Author: Novels

  • Kanwar Maza 26

    Kanwar Maza 26

    BOOK 2 PAGE 5

    *Paid book ne, 500 ne via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank, sai a tura shaidar biya ta 08081012143, wanda suke ba a Nigeria ba kuma, za su iya saya a arewabooks*

     

    Tsuru-tsuru suka yi suna kallon umar, sai dai yanayinsu ya nuna a razane suke, kuma aka rasa wanda zai yi magana.

    Ƙarasawa yayi gabansu, ya karɓi wayar daga hannun Aliyu, ya yi dialing lambar ɗanlami, yana kira ya ɗaga tare da yin sallama. Sai dai ɗanlami na jin muryar mai sunan baba cikinsa ya kaɗa, dan ba ƙaramin tsoron tijarar mai sunan Baba suke ba.

    Cikin kakkausar murya Umar ya ce “Me ka gaya musu? Ina ruma take?”

    Ɗanlami ya ɗan rikice sannan ya ce “Malam umar a saka addu’a, amma Akwai damuwa, ka san shi lamarin ƙaddarar Ubangiji ba ayi mata shamaki”.

    Cikin hasala ya kuma cewa”Ba nasiha na ce kayi mini ba, tambayata zaka amsa mini, damuwar me, ka yi mini bayani ina rumaisa take?”

    Tamkar an ritsa ɗan lami da bindiga ya ce “Umar wallahi ‘yan bindiga sun tafi da rumaisa, kuma ba da ita kaɗai suka tafi ba, amma an sanar da jami’an tsaro za su yi ƙoƙari a kai, za abi bayansu”

    Cikin tashin hankali ya ce “Ya isa haka ɗanlami, amma kun san garin nan babu cikakken tsaro kuka tura yarinyar nan? Babu yadda ba ayi ba a kan gwaggo ta bayar da yarinyar nan a dawo da ita gida amma taƙi, ta turata in da ta san babu tsaro, duk yadda ake ciki ku san yadda zaku yi, ni ban san wata magana ba kawai an haɗa baki da ku an yi garkuwa da yarinya ku san yadda zaku yi”.
    Ɗanlami zai yi magana, mai sunan Baba ya kashe wayar ya cillar ya fice a fusace dan gaba ɗaya jijiyoyin kansa sun miƙe saboda ɓacin rai da tashin hankali.

    Mama ce ta fito tsakar gida ta na faɗin “Wai babana shi da wa yake ɗaga murya, me kuka yi masa ne yake ta magana sama-sama?”

    Cikin sanyin jiki Usman ya ce “Saɓani ne aka samu, kin san halinsa da zuciya da saurin fushi”

    Mama ta ce “A’a ai kuwa bai fiye yin magana ba, sai an ƙure shi, wani abun dai ku ka yi masa, ko kuma faɗa kuke a tsakanin ku” gani tayi sun jeru basu ce mata komai ba, sai dai fuskokinsu ɗauke da damuwa, kamar a firgice suke.

    Ta dubi Aliyu da kyau ta ce “Gadanga wai menene, na ganku duk wani iri me yake faruwa ne, ko akwai wata matsala ne?”

    Aliyu ya dake ya ce “Babu komai mama, ni bari na fita zan sayo omo na yi wanki”.

    “Ban da omon da babana ya sayo shekaranjiya ya shigo da shi kaya guda, kusan kayan, wane omon kuma ka ke nema ko ka manta ne?”

    Ya dafe kai ya ce “Ohh na manta, aski zani, ai na manta shaf da Oman ne, idan na dawo daga askin sai na yi wankin” yana yin maganar yayi waje, Usman ya rufa masa baya.

    Gaba ɗaya mama ta kasa gane kansu, kuma ba wanda yayi mata bayanin wani abu. Kawai ta share ta cigaba da sabgoginta.

    Duk yadda usman ya so dakewa abu ya gagara, a soro ya durƙusa ya fashe da kuka, shi ya riga ya karaya ya san ubangijin da ya halicci ruma ne kawai zai fitar da ita.

    Aliyu ya rungumo shi ya ce “Haba usyy so ka ke sai mama ta gane ne? Dan Allah ka jure kan mu san abin yi, kar mu bari ta gano akwai matsala idam ta gane, ka san tana da hawan jini, yanzu zai iya tashi”

    Usman ya ce “Wane abun yi da me zamu karɓota? Me muke da shi? Mutanen da ba imani ne da su ba, ‘ya mace ce fa, Allah kaɗai ya san me zasu yi mata, gara ace mutuwa ta yi ga gawarta da wannan tashin hankalin, wa zai kula da ita?”.

    Aliyu da tasa zuciyar ma ke daf da karyewa ya ce “Na sani, amma addu’a ba ta bar komai ba Usman ita zamu dagewa, kayi haƙuri tashi ka daina kuka kar mama ta zo ta samemu” haka yayi ta rarrashin Usman.

    Mai sunan baba kuwa ji yayi duniyar ta yi masa zafi, ina ma shi aka ɗauka aka bar ruma. Yaya mama za ta ji idan ta samu labarin an yi garkuwa da rumaisa?.
    Zuciyarsa ta din ga zafi yana jin da zai ga gwaggo sai yayi mata rashin mutuncin da bata taɓa tunani ba, dan yana jin zai iya mangareta dan duk ita ta janyo wannan masifar, duk da tana ƙanwar mahaifinsu, cewar da aka yi tana gadon asibiti jininta ya hau bai dameshi ba, dan da jinin tasa uwar ya hau ko wani abu ya samu ruma, gara duk abin da zai faru ya faru.

    ***
    Zuwan takawa a Abuja a wannan karon ya sanya ya samu abubuwa masu muhimmanci da bincikensa bai kai masa ba a baya, sai dai zuciyarsa na ta azalzalarsa a kan lallai ya koma gida, jinsa yake tamkar a kan wuta, idan bai bar garin ba kamar wani mummunan abu zai faru da shi, dan haka babu shiri, ya tattara kayansa ya taho Kano, dama ga Ammi na ta waya dan duk a tsorace take, saboda yanayin jikinsa, Jabir ma duk ya addabeshi a kan nan kano ma akwai aiki, dan haka ya haɗa kayansa ya koma kano.

    Sai ka ce a wannan karon ya fara tafiye-tafiye, Ammi sai hamdala take a kan dawowarsa gida lafiya, dan ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba, da yayi tafiyar nan dan sam ji ta yi ba ta son tafiyar ta sa.

    A gidan Turaki suka haɗu, da takawa, da Jabir da kuma Jamil da ya kasance wa ga Samha kuma cousin ɗin sa.
    Hira suke yi sosai, suna tattaunawa a kan rayuwa.
    Jamil ya zunguri Takawa ya ce “Kai, wai me kake nufi da ni ne, ba fa ka taka gidana ba, ranar da na tare ma ko rakiya ba ka yi mini ba, kuma ba ka zo ba sai harkokinka kawai kake”

    Ɗan shiru Adam yayi, tun daga lokacin da ya ji muryar ruma a ranar ya rasa nutsuwarsa, kilisar ma da ƙyar aka ƙarasata da shi, tunani ya fara yi ko zuwa unguwar su zai yi.
    ‘Ka je ka yi mata me?’ wata zuciyar ta tambayeshi.
    Tsaki yayi wanda ya fito fili bai sani ba.

    “Tsakin me kake kuma?” Adam ya tambaye shi.

    Girgiza kai yayi bai ce komai ba.

    Jabir ya ce “Yauwwa Takawa, ina mutuniyarka kuwa wannan yarinyar?”

    Haɗe rai Adam yayi tare da basarwa, Jamil ya ce “Wace yarinyar, budurwa yayi ne? Kai ka isa ka yi wa ƙanwata kishiya?”

    Jabir ya ce “To bana ce ba, wata ‘yar figigiyar yarinya ce mai kama da bainu, ban taɓa ganin yarinya mara mutunci da rashin tsoro irinta ba”.

    Adam a ransa ya ce “Ai ba ka san mara mutunci ba, sai ka ga wasiƙar da ta rubuta mini’ amma a zahiri yayi shiru kamar ba da shi suke hirar ba.
    ***
    “Ina sonka Adam, so bana wasa ba, so mai tsananin gaske son da nake jin zan iya komai domin na mallake ka, duk da na rasa dalilin da ya sanya bana gabanka, ko da yake ba rasa dalili na yi ba, nafi kowa sanin dalilin da yasa bana gabanka, kuma ina daf da magance komai domin in samu miƙaƙƙiyar hanya ɗoɗar ta cimma muradina na rayuwa da kai, ko baka aureni ba ina son kasancewa da kai na rayu ƙarƙashin kulawarka. Ban sani ba ko zuwa nan gaba asirina ya tonu duk da bana tunanin faruwar hakan, amma idan ma ya farun ka yi mini uzuri soyayyar ka ce ta janyo mini hakan” tamkar taɓaɓɓiya haka samha ta saka hoton Adam a gaba ta na surutu, hoton yana sanye da kaya ne na sarauta, ya ɗan sauke rawaninsa yana murmushi, wanda aka ɗauka da hawan wata salla.
    Sai da ta gama soki burutsunta, ta mayar da hoton ma’ajiyarsa, ta tashi ta ƙarasa shirinta ta fice.

    Mummy ce tare da aminiyarta zaune a ƙuryar ɗakin Mummy suna tattaunawa.

    “Wai hajiya Lubabatu babu wani zazzafan malami ne, abubuwa kamar sun tsaya mini, sun ƙi cigaba kamar yadda nake so”.

    “Haba Jamila, ke kin san an daɗe muna haƙa rijiya, rijiyar da muke saka ran samun ruwa a kowane lokaci, mun shirin da idan balli ya tashi akwai rikici, ke dai mu cigaba da haƙuri”.

    Mummy ta girgiza kai ta ce “Ya ci ace burina ya gama cika, nifa da dai da mintuna biyar bana son ruhin Binta ya kasance cikin kwanciyar hankali da farinciki, so nake ta dauwwama a baƙin ciki har ƙarshen rayuwarta”.

    Dariya Hajiya Lubabatu ta yi ta ce “Haba Jamila, ai ko a haka kika barta wallahi ta yabawa aya zaƙinta, kuma ta ɗanɗana kuɗarta, amma ki cigaba da haƙuri ai mun ɗana tarko daban-daban”.

    Mummy ta jinjina kai ta ce “Shikenan, bari mu ga zuwa yaushe, na cigaba da sanya musu ido, duk wani motsinsu uwani na gaya mini, kuma na ce lallai ta kawo mini maganin da waccan ‘yar tsintuwar ke shafa masa”.

    “To shikenan, to bari mu ga yadda abubuwa zasu kaya”.
    ***
    Har azahar babu wanda ya kula su ruma, masu kuka na yi masu addu’a na yi, ga yunwa ta addabeta a gida wataran ƙarfe bakwai ta karya, amma har bayan azahar babu wanda ya kulasu balle ya basu wani abu.
    Tashi ruma ta yi ta samu ɗaya daga cikin ‘yan bindigar ta ce “Bawan Allah yunwa nake ji, ku bani abinci na ci”

    Wani mugun kallo ya yi wa ruma ya ce “Zo ki cinyeni, an gaya miki nan wurin hutu ne da jin daɗi?”.

    “Ai ni ba mayya bace da zan cinyeka, idan ma cin ne ban ga abin ci a nan ba, idan ba za a bamu abinci ba meyasa zaku kawo mu nan?” Ta na rufe baki yana hankaɗeta sai dai faɗi ƙasa ya saita ta da bindiga “Idan ki ka yi mini hauka, yanzu na lahira zasu yi maraba da ke”.

    Ruma ta kalli yadda ta faɗi ƙasa, wata irin zuciya ta harziƙota ta miƙe tsaye ta sake kallonsa ta ce “Na faɗa a bani abinci yunwa nake ji, ai daɗinta idan ka kasheni ba a wuta zaka sakani ko aljanna ba, hisabi na Allah ne, to na faɗa a bani abinci yunwa nake ji, harbeni maza kai kuma a ƙara maka kwanakinka a duniya”
    Babu alamar tsoro ko shakka a tare da ruma, kowa sai da ya Zubo mata ido, saboda ƙarfin halinta.

    A fusace ya tashi yayi kan ruma, amma wani ya riƙe shi, ya ce kar ka kuskura, ƙyaleta idan ka yi mata wani abun za’a iya samun matsala, ka bari oga ya zo ya faɗi ya za ayi”.

    Huci ya din ga yi yaso ya tattaka ruma, ko ya keta mata haddi a gaban mutanen wurin, ya kawo ƙarshen harshenta.

    “Ni baka kyauta mini ba da baka bari ya kasheni na huta ba”

    “Wato ke dai bakinki ba zai mutu ba ko?”

    “Idan har so ku ke na yi shiru, to ku kasheni ko ku mayar da ni gidanmu, wannan ai zalunci ne ni yunwa nake ji” tayi maganar tana share hawaye.

    Dattijon nan ne dai na jiya ya ce “Yarinya ki yi shiru da bakinki, kar su citar da ke, wannan mutanen ba ayi musu haka”.

    “To ni yunwa nake ji” tayi maganar har cikin zuciyarta.

    Duk wani kurari da zare ido ruma taƙi yin shiru, kamar ma da gayya take yi dan ta tunzurasu su yi mata abin da za su yi mata.

    ***
    Har dare mama ba ta san abin da ya faru ba, kuma an rasa wanda zai gaya mata, sai mita take musu cewar ita fa ta kasa haƙuri ta kira gwaggo idan an dawo da ruma ta haɗata da ita, amma wayar gwaggon ba ta shiga. Sun yi mamaki da duk jin rediyon mama ba ta ji batun kai harin ba.
    Ganin tana ta surutu ita kaɗai ba wanda ya tanka mata, ya sanya ta magantu “Wai ba zaku gaya mini meke faruwa ba ne? Duk cikinku fa yau babu wanda ya ci abinci, kun ƙi walwala kun ƙi magana, kuma kun ƙi gaya mini menene?”

    Usman ne ya tashi ya ce “Mama sai da safe, ni dai bana jin daɗi ne”.

    Babu wanda ya bawa mama amsa, a hankali duk suka watse daga tsakar gidan, mama ta sha jinin jikinta ta fara tunanin menene ya faru haka, da basa son gaya mata?.

    Babu wanda ya saurari su ruma sai bayan la’asar, aka zo da wasu kuloli a kan babur, aka rarraba musu wata busashshiyar gurasa, gaya guda ɗai-ɗai, sai pure water ɗaya tamkar mabarata.
    Ruma ta kalli gurasar nan, duk uwar yunwar da take ji, amma a rasa me za a bata sai wannan takurarriyar abar a bushe, babu mai babu komai a jiki.
    Gashi duk ta bushe kamar ƙanzo.

    Ruma ta gasta ta fara ƙoƙarin haɗiya, amma ta kasa haɗiyewa, da ƙyar ta dannata da ruwa, daga gutsura ɗayar nan ba ta ƙara ba ta shanye ruwanta ta yar da ledar, sauran kuwa tuni kowa ya kama gurasar nan suka cinye.

    ***
    Duk wata tattaunawa su Usman da sauran ‘yan uwansa sun yi, amma sun rasa ta ina zasu ɓullowa lamarin, duk in da zasu buga sun yi, amma babu wani labari game da in da su ruma suke, gashi da wani ya ce zai je katsinan mama za ta gano akwai abin da yake faruwa, dan a yanzu haka ma duk ta tsargu, mussaman yadda suka daina walwala ga kuma ta fara shiga damuwa rashin shigar wayar gwaggo.
    Su huzaifa ma sun gano abin da yake faruwa, sai dai yanayin ruɗewa da Huzaifa da Yasir suka yi, ya sanya mama cigaba da jefa musu zargi da kuma kokwanto.

    Yau ƙarfe tara na safe taga duk sun fito daga ɗakinsu sun jeru a tsakar gida, kamae kullum babu wanda yake walwala a cikinsu, kuma babu mai sunan Baba a cikinsu.
    Mama ta girgiza kai ta ce “Koma menene Allah yayi muku maganinss, tunda ni dai ina tsakaninku ba zaku gaya mini ba”.

    Ta fito daga banɗaki kenan, Abubakar yayi sallama ya shigo da jakarsa ta makaranta, sai dai kallo ɗaya tayi masa shima ta ga tsananin tashin hankali a fuskarsa.

    Mama tayi saroro tana kallonsa, cikin ƙarfin hali ta ce masa “Kai kuma me ya dawo da kai yanzu?”

    Suka haɗa ido da Aliyu, Aliyu ya sunkuyar da kai, Yasir kuma ya hau goge hawaye.

    “Saddiƙu, dan Allah kai ka gaya mini menene? Ku daina ɓoye mini koma menene, na kasa nutsuwa sun ƙi su gaya mini abin da yake faruwa, na rasa gane kansu, dama har akwai abin da ban cancanci in sani ba?”

    Abubakar ya ajiye jakarsa ya kamo hannun mama ya ce “Mu je ɗaki mama sai mu yi magana”

    Mama ta buge hannunsa ta ce “Ba in da zani, ku yi ta riƙe abin ku a cikinku nima bana son ji, idan abin da bana ƙauna a rayuwata bai wuce ganin fuskokin da ba sa son damuwata in gansu cikin damuwa ba, ko ba zan maganta muku ba ai na yi addu’a” ta juya za ta wuce ɗakinta.

    “Mama ruma ce” ya furta a hankali, cak mama ta tsaya ta kasa gaba ta kasa baya, ta ji maganar ta sa kamar bai faɗeta dai-dai ba.

    Ba tare da ta waiwayo ba ta ce “Mutuwa ta yi?”

    “An yi garkuwa da ita, a garin su Iya, a cikin harin da aka kai ƙauyen har da ita aka ɗauka”.

    Innalillahi wa Innalillahi raji’un, mama za ta iya cewa ko mutuwar iyayenta ba ta girgizata kamar wannan abu da ta ji yanzu ba, ji ta yi kamar ba a hayyacinta ta ji maganar ba, tamkar an mata yayyafin wuta, Rumaisa a hannun ‘yan biniga, gara ace kashe mata ita suka yi, ta tura a ɗauko mata gawarta, amma ruma ‘ya mace ƙarama a hannunsu a tsakiyar dajin Allah, Allah kaɗai ya san me za su yi mata, ga halin ruma da ta sani na rashin kunya da surutun tsiya, tsaf za su illata ta.
    Jikin mama ne ya hau rawa, ta sake ƙare musu kallo, Huzaifa da Yasir suna ta kuka, Aliyu kuma ya sunkuyar da kai, haka Abdallah, Usmsn kuwa barin tsakar gidan ya yi, babu mai sunan Baba ko ba a gaya mata ba ya tafi katsinan ne.

    Ta yinƙura da niyyar ɗaga ƙafarta, ta tafi luuu gaba ɗaya suka yi kanta suna kiran sunanta

    Ayshercool

  • Kanwar Maza 20

    Kanwar Maza 20

    P 20

    *MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

    *SHI YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR  DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA? TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN FATA NE? KO KUWA SO KI KE FATARKI TA DIN GA SHEƘI TA NA HASKAWA? MAZA KI GARZAYO WURIN MEENA DOMIN SAMUN MAFITA*

    *Royal jelly big 22000*
    *Royal jelly 30 pieces 2200*
    *Royal jelly small one 60 pieces inside the pack 3000*
    *Vitamin C-100, 2700*
    *Vitamin E big 3000*
    *Pesona 2300*
    *Dara 2300*
    *Cantik ayu 2300*
    *GLUTA white 2700*
    *Khusus ibu 3800*
    *Sugar wanita 3500*
    *Majakani 3 in 1 3200*
    *Eve Care 3700*
    *Juliet eve 11,500*
    *Phyton buster 18,000*
    *Phyton collegen 18,000*
    *Glute sparkling 18,000*
    *7 days ginger oil for hair 1,200*
    *Papaya oil for breast 1,200*
    *Garlic oil for hips 1200*
    *Vitamin C serum 1,500*
    *Vitamin E serum 1,500*
    *Busty blend 2800*
    *Gluta prime 2800*
    *Collegen+C 3800*
    *Yan uwa abun fa da yawa bazan iya kawosu gaba daya ba amma muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*

    https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
    *Wai ina da ku fans, ace haryanzu ban haɗa 1k subscribers a channel ɗina ba, anya akwai amana kuwa😒*

    Ku yi subscribing YouTube channel ɗin
    @Cool Hausa Novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro.

     

     

     

    P20

     

    *Page ɗin sukutum guda naki ne masoyiyya Zainab kumurya, idan kin ga dama ki yayyaga shi ki zubar ko ki kashe Ruma, tun da naki ne😂. Ke kuma marubuciyar mijin malama Nimcy ki ji tsoron Allah, wallahi ana ta ƙorafi kin sako jaruma da masifu amma kin yi burus da mutane, zan karɓe rubutun mijin malamar nan fa😂 wanda bai karanta ba ya garzaya mijin malama an gama book1 labari mai tsayawa a zuciya*

     

    A gigice Iman ta riƙo Ammi tana jera mata sannu, jinjina mata kai kawai Ammin ke iya yi, amma ta kasa magana.
    Iman ta rungumota ta zaunar da ita a kan gado, cikin damuwa ta ce “Ammina, dan Allah ki yi haƙuri, ban nuna miki dan na tayar miki da hankali ba”

    “Kar ki damu Iman, ba ki tayar mini da hankali ba, kawai dai tari ne ya taso mini, kawo mini ruwa a fridge mai sanyi na sha.

    Cikin rawar jiki Iman ta tafi ta kawowa Ammi ruwa, ta karɓa ta sha, sannan ta ɗan kwanta ta lumshe idonta. A take ƙwaƙwalwaarta ta shiga tariyo mata abin da suka wakana a shekarun baya, daga kafuwar gidan zuwa yanzu, abubuwa da dama sun faru masu matuƙar wahalar mantawa da kuma ruɗani, wanda haryanzu a haka ake, komai sake dagulewa yake yi. A hankali ta gyara kwanciyarta tana son ta kawar da tunanin daga zuciyarta, amma sai kaiwa da komowa abubuwa suke a ƙwaƙwalwarta suka hanata sukuni.

    ***
    Ruma kuwa a ‘yan kwanakin nan ta addabawa Yasir, kusan kullum tana liƙe da shi tana kallon waya, idan anjima ta ɗau wayar Usman ta fara game, ya zo yayi ta zaginta ya ƙwace, sai ta koma gefe ta ɗau wayar mama, ta yi ta yi wa ƙawayenta fulashin, wasu su biyo wasu kuma suma su yi ta mata fulashin, babban abin da yake ƙonawa mama rai fulashin, wataran wayar haske kawai take yi, ko sai ta fara ringing ta zo ɗagawa ta katse, mama ta yi ta masifa ta ce “Idan baki kiyayeni ba, da ke da ƙawayen naki sai na saɓa muku, gayyar rashin hankali”.

    Yasir yana ɗan taɓa gyaran wayoyi, ya iya harkar jagwal, shine gyaran waya, system da sauran kayan electronics.
    Wata waya ya samu, ta sha jiki, ya sayo layin data, ya saka a wayar, ya bawa ruma ya ce “Gashi nan, ki dinga kalle-kallen ki a wannan ki ƙyale mini wayata, kuma ki daina ɗaukar wayar mama kina fulashin, ki yi da wannan, saura ki lalata kuma akwai lokacin da zan dinga karɓa, dan ba bar miki na yi ba. Na buɗe miki account amma ban saka sunanki ba, ƙanwar maza na saka na ɗora miki hoton flower a dp kar a gano mu”.

    Ruma tamkar ta goya Yasir dan murna da farin ciki, ta gurfana ta dinga yi masa godiya, tare da sanya masa albarka.

    “Amma ki ja bakinki ki yi shiru, kar ki gayawa kowa”

    “In Allah ya yarda ba zan gaya wa kowa ba, bakina ƙanin ƙafata, amma me yasa ba zaka saka mini sunana ba da hotuna na nima?”

    “Dan ubanki gidanku kuna da background ɗin da zaki dinga hoto ne? Kuma ni ban baki dan ki saka hotunanki ba, dan wallahi kin san idan suka gano kashinmu ya bushe, idan kin san ba zaki bi abin da nace ba, to tun wuri na karɓe kowa ma ya huta”

    “A’a Allah ya baka haƙuri, da wasa nake maka nima, idan bana komai sai ka dinga bani ina ganin duniya nima, a daina hantarata dan na leƙa waya”.

    Tun da Yasir ya bata wayar nan, aka samu sauƙin neman magana a cikin gida, kusan koda yaushe tana kan wannan jagwal ɗin wayar, kuma Yasir abubuwan karatu yayi mata following, dan haka su tafi gani, kuma sosai suke ɗauke mata hankali, ya fi bata da daddare idan ya tabattar ta gama ayyukanta, da assignment, sai ya bata ta zauna a kusa da shi ta kalla, da lokacin kwanciya ya yi ya ƙwace wayar ya korata ta kwanta.

    ***
    Zuwa la’asar Ammi ta ɗan samu nutsuwa, sai dai kallo ɗaya zaka yi mata ka san tana cikin damuwa.
    Takawa ya fuskanci damuwa ƙarara a fuskar ta, sai dai ganin yadda take basarwa ba ta son magana, ya sanya shi yin shiru bai yi ƙoƙarin tilasta mata jin abin da yake damunta ba.

    Wurin Jabir ya tafi, domin samun sauƙin wasu damuwoyin da suke damunsa, kasancewar sa ɗan uwa ɗaya tilo da ya fi yarda da shi.
    Jabir na ganinsa ya ce “Sarkin matsala, tun kafin ka yi magana, fuskarka ta nuna akwai damuwa, yau kuma menene?”

    Takawa ya ɗan yi shiru, sannan ya ce “Khalifa Usman wakili”

    Jabir ya tsuke fuska ya ce “Ba zaka rabu da sabgar wannan yaron da ahalinsa ba ko?”

    A hankali Adam ya ɗan lumshe idonsa, ba ya son yin dogon jawabi da ga Jabir, tun da shi jabir haryanzu ya kasa gane abin da yake nufi game da khalifa, dan haka kawai yayi shiru ya cigaba da tunani.

    “Ina Ammi?”

    Adam ya buɗe idonsa ya kalli jabir, amma bai yi magana ba, so yake yayi masa zancen muryar nan da yake ji, wadda haryanzu ya kasa daina jinta a kunnuwansa, amma ya san da ya ɗago zancen Jabir zai yi masa wata fassarar. Bai gama fahimtar mai Jabir ya cigaba da cewa ba, sai jin sunan Iman da yayi Jabir ya furta.

    Ya ce “Me ka ce ne?”

    “Ni fa matsalata da kai wulaƙanci, duk surutun da nake ba ka ma gane me nace ba?”

    “Sorry” ya faɗa a taƙaice yana tsare Jabir da ido alamar yana son ya maimaita masa me ya ce.

    Jabir ya ce “Well, cewa na yi, wai me ƙaninka yake nufi da Iman ne, yana takura mata da yawa fa”

    “And so…?”

    “Kana nufin ba ka damu ba kenan?”

    “Kaga ni ka ƙyaleni da sabgar gidan nan, bana iya tunanin komai a kai, ko na fara ma kaina ciwo yake yi, gaba ɗaya bana son yin tunani a kan matsalolin gidan nan “.

    Jabir ya yi ajiyar zuciya ya ce “Haka ne, ni auren Iman nake son ku bani, ka wuce mini gaba zuwa wurin Ammi mana”.

    Wani irin kallo Adam ya yiwa Jabir ya ce “Ba ka da hankali ne?”

    “Ban gane ba ni da hankali ba?”

    “Amma ka san ba abu ne da zai yiwu ba ko?”

    Jabir ya ce “Saboda me, wai ni ko dai kai ne ka ke son ta ne?”

    Tsaki Adam ya yi ya tashi ya ce “Ka san idan har zan auri Iman, zan iya auren su Nusaiba ko Fauziyya, kai ma ka san ba zan bari ka auri Iman ba, kuma ka san dalili”.

    “Amma a tunanina wannan bai kai hujjar da za a hanani aure ba”

    A ɗan hasalae takawa ya ce “A ganinka ba”

    “Amma…..” Bai jira jabir ya gama maganar ba, ya fice ya bar Jabir.

    ****

    Ruma ce a tsakar gida, ta zage tana ta dakan ƙuli-ƙuli, zata yiwa Yasir kafi kaza, dan ya ƙara samun ƙwarin gwiwar bata waya tana jagwalgwalo, dan wayar ta fara shiga ranta sosai, ga cacar kuɗin data yana yi mata, da na caji wasu lokutan, tayi kiran ƙawayenta a wayar iyayesu su yi ta shashashanci ta daina ɗaukar ta mama.
    Mama tana ganin wayar a hannun ruma, tana mitar ba ta son yawan duba wayar nan da take yi, a zatonta wayar Yasir ce kawai yake bata ta yi game da wasanta ta bashi kayarsa.

    Mai sunan Baba ya nutsu ya tattara hankalinsa a kan litattafansa, sai dai hankalinsa ba a kan litattafan yake ba, damuwa da tunani ne fal a ransa, zuwa yanzu yakamata a sake aikawa da Abubakar kuɗi ko babu yawa ne, dan har zuwa yanzu ya ce masa bai samu wani aikin ba, leburanci ne ya kan shiga cikin gari ya nema idan ba shi da lectures, kuma gashi ɗan abin da za a baka na leburancin nan, bashi da wani yawa ga wuni ana aikin ƙarfi.
    Ga kuɗin saukar su Yasir, ga kuɗin Necon su, dan dai suma yaran suna da ƙoƙarin neman na kai, da karambani Yasir ya koyi gyaran fitila, da wayoyi gashi ya san kan computer sosai, yanzu zai kashe wata wayar  ya tashi wata yana da kai a wannan fannin.
    Shi kuma Huzaifa big boy ne, shi baya tanadi, idan ya samu kuɗi kawai ya kashe su, a huta. Sai dai bashi da rowa, yana zuwa shagon ɗinki da na aski, amma mugun mashiririci ne na gaske.
    Sallamar da aka yi ne, ta dawo da mai sunan Baba daga tunanin da ya tafi.

    Wata yarinya ce sa’ar ruma, sai kuma wata ‘yar budurwa suka yi sallamar.

    Fuskarsu kawai ya kalla, ya san da ƙuyar idan ba ruma ce, ta yi wata tsiyar ba.

    Suka gaida mama cikin ladabi, shi kuma ya mayar da hankali a kan littafin gabansa kamar bai san da zuwansu ba.

    Zumbur ruma ta miƙe, za ta janye su, mama ta ce musu yaya aka yi, saboda ita mama a tarbiyyar ta ƙawaye ba sa biyo ruma gida, idan ba wani abu ne mai matuƙar muhimmanci ya kawo su ba.

    ‘yar babbar ta ce “Kuɗin da ƙanwata take bin ruma, muka zo karɓa”.

    Cikin mamaki Mama ta ce “wane kuɗi kuma?”

    Yarinyar ta ce “Ranar an aiki ƙanwata, suka haɗu da ruma, shi ne a canjin mamanmu, ruma ta ranci naira ɗari biyu ta bawa wani  tsoho almajiri, wai  ya bata tausayi da ga gani yunwa yake ji, wai zata bata kuɗin kuma haryanzu ba ta bayar ba, mamanmu kuma so take ta yi amfani da kuɗinta”

    Mama ta ce “Innalillahi wa Innalillahi raji’un, ita ruman? Uban waye ya ce ki karɓar musu kuɗi kiyi sadaka da su?”

    “Wallahi mama tausayi ya bani, cewa yayi na taimaka masa, kuma idan na bayar da kuɗinki zaki yi mini faɗa, shi ne na ranci canjin babarsu, kuma malam ne ya ce mana sadaka maganin masifa ce”

    “Ke a cikin wace masifar ki ke? Ko da yake akwai masifar da ta wuce ɗauko mini magana da ki ke yi ba yau ba gobe, baki yi sadaka da kuɗin uwarki ba sai na uwar wasu, saboda tsabar rashin ji?”

    Abdallah ya ce “Wallahi mama yarinyar nan da ƙyar idan ba ta da taɓin hankali”.

    Mama rasa me zata yiwa ruma ta huce ta yi, saboda yadda take caza mata kai abin ya wuce hankali, sai ƙifta ido take kamar an kwashewa karya ‘ya’ya, gefe ɗaya kuma tana hararar yaran.
    Mai sunan baba ya kalli Ruma, ya ga tana yiwa yarinyar alamar idan suka haɗu sai ta yankata.
    gashi yau Mama ba ta da wani kuɗin kirki, ga ruma zata ja mata fitar naira ɗari biyu ba dalili.

    Mai sunan Baba ya saka hannu a aljihunsa, ya ciro naira ɗari biyu ya ajiye ya kalli yaran ya ce “zo ki ɗauka”

    Cikin fargaba da tsoro yarinyar ta tafi ɗaukar kuɗin, dan fuskarsa ma kawai abar tsoro ce saboda kwarjini.

    Har ta durƙusa ta ɗau ɗarin, ya kalleta sai da hantar cikinta ta kaɗa, ta dakata da ɗaukar kuɗin.

    “Ke shashashar ina ce da wata za ta ce ki bata aron kuɗin babarki, ki bata ta bayar kina tsaye san sokwanci”

    Jiki na rawa ta ce “Idan ban bata ba zata iya dukana”

    “Idan ta dakekin ba zaki iya ramawa ba, ko ƙarfinki ta fi? Daga yau idan kuka kuma bata wani abinku, ku ka biyota gida kawo ƙara, da ku da ita zan haɗa na zane, ɗauki ki tashi ki bani wuri”
    Kamar mai shirin ɗauko wani abu a wuta, haka ta miƙa hannu ta ɗauko kuɗin, ta tashi suka fice da sauri.

    “Ke kuma zo nan” yayi ya yana kallon inda ruma take.
    Jikinta har wata tsuma yake, ta taso ta zo in da yake ta durƙusa.

    Ya ƙare mata kallo ya ce ‘har kin manta sharaɗinmu ko?” Ta girgiza kai.

    “Da kyau, nan da gobe in Allah ya ki nemo kuɗina da na bayar ki biyani, dan ba zan ɗau asara ba, kuma ban yarda ki tambayi wani a gidan nan ya baki ba, kuma ki ka je waje ki ka ɗauko magana sai na takaki a gidan nan, mara kan gado tashi ki bani wuri” da sauri ta zabura ta bar gabansa tana tsuma, ita yanzu a gidan uban wa za ta samo kuɗin da zata biya shi?.

    Haka ta koma tayi zuruuu, kamar ruwa ya jiƙa mage, tana ji a ranta idan ta kama yarinyar nan sai ta daku, saboda ja mata damuwa da ta yi.

    ****
    Samha ce zaune a falo, tana shan twa da biscuit tana yi tana kallon tv, tare da kaɗa ƙafa.
    Wayarta ce ta fara ringing, dan haka ta ajiye kofin tean, ta ɗau wayar ta kara a kunnenta.

    “Samha” ya kira sunanta a taƙaice.

    “Waye?” Tayi maganar cikin ƙosawa.

    “Khalifa Usman wakili”

    “Wai meye haɗina da kai ne? Me ka ke so kuma?”

    “Easy mana, a kan maganarmu ne dai da muka fara”

    Samha ta ja tsaki ta ce “Wai kai baka ganewa ne? Ba mun gama wannan maganar da kai bane ba?”

    Ya ɗan yi shiru sannan ya ce “Ina ƙara baki lokaci ne, gudun kar ki dawo kina cizon yatsa daga baya, kin fi kowa sanin halin sa da taurin kai, ke a tunaninki ta ina burinki zai cika, kina daga zaune kina shashashanci lokaci na ƙure miki? Kiyi abin da ya dace ki samu burinki ya cika, ganin bayan Adam baya na nufin yi masa illar da ba zai amfanu a gareki bane ba, amma ganin bayan nasa shi ne samun damarki na biyan taki buƙatar. Idan so nake na kawar da Adam, abu ne mai sauƙi a gareni, amma ni ba hakan nake buƙata ba, haɗin kanki kawai kiyi tunani amma”.
    Bai tsaya jin amsarta ba, ya katse wayar, Samha ta bi wayar da kallo, tamkar za ta ga Khalifa a ciki. A hankali ta ajiye wayar ta yi shiru tana jujjuya maganar sa, sai dai ta kasa gano cikakkiyar mafita a kan lamarin.

    “Samha, me ki ke tunani ne?”

    Samha ta kalli mai maganar ta girgiza kai ta ce “Babu komai”

    “Ki yi sauri ki je ki duba kayan nan, bana son sai an fitar mutane sun gama zaɓa tukuna”

    Samha ta ce “Shikenan” sai dai hankalinta da nutsuwarta sam ba sa tare da ita.

    ***
    Sam ruma ta rasa sukuni, gaba ɗaya sallolinta addu’a take a kan Allah ya sa mai sunan baba ya huce, idan bai huce ba bata san in da zata samo ɗari biyun nan ba, gashi ya ce kar ta sake ta tambayi kowa a gidan.
    Gashi har wayewar garin yau ba ta samu kuɗin ba, wunin ranar bai kulata ba, bai kuma ce ta bashi kuɗin ba, sai da dare yayi, ta rasa dalilin da ya sanya yake son hukunta ta da daddare ya hanata bacci.
    Tana zaune zuruu ta takure, tana zancen zuci ta ga ƙafafuwan sa, tana ɗaga ido suka yi ido huɗu.
    Take ta rikice ya fara “Wallahi yaya ban samo kuɗin nan ba, ban san a in da zan samo su ba, kayi mini rai dan Allah”.

    “Kin san ba ki da inda zaki samo kuɗin kika arar mata kuɗi, da uban wa zaki biyata da? Wato sata ki ke kenan”

    Cikin kururuwa ta ce “Innalillahi wa Innalillahi raji’un, wallahi ban taɓa ɗaukar kayan wani ba. Wallahi dama niyyata na tara mata, sai na biyata amma wallahi bani da kuɗin da zan biyaka dan Allah kayi haƙuri”

    Cikin kaushin murya ya ce “Sai fa kin nemo kuɗina kin biyani, ko a ina ne”

    “Wallahi sai dai in kayana za a sayar a biyaka, amma wallahi bani da su”

    “Wallahi da kin samo kuɗin nan kin bani, sai na taka kanki, ta tabatta sata ki ke yi, ko a gida ko a waje, amma sai Allah ya ƙwace ki, kin yi sa’a da kin gane shayi ruwa ne, sai na sakaki a mari na kulle, kuma ki cigaba da abin da ki ke yi kar ki fasa, idan ki ka kaini bango sai dai ki ji an ɗaura auranki da malam Ladan, ko na sakaki a mari” jikin Ruma har ɓari yake, saboda wannan taratsin da yake yi mata kamar ta yi fitsari haka take ji. Ba ta samu damar shaƙar isashiyar iska ba, sai da ya bar ɗakin ta dinga ajiyar zuciya.
    Mama kuwa sam ba ta tanka musu ba, dan a yanzu kowane hukunci mai sunan Baba zai ɗauka a kan ruma, ba zata nema mata sassauci ba, saboda ruma babu alamar shiriya a tare da ita.

    Sai da wannan ƙurar ta lafa, sannan ruma ta samu nutsuwa, ta cigaba da harkokinta.

    Kamar mai ɗaukar karatu, haka ta nutsu a kan waya, tana kallo a Instagram wani abun ta yi dariya wani tayi tsaki.

    Kan wani hoto taje, wani kyakkyawan mutum, ya sha kayan graduation, yanayinsa bai yi yanayin fara’a ba, amma ya ɗan geɓare baki yayi murmushi, har za ta yi liking saboda a rayuwarta tana son ta ga mutanen da suka yi nasara, musamman ta kammala karatu.
    Kawai sai ta sake wurgawa, ta ga wani hoton nasa a cikin turawa, ta dinga dubawa, sauran hotunan duk a cikin turawa, da kuma aji na karatu, ajin tamkar ofishin wani shugaban ƙasar.
    Haushi ne ya kama ruma da tuno yadda ajinsu yake, sheranjiya da aka yi ruwan sama, suka je suka tarar ruwa ya cika ajinsu, murfin kwano ya yaye, sai haɗesu suka yi a wani ajin.
    Ai babu tunani ta shiga comment section ta ce An ɗibi haramun an je karatu, Allah ya isa kuɗin talakawa, ɓarayin kuɗin mutane, bamu yafe ba muna fama ajinmu ko rufi babu.  daga haka ta ƙara gaba, ta cigaba da kallonta.

    Ta gama abin da take, ta ajiye waya ta shiga nata shagali.

    Sai da daddare ta dawo, ta sake ɗaukar waya, ta ga an yi mata reply a message, ta yi ta murna yau an kulata a Instagram, dan ganin mutanen Instagram ɗin take wasu mutane daban.

    Sai dai tana dubawa ta ga wani yayi mata replying da ‘Ya aka yi ki ka san da kuɗin talakawa ya yi karatun’

    Cikin zafin rai ta rubuta ‘Idan gaskiya ne meyasa ya tafi ƙasar waje karatun, su yi a Nigeria mana” ta rufe datar ta ajiye tana huci, tare da ɗan jin releif a ranta, dan ta daɗe tana son samun damar da zata isarwa irin wannan mutanen abin da yake ranta.
    Yanzu take jin kallon waya yayi mata rana, da ta ƙi yin zuciya har ta iya yadda ake amfani da irin wannan abubuwan.

    ***
    Takawa ne riƙe da waya a hannunsa, Jabir sai surutu yake yi masa, amma kasancewar suna da banbancin hali shi da Jabir, ya sanya Jabir bai damu da rashin amsawar Takawa ba, saboda shi mutum ne ba mai yawan magana ba.

    Can Adam ya ɗago rai a haɗe ya ce “Kai, wai ban hanaka ɗora hotuna na a social media ba?”

    Jabir ya yi dariya ya ce “Tuna baya ne, ya sanya na ɗora gashi ka yi kasuwa ‘yan mata sai comment suke yi, waɗanda kuma suka sanka, suna yabawa tare da jinjina maka”

    Adam ya yi guntun tsaki ya ce “Kana da matsala” har ya wuce account ɗin Jabir, kawai ya koma ya shiga comment section yana dudduba abin da aka ce.

    Sai dai lokaci ɗaya annurin fuskarsa ya ɗauke, har wata zufar ɓacin rai ta fara tsatstsafo masa a goshinsa, duk kusan ko yaushe a cikin damuwa yake, amma ya daɗe bai ci karo da abin da ya daki zuciyarsa kamar wannan ba.
    Ya ɗaga ido yana kallon Jabir, Jabir ya ce “Ya dai, ya na ga kana kallona?”

    Riƙe wayar yayi, ya cigaba da kallon Jabir, Jabir ya miƙe ya duba wayar, ya yi tozali da abin da ya sanya Adam ɓacin rai.
    Jikinsa ne yayi sanyi, dan sam bai san an yi wannan comment ɗin ba. Yana ƙoƙarin yin magana takawa ya ce “Kira mini Sidi a waya, ayi mini tracking ɗin account ɗin nan”

     

    (Mun kusa kammala book1 in sha Allah, mai buƙata yana iya yin payment na book 2.
    500 ne via 0009450228
    Aisha Adam jaiz bank. Sai a turo mini evidence of payment ta 08081012143, zan ɗan bada time kan na cigaba da book2, sai an gama payment, hajiyata idan har kina iya sayen data ki saka a wayar ki, to ki tara kuɗi ki sai book ɗin Ƙanwar maza, you will never regeret tafiyar akwai ƙaruwa a cikinta. Ina alfahari da ku masoya)

    Ayshercool
    08081012143
    ƘANWAR MAZA
    Na Aisha Adam (Ayshercool)

    MIKIYA WRITER’S ASSOCIATES

    P21

    *MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

    *SHI YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR  DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA? TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN FATA NE, KO INFECTION? KO KUMA SO KI KE FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI,
    SANNAN YAN UWA KUSANI DUK SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA’A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN SUPPLEMENT AKWAI WASU KA’IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO*

    Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu.

    👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin* su.
    *1 Supplements na gyaran jiki*

    *2 Supplements na gyaran gashi*

    *3 Supplements mai da* *tsohuwa yarinya anti aging*

    *4 Supplements na karawa* *fata kyau da sheki  glowing skin*

    *5 Supplements na masu ciwon jiki da stress

    *6 Supplements na masu ciki, da masu shayarwa*

    *7 Supplements na masu  shayarwa*

    *8 Supplements na tsofaffi*

    *9 Supplements na karin ni’ima da tighteningn*

    *10 Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*

    *11 Supplements na gyaran* *nono da mazaunai breast/hips*

    *12 Supplements na gyaran* *HQ ciki da waje*

    *13 Supplements na rage* *tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
    *14Supplement na whitening/glowing skin*

    *15 Supplement for Acne, dark spots remover*

    Da duk wasu nau’in supplement da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158

     

    https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
    *Wai ina da ku fans, ace haryanzu ban haɗa 1k subscribers a channel ɗina ba, anya akwai amana kuwa😒*

    Ku yi subscribing YouTube channel ɗin
    @Cool Hausa Novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro.

     

     

  • Kanwar Maza 8

    Kanwar Maza 8

    P8

    Da rige-rige Usman da Abdallah suka shigo ɗakin, suna tambayar meyafaru da ruma take wannan uban ihun.
    Kallonta Usman ya yi, ya kalli mama ya ce “Mama meya sameta ne?”

    Mama ta ce “Ku tambayeta mana, ba gata nan a zaune ba”

    Abdallah ya ce “Ke menene?”

    Nuna masa hannunta ta yi, tana sake fashewa da wani uban kukan.

    “Wannan ledar ta meye haka a hannunki, kamar wata miskiniya”

    Ɓare baki tayi, ta cigaba da kuka iya ƙarfinta.

    “Dalla ki rufewa mutane baki, kiyi mana bayanin menene?” Usman ya daka mata tsawa.

    “Ba mama ce ba”

    “Me maman tayi?”

    “Ta yi mini lallen tsofaffi wai tsohuwa ta faɗa kwata ina bacci, wallahi dariya za ayi mini idan aka ganni da shi”.

    “Kuma saboda baki da mutunci, ki ke mana wannan uban ihun da Asubar nan, ke dai ba zaki yi hankali ba ko?”

    “Wallahi mama ba ta sona, ban san meyasa ta tsaneni ba, wayyo Allah na”

    Abdallah ya ce “Allah ya ƙara, a wannan shegen baccin naki, har aka yi miki lallen baki sani ba”.

    Mama ta ce “Ki tashi ki kwance lallen nan kiyi salla”.

    Ko motsi ruma ba ta yi ba balle ta tashi.

    Abdallah ya ce “Wai wane irin lalle ne tsohuwa ta faɗa kwatar ne?”

    Cikin kuka ruma ta ce “Irin fa wanda mama take yi a ƙafarta”

    Dariya ce ta ƙwacewa Abdallah, ya ce “Haba mama, ya zaki yi mana haka?”

    Mama ta ce “Hukunta ta nayi, duk rashin jin da take yi ba ta zaci ina da hanyar hukunta ta ba, na bada kuɗi ayi mata abin arziki na zamani, amma taƙi zama, ai da ni ki ke zancen, kuma ajima da kaina zan kai ki kitso zane huɗu za ayi miki”.

    Sosai ruma take kuka, Usman kuwa ficewa yayi ya cigaba da sabgarsa, Abdallah ne ya kaita bakin rariya, ya tayata ya cire ta wanke, aikuwa hannunnan yayi jawur, lalle ya kwanta ɗoɗar hannunta da ƙafarta.

    Da gari yayi haske kuwa, Huzaifa ya ga lallen rumaisa, ya zauna ya sakata a gaba ya dinga yi mata dariya, har da kifawa, wai hannunta kamar kuturwa.

    Ko Abincin safe ruma ba ta ci ba, sai kuka da goge hawaye, wajen ƙarfe goma na safe, mama ta sakata a gaba zuwa gidan kitso.

    Kamar yadda mama ta faɗa, kitson hannu biyu aka yiwa ruma, gashi ta sha azaba a wurin mai kitson, saboda da ta ƙi tsayawa, mama na dukanta, matar kuma ta matse mata kai a tsakanin cinyoyinta, ga kitson azabar zafi tamkar za a zaro ƙwaƙwalwarta saboda yadda matar ke jan gashin.
    Ko da aka gama kitson, ruma ta haɗa gumi ga hawaye da majina saboda azabar zafi, mama ta sakata a gaba suka tafi gida.

    Ruma da ta kalli hannunta ranta yake ɓaci, saboda hannun ganinsa take kamar ba nata ba.

    Har ana gobe salla ruma bata farin ciki, ji take ina ma ace an fasa sallar idi wannan shekarar, saboda wannan yankan ƙauna da mama tayi mata.
    Har bata son a aiketa, dan idan ta fita ta ga yara sun sha kitso da ƙunshi, sai ta yi kuka, saboda yadda ta ƙarfi ita aka mayar da ita zamanin mutanen da.
    Yanzu haka tana tafe a hanya, zuwa aiken da mama tayi mata, ta gaji da tafiya ga ɓacin rai, ta samu wuri tayi zamanta a kan wata baranda, tana share hawaye.

    “‘Kukan me ki ke yi ne haka, ba aiken ki aka yi ba?”

    Ta ɗaga kai taga mai maganar, Auwal ne, na makarantar islamiyya da ta yiwa bori rannan.
    Shiru tayi masa tana tura baki.

    “Meyasa ki ke kuka?”

    Miƙewa ta yi tsaye tana faɗin ‘Babu komai”

    Ya ɗan girgiza kai ya ce “Ina Yasir?”

    Cikin ƙunƙuni ta ce masa bata sani ba, tayi wucewarta.
    Mamaki ne ya kama shi, duk in da ta ganshi ko ba zai kulata ba, sai ta yi masa magana, amma yau tayi masa wulaƙanci.

    Aiken da bai fi tayi shi a mintuna ashirin ba, sai da ta shafe awa biyu da rabi, ta koma gida Aliyu sai da ya murɗe mata kunne, saboda yadda ta je ta daɗe.

    Da safiyar salla kuwa, an kai ruwa rana da hajiya ruma kafin tayi wanka, dan cewa ta yi ba zata je idi ba.
    Huzaifa kuwa musamman ya ƙi shiri da wuri, sai ya ga shigar da ruma zata yi yayi mata dariya.

    Ta na kuka, mama ta watso mata wannan atamfa da ta zauna ta dinga kushewa.

    “Mama dan girman Allah ki barni na saka tsofaffin kayana, wallahi bana son kayan nan”.

    “Ni ki ke gayawa ba kya son kayan nan, zaki saka ki wuce ko kuwa?”

    Za ta tsaya gardama Aliyu ya yi mata tsawa, ya ce ta ɗau kayan ta saka su wuce sallar idi.

    Ga lalle dungulmi, ga kaya ɗinkin mutanen farko, ga kai babu kitso mai kyau, ba yari ba sarƙa  koma kamar ‘yar ƙauye.
    Huzaifa kamar ya shiɗe don dariya.

    “Yarinya kin yi kyau kamar bafulatanar ƙauye” Yasir ya yi maganar yana dariya.

    “Babu ruwanka da ni Yasir, zan maka rashin mutunci wallahi”.

    “Na kuma jin bakin ki sai na ɓarara da ke, maza wuce mu tafi” Aliyu yayi Maganar yana nuna mata hanyar fita.

    Usman ne ya miƙo mata sabon hijjabi ya ce “Gashi nan ba dan hakinki ba”.
    Ajiyar zuciya ta yi, ko ba komai hijjabin zai taimaka mata ta rufe wannan buhun ɗinkin, tun da hijjabin dogo ne.

    Karɓa tayi tana yi masa godiya, ta saka suka tafi idi.

    ********

    “Masha Allah, looking take away my beautiful angel” Ammi ta faɗa tana kallon Iman.

    Murmushi iman tayi ta ce “Ammina, an yi salla lafiya”

    “Alhamdilillah my dear, ina fatan dai an yi mini Addu’a”

    Murmushi ta yi ta ce “Ba dole ba Ammina”

    Wata matashiyar budurwa da ke zaune a kan kujera, ta ɗago ta ce “Wai mu Ammi baki ganmu bane?”

    “Na ganku mana”

    “Ai shikenan Ammi, wannan wariyar launin fata tayi yawa, mu shikenan ba za ki dinga kallanmu ba, sai wannan mai kama da bafulatanar dajin” cewar ɗaya yarinyar.

    Ammi ta ce “Kun dai ji kunya, da ku ke kishi da ƙanwarku”

    Iman tayi musu gwalo ta ce “Iya wuya dai, nice ta gaban goshin Ammina”

    ‘Ta mayar da ke ciki, ko a saka ki a zanin goyo a baki Nono, ƙarshen ƙauna”

    Ammi ta girgiza kai ta ce”Allah ya shirye ku, Iman ki je ki shirya direba zai kai ki gidan zinariyar Galadima, ki kai musu Abincin salla”.
    Ɓata fuska Iman tayi ta ce “Ammi”

    Kan ta ƙarasa maganar, Ammi ta ɗora yatsanta a kan lips ɗin ta ta ce “Shhhh, bana son musu, tana ta complain ba kya zuwa” Ɗan gyaɗa kai Iman tayi ta ce “Shikenan Ammi, bari na shirya”

    *****
    “Ke ba zaki ta so ki fara kai tuwon nan ba”
    Ruma ta kwaɓe fuska ta ce “Dan Allah mama ki yi haƙuri, ki bawa su huzaifa su kai wallahi idan na fita dariya za ayi mini”

    “Ni nake aiken ki, ki ke cewa na aiki wani ruma, ni ko ruma?”

    “A’a mama ba haka bane ba, wallahi dariya yara suke yi mini” tayi maganar hawaye na taruwa a idonta”.

    “Tashi ki wuce ki je aiken da aka yi miki” Usman ya daka mata tsawa.

    Jiki na rawa ta tashi, ta ɗau kwanukan da mama ta zuba tuwo, ta fara kai wa.

    A hanya ta haɗu da wasu ‘yan makarantar bokon su, cikin fara’a ɗayar ta ce “Laa ruma, ya ki ke ina kayan sallar ki?”

    Ruma ta kalleta ta ce “Ji masifa, to ba ni da su, ba a ɗinka mini ba”

    “Daga tambaya sai masifa?”

    “Eh, ina ruwanki da ina kayan salla na, tsirara ki ka ganni?” tayi maganar tana saye hannun ta a cikin hijjabi.

    “Kutmelesi, ruma meye wannan a ƙafarki?” Gaba ɗaya suka kalli ƙafar ruma, da take sanye da silifas ɗan madina, ga ƙafa tayi maroon da lalle, kasancewar ruma ba  iya ɗaurin zani ta yi ba, zanin ya ɗage har ƙwaurinta, kuma hijjabin bai gama rufe ƙafar ba.

    “Kutmelesi, wane irin lalle aka yi miki, lallai mai lallen nan ta cuceki, kut kamar ƙafar tsohuwa”

    Dariya yaran suka kwashe da ita suna sake leƙa ƙafarta.
    Cikin takaici, ta juya zata tafi, amma wata zaƙaƙurar yarinya, ta biyo ruma tana ɗage mata zani.
    Mai jiran ƙiris ya samu a sarari, tuni ruma ta yi watsi da kwanuka, ta fara sana’ar ta ta dambe.
    Kasancewar a ƙule take dama, ta rasa in da zata sauke fushinta, dan haka ta zage ta kama yarinyar nan ta dinga jibagarta kamar Allah ya aikota.
    Suna cikin damben Allah ya bawa yarinyar sa’ar ketawa ruma hijjabi, hakan ya ƙara tunzura ruman, ta danne yarinyar tana duka.

    “Wannan yarinya an yi jarababbiya, duk in da ta tsuguna sai dambe, sai ka ce annoba” cewar wani mai awo a gefe, da bai raba su ba sai zance.

    Ɗagowa ta yi cikin masifa ta ce “Wallahi ni ba annoba bace ba”

    Ta duƙa ta cigaba da dambenta.  ji tayi an yi sama da ita, ta fara kokowar ƙwacewa tana kai duka.

    “Zaki nutsu ko sai na kakkarya ki” yaya Aliyu ne ya tsare ta da ido.

    “Dama abin da ta aiko ki kenan?” Ta yi shiru tare da sunkuyar da kai.

    “wuce mu tafi, dage uwar faɗa”

    Haka ta kwashi kwanukan, da yagaggen hijjabinta a hannu ya tasa ta a gaba, zuwa gida.

    Mama na ganin ruma ta shigo tare da Aliyu, a yadda ta shigo kawai mama ta gane halin ta je ta gwada a waje.

    “Damben ki ka je ki ka yi kenan ko, mara kintsi?”

    Wage baki ruma tayi zata fara yiwa mama bayani, amma mama ta katseta ta ce “Ban tambayeki ba ruma, ki je ji yi tayi, bakin mutane kawai ya ishe ki”

    Gefe ta koma ta zauna, tana jin yadda ba ta gamsu da dukan da ta yiwa Hauwwa ba, saboda dariyar da suka yi mata.

    Yaya Umar ne ya fito daga ɗakin su, cikin wata dakakkiyar shadda dark blue, ya karya hula sai ƙamshi yake zubawa.
    Tsuruu ruma ta yi da ido, tana jiran ya sauke mata masifa, tun da ya ji ance ta yi dambe.

    Nufota ya yi, ita kuma ta ƙura masa ido ko ƙiftawa ba ta yi.

    Ya kalleta ya ce “Na canza miki ne?”

    Ta girgiza kai ta ce “A’a ka yi kyau ne”

    Murmushi ya yi, ya miƙa mata leda ya ce “Je ki ka gwada wannan” da sauri ta tashi, ba tare da sanin meye a ciki ba ta karɓa ta shiga ɗaki.

    Doguwar riga ce ta shadda kalar kayansa, da mayafi da sabon takalmi da yari da sarƙa.
    Ko da ta saka ta fito ba ƙaramin kyau ta yi ba.

    “Mama kin ganni, na yi kyau”

    Aliyu ya ce “Saboda son kai, shine ku ka yi kaya iri ɗaya babu ko labari”

    Cikin tsananin farin ciki ta ce “Yaya Ussy, kalleni dan Allah na yi kyau?”

    “Eh to, babu laifi sai ki ka zama kamar budurwa, duk da ƙwaila ce”.

    Cikin tsananin farin ciki, ta faɗa jikin yaya Umar tana murna “Yaya na gode sosai, Allah ya saka maka da alkhairi ya sa ka gama da duniya lafiya”

    Ganin yadda take murna ya sanya shi yin murmushi na gefen baki ya ce “Allah ya sa ki daina rashin ji”.

    “Iyee, lallai mai sunan Baba, ni sai ka haɗani da atamfa kala uku, amma kai da ƙanwarka ka yi muku kaya iri ɗaya, wato an fi son ta a kaina” mama tayi maganar cikin sigar wasa.

    Murmushi ya yi, dan ya san halin mama da barkwanci wasu lokutan.

    Mama ta shiga ɗaki, ta fito da wata ƙatuwar leda, ta miƙawa ruma ta ce “Gashi nan, ba dan halinki ba, kayayakin da suka yi miki ne, na wannan sallar naƙi nuna miki dan in hora ki”

    Rikicewa ruma tayi, dama suna yi mata ɗinke-ɗinke, amma sallar bana bata san sun yi mata ba, dan a ƙalla ta tashi da kaya ku san dozen, banda hijjabai da abun hannu da sauransu.

    “Wayyo Allahna, dama kuna so na haka? Duk nawa ne wannan mama kin ga fa duk nawa ne”

    Gaba daya suka kewaye ta suna murmushi, ganin yadda ta rikice tana murna.

    Bin su ta dinga yi ɗaya bayan ɗaya tana yi musu godiya, tana zuwa kan Huzaifa ya wani maze ya ce ‘Kar ki damu, wannan fa bakomai bane ba, idan har zaki dinga biyayya”.

    “Ba zan yi biyayyar ba, na san ma ba uwar da ka saya mini, duk gidan nan waye ya kai ka talauci da son banza?”

    “Laaaa, ke fa ba a abin arziki da ke ko?”

    “A’a yi haƙuri mama, shi ɗin ne zai ɓata mini rai, yanzu a cigaba da zuzzuba tuwon ina kaiwa, amma wallahi duk in da na san ba za a bani kuɗi ba, sai dai Yasir ko Huzaifa su kai”

    Haka tayi ta rabon Abinci cikin annashuwa, gidan da aka bata kuɗi tayi ta murna, idan ba a baya ba tayi ta jin haushi.

    ********
    Ba zata iya ƙayyade rabonta da gidan nan ba, dan haka ta ɗaga kai take ta na kallon sauye-sauyen da aka yi a gidan.
    Ya ƙawatu, duk da ginin yana nan a yadda yake, amma an yi wa gidan gyara sosai.
    Da haka ta ƙarasa cikin ƙaton falon da ke cikin gidan.

    Hadimai ne ke ta kaiwa suna komowa a cikin tangamemen falon, suna aikace-aikace.

    Ɗaya daga cikin hadiman ce ta kalli Iman da fara’a ta ce “Maraba da zuwa”.

    Iman ta ce “Yauwwa sannunku da aiki, Ummma fa?”.

    “Tana cikin turaka, bari ayi miki iso”

    Babu jimawa hadimar ta fito, ta kalli Iman ta ce “Bisimillah, ta ce ki shiga”

    Bayan hadimar Iman ta bi, zuwa turakar Ummma.
    Shigarsu ɗakin ke da wuya, gaban Iman ya faɗi, bisa tozali da mutanen da ba ta son ko haɗa hanya da su, ba dan jinin Ummma bane su, to tabbas da kai tsaye zata iya cewa mutanen da ba ta ƙauna.

    Faɗaɗa murmushi Ummma tayi ta ce “Masha Allah, Iman dama talaka na ganinki?”

    Murmushin yaƙe iman ta ƙaƙalo, ta durƙusa a kan gwiwoyinta tana gaida Ummma.

    Cikin mutuntawa Ummma ta amaa mata, tare da tambayarta ya Ammi.

    “Hajiya Iman, manya manyan ‘ya’ya a gidan Galadima, ya kike ya school?” cewar wata matashiya da ke zaune a gefen Ummma.

    Ko ba a gaya mata ba, ta san da biyu budurwar ta yi wannan maganar, ta dake ta ce “Lafiya lau Anty Soafy, an yi salla lafiya?”

    “Hmm lafiya lau, irin wannan ado haka, Ummma wannan leshin kamar irin sa Khairiyya ta saka ranar kamunta ko?” Tayi maganar tana ƙarewa Iman kallo.

    Umma ta ce “Eh irinsa ne”

    “Wow, it worth 120k fa, lallai autar gidan Galadima, kin riƙe wuta”.

    Iman jin ta take tamkar a kan wuta, dan haka a gurguje ta ce “Ummma dama abincin salla ne, Ammi ta ce na kawo miki, kuma nazo mu gaisa, bari na tafi”.

    “Kai Iman tun da wur haka, ke dai ba kya son mutane, shikenan bari na baki barka da salla”.

    “A’a Umma, ai na girma da barka da salla” iman tayi maganar tana miƙewa .

    “Ƙaniyarki, tsaya ki karɓa mana” girgiza kai iman tayi, ta fice daga ɗakin da sauri.

    Har ta kai tsakiyar falon, ta ji an riƙe mata jaka.
    Ta waiwayo tana kallon wadda ta riƙeta.

    “Duk na san kin ci kin ta da kai, Ammi tana ji dake, na san kina da kuɗi baki rasa komai ba, amma yakamata ki karɓa tun da kin san baki da gado a cikin dukiyar gidan Galadima?”

    Cikin rauni Iman ta ce “Anty Soafy me kuma ya kawo wannan maganar?”

    Cikin ko in kula Soafy ta ce “Yau aka fara gaya miki irin wannan maganar ne, ai gara a dinga yi ana tuna miki, ko ba haka ba?” Ta fizgi jakar iman, ta saka mata kuɗin, ta saƙala mata jakar a kafaɗarta ta koma ciki.

    Gwiwa a saɓule, iman ta nufi fita daga falon, tuni idanunta suka cika da hawaye, sai dai tana fitowa ya sha gabanta, ya ƙureta da idanuwansa.

    Ƙoƙarin ratsewa take ta wuce, amma ya ce “Me ta ce miki ne, har ta saka ki kuka?”

    Girgiza masa kai tayi alamar bakomai.

    Yayi murmushin gefen baki ya ce “Anyway, kin yi kyau sosai a outfit ɗin nan, ashe yayanki yana Saudiyya babu ko sallama?”.

    “Uncle J, am sorry sauri nake, Ammi na jirana” daga haka ta wuce ta bar shi a wurin a tsaye.

    **********

    Zuwa yamma mama ta saka ruma a gaba sai sa ta cire shaddar nan, dan idan ta bar ruma da ita sai shaddar ta fita daga hayyacinta.

    Kwanukan da aka ɓata, Yasir ya tattara yana wankewa, mama ta ce “Ke, shiga ɗakinsu ki dudduba mini idan da kwanukana, cokula ko kofi, duk ki fito mini da su, dan na san hali, sai a kai mini kwano ɗaki a ƙi fito da shi”
    Ruma ta tashi ta nufi ɗakin samarin nan, ba tare da ko sallama ba.
    Usman ne a kwance yana waya, kuma da alama da mace yake wayar.
    Buɗe baki tayi, ta tsaya tana kallonsa. Zumbur ya tashi zaune, ya katse wayar ya ajiye ya haɗe rai ya ce “Zo nan” ba musu ta ƙarasa in da yake.

    “Me ki ka ji?”

    Ta ce “A ina?”

    “Ina tambayarki kina tambayata? Nace me ki ka ji?”

    “Wallahi ban ji komai ba, kawai dai na ji ka ce…..” Sai kuma ta yi shiru.

    “Ba zaki faɗa ba sai na taka ki?”

    Ta tura baki sannan ta ce “Na ji ka ce, wai kwalliyar ta tayi kyau, kamar farin wata”.

    “Sai kuma me?”

    “Shikenan na ji wallahi ”

    “To na rantse da girman Allah, idan ki ka sake ki ka faɗa, wallahi sai na yi miki dukan tsiya, ƙanwar abokina ce ba wata ba”

    “To ai ni dama ban ce zan faɗa ba, mama ce ta aikoni” daga haka ta shiga duddubawa mama kwanukanta.

    Aikuwa ruma ta fito da kwanuka a hannuta tana faɗin mama “Kin ga kofin ki, an sha fura a ciki sha zumamu ya siɗe miki kofi tas, har ɓera ya fara ci. Kin ga plate ɗin ki har da sauran alalar da ki ka yi tun sati biyu da suka wuce”.

    Yasir ya ce “To munafuka, uban waye ya saka ki wannan sharhin?”

    Mama ta ce”Ai ba ƙarya ta yi ba, ku yi ta kwasar mini kwanuka kuna kaiwa ɗakin ku, sai na bi na tsinto abina, ƙazaman banza kawai”

    Mama na tsaka da mitar sai ga Aliyu ya shigo, ya ce “Ina ruma”

    Ta ce “Gani”

    “Yo sauri, abokaina ne na filin ball suke tambayata kina ina, shi ne suka biyo ku gaisa, saura kiyi wani haukan da zaki zubar mini da mutunci “.

    Murmushi ta yi ta ce”A’a ba zan zubar maka da mutunci ba, bari na sako gyalena”

    Yana maganar ya fice, Huzaifa ya ce “Mama ke ba a zo gaishe ki ba, sai wannan yarinyar lallai ruma”.

    Ta fito daga ɗakin mama da sauri, ta kalli Huzaifa ta ce “Ka yi mini Addu6, Allah ya sa su bani kuɗi” tana gaya masa ta kwasa da gudu ta fita waje.

    Da fari gaishe su tayi kamar nutsatsiya, suka amsa mata cikin mutuntawa.

    “Ya makaranta ya rikici2?”

    Ta ce “Makaranta lafiya ƙalau, amma ni bana rikici” suka din ga jan ruma da hira ita kuma tana zuba, Aliyu sai hararta yake amma ta cigaba da zuba.

    Dariya suka dinga yi mata, suka babbata barka da salla, ko ɗan cewa ba zata karɓa ɗin nan ba tayi ba, zuruf ta miƙa hannu ta karɓe tana godiya.
    Wani mugun kallo yake wa ruma, amma ko saurararsa ba tayi ba.

    Ta duba a cikin kuɗin da aka bata, akwai ɗari biyu da ta tsufa sosai, ta kalli wanda ya bata ya ce “Ɗan uwanmu ɗan canza mini wannan, ba zata karɓu ba” buɗe baki Aliyu ya yi yana bin ruma da kallo.

    Aikuwa ya karɓa ya canza mata wata, ta ce ta gode ta shige gida.

    “Mama kin ga abokan yaya Aliyu sun bani, kuma sun ce suna gaishe ki”

    Mama ta ce “To madalla”

    “Mama gashi ki ajiye mini, ki ɗora da lissafi, idan kin manta ni ina sane da lissafin, dan Allah mama kar na zo karɓar kuɗina ki fara ce mini, abubuwan da ki ke mini ba da kuɗina ki ke yi mini ba, wallahi mama da za ayi lissafi ban san iya adadin kuɗin da nake bin ki ba”

    Cikin gatse mama ta ce “To Anty ruma, ki zauna ki lissafa duk kuɗin da ki ke bina, na biyaki”

    “Dan Allah mama da gaske ki ke?”

    “Eh mana” murna ta dinga yi tana cewa ‘Ai mama kuɗin da nake binki, sai ma zauna musamman na yi lissafi, tsaf sai na zama attajira da kuɗin nan, unguwar da muke zuwa a bani kuɗi ai da yawa”

    Yasir ya ce “Ba zaki taɓa hankali ba”.

    Aliyu ne ya shigo rai a ɓace yana hararar ruma.
    Kawar da kanta tayi gefe taƙi kallonsa.

    “Dole ki kawar da kai mana, yarinyar nan ana bata kuɗi ta karɓe, wai har da cewa wai wata ba zata karɓu ba, da yake ke ki ka basu ajiya”

    “Yaya ba kyau mayar da hannun kyauta baya fa”

    “Zaki mini shiru, ko sai na mareki, mara kai kawai”

    A ranta ta ce “Ohoo dai, tun da Allah ya sa na karɓa”.

    Bayan sallar isha’i yaya Umar ya dawo, duk sun daddawo suna gida, ana ta hira.
    Ruma tayi gyaran murya, ta kalli Yaya Usman ta ce “Mama kin san me?”

    Mama ta ce “A’a”.

    Usman ya zubo mata ido, kowa ya yi shiru yana sauraron wani shirmen zata faɗa.

    Ayshercool
    08081012243

    (INCLUDE ME IN YOUR PRAYERS PLEASE 🙏)
    [05/07, 5:40 pm] JAKADIYAR AREWA:                     ƘANWAR MAZA
    Na Aisha Adam (Ayshercool)

    MIKIYA WRITER’S ASSOCIATES

    https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

    Ku yi subscribing  YouTube channel ɗin
    @Cool Hausa Novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro.

  • Kanwar Maza 9

    Kanwar Maza 9

    P9

    Wani irin kallo Usman yake mata, amma ta basar ta ce “Mama kin san me yaya Usman ya yi?”

    Mama ta ce “A a sai kin faɗa”

    Usman ya ce”Haka muka yi da ke ruma?”

    “Oho ni dai bana munafurci da rashin gaskiya, duk abin da aka yi mama bata nan sai na gaya mata, ba zan ga ana ba dai-dai ba mama bata sani ba na yi shiru”.

    Kamar ya yi kuka ya ce”Amma haka muka yi da ke?”

    Mama ta ce “Gaya mini ina jin ki”

    Ruma ta kalli Usman ta ce “Sai dai ka yi haƙuri fa, amma wallahi sai na faɗa a gaban kowa da kowa, ba zan zuba ido ana abin da ba dai-dai ba”

    Ba dan ya san idan ya yinƙura zai yi mata wani abu mama zata hana ba, da sai ya kife Ruma da mari, ya san idan ta ɗaga maganar nan akwai damuwa, zai sha faɗa da mita.
    Uwa uba ga Yaya Umar a zaune a wurin, kuma ba shi da tabbacin iya abin da ruma ta gaya masa ta ji, shi kaɗai ɗin ta ji, dan kawai ɗaga kai ya yi ya ganta a tsaye lokacin da yake wayar.

    Ta gyara zamanta sannan ta ce “Ɗazu, da ki ka aikeni kai tuwo gidan mai ƙuli, na ganshi a ƙofar gidan su wannan abokin nasa Yahaya, shi da abokansa sun dawo daga idi, ko gida ba su zo ba, ya zauna an fito da abinci sun haɗu suna ci, kuma kin hana hakan”

    Ajiyar zuciya ya yi, yana hamdala da ba wancan zancen ta yi ba.

    Mama ta ce “To wannan abun ne ki ke ta zuzutawa, ai shima ya zo ya ɗau abinci ya fita da shi sun ci tare”

    “To mama sai aka ce ya je ya zauna a ƙofar gida yana cin abinci ai rashin kamun kai ne, kuma ke ki ka ce rashin kamun kai ne fa”.

    Mama ta ce “To shikenan, za a yi masa faɗa”.

    “To mama kiyi masa faɗan mana yanzu”

    A fusace ya ce “Ke wai ni sa’an ki ne?”

    Umar ya ce “Maganinku kenan da ku ke wasa da ita”

    Can ta sake gyara zama ta kalli mama ta ce “Mama, kin san wani abu?”

    “Ke na gaji da wannan shirmen naki fa” mama ta faɗa cikin ƙosawa.

    “Mama ba shirme zan ba, ɗazu na ga Habiba a masallacin idi, da tsofaffin kaya na ganta”.

    “To ina ruwanki? Kin ga ina rabaki da sabgar munafurci amma ba zaki dai na ba ko?”

    Jiki a sanyaye ruma ta girgiza kai ta ce “Mama so nake a bata kaya ɗaya a cikin kayana” gaba ɗaya juyowa suka yi suna kallon ta jin abin da ta ce.

    Huzaifa ya ce “Kina da hankali kuwa?”

    “Amma dai ka san tun da nake ni ba mahaukaciya ba ce ko? Mama dan Allah a bata ita ma ta saka sabon kaya”

    “Rufewa mutane baki, mara zuciya nan babarta ta zo ta ciwa mutane mutunci, amma ki ka cigaba da shishshige mata, ba za a bayar ba ɗin” Aliyu ya faɗa yana zaro ido.

    Mama ta girgiza masa kai, ta dubi ruma ta ce “Allah ya kaimu gobe, sai ki zaɓi wanda zaki batan”

    Murmushi ruma ta yi ta ce “Na gode mama, Allah ya saka da alkhairi, to zaki ɗan zuba mini naman kazar ita ma na kai mata ta ci, na san su basu yanka kaza ba”.

    Yasir ya ce “Dama ta yaya zasu yanka, wannan babar ta su tana kiwon kaji kamar su kasheta, amma ba zata yanka su ci ba, bayan talauci har da son zuciya”

    “Ka daina zagar mini babar ƙawa dan Allah”

    Mama ta ce “Kin ga, tashi ki wuce ki je ki kwanta”
    Ta miƙe ta shige ɗaki, mama ta mayar da idonta kan Aliyu ta ce “Aliyu, kar ku hora yarinyar nan a kan halin rowa, duk rashin jin ta tana da tausayi da son taimako, idan har abin da za ta yi bai saɓawa shari’a ba ku ƙyaleta”

    Aliyu ya jinjina kai. Ruma kuwa ji take kamar ta janyo washegari, ta kai wa habiba wannan kayan, ita ma ta saka ta ji daɗi.

    Washegari da wuri ruma ta yi wanka, ta yi kwalliyar salla da ɗaya daga cikin kayanta, ta zauna ta ɗaukarwa Habiba set ɗaya na atamfa har da ribbon da abin hannu.
    Mama bata hanata ba, ta ƙulle mata nama ta bata ta kai wa Habiban.
    Har zata ɗauka ta fita, ta tsaya ta ce “Mama, dan Allah idan ta yi kwalliyar zamu je gidan ‘yan ajinmu mu yi wasa”.

    Mama ta ɗan ɓata fuska ta ce “Amma dai kin san babna son wannan abun ko, ba na son yawace-yawace”

    Ta ɗan marairaice ta ce “Dan Allah mama, kin san bana yawo, daga aike sai makaranta, yanzu fa salla ce”.

    “Shikenan, na ji, saura kuma ki je ki zauna sai an nemo ki, ina da ina zaku je?”

    Ruma ta lissafa mata, mama ta yi ajiyar zuciya ta ce”Yanzu ƙarfe goma da rabi, kar ki wuce sha biyu, idan ki ka wuce abin da zai zo biyo baya ba zai yi miki daɗi ba”.

    Cikin murna ta ce “Mama da wuri zan dawo in sha Allah ” ta yi waje ta na murmushi.

    Kai tsaye gidansu Habiba ta nufa, ko da ta je ta yi ta sallama, shiru ba a amsa ba.
    Tsayawa ta yi a tsakar gidan ta cigaba da sallama.
    Sani ne ya leƙo yana amsawa, yana ganin ruma yayi saroro ya ce “Ke uban me ki ka zo yi mana a gida?”

    Hararsa ta yi ta ce “To ina ruwanka ai ba wurinka na zo ba, ba yayana yayi maka tsakani da ni ba, babu ni babu ba, ko kuma na kira shi, ya zo ya ƙara kumbura maka fuska”

    Tana tsaka da maganar, sai ga babar Habiba ta fito daga banɗaki, tana ganin ruma ta tsuke fuska ta ce”Ke me ki ka zo yi mini a gida?”

    “Gurin Habiba na zo”

    “Da izinin wa ki ka zo wurin Habiban?”

    Habiba ce ta fito daga ɗaki, hannunta riƙe da kwanon tuwo da miyar kuka, tana ganin ruma ta ce “Laaa ruma, kin dai na zuwa makarantar allo ”

    Ruma ta ce “Ba na ganki a masallacin idi ba ki ka ƙi kulani”

    Habiba ta ce “Wallahi ruma ban ganki bane ba? Ya salla?”

    “Lafiya lau, wurin ki na zo, zo ki ji?”

    Mamaki ya cika babar su Habiba, ta riƙe haɓa ta ce “Habiba, wato cigaba da shiga sabgar yarinyar nan ki ka yi ko?”

    Habiba ta girgiza kai ta ce “Wallahi Ummanmu ba kulata nake yi ba, na daɗe ma bamu haɗu ba”.

    Ruma ta miƙowa Habiba leda ta ce “Kawo miki na yi, ki zo ki karɓa ki gani”
    Babu musu ta ƙarasa ta karɓi ledar, taga ɗinkakkiyar atamfa ga abin hannu da ribbon, sai kuma ƙullin nama.

    Habiba ta ce “Ruma wannan na waye?”

    “Naki ne, in gaya miki, kayan salla na  kala goma sha biyu da hijjabai, har da abin hannu da sarƙa, shine na ce bari na kawo miki ɗaya, ki saka mu je yawon salla”.

    Babar su Habiba ta ce “Ba ta so ba zata karɓa ba, bana son shishshigi, ba ta kayanta ce muku aka yi tana buƙata? Ita ma tana da kayan salla”

    Idon Habiba ya cika da hawaye ta ce “Wallahi Umma bani da kayan salla, ina son kayan dan Allah ki bar ni na saka”.

    Ruma ta ce “Dan Allah Umma ki bari ta saka, mun shirya ai mun dai na faɗa, dan Allah ki bari ta saka”

    Umma ta kalli yadda Habiba ta rungume kaya tana kuka, wai tana so, haka ta ƙyaleta. Habiba ta shiga ɗaki ta saka kayan, aikuwa tamkar dan ita aka ɗinka su suka yi mata kyau.
    Sani ya din ga ce wa habiba mara zuciya.

    Abin ka da ƙuruciya, tuni habiba ta shirya a cikin kayan, duk da babar Habiba na jin haushin ruma, hakan bai hanata rawar jiki wurin raba naman kazar da ruma ta kawo ba, fan kuwa an daɗe ba a haɗu ba.
    Daga haka suka fita nasu yawo.

    Tamkar awakai haka suka dinga yawo, kusfa kusfa gidajen ƙawayensu, wasu a haɗu a rabu da su ƙalau, wasu kuma a ƙare da faɗa. Ruma ba ta tashi tuna kashedin mama ba, sai bayan azahar tana ta gararanbarta a gari.

    A suwkane ta nufo gida, tana ta tunanin yadda za ta kare kanta a wurin mama, dan ta san zuwa yanzu ana can ana nemanta kamar kuɗin guziri.

    Yaya Usman ta hango a tsaye a jikin wata mota, ya sha kwalliya, shi da abokansa, da alama fita za su yi.
    Da gudu ta ƙarasa in da yake tsaye ta ce “Yaya ussy, me ka ke yi a nan?”

    “Ban sani ba, wuce ki tafi gida, ki kai aiken da aka yi miki” abin da ya faɗa ne ya sanya ta fuskanci kamar mama ba ta neme ta ba, dan haka ta ce “Dan Allah ina zaka?”.

    “Zamu ɗan fita chilling ne”

    “Meye chilling kuma?”

    Ya haɗe rai ya ce “Cewa na yi fa ki tafi gida ko?”

    “Dan Allah ka yi haƙuri, zan bika dan Allah”

    “Ke wai ni sa’an wasanki ne? Ba zaki wuce ki tafi gida ba?”

    Ta sake marairaice wa ta ce “Dan Allah Yaya”

    Riƙe rigarsa tayi tana kallonsa kamar za ta yi kuka. Tunawa ya yi da haushin ƙin tafiya da ita zai iya sanyawa ta tona masa asiri.

    Yayi ƙasa da murya ya ce “To ki je ki tambayo mama, idan ta yarda sai mu tafi”

    “Wallahi na san idan na tafi, tafiya zaka yi”

    “Shegiya sai ka ce mayya, idan na tafi da ke a ina zan saka ki motar ba space” yayi maganar a ƙule.

    “Sai na zauna a cinyarka” duk yadda ya so ya yakice ruma, taƙi ta nace, gashi ya san zai sha kunya, idan har ruma ta tona masa asirin yana waya da budurwa, dan ya san sai dai ya kasheta bayan ta faɗa zare idonsa ba zai hanata faɗar abin da ta yi niyya ba.

    Haka ya sakata a motar, dama ta abokinsu ce, ita kaɗai a cikin maza, sai zaginta yake, amma ko a jikinta, ya sakata a gefensa.

    Abokansa sai dariya suke masa, suna “Ka ga Ƙanwar maza, suke mulkin amma dole a biki ko ba a so” ba wanda ta kula a cikinsu suka tafi.

    Wurin shaƙatawa suka je, duk abin da suka ci sai da suka sayawa ruma ita ma ta ci, da ta ji ta ƙoshi ta kalli Usman ta ce “Yaya ussy, a samo leda a ɗaure mini sauran na tafi da shi gida”

    “Saboda kowa ma bashi da hankali kamar ke? Wallahi baki isa ba” ba dan ya ji daɗin fitar ba, ya azalzali abokansa suka koma gida, saboda yadda ruman ke ta zubar masa da mutunci a idon abokansa.

    Ko da suka je gida, mama a kiɗime take, tun sha biyu ake nemanta ba a ganta ba.

    Bin su da kallo mama ta yi, ta dubi Usman ta ce “A ina ka ganota?”

    “Nima a hanya na ganta bayan la’asar, zamu fita da abokaina, ta nace sai ta bini, na kira Aliyu a waya na gaya masa muka tafi da ita”.

    “Ku ka je ina?”

    “Wurin wani cin abinci ne, ni da su Isma’il ne”

    “Kuma ita kaɗai a cikin maza Usman, ka san tun yaushe yarinyar nan ba ta gidan nan, ka ga tashin hankalin da na shiga kuwa? Wallahi yau sai kin ci ubanki”
    Abdallah ya ce “Wallahi mama ko ba ki daketa ba, sai na zaneta yau, ki yi mata bugun shekararriyar dawa, yarinyar nan ta ci a bata gado a Asibitin mahaukata”.
    Mama a tsananin fusace ta janyo ruma, ta din ga turjewa tana ihu, mama ta zaro bulugari ta dinga bugunta da shi tana kurma ihu tana neman taimako.

    Mama ba ta saba tarbiyya da duka ba, amma idan ta kai bango jikin mutum yana gaya masa, sai da Usman ya ƙwaci ruma da ƙyar a hannun mama.

    Tun daga ranar, mama ta ce ba zata bata sauran kayan sallar baz gashi an aiko mata da kayan salla daga can garin su, ga dangin mahaifin su ma, sun ɗinko mata kaya, sun aiko mata da su, duk mama ta ce ba zata sake sakawa ba ta gama kwalliyar salla.
    Washegari ta na ji ta na gani mama ta shirya, ta tafi cikin gari, ta bar ruma a gida.

    Gidan duk ya yi mata babu daɗi, sai faɗace-faɗace take da su Yasir.
    Suka gama suka fice suka bar ta a gidan. Ta ji babu daɗi rashin tafiya da ita da mama ba ta yi ba, gaji da zama ta tashi tana neman abun yi.
    Ɗakin ‘yan mazan ta shiga, ta fara gyara musu ta ci karo da shaddar yaya Umar ya saƙaleta.
    Wani tunani ta yi, ta kwaso shaddar ta fito da ita tsakar gida. Ta zuba ruwa a bokiti ta tuttula omo ta zunduma shaddar nan a ciki, ta koma ta cigaba aikin gyaran ɗakin.
    A ƙalla shaddar nan ta kai awa biyu a ruwa, ruma ta fito ta jagwalgwala ta shanya. Ai kuwa shaddar nan gaba ɗaya ta daina wannan shining ɗin da take yi saboda azabar omo.

    Aka jima, ya haɗa wuta a dutsen guga, ta hau goge masa ita.

    Abdallah ne ya dawo, ya tarar da ruma ta duƙufa tana guga.
    Ya tsaya yana ƙoƙarin gane me take gogewa.

    “Wai meye wannan ki ke gogewa haka?”

    Ta ɗago ta kalleshi ta ce “Kayan yaya Umar ne, na ga ya saƙale su a ɗaki, na san wankewa zai yi, shi ne na wanke masa nake goge masa”.

    Abdallah ya ce “Innalillahi wa Innalillahi raji’un, ruma da me ki ka wanke shaddar nan haka?”

    “To za ayi wanki ba da ruwa da omo bane?”

    “Uban waye ya ce miki ana wanke shadda da omo?” Ai suna cikin maganar ruma ta ƙone gaban rigar.

    Dafe kai ta yi ta ce “Innalillahi, na shiga uku, Abdallah ya zan yi na ƙona masa shadda?”

    Abdallah ya ce “Maganinki shegen karambani, kya san mai zaki gaya masa”

    Hannu ruma ta ɗora a ka ta dinga kuka, dan ta san yau kashinta ya bushe, sai yadda Allah ya yi da ita.

    Haka mama ta dawo ta tarar da ita, tana ta uban kuka, Abdallah ya gaya mata abin da ta aikata.

    Cikin kuka ruma ta ce “Dan Allah mama ki bashi haƙuri, yau na san na mutu wallahi, dan Allah mama kar ki bari ya dakeni ko ya saka ni punishing”.

    “Ba ruwana, ai nima ba jin maganata ki ke yi ba”.

    Abu kamar wasa, har bayan la’asar ruma ba ta ci ko Abincin rana ba, sai kuka take yi.

    Huzaifa ya ce “Ni ne mutum na farko da zai sanar da mai sunan Baba wannan taɓargaza da ki ka aikata masa”

    Duk da mama a ƙule take da ita a kan laifin da ta yi mata jiya, amma hakan bai hanata saka ruma ta ci abinci ba, amma ruma taƙi ci sai aikin kuka. Ita kanta mama na tausayawa ruma hukuncin da zata fuskanta a wurin Umar idan ya dawo ya tarar da ɓarna da ta aikata masa, sai dai ita ta janyo kanta, rashin jin ta ya yi yawa.

    Mai sunan Baba bai dawo ba sai bayan sallar magariba, tun da ya shigo ta sake takurewa tana uban kuka.
    Ya dube ta, cikin kakkausar muryarsa ya ce “Kukan me ki ke yi?”

    Huzaifa ya gyara zama, ya wassafa masa ɓarnar da ta aikata.
    Duk da babu isasshen haske a tsakar gidan, ta tsorata da kallon da ya yi mata.

    “Dan Allah yaya ka yi haƙuri, ba a son raina na aikata hakan ba, wallahi kawai niyyata na baka mamaki, na wanke maka na goge maka ban san haka abin zai zama ba”

    Kalmar ta bashi mamaki sai da ta saka Aliyu dariya, ya ce “Lallai kin bashi mamaki kam”

    Yadda ta firgice ne, ya sanya Yasir ya ce “Dan Allah yaya ka yi haƙuri, kuskure ne, tun da tsautsayin nan ya faru ba ta ci Abinci ba”

    “Zaka ɗau hukuncin da zan yi mata kenan?” Yayi maganar ba tare da ya kalli Yasir ba.

    Yasir ya ce “Eh ni ka hukunta ni a madadinta, a tsorace take”

    A ɗan tsawace ya ce “Tashi ki ɗauko mini kayan na gani”

    Sumi-sumi ta tashi ta je ta ɗauko kayan, ta miƙa masa.
    Ya karɓa ya duba, gaba ɗaya kayan sun tashi daga aiki, jikinta sai rawa yake yi.

    “Tun da ki ke na taɓa saka ki wanki?” Ta girgiza kai.

    “To Meyasa ki ka wanke nawa kayan?”

    “So nake nima na yi abin arziki, ban zaci zai zama na tsiya ba”

    Ya girgiza kai ya ce “Zubo mini Abinci” ta tashi tana ta tsuma, ta je ta zubo abinci ta kawo masa tana kallonsa.

    Ya karɓi Abincin, ya ajiye a gabanta ya ce “Ci Abinci”

    Fuska duk hawaye ta ce “Dan Allah ba zaka saka ni kama kunne ba?”

    Ya girgiza mata kai ya ce “Ba zan saka ki ba” yayi maganar yana ɗebo Abincin ya kai bakinta.

    “To ka haƙura?” Ya jinjina mata kai alamar eh.

    “To dan Allah ka yi haƙuri, tsautsayi ne”

    “To, ci abinci” sai a lokacin ta ji ranta ya yi sanyi, har ta fara cin abinci, babu wanda bai yi mamakin yadda mai sunan Baba ya ƙyale ruma ba, basu taɓa kawo zai rabu da ita ba.

    Sai da ta ci ta ƙoshi sannan ta ce “Me sunan Baba”

    “Na’am”

    ‘Dan Allah ka yi haƙuri, zan karɓi kuɗina na wurin mama sai na saya maka wata “murmushin gefen baki ya yi ya ce ‘To Shikenan”.

    Bayan yaya Umar ya fita, Huzaifa ya lallaɓa ya bi ruma ɗaki yana cewa “Ruma, wace addu’a ki ka yiwa mai sunan Baba ya ƙyale ki ne? Zo ki gaya mini”

    Usman ya ce “Wallahi nima na yi mamaki duk ɓarnar nan da ta yi masa ya ƙyaleta”

    Babu wanda ta kula a cikinsu ta kwanta tana yiwa Allah godiya.

    Hidindimun Salla suka wuce, aka koma makaranta, ruma ta koma makaranta, sai dai fafur ta ƙi zaman ajinsu, wai malaminsu baya son ta, wani malam Habibu ɗan mai makarantar ta liƙewa, duk ajin da za shi ya yi ƙari sai ta bishi, gashi ta maƙalewa Auwal, yaya sama yaya ƙasa haka take kiransa saboda yana sayen tsami gaye da goriba ya bata.

    Yanzu ma ‘yan ajin su Yasir suna jiran malam Habibu ya zo yayi musu ƙarin Alqur’ani, sai ga shi ya shigo shi da ruma.
    Yasir yana ganinta ya tsuke fuska, dan tun wancan hansfreen da ta yi masa a gida, ya hanata zuwa ajinsu, amma sai gata.
    Malam Habibu ya zauna, ya ce ta shiga cikin mata ta zauna. Aikuwa ta shiga ta zauna, ta nutsu kamar gaske aka yi ƙarin nan aka idar.
    Aka zo kowa yana biyawa, aka zo kan Yasir shi ma ya biya, sai cewa ta yi ‘Inyee ashe ka na ja, hmm da ba ka iya ba wallahi da sai na faɗa a gida, in ce kai ma baka iya karatu ba”

    Dariya ‘yan ajin suka hau yi suna kallon Yasir, ya sunkuyar da kai yayi mata shiru.

    Kowa ya gama biyawa, ruma ta ce “Malam nima zan karanta”

    Ya ce “To bisimillah”

    Abun mamaki sai ga ruma ta karanta shafi guda, duk da tana yi ana cin gyaranta, amma ta kai shafi guda, ba ƙaramin mamaki ta bawa Yasir ba, yarinyar da ta ce ita gejinta aya biyu kawai.

    Ɗari biyar malam Habibu ya bata, tare da jinjina mata, dan babu wanda bai san ruma ba ta ja ba.
    Da ya kammala ƙarin ya ce ta ta so su tafi, amma ta kalli yadda Yasir ya haɗe rai ta ce “Malam ni ka bar ni a nan ajin”

    Malam Habibu ya ce “To shikenan, duk malamin da ya zo ace masa ruma ajiyata ce, sanna ba ruwan kowa da ita kar a takura mata”

    Suka ce to.

    Yasir kuwa kamar ya zo ya rufeta da duka, dan ba zata taɓa zama shiru ba.

    Ruma ta shige cikin ‘yan mata, suna hirarsu, ita kuma tana shan farar ƙasarta, amma duk tana jin me suke faɗa.

    Yau har aka tashi tana ajin su Yasir, sai da aka tashi ta bar ajin.

    Ta je ta samu tsohuwar da take sayar da kayan yara a a ƙofar makarantar, ya titsiyeta wai sai ta bata farar ƙasa kyauta.
    Duk shegen son kuɗi irin na iya, sai da ta bawa ruma farar ƙasarar nan, saboda shegen surutun ta da nacin tsiya.

    Ta karɓi farar ƙasarta ta yi gida, haryanzu makarantar nan ba ta da ƙawaye, a cewarta ɗaliban ba su yi mata ba, kuma ba komai bane su ɗaliban sa’aninta kowanne ya mayar da hankali a kan karatunsa ne, ita kuwa ruma ‘yar abi yarima a sha kiɗa ce.

    Tun da ta je gida take tafa hannu tana masifa, “Wallahi an mini laifi a gidan nan, kuma sai kowa ya hallara zan faɗi me aka yi mini” jin kowa ya shareta ya ƙi kulata ya sanya ta ce “Mama yanzu dan Allah abin da ake yi mini a gidan nan ya dace?”

    “Da aka yi miki me?”

    “Mama a gabanki ‘ya’yanki suke ce mini ƙwaila, amma baki taɓa hana su ba”

    Mama ta dubeta ta yi murmushi cikin manyance ta ce “To ba ƙwailar bace ba?”

    Ruma ta buɗe baki ta ce “Au mama har da ke?”

    Aliyu ya ce “To meye dan an ce miki ƙwaila, ai ƙwailar ce”

    Ruma ta ce “Kutt, ƙwaila fa wadda ba ta da nono kenan?”

    Aliyu ya ce “Innalillahi wannan gingimemiyar maganar fa”

    Mama ta ce “ke waye ya gaya miki haka?”

    “‘yan ajin su Yasir ne suke faɗa, matan nan ina jin su da kunnen nan nawa, sun zaci bana jin su”

    Mama ta ce “To ke nonon ne da ke da ba za ace miki ƙwaila ba?”

    “Mama gori dai ake yi mini kenan? Sai in je wurin Mai furar nan na bakin hanya, na sayo nonon, na zo na ƙulla a leda na dinga sakawa” cike da takaici mama take bin ruma da kallo, ta ma rasa me zata ce mata. Usman yana tsakar gida, sai ƙyaƙyata dariya yake ƙasa-ƙasa lamarin ƙanwar nan ta su sai Addu’a kawai.

    Aliyu ya ce”Ke da ki ke ƙanwar maza, me zaki yi da wannan abun? Ki yi zamanki a haka ai sai kin fi kyau”

    Ta ce “Kuma fa haka ne” ta cire rigar islamiyyar, daga ita sai vest, ta sinsina rigar ta kuma cewa “Mama, dan Allah yaushe zan fara warin hammata, ina son idan na cire riga na sansana na ji tana ɗan warin nan da ƙamashin turare ”

    “Fitar mini daga ɗaki dan ubanki, shashasha mara alƙibla fita ki bar mini ɗaki”.

     

     

    AYSHERCOOL
    08081012143
    [08/07, 4:58 pm] JAKADIYAR AREWA:                   ƘANWAR MAZA
    Na Aisha Adam (Ayshercool)

    MIKIYA WRITER’S ASSOCIATES

    https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

    Ku yi subscribing  YouTube channel ɗin
    @Cool Hausa Novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro.

    *A TAIMAKA AYI SUBSCRIBING YOUTUBE CHANNEL ƊINA NA COOL HAUSA NOVELS, KO IN KOMA POSTING SAU ƊAYA A SATI 😒*

  • Kanwar Maza 6

    Kanwar Maza 6

    P6

    Iya ƙarfinta take ihu, tana kiciniyar sai ya sauketa, amma yayi burus da ita, sai da ya je soron gida, sannan ya sauketa ya ja hannunta zuwa cikin gidan.

    Aliyu ne a tsakar gida yana yiwa mama wanki, ya ɗago ya kallesu ya ce “Ya dai, ya kake jan ta tana ihu, makarantar fa?”

    Hauzaifa bai amsa masa ya tambaye shi”Mama tana nan?”

    “Eh tana nan” Aliyu ya bashi amsa.

    Jin ihun ruma ne ya sanya mama katse sallar walahar da take yi, ta fito tana tambayar lafiya.
    Hakan yayi dai-dai da fitowar Yaya Umar, shi ma ya yi shirin fita. Duk suka zubo musu ido suna jiran jin ba’asi.

    “Mama wallahi yarinyar nan ba ta da mutunci, daga sakata a makarantar nan ta fara tayar mana da hankali, yaushe yarinyar take da sikila ban sani ba?”.

    Mama ta ɗan yi sororo ta ce “Wace irin sikila kuma?”

    “To haka ta je ta ce wai sikila ce da ita, ta tashi tsaye ma ta ƙi sai a bayana na goyota”

    Yaya Umar ya kalleta ya ce “Ke meya sameki?”

    Cikin in da in da ta ce “Dukana aka yi, kuma wallahi na ji zafi sosai shi ne na ce musu sikila ce da ni, na ga wata ‘yar makarantar bokonmu ba a dukanta saboda sikila ce ita”.

    “Shi ne ki ke yiwa kan ki fatan ciwo saboda baki da hankali, ke dama za a zauna da ke baki yi abin da za a dake ki bane ba, me ki ka yi aka dake ki?” Yayi maganar cikin tsare gida.

    Cikin kuka ta ɗage ƙafar wandonta, shatin bulala ya kwanta a kan fatarta, ta kalli mama ta ce “Mama kin ga fa, dan Allah a cireni wallahi ni ba zan iya makarantar nan ba, wai ban iya karatu ba shi ne aka yi mini wannan dukan, ni wallahi ba zan iya karatun nan ba, ga duka ga karatu mai yawa, da wanne zan ji?”

    Cikin tsawa Yaya Umar ya ce “Wuce mu je makarantar, sai kin ci ubanki yau, ai dama karatu aka turaki ba wasa ba”
    A karo na farko ta yi wa yaya Umar gardama tana kuka, ta riƙe hannun Huzaifa, ta ɓuya a bayansa.

    “Ni nake miki magana ki ke ɓuya a bayansa, ba zaki fito ki wuce ba”

    “Dan girman Allah kayi haƙuri, wallahi idan suka san ƙarya nake, sai sun kusa kashe ni, wallahi duka ake na tashin hankali a makarantar nan” kuka take wiwi kamar wadda aka yiwa mutuwa, mama dai ta kasa magana.
    Huzaifa kuwa janyota ya yi daga bayansa, ya ce Wallahi ba zai kareta ba sai dai ayi mata duk abin da za ayi mata.

    Yaya Sadik ne ya fito daga ɗakinsu, yana zuwa ya ture Umar, ya kamo hannun Rumaisa, ya wuce da ita ɗakin su.

    Suna shiga ya zaunar da ita, shima ya zauna ya ɗan ƙura mata ido sannan ya ce “Auta, meke damunki ne, kullum sai an yi rigima dake an ce ba kya ji, ke ko haushi ba kya ji?”

    Ta girgiza kai ta ce “Wallahi ina jin haushin yadda aka tsane ni kullum ace bana ji”

    “To yanzu meyafaru, har aka dake ki ki ke cewa sikila ce dake? Kin san sikila kuwa meyasa ki ke fatan wannan ciwon?”

    “Gani nayi za a kashe ni da duka, ni bana son a dake ni”.

    “Gaskiya ba ka kyautawa, dan me yarinya za ta yi laifi ka hana a hukunta ta, me kake ƙoƙarin koya mata ne?” Umar yayi maganar a mugun fusace.

    Yaya Sadik ya waiwayo ya kalli Hussainin na sa, ya haɗa hannayensa alamar ban haƙuri ya ce “Tuba muke, zan wa tufkar hanci in sha Allah, on behalf of her, ayi haƙuri gobe in Allah ya kaimu da kaina zan mayar da ita makarantar in basu haƙuri” gajeren tsaki Umar yayi yai waje, babu wanda yake masa katsalandan kamar yadda Abubakar yake yi masa, ya fuskanci idan aka biyewa Yayan nasa ruma tsiyarta zata tsula ba tare da an kwaɓeta ba, da tayi laifi sai ya ce ƙuruciya ce.

    Wunin ranar kowa share ruma yayi, yaya Sadik ne kawai yake kulata, Huzaifa da yasir suka ƙare mata zagi tsaf suka tsangwameta.
    Ko a jikinta, tun da Allah ya sa ba a mayar da ita makarantar an ce ƙarya take ba, hankalinta ya kwanta.
    Washegari Yaya Abubakar da kansa ya rakata makarantar, aka dinga yi mata sannu ana mata ya jiki, ta basar ta dinga amsawa.

    ************

    Sanye yake da fararen kaya ƙal, fuskarsa sanye da fari siririn glashi, taku yake cike da ƙasaita ya biyo wata doguwar baranda.
    Sannu a hankali ya ƙarasa gaban wata ƙatuwar ƙofa, ya sa hannu ya murɗata a hankali. A take ta buɗe wani sassanyan ƙamshi ya daki hancinsa.
    Da sallama ya shiga ya mayar da ƙofar ya kulle, babu kowa a falon sai wata matashiyar budurwa tana saka turaren wuta.
    Amsa masa tayi tare da faɗin “Sannu da zuwa”.

    “Yauwwa ‘yar aikin Ammi, ina ma’aikatan ne ki ke aikin da kan ki?”

    Ta ɗan kalle shi sannan ta ce “Nima ‘yar aikin ce ai” yayi murmushi ya ce “Sorry idan haushi ki ka ji, ina Ammi?”.

    “Bacci take” ta bashi amsa lokacin da take cigaba da saka turaren wuta.

    “Ba kowa kenan?”
    Cikin ƙosawa da tambayoyinsa ta ce “Duk sun tafi makaranta”.

    “Ke me ya hana ki je makarantar?”

    “Ohh God, uncle J am sick shi ya sa ban je ba, Ammi idan kana son ganinta ka dawo an jima, ina fatan zan iya tafiya na gama amsa tambayoyin ka?”

    Ya girgiza kai ya ce “No, saura ɗaya ina yayan ku?”

    Tayi murmushi ta ce”Wannan tambayar ai kai yakamata a yiwa, i don’t know ” daga haka ta bi wata hanya ta bar falon.

    Ya girgiza kai a hankali ya ce “Wannan yarinyar ta fi mai kora shafawa, izzarki tayi yawa”
    Wayarsa ce ta fara ringing, ya zura hannu a aljihunsa ya ciro wayar.

    “Ke nifa kin isheni, ni kaina ban san in da yake ba, anjima kuma kilisa zan fita, zan neme ki amma” daga haka ya kashe wayar, ya saka a aljihunsa ya fice.

    *********
    Ruma ta sha kashedi a wurin su Huzaifa, a kan ta shiga hankalinta a makarantar nan, dan ba ƙaramin girmansu ake gani ba, halinta ba zai sa mutuncinsu ya zube ba.
    Ta cigaba da zuwa makaranta, amma ba ta gane komai, idan Yasir ya zaunar da ita zai koya mata kuma, sai ta ce ita ta gaji ba ta so.

    Ranar wata juma’a da yamma, Abdallah yana ta haɗa kayan miya, za a kai markaɗe, Yasir ya kalleshi ya ce “Abdallah kyanta na ɗau hotonka kana haɗa kayan miyar nan, na je na nunawa yarinyar nan mai awara”.

    Haɗe rai Abdallah ya yi ya ce “A’a mai wake zaka nunawa ba mai awara ba”

    Yasir ya yi dariya ya ce “Zaka ga mai wake, wallahi yarinyar nan ta mato a kan ka, kawai ka nutsu ku daidaita, wallahi shar da kai awararka zaka yi ta ci”

    “Na rantse idan ba ka yi mini shiru ba sai na ɓarar da kai”

    Yasir ya ce “Yaya ba zan ƙoƙari na tayata kafa gwamnatin ta ba, kullum sai ta kyauta mini”.

    Buut Ruma ta fito daga ɗaki ta ce “Yasir yakamata muje ka gabatar mata da ni, na dinga biyawa idan zan je makaranta”.

    Tsaki Yasir ya yi “To munafuka waye ya sako dake, na zaci ma bacci take wallahi ”

    Abdallah ya ce “Wallahi ko da wasa ki ka je, sai na kakkarya ki”.

    “To ni ce maka ma nayi zan je?”

    “Ke dai ki ka sani gulayya” Yasir yayi maganar yana hararta.

    “Wallahi ni ba gulayya ba ce” shareta suka yi suka cigaba da hirarsu, yayin da Ruma ta koma gefe tana naɗar abin da suke faɗa.

    Kamar yadda a islamiyya ruma ba wani ja take ba, haka ma makarantar boko ba uwar da take ganewa sai wasa.
    Ta na cikin top 10 na marasa ganewa a aji, sannan ta farko a sahun marasa ji.
    Yau bayan an taso daga makarantar boko, ta biyo ta hanyar da lambun mai unguwa yake. Ƙaton lambu ne da ya kasance mallakin wani a babba masarautar Kano, wanda yake ƙarƙashin kulawar mai unguwa, ba kowa ya san da hakan ba sai ɗaiɗaikun mutane.
    Gaba ɗaya hanyar ba ta cikin jerin hanyoyin da zata bi su sada ta da gida, amma tun da ta ji ‘yan ajinsu suna labarin mangwaron lambun ya fito yayi kyau, tayi alwashin bi ta hanyar dan ganewa idonta abin da suka gaya mata.
    Aikuwa babu ƙarya, lambun ƙato ne na gaske, wani wurin an kewaye shi da katangar bulo, wanu wurin kuma aka ƙarasa kewaye shi da waya.
    Akwai bishiyoyi kala-kala a ciki, wasu duk sun yi ‘ya’ya kasancewar lokaci ne na damuna.
    Mangwaron nan yayi ‘ya’ya sosai gwanin ban sha’awa.
    Ƙatuwar ƙofar shiga wurin ta gani, babu kowa a wurin, dan haka kai tsaye ta kutsa a gaban wata ƙatuwar bishiyar mangwaro ta tsaya, yanayin wurin yayi mata kyau sosai da sosai.

    Ta samu dutse, ta dinga jifan bishiyar, suna faɗowa tana ɗiba, ta tara ta cika jakarta, sannan ta nufo hanyar fitowa.
    Tana fitowa wani matashi yayi caraf ya danƙeta yana faɗin “Alhamdilillah, shegiya ɓarauniya ashe ku ne masu shiga lambun nan suna ƙurguma mana sata”.

    “Ban gane ba wace iri ɓarauniya me nayi maka?”

    “Zaki ga me ki ka yi mini, gidan mai unguwa zan kai ki, ke saboda ƙwarewa ma, da ki ka sata sai ki ka biyo ta ƙofa zaki fita, kina ‘ya mace kina sata”

    Cikin rashin kunya Ruma ta ce “Wallahi ni ba ɓarauniya bace ba, ta ƙofar nan fa na shiga, ba wanda ya haura gida ne ɓarawo ba?”

    “To da ki ka bi ta ƙofar, wa ki ka tambaya ki ka shiga ki ka ɗebo abibda ba naki ba?”

    “A’a, to ni wa na gani a wurin, kuma ma naga ai bishiyar ta Allah ce, Allah ne ya fito da ita, kuma sai ace sai an tambayi wani sannan za a ɗau abin da Allah ne ya fito da shi, kai iskar da ka ke shaƙa wa ka tambaya ka ke shaƙarta?” Saroro ya bi ruma da kallo, wata ‘yar cukul da ita sai shegen surutun tsiya.

    “Zaki yi bayani, sai na kai ki gaban mai unguwa”

    “Daɗinta shi mai unguwar ba shi da wutar da zai sakani, kuma duk in da za a je ai bishiyar Allah ce, kuma ka sakar mini hijjabi dan ni ba ‘yar iska bace ba.
    Bai ko saurareta ba, ya figi hijjabinta ya fara janta.
    “Ka dai na ja na haka kamar wata akuya, ba ƙaramin aikina bane na cire maka hijjabin nan na ƙara gaba.

     

    Mama sai kallon agogo take yi, tana kallon hanyar shigowa, amma babu ruma babu alamunta.
    Tsakar gida ta fito tana kiran Usman, kasancewar shikaɗai ne a gidan, ya dawo da wuri bashi da lectures.
    “Ka ga haryanzu yarinyar nan shiru ba ta dawo ba”

    Usman Ya ce “wataƙila tana can tana rashin hankali a titi da ƙawayenta, amma maybe ki ganta yanzu”.

    “A’a zunnuraini, shi biyu da rabi fa take dawowa amma kalli yanzu ƙarfe ɗaya da rabi, hankalina ya kasa kwanciya”
    Ya ɗan yi shiru sannan ya ce “Kuma fa kamar ma ga ‘yan makarantar su lokacin da nake hanyar dawowa, amma bari na je makarantar ta su” yana rufe bakinsa, suka ji ana ƙwala sallama a waje.

    Usman ya amsa, ya nufi ƙofar gidan, aikuwa yana zuwa ya tarar da an riƙo ruma, tana rungume da jakar makarantar ta, sai kumbura baki take, tana cika tana batsewa.

    Kallon matashin saurayin yayi, ya ce “Bawan Allah lafiya, ya zaka riƙo yarinya haka kamar ka riƙo ɓarauniya?”

    Matashin ya ce “To kusan hakan ne, karɓi jakarta ka duba ka gani”

    “Ka saketa mana” yayi maganar a fusace yana fincike hannun matashin daga hijjabinta.
    “Me tayi maka haka?”.

    “Nan matashin ya kwashe komai ya gayawa Usman”

    “Wallahi ni ba ɓarauniya bace ba, tun da ta ƙofar wurin na shiga kuma ban ga kowa ba, ai ba haurawa na yi ba”

    Usman ya fizgi jakar ruma, ya buɗe ya ga mangwaro ya kai takwas a ciki manya, nunannu da ɗanyu, sai goba guda huɗu.

    Ya kalli ruma, sannan ya kalli matashin ya ce “Yanzu kai a kan wannan zaka danƙota ka keto layi da ita haka? Ka taɓa kamata ta shiga ta ɗaukar muku abu ne?”

    Matashin ya ce “Ban taɓa kamata ba, amma ana haura mana, ayi sata”

    “To kuma sai aka ce maka nice nake yi, ni wallahi ban taɓa shiga ba sai yau”.

    Usman ya zura hannu a aljihunsa, ya ɗauko dubu ɗaya, ya miƙawa matashin ya ce “Na san dai abin da ta ɗauka, bai kai na hakan ba, gashi nan na biya, kuma kar ka sake kiranta ɓarauniya Please, ba halinta bane ba ba ta taɓa yi ba, dan ka ci sa’a da na biyewa zuciya sai na kifar da kai, saboda yadda ka riƙo mata hijjabi, ka keto unguwa da ita, saboda ɗanyen mangwaro”
    Yana gama maganar, ya ingiza ƙeyar ruma zuwa cikin gidan, suna shiga gidan ya danƙota ya ƙwace jakarta, ya durƙusar da ita ya ce “Oya tsallen kwaɗo maza”

    Waiwayo ruma tayi, ta kalleshi cikin mamaki, amma taga babu alamar wasa a tare da shi, cikin tsawa ya kuma cewa tayi tsallen kwaɗo.

    Mama ta fito tana faɗin “Lafiya, me aka ce tayi, sallamar da ake kenan?”

    Usman ya ce “Ƙyaleni da ita mama” nan ruma ta kama tsallen kwanɗo.

    Duk yadda mama tayi a kan Usman ya gaya mata me aka ce ruman tayi, amma yaƙi, sai dai ruma ta ci ƙwal ubanta, dan ko miƙewa kasa wa tayi.

    Duk yadda mama ta kaɗa ta raya, amma bai gaya mata ba, kuma babu wanda ya gayawa abin da ta aikata.

    ****
    Islamiyyar su ruma, sanya mata ido suka yi, dan ba ta iya karatu balle kawo hadda, ko karatun aka zo sai dai a tsallake ta, dan ba iyawa take yi ba.
    Malamin ajin ko sabgarta ba ya shiga, tun daga ranar da ya dake ta ta ce ita sikila ce. Yau dai ya kasa jurewa yace mata “Wai ke ba kya jin haushi yadda ‘yan ajin ku suke karatu, amma ke ba kya iya wa?”

    “To malam karatun yayi mini yawa, yaya zan yi?”

    “Su sauran da suke iyawa, da me suka fiki?”

    Ita kanta ruma gaba ɗaya malamin bai yi mata ba, dan bai fi sa’an Abdallah ba, shi ma ɗalibi ne a makarantar, amma ya dinga takura mata.
    Tayi masa banza tana kallon wani gefen daban.
    “Magana fa nake miki?”

    “To ya sayyadi me zance maka? Ni wallahi ba zan iya karatun nan ba, ni fa tun farko ba son makarantar nake ba, kawai dan yayana ya kawo ni ne”.

    Ita gaba ɗaya kanta tsaye take faɗar magana, ko tayi maka daɗi ko kar ta yi maka kai ta shafa.

    Tsaki yayi ya ce “Daƙiƙiya mara zuciya”

    Ɗagowa tayi ta kalleshi ta ce “Malam wannan ba halin musulmi nagari bane ba, ba koyarwar addinin Musulunci bace. Saboda bana iya karatu dama duk ka bi ka tsaneni Allah ya buɗa mini ƙwaƙwalwata nima. Zuwa zan yi a canza mini aji” ta tashi ta ɗau jakarta ta bar ajin, ba tare da ko izini ta nema ba.

    Ta bala’in jin haushin cin mutuncin da ya yi mata a gaban ‘yan ajinsu, wai daƙiƙiya mara zuciya.
    Ofishin shugaban makarantar ta nufa, dan ta sanar masa a canza mata aji, malaminsu ya tsaneta, amma ta tarar baya nan.
    Azuzuwa ta shiga dubawa, aikuwa ta ganshi a ajin su Yasir yana yi musu karatu.

    A ƙofar ajin ta tsaya ta ce “Headmaster ina wuni?”

    Ya ɗago ya kalleta, ba wanda yake ce masa wani head master sai yau a bakinta.

    Ya ce “Lafiya lau”

    “Malam zuwa na yi ka canza mini aji, ni na gajj da ajin nan, malamin ya tsaneni”

    Dariya ‘yan ajin suka fara yi, Yasir kuwa ya sunkuyar da kai ƙasa.

    Yayi murmushi ya ce “To shikenan, ki je ki jirani, idan an tashi sai mu yi magana”

    “To, Yasir in jiraka idan an tashi mu tafi tare?”

    Wani mugun kallo ya yi mata ya ce “Da tare muka zo”

    Murguɗa baki tayi, ta koma kan barandar ajin ta zauna, shiru-shiru ta gaji basu tashi ba, ta kaɗa kai tayi tafiyarta gida.

    A hanya ta biyo ta filin ball ɗin su Yaya Aliyu, maza sun yi cincirindo, ana kallon ball, ta tsaya tana leƙawa ko zata hango yaya Aliyu.
    Kutsawa ta dinga yi, sai gata ita ɗaya a cikin maza.

    “Ruma me ki ke yi a nan?” Ta ɗaga kai ta kalli mai maganar, abokin Aliyu ne.

    “Yaya Aliyu nake nema”

    “To ai yana cikin fili, ball yake”

    “To ai na sani, kallonsa zan yi”

    Ya jinjina kai ya ce “To ai shikenan”

    Kamar daga sama ya ji ana kiran sunansa, da ‘yar siriryar muryarta.

    Duk da yadda ya taso ball ɗin a gaba, amma sai da ya tsaya ya waiwaya.
    Ruma ya hango a gaban garada, tana ɗago masa hannu.

    Waro ido ya yi, ya nufi in da ruma take.
    Coach ɗin su Aliyu ya fara masifa, dan ajiye ball ɗin da ya yi, ya waiwaya aka ci su ɗaya.

    “Ke me ki ke yi a nan?”

    “Wucewa zan na ce bari na zo na ganka”
    Ya dafe kai ya ce “Innalillahi wa Innalillahi raji’un, ki wuce ki tafi gida”

    “Dan Allah ka bari na gani”

    Hankalinsa na kan ruma, coach kuma na ta masifa.
    “Kai dalla wacece wannan, ku koreta daga wurin nan”.
    “Wallahi ba inda zani, ai wurin yayana na zo”.
    Aliyu ya kalli abokinsa ya cewa “Aminu, dan Allah jire mini yarinyar nan” ya koma cikin filin yana waiwayenta.

    Aminu ya bata wata ƙatuwar jaka ta zauna a kai, ita kaɗai mace a cikin maza.

    Yana ball ɗin amma hankalinsa yana kanta.

    Ta dinga yi masa tafi tana bashi ƙwarin gwiwa, kusan duk hankali ya dawo kanta, gaba ɗaya ta bawa wasu dariya a wurin.

    Da yaya Aliyu ya ci ball kuwa, ta dinga tsalle tana murna, ya ci ball biyu.

    Da aka tashi har hoto aka yi mata, ita da Aliyu ta riƙe kofin da suka ci, kasancewar ball ce ta cikin unguwa.

    Ba a tashi daga ball ɗin ba, sai ana kiran sallar magariba, mama tana can ta sa an yi sahu ya kai uku a makarantar su, ana nemanta.

    Suna tafe a hanya tana yabawa yaya Aliyu, abokansa sai tsokanarsa suke yi a kan ruma.

    “Yaya Aliyu, akwai wani wanda kuna ball ɗin, ya dakar maka ƙafa, na ji haushi idan na ganshi sai na buga masa dutse wallahi”.

    “Ni ban saki ba, kuma baki ga an bamu pk ba da ref ya gani”

    “Oho ni na san wani pk, amma da ka tsaya ja masa duka ka rama, daga wasa sai cin zali”

    Haka suka ƙarasa gida, mama na tsaye da carbi a tsakar gida, tana tunanin ta ina ruma zata dawo.

    Sai gata ita da Aliyu, yana riƙe da hannunta.

    Mama ta kalleta ta ce “Ke daga ina?”
    Sai a yanzu ta tuna daga islamiyya ko gida ba ta zo ba, ta kalli ya ya Aliyu ya kalleta.

    “A ina ka ganta?” Mama ta tambaye shi tana kallon ruma.

    Aliyu ya ce “wallahi mama nima kawai ganinta na yi a filinmu, ban san ina za ta tsaya ba idan na ce ta taho, shi ya sanya na ce ta tsaya”

    “Kina mace uban me ya kai ki filin ball?” Huzaifa yayi maganar a ƙufiule, dan takalminsa har tsinkewa ya yi saboda nemanta.

    Hararsa tayi ta sake noƙewa a jikin Aliyu.

    Duka Huzaifa ya kawo mata, Aliyu ya tare ta, ya ce laifina ne duk Allah ya baku haƙuri.

    Mama ta fara tunanin anya ba zata kai ruma wurin malaman ruƙiyya ba, abin na ta ya fara bawa mama tsoro sosai da sosai.

    Kamar yadda ruma ta saba kwatsa zance, bayan kowa ya halarra, haka yau ma sai da kowa ya halarran, an gama cin abinci sannan ta gyara murya ta ce “Yasir, wai yaushe ku gama karatun ɗazu da naje ajinku”.

    “Ban sani ba” ya bata amsa.

    “Mhmm ai dama ba zaka sani ba, nifa gaba ɗaya mutuncin malamin nan ya zube a idona, wallahi mama idan kin ji me yake gaya musu sai kin riƙe baki, duk da wani abun bana ganewa, duk basu san daga waje ina jiyowa ba, kuma maimakon Yasir ya fito daga ajin nan, amma ina yana zaune ana koya musu abin da bai kamata ba.

    Saroro yasir ya yi, ya ji me aka koya musu da bai kamata ba, suna haɗa ido da ruma, ya tuna karatun da aka yi musu, kan ya kai ga ɗaukar mataki ta ce “Ina ji ai yana ce muku, wai ko idan mutum ya rungume mace alwalarsa ba ta karye ba, ko kiss, dan Allah wannan mama ba iskanci bane da ɓata tarbiyya, nan idan muna kallo aka nuno kiss ɗauke tashar ake yi, amma wai malaminsu yake gaya musu.
    Kuma naga ai turawa ne kawai suke rungume-rungume da kiss, mu wannan ba ɗabi’ar mu ba ce amma yake gaya musu, wallahi makarantar nan ɓata tarbiyya ake yi”.

    “DANƘARI!!”

  • Kanwar Maza 11

    Kanwar Maza 11

    P11

    Girgiza kai kawai Abubakar ya yi, ya ja bakinsa ya tsuke.

    “Yaya ya na ji kuma kayi shiru?”

    “To ruma ba dole na yi shiru ba, kowa yana nemawa kansa mafita a rayuwa, amma ke in da ki ka dosa daban?”

    “To wai me na faɗa ba dai-dai ba?”

    “Yanzu ke tsakanin ki da Allah, kin taɓa ganin mace a titi tana bada hannu a ƙasar hausa?”

    Ta ɗan yi shiru sannan ta girgiza masa kai ta ce “A’a, to mawaƙiya fa ko film?”

    Abubakar ya ce “Ba kushe sana’ar wani zan yi ba, amma ki yi tunanin wani abun daban”

    “To ba sai a buɗe mini kanti ba”

    “Yanzu a unguwar nan gaya mini shagunan da ki ka ga mata ne a ciki suke sayar da abu?”

    Ta yi farat ta ce “Ga maman Olu beyerabiya”

    “To ke bayerabiya ce?”

    “A’a amma dai…..”

    “Kin ga, ya isa haka, dama ni a kan career ki nake magana, tun da baki gane me nake nufi ba shikenan” ita sam ba ta ga aibun abin da ta ce tana so ba, dan haka ko a jikinta ta share.

    Gwaggo ta fara shirin tafiya, su Yasir suna ta murna, dan dama duk ta ishe su da faɗa da azabar saka ido.
    Shi kansa mai sunan Baba murna yake ta tattara ta tafi ta bar musu gida su huta, dan ta saka shi a gaba da yawa, dan ma Allah ya taimaki Abubakar bai fi sati ba ya koma makaranta.
    Amma kullum cikin surutu takewa mama “Hauwwa wannan zagada zagadan yaran naki, duk sun isa aure amma kin tare su a gaba kina ado da su a gida, ga ƙauye can muna da mata burjik, amma dan mugunta kin tare su kin hana su motsi’

    Mama ta ce “Haba Gwaggo, guda nawa yaran suke, haryanzu su Baba basu haɗa talatin ba fa, duk girman jiki ne, kuma kina ganin irin rayuwar da ake sai godiyar Allah, babu mai ƙwaƙwarar sana’a sai ƙarfin hali, idan suka ɗauko aure da yaya za su riƙe?”

    “Ba wani nan, idan mutum yayi aure Allah zai warware, amma kallesu dan Allah tuma-tuman gwauraye ki na ado da su a gida, babu mai mata, kalli dai wannan zagaren, sai dai ya shigo fuska kamar bajimin sa, ya zo ya ɗau abinci ya fita yana zazzare ido kamar wani zaki, ko fara’a ba ya yi, kai haka zaka yi wa matar ma idan an aureka?, ko da yake ma wace macence za ta auri mutum ba fara’a ba komai fuska kamar kunun kanwa ba rahama”
    Lomar Abincinsa kawai yake kawai, ko motsi bai yi ba, balle ya nuna ya san da shi take, yana jin ta ya share ta.
    Ruma kamar ta kwashe da dariya, jin an ce fuskar yaya Umar kamar kunun kanwa, amma sanin ruwa ba sa’an kwandon ba ne ya sanya ta ja bakinta ta tsuke.

    “Umaru da kai fa nake” A hankali ya ɗago idanunsa ya yi mata wani irin kallo, ya mayar da kan sa ya cigaba da cin abinci.

    “To Allah ya kyauta, ka ma dai mayar da ni mahaukaciya, ka je ka ƙarata, tattara kayana ma zan yi na bar muku gidan ku, gobe goben nan zan bar garin nan.
    A hankali yasir ya ce “Alhamdilillah, Allah ya raka taki gona”
    A rikice ruma ta ce “Haba Gwaggo, ni bana son ki tafi, dan Allah ki zauna bamu gaji da ganinki ba”.

    Huzaifa ya yi ƙasa da murya ya cewa Abdallah”Ji munafukar ‘yar nan, ko a gidan uban waye bamu gaji da ganin na ta ba, mata duk ta addabi mutane?”

    Abdallah ya ce “Ashe ka manta wacece ruma, ai wannan yarinyar tsaf sai ta haɗa yaƙin duniya na uku, duk abin da ta san za ta aikata wanda ba a so shi take yi”‘

    Kamar wasa ruma har da kuka, wai kar Gwaggo ta tafi, ji suka yi kamar su yi wa ruma taron dangi su zaneta.

    Ganin ruma na kuka, ya sanya Gwaggo ta ce ba zata tafi yanzu ba, saboda ruma.

    *****
    Sauri-sauri take yi, tana tafe tana duba agogon hannunta, tana daf da makara zuwa wurin da zata.
    Tana ƙarasawa harabar gidan ta ɗan ɗaga murya ta ce “Gali, gani na fito zo mu je na makara”

    Cikin girmamawa da murmushi Gali ya taso ya ce “Allah ya taimaki ‘yar gaban goshi, Allah ya ƙara miki lafiya uwar ɗakina, ai tun ɗazu ke nake jira, tun da tun huɗu ki ka ce mini”

    “Kai dai bari, na tsaya na yiwa Ammi girkin dare, kar na je ban dawo da wuri ba ka san ba komai take ci ba”

    Ya ce “Haka ne, bari na fito da motar” ya yi gaba ita kuma ta tsaya.

    ‘yan mata ne su huɗu, suka fito ta ƙofar wani sashi na cikin gidan, suka tunkaro in da take wajen harabar gidan, hakan ya yi dai-dai da fito da motar da Gali ya yi.
    Kai tsaye suka tinkari motar ba tare da sun kulata ba, suna ƙoƙarin buɗewa su shiga.
    Da sauri Iman ta ce “Kai, fita fa zan yi, zai kai ni unguwa ne”

    Ɗaya daga cikin su ta kalleta ta ce “Saboda ta ki fitar zamu fasa tamu ne?”

    Iman ta ce “A’a ba haka nake nufi ba, na ga kun iya driving, kuma ga wasu motocin, ni Ammi ta hanani tuƙi ne, kuma na yi magana da Gali tuntuni a kan zai kai ni unguwa”

    Cikin tsawa ɗaya daga cikin su ta ce “Shut up! Mu ki ke kallo ki ke gayawa haka, kin manta a tuna miki ne?”

    “Me ku ke yi haka a tsatstsaye?” Gaba ɗaya suka waiwaya suka kalli mai maganar.
    Jikin Iman ne ya yi sanyi, tare da shiga wani yanayi mai wuyar fassara, bayan sanya idanuwanta a cikin nasa.

    Fauziyya ta cire glass ɗin fuskarta ta ce “Bro, wannan ƙanwar ta ka ce take yiwa mutane rashin kunya, duk motocin gidan nan ta rasa wadda za ta hau, sai da muka zo muka ce a kai mu unguwa, wai ita ma tilas ita zata hau a fita da ita”
    Ya tsuke fuska ya kalli Iman ya ce “Wato ke tsagerancin naki har ya kai ki din ga yiwa na gaba da ke rashin kunya ko? Sa’anninki ne su?”

    Jiki a sanyaye ta kallesu, sannan ta mayar da idonta kan sa, sai dai ta kasa magana, sai hawaye da suka cika mata ido.

    “Ina magana zaki yi mini kuka, get out from my sight, stupid girl”

    Gaba ɗaya ta rasa meya kamata ta yi, jiki a sanyaye ta nufi hanyar fita daga gidan.
    “Ke zo nan” ta ji muryarsa ba tare da ta yi tsammanin hakan ba.
    Ta juyo ta dawo in da yake tsaye.

    “Ina zaki?”

    “Napep zan je na hau”

    “Wuce ki koma, ba zaki fita ba” yayi maganar cikin bayar da umarni. Ta kalli yadda motar da su Fauziyya suka shiga ta bar gidan. Ba ta ce masa ƙala ba, ta koma sashin su, sai dai duk yadda ta so ta riƙe hawayenta abin ya faskara, tuni hawayen suka wanke mata fuska.

    “Subhanallah, abar ƙaunata ya haka? Meyafaru? ya baki tafi ba?” Ammi ta yi mata tambayoyin a jejjare cikin ruɗewa bayan ganinta ta na kuka.

    Iman ta share hawayenta ta ce “Bakomai Ammi, kawai fasawa na yi”

    No ban yarda ba, gaya mini”

    “Ammi su Fauziyya ne da Yaya Mahmud”.

    Nan da nan Annurin fuskar Ammi ya ɗauke gaba ɗaya ta ce “Mahmud again? Tura fa ta fara kaiwa bango, meya yi miki?”

    Iman ta share hawayenta ta ce “Ammi dan Allah ki bar maganar, kar ranki ya ɓaci, bana son ki damu”

    Ammi ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce “Na ji, amma me suka yi miki?”

    “Dan Allah kar ki damu Ammi, bakomai ki yi haƙuri”

    Jinjina kai Ammi ta yi sannan ta ce “Yanzu shikenan, kin fasa fitar kenan?”

    Iman ta ɗaga mata kai alamar eh. Ta ja hannun Iman suka bar falon.

    ****

    Cikin rarrashi mama take magana, “Ruma, aiken ki nake son yi, amma bana son ki je ki yi mini shirme, ko ki tsaya a in da ban aike ki ba”

    “In sha Allah mama, ba zan tsaya a ko ina ba, fiii zan ware dogayen ƙafafuwana da bala’in gudu na je na dawo”
    Mama ta ce “Wane irin gudu kuma? Kalen ki watasar mini da kayan aiken, ki tafi a hankali, ki yi sauri ki je ki dawo”

    “In sha Allah zan yi sauri, na je na dawo”

    Mama ta gaya mata in da take so ta je, tare da abin da za ta kai, ruma ta sauya kaya ta saka hijjabi, ta fita yi wa mama aike, ta ƙuduri aniyar za ta je ta yi sauri ta dawo ko dan ta farantawa maman.
    Tashin farko ta bi ta cikin unguwa, tana tafe tana kalle-kallenta, duk wani lungu da saƙo idan ta bi sai an kira sunanta, dan kusan kowa ya santa.

    A ƙofar wani shagon aski ta ga keken Huzaifa, hakan ya tabattar mata da yana cikin shagon.
    Murmushi ta yi ta nufi ƙofar shagon askin, da sallama ta buɗe ta shiga cikin shagon.
    Duk maza ne a ciki, ga Huzaifa ya zauna a kan kujera za ayi masa aski, jin sallamar mace ya sanya dukkansu suka juya suna kallonta.

    “Ohh Huzaifa yau Allah ya yi zaka cire wannan sumar kenan? Kuma wallahi aka yi maka askin ‘yan iska kai da mai sunan Baba”

    A ƙule Huzaifa ya ce “Ke uban me ya kawo ki nan? Ba ki ga shagon aski bane?”

    “To ni ina ruwana da wani shagon aski, ba dai mutane ne a ciki ba, keken ka na gani a waje na san kana nan, na ce bari na leƙo na ganka”

    “To na ji na gode, fita ki bar wurin nan”

    “To sai ka tsaya na gama kallon kalandar askin nan, sai na tafi ” tayi maganar tana riƙe ƙugu, tare da zubawa kalandar ido.

    “Ni wannan yarinyar ba ke na taɓa rabaku faɗa da wasu yara ba, kun dawo daga makaranta?” Cewar wani da yake zaune shima yana jiran askin.

    “Eh nice, me na yi kuma?”

    Ya ce “A’a gane ki kawai na yi”

    “To yanzu da ka gane ni lada nawa aka baka?”

    Mai aski ya ce “Deluwa, dan Allah ki yi haƙuri, wurin nan duk maza ne, ki je aiken da aka yi miki, ko kuma in saka a riƙe mini ke na yi miki aski”

    “Aikuwa da sai ka kasa zaman Ɗorayi, sai na saka yayyena sun kakkaryaka sun zubar, ni zaka yiwa aski?”

    Huzaifa ya miƙe tsaye rai a ɓace ya ce “Bi ƙofar da ki ka shigo ki fita”

    Ta ɗan kwaɓe baki ta ce “Huzaifa ba ayi maka gwaninta, daga ziyara?”

    “Ki fita na ce, wallahi na zo in da ki ke sai na gwara kan ki” ja ta yi ta tsaya cike da taurin kai tana kallon idonsa, hakan ya ƙara tunzura shi, yayi kanta amma suka riƙe shi, ta fita da gudu daga shagon.

    Tana fita ta yi ƙwafa, ta tura keken sa ta ji bai rufe ba, keken ya fi ƙarfinta, amma ta haye ta yi gaba.

    Wani ya leƙa shagon askin ya ce “Huzaifa ƙanwarka ta ɗau keken ka fa ta tafi”

    Da sauri ya miƙe ya leƙo, ai tuni ta kusa ƙarshen layin, ya san ko da ya bita ba zai cimma ta ba.
    Kawai yayi tsaki ya koma ya zauna, zuciyarsa na tafasa, ‘yan cikin shagon suka din ga dariya, kowa na tofa albarkacin sa a kan halayar ruma.

    Haka nan tun da ruma ta fita, mama ta kasa nutsuwa, kawai dai gata nan ne dai, ta fara dana sanin dalilin ma da ya sanya ta aiketa.

    Tun tana saka ran ta ga ta ina za ta shigo gidan, har ta fara fidda rai, yanzu ba ta fiye ɗaga hankalinta ba, idan ruma ta fita makaranta ko aike ba ta dawo da wuri ba, sai dai fargabar mai za azo ace mata ruman ta aikata.

    Aikuwa ilai, tana cikin wasi-wasi sai ga sallamar wata matashiyar budurwa da wata yarinya, yarinyar bakinta a fashe, jikinta duk kwata ga fasashshiyar roba, da sauran gari a cikin ta, yarinyar sai kuka take, yawu da jini yana zuba daga bakinta.

    Cikin kaɗuwa mama suka gaisa da matashiyar yarinyar, mama ta hau tambayar ba’asi.

    Babbar ta ce “Dama cewa aka yi na zo gidan su na faɗa, ruma ce ta taho a kan wani ƙaton keke kashe gardi, ta taho da gudu, ƙanwata ta karɓo niƙa, ta bugeta da keken ta faɗa kwata, ita ma ta faɗi a gefe, ta tashi ta karkaɗe jikinta ta hau keken ta gudu, kuma ba iya ƙanwata ta buge ba, tun da tana tafe tana faɗuwa a kan keken”

    “Innalillahi wa Innalillahi raji’un, ya Allah kai ka jarrabeni, Allah ka dube ni, ka bani ikon cin wannan jarrabawa” mama ta kamo hannun yarinyar da aka jefa kwatar, ta wanke mata jiki, ta basu dubu ɗaya tare da basu haƙuri ta ce zata zo har gida ta basu haƙuri.

    Gwaggo kuwa ta hau masifa “Wallahi mutanen maraya ba ku da kara a kan ɗa, yanzu saboda wannan ɗin aka wani aiko yawon kan ƙara, ai ɗa na kowa ne, kuma fitinar maraya ai daban take”

    Kamar mama za ta yi kuka ta ce “Ba wnai fitinar maraya, dama can haka ake fama da ita, a ina ta samu keken da ta hau ni da na aiketa wuri daban, kullum sai ruma ta sakani asarar kuɗi da yawon ban haƙuri, nan gaba idan ba ayi wasa ba, sai wasu sun kai ƙararmu ga hukuma”

    “A’uzubil’ahi kina uwa ba zaki faɗi alkhairi a kan yarinyar ki ba, ƙuruciya ce, kowa da irin ta sa” mama ba ta kuma cewa komai ba, idan ta biyewa zuciya, za ta iya musayar yawu da Gwaggo, wanda ba za ta so hakan ba.

    Huzaifa ya shigo a kumbure yana bala’i “Mama! Ina ruma take wallahi yau sai na tattakata, sai na ci mutuncinta”
    Mama da take a ƙule ta kalle shi ta ce “A ina ka ganta?”

    “Mama shagon aski fa ta bini, na koreta shi ne ta ɗauke keke na ta gudu, ni sa’an wasanta ne ita duk wani halin zubar da mutunci ta iya”

    Mama ta safe kai ta ce “A ina da ta samu keken kenan? Za ta gane ba ta da wayo da Baba zan haɗata bari ta dawo”

    “A’a ke wace irin uwa ce, wannan mugun ɗan na ki, haka kawai ya kassarata a’a ban lamunta ba ”

    Huzaifa ya harari Gwaggo ya ce “Wallahi ko ba a gaya masa ba, da hannun nawa zan ci ubanta, sai na girgiza ƙashin haƙarƙarinta ”

    Har gefin magariba babu ruma babu alamarta, tun mama tana jurewa, har ta saka aje a nemo mata ruma.

    Aliyu Allah ya bawa sa’a, ya ganota a wata tawagar ‘yan d.j, ana biki an kunna d.j, ta shige tsakiyar manyan mata, ana rawar sabada, ta gantsare sai rawa take, tana wani juye-juye sai ka ce an saka mata batir, ga ta a shafe ba gaba ba baya ama sai karkaɗa jiki take.
    Cikin ‘ya’yan Mama, Aliyu Ustaz ne, ba shi da ra’ayin wannan abubuwan, amma yau a saboda ruma, sai gashi a tsakiyar mata, ya samu bayan ruma da take ta juyi, ya tsula mata tsumagiya.
    A zafafe ta ƙandare ta juyo, a zaton ta yaron mai D.J ne ya daketa, dan dama yana ta korar yara daga cikin filin rawar taƙi tafiya. Ba kuma rawar kawai take yi ba, har da satar kuɗin liƙi tana sakawa a cikin hijjabinta, sai ta gantsare tana rawa idan aka liƙo sai ta wayance ta ɗauke kuɗin.

    Cak ta tsaya tana kallon Aliyu, ta ɗaga kai ta kalli yadda gari ya yi duhu.
    “Sannu ‘yar makaɗa, aike da aka yi miki kenan ko? Fita ki wuce mu tafi”

    Kasa magana tayi, a take tayi saranda, da jin za ta iya ɗaukar kowane hukunci, saboda ita kanta ta san ta tafka ta’asa.
    Ta janyo keken Huzaifa, da Allah ya sa ba a sace ba, ta hau turawa, Aliyu ya haske keken, tayoyi duk sun sace, dan ɗayar ma fashewa ta yi, ga kaca ta zube keken duk wani gurin ya lotse, adon fitulun da ya yiwa keken kuwa, suma wasu duk sun fashe.
    Yana tafe yana kallon ruma, yana tunanin anya ruma mutum ce, fitinarta ko su da suna kamarta ba su yi haka ba, su dai akwai dambe kamar zakaru, kamar su cinye juna, amma rashin ji a gida, rashin ji a unguwa rashin ji a makaranta wannan sai Ruma ƘANWAR MAZA.

    A ƙofar gida suka tarar da Uamar, yana tsaye yana waya, tana ganinsa ta fara kuka, tana cewa “Kashina ya bushe”
    Aliyu ya ingiza ƙeyarta zuwa cikin gidan, da sauri Huzaifa ya taso, dan ta kekenaa yake yi, sai dai yana kallon keken ya san ko a wurin ‘yan gwan-gwan wannan keke ba zai daraja ba, kamar yayi shekara da shekaru.
    A ka rasa wanda zai ce mata komai, duk suka zubo mata ido.

    Mama ta ce “A ina ka ganota?”

    “Ga ta nan ku tambayeta”

    Cikin muryarsa mai razanata musamman idan ba ta da gaskiya ya ce “Daga ina ki ke?”

    Jikinta ya hau rawa ta ce “Dan Allah mai sunan Baba……

    “Daga ina ki ke fa kawai na ce?”

    Gwaggo ta ce”Ya zaka razanata da wannan muryar ta ka, ka tambaye ta cikin nutsuwa mana”

    Huzaifa ya daɗe bai ji abin da yake shirin sanya shi kuka ba irin yau, ya kasa ko tari tun bayan tozali da kekensa.

    Rarraba ido kawai take tana kokowa da numfashi, ganin yadda kowa ita yake kallo yana jiran amsarta.

    Wata irin gigitacciyar danƙa Uamar ya yiwa kunnenta, ta kurma ihu, ya janyota har tsakiyar tsakar gidan, ya dungurar da ita, ya naɗe hannun rigarsa cikin tsawa ya ce”Ina ki ka je da aka aike ki?”

    Cikin kiɗima da razani, ruma ta wassafa komai, ba ta ɓoye ba ciki har da zuwa wurin aski da yadda ta ɗau keke tana tafe tana faɗuwa, duk ta gurje gwiwa, da yadda bayan ta dawo daga aike ta tsaya wurin ‘yan bikin da ba ta san suwaye ba ma, tana rawa tana satar kuɗin liƙi.
    Sai a lokacin ta faɗi har faɗa suka yi da yaron dj yana ce mata shegiya ɓarauniya.
    “Yanzu ina kuɗin da ki ka ɗebo ɗin?” Yayi maganar yana miƙa mata hannu.
    Aikuwa ta zura hannu a rigarta, sai ga kuɗi, a ƙalla idan aka ƙirga sun kai dubu uku da ɗoriya.

     

    (SORRY FOR THE LATE UPDATE, AYYUKA SUN YI YAWA NE, INA GODIYA DA TARIN ADDUOI DA ƘAUNAR DA KU KE WA BOOK ƊIN ƘANWAR MAZA)

    Ayshercool
    08081012143
    [13/07, 9:01 pm] JAKADIYAR AREWA: ƘANWAR MAZA
    Na Aisha Adam (Ayshercool)

    MIKIYA WRITER’S ASSOCIATES

    https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

    Ku yi subscribing  YouTube channel ɗin
    @Cool Hausa Novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro.

     

  • Kanwar Maza 13

    Kanwar Maza 13

    P13

    Kwanci tashi asarar mai rai, ruma ta kammala primary school za ta shiga sakandare, sai murna take yi, sai dai babu abin da ya sauya a halayenta na rashin ji, ta hanasu sakat,a gidan, da an jima sai ta buga tsalle ta ce “Wooo ni zan shiga sakanni in dire”

    Yasir ya ce “Ji banza, me aka yi da maza meye wata sakandare, ai yanzu aka fara”

    “A’a bar ni na yi tsalle, na samu cigaba a rayuwa ta, Sakandire fa, zan shiga jss1 ai girma ya zo, yanzu ni ma zan yi tsayi tun da zan shiga Sakandire”

    Usman ne ya miƙo mata kuɗi ya ce “Yi sauri ki je wurin mai shayi, ki karɓo mini madara zan karya”

    Ɗan ɓata fuska ta yi ta ce “Mama fa ta hana ni zuwa wurin mai shayi, da mai kifi da mai nama”

    “Za ki wuce ki je ko sai na zo kan ki?”

    Ba dan ta na son aiken ba, ta karɓa ta saka hijjabi ta fita, tama tafe tana shan farar ƙasa, bakinta yayi fari tas, kai ka ce akuya ce ta dumbuji dusa.
    Ko da ta isa rumfar, dandzon matasa ne a ciki, sun cika kuma galibi abokan yayyenta ne, ba wanda ta kula a cikinsu ta miƙa kuɗi a bata madara.

    “Rumaisa, ina Dambele?” Cewar wani matashi da yake ƙoƙarin kai lomar indomie.
    Ta kalleshi ta ce “waye kuma dambele?”

    “Ussy mana, na gidanku”

    “Sai ka ce mini wani dambele kuma, kamar sunan rago, yana gida ya aka yi?”

    “A’a ba komai, kawai na tambayeki ne, kin san Usman dambele wani ɗan ball ne, shi ma haka ake ce masa a filin ball”.

    “Ni zaka gayawa dambele ɗan ball me, ai sai dai na baka labari”

    Kan kace me, aka ɓarke da hirar ball a teburin mai shayi tare da ruma, yadda take bayanin ball ya isa ka gane ƙanwar maza ce, gaba ɗaya ta manta da aike da aka yi mata, ta tsaya ana sharhi da ita.

    A ƙalla ta kai mintuna arba’in a wurin, ta manta da aiken gaba ɗaya, ga wurin shayin a ƙofar gidan su yaje, ya ci ace ta je ta dawo, amma babu ruma babu dalilinta.

    Ba shiri Usman ya sanya riga, ya fito nemanta, ‘yar muryarta kawai yake jiyowa, tana bayani, har da dukan teburin mai shayi tana mayar da yadda aka yi.

    “Ke! Meye haka?” Firgigit ta waiwaya, ta ga Usman a tsaye a bayanta.

    “Aiken da na yi miki kenan?”

    Kame-kame ta tsaya yi, dan har ga Allah ta manta da wani aike, musun ball na ɗibarta a rumfar mai shayi.

    “Dambele yanzu nake tambayar ruma kai, ashe kana gidan ma, yarinyar nan ta burgeni, ta san ta kan ball abin mamaki, gaskiya na yarda ƙanwar maza ce”

    A ƙule ya ce “Kai dilla ware, wannan ai hauka ne, kawai kun saka yarinya a gaba, kuna wani surutu, meye alaƙarku da ita?”

    “Haba Usman, Ruma ai ƙanwarmu ce”

    “Ba wani ƙanwarku, baku haɗa alaƙar komai da ita ba, ke kuma wuce kan na saka ƙafata, na kifa ki a wurin” sumi-sumi ta bar rumfar mai shayin ta nufi gida.

    Ya bita gidan, ya dinga yi mata masifa, kamar zai cinye ta ɗanya.

    *****

    “Hutawarki lafiya uwar ɗakina ta kai na, jirgin sama maƙurar tafiya komai nisan ta”

    Gyara zama ta yi ta dubeta ta ce “Bani labari, me ake ciki ne?”

    “A’a, labarin bai gama nuna ba, amma ki bari ya ƙarasa tukuna, amma fa gida ya ƙara hargitsewa, ina ta gwara kawuna ta ko ina, na hanata sukuni, kusan tun bayan da Mahmud ya sa ƙafa yayi fatali da ƙudurinta”

    “Hajiya Jamila, idan har muka tafi a kan tsarin da muka yi da farko, to tabbas zamu cimma buri, sarautar ta bar gidanku har abada”

    Hajiya Jamila ta yi murmushi ta ce “Ai hakan na fi so, gara ai ayi biyu babu, sai na yi mata kassarawar da zata bar gidan nan da ƙafafuwanta, tun da dai na fuskanci asiri ba ya cin ta, gara ayi mutuwar kasko”

    Dariya suka yi a tare, suna tafawa cike da duniyanci, tare da cigaba da tattaunawa a kan cikar muradansu.

    ****
    Tamkar mai shirin zarewa, haka yake kai gwauro, ya kai mari a cikin katafaren falon, da ya sha ado da kayan alatu kamar ba za a bar duniyar ba.

    Gefe guda wani babban mutum ne, zaune a ɗaya daga cikin jerin kujerun da suke falon, hannunsa riƙe da wani kwagiri, fuskarsa ɗauke damuwa.

    Matashin ya daki teburi ya ce “Daddy meye abin yi ne? Ka na zaune ba ka ce komai ba?”

    Dattijon ya numfasa sannan ya ce “Ka bini a hankali, ina tunanin wani abu ne”

    “Daddy ba mu da isasshen lokaci fa, you know am following your footsteps, idan aka ɓata siyasarka, zai shafeni, mutum mai girma da daraja, kamar kai wannan ɗan ƙaramin alhakin zai kawowa barazana, gaba ɗaya gidajen jaridu, da dandalin sada zumunta, an buga labarin nan, kamar kai ka cancanci haka a ƙasar nan”
    Murmushi mutumin ya yi ya ce “Easy Khalifa, ai ja da baya ga zaki ba tsoro bane ba, shirin yaƙi ne, haka zalika yaro bai san wuta ba sai ya taka, ka ƙyale shi, a yanzu ba ta tasa ma nake yi ba, na zuba ido ne in ga wani mataki za a ɗauka a kansa. Saboda idan ya matsa sai ya fasa ƙwai, to ba ni kaɗai za ta shafa ba, zata shafi manyan ƙasar nan da dama, yaron tone-tonensa ya yiwa, amma yana daf da tona wuƙar da za ta yi ajalinsa”

    “Ohh my God, Daddy sai wasu irin maganganu ka ke yi, amma haryanzu ba ka gaya mini menene mafita ba”

    Alama ya yiwa Khalifa da ya je, Khalifa ya ƙarasa gabansa ya durƙusa. Ya tallafo kan Khalifa ya yi masa raɗa a kunne.
    A take damuwar kan fuskarsa ta gushe, murmushi ya mamaye fuskar ta sa ya yiwa mahaifin na sa alamar jinjina da hannunsa.

    ****
    Sati biyu kenan da fara zuwan ruma makarantar sakandare, kullum sai ta yi gugar kaya, wai kar ta je da ƙazanta kamar ba ‘yar sakandare ba, amma idan ta tashi dawowa tamkar ta yi dambe da kura, kayan nan duƙun-duƙun haka take dawowa da su.
    Haka kawai yau zuciyarta ta raya mata, ta bi ta hanyar gidan mai unguwa, kasancewar a hanyar makarantar da take gidan yake.

    A layin gidan mai unguwar, ta ga manyan motoci a fake, da alama wani abun ake yi. Hankalinta na kan lambun da ta taɓa zuwa ta ɗebo mangwaro mai gadi ya ce mata ɓarauniya, dan haka ba ta tsaya jin me ake a layin gidan mai unguwar ba.

    Sai dai ko da ta ƙarasa layin lambun, wasu manyan motoci ta tarar guda uku a ƙofar lambun.
    Lelleƙawa ta shiga yi, ta na haɗiyar yawu, saboda yadda take iya hango cincirindon bishiyoyin mangwaro da yadda  suka yi ‘ya’ya, ban da sauran ‘ya’yan itatuwa.

    “Ke uban me ki ke yi a nan wurin?”

    Da sauri ta waiwaya, ta ga waye yake yi mata tsawa haka.
    Ɗan gidan mai unguwa ne dai, da ya taɓa kamata.

    “Taɓ dama kana nan?”

    “Eh ina nan, yau ma satar ki ka zo yi?”

    Ta tsuke ɗan bakinta ta ce “Ba yayana ya ce kar ka sake ce mini ɓarauniya ba?”

    “Oho miki dai, ai ɗiba ki ka yi ba a baki ba”

    “Eh amma ai dai ya biya”

    Cikin hanzari ya ce “Wai me ma ki ke yi a nan wurin ne?”

    Ruma ta ɗan riƙe haɓa ta ce “Hmmm, ashe haryanzu ka na nan, ba ka cigaba ba, ni gashi har na gama primary na shiga sakandare”

    “Ke dalla ware, tun kan a haife ki na yi sakandare na gama, fitsararriya wai wani ban cigaba ba, ɓace ki bar nan wuri muna da baƙi”

    Ta ɗan yi ƙasa da murya ta ce “Wai su waye suka zo, na ga ƙofar gidanku ma da mutane”

    “Ban sani ba, ba zaki wuce ba sai na zane ki?”

    “Dan Allah ɗan uwanmu mangwaro zaka san mini, ka ga dai yau ba sata na yi ba ko?”

    Dariya ya kwashe da ita ya ce “A ina na zama ɗan uwanku?”

    “Ai kai ɗan uwanmu ne na Musulunci”

    Girgiza kai ya yi, zai wuce ta ya shiga cikin lambun, amma ta biyo shi.

    “Wai ke baki da hankali ne, na ce miki muna da manyan baƙi masu wurin ne suka zo”

    Cikin ko in kula ta ce “To ni ina ruwana, koma suwaye ai mutane ne ba mala’iku ba, dan Allah in biyoka ka san mini, ni sai na je na tambayo mai unguwa ma, na san shi zai ce ka bani”

    Ya ƙarewa ruma kallo tsaf, a rashin hankalinta, tsaf za ta aikata abin da ta faɗa, na zuwa tambayo mahaifinsa, gashi yana tare da baƙi, ya dubeta ya ce “Yanzu abin da za ayi, ki zauna ki jirani, bari baƙin su tafi sai na baki”

    “To, bari na je na zauna, kuma idan baka fito ba, biyoka zan yi”

    “Wallahi ki ka shigo, zane miki jikinki za su yi”

    “Su waye wai?” Ta yi maganar tana sake leƙa lambun.

    “Kin ga tsaya, bari na je na samo miki” ya ƙarasa maganar tare da shigewa cikin lambun.

    Dandamalin wani gida ta samu, ta ajiye jakarta, ta ɗebi duwatsu ta hau ‘yar carafke.
    Tun ‘yar carafken na ɗauke mata hankali, har ta gaji da jiran ɗan gidan mai unguwa. Ta zube duwatsun ta tashi, ta je ƙofar shiga lambun ta tsaya, ta ɗaga murya ta ce “Ka cika alƙawari, zan shigo fa” magana ta fara ji ƙasa-ƙasa na mutane, alamar za a fito, ba ta yi niyyar matsawa daga bakin ƙofar ba, sai da ta hango akuya na shirin watso mata litattafanta, ta ci, ta nufi wurin jakarta, ta ɗau jakar ta na zagin akuyar, har da kiranta mayya mayuwanciya kamar tana magana da mutum.

    Tana waiwayo wa, taga mutanen sun fito, sai dai kusan duk sun yi rawani, sai mutum ɗaya da suke takewa baya, shi kuma suit ce ma a jikinsa.

    Da gudu ruma ta kwaso, ta tsaya daga baya ta ce “Laaa sarki ne wannan?” Jin ‘yar shilar muryarta ya yi, tamkar busar wata ‘yar sarewa a kunnensa, duk da akwai dandazon yara da suke wurin, galibi suna zuwa idan har ya zo, saboda ya kan basu kuɗi. Har ya ɗan juyo, zai waiwayo ya ga wacece a cikin yaran, bai juyo gaba ɗaya ba, dogon hancinsa kawai ta iya ganowa, ya ɗauke kansa ya shige motar da aka buɗe masa.

    “Sarki ka ganni, ka juyo ka kalleni, ko dai ba sarki bane ba, na ga sarki ba ya saka ƙananan kaya ai”

    “Ke! Hattara yarinya ‘yar talakawa, ba a yiwa takawa karan tsaye”

    Shiru ta ɗan yi ta dube shi ta ce “‘yar talakawa kuma, to wallahi gidanmu akwai abinci, mu ba talakawa bane ba, kuma ba gara ni ba ma, Idan mu ka je kallon hawa mandawari, mama ta ce mini masu irin kayanka bayi ne, sayar da su ake yi zamanin baya a karɓi kuɗi”
    Kowa waiwayowa ya yi yana kallon ruma, ya yin da dogarin ya zabura ya yo kan ruma, aikuwa ta kwasa da gudu ta tayar da uwar ƙura, shi kuma ya bita yana a tare ta.

    Da ƙyar ruma ta kai gida afujajan, ta na ta haki kamar numfashinta zai ɗauke, ta shige ɗakin mama ta ƙule ta na ta sauke numfashi.

    Mama ta biyo ta ɗakin ta na faɗin “Ke!ke ruma ke da waye haka? Yanzun ma tsokanar ki ka yo ko? Tun yashe aka tashi ‘yan makarantar ku, amma Allah bai nufe ki da shigowa ba sai yanzu ko? Ba zaki fito ba ina yi miki magana?”

    Sumi-sumi ta fito, tana waige-waige sannan ta mayar da idonta kan mama.

    “Daga ina ki ke?”

    Ruma ta ɗan ɓata fuska ta ce “Mama ba ko ina fa”

    “Zaki gaya mini ko na bari sai ya shigo?” Cikin kiɗima ruma ta ce “A’a, dan Allah kar ki yi mini haka, wallahi kallon sarki na tsaya, a lambun mai unguwa, shi ne wani bawa ya ce mini ‘yar talakawa, shi ne” sai kuma ta yi shiru.

    “Shi ne me?”

    “Cewa na yi, ai gara ni ba baiwa ba ce, shi fa kayan bayi ne a jikinsa, wanda ki ka gaya mini ɗin nan ranar da muka je cikin gari kallon hawa, shi ne ya biyo ni da gudu”

    Tafa hannu mama ta shiga yi tana faɗin “Innalillahi wa Innalillahi raji’un, dama can na aike ki, na ce idan an tashi ki dinga zuwa wani wur?” Ta girgiza kai.

    “Saboda tsabar rashin kunya da rashin hankali, ki ka tsaya kina cewa babban mutum bawa, daga yi miki bayani ranar, ke ba zaki taɓa hankali ba ko? Ina ma ya kama ki ya yi miki dukan tsiya, na gaji da halinki ruma, ki na girma ki na sake shiga dawa, gaba ɗaya babu alamar hankali balle nutsuwa a tare da ke. Ki je ki cigaba da abin da Allah ya nufe ki da yi, Allah ya gani na yi iya yi na, ban yi miki irin wannan tarbiyyar ba Allah ya shiryeki”
    Ruma ta yi shiru, tana sunkuyar da kai kamar gaske.

    A ɓangaren karatu, an samu sassauci daga halin ruma, kullum Usman ya na ba ta ƙwarin gwiwa, a kan kar abin da ya bata tsoro, duk wani abu da wani zai yi, ita ma za ta iya.
    A makarantar islamiyya kuwa, tun da malam Habibu ya taɓa hannunta garin karɓar bulala ta daina bin sa, sai dai yau ta zauna a ajinsu, gobe ka ganta a wani ajin, ɗaukar magana kuwa ba ta fasa ba. Dan saboda tsaurin ido, har manyan ‘yan matan nan haka take zagewa ta yi musu rashin kunya, ba abin da ya yi mata zafi. Kuma ku san ko yaushe ta na cikinsu, ba ta yawo da sa’aninta.

    ****
    “Allah ya taimake ki Hajjaju Mummy”

    Murmushi ta yi cikin isa da izza ta ce “Abin ƙauna, ka yi breakfast ɗin ne?”

    “Eh, na yi” ya yi maganar ya na zama a kusa da ita.

    Ta saka hannu ta shafi sumar kansa ta ce “Mahmud, ya kamata a rage sumar nan”

    Yayi murmushi ya ce “Haba Mummy, wannan sumar yadda ki ka ganta ki bar ta kawai”

    “Hmm to ai shikenan, ya shirye shiryen komawa school?”

    “Alhamdilillah, ina nan ina yi, very soon zan koma”

    Fauziyya ce ta fito falon riƙe kofin shayi, ta kalli Mahmud ta ce “Yaya Mahmud, barka da safiya”

    “Yauwwa, ina Ruky, ban ganta ba?”

    Ta nemi wuri ta zauna ta ce “Ba ta tash ba, bacci take yi” ya kalli agogon hannunsa ya ce “By this time?”

    Mummy ta ce “Ka san ta na karatun dare, dole ta yi bacci da safe”

    Ya jinjina kai ya ce “Haka ne”.

    “Amm Yaya Mahmud, takawa ya dawo fa, yakamata ku haɗu kan ka koma, kun daɗe baku haɗu ba” tsuke fuska ya yi, ya kalli Fauziyya ya ce “Yaushe ki ka fara tsara mini abin da zan yi a rayuwata? Ubana ne shi da lallai sai na ganshi? Na gan shi jiya mana so what?”

    Mummy ce ta katse hirar, ganin Mahmud har ya ɗau zafi ta ce “Is ok, ya isa haka, ku dai idan ya shigo ku je ku yi masa sannu da zuwa, bana son ƙananun maganganu irin na gidan nan”.

     

    Sannu a hankali yake danna system ɗin da ke gabansa, kamar ya na tausayaa mata, hannunsa ɗaya kuma riƙe da cup ya na shan tea, idan ba ka kalleshi sosai ba, zaka ɗauka Mahmud ne a zaune.
    Muryarta ce take dawo masa kunnesa, kamar a yanzu take magana *laa sarki ne wannan? Sarki ka juyo ka kalleni* ya tuna ƙarfin hali da ta dubi ɗaya daga dogarinsa, ta ce masa bawa, koma dai wacece a muryarta ya ji akwai yarinta da kuma tsananin tsaurin ido, idan sarkin ne shi a haka zata yi masa magana kenan, ba girmamawa?
    Iman ce ta fito daga sashin Ammi, hakan ya kaste masa tunaninsa, ta ƙaraso falon ta zauna, ta kalle shi ta ce “Barka da hutawa ranka ya daɗe” tun ɗazu Nusaiba take falon, tun da suka gaisa ta ja bakinta ta tsuke, ta kasa ce masa komai, shi ma kuma bai kulata ba, amma Iman na fitowa ya yi murmushi.

    “Barkanki dai auta ta Ammi, kin tashi kenan?” Ta jinjina masa kai sannan ta ce “Once again Ya hanya, ya kuma ibada?”
    “Alhamdilillah, ya karatun?”

    “Ina nan ina ta yi Yaya, ka yi mini Addu’a kuwa da ka je?”

    Ya jinjina kai ya ce mata “Sosai, ban yiwa kai na Addu’a da na yi miki ba, na so mu tafi tare da ke, amma na san Ammi ba lallai ta yadda, sai dai ku je umarar azumi ke da ita”

    Iman ta yi murmushi ta ce “Nima ina yi maka addu’a sosai yaya, Allah ya kawo abin da Ammi take ta fata”

    Nusaiba ta jinjina kai, da wani ne ya tsare Yaya da wannan maganar da ya shiga uku, to wa ma ya ga fuskar hakan, ai sai Iman ɗin.

    “Iman, ai kuma zaku iya samarwa Ami abin da take burin, ku fito mana da tsayayyu, a wuce wurin kawai”

    Iman ta ɗan rausayar da kai ta ce “Sai dai Anty Nusaiba, amma ni dai kam sai a hankali ” tayi maganar jiki a sanyaye.

    Alama ya yi mata da hannu da ta zo.
    Ta tashi ta tafi in da yake ta zauna, ya matsa kusa da ita, yayi ƙasa da muryarsa ya ce “Na ji abin da ya faru lokacin ina Saudiyya, abin bai yi mini daɗi ba sam, da Ammi ta yi shawara da ni, ba za ta yanke wannan hukuncin ba, ai Allah ke da rayuwar kowanne bawa. Ki ɗau abin da ya faru a matsayin Mafi alkhairi, Allah ya tanadar miki mafi alkhairi, ni kai na example ne a gareki, dan haka mu cigaba da Addu’a gaba ɗaya” ta jinjina masa kai ta na share hawaye.

    *******
    Usman ne a zaune ya gama cin abinci, ya kalli Abdallah ya ce “Kai ka san wani hau da wannan Anas ɗin yayi mini yau?”

    Abdallah ya ce “Sai ka faɗa”

    “Wai ni zai tara ya ce mini ya na son ruma, yarinyar da ko ciwon kan ta ba ta sani ba, ni kuwa na ci ubansa, sai kaɗan na kikkifa masa mari”

    Abdallah ya yi dariya ya ce “Ba abokin ka bane ba, na ga filin ball ɗin ku ɗaya ma”

    “Dan abokina ne, sai ya ce yana son ƙanwata, mahaukacin ina ne shi?”

    “Amma wallahi yaya Usy ba ka kyauta mini ba, ‘yan ajinmu na Islamiyya su yi ta labarin saurayi, ni kuma ba ni da saurayi, duk wadda ba ta da saurayi fa wai baƙin jini ne da ita, sai an kai ta wurin malamai sun yi mata Addu’a ”

    Abdallah ya ce “Saurayin uban wa? Ke ya zaki yi da wani saurayi, ko yake shi Anas ɗin ne ma mara hankali, shi ma irinki ne ai mara kan gado perfect match”

    Ɗan saroro ta yi ta ce “Wai Anas ɗin gidan mai taya?”

    Abdallah ya ce “Ƙwarai kuwa”

    Ta ce “Taɓ, Astagfirullah Allah ba irin wannan ba, kenan addu’a ta ba ta karɓu ba, ina ta Addu’a Allah ya bani saurayi mai kyau, mai kuɗi, mai ƙarfi sosai wanda zai din ga goyani kamar girman brownstrawman na wrestling, kawai sai wani Anas ya ce yana so na, wata uwar ƙeyarsa kamar sirdin keken baban su Ade, gashi siriri da kaɗan ya fi taliya. Ina ga sai na ƙara dagewa da Addu’a “.

    Usman ya ce”Ke, kina halitta ne da zaki din ga kushe wasu? Kin ga ki shiga hankalinki, ba ke ce baki da kamun kai ba, dole kowa ma ya ce zai ce yana son ki, kuma wallahi idan ba ki shiga hankalinki ba, sai na bashi ke”

    “Allah ya kiyaye, wallahi ba zan aure shi ba, gashi baƙi ƙirin kamar an rina shi”.

    “Ke zan ci ubanki na kuma jin kina kunshewa wani halitta, ke kyan ne da ke. Ni kullum fatana Allah ya baki miji na gari ko ya fi biri muni” mama ta yi maganar a hasale.

    “Mama biri kuma, ba amin ba gaskiya, dan Allah idan irin wannan addu’a ki yi mini ki daina, ni wallahi kyakykyawa na ke so”

    “Kyan banza da na wofi, kyan ɗan maciji ki auri kyan ya din ga gasaki ba gara mummuna na gari ba”

    Ruma kamar za ta yi kuka ta ce “Ina wani abin arziki a muni”

    Mama ta hau ruma da faɗa, ruma ta yi shiru, amma a duk sa’ar da mama ta ce Allah ya bata miji nagari duk muninsa a zuciyarta za ta ce ba Amin ba.

    Yau ruma Alla-Alla take gari ya waye, sai murmushi take ita kaɗai.

    Yasir ne ya lura da ta na fara’a, dan haka ya ce “Wai ke murmushin me ki ke yi ne haka?”
    Ta gyara zama ta ce “Ka san tun da na shiga sakandare, ban yi faɗa da kowa ba, so nake na zama ‘yan mata, in din ga tsayawa a cacar baki, to ni cacar baki ba ta biya mini buƙata, na fi son na haɗawa yarinya malaman jikinta, muka yi faɗa da wata yarinya, ka san ni ba na zagi, ta dinga zagina in gaya maka, amma ban yi kuka ba.
    Kawai yau na ga babarta ta zo makarantar mu, da ƙyar ta shiga ofishin principal saboda girmanta, ina ga ta yi rabin bangon ɗakin mama.
    Kai ina ga fa ta yi yakuzuna na jikin receiver girma, koma ta fishi, shi ya sa nake son Allah ya kaimu gobe, za ta gane ba ta da wayo, ba dai har da cewa babata tsohuwa ba ce, wallahi a jikin allo zan zana babarsu.

     

    Ayshercool
    08081012143
    [19/07, 8:42 am] JAKADIYAR AREWA: ƘANWAR MAZA
    Na Aisha Adam (Ayshercool)

    MIKIYA WRITER’S ASSOCIATES

    https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

    Ku yi subscribing  YouTube channel ɗin
    @Cool Hausa Novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro.

  • Kanwar Maza 12

    Kanwar Maza 12

    12

    Mai sunan Baba ya kalleta a tsanake ya ce “Sata ki ka koma yi kenan ko?”

    Ta girgiza kai da sauri ta na zazzare ido.

    “Ba zaki buɗe baki ki yi mini magana ba?”

    “A’a Yaya wallahi ba sata nake yi ba”

    “To idan ba sata ba, me ki ka yi, kin san su masu bikin ne, ko kuma sun sanki, idan ba sata ba baki suka yi, ko nan aka aike ki?” Ta girgiza masa kai.

    Ya ce “Good, tashi ki je ki yi alwala ki yi salla, zan gauraya da ke, tashi maza ina jiran ki”

    Huzaifa da yake ta huci, ya cika ya batse kamar ya sha yeast ya ce “Wallahi yau sai na lallasaki, za ki gane baki da wayo”

    Gwaggo ta ce “Ku dai din ga haƙuri yarinya ce, ƙuruciya ce kawai take damunta”

    Huzaifa ya yi ƙwafa ya ce “Ba ƙuriciya da yarinta ba, Allah ya sa ɗanyar ƙwaƙwalwa ce a kan ta da ba ta nuna ba, sai na lallasata na koya mata hankali”

    Duk da tana cikin tashin hankalin rashin sanin hukuncin da za ta fuskanta, hakan bai hanata murguɗawa Huzaifa baki ba, tana harararsa, duk da laifin da ta tafka masa.

    Daga shiga banɗaki alwala ta tsiri kashi, duk dan ta ɓata lokaci kar ayi mata hukunci mai wahala, ta na fitowa, Umar ya ce a tsakar gida za ta yi sallar, dan haka ta ɗau hijjabi ta tayar da salla.

    Ita kanta ba ta san adadin raka’ar da ta yi ba, kawai yin sallar take cike da zullumi, a sujudar ƙarshe kuwa kai kace neman gafara take ko bacci tayi, amma babu ɗaya nazari kawai take.
    Haka ta idar ta saka addu’a, abin da ba ta saba ba, ko sallar ta yi sai mama ta yi ta faɗa sannan take zaman yin addu’a.

    Ganin taƙi sallame addu’a ne ya sanya Umar yi mata wani irin kallon, da babu shiri ta shafa addu’a ta tashi.

    Ya ce “Oya, kamun kunne”

    Cikin marairaicewa ta ce “Dan girman Allah Yaya…..

    “Shut up! Zaki abin da na ce ko kuwa?”

    Jiki a sanyaye, ta durƙusa ta kama kunnenta, nan da nan jikinta ya hau rawa, ta fara gajiya ta saka kuka.

    Gwaggo ta ce “Kai ina mace ina wannan goho, kai meyasa ba ka tsoron Allah ne? Ke tashi dalla wannan wace irin azaba ce?”

    Ruma ta ce “A’a Gwaggo, ba zan iya tashi ba sai ya ce dan Allah ku tayani bashi haƙuri”

    Mai sunan Baba yayi shiru, ya ƙi kula Gwaggo, ta dubi mama ta ce “Ke ba zaki saka baki ya ce ta tashi ba, tun da ni ban isa ba?”

    Mama ta ce “Ba haka bane Gwaggo, ai gara a din ga hukunta ta idan ba haka ba, sangarta da rashin jin da zata yi sai Allah ruma ba ta ji sam” ƙarshe mai sunan Baba ya tashi ya bar gidan ma gaba ɗaya ruma kuma ko da wasa ba ta tashi ba daga kamun kunnen, sai dai ta cika musu gida da koke-koke da magiya.

    “Innalillahi wa Innalillahi raji’un, dan Allah mama ki saka baki, na tuba na bi Allah, dan Allah ki bashi haƙuri ya ce in tashi”

    “Babu ruwana, ba dai ba kya ji ba, ai na gode Allah da ya bani waɗanda zasu hukunta ki idan ki ka yi ba dai-dai ba, kuma kar ki sake kiran sunana”

    “Wayyo Allahna na shiga uku, wallahi mama zan iya rasuwa, kaina da wuyana ciwo suke yi mini, bana son na mutu yanzu, bana nafila karatun Alqur’ani ba kullum nake yi ba, gashi ina yi miki abin da ba kya so, bana son na mutu yanzu ban tuba ba, wallahi mama zan iya rasuwa a wurin nan”

    Yasir ya ce “Ba ki jigata bane ba, da ki ke iya wannan surutun”

    Gwaggo ta ce”Ji min kafirar yarinya, ba nace ki tashi ba kin ƙi, ni babu abin da ya ƙular da ni, irin wannan goho da ya saki kina ‘ya mace, kema da azababben taurin kai na ce ki tashi kin ƙi”.

    Ruma ba ta kula Gwaggo ba, sai cigaba da rusa kuka da tayi, tana magiya da neman taimako.

    Cike da ƙuluwa Yaya Aliyu ya ce”Ki yi mana shiru dan ubanki, tun da ba wani ne ya aike ki ki aikata abin da ki ka yi ba” haka ruma ta ja bakinta ta tsuke, tana kuka ƙasa-ƙasa dan wasu lokutan yaya Aliyu ma ba daga nan ba wuri8iya tsare gida da hukunci, dan daga yaya Umar sai shi a zafi.

    Har mai sunan Baba ya dawo ruma tana nan tana aikin kamun kunne, tana yi tana faɗuwa tana tashi.

    Sai da ya dawo sannan ya ce ta tashi, kuma ya ce mata washegari za su gauraya.

    Tana miƙewa tsaye jiri ya kwasheta sai amai, Gwaggo ta fito da sauri ta kama ruma, kanta sai juyawa yake saboda azabar wahala.

    A zaune ta yi alwala tayi sallar isha’i, ko abinci ba ta nema ba, ta kwanta saboda galabaita, cinyoyinta sai azabar ciwo suke yi mata, dama da fari suna ciwo saboda hawan keke, gwiwoyinta na raɗaɗi saboda duk ta ƙuje su saboda keke, yanzu kuma ga kamun kunne, jikinta kamar an mata duka haka take jin ta, a take wani irin wahalallen bacci ya kwasheta.
    Sai dai kwana ta yi da wani irin zazzafan zazzaɓi, wanda ita kanta ba ta san ya hau ta ba, jin surutan ta ya yi yawa a baccin ne ya sanya mama zuwa ta taɓa jikinta, ta ji da zafi sosai.

    Duk da mama a ƙule take da ruma, haka ta fita ta ɗebo ruwa ta sanya ɗan ƙaramin towel, ta din ga shafawa ruma ruwa a jikinta.
    Tun asubar fari kuwa, ruma amai ne ya tasheta, saboda har a lokacin jiri take yi.
    Yanzu ma a zaune ta yi sallar asuba, ta nemi wuri ta kwanta.
    Tun mama na basar da ita, har kuma ta fara damuwa, Gwaggo kuwa ta samu wuri ɗaya ta zauna sai mita take na masifa a kan mama tana gani aka bawa ruma gwale-gwale amma ba ta ce komai ba.

    Bayan gari ya gama wayewa, Gwaggo ta karya ta yi haramar tafiya, sai dai a lokacin ruma ta samu bacci, dan a galabaice take. Gwaggo ta ce kar a tasheta, Abdallah ya tafi rakata tasha, suna ta murna zasu huta, dan dama Gwaggon ta ishe su,  ruma ce kawai take son zamanta a gidan.

    Mama ta tashi ruma, ta matsa mata a kan lallai ta ci Abinci, ta na ci tana kuka ta ɗan sha tea kaɗan ta kuma kwanciya, sai dai ko mintuna goma ba ayi da cin Abincin na ta ba, ta tashi ta cigaba da amai.

    Ba shiri mama ta ce Aliyu ya zo ya kai ruma chemist a dubata.

    Da ƙyar take iya tafiya, suna tafe tana kuka, har sai da ran Aliyu ya fara ɓaci, amma ya shareta suka cigaba da tafiya a hankali. Cikin sa’a kuwa suka tarar ya fito, kasancewar asabar ce, ranar ba ya zuwa aiki.

    Ya na ganinsu cikin kulawa ya ce “Subhanallah, ‘yar gidan mama yau ke ce ba lafiya?” Ita dai ba ta iya magana ba ta nemi wuri ta zauna. Aliyu ya zauna ya rungumeta, saboda ƙoƙarin faɗuwa take yi.

    “Meya sameta haka?”

    Aliyu ya ce “Ina ga zazzaɓi ne dai, da amai ta fara jiya”

    Bakinta bai mutu ba, ta ce “Kamun kunne aka sakani, kusan awa goma shine ya sani rashin lafiya”

    “Subhanallah, waye ya saki kamun kunne kuma?”

    “Mai sunan Baba ne”

    “To ki yi haƙuri, yanzu dai zan ɗibi jininki na yi miki gwaji, in duba meye ya haddasa zazzaɓin”

    Ɗiban jinin da za’a yiwa ruma, tamkar za a cire mata ido, ta dinga kurma ihu, tana fizge-fizge, ga ta da shegen ƙarfi, da ƙyar Aliyu ya riƙeta aka ɗebi jinin nan.
    Kuka har da majina, Aliyu ya dinga dungure mata kai yana zaginta.

    Ya gama gwaje-gwajen da zai yi mata, ya ce “Malaria ce ke damunta, dan haka akwai buƙatar ayi mata allurai, da kuma magunguna”

    Ruma ta yi masa zuru da ido, tana jiran ta ga a ina za ayi allaurar.

    Ya haɗa alluransa ya nufo ta, ta miƙe tsaye.

    “Ke malama ki tsaya, dan ba zaki sake wahalar da ni ba”

    “To a ina za ayi mini allurar?”

    Mai chemist ya ce “Ai a baya ake yin ta”

    “Wai bayana” tayi maganar tana nuna bayanta.

    Nasiru mai chemist ta ce “A’a a mazaunai”

    “Suwaye mazaunan?”

    Aliyu ya haɗe rai ya ce “Ke juya ki tsaya ayi miki allurar nan mu tafi, kin san sarai a in da za ayi”.

    Ta riƙe skirt ɗin ta gam ta ce “Ni wallahi ba zai ganni ba”

    Aliyu ya fizgota, ya riƙeta da ƙyar suka danneta suka yi mata, Aikuwa ta din ga zunduma ihu, kamar sun mata wani abu.

    Haka aka gama yi mata treatment, suka taho gida, ban da uban kuka babu abin da take yi.
    “To subhanallah, ko me aka yi mata kuma take wannan uban kukan haka oho” mama ta yi maganar tana fitowa tsakar gida.

    Aikuwa suna shigowa, ta nufi mama tana kuka.

    “Meye haka, kukan me ki ke haka,ki ke ɓare baki?”

    “Mama yaya Aliyu ne da Nasiru mai chemist”

    “Suka yi miki me?”

    “Bayan ya ɗibar mini jini, kuma suka buɗe mini tsiraici na aka yi mini allura”

    Mama ta ce “Subhanallah”

    “Mama ba ke ki ka ce ɗuwawu tsiraici bane ba, amma har da Yaya Aliyu ya riƙe ni, Nasiru mai chemist ya ganni, wallahi ban yafe ba”

    Mama ta girgiza kai, ta ƙiftawa Aliyu ido sannan ta ce “Haba Haidara, ya zaka yi mini haka, dan me za’a buɗe mata jiki ayi mata allura?”

    Aliyu ya ce “To mama ai larura ce, ko a addinance ba haramun bane”.

    Cikin masifa ta ce “To shi yayana ne da zai ganni? Har da taɓani ya yi mini allura a wurin”

    Aliyu ya ce “Sa’anki ne ni, uban me za a kalla a jikin naki?”

    “Wallahi ba zan taɓa yafewa ba, Allah ya jijjigo bala’in duniya da lahira ya ɗora masa, tun da ya ganan mini tsiraici na”

    Mama ta ce”Innalillahi wa Innalillahi raji’un, wace irin Addu’a ce haka, kar in kuma ji, baki san larura ba?”

    Aliyu ya ce “Sakarya, kamar ba tsairaicin ki ka je kina kaɗawa a gaban mutane ba jiya”

    Umar ya shigo ɗakin mama, suna magana, bai kula ruma ba amma dan ya duba jikinta ya shigo.

    Tana kwance ga zafin ciwo, ga na takaicin allurar da aka yi mata, zafin allaurar bai dameta kamar ganinta da mai chemist ya yi.

    Sai da yamma mama ta sakata ta yi wanka, ta canza kaya ta ɗan ji ƙwarin jikinta.
    Sai da ta kwana uku tana fama, sannan ta ware gaba ɗaya, sai dai rashin lafiyar da tayi ya sanya aka mance da laifin da ta tafka, kowa sai lallaɓata yake, ban da Huzaifa.

    Ta ware sarai har ta koma makaranta, kullum mama cikin nasiha take yi mata, tare da yi mata addu’a da fatan shiriya.
    Tun daga ranar ruma ta daina bi ta hanyar chemist ɗin Nasiru, idan kuwa ta ganshi ko kallonsa ba ta yi, balle ta gaishe shi, a cewarta ɗan iska ne tsairaicin ta ya kalla.

    “Mama wai yaushe zaki haihu ne, babannin ‘yan ajinmu sai haihuwa suke yi, amma ke ban taɓa ganin kin haihu ba”

    Mama ta ce “Ikon Allah, ba gaki na haife ki ba, ai ke ce auta ha zan kuma haihuwa ba, sai dai in kin girma kin haifa na ɗauka”

    “To ni yaushe zan haihun?”

    “Sai kin girma kin yi aure”

    Ruma ta ɗan yi jimm sannan ta ce “To ni so nake na haihu, ina son ƙani ko ƙanwa da zan din ga wasa da su”

    “Ruma ki ka haihu yanzu ai a nemi tsari, sai an yi aure ake haihuwa”

    “To gaskiya mama ni so nake na haihu yanzu”

    Usman da yake jin hirar ta su ya ce “Ke, idan ki ka haihu ba aure tsanarki za ayi, a kore ki daga gidan nan da unguwar ma gaba ɗaya, shi ya sa ba a wasa da maza, ki ka bari namiji ya taɓa ki to ciki zaki ki haihu, kuma korar ki za mu yi”

    Waro ido ruma tayi ta ce “Amma ku kuke taɓani?”

    “Ai mu yayyenki ne, muharramanki ne mu”

    Ruma ta dafe ƙirji ta ce “Allah ya rufa mini asiri, ai da ban sani ba, taɓ idan aka koreni ina zani?”

    “Oho miki dai, wannan damben da ki ke da maza ma, idan ba ki daina ba, sai dai ki ga kin haihu, kuma sai kin bar mana gida”

    Ta yi ajiyar zuciya ta ce “In sha Allah hakan ma ba zata faru ba, ai ni ban san hakan abin yake ba, Allah ya sa na yi tsawo na auri kyakykyawa mai kuɗi”.

    Mama ta ce “Ke zan ci ubanki ke da kyakykyawa mai kuɗin nan, miji na gari ake roƙon Allah, fitsararriya”

    “Ni dai gaskiya bana son mummuna, mai kyau nake so”

    “Ke dalla ware, da wannan munin za ki auri kyakykyawa?”

    “Ni dai yaya Ussy, ka yi mini Addu’a, ka san wa zan aura a cikin ‘yan ball”.

    Miƙewa ya yi ya ce “Ba ni da lokacin jij wannan shirmen na ki”.

    Tun daga wannan lokacin, ruma take kaffa-kaffa, da gudun kar wani namiji ya taɓa ta, saboda kar ta haihu a koreta ta shiga uku, kuma ta san idan aka koreta ba kuɗin mota za a bata ba, balle ta tafi ko ƙauye ne wurin Gwaggo.

    Yau gaba ɗaya mama ta kasa gane kan ruma, tun da ta dawo daga makaranta yanayinta ya nuna kamar tana cikin damuwa.
    Ba irin tambayar da mama ba ta yi mata ba, amma ta ƙi gayawa maman dalilin damuwarta ta, ta ce cikinta ne yake yi mata ciwo kawai

    Mama ta aiki ruma sayen maganin sauro, ta je ta sayo, ta dawo ta tsaya a soro tana kuka.
    Huzaifa ne ya sameta a soron tana kuka, dan sai da ya ɗan tsorota.
    “Ke me ki ke yi a nan?”

    Cikin kuka ta kira sunansa “Huzaifa”

    “Na’am” ya amsa.

    “Ka san wani abu?”

    “A’a sai kin faɗa”

    “Yaya Usyy ne ya ce mini idan namiji ya taɓani, zan yi ciki in haihu, kuma korata za ayi daga gidan nan, sai malam ya aikeni karɓo masa chalk, da na kawo masa hannunsa ya taɓa nawa. Na tambayi ‘yan babban aji na gaya musu abin da yaya ussy ya gaya mini, suka ce eh haka ne wai ciki ne da ni, ka ga cikina ma ya fara kumbura yanzu ya zan yi bana son a koreni dan Allah ya zan yi” ta yi maganar har cikin zuciyarta tana rushewa da kuka.

    Huzaifa a ransa ya ce ‘Alhamdilillah, na samo maganinki’

    “Tabbas Deluwa kin kwaso mana abin kunya, yanzu abin da zai faru shi ne, ki haɗa kayanki a ɓoye, cikin dare na kai ki tasha ki bar gidan nan, dan idan mai sunan Baba ya sani sai ya jefa ki a rijiya”

    Sake rushewa ta yi da kuka har da majina, ya yi saurin cewa “Sai mama ta jiyo kina kuka asirinki ya tonu ko?”

    Ta goge hawanyeta ta ce “To ya zan yi?”

    “Shikenan, zan rufa miki asiri, amma zaki din ga yi mini wankin uniform”.

    “Eh na yadda, amma dan Allah kar ka faɗawa mama, bana son a koreni dan Allah”

    Huzaifa ya yi wani murmushi cikin mugunta ya ce “To na ji, goge hawayen ba zan tona miki asiri ba”

    Abu kamar wasa, ruma ko abinci ba ta iya ci, gashi kullum sai ta wanke wa Huzaifa kayan uniform.

    Mama ta gaji ta ritsa ruma, har da bulala sannan ta zauna ta yiwa mama bayanin abin da yake damunta.
    Mama ta yi salati ta sanar da Ubangiji, gaba ɗaya ruma ba ta da wayo, ga shegiyar tambaya idan kuma ka yi mata bayani yadda za ta fahimta, nan ma ta yi wata kwaɓar.

    Sai da mama ta yi da gaske, sannan Ruma ta yadda ba ta da ciki, dan har da nunawa mama cikinta wai ya kumbura ɗa ne a ciki.

    ******

    Ta na zaune a kan sallaya ta idar da salla, sai dai ta lula duniyar tunani, ba lazamin take yi ba.

    Kamar daga sama ta ji ana kiran sunanta, ta yi firgigit ta dawo hayyacinta.

    “Ohh Nusaiba, an gama girkin daren ne?”

    Nusaiba cikin damuwa ta dubi Ammi sannan ta ce, “Ammi, tunanin me ki ke yi haka ne? kin san fa ba ki da cikakkiyar lafiya”

    Ammi ta yi ajiyar zuciya ta ce “Nusaiba tunanin nan na dole ne, shi yake yin kansa, abubuwa sun yi mini yawa, bana son na nuna gazawata amma ni na san na gaza na kasa shawo kan komai, al’amura na ta ƙara dagule mini”

    “Me kuma ya faru ne?”

    “Mahmud, lamarinsa yana damuna, ga kuma yadda aka addabawa yarinyar nan a cikin gidan nan, haƙurina ya fara ƙarewa, duk wanda ya taɓa Iman ni ya taɓa raina ya na ɓaci fiye da tunaninki”

    Nusaiba ta gyara zamanta ta ce “Ammi, kin san wannan duk shirin Mummy ne, so take ki magantu ku raba abin faɗa a cikin garin nan, ita take buga miki wannan wasan, ki ƙyaketa kuma ki yi haƙuri ki ɗauke kan ki daga Mahmud, ba ga takawa nan ba, mu da shi mun isheki rayuwa su je su ƙarata mana”

    Ammi ta girgiza kai ta ce “Nusaiba kenan, ba zaki gane ba, tashi maza ki je ki tabattar an gama komai, sannan ki kira mini Iman, ba na son zamanta ita kaɗai”

    Nusaiba ta ce “To shikenan Ammi, bari na je”.

    Sannu a hankali yake tafiya, tamkar ya na tausayawa ƙasar da yake takawa, har wani rangaji yake kamar wanda ake yiwa kiɗa.
    Fuskar nan a murtuke babu annuri, in da ya sa a gaba kawai yake kallo, yake burin cinmma. Babu tsammani suka yi kiciɓis a baranda, ba tare da ɗaya ya san ɗaya ya taho ba, kuma aka rasa wanda zai bawa wani hanya ya wuce.
    Kallon-kallo suka yi na wani ɗan lokaci, sannan ya lumshe idonsa a hankali ya buɗe. “Banihanya”
    Kallonsa ya yi irin kallon ba ka isa ba ya ce “Ni da kai waye ya tarewa wani hanya?”
    Cikin tsawa da zafin zuciya ya ce “Ka bani hanya na ce”
    Murmushin gefen baki yayi, tare da rausayar da kai, yayi taku biyu ya koma gefe ya bashi hanya.
    Sai da ya ƙare masa kallo, kamar ba zai wuce ba, sannan ya cigaba da takawa sannu a hankali ya wuce.
    Ya waiwaya ya bi bayansa da kallo, yayi wani murmushi sannan ya ce “Zamu ga wanda ya fi iya buga wasan sa”
    (A mini afuwa ban editing ba)
    AYSHERCOOL
    08081012143
    [19/07, 8:42 am] JAKADIYAR AREWA: ƘANWAR MAZA
    Na Aisha Adam (Ayshercool)

    MIKIYA WRITER’S ASSOCIATES

    https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

    Ku yi subscribing  YouTube channel ɗin
    @Cool Hausa Novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro.

  • Kanwar Maza 17

    Kanwar Maza 17

    P 17

     

     

    *MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

    *SHI YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR  DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA? TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN FATA NE? KO KUWA SO KI KE FATARKI TA DIN GA SHEƘI TA NA HASKAWA? MAZA KI GARZAYO WURIN MEENA DOMIN SAMUN MAFITA*

    *Royal jelly big 22000*
    *Royal jelly 30 pieces 2200*
    *Royal jelly small one 60 pieces inside the pack 3000*
    *Vitamin C-100, 2700*
    *Vitamin E big 3000*
    *Pesona 2300*
    *Dara 2300*
    *Cantik ayu 2300*
    *GLUTA white 2700*
    *Khusus ibu 3800*
    *Sugar wanita 3500*
    *Majakani 3 in 1 3200*
    *Eve Care 3700*
    *Juliet eve 11,500*
    *Phyton buster 18,000*
    *Phyton collegen 18,000*
    *Glute sparkling 18,000*
    *7 days ginger oil for hair 1,200*
    *Papaya oil for breast 1,200*
    *Garlic oil for hips 1200*
    *Vitamin C serum 1,500*
    *Vitamin E serum 1,500*
    *Busty blend 2800*
    *Gluta prime 2800*
    *Collegen+C 3800*
    *Yan uwa abun fa da yawa bazan iya kawosu gaba daya ba amma muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*

    https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
    *Wai ina da ku fans, ace haryanzu ban haɗa 1k subscribers a channel ɗina ba, anya akwai amana kuwa😒*

    Ku yi subscribing  YouTube channel ɗin
    @Cool Hausa Novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro.

    *Ina yiwa ‘yan uwa musulmi barka da shigowar, sabuwar shekara musulunci, Ubangiji Allah ya sada mu da alkhairan da yake cikinta, akasin haka kuma Allah ya iya mana*

     

    Shiru ta yi ta kasa cigaba da maganar, ta zuba masa ido ta na jiran ta ji mai zai ce.
    Ya tako a hankali ya zo gabanta ya tsuguna, ya na kallon idonta. Cikin sauri ta sunkuyar da kan ta ƙasa, tana jin yadda abincin da ta ci ya tsaya mata a ƙirji, ga wani irin ƙugi da cikinta yake yi mata saboda tsoro.

    “Aure ko, shi ki ke so?” Da sauri ta girgiza masa kai alamar a’a.

    “Ki je ki dawo daga makarantar, za mu yi magana in dai aure ne baki da matsala, za’a aurar da ke tun da shi ki ke so” da sauri ta ɗago, ta kalleshi za ta yi magana, amma ya sanya yatsansa a kan leɓensa ya ce “Shhh, tashi ki wuce ki tafi makaranta”
    Kamar wadda aka gayawa mummunan saƙo, jiki babu ƙwari ta bar gidan ta tafi makaranta, sai dai kamar ta faɗi a hanya, dan jefa ƙafarta kawai take yi, maganar mai sunan Baba ta tsaya mata da yawa.

    ***
    Samha ce zaune a kan gado, hannunta riƙe da waya, ɗaya hannun kuma tana wasa da gashin kanta, amma hankalinta ba a kan wayar ba, zancen zuci take yi.
    Ƙarar buɗe ɗakin ne ya dawo da ita hayyacinta.
    Fauziyya ce ta shigo, ta ajiye jakarta ta zauna a kan gadon, ta dubi Samha ta ce “Ke jiya ki ka shanya ni ina jiranki, amma ki ka ƙi zuwa”
    Samha ta ɗan lumshe ido, ta buɗe tare da ajiyar zuciya.

    “Ke wai meye haka ne?”

    “Ke bari kawai”

    “Ban gane in bari ba, kin san ba ma ‘yar haka da ke, explain kawai madam”

    Samha ta dubi Fauziyya ta ce “Jiya na je mun haɗu da gayen nan fa”

    Fauziyya ta waro ido wace ta ce “Ki na da hankali kuwa? Mutumin da baki sani ba ki ka je wurin sa?”

    “Eh tare da security na je, sai dai ban bari ya sani ba, kin san waye ma tukuna?”

    “A’a, sai kin faɗa”

    “Khalifa Usman wakili”

    “Meye haɗinki da shi? Ko ya na ciki ne?”

    Samha ta yi tsaki ta ce “Ke ba wannan ba, wai yayi bincike a kaina, so yake na taimaka masa ya kai takawa ƙasa, saboda yana barazana ga feature ɗin sa, da mahaifinsa”

    Fauziyya ta zaro ido ta ce “Yaya Adam dai?”

    “Shi fa”
    “To me ki ka ce masa?”

    “Fauza, kin san ina son Adam, ba zan goyi bayan a cutar da shi ba, dan haka nace masa ba zan iya ba, kar kuma ya sake nemana”

    “To meyasa?”

    “Fauza yayanki ne fa, kuma kin san abin da yake zuciyata game da takawa”

    Fauziyya ta jinjina kai ta ce “Na san yayana ne, amma ke yanzu haryanzu ki na nan a kan bakanki kina son sa, ana barin halak dan kunya fa”

    “Ke ki ka san ta, ita halak ɗin, bari na shiga wanka” ta yi maganar tana miƙewa.

    Ɗan shiru Fauziyya ta yi, ta fara zancen zuci ‘wannan ai wata damar ce ga Mummy, tabbas Khalifa wakili zai yi wa mummy amfani’ da hanzari Fauziyya ta tashi ta fice daga ɗakin.

    ***
    Yau wunin ranar ruma ba a hayyacinta take ba, duk ta rasa abin da yake yi mata daɗi. Allah ya taimaketa mai sunan Baba bai dawo ba sai dare, tun da ya dawo ta rasa sauran nutsuwarta, tana jiran mai zai ce mata.
    Sai da ya gama abin da yake, har ta kwanta ta fara bacci, ta ji ana dukan gefen katifarta.
    Gabanta ne ya faɗi da ta yi tozali da shi, ta tashi zaune tana rarraba ido.
    Da hannu yayi mata nuni da ta fito ta biyo shi.
    Haka ta fito ya na gaba tana baya, zuwa tsakar gida.
    Ya ja kujera ya zauna, ita kuma ta zauna a ƙasa tana sunkuyar da kai.

    “Ɗago ki kalleni” ya faɗa a kausashe, amma ta kasa ta sake sunkuyar da kanta ƙasa.

    “Aure ki ke so ko?” Nan ma ba magana sai girgiza kai.

    “Shikenan, na fahimta na baki nan da kwana uku, ki kawo wanda zaki aura ɗin, ranar juma’a in Allah ya kaimu sai a yi miki auren kowa ya huta”

    Da sauri ta ɗago ta kalleshi, “Wallahi yaya ba haka nake nufi ba, wallahi ba aure nake so ba”

    “Ƙarya ki ke yi, baki da aiki sai zance da tambayoyin batsa, aure ki ke so”

    “Wallahi a’a, ban san batsa nake tambaya ba”

    “Na gaya miki, sai kin fito da miji, ranar juma’a za a ɗaura miki aure”

    “Wallahi bani da saurayi, saurayina bai sanni ba”

    “A ina saurayin naki yake?”

    “A cikin tv nake ganinsa, ɗan wrestling ne, amma ban san a ina yake ba”

    Mai sunan Baba ya kalleta ya ce “To tun da baki da saurayi, ni zan nemo miki, ba har da mafarki ana bikinki ba, to saƙonki ya isa za ayi abin da ki ke so”

    “Wallahi yaya ba haka nake nufi ba”

    “To ya ki ke nufi? Da kunnena fa na ji ki na cewa, ayi miki aure ayi addu’a ki yi tsawo ayi miki aure, tukuna ma me ake yi a auren da ki ke son auren?”

    Cikin kuka ta ce “Wallahi ban sani ba”

    Ya sake tsuke fuska ya ce “Ƙarya ki ke yi, sai kin gaya mini ko na taka cikinki a wurin nan”

    “Wallahi ban sani ba, ‘yan ajinmu na islamiyya dai sun ce ana soyayya, kuma ina son in ga an sai mini kujeru da kuma sabuwar katifa”

    “Wace irin soyayya?”

    “Wallahi ban sani ba, na ji dai suna cewa, soyayya ta na da daɗi, kuma ana soyayya idan an yi aure, shi ya sa nake son na yi saurayi na ji me ake a soyayyar, amma wallahi ba aure nake so ba”.

    Ya yi ajiyar zuciya ya ce “Shikenan, yanzu dai tun da baki da saurayi, ni zan samo wanda nake so na aura miki, tashi ki je ki kwanta, ranar juma’a ɗaurin aure”

    “Innalillahi wa Innalillahi raji’un, dan girman Allah ka yi haƙuri, manya ake yiwa aure ban da yara”

    Cikin zafin rai ya ce “Ni zaki gayawa abin da zan yi, tashi ki bani wuri” jiki na rawa ta tafi ɗaki, tare da fashewa da kuka.
    Gaban mama ta je tana kuka ta ce “Mama dan Allah ki saka baki, wai aure mai sunan Baba zai yi mini”

    “To ai haka ki ke so ruma, Allah ya sanya alkhairi, duk wanda ya zaɓa miki shikenan”

    “Innalillahi wa Innalillahi raji’un, dan Allah mama ki saka baki, wallahi wasa nake yi, ni ba da gaske nake ba wallahi”

    Mama ta ce “Maganarku ce ke da shi, babu ruwana, ni gafara nan na kwanta, gobe in Allah ya kaimu na tafi kasuwa na fara yi miki sayayya”

    Mama tayi kwanciyarta ta bar ruma, kuka wiwi kamar ba gobe, haka ruma ta din ga yi, ƙarshe a nan wurin bacci ya kwasheta.
    Da safe kuwa wasan ɓuya aka shiga yi tsakaninta da mai sunan Baba, taƙi yadda su haɗu, ko karyawa ta kasa yi, haka ta tafi makaranta.

    Ruma fa gaba ɗaya hankali ya tashi, ta rasa nutsuwa ko maganar kirki ba ta iya yi, tamkar wadda wani mummunan abu ke shirin faruwa da ita.
    Mama tana kallonta, abinci sai dai ta cakala idan ta ɓuya sai kuka, duk ta rasa sukuni.
    Mama ta shiga banɗaki ta lallaɓa ta ɗau wayarta, ta kira Abubakar.
    Yana ɗagawa ta fashe masa da kuka, har sai da gabansa ya faɗi “Ruma, menene? Meyafaru?”

    “Yaya, mai sunan baba ne”

    “Me ya same shi, me ya yi miki?”

    “Wai aure zai yi mini, dan Allah ka yi masa magana, mama taƙi hana shi, dan Allah ka ce masa ni yarinya ce, dan Allah kar ayi mini auren nan bana so”

    Cikin rashin fahimta ya ce “Wani irin aure kuma?”

    “Haka ya ce wai ranar friday zai mini aure da wani, dan Allah ka hana shi”

    “Kwantar da hankalin ki ‘yar gudaliyar, zan kirashi in sha Allah, ki daina damuwa”

    “A’a ba zan iya dainawa ba, ka kirashi yanzu kawai”

    “To an gama, kiyi haƙuri babu mai yi miki wani aure yanzu”.

    Ya yi ta kwantar mata da hankali, har ta samu ta ɗan nutsu.

    ***
    Yana zaune a falo, yana duba labarai a wayarsa, Mummy na gefe tana shan fruit, ta kalli yadda ya sha fararen kaya, da shuɗiyar alkyabba hannunsa ya sha zobbunan azurfa, sai kaɗa ƙafa yake a hankali.

    Ta yi murmushi ta ce “Ka ga kyan da ka yi kuwa? Sai ka fito a basaraken ka na asali jinin galadima, Allah ya kawo gingimemiyar kujera”

    Bai kalleta ba ya ce “wace irin kujera ce gingimemiyar?”

    “Ka gaji Galadima mana, ko ma kujerar garin gaba ɗaya”

    Mahmud ya ce “Mummy you are funny, ni fa sabgar sarautar nan ba ta dameni ba, ki bar ni da karatuna, na kammala na samu aikina period, shi dai da yake ta zazzare ido, na san bai wuce a kan sarautar ba, sai ya je yayi ta yi”

    Cikin mamaki ta kalli Mahmud ta ce “Mahmud, wai kai meyasa ba ka da kishin zuci ne, sarautar nan fa taku ce, ta mahaifinku ce gaba ɗaya a ka ɗauka aka kai wani gidan, kuma muna saka ran za ta dawo mana, tun da galadiman yanzu shi ma yana can babu lafiya, kuma da zarar ya mutu babu batun wani ya gaje shi, tun da duk ‘ya’yansa mata ne, Jabir kuma bai isa ya saka rai ba, dole gidan nan za ta dawo. Dan haka ba zan zuba ido a bawa Adam sarauta bayan ga ka ba, kai ma ɗan galadima ne, dan haka kai ma ka cancanci ka gaji sarauta”.

    Mahmud ya ɗan yi shiru ya na tunani, amma bai ce komai ba.

    “Mahmud, kar ka watsa mini ƙasa a ido, idan ba haka ba, haka fa zamu cigaba da zama Giwar Galadima ta mamaye komai, ta cigaba da juyamu yadda take so, yaka ke gani idan sarauta ta dawo Adam ya samu, kai menene naka, a wani babin ka tashi?”

    Ajiyar zuciya Mahmud ya yi, ya fesar da iska daga bakinsa, ya kalli agogon hannunsa sannan ya kalleta ya ce “Mummy, zan je salla daga nan zan ɗan shiga gari, sai na dawo” yana gama maganar ya miƙe a hankali ya bar falon.

    Fauziyya da ke laɓe take jin su ta fito, ta nufi wurin Mummy ta zauna tana murmushi ta ce “Hajiya Mummy, mai abubuwan ban mamaki, irin wannan famfo haka?”

    Mummy ta yi murmushi ta ce “Ai ba ayi komai ba ma tukuna, dole sai na sakawa Mahmud ƙawazucin kujerar nan, yaron nan akwai baƙin taurin kai, ɗan uwan ɗayan ne a taurin kai, tun da ƙuruciya nake kwaɗaita masa daɗin mulki, amma yaƙi ganewa, amma zan cigaba da gwada masa fa’idar ace mulki yana hannunsa, in sake rura wutar ƙiyayya a tsakaninsa da Adam, kuma in toshe kafar da sarautar za ta dawo gidan nan, dan ita ma Hajiya Lubabatu kwaɗayi take na ta ɗan ya gaji sarautar idan mahaifinsa ya mutu”
    Fauziyya ta jinjina kai ta ce “Mummy kenan, akwai lissafi, na zo miki da wani labari ne mai daɗi”

    “Wani labarin kenan?”

    “Khalifa Usman wakili, kin san case ɗin su da takawa, kusan shi ne yake trending a media yanzu”

    Mummy ta jinjina mata kai.

    “To dai in gaya miki shi ne ya gayyaci Samha, wai yana son su haɗa kai, su kawo ƙarshen yaya Adam, ita kuma ta ce bata yadda ba, kin san son shi take yi”

    “Eh, na sani, ai itama Samha wata makami ce da nake amfani da shi ta ƙarƙashin ƙasa, amma labarin nan yayi mini daɗi sosai, ke dai ku cigaba da baza kunnuwa, duk abin da ku ka ji, ko kuka gani kawai ku sanar da ni”

    “In sha Allah Mummy, Allah ya ida nufi”

    Suka yi murmushi gaba ɗaya.

    Takawa ne zaune a wani ƙaton falo, mai ɗauke da kayan ado na gidan sarauta, gefe gud kuma tarin litattafai ne a jere a cikin wata drower.
    Ya sanya system a gaba, yana dannawa yana ɗan juyi a jan kujerar da yake kai.
    Jabir na zaune a kan kujera yana facing ɗin sa. Jabir ya tattara nutsuwartsa a kan Adam ya ce “Takawa, kana bibiyar shafukan sada zumunta kuwa?”

    “Meyafaru?”

    “To ai gani na yi ka yi burus, kamar baka bibiyar meke faruwa”

    “Shi ya sanya na tamabayeka, meyafaru?”

    “Tone-tonen da ka ke ƙoƙarin yiwa Senator usman wakili, akwai ƙura fa sosai da sosai”

    Ya ɗan ɗago ya kalli Jabir ya ce “Ai ni ƙurar nake son ta tashi, ta hana kowa nutsuwa, saboda haka nake wannan aikin”

    “Duk da haka, ko dan tsaron kannka da lafiyarka, yakamata ka san yadda zaka din ga gudanar da ayyukan ka, taɓa manyan nan ba abu bane ba sauƙi ba fa”

    Adam ya yi murmushi ya ce “Na fahimce ka mutumina, kar ka wani damu, ka tayani da addu’a kawai, amma dole mu yi wa ƙasarmu hidima”

    Jabir ya jinjina kai ya ce “Haka ne”.

    ***

    Bil haƙƙi mai sunan Baba ya nunawa ruma aure zai yi mata, ya je ya a sayo sabuwar katifa ta ‘yan makaranta, ya ce wa mama gata nan a ajiye ta ruma ce, ya sayo kwano da kofin silba mai murfi da sabuwar buta, shi ma ya ce na ta ne.
    Hakan ya ƙara dugunzuma hankalinta, cikin dare mama ta na bacci ta ga ruma tana shimfiɗa sallaya tana kuka.

    Mama ta ce “Ke lafiyarki kuwa?”

    “Sallar dare zan yi, na roƙi Allah a kan mai sunan Baba, tun da kin ƙi ki hana shi, an rasa wanda zai hana shi yi mini aure”.

    Mama ta yi murmushi ta ce “Ke fa ki ka ce kin ji kin gani, ki yi addu’a kawai Allah ya baki zaman lafiya da ke da wanda zai aura mikin”

    Zaman dirshan ruma tayi, ta ɗora hannu a ka tana kuka, mama ta rufe fuska tana yi mata dariya ba tare da ta sani ba.

    Ruma ta daɗe a sujjada tana addu’a, sannan ta koma ta kwanta.

    A islamiyya kuwa, malamin ajin da take ne, ya lura yana ƙari tana kuka, dan yanzu a ɗan samu cigaba, ta daina guje-gujen aji, a babban aji da ajin su Yasir take zama, kuma yanzu tana iya karatu ba kamar da ba.

    Sai da ya kammala ƙarin Alqur’ani, sannan ya kira ruma yana tambayarta me ya sa take kuka?
    Ba ta gaya masa ba, ta ce mai babu komai, ƙarshe sai ƙyaleta yayi.

    Ranar juma’a kuwa da farar safiya da kuka ta tashi, dan yau ne kwanakin da mai sunan baba ya ɗibar mata suka cika, ba tare da ta samu wanda za ta kawo ba, a matsayin wanda take so, to ita wa ma take da shi.

    Mama sai fama take da ita ta shirya ta tafi makaranta, amma ta rungume uniform ɗin tana kuka.
    Umar ya fito fuska a haɗe ya daka mata tsawa, cikin tsuma ta hau saka kayan ba tare da ta yi ko wanka ba.

    “Ki fice ki tafi makaranta, idan kin je can sai ki yi musu kukan, shi ne ki ka gayawa ɗan uwa wai zan yi miki aure ko? To shi ma bai isa ya hanani abin da na yi niyya ba, ai ke ki ka nuna ki na son auren, wuce ki bawa mutane wuri”

    Kamar korarriya, ta ɗau jakarta ta tafi makaranta.

    Bayan fitarta, mama ta kalleshi ta ce “Babana, a sassauta mata ta horu haka, kwanaki uku kenan ba ta ko cin abinci, ayi mata afuwa babana”

    “Ƙyaleni da ita, horata kawai nake, amma yau zan ƙyaleta in sha Allah”

    Ƙin shiga makarantar ta yi, ta tsaya a waje tana kuka, mai gadi ne ya ganta, ya ja ta ya kaita ofishin Headmaster, ya sanar masa da a waje ya ganota ta tsaya ta na kuka.

    Headmaster ya ce “Ai ni rigimar yarinyar nan nake tsoro, ke me aka yi miki?”

    “Yayana ne ya ce zai yi mini aure yau”

    Waro ido ya yi ya ce “Aure kuma? Waye zai kwasa? Ke bana son wasa”

    “Wallahi haka ya ce”

    Headmaster ya kalli ruma, sai ya kawo ko rashin hanklin ruman ne ya motsa, dan haka ya ce “To shikenan, ki yi haƙuri ki tafi aji, zan kira gidan na ku mu yi magana da su” yayi ta lallaɓa ruma ya kaita aji.

    Ba ta sake tsinkewa da lamarin ba, sai da ta dawo gida ta tarar mama tayi tuwon shinkafa da miyar taushe, da wainar masa wai azo a kai maƙwabta ace na auren ruma ne, mai sunan Baba ya ci farar shadda ya fito tsakar gida ya ce “Mama, idan an idar da sallar juma’a za a ɗaura mata aure, sai ayi mata addu’a”

    “Na shiga uku, mama wai da gaske ne? Mama ku yi mini rai ban isa aure ba wallahi”

    Wani mugun kallo ya yi mata, ta shige ɗaki da gudu tana kuka, ya fice ya bar gidan.
    Dariya Huzaifa ya din ga yi mata yana “Ruma, Allah ya sanya alkhairi zan kawo miki goron ɗaurin aurenki har gida ki tauna, dan mijin naki ma tsoho ne, malam labaran ladan ne”

    Ruma sam ba ta shiri da malam labaran ladan, saboda ya taɓa tsula mata carbi, wataran yana kiran salla, ta taɓa tsayawa a ƙofar masallaci tana  kiransa da ƙarfi, wai saboda muryarta ta fito a sufika, ya idar ya kamata ya zane ta da carbi, gashi tsoho sosai.

    Mama ta shiga ɗaki ta tarar da ruma sai rizgar kuka take.

    “Haba amarya, ya da kuka kuma kamar ba amarya ba?”

    “Dan Allah mama ki bani kuɗin mota na gudu”

    Mama ta kwashe dariya ta ce “Dama ruma akwai abin da zai baki tsoro haka?”
    Rungume mama tayi cikin kuka ta ke faɗin “Dan Allah mama kar ayi mini aure, wallahi na daina rashin ji, ina sonki sosai, bana son na rabu da ku, mama zaki yadda a aura mini wanda ya dakeni dan Allah mama ki hana shi aurar da ni”

    Rungumeta mama ta yi tana murmushi, tausayin ruma ne ya kamata, dan har ramar dole ta yi, saboda damuwa.
    Mama ta zubo mata abinci, ta zaunar da ita ta bata, amma ruma taƙi ci.

    Mai sunan Baba suka yi sallama, duk suka shigo a tare daga sallar juma’a, duk sun sha kwalliya.

    Aliyu ya ce “Amarya kin sha kuka, to Allah ya sanya alkhairi” ta rirriƙe mama tana girgiza kai tana zubar da hawaye.

    Mama ta kalli mai sunan Baba ta ce “Tuba muke babana, Allah ya bada haƙuri duk ta rame, ayi haƙuri”

    Yasir ya ce “Haba mama, ya zaki yi mana haka?”

    Mama ta yi masa daƙuwa tana harararsa.

    Umar ya ƙarasa gaban ruma da ta takure a jikin mama, tana share hawaye.

    “Kalleni” yayi maganar yana tsareta da ido.

    Ta ɗago a hankali ta kalleshi, idanunta sun yi jawur.

    “Daga rana mai kamar irin ta yau, idan na sake jin ki aikata wani abu na rashin mutunci, ko wannan shegen surutun naki, to ki tabattar aure babu fashi, kin ji na gaya miki?” Wata irin ajiyar zuciya ta sauke tana sake rungume mama.

    Mama ta ce “To madalla godiya muke, Allah ya rayaki, ya kaimu auren ki na gaske, da miji na gari ko?”

    “Ni ba zan aure ba, bana so da ma da wasa nake, kuma ba zan auren ba”

    Mama ta ce “Tashi ki yi godiya, tun da dai ya janye maganarsa”

    “Na gode” tayi maganar tana ɓoye fuskarta.

    Tashi yayi ya bar ɗakin ba tare da ya ce mata komai ba, ta din ga sauke ajiyar zuciya ta ce “Amma an shiga hakkina, Allah zai sakawa marainiya”

    Yana tsaye a bakin ƙofa, karaf maganarta a kunnensa.

    (BOOK 1 FREE NE, BOOK 2 PAID, BOOK1 YA KUSA KAMMALA IN SHA ALLAH, GODIYA TA MUSAMMAN GA MASU BIBIYAR LITTAFIN ƘANWAR MAZA)

    Ayshercool
    08081012143
    [29/07, 7:26 pm] JAKADIYAR AREWA:                    ƘANWAR MAZA

    Na Aisha Adam (Ayshercool)

    MIKIYA WRITER’S ASSOCIATES

  • Noor Al Hayat 74

    Noor Al Hayat 74

    A hankali khadijah ta koma ta kwanta, bata kara minti biyar ba bacci ya dauketa. Da asuba tana jin fitansu tare da Shureim xa su masallaci, ita ma ta mike ta shiga bayi, tana xaune kan darduma tana azkar taji shigowarsu gidan, bude kofar dakinta Aliyu yyi suka shigo tare da Shureim, kallo daya tayi masu ta dauke kai, ya xauna gefen gado Shureim ya nufe ta ya durkusa gabanta yace “Anty ina kwana?” Tana kallonsa tace “How was ur nyt?” Ya wara ido yace “It was cool Anty” Bata ce komai ba ta saci kallon Aliyu suka hada ido, d’an murmushi yayi a hankali yace “Good morning Iman” sunkuyar da kanta tayi bata ce komai ba, ya mike ya nufi kofa Shureim ya bi bayansa da sauri ta bi su da ido har suka fita, ta fi minti ashirin xaune ganin gari ya fara washewa ta mike, tana sane jiya babu abinda tayi a gidan, yau kam ta sauka parlor ta share ko ina ta goge, ta shiga kitchen ma ta gyara ta goge, tana kokarin sa turaren wuta a burner aka danna bell, mikewa tayi tana kallon kofar, ta wuce sama da sauri don dauko hijab ta dawo ta bude, Baby ce tsaye da breakfast, Khadijah ta langwabar da kai tace “Don Allah daga yanxu kar ki sake kawo abinci xan yi girki muna ba Mumy wahala…” Baby ta wara ido sai kuma tayi dariya tace “Xa dai ki girka abinda xa ki ci, tunda nasan ba bama yayana xa ki yi ba, yaron ki kam nasan shi ma xa ki basa, Abbansa dai ne baxa a bai ma ba” tabe baki khadijah tayi ta bata hanya ta shigo ta ajiye abincin nan parlor tace “Da fatan kun tashi lafiya, yau naga har da su gyare gyaren gida meye sirrin Iman?” Tana murmushi da tsigar tsokana ta kare maganar, khadijah ta hade rai tace “Wani irin sirri?” yar dariya Baby tayi tace “Oho, ni dai xan wuce, a gaida min yayana” Daga haka ta nufi kofa khadijah ta bi ta da kallo har ta fita sannan ta tabe baki, ta koma ta ci gaba da abinda take, dinning ta kai breakfast din ta ajiye sannan ta wuce sama ta shiga daki, nan ma ta gyara gadonta tayi goge goge kafin ta shiga wanka, tana xaune gaban mirror bayan ta fito wanka tana shafe shafe aka bude kofar bedroom din, xaro ido tayi tana gyara towel din jikinta, ganin Shureim ne ya shigo ta sauke ajiyar xuciya, ya iso kusa da ita yace “Anty am hungry” tace “Me ya hana uncle din baka breakfast” Ya buda hannu yace “He told me I shud come to you ki bani” Tana shafa mai a kafarta tace “Shi me yake yi?” Shureim ya matso cream din xai shafa mata ta 6alla masa harara tace “Ina wasa da kai koh?” Ya mike yace “Anty taya ki xan yi” toes dinta ta mika masa tace “Toh shafa a nan” ya durkusa yana shafa mata tace “Tambayar ka nayi me uncle din yake?” Ya kalleta yace “He is lying down” shiru tayi bata ce komai ba, a hankali yace “Anty yace min he is not feeling fine” Kamar baxa ta ce komai ba sai kuma tace “What’s wrong with him” Yace “I don’t know” Tace “Je parlor ka jira ni in sa kaya sai in xo in baka breakfast” yace “Toh” sanann ya fita dakin, mikewa tayi ta dau atamfar da xata sa na riga da skirt, sosai dinkin yayi mata kyau tayi simple dauri na dankwali ta sa eye pencil a idonta sai chapette ah two colored lips dinta, sosai tayi kyau, ta fesa turare daga karshe ta fita dakin, har xata sauka stairs sai kuma ta tsaya, ta fi minti biyu tsaye kafin ta karasa kofar dakinsa a hankali ta bude, kwance ta gansa ya rufa da duvet har kansa, ta sauke idonta kasa ta karasa dakin kamar mai counting steps dinta, tana ta tsaye kusa da gadon tana kallonsa, a hankali ta durkusa dab da shi ta cire duvet din fuskarsa, idanuwansa a lumshe suke, ta kai hannu forehead dinsa, lkci daya ya bude idonsa tayi saurin dauke hannunta ta koma baya, kasa tashi tayi kuma bata yarda sun kara hada ido ba ta fara kame kame, kallonta kawai yake, ta dago daga karshe tana kallonsa a hankali tace “Are you sick?” Ya mike xaune yace “No…. am alright” shiru tayi tana kallonsa, ya sauka daga kan gadon ya nufi bayi ta bi sa da kallo don kana ganinsa kasan karfin hali yake yi, Mikewa tayi a hankali ta nufi kofa ta fita dakin, kwance ta ga Shureim ya kunna cartoon yana kallo parlorn yana ganin ta yyi saurin kashe tvn da remote din hannunsa, ta tsaya tana kallonsa tace “Who asked you to switch on the tv?” Shiru yyi yana kallonta, ta wuce dining ta hada masa shayi a cup ta debar masa dankali da kwai da plantain, sannan ta yankar masa bread karami ta daura gefen plate din Irish din, tace “Zo ka xauna nan Shureim” ya taso ta ja masa kujerar dinning din ya xauna ta ajiye masa abincin a gabansa sannan ta koma kitchen ta dauko wani cup din ta dawo ta hada wani shayin, ta debi Irish da kwai a plate, ta dauko wani bowl ta xuba pepper soup na kayan ciki, gaba daya ta daura su kan tray ta dauka ta wuce sama, a hankali ta tura kofar dakin nasa, xaune ta gansa gefen gado ya rike kansa, jin an bude kofa ya dago yana kallonta, kanta a kasa ta iso har kusa da shi ta ajiye tray din ba tare da ta kallesa ba ta mike ta fita dakin. Dining ta koma gun Shureim ta xauna kujerar kusa da na shi ita ma ta hada shayin, a hankali take sha har ta gama, tuni Shureim ma ya gama ya mike pleadingly yace “Anty plss in kunna tv?” Kai ta gyada masa ya juya ya wuce parlor, ta kwashe duk abinda suka bata ta kai kitchen ta wanke sannan ta fito, sama ta wuce ta bude bedroom din Aliyu, kwance ta gansa ya kara rufa da duvet, ta karasa tana kallon breakfast da ta ajiye masa, Bata san lkcn da ta xauna gefen gadon ta yaye duvet din tana kallonsa da damuwa tace “Baka yi breakfast din ba? What’s wrong with you?” Ganin bai bude ido ba kuma bai ce komai ba ta kamo hannun sa da damuwa tace “Talk to me plss” bude ido yyi ya mike xaune, ta dauko cup din shayin da ta rufe ta bude tana mika masa tace “Gashi ka sha sai ka sha magani” karba yyi xata dauko plate na irish ya dakatar da ita “Noo I will take this first” da kyar yyi maganar, ta dago tana kallonsa ya kai shayin baki kamar wanda xai sha magani, kadan ya kurba ya cire a bakinsa, tace “Da zafi ne?” yana girgixa kai ya mika mata, ta hade rai tace “Me xan yi da shi?” Xai ajiye kasa tayi saurin cewa “Kar ka ajiye shi, u better force ur self to drink it…” Bai saurareta ba ya ajiye ya mike ya nufi bayi da sauri, a sanyaye ta mike bi sa da kallo, tana ta tsaye ita dai bata ji yana amai ba kamar ynda tayi tunani, can dai ta bi bayansa, jingina tayi da kofa tana kallonsa ganin aman yyi har ya wanke wajen, ya juyo xai fita bayin ta rikesa a hankali tace “Let me make you water sai kayi wanka” yana gyada kai yace “Finish first” daga haka ya fita, ta hada masa ruwan ta fito, kwance ta samesa ya kara rufe kansa, ta cire duvet din da damuwa tace “Kayi wankan sae mu je asibiti” da kyar ta samu ya mike xaune, tana ta kallonsa ganin har rama yyi, sauka yyi daga kan gadon ya cire jallabiyar jikinsa ta amsa ta ajiye sannan ya wuce bathroom, sai a sannan ta fita dakin a sanyaye. zaunawa tayi gefen gadonta tayi tagumi bayan kusan minti talatin ta tashi ta koma dakinsa, dai dai lkcn ya fito wanka daure da towel, tayi saurin juyawa kamar mai neman abu sai kuma ta fita dakin, turo baki tayi ta sauka downstairs ta tadda Shureim yana ta kallo ta xauna kusa da shi. Jin alamar Aliyu na sakkowa stairs ta kalli direction din, kananun kaya ne jikinsa yana rike da makullin mota ya iso parlorn, ta mike tana kallonsa tace “Where are you going to?” Bai ce komai ba, ya nufi kofa, ta isa gabansa ta hade rai tace “Nace ina xa ka?” Ya ki kallonta yace “To get drugs” kwace makullin hannunsa tayi tace “Let me do the driving” Daga haka ta nufi stairs ya bi ta da kallon gefen ido, mayafi karami ta dauko a daki ta rataya a wuya ya dinga kallonta, ganin ta nufi kofa yace “Iman!!!” juyowa tayi tana kallonsa, yana nuna mayafin kanta yace “Haka xa ki fita?” Kallon kanta tayi daga sama har kasa tana masa wani kallo tace “So?” Kallonta kawai yake bai ce komai ba, ta hade rai ta dawo ta damka masa makullinsa tace “Sai ka ja motar, ka tafi inda xaka” Komawa tayi ta xauna ya bi ta da kallo kafin ya fita parlorn, turo baki tayi jin yana warming mota ta mike ta wuce sama ta dauko Hijab dinta ta sa ta sakko parlor, kashe tv tayi tana hararan Shureim da duk hankalinsa gaba daya na kan kallo as if his life depend on it, ya mike da sauri yana kallonta yace “Anty ina xa ki je” Bata tanka sa ba ta nufi kofa ya bi bayanta, Tun daga nesa Aliyu ke kallonsu daga cikin motarsa ko kiftawa babu har suka iso ya dauke kansa, Ta hade rai tace “Ka koma daya side din” D’an murmushi yayi ba tare da ya kalleta ba ya fito ya koma daya bangaren Shureim na biye da shi a baya, yaron ya bude back seat ya shiga, shi kuma ya xauna front seat, ta shiga maxaunin driver, sabon mai gadi dake bakin gate ya bude gate din ta fita da motar, a hankali take driving din har suka hau saman titi, kamar ana tilastata tace “Wani pharmacy?” Gaya mata yyi idanuwansa a kan titi, kira’ar sheikh Sudais kadai ke tashi a motar in a very low tone, yace “Who taught you how to drive” Bata ce komai ba har suka iso pharmacy din, sai a sannan ta kallesa a takaice tace “A Good Samaritan taught me” Bai ko kalleta ba ya bude motar yayi wucewarsa, ta bi sa da wani kallo, Shureim yace “Anty, Uncle ba shi da lafiya koh” Bata ce masa komai ba, Bayan kusan minti goma Aliyu ya fito rike da ledan drugs ya shiga motar, ganin hanyar da ta dauka, yana kallonta da kyau yace “Ina xa ki je?” Ba tare da ta kallesa ba tace “Xan je gida in dauko ma Shureim wears dinsa” “Noo, mu wuce gida, xan je da kaina in amso masa ba sai kin je ba” A hankali take ta tafiya da motar shi dai bai kara ce mata komai ba, can ta turo baki ta dau hanyar gida… Tana gama parking ya bude motar ya fita ya bude back seat ya fiddo Shureim suka wuce ciki ta bi su da kallo, Babu kowa parlorn da ta shigo, ta ajiye makullin hannunta ta wuce kitchen, Cup din tea ta hada ta fito ta haura sama, bude kofar dakinsa tayi ta gansa xaune yana ballar drugs shureim sai surutu yake masa, ta ajiye masa shayin gabansa ta fita, dakinta ta shiga ta kwanta, Bata san lkcn da bacci ya dauketa ba kawai taji hannu a fuskarta ta bude ido a hankali, lkci daya ta mike xaune tana komawa baya tana kallonsa tace “What?” yace “Kin yi baki downstairs” Ta d’an buda ido tace “Su wa?” Ya mike yace “Suna jiran ki” daga haka ya nufi kofa tace “Shine baxa ka turo Shureim sai ka xo kana wani taba min fuska” har ya fita bai juyo ba balle yace komai, tashi tayi ta gyara daurin dankwalinta ta bi bayansa, Tsaye tayi stairs din karshe tana kallonta ko kiftawa babu. Suka hada ido da Khaleel dake jujjuya makullin motar hannunsa, saurin sunkuyar da kanta tayi, ta karasa shigowa parlorn kanta a kasa, haka kawai taji wani mugun kunyarsa take ji, ta xauna kan kujera taki kallon Jawahir, Khaleel yace “Good afternoon khadijah” Ba ta dago ba tace “Ina yini” ya d’an yi murmushi yace “Lafiya lau, how are you” Bata ce komai ba, Jawahir tace “Ya gidan khadijah” sai a sannan khadijah ta kalleta, Jawahir ta sauke idonta a hankali, Khadijah tace “Alhmdllh” Khaleel yace “Ta ce in kawo ta ku gaisa….” Khadijah tace “Toh nagode” Jawahir tayi kasa da murya tace “Khadijah I am sorry about what transpired between us recently, kiyi hakuri ki yafe min” D’an murmushi khadijah tayi tace “Ae ya wuce” Aliyu ya dawo parlorn ya wuce Fridge ya dauko masu drinks ya ajiye, Khaleel dake ta kallonsa ganin ramar da yayi yyi yar dariya bai dai ce komai ba, Murmushi Aliyu yyi yana shafa kansa, Khaleel yace “Ina Shureim?” Aliyu ya xauna kujera yace “He slept off minutes ago” Khaleel yace “Alryt then, dama madam na kawo, I think we will be on our way now, but before then Ina son xa muyi magana da kai…” Aliyu ya mike yace “Alright” a tare suka fita parlorn, Jawahir ta dawo kusa da khadijah tace “Da gaske kin hakura khadijah?” Khadijah na wasa da xoben finger dinta tace “Sure ya wuce” Shiru Jawahir tayi a ranta tana imagining abinda su Ummanta suka ce, khadijah ta dago suka hada ido, murmushin karfin hali khadijah tayi ta sauke idonta kasa, haka suka ta xaune shiru a parlorn har Aliyu ya dawo yana kallon Jawahir yace “Yana jiran ki waje Madam” Mikewa tayi ta ma Khadijah sallama shi ma tayi masa sanann ta fita, Khadijah ta tashi tana tabe baki ta wuce sama ya bi ta da kallon gefen ido. Da daddare ta fito wanka tana shafe shafenta Aliyu ya shigo dakin, ta xaro ido tace “Noo!! you can’t just come in without….” Kashe wutan dakin yayi ta xaro ido sauran maganan suka makale, yana daga inda yake a tsaye yace “Drugs da kika amsa hannun Shureim daxu, where is it?” Tace “Ka tafi xan kawo maka” a d’an fusace tayi maganan, yayi murmushi ya tako a nutse har inda take, duk da duhun dakin hakan bai hanata ganinsa ba ta dinga komawa baya a tsorace tace “Aliyu meye haka…” Xata gudu ya rikota sai jin ta tayi jikinsa, lkci daya jikinta ya dau rawa ta dinga kokarin kwace kanta amma yaki saketa, Babu abinda ke mata yawo a memory dinta sai incident din Shekaru bakwai da suka wuce, lumshe ido yyi jin yanda ko ina na jikinta ke rawa, murya can kasa yace “Ki gaya min abinda ke xuciyar ki game da ni Iman…. Tell me what u are thinking of me” Ta fashe da kuka tace “I beg you ka sake ni, you are making me….” Bai bari ta kai karshe ba ya hade bakinsu….. Bai xame ko ina da ita ba sai kan gado, ta kwace bakinta jikinta na bari tace “Nooo plss Aliyu, wllh ka bari bana so…. Kana son xuciya na ya fara min ciwo ko” Murya can kasa yace “I will cure it…” Toshe bakinta yayi jin xata fara masa ihu, Sallamar Shureim bakin kofar dakin ya sa shi saketa da sauri, da ta samu ta sauka kan gadon bata xarce ko Ina ba sai bayi ta rufe kofar jikinta na 6ari, Aliyu ya mike tsaye yana kallon kofar ya kunna wutan dakin sannan ya bude, Wayarsa Shureim ya mika masa yace “Uncle Mumy tana kiran ka tun daxu” Ya amshi wayar yace “Are you done with the game?” Girgixa masa kai yayi Aliyu ya kullo mata kofarta yana rike da hannun yaron suka koma dakinsa, Xaunawa yayi gefen gado yayi dialing number Mumy, bayan ta dauka suka gaisa tace “Ya Iman da Shureim?” Yace “Suna lafiya mumy” tace “Maa Sha Allah, Aliyu if it’s okay by you gobe ku shirya don Allah ku je Zaria duba Anty khadijah, duk da ina jin nan da kwana biyu xa a sallameta, Amma ya kamata ku je can din Koh” yace “In sha Allah Mumy” Mumy tace “In ji dai ba matsala” ya lumshe ido ya bude don har sannan bai gama dawowa daidai ba yace “Babu Mumy ga Shureim ku gaisa” daga haka ya mika ma shureim waya ya mike ya shiga bathroom. kasa bacci yayi gaba daya daren ranan sai juye juye yake, a bangaren khadijah kuwa da kyar bacci ya dauketa don duk a tsorace yake duk da ta sa ma dakin makulli….