita har tsahon wadan nan shekarun duka sun gama kasheta,gidan abbas dama duka ba wajen zuwansu bane,don babu fuska daga wajen hafsat din,wannan yasa da yawan dangi suka janye jiki saidai idan an hadu a gaisa,wannan ya sanya da yawa basusan wanne hali yake ciki ba,sai idan taso kawo qorafinta a kansa ta hada qarya da gaskiya ta fada saboda ta bawa kanta kariya.

    “Inason yaran suci gaba da zama a wajenki kafin na gama settling komai”

    “Ko har abada zakace ka barminsu ina maraba da haka” ta fada tana girgiza kai zuciyarta tana karaya,tausayin yaran na sake kamata.

    Murmushi kawai ya saki,yana son yaransa sosai,bayajin zai iya kyautarsu.

    Daren ranar daga hafsat har ummanta babu wanda ya runtsa,sun raba dare suna jajanta abun,don basu taba zaton zai iya sakinta ba,sun masa mugun qullin da tun aurensa da hafsat din sukayi wannan shirin,tsohon shiri ne da ita kanta hafsat din ta manta anyishi,saboda a sannan zuciyarta najin zata iya zama da abbas ba tare da anji kansu ba,zata kuma iya sauke duk wani hakki nasa,tayi abinda yakeso tabar wanda bayaso,don sanda umman ke mata albishir din anyi abun ma ita bata wani daukeshi da muhimmanci ba.
    [24/05, 7:39 am] Mimah Yusuf: *H U G U M A*
    *Arewabooks:Huguma*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • A Rubuce Take Book 2 Page 31

    A Rubuce Take Book 2 Page 31

    Part 02

    Page 31

    Zuwa azahar abba mahmud ya iso,ba dadewa saiga uncle muhsin shima takanas,wanda sam baisan abinda yake faruwa ba sai sannan,suka zauna shida sauran qannensa biyu dake binsa dukka cikin falon ummu,ya dubi widad da fuskar nan tasa dake nuna tsantsar da gaske yake,ya kirayi sunan widad din,wadda duna daya ta yiwa fuskarsa yawun bakinta ya dauke tsaf!!,tasan waye abban,tasan halinsa sarai,baya daukan wasa ko raini,hakanan bayason rashin gaskiya kaf rayuwarsa

    “Ki gayamin tsakaninki da Allah me ya faru?” Bakinta ne ya fara rawa,cikin kakkausar murya yace

    “Ki nutsu kiyimin bayani,idan kuma baki da gaskiya ne kiyi gaggawar fadamin basai kin batawa kowa lokaci ba” ta rufe idanunta sosai tana son bawa zuciyarta haquri ta kuma dai dai tata,saita fara gaya masa komai daki daki harta kammala.

    “Wayeshi abubakar din?”

    “Abubakar dai fa daka sani” uncle bashir ya amsa masa,sake waiwayawa abba yayi ga widad

    “Wannan abun da kika fada ayanzun idan baki qur’ani zaki iya dafawa ki sake rantsewa da hakan shine iya abinda ya taba faruwa?” Da sauri ta jijjiga kai

    “Zan rantse abba wallahi zan rantse”

    “A bani number wayar abubakar din” ya miqawa uncle bashir wayarsa,ya saka masa number abubakar akayi kiransa.

    Yadda widad ta fada din haka shima ya fadi,abba yayi masa sallama ya kashe wahar yana duban widad idanunsa tsar a kanta

    “Ashe kece duk kika jawa kanki wannan,ki gayamin uban da yace miki koni na mutu zaki fita daga gidanki kafin ki shaidawa mijinki,kadin kuma ya baki izni ta hanyar amincewa?”

    “Nayi kuskure abba,kuma naga indai fita ta uzuri ya kama yana barina ko ban gaya masa ba,saidai idan ya dawo din saina gaya masa……. astagfirullah” ta fada a rude hawaye yana zirarowa saman kuncinta sannan ta fashe da kuka,har affan yana daga kai yana kallon fuskarta sosai,dukka saida kowa a wajen zuciyarsa ta karye, dukkaninsu sunsan halinta,bata qarya ko za’a yanka ne zata fadi gaskiya,tun tashinta haka take.

    Sosai ran abba ya sosu,ransa ya kuma baci har ya gaza jurewa

    “Wanne irin aure ne wannan kukeyinsa da zargi?,ina akace anayin aure da zargi irin haka,zina fa?”

    “Wai ba zargi yakeyi ba,har hujja yana da ita”

    “Idan ba zargi bane waye ya gaya masa?”

    “Abokiyar zamanta ce” wani balaeen bacin rai ya tasowa abban, musamman shi da ya taba fuskantar halin makirci irin na mata

    “Abokiyar zamanta?” Ya maimaita wani bacin ran yana ciyoshi,sai kawai ya kasa sake cewa komai saboda tsananin bacin rai,ya miqe tsam yana cewa ummu

    “Ta zauna a wajenki ummu” daga haka ya fice,kowa a wajen ya fahimci yadda ransa yayi mummunar bacin rai,na biyunsa kuwa uncle muhsin ne,wanda shima ya miqe ya fita,ya kuma lalubi number abbas din ya kira.

    Daidai lokacin da yake tsaka da aiki da dukkan qananun police dake qasansa da zasuyi aikin tare.

    Cikin uniform dinsa dake qara masa kwarjini sosai,fuskarsa a dinke tsaf,a yau din baya ga yanayin aiki da yake sawa ya koma hakan,harda wannan qulalliyar damuwar dake qasan zuciyarsa,wadda ta koma masa abokiyar rayuwar ruhinsa,ya saka hannu a aljihun wandon uniform dinsa ya fidda wayar,ganin sunan muhsin din sai yadan gyara tsaiwarsa,tunda abun ya faru ko sau daya basuyi magana ba,sai ya juya a hankali ya taka yana fita zuwa qofar dan qaramin hall din da suke ganawar sirri.

    Kan qaramar barandar dake wajen ya tsaya ya daga wayar,suka fara gaisawa kamar komai bai faru ba,sannan a nutse ya jefa masa tambayar abinda yake faruwa tsakaninsu da widad.

    Yadda ya gayawa uncle bashir haka ya gayawa muhsin din,ransa yabaci shima

    “Yanzun ka yarda da abinda ita ta fada?”

    “Bana ce ba,sai nayi bincike kawai,zan sake bincikawa yanzun haka ina katsina ne” kai muhsin ya jijjiga ransa a bace

    “Saika gaggauta,saboda ran yaaya mahmud ya baci,kuma nasan halinsa sarai” daga haka ya yanke wayar,abbas din ya sauke wayar daga kunnensa yana kallonta,daga can qasan zuciyarsa ana gaya masa bakayi dai dao ba baka kyautawa,wani sashen kuma yana gaya masa shine dai dai,ya rufe idonsa a hankali yana jin kansa yana masa nauyi,a hankali sai ya fara jinsa kamar iska na kadashi hagu da dama,jinsa ya fara yin qasa hayaniyar dake kusa dashi ta fara komawa nesa dashi,sai kuma yaji kamar qafafunsa sun lanqwashe an turashi,ya tafi luuuuu zai fadi,mutumin dake dauke da posting later dinsa ta sauyin gurin aiki daga kaduna zuwa katsinar ya isa gareshi yayi saurin tareshi yana fadin

    “Subhanallah, innalillahi wa inna ilaihi raji’un” sai ya fara neman dauki,wadanda ke kusa suka qaraso suka tayashi riqe abbas din daketa qoqarin daidaita numfashinsa ya kuma miqe ya tsaya da qafafunsa saidai abun yaci tura,sunqi sakinsa don sun tabbatar zai iya faduwa,dole aka dauko motar aiki aka sakashi a ciki suka wuce asibiti dashi.

    Ummu tafi kowa saninta da sanin wacece ita,hatta da mahaifiyarta ba zata gaya mata wacece ita ba,zamanta wajen ummun an dan samu ci gaba kadan,ta lalubo abubuwan da takeson ci ta saka latifa na tanadar mata su,a yadda ummun ta lura sai taga kamar qaramin ciki ke sake wahalar da widad din,koda ta gaya mata a gigice ta daga kai ta kalleta cikin tashin hankali gabanta na wani irin faduwa

    “Ciki kuma ummu?” Yadda taga hankalinta yayi mugun tashi saita saki murmushi

    “Wai hasashe na ne,amma ba lallai ya zamana shi din bane” tabar widad din a haka,don ta fuskanci sanin tana da cikin kamar zai sake zame mata wata qarin damuwa akan wadda take ciki,sai kawai taci gaba da kula da ita a hakan.

    Kwanansa biyu a asibitin yana jin jiki,a kwana na ukun yaji dama dama,ya kuma nemi sallama amma likitan yace bazai bashi yanzu ba,sai ya huta sosai,saboda stress yayi masa yawa,so yana buqatar ya samu hutu sosai.

    Daga wajen aiki sun bashi kulawa sosai,sun kuma saka an saka komai a gidan da aka bashi zai zauna a zaman aikinsa,koda suka gaya masa shi sai yaji duka wannan ba damuwa bace a wajensa.

    Ciki ikon Allah a kwana na ukun yaji ya fara damuwa da yanayin da yake ciki,zuciyarsa ta fara tuhumarsa,ko yaya widad take ba zaka iya zama da ita ba?,ya sadaukar da komai dominka fa. Maganar da wannan raunannan sashen na zuciyarsa ke gaya masa kenan,ya tuna wayarsu ta qarshe da muhsin,wadda daga ita bai kuma kiransa ba,ya kuma tuna yadda ya gaya masa abban ya dauki zafi,mutum me mugun karamci da kirki,sai ya miqe zumbur ya zauna saman gadonsa ya jawo wayarsa.

    Kai tsaye ya kira kawu hassan,bayan sun gama gaisawa ya fara masa bayanin biko yakeso suje masa

    “Ikon Allah,hafsatun abun yakai har da sake tafiya gida?” Kai ya girgiza yana jin zafi a ransa

    “Ba ita bace,widad ce”

    “Widad kuma?” Kawun ya tambaya cikin mamaki

    “Eh kawu” shuru ya danyi sannan yace

    “Allah ya kyauta,amma ya zama dole ka sake zama mai nisan haquri,su mata indai kace ba zaka dinga haquri ba,kowacce ma ba zaka iya zama da ita ba,ko ka auro saisun tafi,kuma zo mu zauna zo mu saba” ya danyi masa fada sannan yace zaiyi magana da ko sunusi ne sai su shiga kanon ko zuwa gobe ne,ya yiwa kawun godiya sosai,yace zai sanya a tura musu kudin da zasu sha mai

    “Don qaniyarka muba iyayenka bane,har sai ka bamu kudin mai banda alkhairin da kake mana” wani busashen murmushi ya danyi kawai,ya sake masa godiya ya ajjiye wayar.

    Shuru yayi ya jingina da gadon idanunsa a rufe,wata zuciyar na gaya masa ya kyauta,wata kuma tana tuhumarsa,kanme zai dawo da ita bayan babban laifin data aikata?,bata cancanci ya zauna da ita ba,ya rasa wanne matsaya yake a cikin biyun?.

    Sai da yayi sallar azahar hafsat ta fado masa a rai,ya dauki wayar yana duba ko akwai kiranta amma babu ko daya tsahon kwana ukun,mamaki ya kamashi,sai ya fara neman layinta.

    Sai data kusa da tsinkewa sannan ta daga,murya a daqile tayi masa sallama,ya amsa sa muryarsa mai laushi

    “Sai yau ka tuna damu,ni kamar ma mu ka kama a hotel din nan” ta fada cikin gatse,sai yayi shuru yana jinta ransa na masa zafi,batayi dogon nazarin taji sauyi a muryarsa ba ta dora

    “Duk masifar ta dawo kanmu,kwana uku kayi tafiya amma ka kasa neman matarka daka bari da yaranka” kansa ya girgiza yana jin ciwo a ransa

    “Ke bakisan ki kira mijinki kiji ya ya isa ba?,idan kinji shuru bakisan ki karashi kiji me yake faruwa dashi ba?,bani da lafiya ina asibiti kwana uku amma rashin kulawarki yasa bakisan da hakan ba,da irin wannan halin naki wataran sai an kawo miki gawata unexpected” sai kuma jikinta yayi sanyi,ta danyi shuru sannan ta fara magana

    “Ni wallahi bansan baka da lafiya ba,sannu Allah ya sawwaqe ya baka lafiya”

    “Ameen” ya amsa can qasa,duk wani karsashinsa babu,sai yaji baya buqatar dogon magana da ita,ya tambayi yara ta hadashi dasu.

    Kusan su suka debe masa kewa,yayi hira dasu mai tsayi sannan yasa suka kaiwa mamar tasu wayar,ta tambayeshi wanne asibiti yake,daya gaya mata ya dauka zatayi batun zuwa ganinsa,amma sai tace masa kawai Allah yasa kaffara,akan haka sukayi sallama,sai ya kashe wayar,widad ta fado a ransa,yayi imanin inda itace da yanzun haka ta rude masa gaba daya,ya mirgina kansa gefe yana jin zafin zuwanta hotel,sai yaji ko sunansa bayason ji.

    *********Sai da ya gama shirin fitarsa kasuwa sannan ya fito gaba daya,ya samu baqin da akace masa suna jiransa a falon saukar baqi na gidan.

    Sukayi gaisuwar mutunci sosai,ya shaida kawu hassan don haka bai buqaci sanin daga ina suke ba,haquri suka bayar kan su din basusan me yake faruwa ba sai daga baya,suka kuma gabatar masa da buqatarsu na abasu bikon widad din tare da alqawarin hakan ba zai sake faruwa ba.

    Gyara zamansa sosai abba yayi

    “To naji dadin zuwanku,don dama inata shawarar neman daya daga cikinku,batun ya sake faruwa ko kada ya sake faruwa dama bazai sake din ba,saboda a yanzun bana buqatar kowa ya nemi bikon widad,abinda nake buqata don Allah,ku gaya masa ya rubuta takardar sakin diyata ya aikomin da ita,ko ya turomin ni tunda yana da number ta,magana ta biyu kuma,ku gayawa ita abokiyar zaman tata mai shaida da shaidu cewa,ta shirya shiga kotu dani uban widad bisa qazafin zinar data yiwa diyata,zamu shiga kotu har sai gaskiya tayi halinta,walau gaskiyarta ko kuma gaskiyar tawa diyar” dukkansu sun girgiza sun kuma ji babu dadi,don basu zaci wannan hukuncin daga wajen abban ba,sai suka fara qoqarin bashi haquri

    “Ai baza’ayi haka ba alhaji”

    “Me zai hana ayi haka?,na gama magana kuyi haquri bana maimaici,ya bayar da takarda ita kuma ta shirya shiga kotu,’yata ba mazinaciya bace,ba kuma zata sake zaman zargi ba” daga haka ya musu sallama cikin girmamawa yabar musu falon.

    Dole bayan sun gama jimanta maganganun a tsakaninsu suka fito,kowa sai da ransa ya baci dajin cewa wai hafsat ce ta gaya masa anyi haka harda bashi shaidu,kawu hassan bai rufeshi da komai ba,ya kirashi yayi masa tatas,ya kuma bashi saqon abban ya kashe wayarsa abinsa.

    *H U G U M A*
    *Arewabooks:Huguma*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • A Rubuce Take Book 2 Page 39

    A Rubuce Take Book 2 Page 39

    Part 02

    Page 39

    Duk da kayanta ne na wancan gidan nasu amma gidan yayi bala’in burgeta,komai ya tsaru,an kuma shirya mata shi dai dai da ra’ayinta da kuma yadda takeson gida ya kasance,ta dinga satar kallon abbas tana mamakin yadda ya karanci komai nata,me takeso,meye bataso,walwala da damuwarta,sai taji zuciyarta ta karaya,ta samu kanta da addu’ar kada Allah ya kawo abinda zai sake rabasu ko ya saka shakka ko rudani a tsakaninsu har qarewar numfashinsu.

    Widad din mutum ce mai matuqar qoqari,a tsaye take kan hidimar gidanta,duk da komai a gyare yake amma sai da tayi goge goge,ta kuma samar musu da abinci duk da akwai taimakon abbas din yana kama mata,sannan suka sake wanka gaba dayansu suka shirya don wucewa gidan saukar yaaya bara’atu.

    Yana riqe da hannunta suka shiga motar tata

    “Inajin aminatu zanje na roqa abarmiki,wannan aikin yana miki yawa” dadi sosai ya kamata,ta murmusa tana cewa

    “Amma da ka kyautamin qwarai,inason yarinyar,tana da hankali,amma kuma ranka ya dade,naga kaman baka da ra’ayin daukan mai aiki” kallonta yayi sannan yayi murmushi

    “Wayon tsiya gareki,nasan me kikeso kice,na farko amintu ai bame aiki bace,qaramin qarfi garesu,daukotan zai zama kamar taimako,kamar yadda tasa aka dauko lawan yaso ya zame mana wani abu daban,na biyu kuma ina da tabbacin ko ire iren aminatu dubu zan cika miki gidanki dasu,ba zaki bari kowacce tayi hidimar mijinki ba,ba kuma zaki sakar musu hidimar gidanki gaba daya sai yadda sukaso suyi ba,munsan aminatu muna da tabbaci akan tarbiyyarta,ba zata batamin yara ba,kuma na tabbatar baki da sakaci da zaki kasa sanya ido a kanta,ko yaya motsinta ya canza nasan in sha Allah zaki kula,zaki kuma tsawatar” shuru tayi tana dan gyada kai,komai yayi wato yana sane,yana kuma da hujja akai

    “To Allah ya zaba abinda yafi zama alkhairi”

    “Ameen ya hayyu ya qayyumu” ya fada cikin nuna kulawa.

    Sai da ya ajjiyeta a qofar gidan sannan ya miqa mata key dinta yana jifanta da wani kallo,saika dauka sabon saurayi da budurwa ne

    “Drivernki ya gama aikinsa ranki ya dade” dariya ta tsuntsire da ita

    “Godiya nake,zan ninka maka salary dinka”

    “Da kuwa kin kyautawa dan marayan Allah” ta girgiza kai tausayinsa yana dan tabata

    “Allah ya jiqansu ya kyauta makwancinsu ya kyauta namu zuwan”

    “Ameen ya Allah,Allah yayi albarka” ta amsa da ameen ya fita a motar yana gaya mata zai qarasa gidan suraj da yake basu da nisa,idan sun shiga wata sabgar yasan zata iya maida kanta gida,idan kuma ya dawo da wuri sai ya maidata

    “Koka maidani dawowa zakayi,kasan dai kwanan waye ai” harara ya balla mata,tayi kamar bata gani ba ta wuce ciki tana qunshe dariya tana riqe da hannun affan da ya fara koyon tafiya,wannan yasa ta dinga takawa a hankali cikin kula da takatsantsan.

    Tun daga qofar gidan jama’a ne,ta dinga gaisawa da mutane sunayi mata sannu saboda ganin yadda tayi nauyi sosai da uban ciki a gaba,yan mata matan suka daukar mata affan din suka kutsa cikin gidan dashi ita kuma ta tsaya tana ci gaba da gaisawa da mutane.

    Hafsat din na tsakar gida anata rabon tuwon sauka,gaba daya ba cikin sukuninta take ba ganin yadda su mimi suka shiga sabgarsu cikin mutane,ko ta kanta basayi,yaran sunyi fes dasu sunyi haske sunyi qiba

    “La la la,da gani babu tambaya wannan yaron sir abbas ne” wata qanwar mijin yaaya bara’atu ta fada bayan an shigo da affan ciki

    “Tubarkalla ma sha Allah,yaro ya debo ruwa biyu,miqomin shi na ganshi” ta miqa hannu tana karbar affan dake fidda qamshi cikin navy blue din jeans da shirt dinsa.

    Sosai maganar taja hankalin hafsat,gabanta ya fadi ta waiwaya tana kallon yaron dake da yawan fara’a,abinda ya qara masa farinjini kenan,saita dauke kanta wani abu yana tsaya mata a wuya,shi da babansa sukazo lo shi kadai?, indai kuwa shi da babansa ne lallai abun abbas qara ta’azzara yakeyi,har yazo bauchi amma bata da mutuncin da zai gaya mata yazo din?.

    Bata gama wanann taraddadin ba widad ta danno kai,kamar kunna fitila cikin duhu haka ta haska gurin,da kyakkyawar shigarta me aji,dama tunda can din ita gwanar iya dressing ce,tunda quruciya ballantana yanzu data mallaki hankalin kanta,wata lafiyayyar atamfa ce a jikinta wadda tafi kama da material.

    Suna hada ido gaban hafsat din yayi Wani mummunar faduwa,faduwar da sai data rufe idanunta don tanajin sautin bugun zuciyarta har kunnenta,kamar ciki fa take gani a jikin widad din,ciki fa,cikin ma tsoho?,saita miqe tana laluben hanya,wanda banda Allah ya kare tayi hanzarin dafa bango da tuni ta timu a gurin ta fadi.

    Ba wanda ma ya kula da ita suna yiwa widad din maraba,kowa na qoqarin mata godiyar alkhairin da ya samu wannan karon daga wajen abbas din,wanda da yawansu sun tabbatar widad din ce sila,hakan yake kuwa,a wannan karon tayi shirin karbar soyayyarsu ne gaba daya,ribar kasuwancinta ta raba biyu,rabi ta dinga qarawa kowa akan abinda abbas ya saba bayarwar,har sai da suka qare,ita da fahad sukayi,batasan bakinsa bai iya shuru ba sai daya gaya musu,saboda shidai abun mamaki ya bashi,don koda wasa bai taba ganin hafsat din tayi musu haka ba,saidai tayi qoqarin ragewa ma.

    Mayafi da takalminta ta dauka ta sulale sai gidansu,tsananin bacin rai yasa da tashin hankali yasa ta manta da batun daukansu mimi da jiran zuwan abbas tayi masa kwance kwance ya bata yaranta.

    Tana shiga gidan ta dora hannu aka ta sakama maman nasu kuka,tayo wajenta hankali tashe

    “Wani cikinne da ita umma na shiga uku,ta kusa haihuwa fa?”

    “Ina fatan bakiyi wannan haukar a gabansu ba ko?” Ta fada cikin taraddadi,ta jinjina kai kawai don ta kasa cewa komai

    “Shikenan tashi muje ciki” yunqurin miqewa tayi amma sai jini ya soma bin qafafunta,ta fidda idanu waje ta qwala qara tana fadin

    “Wayyo Allah!…..cikina umma” sai kuma tayi baya luuuu ta sume umman tata ta tareta cikin tashin hankali.

    Kai tsaye asibiti suka wuce da ita,bayan an basu gado anyi gwaje gwaje aka tabbatar da zubewar cikin jikinta,kamar zatayi dan qaramin hauka koma ace qaramin haukan ta dinga yi a asibitin,har sai da haushi ya kama ‘yan uwanta.

    Ta ciwa cikin jikinta buri sosai,tasan abbas din da matuqar son yara,ta gama tsara yadda zai zame mata makamin da zata yaqi abbas ta kuma dawo dashi tsundum cikin rayuwarta.

    Ba abinda abbas din baiyi ba na hidimar asibitin,hatta da ruwan da yan dubiya zasu sha bai bari kowa ya siya masa ba,ko dama can shi din tsayayye ne,baya dorawa kowa lalurar iyalinsa.

    Ranar da aka sallameta ranar suke komawa bauchi,don haka duk wani plan dinta ya gama rushewa,umman nata tace kada ta damu,ta bari ta gama jinin biqin nan,sai su shirya ma komai da kyau.

    ********Shirin haihuwa sosai abbas yake yiwa widad din,siyayya yakema twince din da basuzo duniya ba kamar ba gobe,abun yazo masa akan gaba,saboda wani irin budi yake samu sosai,harkokin kasuwancinsa da yake gudanarwa a gefe kamar ana musu yayyafin alkhairi,haka ta fannin aikinsa,ya tsare gaskiya da amana,hakanan koda cikin yaransa ya kamaka da laifin karbar cin hanci ko rashawa to ka kade,dukkansu sun sani kuma suna kiyayewa dokokinsa.

    Already likita ya gaya mata,tana cika watanni takwas to zata iya haihuwa daga sannan,kasancewar cikin twince,kuma ba haihuwar fari bace,don haka kullum abbas din cikin shiri yake,tayita dariya saboda yadda yakeyi din,kamar lokacin za’a fara yi masa haihuwa.

    Ranar da zaije bauchi weekend kamar kada ya tafi,tace sam sai yaje,watansa guda kenan baije ba saboda cunkoson aiki anan katsinan,hakadai ya tattara ya tafin ya barta da aminatu da yasa akaje aka dauko mata ita kafin ya wuce,sai da ya dawo sannan hankalinsa ya kwanta.

    ********Tun kafin su gama cin abincin dare bayanta da mararta ke ciwo,amma take daurewa tana cijewa,suna gama cin abincin tasa aminatu ta dauki affan suka wuce dakinsu,sai itama tace kwanciya zatayi,don bayan sun gama cin abincin fita ta kama abbas din ta gaggawa,don haka suka rufe ko ina,yana da key din kowacce qofa tasan idan ya dawo zai bude.

    Tashinta uku xuwa wani irin fitsari da yake takura mata,a zuwa na hudunne ta durqushe a bakin toilet din tana riqe da mararta da bayanta saboda wani mugun murdawa da tayi

    “Ya hayyu ya qayyumu bi rahmatika astagis” ta dinga maimaitawa,sai ta koma ta zauna sosai a wajen.

    Tun a can yaji jikinsa bai bashi ba,don haka ya katse meeting din,yabar mataimakinsa yace su qarasa,kome ake ciki su gaya masa.

    Yana buda qofar nishinta ya fara ji,a rude ya qaraso inda take yana tambayarta,amma babu baki,sai kawai ya fara sauko da kayan haihuwar data hadasu jiya jiya ya fidda cikin mota,ya kamata ya kaita mota,ya qwanqwasa dakinsu aminatu ta bude,ya gaya mata su kulle ko ina su kwanta,ya bata dukka keys din na gidan yace zasu asibiti,hankalin aminatun a tashe tayi musu addu’a ya fice.

    Kafin su isa ya kira daya daga cikin juniors dinsa,suka sameta a asibitin,bayan an dubata aka wuce labor room da ita.

    Addu’ar data dinga yi ba kadan bace,a wannan karon duk yadda ta zata ba haka bane,ana kiraye kirayen sallar asuba lokacin da abbas ya wuce masallaci cikin hukuncin ubangiji ta haife kyawawan twins dinta dukka maza.

    Yana kuma idar da sallar kira na shigowa wayarsa,ya daga yana sauraren bayanin da ake masa,tafiyar gaggawa ce ta taso musu shida matimakinsa da wanda abbas din ke bi,shine matsayar tattaunawarsu ta jiya,qarfe shida na safe,don dole ba yadda zaiyi haka ya amsa,don a qa’idar aikinsu ba sabawa umarni,ya baro masallacin yazo ya tarar da alkhairin da Allah ya saukar masa a wannan sassanyar asubar,baki da dukka zuciyarsa sun gaza daina furta godiya ga Allah,yaran kawai ya samu gani suma a gaggauce,haka yabar asibitin cike da kewar yaran da kuma mamarsu.

    Tun a hanya ya buga waya ya gayawa dukkan wanda ya dace ace ya sani,daga danginsa zuwa nata,gab da zai shiga gida ya kashe wayar don ya samu ya shirya,bai kunna wayar ba sai da suka dauki hanya.

    Yana kunnawa hafsat ya fara kira don ya fita hakkinta,ko basa tare indai zaiyi tafiya ya saba yana sanar da kowaccensu,bayan ya gama gaya mata tafiyar ya dora mata da batun haihuwar.

    Uffan kasa cewa tayi,saboda wani qaton abu da ya toshe mata qofofin maganarta,twince?,to maza ko mata?,ko Mace da namiji?,kai koma meye yarinyar ta haifa itakam ta shiga uku.

    Shurun da yaji yayi yawa sai ya mata sallama kawai ya katse wayar,ya amsa kiran yaaya bara’atu daya shigo masa.
    [25/05, 1:45 pm] +234 810 324 4136: *H U G U M A*
    *Arewabooks:Huguma*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)