Author: Novels

  • Kanwar Maza 10

    Kanwar Maza 10

    10

     

    Ɗan tsayawa ruma ta yi tana kallon mama, cikin sangarta ta ce “Mama wai me na yi to?”

    “Ban sani ba fitar mini daga ɗaki, mara kan gado, ni ba dan a gida na haifeki ba, cewa zan yi an canza mini ‘ya, idan an yi gabas sai ki arta ki yi arewa, me ake da wani wari ban da rashin kan gado irin naki?”
    Tsayawa ruma tayi tana kallon mama tana wasa da gashin kanta.
    “Ba zaki fita ki bar mini ɗaki ba, sai na taso kan ki?”
    Fitar ta tsakar gida yayi dai-dai da shigowar Yasir, da shi da Huzaifa.

    Yasir ya aika mata da wani irin mugun kallo ya ce “Me na ce miki game da zuwa Ajinmu?”

    Ta murguɗa baki ta ce “Ni wurinka na zo, ai ba wurinka na zo ba, ni da malam Habibu muka zo”

    “To uban me ya hana ki je ajin su Huzaifa?”

    Huzaifa ya yi caraf ya ce “Wallahi ta zo mana aji, sai na mata dukan tsiya, ta zo ɗin ta gani”

    Hararsu ta dinga yi, tana cewa wallahi sai ta je.

    Bayan Huzaifa ya canza kaya, ya shiga ɗakin mama ya ɗau jakarta.
    Ruma ta ɗaga murya ta ce “Mama, ga Huzaifa nan ya ɗaukar miki jaka”

    Ya ce “To munafuka”

    “Wallahi ni ba munafuka ba ce, mama Huzaifa zai satar miki kuɗi”

    Huzaifa ya ce “Mama aron naira ɗari zan ɗauka”

    Mama ta ce “Ajiye mini jakata, ba zan baka aron ba, idan ka ɗaukar mini kuɗi ba bani ka ke ba”

    “Dan Allah mama ki bani, zan baki wallahi”

    Daga kitchen mama ta ce “Ba zaka ajiye mini jaka ba sai na zo ɗakin nan?”

    “Mama wallahi bai ajiye miki ba”

    A fusace Huzaifa ya ajiye jakara, yana yiwa ruma kallon banza, kamar ya kai mata duka haka ya fice.

    Ruma ta ce “Dana sani na bar shi ya ɗauka, nawa nake bin mama ba biyana take ba”

    ***

    Yau za a rufe makarantar su ruma a tafi hutu, yau za ayi spelling B da aka bawa su ruma.
    Sai bin malaminsu take tana ce masa ita fa sai an sakata a cikin masu spelling B.
    Malamin ya ce “Ki kwantar da hankalinki, zamu san yadda za ayi”.

    Azabar nacin ruma sai da ya sanya aka sakata a cikin masu spelling B, amma aka ce kar ta yi magana.

    Ƙarshe dai ruma ce ta taimaki ‘yan ajinsu, gaba ɗaya kalmomin nan babu wanda ba ta haddace ba, ruma ta bawa malaman makarantar su da ɗaliabai mamaki, dan ko bata takardar da aka yi, tsabar naci ne ya sanya a ka bata.

    Ai kuwa ruma ta samu kyaututtuka sosai, karo na biyu a rayuwarta, da ta samu wani abun arziki a saboda harkar karatu.
    Aka bata litattafai kaya guda, da kayan koyon karatu.

    Ruma baki har kunne ta je gida, mama ta ganta da kaya niƙi-niƙi.

    “Ke wannan kayan na menene?”

    Ruma ta zubewa mama kayan ta ce “Mama, duk nawa ne a makaranta aka bani”

    “Meyasa aka baki?”

    “Wannan takardar da aka bani ce a makaranta, kowa ya ƙi koya mini, na je na yi ta yi da kaina, shine fa aka yi yau na samu wannan kyautar”

    Mama ta ce “Hmm, ai shikenan”

    “Mama wai na ga kamar ba ki yadda da bayanin da na yi miki bane?”

    “Eh to kusan hakan, dan abin da kamar wuya gurguwa da auren nesa”

    Cikin rashin fahimta ruma ta ce “Mama wace gurguwar kuma?”

    Cikin gajiya da halin ruma mama ta ce “Ki tashi ki cire uniform ki yi wanka”
    Ruma ta tashi ta cire kayanta, ta ɗebi ruwa ta shiga wanka. Ta na tsaka da wankan, ta jiyo muryar Usman ya shigo, daga banɗakin ta buɗe murya ta ce “Yaya Usyy Albishirin ka”

    “Ruma ban hanaki surutu a banɗaki ba?”

    Ta ce ‘yi haƙuri mama”

    Ba dan ta gama wankan ba, cikin zumuɗi ta fito daga wankan ‘Yaya usman, bari na nuna maka wani abun mamaki”

    Ba ta san a ya ta fito daga banɗakin ba, sai da mama ta daka mata tsawa, daga ita sai pant ta fito. Ta koma ta ɗauko zani, sannan ta kwaso kyaututtukanta ta nunawa Usman.

    Ya kalli ruma sannan ya kalli kayan ya ce “Ruma ban yarda da ke ba”

    Ta ce “Saboda me?”

    “Ina ki ka ga kwanyar da zaki yi wani abun arziki ke?” Tsuke fuska ta yi tana kallonsa ta ce “To me ka ke nufi?”

    “Ɗauko takardar da aka baki, na yi miki tambayoyi” ta miƙe ta je ta ɗauko masa takardar ta miƙa masa.

    Ga mamakinsa duk abin da ya tambayi ruma, sai ta bashi amsa daidai ko gyaranta ba ya ci.
    Ya ajiye takardar, ya kalli ruma ya ce “Ni fa haryanzu mamaki nake, matar da take zuwa ta kusa da ta ƙarshen aji, ita ta yi wannan ƙoƙarin”

    Ruma ta yi murmushi sannan ta ce “Ikon Allah kenan, baku san haushin da nake ji idan aka ce mini daƙiƙiya ba, shi ya sa na dage na je na iya”

    “Congratulations, ina ma zaki cigaba da dagewa da kin ga cigaba a rayuwarki”

    Ta taɓe baki ta ce “A’a da wahala gaskiya, ka san baƙar wahalar da na sha kan na iya wannan abun, dan a dai na ce mini daƙiƙiya daga wannan ba zan kuma ɗaukar dala ba gammo ba”

    Usman ya yi murmushi ya dafa kafaɗarta ya ce “Haba ƘANWAR MAZA, rayuwa ce fa, kuma idan da rai da lafiya yanzu aka fara, kar ki sake ɗarsawa ranki cewa akwai wani abu da zai gagareki komai wahalar sa, rayuwa sai da gwagwarmaya da faɗi tashi, musamman ga ɗan talaka. Kar wani abu ya ƙara razana ki, ko ki yadda ke daƙiƙiya ce zaki iya komai kema”
    Ta yi ajiyar zuciya sannan ta ce “Dan Allah da gaske Yaya Ussy?”

    Ya jinjina mata kai ya ce “Sosai makuwa, ki dubi rayuwarmu a cikin gidan nan, tun baki da wayo, har zuwa yanzu a cikin gwagwarmaya muke, farincikinmu kawai ki ke gani, amma kowa akwai kalar ƙalubalen da yake fuskanta, ki kalli mama ba ta yi karatu mai zurfi ba, amma ta cancanci a kirata jarumar uwa, ba lallai ki fuskanci me nake nufi ba a yanzu, amma ki saka maganganun nan a ranki akwai ranar da za su yi miki amfani. Amma ki tsaya a kan ƙafafuwanki, ki fuskanci abin da yake baki tsoro, ke fa jaruma ce, bai kamata sunan daƙiƙiya ya biki ba”

    Ruma ta ɗan yi shiru sannan ta kalli Usman ta ce “Yaya Usy, in sha Allah zan dinga mayar da hankali na yi karatu sosai na daina wasa”

    “Yauwwa ko ke fa, ai hakan ya fi deluwa”

    “Kuma zan cigaba da ƙoƙari, in zama mai ƙarfi sosai, duk wanda ya tsokane ni, in yi masa dukan tsiya in farfasa masa baki da hanci, in kakkarya mutum”

    Mama da take jin su ta ce “Ke kuma ba kya fatan ki girma ki yi hankali, sai rashin hankali ke ba kya fatan Allah ya shiryeki ki daina faɗace-faɗacen banzan man a matsayinki na mace, faɗa ba na ‘ya mace bane”

    Ruma ta ce “A’a mama, gara ki bar ni na koyi ƙarfi sosai”

    “Sai kuma ki yi ai”.

    Usman ya kuma murmusawa ya ce “Ba irin wannan ƙarfin ake magana ba, ƙarfin zuciya da kaifin basira wurin sarrafa duk wata Matsala da za ta tinkaro ki, kar ki bari matsalolin ki su razana ki, ko sau ɗaya kar ki bada wannan damar, ki turje ki dake ƙalubale duk girmansa, ki yi gaba da gaba da shi”

    Ruma ta ce “Mhmm, gashi dai hausa ka ke yi, amma bana gane me ka ke faɗa, sai na ji kamar ma wani yaren ka ke daban, ban wani gane me ka ke nufi ba”

    “Ni ma na san ba zaki gane a yanzu ba shekarunki da hankalinki babu lallai ya kai, saboda ke a yanzu ba ki sa wata damuwa ko matsala. Tashi ki zubo mana Abinci mu ci” Ruma ta miƙe ta tafi kitchen.

    Mama ta ce “Kai ma banda abinka, wannan zaka zaunar ka na wani gayawa wannan bayanan, me zata gane a ciki? Ita ban da wautarta da tambayoyin ta na rashin kan gado me ta sani?”

    Usman ya ɗan yi shiru sannan ya ce “Haka kurum mama ina jin tausayin yarinyar nan, jikina na bani za ta yi gwagwarmaya a rayuwa, gwagwarmaya a bugiren da ba zamu iya tsaya mata ba, ko yi mata wani taimako ba, gwagwarmayar da take buƙatar ta tsaya da ƙafarta ta cimma nasara”
    Mama ta ce “Tooo ikon Allah, to koma dai menene, ni dai addu’a kullum cikin yi muku ita nake, ba ku kaɗai ba, dukkan ‘ya’yan muslmai baki daya, Ubangiji Allah ya shiga lamarinku, ya tsare gabanku da bayanku, ya kula da rayuwar ku”

    “Amin mama, Allah ya ƙara miki lafiya da nisan kwana uwa ma bada mama”

    “Amin ya rabb”

    A ranar duk wanda ya shigo, sai ruma ta nuna masa kyaututtukan da aka bata, har a waya sai da aka kira mata yaya Abubakar ta gaya masa, tun ana tayata murna da Allah ya sanya albarka har ta fara ƙular da mutanen gidan. Dan hatta maƙwabta sai da ta shiga ta gaya musu ai tayi ƙoƙari a makaranta an bata kyauta.
    Da ta je Islamiyya kuwa, har ofishin shugaban makaranta ta je, shi ma ta gaya masa, ya tayata murna tare da sanya mata albarka, ta ƙarasa staff room bayan sun gaisa da malaman suma ta gaya musu ai a makarantar boko tayi ƙoƙari an bata kyaututtuka. Nan suka yi ta mata fatan alkhairi, ji take a duniya yau ta ƙure daɗi tayi abin da ba ta taɓa ba.
    “Malam to idan an idar da salla dan Allah a sanar”

    Wani malami ya kalleta ya ce “A sanar da me?”

    “Na yi ƙoƙari a makarantar boko mana, har na ciyo kyauta, word kusan ɗari biyu da hamsin fa na haddace yadda ake spelling ɗin su”

    “To amma ai nan ba makarantar boko ba ce ba, ki bari idan ki ka yi bajinta a nan ma, sai a sanar wa ɗalibai”

    Ruma ta ce “A’a malam gara ai a sanar, saboda masu ce mini daƙiƙiya su san ƙwaƙwalwata na aiki, wataran zan bayar da mamaki”.

    Malam Habibu ya yi caraf ya ce “Ƙwarai kuwa, dole a sanar da ɗalibai wannan namijin ƙoƙari da ki ka yi, nima ba rannan na yi ƙari kin iya ba, duk za a sanar kar ki damu” cikin jin daɗi ruma ta ce “Yauwwa malam na gode”

    Bayan tafiyarta ya yi dariya ya ce “Yanzu idan ba ku yi yadda take so ba, Allah kaɗai ya san wace tijarar zata yu, amma yanzu idan aka faɗa ɗin, za ta ji daɗi da ƙara samun ƙwarin gwiwa”.

    Ruma da ta ga an idar da salla, ana neman a watse ba a sanar ba, ta tafi ƙofar masallacin maza, ta leƙa ta ce “Malam Habibu kar ka manta fa, na ji ba a faɗa ba”.

    Malam Habibu ya ce “To bari a sanar, ai yakamata wannan abin arziki haka”

    Haka malam Habibu ya tashi ya ce “‘yan uwa ɗalibai da malamai, a taya ‘yar uwa murna, wato ‘ya ta rumaisa, bisa nasara da ta yi a wata gasa da aka shirya a makarantar bokon su, har ta samu kyaututtuka dan Allah ayi mata Addu’a, Allah ya ƙaro nasarori”

    Daɗi kamar ya kashe ruma, masu dariya na yi, masu jin haushi na yi.

    Huzaifa da suka yi salla sahu ɗaya da Yasir ya ce “Ka ji abin da wannan mara kan gadon ta yi ko?”

    “Bar motsatsiya, suma malaman da suka biye mata, idan ba tayi wasa ba sai na ƙona banzayen litattafan da aka bata, kowa ma ya huta”.

    Cike da annashuwa ruma ta tafi gida, ta je ta bawa mama labarin yau har a wurin salla, aka sanar da ta ci kyauta a makarantar boko. Tana shiga gidan ta tarar da Yaya Abubakar ya zo hutu, da kuma waa dattijuwar mata a zaune a tsakar gida.
    Da sauri ruma ta nufi dattijuwar ta faɗa jikinta ta ce “Gwaggo Atine, yaushe rabon da na ganki?”

    Dattijuwar ta washe baki ta ce “Dama ina zaki ganni, nayi-nayi da babarki ta din ga kai mini ke ina ganinki, amma ta ƙi saboda ina ƙauye”.

    Mama ta ce “Haba Yaya Atine, wallahi ba haka bane ba, kin san yanayin makaranta kuma ruma ba ta ji idan aka kai miki ita sai ta gallabe ku”

    Ruma ta haye kan cinyar matar cikin jin daɗi ta zauna.

    Matar ta ɗora da cewa “Ba wani rashin ji, a kawo mini ita a hakan ina son ta, duk rashin jin ta. Ɗan uwana ya ƙallafa rai a kan ta yana son ta, nima ina matuƙar ƙaunarta da na ganta shi nake tunawa amma ba za a kawo mini ita ba, sai wannan ƙartin ne kawai suke zuwa in da nake” ta yi maganar tana fashewa da kuka.

    Mama cewa take “Allah ya baki haƙuri, in Allah ya yarda za a dinga kawota”.

    Ruma kuwa ta kalli Gwaggo ta ƙyal-ƙyale da dariya ta ce “Dan Allah Gwaggo ki daina wannan kukan, ni wallahi fuskarki dariya take bani idan ki na yi, kin ga yadda ki ke yamutsa kuwa?”

    Yaya Aliyu ya ce “Ai gara ta fara gwada miki halin”

    Gwaggo ta tsaya da kukan ta ce “Rumaisatu, kukan nawa ne yake baki dariya?”

    Ruma ta ce “Eh mana, amma ki daina ce mini wata rumaisatu, sai ka ce wata masara, kowa aka saka masa suna mai daɗi a gidan nan, amma aka saka mini wata Rumaisa kamar masa”

    Gwaggo ta jinjina kai ta ce “Ikon Allah”
    “Gwaggo wai ina wannan ‘yar ta ki, mai kamar ni ɗin nan?”

    Jin ruma ta tambayi ‘yar autarta ya sanya Gwaggo yin murmushi ta ce “Au Lawisa tana nan ƙalau, ta na ta a gaishe ki, ita ana biki sun tafi da tuni tare zamu zo”

    Ruma ta yi dariya ta ce “Wai Lawisa, ai har gara nawa sunan ma da nata, wata lawisa kamar za ace lawashi, ta fini girma yanzu?”

    “A’a zaku yi tsayi ɗaya da ita”

    Ruma ta yi murmushi tana kaɗa ƙafa.

    Abubakar ya ce “Ruma ɗaga mata ƙafa mana”

    “A’a ƙyaleta, ai haryanzu yarinya ce, Allah dai ya kai ni auranku ke da Lawisa”

    Ruma ta ce “Amin, ki yi mini Addu’a, Allah ya sa na yi tsawo na isa aure, kuma Allah ya sa na auri kyakykyawa mai kuɗi sosai”

    Mama ta riƙe haɓa ta ce “Ruma, ƙanƙanuwarki da ke, har kin san wani miji mai kyau mai kuɗi?”.

    Gwaggo ta ce wa mama “Wai ke ina ruwanki da mu ne, muna hira kina saka mana baki” ta mayar da hankali kan ruma ta ce “Amin ‘yar albarka, Allah ya kai ki in da zaki huta, mu ci mu sha mu yi wadaƙa”.

    “Amin, kuma Allah ya sa na auri me kyau”.

    Aliyu ya ce”Da wannan shegen hancin naki kamar na aladae zaki auri me kyau?”

    Gwaggo ta ce “Ƙarya ka ke dan ubanka, wallahi kamar ta ɗaya da babanku, kuma hanci ne da shi har baka, in Allah ya yarda sirikina kyakykyawa ne kuma mai abin hannu, tun da ‘ya ta ba daga nan ba”

    “Gwaggo kin san wa nake so na aura?”

    “A’a sai kin faɗa”

    “Kina kallon wrestling?”

    Gwaggo ta ce”A’a ni ban san shi ba”

    ‘To ball fa?”

    “Ni ina zan ga wannan shirmen”

    Ruma ta ce “Da kina kallo, da na gaya miki wanda zan aura a cikin su”.

    Cikin son katse surutun da ruma ke yi ba kunya ba tsoro mama ta ce “Ruma tashi ki canza kaya, zan aike ki” ruma ta miƙe daga cinyar Gwaggo ta tafi sauya uniform.

    Tun da Allah ya sa Gwaggo ta zo gidan nan, ruma taɓara ta ƙaru, don ko me ruma za ta yi ba zata bari a yi mata faɗa ba, gashi kullum cikin faɗa take da mai sunan Baba, dan kome za ta yi idan ruma tayi laifi hukunta ta yake yi.

    “Wannan yaro da fuska kamar bajimin sa, ba ka da imani, wannan ‘yar tatsitsiyar yarinyar guda nawa take, da zaka dinga azabtar da ita wallahi Hauwa wannan ɗan naki mugu ne”
    Gaba ɗaya ruma da Gwaggo suka gallabi gidan nan, ruma kuwa aka samu tikitin rashin ji dan ma tana tsoron mai sunan Baba.

    Yau Malam Habibu yana babban aji, ruma tana tare da shi, yayi musu ƙari, tana ta wasanninta da ciye-ciye, sai da ya kammala yana amsa tambayoyi sannan ruma ta ce “Malam ka ce idan mace tayi mafarkin namiji sai ta yi wanka zata yi salla, to ni kuma kullum sai na yi mafarkin yayyena, Kuma ni sai zan tafi makaranta nake wanka watarana kuma mama ta ce bana fita tayi mini wanka, to yan…..
    Kan ta ƙarasa ‘yan ajin suka hau dariya, dan ba zaka taɓa cewa hankalinta na kan abin da yake koyarwa ba.

    Malam Habibu ya ce ” ‘ya ta ta kaina, ai wankan da mama take yi miki ya wadatar, duk ɗayane”

    Ta ce “Au ho, na gane”

     

    Tana dawowa daga islamiyya ta turke Abubakar ta ce “Yaya Sadik yau ka san meyafaru a makarantar islamiyya ?”

    Sadik ya ce “A’a”

    “Ka san na canza aji a islamiyya, saboda malaminmu baya ƙaunata, Ajin su Yasir kuma ya ce idan na ƙara zuwar musu aji sai ya dakeni, sai na koma ajin malam Habibu gaba ɗaya ajin ‘yan sauka”

    Abubakar ya ce “To ban da abinki kin taɓa ganin an fara gini daga roofing, ai daga tushe ake farawa”

    “Oho dai koma yane, wani karatu aka yi nake son na tambayeka, da zan tambayi malam Habibu na manta”

    “To ina jin ki”

    ” ‘yan ajin ne da su da wasu na ga wataran ba sa salla fa, ko su ƙi zuwa da Alqur’ani izifi sittin wai Haila suke yi. Na tambayesu sai suka ce mini wai ai mata ba kullum suke salla ba, idan ba su yi salla ba haila suke yi ko biƙi. Aikuwa nima na ƙi yin salla, wata prefect ta ce me yasa ba na salla nima na ce biƙi nake”

    Gwaggo da ta idar da salla ta ce “Subhanallahi” jin maganar ruman kamar saukar aradu.

    Ita kuwa ko a jikinta, ta cigaba “Shi ne ta ce dan ubana ni na isa in yi biƙi, na ce ba dai ubana ba sai dai na ta, kuma tun da nima biƙi nake ba zan salla ba, ashe wataran mata ba sa salla amma ni kullum mama sai ta ce sai na yi”

    Abubakar ya ce”To, wannan zancenku ne ke da maman ita zata baki amsa”.

    Ruma ta ce “Mama…..”
    Mama ta katseta ta hanyar cewa “Rufe mini baki, kar ki sake ki yi mini shirme, kuma ki tashi ki yi sallar da ki ka ce baki yi ba dan ubanki”

    “To mama ai idan ana biƙi ba a salla”

    “Biƙin ubanki, ke kin san meye biƙin ne?”

    “To meye biƙin?”

    “Ba zaki tashi ki yi sallar ba, sai na zane ki da bulugarin nan?”

    Ta kalli Gwaggo ta ce “To ke gaya mini”

    Kamar wadda ta tambayi meye wani babban zunubi Gwaggo ta ce “A’a ni babu ruwana, ga uwarki nan ta baki amsa ni zaki tambaya wannan babban al’amari ba a bakina ba, ‘ya’yan binki wayewar ku ta yi yawa”.

    “Ohh ni ruma, komai na yi laifi ne, ai shikenan”

    Tun daga lokacin ba ta kuma kula kowa ba, ta koma tayi shiru wai ita ta ji haushi.

    Har zuwa sallar magariba, ba ta sake kula kowa ba, Gwaggo ma ta gaji da yi mata hirar, amma Ruma taƙi saurarata.
    Yaya Sadik ne yayi gyaran murya ya ce “Ruma, wai ni kuwa idan kin girma me ki ke son ki zama ne? Da na je taron PTA ɗin ku an ce da kun shiga primary 6, za’a fara shirin common entrance, shi ne na ce idan kin shiga Sakandire me ki ke sha’awa Art zaki yi ko science?”

    Ta kalle shi ta ce”Wai in din ga drawing?”

    “Wane irin drawing kuma?”

    “To ai ji na yi ka ce Art, Art ba drawing ba kenan?”

    “A’a ba wannan ba”

    “Ni dai kawai sana’ar da zan samu kuɗi nake so, ko kuma in zama ‘yar sanda, in dinga tsayawa a titi ina bada hannu masu mota suna bani kuɗi, ko kuma a buɗe mini kanti, ko na zama mawaƙiya ko ‘yar film!”

    Ayshercool
    08081012143
    A TAIMAKA AYI SUBSCRIBING YOUTUBE CHANNEL ƊINA NA COOL HAUSA NOVELS, KO IN KOMA POSTING SAU ƊAYA A SATI 😒*
    [11/07, 4:25 pm] JAKADIYAR AREWA: ƘANWAR MAZA
    Na Aisha Adam (Ayshercool)

    MIKIYA WRITER’S ASSOCIATES

    https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

    Ku yi subscribing  YouTube channel ɗin
    @Cool Hausa Novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro.

     

  • Kanwar Maza 5

    Kanwar Maza 5

    P5

    Sak suka yi gaba ɗayansu, lomar da Yaya umar ya haɗiya ya ji taƙi wucewa tana kai komo a wuyansa kamar zata dawo. Amma ya basar kamar bai san me suke faɗa ba.

    Huzaifa kuwa tsam ya miƙe yana faɗin “Ai sai da na ce kar ki saurareta ki ka ƙi, sai ku san abin da zaku gaya mata” yana maganar ya bar tsakar gidan.
    Mama ta rasa mai zata cewa Ruma da hankalinta zai ɗauka, sam yarinyar bata tunani dai-dai da shekarunta.

    “Wai ya na ji kin yi shiru? Me kuma nayi?” Ta yi maganar cikin taɓara.

    Cikin ƙarfin hali mama ta ce “Ke a ina ki ka ji wannan kalmomin da ki ka tambayeni?”

    “Mama ya kuma ki ke tambayata bayan nima tambayarki nayi”

    “Ki amsa mini dan ubanki” mama tayi maganar a hasale.

    Ta ɗan cuna baki sannan ta ce “Ba wani ne ya gaya mini ba, kece ki ke jin radiyo ranar, na ji ana cewa ayi wankan janaba idan aka yi ko me? Oho na manta shi ne nake son na san meye janaban, kuma meye wankan. Shi kuma fayɗe idan aka faɗa a radiyo sai na ga hankalinki ya tashi kina girgiza kai kina Allah ya tsare zuriyar musulmi baki ɗaya, shine nake son na san menene?”

    “Tirƙashi, aiki ga mai ƙareka mama Allah ya bamu alkhairi ” Yaya Aliyu ya faɗa yana ƙoƙarin shigewa ɗaki.

    Yaya Usman ya ce “Kuma duk abin da ake faɗa a radion babu wanda ki ka riƙe sai wannan?”

    Ruma ta ce “To ai akwai wasu ma, mantawa nake yi ne sai yanzu na tuna”

    Mama tayi ajiyar zuciya ta ce “Kina jina ko Ruma?”

    “Eh ina jinki”

    “Yauwwa, zan gaya miki zan miki bayani, amma ba yanzu ba sai an kwana biyu, yanzu ko na yi miki bayani ba zaki gane ba, kuma nan gaba ko ba a gaya miki ba ma, zaki gane da kan ki”.

    Cike da yarinta ta ce “Nan da kwana biyu ranar asabar kenan, in Allah ya yarda zan tuna miki ki gaya mini”

    “Ba wanna kwana biyun nake nufi ba hansai, sai kin ƙara girma da hankali”

    Cikin mamaki Ruma ta ce “Yaushe kuma zan ƙara girman da hankali, wancan karon ma fa na taɓa tambayarki menene MATA MAZA, ki ka ce mini sai na girma, na tambayeki menene haila ki ka ce mini ba yanzu ba, amma da zan yi wani abun sai ki ce ina girma amma bana hankali wane irin girma ki ke son nayi to?”

    “Ke tashi ki wuce ki kwanta dan uwarki, kawai kin saka mutane a gaba da tambayoyinki na shirme, ko a gidan uban wa ki ke jiyo wannan manyan maganganun oho miki, wuce kan na karya ki biyu, ba zaki tambayi abu daidai da hankalinki ba sai wanda ya fi ƙarfin kanki” sai da ta kalli in da Yake zaune yana bata umarni, bayan da fari yayi kamar bai san me suke yi ba.

    A hankali ta tashi ta nufi ɗaki, tana tunanin menene aibun tambayarta?.

    Tafiya ta yi ɗaki, ta gyara shimfiɗarta ta kwanta, tana tunanin meyasa kullum tayi tambaya sai ace mata ba yanzu ba sai an kwana biyu, ko ace wai tana tambayoyin da suka fi ƙarfin ƙwaƙwalwarta me hakan yake nufi kenan?. Da wannan tunane-tunanen bacci yayi awon gaba da ita.

    Da safe tana kwance tana baccinta, duk samarin gidan sun gama komai, har abin karyawa, Kasancewar Asabar ce Ruma tana ta baccin asara, ba aikin fari balle na baƙi, har ƙasan ranta tana matuƙar jin daɗin rashin zuwa makarantar allo da ba ta yi, saboda tana samun isasshen lokacin bacci.
    Ji take ina ma ace bokon ma ta daina zuwa, idan tayi baccinta ta ƙoshi da yamma ta kfa suyar wainar fulawa a ƙofar gida ta tara ‘yan kuɗaɗenta.
    Baccin yayi mata daɗi, tayi nisa sosai a duniyar mafarkai kala-kala, ta ji kamar daga sama ana taka mata ƙafa.
    Buɗe ido tayi a hankali, amma taƙi motsawa, tana son ta tabbatar da a zahiri ne ko duk cikin mafarkin ne.
    Ji tayi an kuma zungurarta da ƙafa, ba tare da ta waiwayo ba ta ce “Wallahi Huzaifa zan maka rashin mutuncin da baka taɓa tunani ba, kar ka sake takani”
    Bai ji kashedin ba, ya sake haurinta da ƙafa, “Allah ya isa wallahi, kuma ba zan tashi ba” tayi maganar tana sake dunƙulewa a wuri guda.

    Ƙashin bayanta ya kuma daka da ƙafarsa, ta yinƙuro a matuƙar zafafe, da nufin ta kafa masa haƙora ko a ina ne, amma me tayi tozali da Umar a tsaye a kanta.
    Jikinta ne ya hau tsuma, ta ma rasa me za ta yi, ko ta ce.
    Shiru yayi yana nazartarta, daga bisani ya ce “Ki tashi ki je ki ki yi wanka ki karya ina jiranki, kuma idan ki ka ɓata mini lokaci kin san sauran”

    Saroro tayi tana kallonsa, da ba ta gama fahimtar me yake nufi ba.

    “Za ki tashi ko sai na yi ball dake?” Cikin hanzari ta tashi, ta ɗauke katifarta ta nufi banɗaki tana mamakin to ina zasu je, kar dai boarding ɗin zai kaita kamar yadda ya ce. Gabanta ne ya faɗi ta fara tunanin ko ta gudu.
    Kai tsaye ta nufi banɗaki, tana shiga ta tarrar da an haɗa ruwan wanka, ba tayi tunanin ko ruwan waye ba, ta rufe ƙofa ta hau wanka da shi.

    Yasir ne ya nufo banɗakin da sauri, wuyansa ɗauke da soson wankansa, zai shiga banɗaki saboda ya kai ruwan wankansa, amma yana zuwa ya ga ƙofar a rufe.
    Iya ƙarfinsa ya hau dukan ƙofar yana faɗin “wani ɗan rainin hankalin ne ya shiga bayan na kai ruwa?”

    Gyran murya tayi masa, tsaki ya ja ya ce “Ki hanzarta zan yi wanka na fita na kusa makara.
    Tun yana saka ran zata fito har ya tashi ya fara zaginta yana bugun ƙofar.
    Ba ta da tabbacin wankan da tayi ta fita, ta buɗe ƙofar banɗakin, zagi ya dinga surfa mata, bai kai ga rufe baki ba, idonsa ya sauke a kan bokitin da ya haɗa ruwa, Ruma ta zubar da komai.

    A hasale ya zura hannu ya janyota tsakar gida ya ce “Wallahi yau mai ƙwatarki sai Allah, na zuba ruwa na kai zan fita makaranta kina can kina bacci, amma ki zubar mini”.
    Babu alamar nadama ta tsuke fuska ta ce “To ba Yaya Umar ne ya ce nayi wanka ba”

    Wani ranƙwashi ya yi mata a tsakiyar ka, da azabar zafinsa ya sanya ta durƙusa a kan gwiwoyinta, tana sakin wani irin kuka mai sauti.

    Yaya Umar ya ɗaga labulen taga ya leƙo ya ce “Ƙyaleta tun da ka daketa” ba ƙaramin ɓaci ran Yasir yayi ba, dan niyyarsa sai ya yiwa Ruma dukan da duk taurin kanta sai ta bashi haƙuri.

    Kasa karyawa tayi saboda kuka, tana tsaye tana duru-durunta, Umar ya shigo hannunsa riƙe da leda ya miƙa mata ya ce “Maza ki shirya ki wuce mu tafi”

    Karɓar ledar tayi tana duddubawa, uniform ne na islamiyyar su Huzaifa, makarantar da ta ce ko aljanna ake rabawa a cikinta ba zata yi ta ba, saboda azabar tsaurinsu, asabar da lahadi tun tara sai biyar ake tashi, ba a fashi balle makara, ga haddar Alqur’ani ake yi da gaske ba wasa ba.
    Saroro tayi tana kallon Yaya Umar, cike da rashin fahimta amma ta kasa yi masa Magana.

    Wata uwar harara da ya yi mata ne, ya sanya ta shiga ɗakin Mama, ta saka uniform ɗin jikinta sai tsuma yake yi, ita ta san har ga Allah ba zata iya zaman makarantar nan ba.
    Mama dai ba ta ce musu kanzil ba, ya tasa ta a gaba suka tafi.

    A zuciyarta tana ta addur Allah ya sa makarantar suce ba zasu karɓeta ba, bata tunanin ko su Huzaifa sun san za a sakata a makarantar su, dan da sun sani cewa zasu yi basu yadda ba.

    Tun da suka shiga makarantar, tashin karatun Alqur’ani kawai ka ke ji, daga kowacce kusurwa, kuma da alama ɗaliban makarantar a nutse suke.
    A ofishin shugaban makarantar aka titsiye Ruma ana yi mata interview, amma ba abin da ta iya, izifi biyun da aka yi mata tambayoyi da ƙyar ta kai.

    Umar ya shiga tunanin tsawon lokacin da Ruma ta shafe tana zuwa makarantar allon nan, me take yi da ta kasa izifi biyu.

    Ransa ba ƙaramin ɓaci ya yi ba, ya hau ta da faɗa a gaban mutane.

    Cikin kuka ta ce “Wallahi yaya na iya karatu”

    “To uwar me ki ka iya, kin kasa izifi biyu”

    Ta ɗan yi shiru sannan ta ce “Eh na iya, amma ba a allona na rubuta na iya ba, na allon wani almajirin malam babba ne, idan aka ƙara masa nake iyawa, ni kuma sai na kasa nawa”
    Murmushi malamin yayi ya ce to biya mu ji “Tiryan-tiryan da ƙira’ar warsh, take karanta suratul Yusuf, ko tuntuɓe babu”

    Shugaban makarantar yayi mata kabbara ya ce “Ahh gaskiya ‘yar baiwa ce, zamu san a in da yakamata mu sanyata, daga islamiyyar har tahfiz ɗin, zaku ga sauyi in sha Allah zata yi karatu”

    Yaya Umar ya ce “To masha Allah, haka muke so” aka saka wani malami ya kai Rumaisa aji.
    Tare suka fito da Yaya Umar, ya dubi Ruma ya ce “Ga makaranta nan na kawo ki, idan kin ga dama kiyi karatu, idan baki ga dama ba nan ma ki yi musu halin naki, kiga abin da zai biyo baya” ta sunkuyar da kai kamar ta Allah, yayi faɗansa ya gama ya tafi.

    Gaba ɗaya ba tayi murna da zuwa makarantar nan ba, haka aka kai ta aji ta nemi wuri ta zauna.
    Gaba ɗaya ɗaliban sun mayar da hankali, suna ta zuba karatu, Ruma kuwa sanyin fanka ne ke nema ya sanyata bacci.

    “Ke ya ba kya karatun?” Cewar malamin da yake kula da karatun nasu.

    Kallonsa ruma tayi, shima uniform ne a jikinsa na ɗalibai, amma ya tsaya zai yi mata iyayi.

    “Sabuwar zuwa ce ni, ban iya wurin ba” ta bashi amsa kanta tsaye.
    Bai kuma saurararta ba, ya cigaba da tilawar tare da sauran ɗaliban.

    Ta dubi wata ɗaliba ta ce “Ke, dan Allah nan aji nawa ne?”
    Ɗalibar ta kalli Ruma sannan ta ce “Aji ɗaya ne”

    “Kutmar, ban gane aji ɗaya ba, kina nufin aji ɗaya aka kawo ni?”

    “Eh mana” yarinyar ta bata amsa.

    Ruma ta jinjina kai ta ce “Lallai ma an raina mini hankali, wallahi ba zan zauna a aji ɗaya ba”.

    Ɗaliban suna ta tilawarsu, yayin da malamin yake jin haddar wasu, amma Ruma hankalinta na kan yadda zata fita daga ajin, dan zaman ajin ya isheta.
    Daga bisani ta koma gefe ta hau gyangyaɗi.
    Lokacin da aka fita break, yunwa ta saka Ruma a gaba, dan ba ta karya ba Yaya Umar ya taso ta a gaba.
    Ɗalibai ne masu yawa sosai a makarantar, dan makarantar sananniya ce sosai a unguwar, dan kusan babu ta biyunta. Daga yanayin mayar da hankalin su Huzaifa da yadda suke bayar da labarin tsananin makarantar ya sanya ta ji ba ta son makarantar sam.
    Tun da aka fita break da salla, wuri ɗaya ta samu tayi zamanta tana bin ko ina da kallo, sai da ta gaji ta tashi ta fara dubawa ko zata ga Yasir ko Huzaifa amma babu wanda ta gani a cikinsu. Haka aka koma aji ba tare da ta samu komai ta saka a cikinta ba.

    Aka dawo aji aka ɗora da karatu babu ƙaƙƙautawa, gaba ɗaya Ruma ta gaji da zaman makarantar. Malamin ajinsu ya fara yi musu ƙari, ta buɗe Alqur’anin ta ajiye, ta cigaba da gyangyaɗinta.

    Tun da Ruma ta shigo ajin ɗazu yake kallonta, sam ya lura babu alamar son karatun a tare da Ruma, daga hamma sai bacci take yi.
    Ƙarshe ta haɗa jakarta ta cewa malamin fitsari take ji, ya ce taje tayi, ta ɗau jakarta ta bar ajin.
    Zagayawa take tana lelleƙa azuzuwa ko Allah zai sa taga mutum ɗaya a tsakanin yayyenta, dan har wani irin jiri take ji, dan a duniya ba ta wuce ƙarfe ɗaya ba ta ci abincin rana ba, yau sai ga ta har azahar babu ko karin kumallo.

    Ajinsu yayi tsit, sun tattara hankalinsu a kan ƙarin karatun da ake yi musu, kamar daga sama ya jiyo muryarta “Huzaifa, dama nan ne ajinki tun ɗazu nake neman ku” gaba ɗaya ajin aka waiwaya don ganin waye yake wannan wautar.

    Kallon da ake yi mata bai sanya ta nutsu ta daina maganar ba “ka ganni a makarantar ku ko? Hmm ɗan zo ka ji wata magana mana”.

    “Ke wacece haka, baki ga karatu muke yi ba?” Malamin yayi maganar yana kallon tagar da Ruma ke tsaye.

    “Yunwa nake ji, shiyasa nake nemansa” ta faɗa tana sake leƙo cikin ajin.

    Shi Huzaifa mamaki ne ya cika shi, yaushe aka saka Ruma a makarantar nan bai sani ba?.
    Ganin babu komai a kan Ruma sai wauta ya sanya malamin ya kalli Huzaifa ya ce “Je ka ka sallameta”

    Cike da jin kunya ya tashi ya fita, yana fitowa ta tare shi da murmushi, shi kuma ya haɗe rai ya ce “Uban waye ya kawo ki makarantar mu?”

    Kallonsa tayi ta kalli harabar da suke ta ce “Sai ka ce wata makarantar arziki, nima ban ce a kawoni ba, wayewar garin Allah kawai mai sunan Baba ya bani uniform ya kawoni, ni wallahi gara na koma na bawa malam babba haƙuri, in koma makarantar allon mu ba zan iya wannan jidalin ba”.

    “Ke dalla rufewa mutane baki, daga zuwanki kin fara nuna hali, kawai ki zo ta window kina kirana saboda hauka, maimakon ki yi sallama ki tambayi malamin, ke Allah sai kin bar makarantar nan, dan ba zaki zubar mana da mutunci ba”.

    “Saboda gani annoba ko?” Tayi maganar tana hararasa.

    “To ba gara annoba ba, idan aka samo maganin ta shikenan ba, ke kuma maganinki sai Allah, yanzu uban me zan miki?”

    Ta yatsuna fuska ta ce “Ni yunwa nake ji, kuma wallahi sonake na tafi gida”
    Huzaifa ya ce “Lallai baki da hankali, to ke da gida sai ƙarfe biyar, wuce muje ajin su Yasir gara mu raba abin, da ki dinga yi mini ni kaɗai”tura baki tayi, ta rungume jakarta, Huzaifa ya sanyata a gaba yana mita suka nufi ajinsu Yasir.
    Ita kuma sai mita take, a kan daga yau ba zata sake zuwa wannan makarantar ba da ake uzzurawa mutane.

    Yasir kansa salati ya dinga yi da salallami “Dan girman Allah meyasa mai sunan Baba zai yi mana haka, ya saka yarinyar nan a makarantar nan ba a shawarce mu ba, wallahi mun kaɗe”

    “Oho muku, ku kwantar da hankalin ku, ni ba kuma zuwa zan yi ba, kawai ku bani Abinci”
    Yasir ya dungure mata kai ya ce “Shegen ci kamar kazar hausa” suka sakata a tsakiya suna tafe suna zaginta, suka saya mata awara da ruwa ta cinye tsaf, sannan suka korata aji.

    Ko da ta isa aji, tuni an gama karatun Alqur’ani, ana jiran wani malamin ya shigo.

    “Ya aka yi daga zuwa fitsari ki ka daɗe, gashi an gama ƙarin Alqur’ani, sati mai zuwa idan Allah ya kaimu zamu bayar da hadda” cewar yarinyar dake kusa da Ruma.
    Ruma ta kalleta ta ce “Ina aka biya ɗin?”.
    Yarinyar ta buɗe Alqur’anin tana nunawa Ruma ta ce “Rabin shafi aka ƙara, gobe in Allah ya kaimu ma za a ƙara rabi, feji ɗaya kenan sati mai zuwa idan Allah ya kaimu sai ki kawo haddar”.

    Cikin ko in kula Ruma ta kawar da kanta gefe, alamar zancen yarinyar ma bai shigeta ba.

    “Ya na ji kin yi shiru ne? Ki buɗe sai na koya miki, idan fa baki iya ba babu ruwan ya sayyadi da sabuwar zuwa ce ke, zaneki zai yi”.

    Rumaisa da shishshigin yarinyar ya fara ƙular da ita ta ce “To a kasheni mana kar a barni da rai, ba cewa aka yi nan aji ɗaya bane ba, kuma sai a ƙara mini rabin shafi, kuma wai na haddace yo ta ina zan iya ni, nifa a makarantar da na baro sai nayi wata ina nanata aya biyu nake iyawa, wannan karatun ma na san ba zan iya ba sai dai ayi kwaɗona da mai da yaji a cinye” galala yarinyar ta bi Ruma da kallo ta jinjina kai ba ta sake cewa komai ba.

    Bayan an kaɗa ƙararrawar tashi, malamin da ya yi mata interview ya kirata ya gaya mata cewar za’a fara karɓar haddarta daga tushe, sannan za ta dinga yi tana haɗawa da wanda ake yi musu a aji.
    Da yake ma bata fahimci bayanin da yayi mata ba, hankalinta na kan ta tafi gida, dan ta san ba iyawa za ta yi ba, kuma ta gama yanke shawarar daga ranar ba zata sake zuwa ba sai dai Yaya Umar yayi mata abin da ya ga dama.

    Ko su Huzaifa ba ta nema ba, ta nufi gida.
    Ɗa da uwa sai Allah, wuni gudan da mama tayi babu Ruma a kusa da ita duk sai ta damu, ta ji gidan babu daɗi, gashi tana ta tunanin ko abinci Ruma bata tafi da shi ba, balle ta samu ta ci haka mama ta wuni sukuku.
    Tana tsaka da tunanin Ruman ne, ta ɗaga kai taga Ruman a tsakar gida.

    “Meye haka, babu sallama ki shigo ki tsaya?”

    Ruma bata amsawa mama ba, sai kumbura baki da take yi, ta cire hijjabinta da jakar makarantar ta dungurar a wurin ta tafi kitchen tana dube-dube.

    Ba ta saurari mama ba sai da ta ci ta ƙoshi, Sannan ta dubi mama ta ce “Ni fa mama gaskiya ba zan sake zuwa makarantar nan ba”.

    “To ai ba ni zaki gayawa ba, wanda ya saka ki a makarantar zaki gayawa”.

    “Mama kin ga uban dukan da ake yi a makarantar nan kamar an samu bayi, kuma dan rainin hankali wai aka kai ni aji ɗaya ni za a kai aji ɗaya saboda raini, to wallahi makarantar malam babba zan koma ba zan iya ba”

    Mama ta girgiza kai kawai, ta cigaba da aikin da take yi, Ruma ta saki baki ta dinga zuba tana cin alwashin ba zata sake zuwa ba.
    Huzaifa ne suka yi sallama shi da Yasir, mama ta amsa musu. Basu kai ga zama ba suka hau mita.

    “Mama dan Allah meyasa aka saka yarinyar nan a makarantar nan ba tare da shawarar mu ba? Kin san halin yarinyar nan tun a yau ta fara nuna halinta”.

    Ruma ta ce “Sha kuruminka ni ba komawa zan ba, daga yau ko za ayi ƙuli-ƙulina ba zan koma ba, wai saboda tsabar abu wai ƙari shafi guda, kuma wani satin ka kawo hadda, ni aya biyu nake iyawa waye zai yi wannan karatun taɓ ga uban duka wallahi ba zan sake zuwa ba

    Yasir ya ce “Ai makarantar mu ba ta daƙiƙai ba ce ba, ki koma inda ki ka fito ba zaki zubar mana da mutunci a makarantar nan ba”.

    Ba tare da sun san Umar yana gidan ba, yana ɗaki a kwance suke ta wannan zubar.

    Tsuru-tsuru suka yi, musamman ruma da ta fi zaƙewa, sai ganinsa suka yi ya fito tsakar gida.

    “To dan ubanki ki daina zuwan kin ji ko, daga yau kar ki sake zuwa ki ga yadda zan yi da ke, kuma na gaya musu ba kya jin magana, idan har ba ki yi karatu ba su kama ki su zane ki”

    Ruma a ranta ta ce “Ai wallahi sai na yi abin da za a koreni waye zai zauna ana jibgarsa kamar jaki”

    Ya kalli su Yasir ya ce “Ku kuma, kune zaku dinga tsayawa a kan karatunta, ku zaku dinga koya mata dan daƙiƙiya ce, duk daɗewar da ta yi tana zuwa makarantar allo ta kasa kawo izu biyu, sai karatun wani ta je tana iyawa, daƙiƙiya ki yi musu shirme na bayar da damar a zaneki”

    Kawar da kai Ruma tayi gefe, Umar ya gama bala’insa ya bar gidan.

    Yana ficewa daga gidan, Ruma ta dasa wa mama kuka, a kan lallai sai ta saka Yaya Umar ya cireta daga makarantar, mama ta ce babu ruwanta.

    Ko da wasa Ruma ba ta sanya a ranta za ta yi wannan karatu ba, dan idan za a kasheta ba ta ma san in da aka ƙara musu ɗin ba, ta cigaba da sabgoginta.

    Da sati ya zagayo zata koma makaranta, sai da a ka kai ruwa rana, tana kuka su Huzaifa suka sanyata a gaba zuwa makaranta, suna tafe suna zaginta suna mita an haɗasu da alaƙaƙai.

    Yau mama ta bata kuɗin makaranta, dan haka ta tsaya ta sayi goriba a ƙofar shiga makarantar.
    Duk da babu malami a ajinsu, amma kowane ɗalibi ya nutsu sun haɗa baki suna ta tilawa.

    Taɓe baki tayi, ta samu lungu ta zauna, ta kashingiɗa tana cin goribar ta a nutse.
    Shigowar malamin bai hanata cigaba da hangale baki tana gwaigwayar goribarta ba.
    Ba ƙaramin ƙulewa malamin yayi ba, tun a wancan satin ya lura ba ƙaramar gaɓuwa ce ba yarinyar.

    Yayi mata alama da hannunsa ta je, ta tashi ta fito da jakarta da goribarta a hannu ta ce “gani”

    Ya ce “Yauwwa, ta kan ki zan fara jin karatu yau, ɗauko Alqur’anin ki ki karanta ƙarin da na yi muku, sannan ki bani hadda” ɗan waro masa idanuwanta tayi sannan ta ce “Gaskiya ban iya ba wallahi, karatun yayi yawa ina laifin aya ɗaya ko biyu”

    “Koma gefe ki tsaya” babu ban haƙuri babu komai ta koma gefe ta ja ta tsaya.

    Ya cigaba da sauraron tilawar ‘yan aji, Ruma kuma ta mayar da hankali a kan cin goribarta, ya ɗaga kai ya kalli Ruma, wani irin takaici ya ƙule shi ko a jikinta abin da ya dameta kawai take yi, ya ce “Ke zo nan”

    Ta ƙaraso ta tsaya, miƙewa yayi ya ɗaga bulala zai daketa.
    Ta ƙwalalo ido ta ce “Kar ka dakeni ba a dukana” bai saurari ruma ba, ya zuba mata a ƙafarta har sau biyu.

    Wani uban ihu ta ƙwala, ta zube a kan ƙafarta tana jujjuya kai.
    Gaba ɗaya ‘yan ajin suka yi shiru suna kallonta, sai a lokacin da ya daketa ya huce sai kuma ya sha jinin jikinsa ganin uban kukan da take yi.

    “Wallahi ni sikila ce ba a dukana, shikenan ba zan iya tafiya ba” gaban malamin ne ya faɗi, amma ya maze ya cewa ‘yan ajin su cigaba da karatu.
    A ƙalla ruma ta shafe awa guda tana kuka babu ƙaƙƙautawa kuma taƙi tashi daga wurin, wai sikilarta ta tashi.

    Abu kamar wasa magana har kunnen malamai, kasancewar malamin nasu, ɗan ajin da suka yi sauka ne yake koyar da su, ba cikakken malami bane a makarantar.
    Malamai suka taru a kan ruma, amma taƙi tashi wai sikila ce da ita, ba zata iya tashi tsaye ba.
    Malamin nasu jikinsa sai rawa yake yana cewa “Wallahi bai san ba ta da lafiya ba”

    Malamin da yayi mata interview ya ce “Kuma ni a form ɗinta yayanta bai rubuta tana da wani ciwo ba, ina ne gidanku?”

    “Ni ba zan gane hanyar gidan ba, akwai yayyena a makarantar nan ku kira mini su su kai ni gida in ga mama zan mutu”

    “Su waye yayyen naki?” Nan gaya musu ajinsu Huzaifa.
    Huzaifa yana can yana karatu aka kirashi, yana zuwa ajinsu ruma ya ganta zaman dirshan malamai sun kewayeta.
    Nan suka yi masa bayani, turus yayi yana kallon ruma yana son gano ko makircinta ne, dan shi a iya saninsa ruma ba ga da wata sikila, ban da zazzaɓi ba ta ciwon uban komai, amma a ina ta samo wata sikila?.
    Ya miƙa mata hannu ya ce “Taso in mayar da ke gida”

    “Ni na kasa motss ƙafata ciwo take mini” tayi maganar cikin kuka.

    Huzaifa ya durƙusa ya ce “To hau bayana na mayar da ke” aikuwa ta ja jiki, ta hau bayansa ya ɗau jakarta ya ce bari ya kai ta gida.

    Sai da suka yi nisa sosai da makarantar sannan ya sauketa, aikuwa ta tsaya cak a kan ƙafafuwanta.

    Ya kalleta ya ce “A gidan uban wa ki ke da sikila?”

    “To gani nayi za a kasheni da duka, naga a makarantar bokonmu ba a dukan wata me sikila, da na ji zafin dukan sai na ji kamar nima ina da sikilar”.

    Galala ya bi ruma da kallo, ‘yar mitsila da ita amma ta iya makirci haka.

    “To mu je ki yiwa Yaya umar abin da ki ka aikata”

    Marairaicewa tayi ta ce “Dan Allah kayi haƙuri”

    “Wallahi ba zan goyo ki a banza ba, ko ni sai na miki shegen duka yau” yana gama maganar ya danƙeta ya saɓata a kafaɗarsa dan zata iya ƙwacewa ta gudu.

     

     

    Ayshercool
    08081012243
    [22/06, 9:49 pm] JAKADIYAR AREWA: ƘANWAR MAZA
    Na Aisha Adam (Ayshercool)

    MIKIYA WRITER’S ASSOCIATES

    https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

    Ku yi subscribing  YouTube channel ɗin
    @Cool Hausa Novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro.
    Ku yi following ɗina a arewabooks a kan account ɗina na ayshercool7724
    Ko watpad Ayshercool7724 kowanne a cikin manhajojin za ku iya samun litattaiafaina da na yi a baya, da wanda nake yi a yanzu na gode.

     

    *AFUWAN BAN EDITING BA*

  • Kanwar Maza 3

    Kanwar Maza 3

    Page3

    ‘yan matasan yaran maza sun girmi Rumaisa, kuma duk da haka ƙarfin namiji da na mace ba ɗaya bane ba.
    Tana cikin tafiya ta ji ana ke!ke! Ta tsaya waiwaya ta ga da wa ake.

    tawagar yara ta gani sun nufota gadan-gadan, tana ganinsu ta san masu dukanta ne, sam bata karaya ba, maimakon ta gudu sai ta durƙusa ta fara kwasar duwatsu, ta shirya duk wanda ya kawo kai, sai ta ƙwale masa kai da dutse.

    Amma a haka sai da wasu daga cikin su suka cim mata.

    Sani Yayan Habiba, ya na zuwa ya kwarfeta da ƙafarsa ta faɗi ƙasa, wani danƙo ya ɗauko a aljihunsa, ya fara dukanta da shi, duka take kai masa ko ta ina da allonta har ta samu ta tashi tsaye da ƙyar a kan ƙafafuwanta.

    Ta yi kukan kura ta kafa masa haƙora a kafaɗarsa, tsananin azabar zafi ya sanya ya kurma wani uban ihu ya ja da baya, dan har ƙashinsa ya ji haƙoram Ruma, sai ka ce mayya.

    Ganin ta gigita Sani, wasu daga abokan nasa kuma suna fama da raɗaɗin jifan da suka sha, ya sanya ta durƙusa ta ɗauki takalminta da hijjabinta a hannu, ta tsula da gudun tsiya.
    Rufa mata baya yaran suka yi, suna a taro ta, amma kamar walƙiya haka take sheƙa da gudu, ba ta tsaya a ko ina ba sai da ta kai filin ball ɗin su Yaya Aliyu. Suna tsaka da ball, sai ratsa cikin ƙartin mazan nan take sai gata a tsakiyar filin da maza ke uban gudu suna ball, ta cinma Aliyu a tsakiyar filin ƙwallon ta rirriƙe shi.

    Mamaki ne ya kama shi, ganin hijjabinta a hannu, kanta sai hula idanunta duk sun yo waje, tana ta haki tana waige-waige.

    Riƙeta yayi yana tanbayarta lafiya? Wasu daga cikin abokansa suma suka tsaya suna tambayarta ko lafiya, amma taƙi magana sai ajiyar zuciya take yi.

    Aliyu ya ja ta gefe, ya sanya mata hijjabinta, ya kalleta a tsanake ya ce ‘Menene?” Shiru ta yi bata yi magana ba sai sauke numfashi take.

    Haushi ne ya fara kama shi ya ce “Dan ubanki menene, me aka yi miki kika biyoni nan cikin maza?” Yayi mata maganar a hasale.

    Fara gaya masa abin da ya faru tayi, kuka ya ƙwace mata.
    Ɗan shiru yayi sannan ya ce “Amma ina fatan baki yi kukan a gaban yaran ba?” Ta jinjina masa kai alamar eh.
    “Kin taimaki kanki, dan da kin yi musu kuka wallahi sai na ƙara miki”.

    Cikin shesheƙa ta ce “Ban yi ba”

    Aliyu ya ce “Bari na canza kayana muje, ɗaya bayan ɗaya ki rakani gidajensu sai naci uban yaran nan, dani suke zancen”

    Ya zaunar da ita a gefe, aka cigaba da tambayarsa meya sami Rumaisa ya ce musu babu komai, su cigaba da ball ɗin su, shi zai tafi.

    Su Sani kuwa tun da Allah ya sanya Ruma ta ɓace musu, suka haƙura da binta, amma suka yi alwashin sai sun kuma saka ranar da zasu naɗa mata duka, dan tayi musu ɓarna sosai.

    Suna tafe a hanya, Aliyu ya ce “Ke amma ba a banza zan je rama miki ba, sai idan ki yadda zaki wanke mini kayan ball ɗina da takalmina”.

    Cikin hanzari ta ce “Eh na yadda, zan wanke maka”
    ya ce “To shikenan”

    Ya sakata a gaba har ƙofar gidan su Habiba, Aliyu ya aika yaro yace a kira masa Sani.
    Sani ya zata a cikin abokansa ne wani yake nemansa, yana ta fama da kafaɗarsa saboda cizon da Rumaisa tayi masa, sai ka ce an sare shi da manjagara a wurin ba haƙorin ɗan Adam ba, ga Habiba ita ma sai kuka take, leɓe yayi suntum ya kusa haɗewa da hancinta, bakin yaƙi rufuwa saboda dukan da ta sha da allo a fuska, sai da bakin ya fashe, banda dukan da ta yi mata a ka da allon, da take jin tamkar an mata rawani da tukunyar ƙarfe saboda nauyin da kanta zuwa fuskarta yayi mata, ba ta iya banbance a wani sashi na fuskarta hancinta da bakinta suke.

    Sani ne ya fito yana waige-waige, yana neman wanda ya aiko a kirashi, Aliyu yayi caraf ya danƙe shi.
    Zazzare ido Sani ya hau yi, Aliyu ya ce “Kai, kaine ka tattaro abokan ka ka daki Ruma ko?”

    Cikin fitsara Sani ya ce “Nima ƙanwata ta daka, kuma ta ɓatar mini da tayata”.

    “Kuma saboda kai mahaukaci ne, sai ka tattaro abokan ka maza su daketa, saboda baka da tarbiyya ko? Meyasa ba ka bari ƙanwarta ka ta rama da kanta ba?”.

    Fizge-fizge Sani ya fara, yana yiwa Aliyu rashin kunya, aikuwa Aliyu ya dinga kifa masa mari, har sai da bakin Sani ya mutu, fuskarsa duk tayi ja. Ya saka shi a gaba zuwa gidan abokansa da suka yi yinƙurin dukan Rumaisa.
    Duk da irin ɓarnar da Ruman ta musu da duwatsu, hakan bai hana Aliyu kama yaran ɗaya bayan ɗaya ya zane musu jikinsu ba, sannan ya saka Ruma a gaba yana rarrashinta suka tafi gida.
    Ko da suka je gida, yanayin Ruman Mama ta kalla ta ga kamar ba ta da gaskiya, amma ta share ba ta kula ta ba, dan idan ta biye wa halin Rumaisa kullum sai ta daketa.

    Da daddare bayan sallar isha’i duk suna zaune a tsakar gida, Rumaisa na ta tunanin me zata ci yau, dan yau ma maƙiyin na ta Mama tayi, wato tuwo, Allah ya sani yau ba ta jin za ta iya cin wannan tuwon, gashi haryanzu ranta a ɓace yake a kan abin da ya faru, dan marin da Yaya Aliyu ya yiwa Sani bai gamsar da ita ba, ji take ba zata huce ba sai ta fasa masa kai, ko ta hankaɗa shi kwata, ga  kuma tuwon nan da Mama tayi ya sake ƙara mata ɓacin rai.

    Yasir ne yayi sallama, hannunsa riƙe da leda, duk suka amsa masa, banda Rumaisa da ta yi zurfi a tunani.
    In da Rumaisa take ya ƙarasa, ya jijjiga kanta ya ce “Ke tunanin me kike?”
    Haɗe rai ta yi ta ce “Meye kuma na dakar mini kai?”

    Yasir ya ce “To kwalba uwar sharri, ni ban dakar miki kai ba”

    Tsaki ta yi ta ce “Ai na saba in dai ƙarya ce”

    Dire mata baƙar ledar yayi a cinyarta, ya wuce ɗakinsu.
    Buɗe ledar tayi ta kwance, gurasa ce fal ta masu tsire a ciki.

    Murmushi ta yi ta ɗaga murya ta ce “Na gode rabin ran”

    Daga ɗaki ya ce “Ko ba rabin rai ba, tun da na baki abin duniya ba, uwar son zuciya”

    Rumaisa ta ce “kai dai Allah yayi maka albarka, kamar ka san ba son wannan tuwon nake ba, tunani kawai nake me zan ci? Wannan tuwon ne yake toshe mini kai bana gane karatu sosai, Allah dai ya biyaka rabin raina ”

    Murmushi Yasir yayi ba tare da ya kuma cewa komai ba.

    Ya gama abin da yake ya fito tsakar gida, zamansa yayi dai-dai da shigowar dodonsu, wato Yaya Umar.
    Cikin muryarsa ta ƙasaita yayi sallama.
    Duk suka amsa masa, ba tare da ya kula kowa ba, ya ajiyewa Rumaisa leda da indomie ya ce “Tashi ki dafa mini” tabbas ba dan Mai sunan Baba ne ba ba zata yi ba, ita a rayuwarta tana son ko aiki zaka sanyata, ka lallaɓata shi kuwa mai sunan Baba bai san wannan ba, ya bada umarni a bi kawai ya sani mutum ya ƙi kuma jikinsa ya gaya masa.

    Haka ta tashi ta je ta kunna wuta ta ɗora masa.

    Rumaisa na tsaka da aiki, suka ji sallama, kai da jin yadda aka yi sallamar, ka san babu alheri a tare da mai sallamar.
    Mama ta amsa tana faɗin maraba.

    Jin yanayin yadda aka yi sallamar ne ya sanya Rumaisa faɗuwar gaba, ta tsaya cak tana sauraron abin da zai biyo baya, dan ta san babu wanda zai aikata abin da za a zo ana musu wannan sallamar a daren nan idan ba ita ba.
    Mama tayi wa matar nuni da tabarma dan ta zauna, amma matar ta ce “A’a ba ma sai ma zauna ba, ai abin bana zama bane na”

    Ɗan zuro kai Ruma tayi daga Kitchen, domin taga wacece, tozali tayi da Habiba da ƙaninta Sani.
    Ita ba zuwansu ne ya ɗaga mata hankali ba, babu tantama ta san ƙararta aka kawo, amma tashin hankalin ta, Mai sunan Baba yana nan.

    “Ban sani ba ko ke ce ki ka sanya ‘yar ki ta dinga abin da ta ga dama a cikin unguwar nan, saboda tsabar rashin mutunci da rashin ta ido, ta kama mini ‘ya ta daka, kalli fuskar Habiba, kuma duk da haka bai isheta ba, ta ɗauko yayanta suka biyo Sani gida shima suka daka, haka ake yi fisabilillahi wallahi sai da na biya na kai ta chemist aka yi mata allura.
    Dawowata gida kenan bana nan kawai na tarar da yarinya baki ya haye, ya fashe ta riƙe kai sai kuka take, shima Sani kalli fuskarsa duk shatin mari tsakani da Allah Wannan adalci ne?” Ta ƙarasa maganar tana haska fuskar Habiba. Fuska ta kumbura suntum, bakin ko rufuwa baya yi, leɓen sama ya ɗage ya kusa danganawa da hancinta, duk dadashi a waje.
    Duk da halin da Rumaisa take ciki na fargaba, amma sai da ta ƙunshe baki tayi dariya ƙasa-ƙasa, saboda yadda fuskar Habiba ta koma kamar an naushi fura.

    Jiki a sanyaye Mama ta ce “Dan Allah dan annabi kiyi haƙuri, yaran yanzu ne sai addu’a kawai, kin ga ni ban ma san tayi ba, daga ita har yayan nata babu wanda ya zo ya gaya mini, ban ma san waye ba a cikin yayyan nata ba, amma kiyi haƙuri”.

    Haidar yayi gyaran murya ya ce “Mama nine, su meyasa yaran ba a tambayesu me suka yi mata ba, hijjabi a hannu suka biyota da bulalai zasu daka…..

    “Rufe mini baki ban tambayeka ba” Mama ta dakatar da haidar cikin tsawa.

    Mama tayi ta bawa Babar su Habiba haƙuri, amma ba kunya babarsu Habiba ta ce “An bar yara babu tarbiyya su yi ta abin da suka ga dama, saboda tana taƙamar ita ƙanwar maza ce, sai tayi ta isakancin da ta ga dama, sai ta kashewa yarinyar fuska ta cuceni, wallahi ban da ana maƙota da sai na kai maganar wurin hukuma, dan ba zan yadda ba, ita ta dakar mini ‘ya, shi kuma ya zo ya zage ƙwanji a kan ɗana”.

    Cikin muryarsa mai ban tsoro da babu alamar wasa a cikinta ya ce “Ke ya isheki haka malama, ke kamar ba uwa ba, kawai ki zo gaban mace kina cewa ‘ya’yanta basu da tarbiyya, tana baki haƙuri kina cigaba da ƙanan maganganu, kar Allah ya sanya ki haƙura ɗin, ki kai duk in da zaki kai ki je ki faɗa, kuma ko yau wani ya kuma yinƙurin taɓa Rumaisa a unguwar nan, sai mun nuna wa duniya ƙanwar maza ce, fice ki bawa mutane wuri”
    Mama zata yi magana, amma mai sunan Baba ya haɗe rai, ya girgiza mata kai, tare da nunawa Babarsu Habiba hanyar fita.

    Jiki na rawa ta saka su Sani a gaba suka fice, duk girma da ƙanƙantar mutum, babu wanda Umar baya yi masa kwarjini.

    Sai da ya tabattar sun tafi, sannan ya dubi ƙofar Kitchen ɗin ya ce “Ke kuma fito nan munafuka” aikuwa kamar munafukar ta fito tana sunkuyar da kai ƙasa.

    Ya ƙare mata kallo sannan ya ce “Muna zaman zamanmu lafiya aka haifeki, shegiya kamar rainon iblis, duk gidan nan babu mai fita ya ɗauko magana sai ke, tana zaman zamanta kin saka an zo har cikin gida ana gaya mata maganganun banza saboda ke, kai ma saboda hauka dan me zaka biye mata ku je kuna dukan ‘ya’yan mutane? Waye ya aiketa ta tsokane su?”.

    Ran Aliyu ya ɓaci, ya harzuƙa ya ce “Bafa maganar hauka a nan, yarinyar nan hijjabi a hannu suka biyota, ba dan filin ball ɗin mu na hanya ba, haka zasu haɗu su yi mata duka, yara maza ba mata ba, har sun fara dukanta baiwarsu ce ita, ko kuma ce musu aka yi ba ta da gata?.

    “Shut up! Ita ka san me tayi musu, wannan Yarinyar da rashin jin tsiya, ai gara su zane ta gobe ba ta kuma ba, ki cigaba da zuwa ki na janyo mata magana, wallahi ba zaki ɗora mata hawan jini a banza ba, da ki cigaba da ɗauko mata magana ana zuwa ana gaya mata maganar banza, gara na takeki na murɗe miki wuya ki mutu kowa ma ya huta”.

    Tun da Mai sunan Baba ya fara sababi, Sentence ɗinsa na ƙarshe ne ya baƙanta mata rai, wai ya murɗe mata wuya ta mutu su huta. Ta yi shiru ya gama bala’insa ya ce ta wuce ta cigaba da yi masa aikinsa, ya fice.

    Rumaisa tana aikin tana kuka, wato ma ba’a sonta, wai da suna zaman zamansu aka haifeta, ta hana mahaifiyarsu kwanciyar hankali.

    Usman ne yayi tsaki ya ce “Wallahi Mama ɗan nan naki yana da matsala, na yi shiru ne kar na tanka masa yayi mini tijara, amma ba damar yarinya ta motsa sai faɗa, ke Ruma” ya kirata.
    Ta goge hawayenta, ta fito daga Kitchen ɗin.

    Ya kalleta ya ce “Duk shegen da ya takaleki kar ki raga masa, ki ci uabnsa idan yafi ƙarfin ki muna nan, yaran unguwar nan marasa mutunci, ki ka zama nusara raina ki zasu yi, duk ɗan da ya miki ki ci ubansa ko mace ko namiji mun tsaya miki”.

    Mama ta ce “Zinnuraini, kai ne kake zigata ta ɗauko magana?”.

    “A’a Mama bance ta ɗauko magana ba, amma duk wanda yayi mata, ta rama babu nusari a cikinmu, ƙanwarmu ba zata zama nusara ba, mu ci uban mutum ya zo kawo ƙara mu ƙara masa”

    Martanin Yaya Usman ne ya ɗan sanya hankalin Rumaisa ya kwanta, ta kammala yiwa Yaya Umar aikinsa ta je ta nemi wuri ta kwanta, ko gurasar da Yasir ya bata ba ta ci ba.
    Tana kwance lamo a kan katifarta, ta ji muryar Huzaifa a kanta yana cewa ki cigaba da ɗauko magana, ai gara ya murɗe miki wuyan ki mutu kowa ma ya huta da tijararki da rashin hankali.
    Banza ta yi masa, kamar ba da ita yake ba, dan idan ta ce zata biyewa Huzaifa faɗa za suyi, kuma a kowane lokaci mai sunan Baba na iya shigowa, yadda yake a ƙule da ita ta san sai jikinta ya gaya mata, idan ya dawo ya tarar suna faɗa da Huzaifa.

    Da safe bayan gaisuwa ba abin da ya haɗata da mutan gidan, tana kwamce a ɗaki, ‘yan mazan suka gyara komai na gidan, suka ɗora abin kari. Ko ta kan abincin safen ba ta bi ba, ta saye gurasarta a hijjabi, ta ɗau allonta ta tafi makarantar allo.

    Sai dai ashe tuni labari ya iske shugaban makarantar su, a kan faɗan da suka yi jiya, malam babba ya tara su ya ce sai ya zane su.
    Idon Rumaisa yayi tsilli-tsilli, dan kusa bulalar malam Babba akwai ɗan karen zafi.
    Kan Malam Babba ya kai ga zuwa ya yanke musu hukunci, ta zari allonta ta kwasa da gudu, ya tsaya yana ƙwala mata kira, amma tayi burus ta bar makarantar ta kama hanyar komawa gida, dan a rayuwar Rumaisa ba ta ƙaunar duka ko kaɗan.

    A soro suka yi karo da Yaya Usman zai fita, ya tsaya yana kallonta, har zata wuce ya ce “Wai me kika dawo yi ne gidan nan yanzu, ina Makarantar kuma?”

    Ta tura baki ta ce “Kashi nake ji shine na dawo gida”

    Tsaki yayi ya ce “Haka dai kika iya, wannan uban cin da kike yi, ba dole kullum ki kasance cikin zawo ba, baki da aiki sai kashi da tusar tsiya” banza tayi masa ta raɓe shi ta wuce tana murguɗa masa baki, ba tare da ya sani ba.

    Ta shiga cikin gidan tana ciccin  magani, ihuu tayi, tare da tsalle ta nufi in da wani dogon matashi ke zaune, mai tsananin kama da Yaya Umar, sai dai banbancinsu, Yaya Umar fari ne shi kuma bai kai shi haske ba, sannan shi wannan fuskarsa ɗauke take da murmushi saɓanin fuskar Yaya Umar.

    Babu tunanin komai, ta faɗa jikinsa tana murmushi.
    Shima rungumeta yayi yana murmushi ya ce “Autar Mama, tun ɗazu zaman jiran dawowarki nake yi”.

    “Babban Yaya, yaushe ka dawo?”

    “Tun ɗazu na dawo, nace kina ina aka ce kin tafi makarantar allo”.

    “Wayyo daɗi, yaushe rabon da na ganka, gaba ɗaya gidan babu daɗi, kowa ya tsane ni, har da cewa na ishesu wai kamar su murɗe mini kai su huta”.

    Waro ido yayi ya ce “Wane mara ta idon ne yayi wannan iƙrarin a gidan nan?” Ta waiwaya sannan a hankali cikin raɗa ta ce “Waye banda ƙaninka, ya tsaneni wallahi”.

    Yayi murmushi ya ce “Ai ba wanda ya isa ya taɓa mini auta ina raye, ai gani a gidan na dawo”.

    Wani matashin ne ya sake fitowa, yana faɗin “Iya rigima, ya halinki?”

    Sake waro ido ta yi ta ce “Yaya Abdallah”.

    Ya amsa da “Na’am uwar rikici”.

    “Haɗa baki kuka yi duk kuka dawo yau kenan?”

    Abdallah ya ce “Eh haka ne, su Baba Atine suna ta gaisheki, sun ce ke ba kya zumunci”

    Ta taɓe baki ta ce “Waye zai barni na je garin, ai ni ina son zumunci kai ni ne ba ayi” Gaba ɗaya sai ta manta da damuwarta, ta shantake suna hira.
    Sai da aka jima sannan ta shiga ɗaki ta ajiye allonta.

    Sabgoginta ta shiga yi, ta zage ta ce ita zata yi wa su Babban Yaya girki, abincinta zasu ci.
    Aikuwa faɗa ya kaure, Huzaifa ya ce ba zasu ci jagwalgwalonta ba su zasu yi girkinsu, ƙarshe Yaya Sadik ya ce na Rumaisa zai ci.

    Zuwa Azahar gida ya ɗinke kowa ya hallara a falon Mama suna cin Abincin rana, Sadik sai jinjinawa ƙoƙarin Rumaisa yake ta yadda ta iya girki mai yawa haka, Huzaifa da Yasir kuwa sai kushewa suke yi.

    Zaratan maza ne su bakwai sai Rumaisa, Mama a hankali take binsu ɗaya bayan ɗaya da kallo, tana tuna baya.

    Hadiza shine sunan Mama na gaskiya, haifaffiyar garin Kano ce, unguwar mandawari. A nan ta taso tayi karatun boko da islamiyya, sai dai tana aji uku na Sakandire, ta haɗu da mahaifinsu Rumaisa, Muhammad Aminu a nan unguwar sabon sara, amma asalinsa ɗan garin Katsina ne, yana zuwa gidan wan mahaifinsa ne a Kano yana koyan harkar kasuwanci, a nan suka haɗu suka yi aure, kan Hadiza ta gama makarantar sakandare.

    Haihuwar fari Mama ta haifi tagwaye Abubakar Sadik da Umar faruk sune ‘ya’yanta na fari, Sai ta kuma haihuwar Usman, sai Aliyu, Abdallah da Huzaifa, Yasir ne kawai ba ɗan ta ba, ɗan ƙanwar mahaifinsu Rumaisa ne, ta haife shi da kwana kaɗan Allah ya yi mata rasuwa, a lokacin Mama tana shayar da Huzaifa sai ta haɗa su ta shayar da su tare, ba zaka taɓa cewa ba ‘yan biyu bane ba, ko ba ita ce ta haifesu ba.
    Mama gaba ɗaya tayi tunanin ta daina haihuwa, saboda galibi bai fin shekara biyu uku a tsakanin yaran take haihuwa, amma bayan haihuwar Huzaifa sai da ya shekara takwas, kawai ta daina ganin al’ada, sai ga cikin Rumaisa.
    Tun da Allah ya sa ta haifi Rumaisa, kowa ya ɗauki soyayya ya ɗora mata, kasancewarta kallabi a tsakanin rawuna, kowa babban burinsa ya faranta mata.
    Mahaifinsu Rumaisa, mutum ne mai matuƙar kulawa da son iyalinsa, kasancewar Ruma ce kaɗai ‘yar sa mace yafi kowa ji da ita, ba shi da magana sai ta Rumaisa, Akwai tsananin ƙauna da shaƙuwa a tsakanin Ruma da mahaifinsu, dan kusan tafi son sa a kan Mama, saboda Mama akwai faɗa, Abba kuwa lallaɓata yake. kwatsam Allah ya yi masa rasuwa tana da shekaru uku kacal a duniya, bayan yayi gajeriyar rashin lafiya.
    Bayan rasuwar sa sai da Rumaisa tayi cuta kamar ba zata rayu ba, saboda alhini. Dangin mahaifin su Rumaisa suna da zumunci sosai, sun so a rarraba musu yaran su riƙe su, amma Mama ta ce ba ta son a raba nata kan yaranta, dan haka ta ce su ƙyale mata su.
    Haka tayi ta ɗawainiya, ‘yan uwa da abokan arziki suna taimaka mata da abin da zasu iya
    Tasowar Rumaisa a cikin ‘yan mazan nan, wannan ya ɗauka wannan ya sauke ya sanya ta taso tamkar namijin ita ma. Ba ta jin magana ga rashin tsoro, ga tsiwa da ɗan karen surutu da iyayi, gashi lokacin da take tasowa girma ya fara kama Mama duk tayi sanyi, dan haka ta mayar da Mama kamar wata kakarta ba uwa ba.
    Mutum ɗaya take tsoro shi ne Baban Mama, Yaya umar mai sunan baban Mama, Allah yayi masa kwarjini shi ko irin wasan nan na yarinta baya yi, ba shi da abokai, ga tsare gida ba shi da fara’a ko walwala baya son shiga mutane sam, idan kaga an taka masa burki kai tsaye to Yaya Sadik ne. Mama tana matukar girmama shi saboda sunan mahaifinta da yake da shi.
    Yanzu Rumaisa tana aji huɗu na Firamare, Abubakar yana Dutse yana karatu,  babu wanda yake da cikakken ƙarfin ɗaukar ɗawainiyar gidan gaba ɗaya, amma kowa babban burinsa ya nemo ya kai gida, komai suka samu mahaifiyarsu da ƙanwarsu kawai suke tunani.

    “Hajiya Mama, ya naga kina ta kallonmu ne kamar da baƙo a cikinmu”.

    Mama tayi murmushi ta ce “Allah nake yiwa godiya, da ya sanya duk ku ɗin nan nawa ne, Allah ya dafa muku ya ƙara haɗa mini kanku”

    Suka amsa da “Amin”
    Yasir ya ce “Mamanmu, maganin kukanmu Allah ya ƙara hore mana, mu gantataki fiye da kowace irin uwa a duniya”

    Huzaifa ya ce “Hmm kamar gaske, nan fa kake zuwa da abin duniyarka ka hanata, ka hana kowa ka bawa waccan  yarinyar mai kama da Akushin”

    Murguɗa baki tayi tana fari da ido ta ce “Tubarkallah zuƙul-zuƙul maye ya ci kansa da kansa, wallahi ni bana kama da Akushi, son kowa ƙin wanda ya rasa”

    “Ke dalla ware, meye son kowa ƙin wanda ya rasa, aba Kamar gurguwar akuya” Yasir yayi maganar yana dariya.

    Haushi ne ya kamata ta buɗe baki za tayi rashin mutunci, ta sanya idonta a cikin na Umar, ta haɗa maganar da zata yi, da lomar abincin ta haɗiye.

    Suka gama cin abincin, Yasir ya kwashe kwanuka, ya fara ƙoƙarin wankewa, Huzaifa ya shigo da tsintsiya zai share ɗakin, Umar ya ce ya ajiye tsintsiyar ya bawa Rumaisa ta share.
    Haushi ne Yakamata ta lura tun da aka kawo ƙararta ya tsaneta, dama can ba wani shiga shirginta yake yi ba.
    Bayan ta kammala sharar ta nemi wuri za ta kwanta Mama ta kalli kan Rumaisa, da ta fara tsifa, tayi rabi ta bar rabi ta ce “Fita ki bar mini ɗaki, karki sake shigowa sai kin gama wannan tsifar.

    Fitowa ta yi ta na tura baki, tana nema ta yi kuka.
    “Autar Mama, meya ɓata miki rai ne?” Cewar Yaya Abubakar da yake ƙoƙarin shiga ɗaki.
    Dama ƙiris ta ke jira, dan haka ta fara kuka “Ba mama ce ta koreni daga ɗakinta ba, wai sai na gama tsefe kaina ba, ni mama ta tsaneni”.

    Girgiza kai ya yi ya ce “Yi haƙuri ki daina kukan, bari na zo na tayaki tsifar”
    Haka suka zauna ya samu kibiya ya tsefe mata kan tsaf, suka wanke gashin, ya ce da safe zai bata kuɗin kitso.
    Mama ta na kallonsu ba ta kula su ba, ta cigaba da sabgoginta.

    Abdallah yana ta dube-dube a kitchen, ya ci karo da allon Rumaisa, duk gefensa ya karye, ga rubutun jiki yayi baƙi ƙirin, ba ta sake wani ba.
    Ya fito da allon a hannunsa ya ce “Ruma, wannan allon naki yaushe zaki yi wani rubutun?” Ta haɗe rai ta ce “To ban iya ba, sai na iya zan wanke”.

    “Haka dai, ba kya ja a ko ina, daga arabin har bokon, Allah ya sa su zaneki idan ki ka je sati mai zuwa, baki wanke allon kin yi wani rubutun ba, gandamemiya da ke amma haryanzu a izifi biyu ki ke”
    Sai da yayi wannan maganar ta tuna yadda malam Babba ya dinga ƙwala mata kira amma ta gudo gida, yanzu sati mai zuwa ta yaya zata je makarantar allon? Kuma muddin abin da ta yiwa malam ya zo gidan nan, ta san ta kaɗe”.

    “Astagfrillah, ni ‘ya su meyasa haka ne, garin in gujewa wani hukuncin sai na faɗa wani tarkon, ya zan yi da raina?.

    Ayshercool
    08081012143

    Kar a manta ayi subscribing YouTube channel ɗina na Cool hausa tv
    [18/06, 2:35 pm] JAKADIYAR AREWA: ƘANWAR MAZA

    BY AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

    Ku yi subscribing YouTube channel ɗin mu, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro.
    https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
    Arewabooks @ ayshercool7724
    Watpad@ ayshercool7724

    MIKIYA WRITER’S ASSOCIATION

     

  • Kanwar Maza 1

    Kanwar Maza 1

    *Ina fatan yadda na fara lafiya, Allah ya sanya na gama lafiya. Ƙirƙirarren labari ne, idan akwai abin da ya yi kamanceceniya da rayuwar wani ko wata arashi ne*

    Page1

    Bismillahirahmanirrahim

     

    Daji Ajiyar Allah! La’asar sakaliya, a lokacin da hasken rana ya fara disashewa, ta doshi yamma za ta faɗi, duhun magariba na ƙoƙarin shigowa ya maye ragowar hasken da ranar ta bari kan ta ƙarasa faɗuwa.
    Gamayyar bishiyoyi ne, dogaye da da madaidaita, haɗe da ciyayi da ga mabanbantan tushe, suka haɗu suka yiwa dajin ƙawanya. Zai iya kasancewa abin sha’awa ga wanda ya zo yawon buɗe ido, idan har bai san mai dajin ya ƙunsa ba.
    Ga wanda ya san abin da ya ƙunsa kuwa, zai kasance wuri mafi razani, firgici da kuma tashin hankali.
    Gudu take yi a tsakanin rayuwa da mutuwa, tana rungume da wani zani a ƙirjinta, babu yadda za ayi daga nesa ka gane me ta rungumo haka take wannan uban gudun.
    Ƙafafuwanta babu takalmi, jikinta babu mayafi, duk da yanayin garin babu zafi, amma laɓɓanta sun bushe tamkar dutsen da ya shekara ruwa bai zuba a kansa ba, babu alamar tana gane in da take jefa ƙafarta. Duk da wannan mawuyacin hali da take ciki, ta bawa abin da take rungume da shi muhimmanci sosai da sosai.
    Cikin rashin sani, tayi karo da wani abu da ita kanta ba ta kai ga tantance ko meye ba, sai dai ƙarfi da nauyin abun ya sanya ta faɗi ƙasa, take ta saki wani marayan kuka, a lokacin da jini ya fara zuba daga ƙeyarta.
    Sai a lokacin abin da take rungume da shi ya tsala kuka, saboda firgitar da ya yi shima.
    Jariri ne ɗanyen goyo, cibinsa ko faɗuwa bai yi ba, jikinsa duk busashshen ƙazantar haihuwa da alama yaron ya kwan biyu, amma ko ruwa bai taɓa gani ba balle a wanke wannan ƙazantar!.

    **************

     

    Cikin garin Kano, unguwar ɗorayi tinga, misalin ƙarfe huɗu na yammacin ranar Alhamis, wani matsakaicin gida ne, cikin rukunin gidajen dake ɗan ƙaramin layin,  kallo ɗaya zaka yi wa gidajen, ka san na masu ƙaramin ƙarfi ne, duba da yanayin kwatoci da kuma kasancewar gidajen awon igiya, ba magudanan ruwa, babu layuka masu kyau, kowa da in da fuskar gidansa ta kalla, haka zalika kowa in da ya ga dama yake sako kwatar gidansa, wasu da gyara wasu babu, ga gidajen ‘yan ƙanana tamkar wani zai hau kan wani.

    “Wai ba zaki fito ki je mini aiken ba, har sai gawayin ya ƙare tukuna?” Cewar wata matashiyar dattijuwa, da take zaune a gaban kurfoti, hannunta riƙe da mafici tana firfitawa, gefe ga farantin silba ɗauke da garin tuwon masara a kai.

    Wata  yarinya ce ta fito daga wani ɗakin da yake bayan matar, hannunta ɗaya riƙe da hijjabinta, ɗaya kuma sai matsar hawaye take yi.

    Matar ta kalleta ta ce “Kukan me  ki ke yi?”

    Aikuwa kamar mai jiran ƙiris, cikin sangarta yarinyar ta ce “Ba Huzaifa bane ba ya….

    “Ni yi mini shiru, haka dai kuka iya faɗa kamar kuna ganin hanjin junanku, idan na hana ki zuwa in da yake ai ba zaki hanu ba, maza ki ɗau kuɗin nan ki je mini gidan Laure, ta baki kuka ta sittin, daddawa ta arba’in sai manja na naira ɗari ki kawo mini canjin, na yi maza in kaɗa miyar nan kan magariba”.

    Kwaɓe fuska yarinyar ta yi ta ce “Wai yau ma miyar kuka za ayi Innalillahi wa innalillahi raji’un”

    Baki buɗe ta bi Yarinyar da kallo, cikin hasala ta ce “Idan na kaɗa kukar kar ki sha, zaki ɗau kuɗin ki fita ko sai na yi fatali da kanki a wurin?”

    Ta durƙusa ta ɗau kuɗin, ta zura hijjabinta ta nufi hanyar fita, a ranta tana jin gara ace yau babu abin da zasu ci, da wannan tuwon kamar na ibada.

    Cike da kashedi matar ta ce “Idan kin ga dama kuma ki je ki zauna, kar ki yi sauri kiga yadda zan yi da ke, ko ki biyewa yara ki tsaya shashanci a hanya”

    Ba to ko waiwayo ba, ta yi gaba abinta tana kalle-kalle.

    Gidansu ƙawarta Habiba ta fara biyawa, ta tarar da maman Habiba a tsakar gida ana yi mata kitso, ta durƙusa ta gaida Maman Habiba, sannan ta ce mata wurin Habiba ta zo.
    Habiba ta fito daga ɗakinsu tana kallonta tana murmushi, ta ƙaraso in da take tsaye ta ce “Ruma ina zuwa ne?”

    Cikin muryar Raɗa Ruma ta ce “Dan Allah Habiba aron tayar Sani zaki bani, Mama ce ta aikeni so nake nayi sauri na je na dawo”.

    Habiba ta ce “Kaii, Ruma kin san Sani yafi kashi ɗoyi, kar na baki ki je ki salwantar da ita, daga ni har ke mu shiga uku”.

    Ruma cikin ƙwarin gwiwa ta ce “Wallahi ba zata salwanta ba, ke dai ki aramini, so nake na yi gudu na ne na dawo”.

    Habiba ta ja Ruma soron gidansu, ta duba saman kejin kajin da ke cikin ɗan tsukakken zauren gidan, ta ɗaukowa Ruma tayar Sani ta bata ta ce “Dan Allah Ruma ki kula, kar wani abu ya samu tayar nan, ki yi maza mi garata ki je ki dawo”

    Ruma tayi murmushi ta ce “Kar ki damu, yanzu zan fyalla naje na dawo, ina son tayar nan ta sani dama ya bar mini, ‘yar dandaɓasa da ita, yanzu zaki ga naje na dawo”.

    Habiba tayi murmushi ta ce “To shikenan, yi sauri kafin ya dawo”.

    Ruma ta dafe kan taya, ta garata ta dinga zura gudu ta lunguna kamar wata namiji ba mace, ba ta tsaya da gara tayar ba har sai da ta isa gidan Laure.
    Ta yo sayayyarta ta gama, ta fito ta kuma garo taya zata tafi gida, can ta hango wasu ‘yan makarantar allonsu, a ƙofar gidan Hanne mai markaɗe suna ‘yanta, ba tare da ta tuna da kashedin Mama ba, ta ajiye kayan aiken da canjin haɗi da tayar da ta aro, ta shiga aka hau ‘yanta da ita.

    Kasancewar ƙwararriya ce a harkar shagala da iya rinto, nan da nan wasa ya ɗau zafi, ganin tana ta cinyesu a ‘yantar ta hanyar rinto, sai wasa ya koma faɗa, daga nan aka hau dambe, a wurin Ruma ta kifar wa da wata markaɗenta ga ta da ƙarfi kamar doki. Da ƙyar wani mutum ya raba faɗan, Ruma ta haɗa yaran mutane ta zane musu jiki, sai da mutumin yayi mata barazanar zai gayawa yayanta, sannan ta haƙura da damben.

    Yarinyar da suka yi damben, ganin an musu asarar markaɗe, an kifar ga duka, ya sanya ita da ƙannenta suka fasawa Ruma Manjan da ta sayo wa Mama, suka kwashe canjin aiken, suka farke ledar aiken suka gudu, daddawar ma sai da ƙyar ta tsinto wasu, an fasa ledar kuka duk ta watse.

    Ta kwashi sauran kayan, ta tafi gida, tana tafe tana tunanin wace ƙaryar za ta jirgawa Mama, dan ta kaucewa faɗanta, dan a duniya ba ta son faɗan Mama, gefe guda kuma tana tunanin irin dukan da zata naɗawa Safiya idan suka haɗu a makaranta allo, saboda abin da suka yi mta.
    Lokacin da Ruma ta isa gida tuni an fara kiraye-kirayen sallar magariba, domin wasu masallatan har sun tayar, sai a lokacin ta sake shan jinin jikinta, tsoro ya ziyarce ta.

    A soro ta rakuɓe tana leƙa cikin gidan, ta hango Mama a gindin rariya tana alwala, Mama ta ɗaga ido tayi mata kallo ɗaya, ta mayar da kai ta cigaba da alwalarta.

    Cikin sanɗa Ruma ta shiga tana satar kallon Mama, ta ji mai Maman za tace mata, amma ta ji ba tace mata komai ba.
    Ta lallaɓa ta ajiye abin da yayi saura na aiken, ita ma ta faɗa banɗaki tayi alwala.
    Ta lallaɓo falo, ta tsaya a bayan Mama ta tayar da sallar ita ma.
    Mama ta idar, ta tashi ta fita tsakar gida, ta duba abin da Ruma ta kawo mata na aiken, taga irin aika aikar da Ruman ta yo.
    Ta dawo falon tana jiran Ruma ta idar da salla ta dirar amata, amma Ruma ta ƙi idarwa, ta hau nafifilin babu gaira babu dalili, matar da wataran sallar ma sai Mama ta haɗa .mata da duka take yi, amma yau sai gashi har da nafila.

    Can da Mama taga abin nata bana ƙare bane ba, sallar taƙi ƙarewa, ta damƙo wuyanta ta baya ta zaunar da ita, ta kalleta cikin haɗe fuska ta ce “Gidan uban wa ki ka je dana aike ki?”

    Cikin tsoro Ruma ta girgiza kai ta ce “Ba ko ina Mama”

    “Ƙarya kike yi, zaki gaya mini ko sai na murɗe miki wuya, tun la’asar na aike ki amma sai magariba kika shigo mini, gidan uban wa kika je?”

    Cikin zazzare ido Ruma take jujjya kai tana rantse-rantsen rashin gaskiya, “Wallahi Mama ban je ko ina ba”

    Cikin tsananin Fushi, Mama ta ce “Ba zaki gaya mini ba!”

    “Mama wallahi dagaske nake”

    “Assalamu alaikum” aka yi sallama a tsakar gida.

    Mama ta amsa sallamar tana huci, wani matashin saurayi ne ya shigo ɗakin, yana faɗin Mama na dawo”.

    Mama ta ce “Sannu da zuwa”

    Ya amsa da yauwa, ya dubi Mama dake tsaye a kan Ruma, Ruma sai wulƙita ido take, kamar ta zagi sarki.

    “Mama meyafaru ne?” Yayi Maganar yana son jin ba’asi.

    Cikin ɗacin rai Mama ta ce “Saboda tsabar iskanci na yarinyar nan, nan da gidan Laure, ta je ta sayo mini kayan miya, tun bayan la’asar sai yanzu ta shigo mini gida, babu aiken babu dalilinsa, kuma babu canjina, nayi-nayi ta gaya mini in da ta tsaya amma taƙi faɗa sai rantse-rantse take yi”.

    Ya kalli Ruma ya ce “Ba zaki faɗi inda kika tsaya ba, kuma ina canjin? Ko zuwa ki ka yi ki ka kashe mata kuɗi tunda kin saba”

    Cikin tsiwa da rashin kunya, Ruma ta ce “Ban sani ba, kai kuma waye ya saka da kai, zaƙin zaƙafere mai gida feraye kabewa, ai ba da kai ake yi…..
    Kan ta ƙarasa Mama ta rufe bakin nata da duka, da sai da tayi zaton bakinta ya fashe.

    Ja da baya tayi da sauri, ta dafe bakinta tana yarfe hannu, saboda ta ji zafin dukan nan sosai da sosai.

    Ya jinjina kai ya ce “Mama ƙyaleta, ba dai bata da kunya ba, kar ki wahalar da kanki, ki bari mai sunan Baba ko Haidar su shigo, sai su tuhumar miki ita”.

    Jin abin da ya faɗa ya sanya Ruma ta yi wata irin zabura, ta ce “wallahi Mama gaskiya na gaya miki, dan girman Allah kar ki gaya musu, canjin ne suka zube a hanya, na faɗi ƙasa man jan ya fashe dan Allah kar ki gaya musu”.

    “Wallahi Mama ƙarya take yi, kin san dai ƙaryarta ba ta salla, ki tuhumeta bari mai sunan Baban ya dawo zaki ci ubanki”.

    Cike da gamsuwa Mama ta ce “Ai hakan za ayi tun da ba ta da mutunci”

    Ya fakaici idon Mama ya yiwa Ruma gwalo.

    “Mama kin ganshi ko yana mini dariya, dan Allah kiyi haƙuri”

    Banza Mama tayi da ita, ta bawa Huzaifa kuɗi ya kuma yi mata wani cefanen.

    Rumaisa ta koma gefe tayi tagumi, zuciyarta na ta zullumin halin da zata iya shiga, idan har aka sanarwa da Mai sunan Baba ko Haidar abin da ta yi, gashi ko giyar wake ta sha ta san ba zata iya gayawa Mama haƙiƙanin abin da ya faru ba.
    Salati kawai take yi, tana roƙon Allah ya rufa mata asiri, kar Mama ta gaya musu, ƙasan zuciyarta kuma tana yi wa Huzaifa Allah ya isa da ya bawa Mama shawarar ta haɗata da su Haidar.

    Ta na tsaka da tunanin, ta jiyo Mama da Huzaifa suna hirarsu a tsakar gida, kamar ba ita ta gama faɗa ba.
    Suna yi mama tana ƙarasa aikin miyarta.
    Sallama aka yi a tsakar gida, Ruma ta rikice, dan kusan muryoyinsu duk kusan iri ɗaya ne, ta ɗan nutsu ne da ta tuna mai sallamar muryarsa ba ta kai ta su Haidar fashewa ba, kuma shi dama sanyin hali ne da shi.

    Jiyo Mama tayi tana faɗin “Fodiyo, an dawo”
    “Eh Mama, ya gidan?”

    “Alhamdilillah, sannu ka je ka watsa ruwa kafin nan na gama miya”

    Usman da Mama ke kira da Fodiyo ya ce “To Mama, ga wannan” yayi maganar yana ajiye mata leda.

    Miƙewa Ruma tayi tana leƙa window, tana son gane me ye a cikin ledar da Fodiyo ya kawo.
    A ranta ta ce “Allah ya sa kifi ya kawo, idan kifi ne a bani kasona, dan idan aka saka a wannan baƙar miyar ban sha.

    Ba ta kai ga gano meye a ledar ba, idanunta suka sauka a cikin na dodonta, da ya shigo gidan ko sallama bai yi ba, gani tayi tamkar yayi mata wani irin mugun kallo, ko dan dai a tsorace take ne oho.
    Mai sunan Baban Mama kenan, Umar faruk.
    Cikin takunsa na ƙasaita ya ƙaraso tsakiyar tsakar gidan, sannan ya yi sallama.

    Hannu Ruma ta ɗora a ka, muryarta ƙasa_ƙasa ta ce “Na shiga uku, yau kashina ya bushe ƙayau idan ya san me nayi”.

    Tun daga sallamar da ya yi, bai cewa kowa komai ba, shi ma ya ajiyewa Mama ledar da ke nasa hannunsa, ya wuce ɗakinsu.
    Bai jima ba ya fito tsakar gida, ya ɗau buta zai yi alwala.
    Ruma ce ta fito kamar munafuka, ta ɗan risuna ta ce “Yaya Faruk sannu da zuwa”

    Ɗaga ido ya yi ya kalleta, bai amsa ba ya mayar da kansa ya cigaba da alwala.

    Cikinta ya ɗuri ruwa, ta ɗau tsintsiya ta tafi falon Mama ta hau shara a daren, kai da gani ka san sharar ba ta domin Allah bace ba.
    Huzaifa ya faki Idon Mama ya bi Rumaisa falon, ya dinga leƙata yana tuntsura mata dariya.

    Ba dan tana cikin yanayi na tashin hankali ba, babu abin da zai hana su kafsa faɗa da Huzaifa a daren nan, amma ta san biyewa Huzaifa su yi faɗa alhalin Faruk yana gidan nan, wata babbar matsalar ce, mai zaman kanta, dan ƙarshe sai tayi kuka.

    “Ba zaki fito ki ɗebi Abinci ki ci ba?” Mama tayi maganar cikin ɗaga murya, yadda za ta jiyota.

    Daga ɗaki Ruma ta ce ‘Mama na ƙoshi”

    A ƙufule Mama ta ce “To uban me ki ka ajiye da zaki ci, ba zaki fito ki ci Abinci ba?”

    Ruma ta ɗan tura baki tayi shiru.

    Usman ya ce “Ai kin san kin yi maƙiyin nata tuwo, mussaman miyar kuka da ma wata miyar ce ba wannan ba, ƙila ta ci”

    Mama ta ce “Abin da nake da shi ba shi zan dafa na bata ba, zan fasa girki ne dan ba ta cin tuwon?”.

    Cikin kakkausar muryarsa Umar ya ce “Ki ƙyaleta, tun da a cikinta zata zuba, ta kwana da yunwa mana”.

    Mama ta gyaɗa kai ta ce “Ai shikenan”

    Muryarsa kawai da ta jiyo, sai da ta sake shiga cikin tashin hankali, tsananta addurta ta yi, a kan Allah ya rufa mata asiri kar Mama ta gaya masa ta yi mata laifi.

    ‘yan mazan nan suka kewaye Mama, suna ta hira kowa da abin da yake ce mata, banda mai sunan Baba, da  yake duba wayarsa, ba tare da ya tanka musu ba.

    Jin suna ta hira, Mama ba ta gaya masa tayi laifi ba, ya sanya take ta murna, tayi maza ta yi sallar isha’i ta shimfiɗa katifar ta ta kwanta.
    Ta cigaba da Addu’a a cikin zuciyarta.

    “Assalamu alaikum” aka yi sallama a tsakar gidan.

    Suka amsa baki ɗaya, Suka zubawa yaran da suka shigo ido mace da namiji.
    Duk da akwai wutar lantarki da fari Mama ba ta gane yaran ba sai daga baya.

    Suka gaida Mama da su Umar, Mama ta kallesu ta ce “Habiba ya aka yi me?”

    Habiba ta ce “Ruma tana nan?”

    Umar yayi caraf ya ce “Yaya aka yi?”

    Kasancewar sa mutum mai tsanain kwarjini, sai da Habiba ta ɗan ruɗe sannan ta ce “Dama ɗazu ne da aka aiketa ta zo ta ce na bata aron taya, zata jewa Mama aike, to tayar ta Sani ce, ta ce zata dawo da ita kuma haryanzu shiru”.

    Mama cikin mamaki ta ce “Taya kuma?”
    Habiba ta jinjina mata kai.

    Gaba ɗaya Ruma ta manta da ta je ta aro taya, sai yanzu da ta ji maganar Habiba, dan tun da aka kwashi damben nan a nan ta yasar da tayar ta yo gida.
    Ɗora hannu tayi a ka ta ce “Na shiga uku, Habiba shikenan kin kasheni”.

    Mama ta ce “Kina ina zo nan, mara kan gado, babu yadda ban yi dake ba a kan ki gaya mini in da kika tsaya, amma kika ce ke baki tsaya ko ina ba, ashe yawon aron taya kika tafi ko, ko ina sai kin nuna hali ƘANWAR MAZA, ina ke ina taya ban da hauka, zaki fito ki basu abarsu ko kuwa?”

    Jikinta na tsuma ta fito ta tsaya daga bakin ƙofar falon Mama, tana satar kallon Umar, amma taga kamar ma bai san me ake yi ba.

    “Ma.m.maama.. wallahi dan nayi sauri ne, ya sanya na aro tayar, kuma wallahi na manta na barota a wajen gidan Hanne mai markaɗe”.

    Mama ta riƙe haɓa kawai, tama rasa me zata ce gaba ɗaya.

    Huzaifa ya ce “Wannan yarinyar idan kina da rabon yin hankali Allah ya shiryeki, ina ke ina taya kina mace?”

    Mama ta kalli in da Habiba take tsaye ita da ƙaninta ta ce “Dan Allah ku yi haƙuri, tun da ta fita nima nake zaman jiranta, ban aiketa ta je ta karɓi kayan kowa ba, da safe in Allah ya yarda zan turata ta je ta dubo muku” Mama tayi ta basu haƙuri, suka juya suka tafi.

    Mama ta zauna ta dasa mita, ta in da ta shiga ba ta nan take fita ba, su Usman na tayata, ita kuwa Ruma da ta san ba ta da gaskiya, sai ta ƙule a kan katifarta, zuciyarta sai bugawa take tana jiran jin me Yaya Umar zai ce, amma shiru bai ce komai ba.

    Har suka watse daga tsakar gida, Mama ta shigo ɗakin, ta sameta ta rufe ido tana baccin ƙarya, still Mama ta cigaba da mita, sai da Ruma ta ji kamar ta tashi ta barwa Mama ɗakin ta huta, saboda Mama mitarta ba ta ƙarewa sam, gefe guda tana yiwa Allah godiya da Dodonta bai yi magana ba.

    Wani irin bacci ne mai daɗin gaske yayi awon gaba da ita. A cikin baccin nata babu zato babu tsammani sai ji tayi an yi sama da ita da hannu ɗaya.

    “Wayyo Allana, Innalillahi wa innalillahi raji’un, warin hannuna na hagu zai karye Mama!” Sai da ya dungurar da ita a tsakar gida, suka yi ido huɗu, ta ga wanda yayi mata wannan aikin.
    Jikinta ne ya hau kyarma, dan idonsa kawai idan ransa a ɓace yake abin tsoro ne.

    A ƙasan zuciyarta ta ce ‘Shikenan tawa ta ƙare, Allah ya sa na cika da kyau da imani!.

    Ayshercool
    08081012243
    [16/06, 9:00 pm] JAKADIYAR AREWA:                    ƘANWAR MAZA

    BY AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

     

    Ku yi subscribing YouTube channel ɗin mu, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro.
    https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
    Arewabooks @ ayshercool7724
    Watpad@ ayshercool7724

  • Noor Al Hayat 81

    Noor Al Hayat 81

    Da asuba khadijah na jin Aliyu ya fita masallaci ta mike xaune a hankali, gabanta ne ya dinga faduwa from experience, duk da dai wannan karan ko ciwon kai bata ji ba balle na jiki amma tsoro ne fal xuciyarta, ganin lkci na wucewa ta mike cike da karfin hali, the pain wasn’t as much as she was expecting… Ta lallaba ta fita dakin ta koma nata ta sa makulli, wanka ta fara yi ta dauro alwala ta fito, tana ta xaune kan darduma tana azkar bayan ta idar taji an murda kofa, kallon kofar tayi sai dai bata motsa daga inda take ba, a hankali yayi knocking yace “Iman, are you alryt…” Shiru tayi bata ce komai ba, tana ji ya bude kofar dakinsa ya shiga, bayan wani lkci ya fito, hade kai tayi da gwiwa jin yana bude kofarta da makulli, bayan ya bude ya tsaya daga bakin kofa yana kallonta, a hankali ya karasa dakin ya duka kusa da ita xai dago kanta ta ki yarda, da damuwa yace “Look at me plss Iman, are you okay…” ganin ba yarda xata yi ta dago ba ya mike ya dagota, ihu ta fasa masa ta boye fuskarta jikinsa tace “Ni dai bana soo” Dariya ta basa yana rungume da ita yace “Meye baki so Ummu Shureim” a hankali tace “Ka fita” murya can kasa yace “Kunya ta kike ji?” Kai ta gyada masa a hankali, sosai ta basa dariya ya nufi gadonta da ita, ya kwantar da ita ta rufe fuskarta da pillow, Xaunawa yayi gefenta yana murmushi yace “Sai ma mun yi wanka tare anjima xaki san meye kunya” Bata san lokacin da ta dago ba ta xaro ido tana kallonsa tace “What???” Sai kuma ta maida kanta da sauri tana murmushi wai ita kunya…. Wani salon soyayya na daban Aliyu ya dinga gwada ma Iman kamar xai maida ta ciki, ko da yaushe suna manne da juna, Khadijah bata taba tunanin haka Aliyu yake ba shi da kunya ko na taro ba, idan aka ce mata xai iya abinda yake mata baxata yarda ba, coz he look so innocent in the face, tun tana kunya tana noke masa har daga karshe tayi give up ita ma a gidan ta sakar masa kanta, gida ya koma kamar na India, kunyan da take ma da daddare shi ma duk ta ajiye sa gefe amma fa cikin duhu, ita kanta bata taba sanin tana da soft spot ma Aliyu ba sai a yanxu, har ranta take jin sa, sannan ko na minti daya bata son ya bar ta duk inda xa su tare suke xuwa. Ranan da suka cika sati biyu gidan tana kwance jikinsa a parlor yana operating laptop, a hankali tace “Abban shureim…” Yana kallonta yayi pecking cheeks dinta yace “Ummu Shureim” ta turo baki tace “kaga mun koma makaranta fa” yace “I thought as much, dama in two days time xa mu koma can ai” Tace “Toh Allah ya kai mu” yana shafa fuskarta yace “Ameen baby” a ranan suka tafi yi ma Mumy sallama da yamma, Khadijah na xaune tare da Baby a dakinta taga Barrister ya kirata yayi sau uku, ita dai bata ce mata komai ba, amma sai suka bata dariya, karfe biyar saura suka shiga dakin Mumy xa su mata sallama don har gidan Umma da umman su jawahir xa su je, Mumy tace “Toh Allah ya kai ku lafiya, ya kiyaye hanya” Khadijah dake durkushe kusa da ita tace “Ameen Mumy” Mumy tace “Toh sai kun dawo biki nan da few months” Aliyu yace “Wani bikin Mumy” sai da Mumy ta fara dariya sannan tace “Na kanwar ka mana” Khadijah tace “Mumy baby?” Mumy tace “Ehh” xaro ido tayi tace “Lahh Mumy ba mu sani ba” Aliyu ya xauna yace “Mumy da Ahmad din?” Mumy tayi murmushi tace “Wannan bada ta kawai Abban ku yayi, ba Ahmad bane, an basa hakuri shi” Aliyu ya d’an hade rai yace “Bada ta kuma? To who?” Mumy tace “Barrister Aliyu” da khadijah ta fara dariya sai da Mumy da Aliyu suka tsaya kallonta, ta mike da sauri ta fita xuwa dakin baby tace “Wato abun har da munafurci koh Baby, ni din ne baxa ki gaya ma ba koh?” Baby tayi murmushi don tasan kwanan xancen, a hankali tace “Shi yace ba sai na gaya maki ba, xai je har gida as a mother ya same ki ya gaya maki” khadijah na murmushi tace “Am soo happy wllh, Allah ya sanya alkhairi, ya nuna mana lokacin lafiya” Har bakin mota baby ta raka su, suka wuce gidan Umma, bayan Umma sun gaisa da Aliyu ta bi bayan khadijah da ta wuce ciki, Ganin yanda tayi kyau ta cicciko Ummu tayi murmushi tace “Ko ke fa da kika kwantar da hankalin ki daughter” murmushi kawai khadijah tayi ta sunkuyar da kanta, Umma ta xauna kusa da ita tace “In ji dai ba matsala?” Khadijah tace “Babu Umma dama sallama muka xo maki xa mu tafi can Uk” Umma tace “Maa Sha Allah, ai hutun ya kare, Allah ya kai ku lafiya my daughter” Khadijah tace “Ameen Ummata” Umma tace “Amma ku je har Umman su jawahir ku yi mata sallama” khadijah tace “Eh dama xa mu je Umma” Umma tace “Toh hakan na da kyau, kin san kawun ki yana yawan kira mu gaisa” Khadijah ta kalleta da sauri tace “Abbansu Safeenah?” Umma tace “A’a ba shi ba, mai bi masa” xaro ido khadijah tayi sai kuma tayi dariya tace “Umma Abban su Maimoon ne, dama umman su ta rasu 3 years back suka gaya min” Umma tace “Toh ya aka yi don Umman su ta rasu, Allah ya ji kanta” Dariya kawai khadijah take, Umma dai sai kallonta take, can ta turo baki tace “Umma ni dai don Allah kar ki ce masa A’a” buda ido Umma tayi, sai tayi dariya tace “Amma baki da kunya yarinyar nan” Khadijah ta mike ta fita tana dariya, minti talatin suka yi a gidan, xa su wuce umma ta ja khadijah xuwa daki tace “Daughter, ya kamata ku je can katsina da Aliyu ki gaida yayan Mahaifin ki” shiru khadijah tayi da farko, sai kuma a hankali tace “Toh Umma xa mu je” Umma tace “Good, Allah ya kiyaye hanya, ki kula da mijin ki fiye da yanda xa ki iya, ki kuma rike tsaftar ki don nasan kina da ita, Allah ya maki albarka” khadijah na murmushi tace “Ameen Umma” da haka suka bar gidan suka dau hanyar gidansu jawahir, can ma basu dade ba bayan sun yi ma Umman jawahir sallama suka koma gida. Da daddare ganin Aliyu xai takurata ta dinga turo baki tana kwace kanta jikinsa, ya kai bakinsa kunnenta murya can kasa yace “Baki son mu tafi da babynmu daga nan Iman” ta marairaice masa tace “Ni dai ka kyaleni bacci nake ji” yace “Plss” kukan shagwaba ta fara masa wanda hakan ya rikita sa, bai kyaleta ba sai da yaga ta fara bacci da gaske, ya fi awa daya kankame da ita, ko da yaushe jin abarsa yake intact, murmushi yayi ya manna mata kiss a lips daga karshe ya kwantar da ita ya shiga bathroom. Washegari suna breakfast tana kallonsa tace “Abban Shureim, Ina son mu je katsina mu gaida Uncle dina” ya kalleta yace “When, Kin san gobe da safe xa mu wuce” Tace “Toh idan mun dawo bikin su baby sai mu je?” Yace “A’a idan kin ce mu je yanxu ma sai mu je ai” ta langwabar da kai a hankali tace “Mu je plss” yace “Alryt then” karfe sha daya suka bar gidan, suka dau flight xuwa kano, daga can yayi masu charter na taxi da xai kai su har kt, tun da suka shigo kt misalin karfe daya da rabi na rana gaban khadijah ke ta faduwa, taxin ya ajiye su dai dai gidan kawunta, ita kanta tayi mamakin yanda ta gane gidan, Aliyu ya fito ita ma ta fito tana kallonsa tace “Mu shiga” Bin bayanta yayi suka shiga gidan, Babu kowa compound din da ya xama wani iri kamar gidan da yayi shekara hamsin, Har parlor ta isa da sallama Aliyu ya tsaya daga bayanta, kallon kawun nata dake xaune k’asa a one side of the parlor yana fama da ciwon kafa sosai tayi, ta kalli Hajiya maimuna da ta fito kitchen jin sallama ta gaisheta a sanyaye, daga ita har yaran dake parlorn kallonta suka dinga yi kamar basu santa ba, ita dai tasan basu gane ta bane, Ta isa har kusa da ita a hankali tace “Mama Khadijah ce” bude baki Hajiya Maimuna tayi tana kallonta da wani irin mamaki, Khadijah ta sauke idonta kasa, ba ita ba har kawu Jibril shi ma bude baki yyi lkci daya hanjin cikinsa ya kada don kullum da threat din Barrister Sudais yake kwana yake tashi, Aliyu ya xauna kusa da shi yace “Ina yini kawu?” Kawu ya kallesa yana maxurai yace “Lafiya lau daga ina, wa ku ke nema” Aliyu yayi kasa da murya yace “Ni ne mijin khadijah, mun xo gaishe ku ne kawai kawu” da sauri yace “Toh madalla… Gaisuwa ce kawai koh” Aliyu ya gyada masa kai yace “Eh kawu” khadijah ta karaso har gabansa ta durkusa kanta a kasa tace “Ina yini kawu?” Yace “Lafiya lau” Kai kana ganin yanda yake maxurai kasan duk a tsorace yake, Aliyu yayi murmushi yace “Ka kwantar da hankalin ka kawu, xumunci kawai ta sa ni in kawo ta tayi” Yana gyada Kai kamar kadangare yace “Madallah” Khadijah dai ta kasa cewa komai, bata taba xaton ganin Kawunta da iyalensa a halin da ta samesu ba, ganin gaba daya mutumin is uncomfortable Aliyu yace “Kawu xa mu koma yanxu, don gobe da safe xa mu wuce uk shine tace in kawo ta…” Kawu ya kasa kallon khadijah sai gyada kai yake yana cewa Madallah Kamar xararre, Dubu hamsin Aliyu ya ajiye gabansa, Kawu ya dauka yana kallonsa, lkci daya idanuwansa suka kada yace “Maa sha Allah, nagode nagode nagode Allah yayi albarka” Aliyu yace “Ameen” a sanyaye Khadijah tace “Allah ya baka lafiya kawu” hawaye ta gani idonsa amma yana ta boyewa bai son su gani yace “Toh Amin, sai a yayyafe….” murmushin karfin hali tayi tace “Nima ku yafe min kawu, Allah ya yafe mana baki daya” hatta Maimuna sai da tace da khadijah a yayyafe da xasu wuce, ganin bata ga kishiyarta ba tace “Mama Ina mamansu Usman?” Maimuna tace “Ta amshi takardar ta ta wuce kusan shekara kenan” khadijah bata ce komai ba duk jikinta yayi sanyi har suka bar gidan xuwa inda xa su samu mota xuwa kano. Sai bayan la’asar suka shigo kano, Khadijah sai bata fuska take irin ita ta gaji din nan, ya langwabar da kai yace “Toh ai we still have 3 more hours journey kike bata fuska madam” ta xaro ido tana kallonsa tace “Ni dai na gaji wllh” murmushi yayi yace “Just reserve this comment, xa su maki amfani anjima idan mun isa gida da daddare” Kallonsa kawai take kamar mai son gane ma’anar abinda yace, can tace “Kamar ya?” instructing din mai adai daitan da ya tsayar masu yyi yace “Airport xa ka kai mu” Khadijah ta turo baki ta shiga shima ya shiga yana matsa cinyarta a hankali, tayi kara tana kallonsa, dauke kai yayi da sauri yana murmushi, har suka isa airport idonsa na kan wayarsa da yake dannawa, ya siyar masu tickets na kaduna, hudu da rabi jirgin ya tashi, cikin few minutes suka sauka kaduna. A gajiye ta shiga parlor ta wuce dakinta direct ta fada kan gado, bayan kusan minti biyar ya bude kofar dakin yana kallonta yace “Sallahn fa?” Kallonsa tayi a hankali tace “Xan yi” yace “Toh tashi kiyi” Sai da ya idar da sllhn shi ma sannan ya fita eatry siyo masu abinci, yana dawowa ya shigo dakinta, xaune ya sameta kan darduma yace “Come down mu ci abinci” Tace “Sai na fara wanka” yace “Toh jira ni in xo muyi” mikewa tayi da sauri ta shige bathroom din ta sa makulli, yana dariya ya juya ya fita dakin. Karfe goma na dare tana kwance parlor kan 3 seater har bacci ya dauketa taji an dauketa kamar baby, ta bude ido a hankali tana kallonsa, ya manna mata kiss a lips dinta ya shiga bedroom dinsa ya kwantar da ita saman gado, ya kwanta shi ma ya shige jikinta… Kamar xata yi kuka tace “Bacci fa nake ji” yayi kasa da murya yace “Wai baki son mu tafi da tsaraban baby mai kama da ke UK ne?” Hararansa tayi ta juya masa baya tana turo baki, ya marairaice mata yace “Plsss Ummu Shureim” kukan shagwaba ta fara masa as usual, nan ta kara rikitar da shi, ita ma dai kamar jira take ta bada kai bori ya hau, they couldn’t just get enough of each other, ta kankamesa kamar xata koma jikinsa su xama daya, ya kai bakinsa kunnenta cikin sanyin murya yace “I love you Iman…” Shiru tayi idonta a lumshe, bayan wani lokaci ta kwanta kan kirjinsa a hankali tace “I love you more Abu Shureim” kissing dinta ya shiga yi, and that really turn her on. Da asuba tare suka yi wanka ya ja su sallah a dakin, a hankali ta dawo kusa da shi ta durkusa murya can kasa tace “Good morning Abu Shureim” ya jawota jikinsa yace “Morning Ummu Shureim….” Murmushi tayi tace “I am missing him” yace “You better don’t, shi din me iyaye ne da yawa, so kar ma ki wani sa shi a rai” shiru tayi bata ce komai ba, yace “Ki hada abubuwan da kika san xa ki bukata, anjima xa mu wuce airport” tace “But I have everything back there, a can gidana…” Kallonta ya dinga yi kafin yyi murmushi yace “Kina tunanin xan je gidan ki in xauna wife?” Shiru tayi tana kallonsa, yyi yar dariya yace “Lallai, I rather rent a new flat, balle ma muna da apartment can din, kawai I prefer staying a gun aunt dina ne saboda kadaici” murmushi tayi bata dai ce komai ba, sai dai ita ma hakan ya mata, coz she don’t think xata iya xama gida daya da su Khaleel, it’s just not possible, lakutan hancinta yyi yace “Kin fi son can ne saboda yar uwar ki” da sauri tace “Not at all, ur wish is my command sir….” Rungume ta yayi yace “That’s sweet of you baby”

    A year and a half later….

    Tun da khadijah ta tashi yau take ta girke girke iri iri duk da xaxxabin da ta dinga yi kwana biyu da suka wuce, kana ganinta ka ga mai karamin ciki, yanxun ma daurewa take girkin da take yi, don aroma din na hawa mata kai but she have no option, Aliyu ne ya shigo kitchen din yana rungume da little Fatima, yarinya da baxata wuce shekara daya da few months ba, she is just a duplicate of her mother, babu inda ta bar khadijah, kyakkyawa ce ta karshe yarinyar, Khadijah ta kallesu tace “Dear kasan yanxu xata ce sai na dauketa kuma ni ba taya ni aiki xaka yi ba” Yar dariya yayi yace “Tsoro nake kar in fita da ita tayi ta min ihu a mota, xan je airport dauko Umma, same flight kuma suka bi da su Baby” Khadijah tace “Lahh da gaske?” Yace “Sure, Aryan ma ba yarda xai yi ya bi ni ba da sai mu tafi tare da su…” Tace “Ae tun daxu na gane gida yake son wucewa ya gaji da mu” dariya Aliyu yyi yace “Aa miskilanci ne kawai, ya ki yarda in dauke sa ma” Ta dauraye hannunta ta amshi Noor ta mana masa kiss a lips dinsa tace “Toh Allah ya tsare babyna….” Yace “Uhn you are looking for trouble koh” yar dariya tayi ta kashe masa ido tace “Don ma ban maka french one ba” Ya wara ido yace “Toh mu je daki ki min” ta hararesa tace “Naki wayon” juyawa yayi ya fita yana murmushi, yau ranan farin ciki ne gareta don a ranan xata sama qualified pharmacist, a ranan xa ayi convocating din su, kafin Aliyu su shigo gidan ta gama komai tana jiran Ummarta da yanxu take auren yayan mahaifiyarta wato dad din su Maimoon, tare da Baby uwar gida ga Barrister Sudais, fitowa parlor tayi jin shirun Aryan yayi yawa, xaune ta ga little balaraben kan kujera kiris yake jira ya fara kuka, ta karasa gun sa tana murmushi ta ajiye Noor, ta daukesa ta rungumesa tace “Haba sweetheart, in dafa maka indomie xaka ci?” Kitchen ta koma tana rike da shi ta daura ruwan indomie sanin abinda yake ci kenan, tana tsaye har ya dahu ta juye a plate ta dawo parlor ta xaunar da shi ita ma ta xauna ta shiga basa, Babu inda ya bar ubansa tun daga kyau har gashin kansa, hatta idonsa irin na babansa ne, murmushi tayi tana ci gaba da ba sa indomien yana ci, tana gama basa ta wuce daki da shi ta sauya masa kayan jikinsa duk da ba su yi komai ba ta dauko masa favourite toy dinsa ta basa ya amsa ta kunna masa cartoon ta xaunar da shi kusa da Noor da ta kwanta kan kujera, sannan ta shiga daki don yin wanka, tana shiryawa bayan ta fito ta ji shigowar mota, ta gama saka kayan da sauri ta fito, Aryan na ganin xata fita ya sauka saman kujera xai fara kuka, ganin haka ta dawo ta daukesa, Noor ta fashe da kuka ita ma, dariya tayi ta dauketa ita ma, tana rike da su ta fita compound, tsaye tayi tana murmushi ganin motar Khaleel ne, jawahir ta fito daga motar, Aryan na ganinta ya fara murna, khadijah ta saukesa yaje da gudu ya rungume uwarsa ta daga sa tana dariya tace “Kai lallai khadijah, dubi yanda kika maida min yaro kato, wani irin abinci kike basa haka” dariya khadijah tayi tace “Bayan ma ya rame, duk kwanan nan a dole yake xaune gidan, naga alamar kewar ki yake” Khaleel ya fito daga mota yana murmushi ya nufo ta yace “Oum shureim good morning” tana murmushi ita ma tace “Morning doctor….” ya amshi Noor yana shafa dogon gashinta idonsa a kan khadijah yace “Congrat once more, Allah ya sanya alkhairi, our pharmacist…” Tace “Ameen Thumma Ameen, thanks much Abu Aryan” Bata rufe baki ba motar Aliyu ya shigo gidan, Baby ce ta fara fitowa daga motar tare da little Amira, khadijah ta wara ido tana kallonsu ta nufe su da sauri, Barrister Sudais ya fito daga gaban motar with Shureim, sannan Umma da ta fito ita ma rike da little Farouq yaron da baxai wuce wata bakwai ba da baby take goyo, khadijah ta rungume baby cike da murnan ganinta suka dinga babbaka dariya, lkci daya ta tafi gun Ummarta ta rungume ta ita ma, tsabar murna ta kasa cewa komai, ta rasa me xata ce, tana sake Umma ta daga handsome yaronta sama ta rungume sa ya dinga kissing fuskarta very happy seeing her….. Aliyu ya fito ya jingina da mota ya rungume hannunsa yana kallonsu, Kamar yanda Barrister Aliyu da Dr Ayman ke kallonsu suna murmushi su ma….

     

    *ALHAMDULILLAH*

    A nan na sauke littafina mai taken *Noor-Al-Hayat* kurakuren da nayi a ciki Allah ubangiji ya yafe min….👏🏻 Darussukan dake ciki Allah yasa mu amfana da su Amin. Ina mika sakon gaisuwata xuwa ga mahaifiyata Hajiya Hajarah… She is my first love, my role model, my momma, my world, my everything… Allah bar min ke Hajjaju Yaya❤ My sweet Anty Didi ur daughter Jiddo is greeting with respect, tnx for being there for me during this book, Allah ya raya su Aneesah… And my second role model Anty Rukaiyya…😍 am so grateful for the encouragement from the beginning of this novel till the end, I always gat ur back small mum ur daughter Khaleesat Haiydar is saying a big thank you, Allah bar mu tare ya raya Little Khaleesat Haiydar, Baby and Jaheed…
    Na sadaukar da littafin *Noor-Al-Hayat* xuwa ga lovely sister na, my Blood… Khadijah M Bello (Amira/Baby) nd my sweet cousin like no other Khadijah Sadi Yusuf (Baby) Allah ya albarkace rayuwar ku ya raya mani ku bisa imani, ya baku ilimi mai albarka da amfani. Sakon gaisuwa ta na musamman xuwa ga wa enda for sure ba siyan littafin Noorul Hayat suka yi ba, ihisani kawai suka min, duk ina sane da ku kuma na so contacting din ku but I lost my contacts, ban san ya xan yi in same ku ba, Amma ku sani I will for ever be grateful, Allah ya biya maku bukatun ku na alkhairi duniya da lahira, nagode nagode…. And finally my fans, ban taba xaton yea da gaske I have fans ba sai a littafin nan, you guys really patronized me fiye da tunani na, you all made me feel loved😥 words alone can’t express how happy I am, ku sani… Billah Khaleesat na ji da ku har ranta, Ina son ku, Ina alfahari da ku, Ina maku fatan alkahiri, Ina maku fatan rabuwa da iyayen ku lafiya, Ina maku fatan daukaka, Ina maku fatan gamawa da duniya lafiya, ina maku fatan samun aljanna, I wish you all the very very very best in life, nagode nagode nagode… Allah ya sa mu cika da imani ya yafe mana kura kuran mu…👏🏻

    Taku har kullum Hauwa Bello Jiddah (Khaleesat Haiydar) 📚✍🏻

    Thanks once more for patronizing my book fans… For those still wanting to buy the complete document it’s just 300 Via transfer 👉🏻 3276052019 Hauwa Jiddah Bello, fcmb.

    07087865788.

  • Kanwar Maza 2

    Kanwar Maza 2

    P2
    Kasa ɗauke idanunta tayi daga kallonsa, saboda azabar firgici da razanar da ta yi.
    Ya janyo kujera ya zauna a gabanta, ya ɗan ƙura mata ido, sannan cikin kaushin murya ya ce “Gidan uban wa kika tafi da ta aikeki, tun la’asar ba ki dawo ba sai magariba?” Yayi Maganar yana tsareta da ido.
    Kasancewar akwai wutar lantarki, ya sanya fes take kallon fuskarsa da idonsa.

    “Ba magana nake yi miki ba, ki ka tsare ni da ido?” Ya daka mata tsawa.

    Zabura tayi ta yinƙura za ta yi magana,amma ya sake cewa “Kuma wallahi kika yi mini ƙarya sai na ci ubanki a daren nan”

    Jiki na rawa ta fara zayyane masa yadda aka yi tun bayan fitarta.

    Huzaifa tun da  yaga Yaya Umar ya shiga ɗakin Mama ya jiyo kukan Rumaisa, ya sha jinin jikinsa, dan ya san yau sai yadda Allah ya yi.
    Mama kuwa girgiza kai kawai ta yi, jin Yadda Ruma take faɗar gaskiya saɓanin ɗazu da ta yi mata ƙarya.

    Umar ya ce “Namiji ce ke da zaki tafi aron taya?” Ta sunkuyar da kai tayi shiru.

    “Kuma me nace miki a kan dambe a hanya, karya ce ke?”

    Ta girgiza masa kai alamar a’a.

    Ya ɗora da cewa “Wato ke duk wani abu da za’a gaya miki sai dai ya shiga ta kunnenki na dama, ya fita ta hagu ko?”

    Ita dai tayi shiru tana rarraba ido.

    “Kyaci ubanki, tashi ki kama kunnenki tun da ba zaki yi hankali ba”.

    Maraicewa tayi zata fara yi masa magiya, amma da yayi mata wani mugun kallo, ba shiri ta miƙe ta durƙusa ta hau kamun kunne.

    Gaba ɗaya Huzaifa ji yayi bai ji daɗi ba, maimakon a hukuntata tun a lokacin amma sai da aka bari ta fara bacci, za a sakata kamun kunne, ya tsaya ta ƙofa yana leƙen tsakar gidan ya san yanzu zata galabaita, gashi babu wanda ya isa ya hana Yaya Umar abin da yayi niyya sai Hassan ɗin sa wato Abubakar Sadik, shi kuma baya nan.

    Umar ya nutsu yana duba litattafansa, Rumaisa kuwa sai tangaɗi take tana neman ta faɗi, amma yayi banza da ita, dan ta san idan ta faɗi ko ta tashi ba zata iya ɗaukar wani hukuncin ba.
    Tun tana kuka ƙasa-ƙasa har ta fara yi da ƙarfi, saboda azabar gajiyar da ta yi.
    “Tashi” ya faɗa ba tare da ya kalleta ba. Ta ɗago duk ta haɗa uban gumi, ga hawaye da majina duk a fuskarta.

    “Kukan uban me kike yi?”

    Cikin kuka ta ce ‘Yaya na gaji ne, dan Allah kayi haƙuri ba zan sake ba, na tuba”

    “Da alama haryanzu baki yi laushi ba, yi zaman babur tun da kin gaji da kamun kunne”

    Babu kalar izayar da Yaya Umar bai yi mata ba a daren, har Sai da Mama ta ji babu daɗi a ranta, amma tuna cewar yarinyar ba ‘yar goyo bace ba, ya sanya tayi banza ta cigaba da laziminta.

    Aliyu ne ya fito daga ɗakinsu, cikin damuwa ya ce “Dan Allah Yaya kayi haƙuri ka ƙyaleta haka ta je ta kwanta dare yayi, wallahi ta horu, kuma ga gobe in Allah ya kaimu da makaranta”.

    A fusace Umar ya kalleshi ya ce “Ka ɓace mini daga gabana ko sai na haɗa da kai?” Ran Aliyu ba ƙaramin ɓaci yayi ba, kawai ya girgiza kai ya shiga banɗaki.

    Sai da ya tabbatar da ta galabaita sannan ya ce ta zauna ta huta, shi kuma ya tashi ya fita.

    Ta dinga kuka kamar ranta zai fita, saboda jin cinyoyinta take kamar babu nama a cikinsu sai rodi, saboda azabar sagewa da suka yi, ƙashin bayanta ma ban da azabar ciwo babu abin da yake yi mata.

    Yaya Umar na fita, Huzaifa ya ƙaraso in da take yana mata sannu cikin tausayawa kamar ba shi ne ya gama bawa Mama shawarar ta haɗata da Yaya Umar ba.

    Ya je ya ɗebo ruwa ya bata, ta karɓa ta kafa kai tana sha tana kuka. Ta gama sha, ya karɓi kofin ya ajiye yana goge mata hawayen fuskarta.

    “Uban me kake a nan wurin?” Basu ji dawowar Yaya Umar ba, sai maganarsa kawai suka ji, suka yi tsuru-tsuru.

    “Zaka tashi ko sai na haɗa da kai?” Jiki na rawa Huzaifa ya tashi, ya koma ɗakinsu.

    Ya kalli Ruma da ke ta ajiyar zuciya, ya tabbatar ta galabaita, ya san yanzu haka jikinta na ciwo, ya jefa mata leda a jikinta ya ce “Maza ɗauki ki shanye”

    Jiki na rawa ta ɗau ledar, doguwar jarka ce cike da youghurt mai sanyi a ciki, ta ɗaga kai ta sha rabi, yana tsaye yana kallonta, ba tare da ta kalleshi ba ta ce “Na ƙoshi”.

    Jin bai ce komai ba ne ya sanya ta ɗago ta kalleshi, ganin yana mata wani irin kallo ne, ya sanya ta cigaba da sha tana yamutsa fuska, da ƙyar ta shanye, ta ajiye robar tana jiran umarni na gaba.

    “wuce ki je ki kwanta”

    Da ƙyar da yinƙura ta tashi, ƙafafuwanta na ta rawa saboda ciwo, ta shiga ɗaki.
    Tana shiga ta tarar da Mama na salla, ta faɗa kan katifa tana kuka.
    Mama har ta idar da sallar ba tace mata komai ba, ta cigaba da kukanta har bacci ya ɗauke ta.

    Cikin bacci ta ji Mama na ɗala mata duka a cinyarta “Tashi” duk da yadda ta ji zafin dukan, amma ta buɗe idonta a hankali ta kalli Mama, ba tare da ta ce komai ba.

    “Saboda tsabar rashin hankali, ki kwanta ki yi fitsari a kwance, ke ba jaririya ba ba ‘yar yaye ba” jin abin da Mama ta faɗa ne ya sanya ta miƙe zumbur, ta ganta luntsum a cikin fitsari.

    Waro ido ta yi ta ce “Na shiga uku, wallahi na zata a mafarki ne, dan Allah kiyi haƙuri”

    Mama cikin ɓacin rai ta girgiza kai ta ce “Innalillahi wa innalillahi raji’un, zaki tashi ki fita kije ki gyara jikinki ko kuwa?”

    Sannu a hankali ta sauka daga kan katifar, saboda yadda jikinta ko ina yake yi mata ciwo, saboda punishment ɗin da Yaya Umar ya sanya ta.
    Da ta fita tsakar gida da rarrafe ta ƙarasa banɗaki, ta wanke jikinta ta dawo ta canza kaya, ta jingine katifar tayi kwanciyarta a ƙasa.

    Har ga Allah, tana jin yadda fitsarin ya matseta, amma ta ji gandar tashi, saboda bacci take ji sosai, ga kuma ciwo da jikinta yake yi, dan haka ta cigaba da baccinta, da ta ganta a banɗaki ta zaci a gaskene ta saki fitsarinta.
    Tana jin yadda Mama ke ta mita, amma ita ko a jikinta, wani nannauyan baccin ne ma yayi awon gaba da ita.

    Da Asuba ma an kai ruwa rana kan Mama ta samu Rumaisa ta tashi ta yi salla, dan sai da ta yi iƙirarin haɗata da Yaya Umar sannan ta tashi ta yi sallar.
    Ta idar da salla Mama tayi mata maganar shirin makaranta, amma ta tura baki ta ce “Ai kina gani jiya mai sunan Baba yana azabtar da ni baki hana shi, ni bani da lafiya, ba zani ba cinyata kamar an mini ɗorin karaya haka nake ji na”

    Mama ta yi mata shiru ta cigaba da laziminta, Huzaifa ne ya fara shigowa ɗakin Mama ya gaisheta, suka gaisa ya tambayi Mama mai za’a ɗora na karin kumallo?.

    Mama ta ce “Bari gari yayi haske, sai a sayo gasara, ka cewa Yasir ya feraye maka dankali, sai a soya”

    Huzaifa ya jinjina kai ya miƙe, har zai fita idonsa ya sauka a kan katifar Rumaisa, ya ɗan yi turus ya dubi Mama ya ce “Mama ba dai fitsarin kwance yarinyar nan tayi ba?”

    “Gashi kuwa kana gani, ai Yarinyar nan sai addu’a kawai”.

    “Innalillahi wa innalillahi raji’un, su Balama an yi asarar kunnuwa, ba sai ki saka ta fitar miki da ita daga ɗaki ba, sai ɗakin ya fara wari tukuna, abinka da fitsarin gardiya bana jariri ba, tashi shashasha” ya ƙarasa maganar yana zuba wa Rumaisa duka a ƙafa.
    A gigice ta tashi zaune ta raba ido, tayi zaton Mama ce ta daketa, amma taga Huzaifa a kanta.

    “Me nayi maka zaka dakeni?” Tayi maganar a ƙule.

    “An dake ki ɗin, tashi ki fitar mata da wannan katifar daga ɗaki, mai abin kunya ƙatuwa da ke kina fitsarin kwance”

    “Ba zan fita da ita ɗin ba, uban shishshigi ko ina ruwanka, tun da ba a kan ka nayi ba, kuma ruwa ne ya zube ba fitsari nayi ba”.

    “Au Mama ƙarya take yi miki kenan, ba zaki tashi ba?”

    Cikin tsiwa ta ce “Ba zan tashi ba”

    miƙa hannu yayi, ya janyota ya ɗagata, ya ce “Wallahi sai kin fita da katifar nan kin wanke kayan da kika yi tsiyar a kan su”. Idan da sabo Mama ta saba da wannan halin nasu na faɗace-faɗace, gashi Huzaifa ya bawa Rumaisa kusan shekaru shida, amma faɗa kamar suna ganin hanjin junansu.

    Mama ta sharesu ta ƙi ko kallon in da suke, Rumaisa ta dinga turjewa tana kwarara ihu.
    Basu yi aune ba suka ga Yaya Umar a tsakiyar ɗakin, take suka yi cirko-cirko suna kallonsa.

    Cikin kaushin murya ya ce “Meye haka karnuka ne ku?”

    Suka girgiza kai a tare.

    “Me kai mata take wannan ihun, da idon Mama bai sanya kun daina ba?”.

    “Fitsari ta yi a kwance, shi ne nace ta fita da kayan”

    Cikin mamaki Umar ya kalleta ya ce “Fitsarin kwance kuma? Kina me kika yi fitsari?”

    Cikin rauni ta ce “Wallahi Yaya tsautsayi ne, kasa tashi nayi”

    “Tsautsayin uban wa? Kwashe kayan ki fita ki wanke ƙazamar banza kawai”.

    Haka ta ja katifar ta fita da ita tsakar gida, ta kwaso kayan da ta yi wa fitsari ta hau wanki.

    Huzaifa ya faki idon Yaya Umar ya dinga yi mata dariya.
    Duk wanda ya fito tsakar gida ya ga katifar Rumaisa sai ya ce me ya fito da katifar, Huzaifa sai yayi farat ya gaya musu ai fitsarin kwance ta yi.

    Tausayinta ne ya kama Usman, ganin yadda take kuka, kuma ba ta saba yin fitsarin kwance ba, ya je ya karɓi kayan ya tayata.
    Kowa da abin da yake faɗa a kan Ruma, wasu na mata Addu’a shiriya wasu kuma na yi mata faɗa har da zagi.
    Tamkar gidan ‘yan mata, haka zaratan samarin nan suka kama aikin gida, wasu na wanke-wanke, wasu shara da Abin karyawa, kan gari ya ƙarasa haske, hatta ruwan da Rumaisa zata yi wanka, an dafa ta haɗa ta yi wanka.

    Haka suka jeru a tsakar gida, tare da Mama suna karyawa, Rumaisa kuwa sai shan kunun take da ƙyar tana yamutsa fuska.
    Can ta kalli Mama ta ce “Mama Kununa bai ji suga ba, yayi tsami da yawa”.

    Haushi ya kama Mama ta ce “Amma a gabanki aka zazzage sugan kowa ya ɗiba ko? Kuma kin san ya ƙare”

    Ta ture kofin kunun ta ce “Nifa dama kunun nan gudawa yake sani, gashi bai ji suga ba, ni cikina ma har ya fara ciwo”

    Umar kawai ya girgiza kai, Rumaisa ba zata taɓa zaman mintuna goma lafiya ba, ba tare da tayi abin da za a yi mata magana ba.
    Haidar ya kalleta, ya zura hannu a Aljihunsa ya ɗauko ɗari biyu ya bata ya ce “Jeki wurin Mamuda ya baki buredi da suga, akwai ruwan zafi sai ki haɗa shayi ki sha”

    Washe baki tayi, ta ce “Allah dai ya biya da aljanna, gadanga na Mama” ta ɗau kofin kununta ta turawa Mama kunun ta ce “Mama ki shanye kunun na bar miki” tayi waje.

    ***
    Da ƙyar ta ƙarasa makaranta yau, saboda ciwon cinyoyi da take yi, sakamakon horon da Yaya Umar ya bata a daren jiya.

    “Ruma hatsari kika yi ne?” Cewar wata matashiyar yarinya sa’ar Ruman, gannin yadda take tafiya da ƙyar.

    Ta haɗe rai ta ce “Me kika gani?”

    “Gani nayi kina tafiya da ƙyar, kamar wadda ta warke daga karaya”

    Cikin gatse Ruma ta ce “Eh, tirela ce tabi ta kaina, da ta wuce na taso na taho”

    “A’a Allah ya baki haƙuri”

    Duk da yadda jikinta babu daɗi, hakan bai hanata faɗace-faɗace da neman rigima ba, dan idan ba tayi hakan ba ace lafiyarta ƙalau ba.

    Bayan an tashi ba ta tsaya ko ina ba ta tafi gida, tana zuwa ta tarar da katifarta a tsakar gida kamar yadda ta barta.

    “Mama yanzu dan Allah a nan aka bar mini katifata, sai anyi baƙi sun tambayi ba’asi ace fitsarin kwance nayi?”

    “Au ba ke kika yi ba, ni nayi kenan?”

    Ta ƙarasa ta zauna a kusa da Mama ta ce “Haba Mama, kema fa kin san tsautsayi ne, rabona da fitsarin kwance tun ina jairiya, tun ban fi wata huɗu ba na daina fitsarin kwance” wani irin kallo Mama tayi mata, jin uwar ƙaryar da ta saki.

    Mama ta ce “Tashi ki cire Uniform, kiyi wanka ki zo kiyi salla, ki tsefe wannan kan naki, ƙazamar banza da yake ban yi magana ba, baki ga dama kin mayar da kai kin tsefe ba, kuma wallahi ya kai gobe in Allah ya kaimu baki gama tsifar nan ba, sai na zaneki”.
    Hannu ta saka ta shafa kanta, ƙanann kitso ne a kanta, a ƙalla guda arba’in da ɗoriya, Mama ta bata kuɗi ta je ayi mata kitson hannu guda biyar, saboda ba ta son tsifa, amma ta karɓi kuɗi a wurin Yaya Usman ta je aka yi mata ƙanana.
    Ta san yau ko Mama zata kwaɗanta ta ta cinye ba zata iya gama wannan tsifar ba, haka nan ta tashi ta je ta yi wanka, ta yi alwala ta saka wasu kayan. Ganin Mama ta tada salla, ta leƙa Window ta ga Usman da sallaya a hannu zai tafi masallacin juma’a, ta ɗau hijjabinta ta bi bayansa.
    Sai da ta fito ƙofar gida sannan ya kalleta ya ce “Ina zaki?”

    “Masallaci mana” ta bashi amsa.

    “Kin tambayi Mama?”

    Ta gyaɗa masa kai alamar eh.

    Ya ce “Shikenan muje” ya sanyata a gaba suka tafi masallaci.

    Mama ta daɗe tana yiwa Rumaisa Addu’a bayan ta idar da salla, kullum cikin Addu’a take yi mata, amma tana girma tamkar ana sake turata, ko alamar hankali babu a tare da Rumaisa.

    Da suka dawo daga masallaci tana kallon Rumaisa, ba ta ce mata uffan ba, Rumaisa sai raragefe take yi, tana sauraron ko Mama zata yi mata magana amma taga ta shareta.

    Ba tare da ta yi tsifar ba, ta ci Abincin ranarta tare da Yaya Aliyu, ya siyo kifi ɗauri biyu, ya bawa Mama ɗaya ya ce gashi nan duka gidan, ɗauri ɗaya kuma suka ci shi da Rumaisa.

    Bayan sallar la’asar, ta ɗau allonta ta tafi makarantar allo.
    Tana zuwa Habiba ta tare ta da harara, tare da sheda mata cewar Sani ya ce sai ya yi mata dukan tsiya, idan ba ta biya shi tayarsa ba.
    Tsaki Rumaisa tayi ta ce “To, ya kasheni ya huta mana, tayar banza da ta wofi, shi bai san tsautsayi ba”

    A ƙufule Habiba ta ce “Au hakama zaki ce? Ki zo girma da arziki na ara miki tayar, amma ki je ki ɓatar ko a jikinki?”

    “To tayar da kuɗi ya saya? Idan da kuɗi ya saya ya faɗi kuɗinta, yayyena su biya shi”

    Habiba da ta gama fusata ta ce “Dalla can, uwar meye a gidan naku, banda gayyar maza da tsiya, sai ka ce wata uwar kuka ajiye, har kike a faɗi kuɗin tayar a biya”

    “Ku kun ajiye wata uwar ɗin ne, da kuna da wani abun ai babarku ba zata sayar da fanke da safe ba” Tayi maganar tana murguɗa baki.

    Cikin rawar murya Habiba ta ce “Kar ki sake ki zagar mana uwa”

    “Ni ban zagi babarku ba, ni dai na san fanke take sayarwa, fanken naku ma mai Shegiyar tsada, ƙanana kamar ƙuli-ƙuli, dan ranar Yasir ya ce har kiyashi ya gani a cikin fanken” kan Rumaisa ta rufe bakinta, tuni Habiba ta shaƙo hijjabinta, zata rufeta da duka.
    Abinka dai mai nema a duhu, balle ya samu a sarari, nan Rumaisa ta zage ƙwanji ta tabattarwa da Habiba ita ɗin ƘANWAR MAZA ce.
    Abin takaici da malami a gefe yana biyawa wasu allo suka harƙe da dambe.
    A fusace ya miƙe ya saka bulala ya zane musu jiki, musamman Rumaisa, tsabar masifarta ya sanya baya son ta a ajinsa, kullum cikin rigima take, ga allonta sai yayi wata ba tayi wani rubutun ba, ga daƙiƙanci da surutu.

    Idan da abin da Rumaisa ta tsana bai wuce duka ba, ta ji zafin dukan bulalar da Malam Ashiru yayi mata  ba kaɗan ba, dan haka ta koma gefe tayi shiru tana kuka. Ta rasa meya sanya ya tsaneta haka.

    Habiba kuwa da ƙawayenta, suka ƙudiri aniyar idan aka tashi sai sun naɗawa Rumaisa duka saboda suna jin haushinta suma, a kan damben da aka yi a ƙofar gidan mai markaɗe ranar Alhamis, gashi ta zagi fanken babar ƙawarsu.

    Ana tashi cike da takaicin dukan da Malam yayi musu, Rumaisa ta ɗau allonta ta nufi gida, sai share hawaye take. Sai dai yau babu tsokana a hanya, babu neman magana saboda bayanta sai raɗaɗi yake na dukan da malam yayi mata, gashi ba ta warke daga ciwon jikin punishment ɗin Yaya Umar ba.
    Babu tsammani ta tarar da su Habiba a wani lungu suna jiran isowarta.
    Turus tayi tana binsu da kallo kamar ba ta sansu ba.

    Babu ko ɗar ta cigaba da tafiya tana yinƙurin ratse su ta wuce.

    Shan gabanta Habiba ta yi ta ce “Ke kin isa ki tafi, ba dai ni kika zaga ba, kika kuma zagi babarmu ba, wallahi yau sai kin gane kuskurenki, kuma wallahi Sani ma ya ce sai kin biya shi tayarsa.
    Ɗaya daga cikin yaran ta ce “Ai wallahi yau sai kin daku, haka nima ranar kika zubar mini da markaɗe, zaki gane baki da wayo”.

    Bin su Rumaisa take da ido, sai kurari suke amma an rasa wadda zata kaiwa Rumaisa duka.
    Sake yinƙurin wucewa tayi, amma Habiba ta janyo Rumaisa ta baya, yaran suka fara kai mata duka.
    Tayi kukan kura, ta ɗaga allonta saukewa Habiba allonta a fuska, wani uban ihu Habiba ta kurma, jin danshi a hancinta.
    Tamkar namiji a filin dambe, haka Rumaisa ta zage ita kaɗai ta dinga dukan yaran nan, yadda ta dunƙule hannu tana kai naushi, kai ba ka ce ‘ya mace bace.

    Da ƙyar da siɗin goshi wani mutum ya rabasu, saboda Rumaisa akwai taurin kai, zuciyarta a bushe ana rabasu tana cigaba da kai duka.
    Ta ɗau allonta ta nufi gida, tana ta huci, duk da dukan da tayi musu sai dai jikinta duk yayi tsami ita ma. Dama ga jikin nata babu daɗi ji

    Sai dai kash, tuni wasu daga cikin yayyen yaran maza suka samu labari, suka yi gaba zasu datse Rumaisa a hanya, su zaneta.

    Ayshercool
    08081012143

    [16/06, 9:00 pm] JAKADIYAR AREWA:                    ƘANWAR MAZA

    BY AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

    Ku yi subscribing YouTube channel ɗin mu, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro.
    https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
    Arewabooks @ ayshercool7724
    Watpad@ ayshercool7724

    MIKIYA WRITER’S ASSOCIATION

  • Noor Al Hayat 80

    Noor Al Hayat 80

    Daren ranan a gidan khadijah ta kwana don Aliyu bai takura ta sai sun koma gida ba shi dai yayi wucewarsa, washegari yayyin mahaifiyar ta maxa duk suka wuce bayan sun cika ta da kyautan kudi mai yawa tunda basu samu sun mata komai na aure ba, Su Safeenah basu yarda sun bi iyayen nasu ba wai sai sun je gidan khadijah, Hajiya Rahamah tace “Gaskiya kam ya kamata ku je sai ku dawo anjima da yamma” Khadijah taji dadi sosai tace “Umma don Allah su kwana mana” Mum dinsu Jawahir tace “A’a su dai dawo da yamma” ta marairaice tace “Toh sai mu dawo tare” Hajiya Rahamah tace “Ki dawo kiyi me khadijah, ina kika taba jin amarya na yawo daga kai ta dakinta, wannan ma ai lalura yasa kika fito…” shiru khadijah tayi bata ce komai ba jikinta yayi sanyi, Driver aka sa ya maida su can gidan nata, Mum din Jawahir tace “Sai ki fara kiran mijin naki ki sanar da shi xuwan ku” a hankali khadijah tace “Toh…” Daga haka ta mike ta tafi daki ta dau wayarta, kiran Aliyu ta shiga yi, yana dagawa yayi sallama yace “Good morning wife” ta turo baki tace “Xa mu dawo gida yanxu da su Safeenah” yace “Ohk, in taho in dauke ku ne?” Tace “A’a driver xai maido mu” yace “Alryt then, Allah ya kawo ku lafiya, am already missing you dear” Bata ce komai ba ta katse wayar ta, Sha biyu saura suka dau hanyar gida tare da Safeenah, Deejah da Maimoon, a waje drivern yayi park duk suka sauka motar suka masa godiya, khadijah ta bude gate din tana gaida mai gadi dake gaisheta shi ma, sauran duk suka gaisa da shi sannan suka bi bayanta, a hankali ta murda kofar parlorn, Babu kowa ciki sai sanyin ac da tv dake a kunne, ta shiga su Safeenah na biye da ita har cikin parlon duk suka xaxxauna, tana murmushi tace “Bari in kawo maku ruwa” Bata jira cewarsu ba ta wuce Kitchen ta dauko tray da cups ta bude fridge ta daura lemo da ruwa a kan tray din ta dawo ta ajiye masu, Safeenah na murmushi tace “Thanks sis” murmushin tayi ita ma ta wuce sama, a hankali ta bude kofar bedroom din Aliyu, xaune ta samesa yana operating laptop, ta hade rai tace “Baxa ka taho ku gaisa da su ba” ajiye laptop din yayi yana murmushi yace “I was waiting for ur instruction ne dama kar in yi laifi” hararansa tayi ta juya ta wuce, yana murmushi ya mike ya bi bayanta, har ya shigo parlorn yana kallon su Safeenah yace “Sannun ku da xuwa” duk suka gaishesa da fara’a, ya xauna saman kujera yana murmushi yace “Lafiya lau, fatan kun baro mutan gida lafiya” duk suka ce “Alhmdllh” yace “Maa sha Allah” sannan ya mike yana kallon khadijah ya koma sama, mikewa tayi tace “Mu je sama ku yi alwala it’s almost time for zuhr” tashi suka yi gaba daya suka wuce sama xuwa dakinta, sai bayan da suka idar ta cire hijab dinta tace “Let me cook something for us” mikewa suka yi gaba daya Safeenah tace “We will do that together” dariya kawai khadijah tayi, tuwon shinkafa da lafiyayyen veg soup suka hada gaba daya, aikin yayi sauri saboda yawansu, Safeenah na gama kwashe tuwon a leda tace “Toh ina xa a sa ma mijin ki” khadijah tace “It’s not necessary, namu ne kadai, nasan eatry xai je shi” Deejah ta saki baki tana kallonta tace “Eatry kuma Namecy?” Murmushi kawai khadijah tayi, Maimoon tace “Uhmm lallai ma, tun yanxu xa ki fara sakaci haka Khadijah?? Har kina son mijin ki ya tafi wani waje ya ci abinci” Kallonta khadijah tayi bata ce komai ba, Safeenah ta dauko wani kwali mai dauke da cooler mai kyau ta fiddo babba da karami ta tafi sink ta wanke shi tas ta tsane sannan ta sa tuwo ta rufe, Deejah ta dau na miyan ta xuba miya da isasshen nama a ciki ta rufe duk suka daura a tray, ita dai khadijah na tsaye tana kallonsu kamar an dasa ta, Maimoon ta dauko plate mai kyau da spoon da cup ta dauraye ta daura kan tray din, Safeenah ce ta hada xobon dake ajiye tun daxu suna jiran ya huce, xobon ya ji kayan kamshi da abarba da cucumber, ta xuba kananun kankara kan thick xobon, sabon jug ta dauko ta kusa cika jug din ta rufe, tana kallon khadijah tace “Sai ki kai masa daki, ko shi ma waitress din eatry xa su maki??” Khadijah bata san lkcn da tayi dariya ba sai dai bata ce komai ba ta dau tray din abincin da drink ta fita kitchen din ta wuce sama, a hankali ta tura kofar dakinsa, yana xaune yana danna laptop har sannan, ya dago yana kallonta har ta iso inda yake ta durkusa ta ajiye tray din ba tare da ta kallesa ba ta mike ta nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fita, yayi murmushi sanin this might not be her thinking, infact it’s not even her thinking… Khadijah ce xata kawo masa abinci haka kawai, shafa kai yyi yana murmushi. Kafin ta koma kitchen din duk sun wanke duk abubuwan da suka bata, Maimoon ta fito masu da abincin nan tsakiyar parlor, Xaunawa suka yi gaba daya suka ci a tare, Deejah ta gyara wajen ta tafi da komai kitchen, suna ta xaune parlor suna hira khadijah ta dinga jin kamar kar su ce xasu tafi, ta dinga addu’ar Allah sa su manta kawai su kwana, suna nan a haka har aka kira la’asar suka wuce sama xuwa dakinta duk suka yi sallah, sai a sannan suka fara shirin komawa gida, duk jikin khadijah yayi sanyi ta xauna can karshen gado tana kallonsu a sanyaye, Dariya Deejah ta dinga mata, Safeenah na gama gyara fuskarta ta dawo kusa da ita tace “Kar ki damu sis xa mu dinga haduwa frequently in sha Allah kin ji, Kuma ga waya xa mu dinga communicating” hawaye ne ya cika idon khadijah, Safeenah tayi dariya tace “Tabb, to mu fa gobe da safe xa mu koma Abuja, Deejah kadai ce a nan, kema nasan soon xa ki koma uk saboda karatun ki” Ita dai khadijah bata ce komai ba, bayan duk sun gama Safeenah tace “I notice something khadijah, it seems har yanxu baki kwantar da hankalin ki da mijin ki ba, are you still thinking of the past koh? I will advice you to just erase that of ur mind idan ba haka ba baxa ki taba samun kwanciyar hankali gidan ki ba, nobody is above mistake khadijah, barin ma irin wannan mistake din da aka yi ba da gangan ba, wllh idan baki maida hankali kin rungumi mijin ki ba kina ji kina gani wata a waje xata yi hakan ga mijin ki very handsome gentleman, Wallahi Kar ki kuskura wata ta hango maki shi a waje, don rashin samun kulawa gun ki xai sa ya ba ta waje dama, Haba sai kace ba wayayya ba Khadijah…” turo baki khadijah tayi, Safeenah ta dawo kusa da ita ta kamo hannunta tace “that’s just it, kiyi hakuri ki xauna xuciya daya da mijin ki, forget the past, ni na tabbatar mijin ki yana son ki kema kuma kina son sa sosai” Khadijah ta sauke idonta a hankali, Maganganu sosai Safeenah ta yi mata da yasa duk jikinta yayi sanyi, daga karshe ta mike tace “Toh mu xa mu tafi khadijah sai mun yi waya” khadijah ta mike a hankali tace “Bari in gaya masa” daga haka ta fita ta shiga dakin Aliyu suka kusa cin karo don fitowa xai yi shi ma daga dakin, jawota yayi jikinsa ya rufe kofar yana kallon eye balls dinta, ta sauke idonta tace “Sake ni” ba musu ya saketa yana murmushi, tace “Xa su wuce” yace “I was thinking kwana xa su yi” ta girgixa kai tace “Gobe da safe xa su wuce Abuja” yace “Ohk ba nan suke ba dama?” Tace “Deejah ce kadai a nan” yace “Alryt am coming now” juyawa tayi ta fita, turarruka da kayan kwalliya na lefenta ta debar masu mai yawa suka sauka downstairs tana jin kewansu, ba a dau lkci ba Aliyu ya sauko, dubu talatin ya ba su gaba daya, suka ki amsa, khadijah ta hade rai ta karbi kudin hannunsa ta bude jakar Deejah tace “Ae ba ku kuka ce ya baku ba toh” Murmushi kawai Aliyu yake yana kallonta, suka masa godiya yace “No thanks sisters, or shud I drop you?” Safeenah tace “A’a mun gode xa mu tadda driver bakin titi” yace “Alryt then, Allah ya kiyaye hanya” duk suka amsa masa da Amin, har bakin gate khadijah ta rakasu, Maimoon tace “Kin ga ki koma haka mun gode sosai Khadijah, Allah bar xumunci” sai a sannan hawaye ya cika idonta cikin sanyin murya tace “I am going to miss you all” rungume juna suka yi gaba daya, tana ji tana gani suka wuce ta juyo ta koma ciki tana goge hawayen dake xuba mata, Aliyu dake parlor ya dinga kallonta har ta wuce sama. Ko minti talatin su Safeenah basu yi da barin gidan ba Barrister ya xo, Aliyu ya bude masa kofa suka gaisa, Barrister ya xauna kan kujera yace “Ya gidan” Aliyu na shafa kai ya xauna shi ma yace “Alhmdllh, ya aiki” Barrister yace “Mun gode Allah, ya mum shureim” Mikewa Aliyu yayi yace “She’s upstairs” daga haka ya wuce sama, bude kofar dakinta yayi ya ganta kwance ta rufe fuskarta da pillow, ya isa kan gadon ya xauna kusa da ita ya dagota a hankali yace “Ummu Shureim” Bude ido tayi tana kallonsa, ya sakar mata lallausan murmushi yace “Mu je ku gaisa da Barrister” tace “Ya xo?” Yace “Sure” shi ya taimaka mata ta sauko saman gadon bayan ta sauko ta kwace hannunta shi dai bai ce komai ba ta sa hijab dinta suka fita dakin, gaisawa suka yi da Sudais ya mika ma Aliyu takardan hannunsa yace “Bata ta gani, I don’t want to do anything without her knowledge” Aliyu ya amsa ya mika mata, karban takardan tayi ta bude tana kallon content din, bayan wani lkci ta Dago a sanyaye tana kallonsa, murmushi yayi yace “Is that okay?” Girgixa masa kai tayi a hankali tace “Barrister ka kyalesa kawai, na yafe masa even for the sake of my dad” Karban takardan Aliyu yyi yana dubawa, Barrister na kallonta yace “Are sure Amira?” Kai ta gyada masa tana murmushi tace “Sure Barrister, na yafe ma kawu na, sai dai kuma tsakaninsa da mahaliccin sa” mikewa Barrister yayi yace “Toh Alhmdllh, Allah ya yafe mana gaba daya, but I don’t think ur forgiveness will count, coz dukiyar marayu yyi tampering da” Aliyu na gyada Kai yace “Haka ne” Barrister yace “Alryt xan koma, abinda ya kawo ni kenan dama” tace “Toh nagode sosai Barrister, bari in kawo maka ruwa” yace “Noo Amira, am okay” Tare suka fita da Aliyu, a sanyaye ta wuce sama don ita da gaske take jin ta yafe ma kawun ta. Gyara bedroom dinta tayi ta share ta goge ko ina, ta fito dakin kenan taga Aliyu ma ya fito rike da tray din abincin da ta kai masa da rana, karasawa tayi ta amsa tray din hannunsa, yana kallonta yace “Thank you” bata ce komai ba ta sauka downstairs ta wuce Kitchen. Tana xaune kan darduma bayan ta idar da magrib ya shigo dakin ya xauna gefen gado yace “Mu je ki raka ni” tace “Ina?” Yace “Gida, xan dauko wasu files a can” ta girgixa kai tace “A’a baxan fita ba, ni….” Ya katse ta yace “Ba fa shiga gidan xa ki yi ba” tace “Eh na sani” ya marairaice yace “Plss Ummu Shureim” turo baki tayi kamar xata yi kuka, yayi murmushi ya mike yace “Am waiting for you downstairs” A hankali ta mike ta linke pray mat din ta fita dakin, a kofar gidansu yayi parking yana kallonta yace “Baxan dade ba xan fito yanxu” kasa cewa komai tayi don sai take ga kamar bai dace ta ki shiga ba, can dai tace “Bari in gaida mumy” yace “Noo, ki bari ran Sunday sai mu xo gaisheta, it’s already late yanxu” kallonsa ta tsaya yi, ya gyada kai yace “Yea dear” daga haka ya juya ya wuce ciki, kamar yanda ya fada bai dade ba ya fito ya ajiye takardun bayan mota sannan ya shiga maxaunin driver suka bar layin, yace “Me kike son ci in siya maki” ta girgixa kai tace “I am not hungry” yace “Nasan bakya Jin yunwa… abun dadi nake nufi” tace “Baxan ci komai ba” ya kamo hannunta yace “A’a, gwara dai a siya maki ko kaxa ce koh?” tace “Ni nace maka bana ci” parking yayi gun da ake siyar da kaji yace “Ai baki isa ba..” Daga haka ya fita ya siyo masu guda biyu, ya bude bayan mota ya ajiye, yana kallonta yace “Fresh milk kike so ko youghurt?” Tace “Daxu fa na ci abinci me xanyi da yoghurt ko fresh milk” Yar dariya yayi yace “Toh naji ni xan siya in sha” gun da ake siyarwa ya kara parking ya fita ya siyo chill fresh milk ya bude back seat ya ajiye sannan suka dau hanyar gida, da kyar khadijah ta yarda ta xauna parlor tana bata fuska, ta dinga kallon kajin da ya ajiye gabanta sai kamshi yake ga Madara a glass cup a gefe, so mouth watering, a hankali ta kai hannu ta dau cinyar kaxa daya tace “Ni wannan ya isheni” ya kalleta bai ce komai ba ya dau naman shi ma ya kai bakinsa, satan kallonsa tayi bayan ta cinye na hannunta don sosai naman yayi mata dadi, ta turo baki tace “Ashe ma da dadi” ya danne dariyar sa ko kallonta bai yi ba, ta dau wani kaxan ta fara ci, a haka sai da ta kusa cin rabin wanda ya ajiye mata, ta dau madaran glass cup din ta shanye gaba daya, sai a sannan ya dago yana dubanta yace “Amma da muka shigo ne kika fara jin yunwan koh?” Mikewa tayi da sauri ta wuce sama tace “Nima ban sani ba” Murmushi yayi ya bi ta da kallo kamar yanda ita ma take murmushin ta wuce sama, cire kayan jikinta tayi ta linke ta ajiye sannan ta shiga bathroom, wanke bakinta tayi, tayi wankan ta fito, Bata wani jima sosai gaban mirror ba, ta feshe jikinta da turarruka kala kala ta dau kayan baccinta ta sa, sannan ta sa net a dogon gashinta ta kashe wutan dakin ta hau saman gado ta kwanta ta ja duvet ta rufe jikinta ta lumshe ido. Har kusan karfe sha daya ta kasa bacci sabida thirst da take ta ji, ta tashi daga karshe ta sauka kan gadon, ta nufi kofa ta bude a hankali ta fito tana kallon kofar dakinsa dake a rufe, sauka downstairs tayi taga wutan parlorn gaba daya a kashe har kitchen, kunna wutan parlorn tayi ta nufi kitchen ta shiga tana kokarin kunna switch taji an cafkota, ihu ta fasa a mugun tsorace, ya kunna wutan da sauri ganin da gaske ta tsorata ya rungumeta yace “I am sorry iman, I didn’t mean to scare the life out of you, wasa nake maki, kiyi hakuri plss” hawaye ya dinga xuba idonta jikinta na bari xuciyarta na bugawa, tausayinta yaji ganin da gaske ta tsorata, ya kasa karasa sauran coffeen da ya rage cup din hannunsa ya ajiye, yana rike da ita ya kashe wutan suka fito yace “I heard ur footsteps shi yasa na kashe wutan, am sorry for scaring you…” ita dai bata ce komai ba har lkcn xuciyarta bai dawo dai dai ba, suna isa stairs ya juyo da sauri yana kallonta yace “Me kika sakko yi” cikin sanyin murya tace “Ruwa xan sha” saketa yayi don xuwa ya dauko mata ruwan ta bi bayansa, yayi murmushi ya bude fridge ya fiddo ruwa ya xuba mata a cup ya mika mata ta amsa ta sha ya karbi cup din ya ajiye, yana rike da ita suka wuce sama bude dakinsa yayi xata kwace hannunta ta wuce nata dakin ya ki saketa ya jawota dakinsa ya rufe kofar, sanyi ne sosai a dakin saboda Ac da ya kure ga fitila kuma a kashe, xata bude kofa ta fita ya riketa murya can kasa yace “Kin san har yanxu ba muyi sallah mun nuna godiya ga Allah.. mu yi addu’ar xaman lafiya da kwanciyar hankali mai dorewa ba Iman?” Da sauri tace “Ni dai nayi, Kai ne dai baka yi ba” yace “Noo kamata yayi muyi tare” tace “I am not clean….” Kallonta ya dinga yi cikin duhun yace “Really??” gabanta na faduwa tace “Ehh” yace “Ban yarda ba” ta hade rai tace “Saboda ni makaryaciya ce?” Yar dariya yayi taji ya dauketa cak sai saman gado, ya kwantar da ita yace “I have to check for my self…” Kara tayi a rikice tace “Nashiga uku, don…” Bai bari ta karasa ba ya rufe bakinta, tun tana turasa tana son kwace kanta har ta gaji, lkci daya kuma jikinta ya mutu, kwata kwata Aliyu bai bata breathing space ba, ya dinga exploring dinta as if his life depend on that… daga karshe ta sakar masa jiki gaba daya, sai dai bakinta bai daina cewa stop it plss idan ma ba kasa kunne kayi sosai ba baxa ka ji me take cewa ba, lkci daya ta rikice masa ganin ba da wasa yake ba, nan ta fara hawaye tana rokonsa, sai take ganin abun kamar na 7 years back, the only difference is that he is not fierce, just romantic and very careful, upon her plea bai iya ya kyaleta ba duk da yayi kokarin ganin yayi hakan amma ya kasa…. Bayan lokaci me tsawo ya dago a hankali ya ga bata gefensa kamar ynda ya bar ta, mikewa xaune yayi da sauri, shesshekar kukanta ya dinga ji can other side of the bed, ya tashi da kyar ya nufi wajen, takurewa tayi waje daya tana kuka a hankali, jikinsa yyi sanyi ya duka gabanta yace “I am very sorry Iman, I….” Rasa abinda xae ce mata yyi ya dagota ta fashe da matsanancin kuka, ya rungume ta xuciyarsa na bugawa yace “I didn’t mean to hurt you again” gaba daya tayi laushi, kuka kawai take, ya dagota ya kwantar kan gadon yace “Kiyi hakuri plss Iman, forgive me….” cikin rawar murya tace “Kace min baxan ji xafi ba” Kallonta yake cikin duhun don bai ma san ya fadi hakan ba, ya kwantar da ita kirjinsa a hankali yace “But did you feeling any pain?” Kai ta dinga gyada masa hawaye na xubo mata, yayi shiru bayan wani lkci ya kai bakinsa kunnenta yace “Just like the 1st experience?” Girgixa masa kai tayi, Yana shafa bayanta yana murmushi sanin da ba dan shi yyi deflower dinta ba da bbu abinda xai hanasa cewa budurwa ce ita, kwantar da ita yayi ya mike ya shiga bathroom, ya hada mata ruwan wanka, ya dawo ya kai ta bathroom din, shi ya taimaka tayi wanka tana nonnokewa sannan ya fito tare da ita, babu bata lokaci kuma bacci ya dauketa, sai a sannan ya kunna wutan dakin yana kallon bedsheet din gadon, Bai ga abinda yake xato ba, yayi murmushi ya dawo kusa da ita yana kallonta yana Kara jin wani mugun sonta na fixgarsa, it’s just great being with her, and it’s the sweetest thing he have ever imagined, tashi yayi daga karshe ya shiga bathroom yayi wanka shi ma ya fito ya shirya sannan ya kashe wutan dakin ya kwanta kusa da ita ta shige jikinsa kamar jira take, ya kankameta hade da lumshe ido.

  • Kanwar Maza 4

    Kanwar Maza 4

    p 4

     

    Ko da sati ya zagayo, Mama tana sa ran ta ga Ruma ta shirya ta tafi makarantar allo, amma ta ga bata da niyyar yin hakan.
    Sai ma aiki take a tsakar gida, wanda ba ta saba ba, tana naɗe yayyenta je komai.
    Aliyu ne ya fito daga banɗaki, hannunsa riƙe da buta ya kalli Ruma ya ce “Ke ina makarantar allon?”
    Ta ɗan ɓata fuska ta ce “Ni na cire kaina na daina zuwa”.

    “Saboda ke ki ka saka kanki, shine sama ta ka ki ka cire kan ki ko? Da alama baki da gaskiya”

    Mama ta fito tsakar gida ta ce “Ali ajiye butar nan ka je mini makarantar allon ka ji me ta aikata, dan ban yadda da ita ba”  dan jikinta ya bata Ruma wani laifin tayi.

    “Wallahi Mama ba abin da na yi, ba sai ya je makarantar ba, idan ya je ma sharri za su yi mini, ba sa sona malaman”

    Mama ta ce “Au malaman ne suke miki ƙarya Rumaisa, ai ko me za ace mini kin aikata ba zan musa ba”

    Huzaifa daga cikin ɗaki ya ce “Dama saboda ƙawayenta ya sa ta ce ita ma a sakata a makarantar, ba dan Allah take zuwa makarantar ba “.

    Aliyu ya saka jallabiyarsa ya tafi makarantar allon.

    Bayan fitarsa rantse-rantse take ta yiwa Mama, akan ita fa ba abin da ta aikata a makarantar nan, amma Mama ta shareta.

    “Ruma!”

    “Na’am Yaya Sadik ”

    “Zo ki sayo mana ƙwai ki soya mana mu karya”
    Kasancewar Ruma akwai kwaɗayi, ya sanya ta daina fargabar zuwan Aliyu makarantar su, ta karɓi kuɗi ta tafi aiken da Abubakar ya yi mata.

    **********

    A kashingiɗe take a kan kujera, ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, ta tattara dukkan wata nutsuwarta a kan ƙatuwar wayar hannunta, da alama ko me take kallo mai muhimmanci ne.
    “Samha me ki ke wa wannan kallon ƙurillar ne?”

    Wadda aka kira da Samhan ba ta motsa ba, balle ta daina abin da take yi.

    Hannu ɗayar ta saka, ta zare wayar daga hannun Samhan, tana dubawa.
    Har a wannan karon, Samha ba ta yi motsi ba, balle ta karɓi wayarta ta ba.

    “Samha kina da hankali kuwa? Wai dan Allah da gaske ki ke dama?”

    Samha ta ja ajiyar zuciya ta ce “Nusaiba, ke da kin ɗauka da wasa nake yi dama?”

    Nusaiba ta jinjina kai ta ce “Eh, ni ban san abin da ki ke faɗa har zuciyarki ba”

    Samha ta gyara zamanta ta kalli Nusaiba, cike da son tabattar mata abin da take faɗa ta ce “Nusaiba, ban fara dan na daina ba, ko zan tafi tsirara zan mallaki abin da zuciyata take muradi”

    Nusaiba ta ɗan jinjina kai ta ce “Amma ya batun alaƙa fa, ko kin manta?”.

    “Alaƙa bata gabana, na san a yadda zan yi wasana. Kar ki manta anjima akwai walima a gidan Shamaki”

    “Hmmm Allah ya kaimu, Allah ya sa ba wani banzan abun zaki yi ba”.

    Wani ɗan guntun murmushi Samha tayi, ta ce “Koma dai menene, we should see”

    ********

    Ko da Runaisa ta dawo gida daga aiken Yaya Sadik, tana daga tsakar 6 tarar da Yaya Aliyu a falo yana wassafawa Mama abin da aka gaya masa a makarantar allonsu, ga Yaya Umar a zaune.

    “Wallahi mama ba ki ji yadda ake complain a kan yarinyar nan ba, malaminsu ya ce dama ko ta dawo korarta za su yi, ba karatun take yi ba, sai tsokana da fitsara, da damben da yaran mutane, wai sam ba ta da nutsuwa da ɗa’a, malam Babba ya tara su zai hukunta su sun yi laifi ta ɗau allonta ta gudu, yana kiranta amma tayi masa banza”.

    Cike da fushi Umar ya ce “Ba kune kuke goya mata baya take wani rashin mutuncin ba, tun da ta san ko me ta ɗauko zaku tare mata ba, ku bari ta tsokano waɗanda zasu nakasata yadda gobe ba zata ƙara ba. Babu wanda yake faɗar alkhairi a kan ta sai sharri” ya ƙarasa maganar yana fitowa tsakar gida cike da fushi.suna yin ido huɗu da Rumaisa ta saki ƙwan hannunta a ƙasa ta na ja da baya, saboda tsoro da fargaba.

    Taku biyu ya yi ya danƙota, ya sanya hannunsa ya riƙe kunnenta ɗaya da ƙarfi.
    Wani irin ihu ta kurma tana riƙe hannunsa, saboda ji tayi kamar zata ɗaga kai ta ga kunnen a hannunsa, saboda azabar zafi.

    “Dan ubanki idan har ba zaki canza hali ba, makarantar kwana zan kai ki, tunda ba ki in da yake miki ciwo ba, ko mu mayar da ke can ƙauye, su miki aure”
    Usman ya ce ‘Ai Rumaisa sai ka ce wadda ta sha nonon aljana, hatsabibancin ta yayi yawa, ba ta jin magana sam”

    Abubakar ne ya fito daga ɗakinsu a fusace, ya ƙaraso ya riƙe hannun Rumaisa, ya kalli Yaya Umar ya ce “Sakar mata kunne” Umar ya ɗan yi turus yana kallon Sadik.

    “Baka ji bane?”

    Sadik ya maimaita masa. Yaya Faruk ya saki kunnen Rumaisa, da idanunta tuni suka yi ja saboda kuka.

    Ya janyota ya zaunar da ita a kan tabarma, ya dinga share mata hawayen fuskarta.

    Cikin ɓacin rai ya ce “Yakamata ku dinga yiwa kan ku adalci a kan yarinyar nan, ita kaɗai ta tashi a cikinmu mace, tayaya zaku ce sai kun tanƙwarata yadda ku ke so? Tayi laifi kowa yayo kanta, ba mai yi mata nasiha, daga mai ce mata munafuka sai me ce mata aljana haka ake rayuwa?”

    Yasir ya ce “Wallahi Yaya Sadik, duk ranar da yarinyar nan ta kwaikwaya maka rashin mutuncin da take aikatawa zaka gane ba tsanarta aka yi ba”

    “Koma dai yane, a dinga barin yarinya ta huta a daina takura mata haka ”

    Guntun tsaki Umar ya ja, ya fice daga gidan gaba daya, suna zaman zamansu Mama ta haifo wannan ‘yar kalen hanjin da ta gallabi rayuwarsu.

    Yau cikin dare, Mama ta tashi tana ibada, kamar yadda ta saba domin a cewarta wanda duk ya tara zuriya yake neman kuma dacewa, bai ga ta bacci ba.
    Fitilar ɗakinta ta kunna, haske ya gauraye ko ina, Rumaisa tayi rashe-rashe a kan katifa, zaninta daban ita daban daga ita sai wando, kanta ko ɗan kwali babu.
    Mama ta girgiza kai, ta janyo zanin ta ɗaura mata, ta saka mata hula ta lulluɓeta, sannan ta fice ta ɗauro alwala ta zo ta tayar da salla. Sai dai sam Ruma ba ta san an yi bama, tana ta fama da bacci.

    Can Mama ta kuma juyawa, amma ta ga Rumisa ta kuma yada zanin, ƙafafuwanta duk suna ƙasan katifar, ta kuma tumɓur tana bacci.
    Haushi ne ya kama Mama, ta ƙarasa in da take, ta ɗala mata duka a cinya. Amma maimakon ta tashi, sai ta sake dunƙulewa tana bacci.
    “Ke Ruma, ba zaki tashi ba sai na saka miki bulala?” Da ƙyar ta tashi tana murza ido tana kalle-kalle.

    ‘tashi ki ɗauki rigarki ki saka, ki ɗaure kanki ki je ki yo alwala ki salla”.

    “Wai har asubar ta yi ne?”

    Mama ta ce “Wato ke idan ba sallar farilla ba, baki san ki yi nafila ba, sai dai ki saki leɓe kina bacci. Ki je kiyi alwala ki zo ki yi salla ki roƙi Allah ya yaye miki wannan wautar da rashin hankali da kike fama da shi” kafin Mama ta gama maganar, Rumaisa ta sake ɓingirewa ta kwanta.
    Aikuwa mama ta ƙule, ta janyo mafici ta shiga rafka mata a cinyoyinta, a razane ta miƙe tana sosh-soshe.
    Mama ta bata riga da ɗan kwali ta ɗaura, ta korata tayo alwala.

    Mama ta koma kan tata sallayar ta cigaba da salla.
    Kusan mintuna arba’in, Mama ta manta ta tura Rumaisa tayi alwala, ta kalli shimfiɗarta taga bata wurin.
    Da sauri ta tashi ta fita tsakar gida tana dubawa, sai dai babu Rumaisa babu dalilinta.
    Lelleƙawa Mama ta hau yi, tana nemanta a cikin gidan amma bata nan.

    “Innalillahi wa Innalillahi raji’un, ina yarinyar nan ta shiga ne haka?” Tayi maganar lokacin da ta ƙarasa soro tana haska fitila, amma taga ƙofar gidan a rufe.

    Ƙofar ɗakin samarin gidan ta tsaya tana bubbugawa da ɗan ƙarfi.
    Usman ne ya taso cikin yanayi ya bacci, ya kalli Mama ya ce ‘Mama lafiya kuwa?”.

    Cikin tashin hankali ta ce “Ruma na tasa tayi sallar dare, daga ta fito tayi alwala, na nemeta na rasa”.

    Ƙwalalo ido waje yayi, ya ce “Ruman? To ina ta tafi?”

    Mama ta girgiza kai ta ce “Ban sani ba, na duba ƙofar gida tana rufe da sakata ba a buɗe ba”

    Mamaki duk ya cika Usman ya ce “To in ta shiga a tsohon daren nan, bari na sako rigata a buɗe gidan a dudduba”.

    Ya shiga cikin ɗakin, ya kunna wutar lantarkin ɗakinsu, sai ga Ruma a tsakiyar su Yasir tana bacci.

    Kunna fitilar ne ya sanya Huzaifa ƙoƙarin yin juyi, amma ya ji mutum a kusa da shi, yayi zaton Yasir ne, dan haka ya dage ya hankaɗa Rumaisa, ta kifa kan Yasir amma ba ta farka ba.

    Usman Ya ce “mama leƙo kiga”
    Jiki na rawa mama ta shiga ɗakin, daidai lokacin da Yasir ya ji nauyi a kansa shi ma ya dage ya hankaɗata gefe guda.
    Mama ta shiga tafa hannuwa tana salati, a irin magagin bacci, da shirme na Rumaisa tsaf za a saceta tana wannan baccin na asara.
    A ƙufule Huzaifa ya tashi yana zage-zage ya zata Yasir ne yake damne shi, amma ya ga Ruma a tsakiyar su, ga su Mama a tsaye.

    “Ke uban me ki ke yi a ɗakinmu, mama meyafaru?”

    Jin hayaniya ya sanya Sadik ma farkawa, ya dinga kallonsu ɗaya bayan ɗaya ‘mama lafiya kuwa’.

    ‘lafiya lau, kai Huzaifa taso mini ita’
    Abubakar ya kalli in da Rumaisa ke ta more laushin katifa tana barci.
    “Wai me ya kawo yarinyar nan ɗakin nan?”

    Usman yayu masa bayani kamar yadda Mama tayi masa.

    Sadik ya ce “Kai Huzaifa, kai da Yasir ku sauko ku bar mata katifar dan Allah, wannan ba tashi zata yi ba”
    Yasir ya ce “Kaii, Yaya haryanzu fa yarinyar nan tana fitsarin kwance, kawai a tasheta ta fita, kar ta tsula mana fitsari dan katifar nan wuyar bushewa za ta yi”.

    Yaya Umar kuwa tun shigowar Rumaisa yana kallonta, lokacin bai daɗe da kwanciya ba, ya ganta ta shigo tana tangal tangal, ta nemi wuri ta kwanta, tun da ta shigo yana kallonta.

    Mama ta ce “Ba zata kwana a nan ba, taso mini ita ta wuce mu tafi”.

    Yasir ya daddaki Rumaisa a kafaɗa, amma ta hau surutai da irin faɗace-faɗacen da suke yi da yara a makaranta.

    Ƙarshe haushi ya ƙule, Umar ya tashi danƙo Ruma ya hankaɗowa Mama ita tsakar gida, ya rufe musu ƙofa.
    Mama har mamakin wannan magagi da kuma suratan baccin da Rumaisa take yi, ita duk wani da mutane suke yi, nata ya zarta ƙa’ida.
    Har mama ta kama hannunta zuwa ɗaki, magagin bacci take yi.

    ******
    Sassanyar iskar da bishiyoyin ke bayarwa ne ya haɗu da ƙamshin furanni, tare da samar wani kyakkyawan yanayi mai sanyawa zukata nutsuwa da annashuwa.

    Duk da wannan tarin ni’ima, gaba ɗaya Samha ba ta jin dadin yanayin sam.
    Wayar hannunta ce ta fara ringing, wadda ta katse mata dogon tunanin da take yi, ɗagawa tayi ta kara wayar a kunneta ba tare da ta ce komai ba.
    “Ki fito mu tafi, ina haraba”.

    “Ok, ya maganar mu? Kun yi magana da ita, zasu zo ne”.
    Nusaiba ta ce “Hmm, Samha kenan ke meya hana ki tambayeta?”

    “Nusaiba bana son wasa, am serious about it”.

    Nusaiba ta ɗan taɓe baki ta ce “Eh, za su zo” Ta sauke wayar daga kunnenta, ta nufi hanyar fita daga lambun.

    ***
    Mama tana yawan yin istigfari da nemawa Rumaisa shiriya, musamman yadda bakin mutane yayi yawa a kanta, duk wani rashin ji irin na ɗa namiji shi take yi, bama irin na mata sa’aninta ba, duk sa’aninta ta kere su a rashin ji. Babu yadda Mama ba tayi ba a kan aje a bawa malaman makarantar allon su haƙuri, ta koma amma mirsisi Yaya Umar ya ce sai dai a sauya mata makaranta, in da zata fi mayar da hankali, amma a ƙasan zuciyarsa zafin maganganun da malaman suka yi a kan Rumaisa ne ya fi ɓata masa rai har ya sanya ya ce ba zata koma ba.

    Ita kuwa Rumaisa ganin Yaya Umar ya hana a mayar da ita makarantar allon Malam Babba, tayi ta murna a ganinta ta huta da zuwa makarantar nan mai cike da takurar tsiya, Allah ya sa makarantar bokon ma a cireta, ta dawo gida Mama ta bata jari ta dinga sayar da wainar fulawa a ƙofar gida. Murmushi ta yi bayan wannan tunanin ya zo ranta.

    Ta dubi Abdallah da yake ninke kayan da ya wanke ta ce “Yaya Abdallah, dan zaka gayawa abokananka zan fara sayar da wainar fulawa, naga kai ne me abokai masu kuɗi, ka talatta musu su zo su dinga saya, ba irin abokan su Huzaifa ba gayyar ƙolawa da tsamaye ba”
    Saroro ya kalleta ya ce “wace irin wainar fulawa kuma?”

    “Eh tun da na daina zuwa makarantar allon, sai Mama ta bani jari na diga sayar da wainar fulawa a ƙofar gida”.

    Huzaifa ya ce “Eh dama kin yi kalar sayar da wainar fulawar ai, ai ni da kai na zan din ga yi miki ciniki, ai suyar wainar ce ta dace da le delu”

    Murguɗa baki tayi ta ce “Da dai ban san halinka bane, ci ka tsere ka rusa mini jari, kama kar ka sake ce mini wata deluna gaya maka.
    Ta mayar da hankalinta kan Abdallah ta ce “Dan Allah Yaya Abdallah ka yi magana mana”.

    “To ai Ruma na rasa me zance miki ne, wace irin wainar fulawa ana zaman lafiya”.

    “To Yaya ba gara ace ina sana’a ba, kuma ku huta ba, ana ta shelar mata su kama sana’a, Mama ai zaki bani jari ki saka mini albarka ko?”

    Mama ta ce “kada Allah ya nuna mini wannan rana, kuma kar ki sake sakoni a cikin shirmenki, idan kuma ki ka sake sai na ci ubanki ke da soya wainar fulawa a ƙofar gidan, tun da ke dai Allah bai sa an raba hankali kin samu ba” ɓata fuska tayi a ranta ta ce ‘sai na tambayi Yaya Abubakar, na san shi ba zai hana ni ba ai, tun tuni ake cewa mata su kama sana’a ni kuma zan yi ana hanani’.

    Umar yana ɗaki yana jin shirmen da Ruma take, ji yake kamar ya ɗauketa ya kai ta boarding kowa ya huta, amma ya san Mama ba zata taɓa amincewa ba.

    Wayewar garin Allah, wurin ƙarfe sha ɗaya na safe, mama na shirin fita, telar da take yiwa Mama ɗinki ta aiko da ɗinkin da Mama ta kai mata, bayan mama ta karɓi ɗinkin ta sallami yaron, ta kalli Ruma ta miƙa mata ledar ta ce “gashi nan kayanki ne”.

    Da murna ta karɓi ledar ta buɗe, cike da son ganin menene a ciki.
    Tana buɗewa tayi karo da wata atamfa koriya da yellow, ta kalli Mama ta kalli atamfar sannan ta ce “Wallahi Mama wannan Salamatu mai kayan ba ta kyauta mini ba, sai da nace ba na son atamfar nan, amma dan taga ba na nan shine ta liƙa miki, ki ka saya amma shikenan na gode, amma dai ba dan an ɗinka ba sai na mayar mata” ba ta gama rufe baki ba, ta buɗe kayan taga riga da zani jaka a tsaye, da wata uwar bunjumemiyar riga kamar zata tashi sama.

    “Ta kalli mama ta ce “Mama wai wannan kayan nawa ne ko kuma naki?” Ruma tayi maganar a rikice.

    Mama ta ce “Ni ce zan saka wannan kayan? Naki ne mana”

    “Innalillahi wa Innalillahi raji’un, yanzu mama wannan ne kayan salla na, dan Allah kalli rigar tsaf sai an saka irina sittin a ciki, mama ko gwada ni fa ba ayi ba aka ɗinka kayan”

    A fusace Mama ta ce “Naji na gode, ki ajiye mini kayana tunda ba ayi miki gwaninta”.

    Yasir ne ya dubi Ruma ya ce “Amma Ruma baki da kirki, yanzu mama ta sai miki kaya ta bayar a ɗinka miki, amma ƙiri-ƙiri ki nuna ba kya so”.

    Mama ta ce “Rabu da ita, ta je ta ƙarata”.

    “Mama kiyi haƙuri, ba cewa nayi bana so ba, amma dan Allah kalli rigar nan, ni ba tattabara ba ina zani da wannan rigar kalli hannun kamar fuka fukai, ba irin wannan rigar na gani a jikinku a wannan tsohon hoton naku ba?”
    Yasir ya karɓi rigar yana dubawa, ƙunshe dariyarsa yayi ya ce “To dan ubanki maje gaba aka yi miki, tun kina yarinyarki da ke, wato kin fi son matsatsun kaya ko, to baki isa ba, wannan rigar da ita zaki yi wankan idi mu je masallaci, maje gaba ce ”
    Haushi ne ya gama cika Ruma, ta tura baki tana jin kamar ta yi ihu.

    “Wace irin maje gaba, ai sai a bari nayi gaban tukuna, sai a ɗin ka mini daidai ni, idan ban je gaban ba fa?”

    Mama ta ce “Rabu da ita, ta gama rashin mutuncinta tun da abin nata haka ne, daga wannan ba zan ɗinka mata wasu ba, da su zata yi sallar, dama ba jin maganata take yi ba, nima an zo wurin da zan fanshe, bana ba kayan salla sai kala ɗaya”.

    Yasir ya ce “Wallahi mama hakan ma ta gode sosai Allah ya saka da alkhairi, ya ƙara buɗi, ai kin yi ƙoƙari, ke Ruma wannan rigar idan ki ka sakata ai ba sai kin ɗaura zanin ba, kaɗan ya rage ta zama doguwar riga, idan kuwa zaki ɗaura zanin sai ki ɗaura shi a kam rigar, ki yi ɗaurin barmana coge wallahi kyau zaki yi”
    Gaba daya ta fuskanci Yasir rashin mutunci kawai yake yi mata, kamar zata fashe haka ta tattare kayan ta kai ɗaki ta zubewa Mama a kan kujera, ta barwa ranta cewa gara tayi zamanta a gida da salla, da ta saka wannan zulumbuwar rigar a matsayin kayanta na salla ta fita ayi mata dariya.

    Mama ta fita yin barka a maƙwabta, hakan ya bawa Yasir damar zama ya sanya Ruma a gaba ya dinga tuntsira mata dariya, duk wanda ya shigo sai ya ɗauko masa kayan ya nuna masa, daga atamfar har ɗinkin irin na zamanin su Mama ne.
    Huzaifa ya fi kowa ƙyaƙyatawa, ya ce “Lallai mama ta iya punishment, ai ni ta biyani da aka miki wannan ɗinki, kamar yadda Yasir ya faɗa, idan ki ka saka kayan nan, ki ka kafa ɗauri irin na barmana mu samo ƙorrai, da sallar nan mu baza kiɗan ƙwarya a cikin unguwa, wallahi kuɗi zamu samu, dan dama mutane duk sun watsar da al’ada”.
    Abdallah har da yi mata magiya a kan ta gwada kayan yanzu, ya ga yadda za su yi mata. Tayi musu banza ta koma gefe ta ci magani.
    Yaya Usman ne ya zare mata ido, wai sai ta gwada kayan sun ga yadda za suyi mata, kasancewar tana shakkarsa shima, haka ta je ta saka kayan ta fito tana danne kukan da yake ƙoƙarin ƙwace mata.
    Tana fitowa tsakar gidan Huazaifa ya bushe da dariya ya ce “Waya ga babba da jaka”.

    Abdallah ya ce “Allah ya bar mana Delun mu, wallahi dama delun aka saka miki, kin yi kyau”.

    Usman Ya ce “Abdallah, yi mata ɗaurin barmana cogen, mu gani, zan mata video”
    Duk yadda ta so haɗiye kukan sai ta kasa, sun kewayeta sai dariya suke kamar sun ga mahaukaciya, ga Usman yana yi mata video da wayarsa suna dariya.
    Huzaifa sai kifawa yake, kamar wanda ya zare, yana cewa Usman”Ka yi mata hoton da Black and white mu ce ga kakar su Mama 1940″
    Babu tsammani Umar ya shigo, ya tarar da Rumaisa a tsaye kamar an dasa ta, ga uban ɗauri a ka, ta ɗaura zani a kan riga, tana tsaye tana kuka su kuma sun kewayeta suna dariya.

    “Meye haka?” Yayi maganar a kausashe.

    Usman ya ce “kayan sallarata ne, aka kawo take ta rashin mutunci wai bata son kayan, shine nake punishing ɗinta, nan gaba ta koyi godiya ga Allah a kan duk abin da ya bata, sannan ta godewa wanda ya batan”.
    Shi kansa Yaya Umar ji yayi kamar ya yi dariya, saboda yadda Ruman tayi a kayan, kai da gani ka san sun yi mata yawa, sai tayi kamar wadda ta kawo tallan kalwa birni.
    Gimtse dariyarsa yayi ya wuce ɗakinsu, suka gama yi mata rashin mutunci sannan suka sallameta.

    Da ta koma ɗakin ma, sai da ta sha uban kukanta, ta cire kayan ta ajiye tana jin yadda ranta yayi mugun ɓaci a kan abinda suka yi mata.

    Kasancewar yau ba tuwo mama tayi da daddare ba, ya sanya ruma zaman cin abincin dare ba tare da mita ko ƙunƙuni ba, ga kuma uwa uba a ƙule take da rashin mutuncin da su Yaya Abdallah suka yi mata. Tana ta lissafa yadda zata rama abin da suka yi matan ta huce.
    Duk da yadda yau tayi shiru, babu wanda ya kula da shirun nata, dama mama na jin haushin tayi mata abu ta kushe, mama ta mayar da hankalinta kan ‘yan mazanta suna ta hira.

    “Mama ina da tambaya” duk suka waiwayo suka kalleta.

    mama ta ce “To ina jinki, Allah ya sa na sani”

    “Wallahi na san ƙarshenta banzayen tambayoyinta ne marasa kan gado, dan Allah mama kar ki saurareta” Huzaifa yayi maganar yana kallon Ruma.

    Cikin tsiwa ta ce “Ban kasa da kai ba, dan haka babu ruwanka da ni”.

    Mama ta ce “Yi tambayarki ina jin ki”

    “Yauwa, dan Allah kar na tambayeki kuma kice mini sai an kwana biyu, menene Janaba, kuma meye fyaɗe!!!”

    Ayshercool
    08081012143

    Kar a manta ayi subscribing YouTube channel ɗina domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro
    https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

    [20/06, 6:52 pm] JAKADIYAR AREWA: ƘANWAR MAZA
    Na Aisha Adam (Ayshercool)

    MIKIYA WRITER’S ASSOCIATES

    https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

    Ku yi subscribing  YouTube channel ɗin
    @Cool Hausa Novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro.
    Ku yi following ɗina a arewabooks a kan account ɗina na ayshercool7724
    Ko watpad Ayshercool7724 kowanne a cikin manhajojin za ku iya samun litattaiafaina da na yi a baya, da wanda nake yi a yanzu na gode.

     

     

     

  • Noor Al Hayat 75

    Noor Al Hayat 75

    Washegari da safe karfe bakwai khadijah ta ji fitan Aliyu da mota, mikewa tayi ta fito tana mamakin inda xa shi da sassafe, ta bude kofar dakinsa ta ga Shureim kwance yana bacci, rufe kofar tayi ta koma dakinta, sai bayan da tayi wanka ta sa wata doguwar riga mara nauyi sannan ta sauka downstairs don tsaftace gidan, kafin karfe takwas da rabi ta gama komai, tana kokarin sa turaren wuta aka bude kofar parlorn, da sauri ta juya ganin sa ta dauke kai, ya karaso ya ajiye jakar hannunsa da Breakfast din su yana kallonta ta ki juyowa, bai ce mata komai ba ya wuce sama, sai a sannan ta mike ta isa gun jakar ta bude ta ga kayan shureim ne a ciki, ta rufe a hankali ta koma daki ta dau wayarta, ta fi two minutes tana kallon wayar kafin ta turo baki tayi dialing number Umma, Umma na dagawa tace “Fatan kun tashi lafiya Daughter” a hankali Khadijah tace “Umma shine baki kira ba koh?” Umma tayi murmushi tace “Toh ke ba gashi kin kira ba yanxu, ya grandson dina?” Khadijah tace “Yana lafiya” Umma tayi kasa da murya tace “Kiyi hakuri da abinda kika gani kin ji khadijah hakan kadai ne rufin asirin ki, and I am sorry for hiding that from you ban san yanda xaki dau hakan ba shi yasa…” Khadijah ta ji hawaye ya kawo idonta ta rasa abinda xata ce, Umma tace “Soon xa ki fahimce gata mu ka maki, nasan ki da taurin kai khadijah don Allah ki ajiye makaman yakin ki ki rungumi mijin ki ki manta komai, a role dina na matsayin mahaifiya a gare ki nake baki shawarar ki daina riko ba shi da amfani khadijah, wllh na tabbata son da Aliyu yake maki baxai misaltu ba da dadewa na gane haka, ke kam ba lallai ki gani ba tunda kin sa ma kanki k’in sa saboda kaddarar da ya faru tsakanin ku, Wai ma in tambaye ki… Tunda kike kin taba ganin wanda yayi ma mace fyade ya damu kamar yanda Aliyu ya damu? Ko akwai it’s very rare in today’s world khadijah, sure from the beginning Barrister Sudais ya xame maki wani Haske a rayuwar ki, ya haskaka maki rayuwar ki, abinda kuma baki sani ba shine, bar ma Aliyu auren ki da Barrister yayi duk cikin haskaka maki rayuwa ne coz Aliyu is the best husband for you duba da irin duniyar da muke ciki a yau, shi kadai xa ki aura ki samu kwanciyar hankali da nutsuwa ku xauna lafiya tare da d’an ku, shi yasa ya hakura ya bar masa ba don baya so ba, Kuma ya tabbata Aliyu xai daura daga inda ya tsaya, Barrister abun girmamawa da mutuntawa ne a gun ki khadijah, kinga Babu abinda bai maki ba don tabbatar da Haske a rayuwar ki, and Dr Ayman nasan shi ma har abada baxa ki mance shi ba don ya maki abinda mahaifin ki bai maki ba yana da rai, duk da nima na so kwatanta hakan amma babu dama, ban kuma san ta inda xan fara ba, don haka mutanen nan biyu babu da abinda xa ki iya biyansu sai dai kullum ki masu addu’ar gamawa da duniya lafiya, Allah ya ba ku xaman lafiya my daughter….” a sanyaye khadijah tace “Amin Ummata nagode” Umma tace “Maa sha Allah, my regards to both father and son” d’an murmushin karfin hali khadijah tayi daga haka ta katse wayar dai dai shigowar Aliyu dakin, kin kallon direction dinsa tayi, yana kallonta yace “We are going out anytime soon, ki shirya, and am hoping kin ga breakfast downstairs…” sai a sannan ta kallesa ta daure fuska tace “Xuwa ina?” Yace “Idan mun fita xa ki gani” daga haka ya juya ya fita, komawa tayi ta kwanta kan gado duk jikinta a sanyaye daga maganganun da Umma tayi mata, ta kusa minti talatin kwance Shureim ya shigo dakin da sallama, tana kallonsa har ya karaso kusa da gadon yana ta xuba kamshi, yana murmushi yace “Anty ina kwana” tace “How was ur night” yace “Alhmdllh” tace “wa ya maka wanka?” Yace “Uncle, Anty we are going out yace in kin shirya ki fito, muna jiran ki” ta hade rai tace “Kayi breakfast ne?” Yace “Eh mun yi da uncle” ta mike xaune tace “Toh ni ce baxan yi breakfast din ba xa ka wani ce kuna jirana” Tsayawa yyi yana kallonta, Aliyu ya bude kofar dakin, sanye yake da shadda milk color, lkci daya kamshinsa ya cika ko ina na dakin, yana kallonta yace “Iman, ke nake jira” Ta kallesa tace “Ku kunyi breakfast ni kuma sai in fita haka?” Ya daga kafada yace “Nobody stopped you from Breakfasting….” Tashi tayi tsaye ta nufi kofa kamar xata tashi ta bi gefensa ta fice dakin ya bi ta da kallon gefen ido kafin yayi murmushi, Shureim yace “Uncle da mun kawo mata nata daki koh?” Karasowa yayi yana murmushi ya xauna gefen gadon ya dafa kafadan yaron yace “Ko mun kawo mata cewa xata yi who sent us…” Shureim yayi dariya yace “Uncle but why is she even angry, ko bata son gidan nan ne, or she don’t want you to leave with us?” Murmushi kawai Aliyu yayi yana shafa sajensa a hankali yace “I don’t know also, amma ka tambayeta” ya xaro ido yana yar dariya yace “Xata doke ni ne” rungume sa Aliyu yyi a hankali yace “Not when am around darling” Suna ta xaune dakin har ta dawo, Bata yi xaton xata samesu a ciki ba, Bata rufe kofar ba tace “Can you both excuse me” Ya kalli Shureim yace “Tafi downstairs gani nan xuwa nima” fita yaron yyi a dakin, khadijah ta xaro ido tace “Cewa nayi both…” yana murmushi yace “Ni ba mijin ki bane xan yi excusing din ki?” ta daure fuska tace “Ni dai ka fita xan canxa kaya” Yace “But am not stopping you Iman” ya kalli agogon wrist dinsa yace “Kina ta bata mana lokaci kuma da nisa xa mu je” Tace “Toh ka fita, ko kuma in fasa xuwa” Yana kallonta kamar mai counting word din yace “I.. am.. going.. no where!” Wani kallo ta dinga masa, lkci daya ta nufi can karshen gado tayi kwanciyar ta ta juya masa baya, murmushi yayi ya hau saman gadon tana ganin haka tun kan ya matso kusa da ita xata tashi yyi saurin cafkota, Kamar xata yi kuka tace “Don Allah Aliyu ka bari, bana so, to nace ka fita in sa kaya ka ki fita, ya xanyi?” Sosai xuciyarta ke bugawa tana kallonsa, ya jawota jikinsa a hankali ya kai bakinsa wuyanta murya can kasa yace “Me yasa xan fita, what is it that u are hiding” turasa tayi da karfi tace “Stop it Aliyu..” Ya dago yana kallon idanuwanta yace “Really?” Jin yanda muryarsa ya canxa ta hadiye wani abu da kyar tace “Alryt, since you are not going na ji xa sa kayan haka, sake ni” a hankali ya saketa yana kallonta, sauka tayi daga kan gadon ganin inda ta nufa da gudunta ya mike da sauri ya riga ta isa kofar ya sa makulli yana kallonta, juyawa tayi kamar xata yi kuka tace “Me yasa kake min haka don Allah” ganin irin kallon da yake mata da lumsassun idonsa ta koma gun kayanta ta fiddo wanda xata sa kamar xata yi kuka, bathroom ta nufa ya bi ta, ta tsaya bakin kofar pleadingly tace “Don girman Allah ka bar ni in sa kaya Aliyu, Kai fa kace ina bata maku lokaci… ” bathroom din ya shiga ya jawota xata yi ihu ya sa makulli yace “Ki sa a nan tunda kina kunyar sa wa a cikin dakin” Bata fuska tayi tace “Ni wllh bana son abinda kake min…” Ya amshi kayan ya daura kan washing machine yace “Let me help you” Bai jira cewarta ba ya jawota lkci daya ya sauke doguwar rigar jikinta idonsa ya sauka kan tabon Cs dake cikinta, tayi kara a rikice ta durkushe wajen jikinta na rawa, dagota yayi yana kallonta a sanyaye ko kiftawa babu, ta dinga nonnokewa tana cewa “Don girman Allah ka bari Aliyu, wlh kunya nake ji” a hankali ya saketa yace “Toh sa kayan ki” jikinta na bari ta dau skirt din atamfar da sauri ta sa, sanann ta dau rigar ma ta saka, ya jawota jikinsa ya ja mata zip din rigar a hankali, ta kasa kallonsa, dago kanta yayi a hankali, ta rufe idonta da sauri, yayi murmushi yyi mata light French kiss, a rude ta bude idonta ya saketa ya bude kofar ya fita bathroom din, da kyar ta fito daga karshe duk jikinta ya mutu, Kasa shafa komai tayi a fuskarta ta sa turare da hijab kawai ta sakko downstairs, yana xaune parlorn Shureim na kwance jikinsa, ta ki yarda ta dago kanta har ta iso ta tsaya daga bayan kujera, kallonta kawai yake ganin ta kasa dagowa yayi murmushi yace “Ko d’an kwalliya baxa ki yi ba” Ta turo baki tace “Baxan yi ba” ya xaunar da Shureim yace “Toh mu je in fada maki me yasa xa ki yi” da sauri ta dago tana kallonsa tace “A’a ni bana so…” Yace “Toh je ji gyara fuskar ki” juyawa tayi da sauri ta koma sama tana waigen ko ya biyota, tana shiga daki ta sa makulli, eye pencil ta sa ta goga powder a fuskarta ta sa chappete, lokaci daya tayi wani sanyayyen kyau, ta maida hijab dinta ta sauko rike da flat shoe dinta, kallonta kawai Aliyu yake ko kiftawa babu har ta shigo parlorn, ya mike yana kallon Shureim yace “Tafi daki ka dauko min makullin mota” tashi yyi ya wuce sama, Aliyu ya mike ya nufo ta, tana ganin haka tace “Wayyo don Allah ka bari, Kar ka xo kusa da ni ka ga yanxu Shureim xai….” Toshe bakinta yyi ganin ihu xata masa, yana kallon eye balls dinta yace “You… Are beautiful Iman” Tayi saurin sauke idonta gabanta na faduwa, ya xame hannunsa bakinta, Bata ankara ba sai jin kiss tayi, duk sai da ya rabata da chappete din da tasa ta kasa kwakkwaran motsi wajen, ganin faduwa xata yi yayi saurin rikota tayi regaining balance dinta, dai dai lkcn da Shureim ya bude kofa, Saketa Aliyu yyi ya fita parlorn da sauri, Shureim ya sakko yana kallon mum din tasa da tayi stiff inda take yace “Anty what are you looking at” da sauri ta dawo ta fara kame kame, sai kuma tace “Toh ka kai masa makullin mana” waje ya tafi ta karaso cikin parlor da kyar ta xauna, Tana jin ya gama warming mota don ma kar ya biyota ta mike ta fito da sauri, har lkcn xuciyarta bugawa yake, Sosai ta ji dadin ganin Shureim xaune a gaba, ta bude back seat xata shiga Aliyu ya kalli Shureim yace “Kai koma baya sweetheart sai Anty ta xauna gaba” hade rai khadijah tayi tana kallonsa, Shureim ya fito ya dawo baya, Tana masa wani kallo tace “Nima a bayan xan xauna” juyowa Aliyu yyi ya kafeta da idanuwansa, sauke nata tayi da sauri, ta rufe motar ta xaga ta shiga gaba kamar xata yi kuka, har suka fita gidan bata yarda ta kallesa ba, sai bayan da suka hau titi yace “Zaria xa mu je” ba tare da ta kallesa ba tace “To do what?” Yace “Xa mu je gaida Anty khadijah, daga can sai mu biya family house din su iklima tana can” Lkci daya jikin khadijah yayi sanyi sosai, a hankali Aliyu yace “But idan baxa ki shiga ba sai ki tsaya a mota mu shiga ciki da Shureim” Ta girgixa kai tace “A’a xan shiga” almost half of the journey surutun Shureim kadai ne ke tashi a motar, daga karshe khadijah da abun ya isheta ta juya tana masa mugun kallo tace “You keep ur mouth shut…. ka dame ni” Aliyu ya bude ido sosai yace “Ni fa yake ba labari ba ke ba malama” Hararansa tayi tace “Ehh nace ya ishi kunne na, ya dakatar da labarinsa haka” Murmushi Aliyu yayi a hankali yace “Toh Anty…” Ganin sun kusa Zaria a hankali Khadijah tace “Toh baxa mu kai mata komai ba?” Aliyu ya d’an kalleta ya mayar da hankalinsa kan titi sannan yace “Like what?” Tace “Kamar fruits da dai abubuwan da marasa lafiya suke so” Murmushi yayi, bayan sun shiga Zaria yayi parking gun wasu masu siyar da kayan marmari, ya siya mai yawa, ya sa bayan mota ya dawo side din khadijah yace “I think fruits din ma sun isa” Khadijah tace “Toh iklima fah?” Yace “We will get her something idan mun fito” Bata ce komai ba ya xaga ya shiga maxaunin driver ya tada motar ya ci gaba da driving. karfe sha daya saura suka isa asbitin da Anty khadijah take a Zaria, Aliyu na gama parking gaban khadijah ya dinga faduwa, ga mugun fargabar da ya ziyarce ta, Aliyu na lura da ita bayan sun fito ya dawo gefenta a hankali yace “You need not to be afraid of anything Iman, relax ur mind, or you stay behind, baxa mu dade ba xamu fito” Ta girgixa kai tace “A’a xan shiga” daga haka ta bude bayan motar ta fiddo fruits din shi kuma yana rike da hannun Shureim suka shiga babban asibitin, har ward din da Anty khadijah take suka tafi, Aliyu ya bude kofar a hankali hade da sallama, shi ya fara shiga tare da Shureim sanann khadijah dake makale a bayansa, ta dade bata yi fargaba irin na lokacin ba, Baby ce xaune ward din tana xuba mata abinci, daga one side kuma Barrister Sudais ne yana xaune saman kujera rike da makullin mota, da alamar dai lokacin suka xo su ma, Aliyu ya dinga kallon Anty khadijah dake kan gado….

    ✨ *NOOR-AL-HAYAT*✨

  • Noor Al Hayat 77

    Noor Al Hayat 77

    Ya kwantar da murya a hankali yace “Haba my Ummu Shureim…” turo baki tayi ta dauke kai tana goge idonta, ya juya yana kallon shureim, murmushi yayi yace “Toh kaga tayi shiru kai ma kayi shiru” Kai ya gyada masa yana kallon mum dinsa, ya dawo kusa da ita a hankali yace “Anty kiyi hakuri” kallonsa tayi, tayi d’an murmushi tace “Toh na yi” komawa yayi ya xauna, Aliyu ya tada motar ya ci gaba da driving, murya can kasa yace “Mu bari next time sai mu je duba iklima, coz i really don’t have the energy to start consoling you again” tace “Ni ka kai ni yanxu, ba wani next time, I will be going back to schl soon” murmushi yayi yace “Ohk then” hanyar family house din su iklima Aliyu ya dauka, bayan minti kusan sha biyar suka isa babban gidan, yayi parking a waje suka shiga, yan gidan basu wani tarbe su ba, hakan bai wani dame Aliyu ba, ita dai khadijah jikinta yayi sanyi, autar su mahaifin Iklima ta nuna masu wani kofa tace “Tana can” Aliyu ya mike yana kallon khadijah ita ma ta mike, Shureim xai tashi ya duka ya dafa shoulder dinsa a hankali yace “You wait for us here sweetheart ka ji?” Kai Shureim ya gyada masa ya koma ya xauna, Aliyu ya nufi kofar dakin khadijah ta bi bayansa gabanta na faduwa, ita kadai ce kwance dakin mai dauke da yar katifa ko leda babu, katifar ma babu xanin gado, da ganin dakin babu me shiga ciki, Ga cup da plate da spoon dinta nan gefen gadon, da kadan iklima ta fi skeleton kwance a kan gadon, khadijah ta kasa karasawa cikin dakin tana iya kokarin ganin bata fashe da kuka ba ta toshe bakinta, Aliyu ya karasa ciki yana kallonta shi ma a sanyaye, Durkusawa yayi kusa da ita a hankali yace “Sannu iklima” maimakon ta amsa masa sai hawaye, duk jikinsa yayi sanyi ya kasa cewa komai lkci daya shi ma idonsa ya kada, khadijah ta fashe da kuka sosai ta juya ta fice daga dakin, Da kyar Iklima ta iya bude baki tace “Kace ta yafe min don Allah” Ya sauke idanuwansa kasa a hankali yace “Kina shan magani iklima?” Girgixa masa kai tayi hawaye na xuba idonta, ya fi minti biyu durkushe gabanta bai iya yace komai ba, can ya dago da kyar yace “Wa ke kula da ke?” Nan ma ta girgixa masa kai, cikin sanyi yace “Yaushe rabon ku je asibiti?” Kallonsa kawai take alamar maganar ma baxata iya ba, mikewa yayi a hankali ya fita dakin, ya kalli khadijah da ta hade kai da kujera tana kuka Shureim na kusa da ita shi ma yana kukan yana kallonta, Babu wanda yace masu komai, kowa na harkan gabansa a babban gidan, gun yayar mahaifin iklima da ya sani ya nufa a waje, tana xaune su kusan uku suna hira, ya d’an duka ya gaishe ta, ta amsa tana tambayarsa yaushe ya xo, yace “Ba mu jima ba, mama nace iklima na xuwa asibiti kuwa?” Matar tace “An kwan biyu ba aje ba tunda uban nata bai turo kudi ba kilan ya gaji shi ma, mu kuma ya bar mu da wahala” Shiru Aliyu yayi yana kallonta, can ya mike yace “Toh bari mu je yanxu” tace “Kar ma ka bata lokacin ka ko tashi bata iya yi, idan ba likitan xaka je ka gayyato a asibiti ba” Bai ce komai ba ya koma parlorn sannan ya shiga dakin da iklima take, Kallonta kawai yake yana kokarin gano stage din da cutar nata yake, bayan wani lokaci ya juya ya fita, gun khadijah ya nufa yace “Tashi mu je” Ta mike da kyar har lokacin kuka kawai take, Aliyu ya dau shureim ya rungumesa suka fita, bank ya fara tsayawa, ya kalli khadijah kafin ya bude motar ya fita xuwa gun automated teller machine, ba a dau lkci ba ya dawo ya shiga motar, wani babban pharmacy dake area din ya tafi, yana kallon khadijah da taki daina kuka yayi kasa da murya yace “Am begging you ki daina kukan nan Iman, baki kyauta ma yaron nan, even for his sake kiyi hakuri ki daina kukan” Juyawa tayi tana kallon Shureim da ke kuka bakin rai shi ma, hadiye kukanta tayi xuciyarta na mata xafi, Aliyu ya bude motar ya fita, bayan kusan minti goma ya dawo rike da ledan magani masu yawa da tsada, murmushi yayi ganin yanda Shureim yayi shiru yana kallon khadijah dake ta kukan xuci, Bata taba tunanin ganin Iklima a yanda ta ganta ba, ta ji duniyar ba bakin komai yake ba, wani store Aliyu yayi parking ya fita ya siya cartons of malts da Madara masu yawa, sai locozade boost, a booth aka xuba abubuwan da ya siya, ya shiga motar ya kalli khadijah da ta jinginar da kanta jikin kujera ta fada duniyar tunani, kamo hannunta yayi ta juya a hankali tana kallonsa, murmushi ya sakar mata yace “Kowa da irin kaddararsa, su irin tasu kenan, so you just have to pray for them, Allah ya sa mu cika da imani” wasu sabbin hawayen suka sakko idonta, ya tada motar suka bar wajen, shi kadai ya shiga dakin iklima ya ajiye magungunan gefenta yaran gidan suka dinga shigowa da abubuwan da ya siyo, Yana kallon iklima ya fiddo magungunan gaba daya ya shiga nuna mata yanda xata sha, kallonsa kawai take bata ce komai ba, bayan ya nuna mata yace “Idan kin ji kina jin yunwa sai ki daure ki tashi ki sha malt ko madara, idan lokacin shan maganin ki yayi ba a baki abinci ba sai ki sha malt ki sha drugs din kin ji?” a hankali ta gyada masa kai, ya fiddo dubu talatin a aljihunsa ya daga gefen katifar ya ajiye mata yace “Ki dinga aika yaran gidan su siyo maki fruits sai ki basu ko dari biyu don su dinga xuwa kin ji?” Nan ma ta gyada masa kai, ya d’an yi murmushi yace “Allah ya sauwake lil sis, idan kina son ki samu lafiya sai kin yi ta shan drugs din ki” Nan ma dai ta gyada masa kai, yace “Xan dinga xuwa duba ki always, idan kika fara samun sauki xan kai ki gun Mumy dama Abbanki ne yace a kawo ki nan” kallonsa kawai take, jikinsa yayi sanyi ganin hawayen dake sauka idonta, da kyar yace “I will be back soon” daga haka ya mike ya fita dakin ta bi sa da ido, Har suka shigo kaduna, Daga khadijah har Aliyu duk jikinsu a sanyaye yake, tuni Shureim yayi bacci bayan motar, Aliyu na gama parking ya juya yana kallon khadijah da ta bude motar ta fita, fitowa yayi shi ma ya bude back seat ya fiddo Shureim, ya rufe motar ya bi bayanta, bedroom dinsa ya shigar da Shureim ya kwantar da shi, ya fita ya shiga dakin khadijah, kwance ya sameta tayi lamo jikin pillow, ya xauna gefenta yana kallonta, ita dai bata yarda ta kallesa ba, kamo fingers dinta yayi yace “You need not to worry this much Iman, kin san condition din ki fa” Bata san lkcn da ta fashe da kuka ba ya dagota ya rungume ta, ta kwantar da kanta kirjinsa tana shesshekar kuka, murya can kasa yace “Kiyi addu’ar Allah ya basu lafiya Iman” Sun fi minti biyar a haka, Ya dago kanta a hankali yana kallonta, rufe idonta tayi, yyi murmushi yana kallon cute lips dinta, kamar tasan me yake yi ta kwace kanta ta mike ta koma can karshen gado ta kwanta, shafa kansa yyi yace “Ki tashi kiyi sllh” daga haka ya mike ya nufi kofa ta bi sa da ido har ya fita, throughout ranan haka khadijah ta kasa samun natsuwa, Aliyu yayi lallashin har ya gaji, duk ta 6ata mood din little Shureim ma, Bayan magrib ya dawo masallaci ya shiga bedroom dinsa dai dai lkcn da wayarsa ya katse, karasawa yayi ya dauka yaga Mumy ce ta kirasa, ya xauna gefen gado ya shiga kiranta, tana dagawa yayi mata sallama, jin yanayin muryarta a hankali yace “Mumy baki da lafiya ne?” Mikewa yayi yace “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” lkci daya ya ajiye wayar ya koma ya xauna ya rike kansa, bai san lkcn da hawaye ya dinga xuba idonsa ba, ya fi minti biyar a haka kafin ya mike da kyar ya share idonsa ya dau makullin motarsa ya fita daki, yana ta tsaye corridor kafin ya bude dakin khadijah xaune ya ganta kan darduma ta jinginar da kanta da gado, Shureim na xaune kusa da ita, kasa karasawa cikin dakin yayi yana daga bakin kofar yace “Iman xa mu je can gida yanxu” ta kallesa kafin tace komai har ya juya ya wuce, a tunaninta gaida Mumyn xa su je su yi, ta mike ta linke pray mat din ta ajiye, ta kama hannun Shureim suka fita bayan ta kashe wutan dakin, ganin yanayin Aliyu ta kallesa da damuwa tace “Ko dai wani abu ya faru ne?” Yana driving idonsa kan titi yace “Nothing” har suka isa gida bata sake cewa komai ba, yayi parking ya fito ita ma ta fito tana rike da shureim suka bi bayansa, sosai gabanta ya fadi ganin mutane a parlorn, Aliyu ya isa gun Mumy ya durkusa gabanta, khadijah ta kasa karasawa xuciyarta na bugawa, upstairs ta wuce xuwa dakin baby da sauri, baby na ganinta ta fashe da kuka sosai, cike da karfin hali khadijah ta durkusa gabanta tace “Me ya faru baby” Baby tace “Iklima…” Hawaye ya shiga sakko ma khadijah ta hade kanta da gado tana salati a ranta. Daren ranan a gidan suka kwana gaba daya, mutuwar Iklima ya girgixa kowa barin khadijah da Baby, da ta tuna yanayin da suka sameta daxu da rana sai taji hawaye ya ki tsaya mata ashe mutuwa xata yi, gashi ko magana bata samu ta mata ba saboda tashin hankali, babu wanda ya wani rintsa a gidan har asuba. Washegari da safe Umma suka xo gidan da Nanny don yi ma Mumy gaisuwa, da Umma ta tashi tafiya Shureim yace xai bi ta, haka Umma ta wuce da shi don har da kukan sa, sai bayan da aka yi sadakan uku Khadijah da Aliyu suka koma gida da daddare, har sannan shock din bai bar ta ba, har ranta taji ta yafe ma Iklima don ita a iya tunanin ta ma bata mata komai, ajiye abincin da Mumy ta basu su tafi da shi tayi a nan tsakiyar parlor ta wuce sama Aliyu da ya bi ta da kallo yace “Iman” juyowa tayi tana kallonsa, yace “Baxa ki ci abincin ba” ta girgixa masa kai, yace “Ba fa ki ci komai tun daxu ba” Bata ce komai ba ta haura sama, kitchen ya shiga ya dau plate ya wanke sannan ya dawo parlorn ya bude abincin ya dibar mata ya rufe sauran ya wuce sama, kayanta ya sameta tana cirewa, tana ganinsa ta durkushe kasa da sauri kamar xata yi kuka tace “Baka iya sallama ba ne” d’an murmushi yayi ya sauke idonsa daga kallonta yace “Yi hakuri” ta turo baki tace “Ka ajiye ka tafi” Ajiye mata abincin yayi ba tare da ya kalleta ba ya juya ya fita, zani ta dauka ta daura ta xauna kusa da shinkafa da miyar da ya ajiye mata ta dau spoon din ta fara ci a hankali, Bata wani ci da yawa ba don har sannan bata da appetite ta mike ta shiga bathroom, sai da ta wanke bakinta sannan tayi wanka ta fito, Hijab ta sa ta dau sauran abincin da ta rage ta fita da shi ta dawo dakin, ta dau lkci xaune gaban madubi tana shafe shafenta ya bude kofar, xaro ido tayi ta duka, ya koma da sauri yace “Ohh sorry, Assalamu alaikum…” Tayi saurin daukan hijab dinta ta sa ganin har ya sake shigowa ta hade rai tace “Bana son haka Aliyu, ba sai an amsa ake shigowa ba” dariya ta basa sai dai bai yi ba, ya mika mata wayar hannunsa yana kallonta yace “Gashi Dr Ayman xai maki gaisuwa” ta hararesa ta karba wayar tace “Toh ni ka fita” juyawa yayi ya fita dakin, ta kai wayar kunne, muryar Khaleel taji yace “Uhm lallai, ya fita koh?” Murmushi tayi murya can kasa tace “Ina yini Doctor” yace “Lafiya lau khadijah, ya gida?” Tace “Alhmdllh, ya jawahir” yace “She’s fyn, ya karin hakuri?” A sanyaye tace “Mun gode Allah” yace “Allah ya mata rahama” tace “Ameen mun gode” yace “Maa sha Allah, good nyt” tace “Alryt, my regards to jawahir” yace “In sha Allah” daga haka ya katse wayar, ta ajiye gaban madubin ta mike ta cire hijab dinta ta dau kayan baccin da ta fiddo ta saka, ta linke Hijab dinta ta ajiye sannan ta kashe wutan dakin ta kwanta, har bacci ya fara daukanta taji an bude kofar dakin ta bude ido da sauri, tana ji ya rufe kofar, Bai kunna wutan ba yana tsaye daga inda yake a hankali yace “Iman, wayana fa?” Shiru tayi bata ce komai ba, ya fi minti daya tsaye kafin ya juya ya fita a hankali ya rufo mata kofar, sai a sannan ta mike xaune, tana ta xaune kan gadon kafin ta sauko ta tafi gun mirror ta dau wayarsa ta saka hijab ta fita, a hankali ta bude kofar dakinsa ta shiga.