Hausa NovelsKanwar Maza Hausa Novel

Kanwar Maza 2

Sponsored Links

P2
Kasa ɗauke idanunta tayi daga kallonsa, saboda azabar firgici da razanar da ta yi.
Ya janyo kujera ya zauna a gabanta, ya ɗan ƙura mata ido, sannan cikin kaushin murya ya ce “Gidan uban wa kika tafi da ta aikeki, tun la’asar ba ki dawo ba sai magariba?” Yayi Maganar yana tsareta da ido.
Kasancewar akwai wutar lantarki, ya sanya fes take kallon fuskarsa da idonsa.

“Ba magana nake yi miki ba, ki ka tsare ni da ido?” Ya daka mata tsawa.

Zabura tayi ta yinƙura za ta yi magana,amma ya sake cewa “Kuma wallahi kika yi mini ƙarya sai na ci ubanki a daren nan”

Jiki na rawa ta fara zayyane masa yadda aka yi tun bayan fitarta.

Huzaifa tun da  yaga Yaya Umar ya shiga ɗakin Mama ya jiyo kukan Rumaisa, ya sha jinin jikinsa, dan ya san yau sai yadda Allah ya yi.
Mama kuwa girgiza kai kawai ta yi, jin Yadda Ruma take faɗar gaskiya saɓanin ɗazu da ta yi mata ƙarya.

Umar ya ce “Namiji ce ke da zaki tafi aron taya?” Ta sunkuyar da kai tayi shiru.

“Kuma me nace miki a kan dambe a hanya, karya ce ke?”

Ta girgiza masa kai alamar a’a.

Ya ɗora da cewa “Wato ke duk wani abu da za’a gaya miki sai dai ya shiga ta kunnenki na dama, ya fita ta hagu ko?”

Ita dai tayi shiru tana rarraba ido.

“Kyaci ubanki, tashi ki kama kunnenki tun da ba zaki yi hankali ba”.

Maraicewa tayi zata fara yi masa magiya, amma da yayi mata wani mugun kallo, ba shiri ta miƙe ta durƙusa ta hau kamun kunne.

Gaba ɗaya Huzaifa ji yayi bai ji daɗi ba, maimakon a hukuntata tun a lokacin amma sai da aka bari ta fara bacci, za a sakata kamun kunne, ya tsaya ta ƙofa yana leƙen tsakar gidan ya san yanzu zata galabaita, gashi babu wanda ya isa ya hana Yaya Umar abin da yayi niyya sai Hassan ɗin sa wato Abubakar Sadik, shi kuma baya nan.

Umar ya nutsu yana duba litattafansa, Rumaisa kuwa sai tangaɗi take tana neman ta faɗi, amma yayi banza da ita, dan ta san idan ta faɗi ko ta tashi ba zata iya ɗaukar wani hukuncin ba.
Tun tana kuka ƙasa-ƙasa har ta fara yi da ƙarfi, saboda azabar gajiyar da ta yi.
“Tashi” ya faɗa ba tare da ya kalleta ba. Ta ɗago duk ta haɗa uban gumi, ga hawaye da majina duk a fuskarta.

“Kukan uban me kike yi?”

Cikin kuka ta ce ‘Yaya na gaji ne, dan Allah kayi haƙuri ba zan sake ba, na tuba”

“Da alama haryanzu baki yi laushi ba, yi zaman babur tun da kin gaji da kamun kunne”

Babu kalar izayar da Yaya Umar bai yi mata ba a daren, har Sai da Mama ta ji babu daɗi a ranta, amma tuna cewar yarinyar ba ‘yar goyo bace ba, ya sanya tayi banza ta cigaba da laziminta.

Aliyu ne ya fito daga ɗakinsu, cikin damuwa ya ce “Dan Allah Yaya kayi haƙuri ka ƙyaleta haka ta je ta kwanta dare yayi, wallahi ta horu, kuma ga gobe in Allah ya kaimu da makaranta”.

A fusace Umar ya kalleshi ya ce “Ka ɓace mini daga gabana ko sai na haɗa da kai?” Ran Aliyu ba ƙaramin ɓaci yayi ba, kawai ya girgiza kai ya shiga banɗaki.

Sai da ya tabbatar da ta galabaita sannan ya ce ta zauna ta huta, shi kuma ya tashi ya fita.

Ta dinga kuka kamar ranta zai fita, saboda jin cinyoyinta take kamar babu nama a cikinsu sai rodi, saboda azabar sagewa da suka yi, ƙashin bayanta ma ban da azabar ciwo babu abin da yake yi mata.

Yaya Umar na fita, Huzaifa ya ƙaraso in da take yana mata sannu cikin tausayawa kamar ba shi ne ya gama bawa Mama shawarar ta haɗata da Yaya Umar ba.

Ya je ya ɗebo ruwa ya bata, ta karɓa ta kafa kai tana sha tana kuka. Ta gama sha, ya karɓi kofin ya ajiye yana goge mata hawayen fuskarta.

“Uban me kake a nan wurin?” Basu ji dawowar Yaya Umar ba, sai maganarsa kawai suka ji, suka yi tsuru-tsuru.

“Zaka tashi ko sai na haɗa da kai?” Jiki na rawa Huzaifa ya tashi, ya koma ɗakinsu.

Ya kalli Ruma da ke ta ajiyar zuciya, ya tabbatar ta galabaita, ya san yanzu haka jikinta na ciwo, ya jefa mata leda a jikinta ya ce “Maza ɗauki ki shanye”

Jiki na rawa ta ɗau ledar, doguwar jarka ce cike da youghurt mai sanyi a ciki, ta ɗaga kai ta sha rabi, yana tsaye yana kallonta, ba tare da ta kalleshi ba ta ce “Na ƙoshi”.

Jin bai ce komai ba ne ya sanya ta ɗago ta kalleshi, ganin yana mata wani irin kallo ne, ya sanya ta cigaba da sha tana yamutsa fuska, da ƙyar ta shanye, ta ajiye robar tana jiran umarni na gaba.

“wuce ki je ki kwanta”

Da ƙyar da yinƙura ta tashi, ƙafafuwanta na ta rawa saboda ciwo, ta shiga ɗaki.
Tana shiga ta tarar da Mama na salla, ta faɗa kan katifa tana kuka.
Mama har ta idar da sallar ba tace mata komai ba, ta cigaba da kukanta har bacci ya ɗauke ta.

Cikin bacci ta ji Mama na ɗala mata duka a cinyarta “Tashi” duk da yadda ta ji zafin dukan, amma ta buɗe idonta a hankali ta kalli Mama, ba tare da ta ce komai ba.

“Saboda tsabar rashin hankali, ki kwanta ki yi fitsari a kwance, ke ba jaririya ba ba ‘yar yaye ba” jin abin da Mama ta faɗa ne ya sanya ta miƙe zumbur, ta ganta luntsum a cikin fitsari.

Waro ido ta yi ta ce “Na shiga uku, wallahi na zata a mafarki ne, dan Allah kiyi haƙuri”

Mama cikin ɓacin rai ta girgiza kai ta ce “Innalillahi wa innalillahi raji’un, zaki tashi ki fita kije ki gyara jikinki ko kuwa?”

Sannu a hankali ta sauka daga kan katifar, saboda yadda jikinta ko ina yake yi mata ciwo, saboda punishment ɗin da Yaya Umar ya sanya ta.
Da ta fita tsakar gida da rarrafe ta ƙarasa banɗaki, ta wanke jikinta ta dawo ta canza kaya, ta jingine katifar tayi kwanciyarta a ƙasa.

Har ga Allah, tana jin yadda fitsarin ya matseta, amma ta ji gandar tashi, saboda bacci take ji sosai, ga kuma ciwo da jikinta yake yi, dan haka ta cigaba da baccinta, da ta ganta a banɗaki ta zaci a gaskene ta saki fitsarinta.
Tana jin yadda Mama ke ta mita, amma ita ko a jikinta, wani nannauyan baccin ne ma yayi awon gaba da ita.

Da Asuba ma an kai ruwa rana kan Mama ta samu Rumaisa ta tashi ta yi salla, dan sai da ta yi iƙirarin haɗata da Yaya Umar sannan ta tashi ta yi sallar.
Ta idar da salla Mama tayi mata maganar shirin makaranta, amma ta tura baki ta ce “Ai kina gani jiya mai sunan Baba yana azabtar da ni baki hana shi, ni bani da lafiya, ba zani ba cinyata kamar an mini ɗorin karaya haka nake ji na”

Mama ta yi mata shiru ta cigaba da laziminta, Huzaifa ne ya fara shigowa ɗakin Mama ya gaisheta, suka gaisa ya tambayi Mama mai za’a ɗora na karin kumallo?.

Mama ta ce “Bari gari yayi haske, sai a sayo gasara, ka cewa Yasir ya feraye maka dankali, sai a soya”

Huzaifa ya jinjina kai ya miƙe, har zai fita idonsa ya sauka a kan katifar Rumaisa, ya ɗan yi turus ya dubi Mama ya ce “Mama ba dai fitsarin kwance yarinyar nan tayi ba?”

“Gashi kuwa kana gani, ai Yarinyar nan sai addu’a kawai”.

“Innalillahi wa innalillahi raji’un, su Balama an yi asarar kunnuwa, ba sai ki saka ta fitar miki da ita daga ɗaki ba, sai ɗakin ya fara wari tukuna, abinka da fitsarin gardiya bana jariri ba, tashi shashasha” ya ƙarasa maganar yana zuba wa Rumaisa duka a ƙafa.
A gigice ta tashi zaune ta raba ido, tayi zaton Mama ce ta daketa, amma taga Huzaifa a kanta.

“Me nayi maka zaka dakeni?” Tayi maganar a ƙule.

“An dake ki ɗin, tashi ki fitar mata da wannan katifar daga ɗaki, mai abin kunya ƙatuwa da ke kina fitsarin kwance”

“Ba zan fita da ita ɗin ba, uban shishshigi ko ina ruwanka, tun da ba a kan ka nayi ba, kuma ruwa ne ya zube ba fitsari nayi ba”.

“Au Mama ƙarya take yi miki kenan, ba zaki tashi ba?”

Cikin tsiwa ta ce “Ba zan tashi ba”

miƙa hannu yayi, ya janyota ya ɗagata, ya ce “Wallahi sai kin fita da katifar nan kin wanke kayan da kika yi tsiyar a kan su”. Idan da sabo Mama ta saba da wannan halin nasu na faɗace-faɗace, gashi Huzaifa ya bawa Rumaisa kusan shekaru shida, amma faɗa kamar suna ganin hanjin junansu.

Mama ta sharesu ta ƙi ko kallon in da suke, Rumaisa ta dinga turjewa tana kwarara ihu.
Basu yi aune ba suka ga Yaya Umar a tsakiyar ɗakin, take suka yi cirko-cirko suna kallonsa.

Cikin kaushin murya ya ce “Meye haka karnuka ne ku?”

Suka girgiza kai a tare.

“Me kai mata take wannan ihun, da idon Mama bai sanya kun daina ba?”.

“Fitsari ta yi a kwance, shi ne nace ta fita da kayan”

Cikin mamaki Umar ya kalleta ya ce “Fitsarin kwance kuma? Kina me kika yi fitsari?”

Cikin rauni ta ce “Wallahi Yaya tsautsayi ne, kasa tashi nayi”

“Tsautsayin uban wa? Kwashe kayan ki fita ki wanke ƙazamar banza kawai”.

Haka ta ja katifar ta fita da ita tsakar gida, ta kwaso kayan da ta yi wa fitsari ta hau wanki.

Huzaifa ya faki idon Yaya Umar ya dinga yi mata dariya.
Duk wanda ya fito tsakar gida ya ga katifar Rumaisa sai ya ce me ya fito da katifar, Huzaifa sai yayi farat ya gaya musu ai fitsarin kwance ta yi.

Tausayinta ne ya kama Usman, ganin yadda take kuka, kuma ba ta saba yin fitsarin kwance ba, ya je ya karɓi kayan ya tayata.
Kowa da abin da yake faɗa a kan Ruma, wasu na mata Addu’a shiriya wasu kuma na yi mata faɗa har da zagi.
Tamkar gidan ‘yan mata, haka zaratan samarin nan suka kama aikin gida, wasu na wanke-wanke, wasu shara da Abin karyawa, kan gari ya ƙarasa haske, hatta ruwan da Rumaisa zata yi wanka, an dafa ta haɗa ta yi wanka.

Haka suka jeru a tsakar gida, tare da Mama suna karyawa, Rumaisa kuwa sai shan kunun take da ƙyar tana yamutsa fuska.
Can ta kalli Mama ta ce “Mama Kununa bai ji suga ba, yayi tsami da yawa”.

Haushi ya kama Mama ta ce “Amma a gabanki aka zazzage sugan kowa ya ɗiba ko? Kuma kin san ya ƙare”

Ta ture kofin kunun ta ce “Nifa dama kunun nan gudawa yake sani, gashi bai ji suga ba, ni cikina ma har ya fara ciwo”

Umar kawai ya girgiza kai, Rumaisa ba zata taɓa zaman mintuna goma lafiya ba, ba tare da tayi abin da za a yi mata magana ba.
Haidar ya kalleta, ya zura hannu a Aljihunsa ya ɗauko ɗari biyu ya bata ya ce “Jeki wurin Mamuda ya baki buredi da suga, akwai ruwan zafi sai ki haɗa shayi ki sha”

Washe baki tayi, ta ce “Allah dai ya biya da aljanna, gadanga na Mama” ta ɗau kofin kununta ta turawa Mama kunun ta ce “Mama ki shanye kunun na bar miki” tayi waje.

***
Da ƙyar ta ƙarasa makaranta yau, saboda ciwon cinyoyi da take yi, sakamakon horon da Yaya Umar ya bata a daren jiya.

“Ruma hatsari kika yi ne?” Cewar wata matashiyar yarinya sa’ar Ruman, gannin yadda take tafiya da ƙyar.

Ta haɗe rai ta ce “Me kika gani?”

“Gani nayi kina tafiya da ƙyar, kamar wadda ta warke daga karaya”

Cikin gatse Ruma ta ce “Eh, tirela ce tabi ta kaina, da ta wuce na taso na taho”

“A’a Allah ya baki haƙuri”

Duk da yadda jikinta babu daɗi, hakan bai hanata faɗace-faɗace da neman rigima ba, dan idan ba tayi hakan ba ace lafiyarta ƙalau ba.

Bayan an tashi ba ta tsaya ko ina ba ta tafi gida, tana zuwa ta tarar da katifarta a tsakar gida kamar yadda ta barta.

“Mama yanzu dan Allah a nan aka bar mini katifata, sai anyi baƙi sun tambayi ba’asi ace fitsarin kwance nayi?”

“Au ba ke kika yi ba, ni nayi kenan?”

Ta ƙarasa ta zauna a kusa da Mama ta ce “Haba Mama, kema fa kin san tsautsayi ne, rabona da fitsarin kwance tun ina jairiya, tun ban fi wata huɗu ba na daina fitsarin kwance” wani irin kallo Mama tayi mata, jin uwar ƙaryar da ta saki.

Mama ta ce “Tashi ki cire Uniform, kiyi wanka ki zo kiyi salla, ki tsefe wannan kan naki, ƙazamar banza da yake ban yi magana ba, baki ga dama kin mayar da kai kin tsefe ba, kuma wallahi ya kai gobe in Allah ya kaimu baki gama tsifar nan ba, sai na zaneki”.
Hannu ta saka ta shafa kanta, ƙanann kitso ne a kanta, a ƙalla guda arba’in da ɗoriya, Mama ta bata kuɗi ta je ayi mata kitson hannu guda biyar, saboda ba ta son tsifa, amma ta karɓi kuɗi a wurin Yaya Usman ta je aka yi mata ƙanana.
Ta san yau ko Mama zata kwaɗanta ta ta cinye ba zata iya gama wannan tsifar ba, haka nan ta tashi ta je ta yi wanka, ta yi alwala ta saka wasu kayan. Ganin Mama ta tada salla, ta leƙa Window ta ga Usman da sallaya a hannu zai tafi masallacin juma’a, ta ɗau hijjabinta ta bi bayansa.
Sai da ta fito ƙofar gida sannan ya kalleta ya ce “Ina zaki?”

“Masallaci mana” ta bashi amsa.

“Kin tambayi Mama?”

Ta gyaɗa masa kai alamar eh.

Ya ce “Shikenan muje” ya sanyata a gaba suka tafi masallaci.

Mama ta daɗe tana yiwa Rumaisa Addu’a bayan ta idar da salla, kullum cikin Addu’a take yi mata, amma tana girma tamkar ana sake turata, ko alamar hankali babu a tare da Rumaisa.

Da suka dawo daga masallaci tana kallon Rumaisa, ba ta ce mata uffan ba, Rumaisa sai raragefe take yi, tana sauraron ko Mama zata yi mata magana amma taga ta shareta.

Ba tare da ta yi tsifar ba, ta ci Abincin ranarta tare da Yaya Aliyu, ya siyo kifi ɗauri biyu, ya bawa Mama ɗaya ya ce gashi nan duka gidan, ɗauri ɗaya kuma suka ci shi da Rumaisa.

Bayan sallar la’asar, ta ɗau allonta ta tafi makarantar allo.
Tana zuwa Habiba ta tare ta da harara, tare da sheda mata cewar Sani ya ce sai ya yi mata dukan tsiya, idan ba ta biya shi tayarsa ba.
Tsaki Rumaisa tayi ta ce “To, ya kasheni ya huta mana, tayar banza da ta wofi, shi bai san tsautsayi ba”

A ƙufule Habiba ta ce “Au hakama zaki ce? Ki zo girma da arziki na ara miki tayar, amma ki je ki ɓatar ko a jikinki?”

“To tayar da kuɗi ya saya? Idan da kuɗi ya saya ya faɗi kuɗinta, yayyena su biya shi”

Habiba da ta gama fusata ta ce “Dalla can, uwar meye a gidan naku, banda gayyar maza da tsiya, sai ka ce wata uwar kuka ajiye, har kike a faɗi kuɗin tayar a biya”

“Ku kun ajiye wata uwar ɗin ne, da kuna da wani abun ai babarku ba zata sayar da fanke da safe ba” Tayi maganar tana murguɗa baki.

Cikin rawar murya Habiba ta ce “Kar ki sake ki zagar mana uwa”

“Ni ban zagi babarku ba, ni dai na san fanke take sayarwa, fanken naku ma mai Shegiyar tsada, ƙanana kamar ƙuli-ƙuli, dan ranar Yasir ya ce har kiyashi ya gani a cikin fanken” kan Rumaisa ta rufe bakinta, tuni Habiba ta shaƙo hijjabinta, zata rufeta da duka.
Abinka dai mai nema a duhu, balle ya samu a sarari, nan Rumaisa ta zage ƙwanji ta tabattarwa da Habiba ita ɗin ƘANWAR MAZA ce.
Abin takaici da malami a gefe yana biyawa wasu allo suka harƙe da dambe.
A fusace ya miƙe ya saka bulala ya zane musu jiki, musamman Rumaisa, tsabar masifarta ya sanya baya son ta a ajinsa, kullum cikin rigima take, ga allonta sai yayi wata ba tayi wani rubutun ba, ga daƙiƙanci da surutu.

Idan da abin da Rumaisa ta tsana bai wuce duka ba, ta ji zafin dukan bulalar da Malam Ashiru yayi mata  ba kaɗan ba, dan haka ta koma gefe tayi shiru tana kuka. Ta rasa meya sanya ya tsaneta haka.

Habiba kuwa da ƙawayenta, suka ƙudiri aniyar idan aka tashi sai sun naɗawa Rumaisa duka saboda suna jin haushinta suma, a kan damben da aka yi a ƙofar gidan mai markaɗe ranar Alhamis, gashi ta zagi fanken babar ƙawarsu.

Ana tashi cike da takaicin dukan da Malam yayi musu, Rumaisa ta ɗau allonta ta nufi gida, sai share hawaye take. Sai dai yau babu tsokana a hanya, babu neman magana saboda bayanta sai raɗaɗi yake na dukan da malam yayi mata, gashi ba ta warke daga ciwon jikin punishment ɗin Yaya Umar ba.
Babu tsammani ta tarar da su Habiba a wani lungu suna jiran isowarta.
Turus tayi tana binsu da kallo kamar ba ta sansu ba.

Babu ko ɗar ta cigaba da tafiya tana yinƙurin ratse su ta wuce.

Shan gabanta Habiba ta yi ta ce “Ke kin isa ki tafi, ba dai ni kika zaga ba, kika kuma zagi babarmu ba, wallahi yau sai kin gane kuskurenki, kuma wallahi Sani ma ya ce sai kin biya shi tayarsa.
Ɗaya daga cikin yaran ta ce “Ai wallahi yau sai kin daku, haka nima ranar kika zubar mini da markaɗe, zaki gane baki da wayo”.

Bin su Rumaisa take da ido, sai kurari suke amma an rasa wadda zata kaiwa Rumaisa duka.
Sake yinƙurin wucewa tayi, amma Habiba ta janyo Rumaisa ta baya, yaran suka fara kai mata duka.
Tayi kukan kura, ta ɗaga allonta saukewa Habiba allonta a fuska, wani uban ihu Habiba ta kurma, jin danshi a hancinta.
Tamkar namiji a filin dambe, haka Rumaisa ta zage ita kaɗai ta dinga dukan yaran nan, yadda ta dunƙule hannu tana kai naushi, kai ba ka ce ‘ya mace bace.

Da ƙyar da siɗin goshi wani mutum ya rabasu, saboda Rumaisa akwai taurin kai, zuciyarta a bushe ana rabasu tana cigaba da kai duka.
Ta ɗau allonta ta nufi gida, tana ta huci, duk da dukan da tayi musu sai dai jikinta duk yayi tsami ita ma. Dama ga jikin nata babu daɗi ji

Sai dai kash, tuni wasu daga cikin yayyen yaran maza suka samu labari, suka yi gaba zasu datse Rumaisa a hanya, su zaneta.

Ayshercool
08081012143

[16/06, 9:00 pm] JAKADIYAR AREWA:                    ƘANWAR MAZA

BY AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

Ku yi subscribing YouTube channel ɗin mu, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro.
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
Arewabooks @ ayshercool7724
Watpad@ ayshercool7724

MIKIYA WRITER’S ASSOCIATION

Back to top button