Hausa NovelsNoor Al Hayat Hausa Novel

Noor Al Hayat 24

Sponsored Links

Da washegari har baby suka wuce makaranta bata yarda ta kalli inda khadijah take ba, ba Anty khadijah ba, har Mumy ta tambayeta me ya sami idonta tace babu komai, har daki Anty khadijah ta kai kan ta gaya mata ko an mata wani abu ne amma baby taki gaya mata komai, khadijah kuwa tunda ta shiga kitchen safiyar ranar jin muryar Anty khadijah ta makale ta ki fitowa, Allah ya gani ko matan kawu ba ji tsoron su kamar yanda take tsoron Anty khadijah ba, babu kalan xagin da kyauta bata yi ma Anty khadijah ba jiya a daki bayan Khadijah ta gaya mata abinda ya faru, har tsine mata sai da tayi, daga karshe rub ta shafa ma khadijah a bayanta da jikinta sannan ta sa ta ta kwanta ta dungureta tace “Gobe kya tsaya kallon shegen tv dinsu ke ma mayya” ita dai khadijah bata ce komai ba, wannan dalili ne ma yasa tun da khadijah ta shigo kitchen kyauta bata sa ta ko da dauko cokali ba, tana dai tsaye gefe tana kallonta, kyauta ta fita kai ma Anty khadijah dake xaune parlor Lipton a cup, mumy tace “Ban ga khadijah ba kyauta, ko bata tashi bane?” kyauta tace “Tana kitchen Hajiya, tare muka fito” Anty khadijah ta tabe baki tana kai Lipton din hannunta baki, kyauta na komawa kitchen tace “Kin min tsaye a kai tun daxu, ki tafi ki gaida Hajiya” Khadijah tayi shiru tana kallonta, turata waje kyauta tayi, hakan yasa khadijah ta turo baki ta wuce parlorn, Mumy na kallonta da mamaki tace “Me ya samu fuskarki?” Girgixa kai tayi tana sauke idonta kasa tace “Ba komai Anty” mumy tayi shiru tana kallonta hakan yasa ta durkusa kasa tace “Ina kwana” Mumy tace “Lafiya lau, kira min kyauta” Khadijah bata tashi ba sai da ta gaida Anty khadijah da ta amsa da kyar tana jifanta da wani kallo sannan ta wuce kitchen tace da kyauta Anty na kiranta, mumy na kallon kyauta bayan ta xo tace “Kyauta me ya sami khadijah fuskarta ya tashi haka?” Kyauta tayi kasa da kai tace “Hajiya nayi tambayar duniyar nan taki gaya min, haka nima naga fuskar kamar an mareta har ma da jikinta duk mintsili ne, nayi nayi da ita ta ki gaya min” Mikewa Mumy tayi ta wuce gun khadijah da taki fitowa daga kitchen, tana dubanta da kyau tace “Akwai wanda ya doke ki a gidan nan ne khadijah?” Khadijah ta girgixa kai da sauri tace “A’a Anty” Shiru mumy tayi tana kallonta, can ta juya ta fita kitchen din ta wuce sama gaba daya, Anty khadijah ta bi yayar tata da harara, da sauri kyauta ta shige kitchen tun kan su hada ido. Driver ne ya kai su kyauta da khadijah kasuwa misalin karfe sha daya domin yi ma khadijah siyayyar da mumy tace, Kyauta ta daukar mata duk wani abin da ta san xai amfaneta, har kayan sa wa, sai da kudaden suka kare sannan ta hakura suka koma gida, khadijah na ta lekan kayan daga cikin ledan kyauta ta kai mata rankwashi ta daure ledan da kyau. Xaune suka tadda Aliyu da abokin sa Farouq a parlor, kyauta ta gaishesu ta wuce daki, Khadijah ta kalli Aliyu da bai kalli inda suke ba tace “Good evening” yace “Evening” daga haka ta bi bayan Kyauta, Farouq na tambayarsa wacece ita bai taba ganinta ba. Ranan asabar mumy tasa khadijah ta shirya su je islamiyyar da su Siyama ke xuwa ayi mata register, saukin abun Anty khadijah na can daki tana ta bacci kamar matatcciya bata san abinda ake ciki ba, Da farko mumy driver tace yaje yyi mata komai a makarantar, amma ganin Aliyu ya shigo gidan daga clinic tace “Abuturrab tunda ka dawo ko xa ka taimaka kai ta ayi mata register?” Ya d’an hade rai yace “Noo Sanusin dai yaje ni yanxu shiryawa xan yi in tafi daurin aure zari’a” Mumy tace “Zaria? Sai ka dawo yaushe?” Yace “Anjima in sha Allah” tace “Toh shkkn” daga haka ya wuce sama, dole Sanusi ne ya tafi da su gaba daya makarantar khadijah dai na xaune daga jikin kofar motar su Siyama ko kallonta basu yi ba sai ma hade rai da suke ta yi, ko wace bata son jikinta ya taba nata don kuwa taxara sosai ne tsakaninsu a cikin motar, a ajin baby aka sa khadijah bayan anyi mata interview, nan Sanusi ya biya duk kudin ya karbar mata form ya koma gida don a cike mata, a ranan kuma mumy tasa ya je kasuwa ya yankar mata uniform da Hijab, kyauta sai murna take tayi mata bayan sun dawo da yamma, khadijah kuwa sai washe baki take tana bata labarin yanda islamiyyar yake, can kuma kyauta ta hade rai tace “Toh ni me yasa basu sani islamiyyar ba” khadijah ta xaro ido ta rike kugunta tace “Kaji Anty mai girki bayan kin girma?” Ranan lahadi bayan sun dawo islamiyya da yamma mumy ta sa Sanusi ya kai su saloon kasancewar duk lahadi suke gyaran gashi, tun da khadijah ta ji Mumy tace aje da ita hankalinta ya tashi, ta tafi ta kwanta kamar mai bacci a dakin kyauta, kyauta ce ta shiga ta korota waje ta rufe dakinta, haka dai suka tafi saloon khadijah kamar an aiko mata mutuwa duk ta daga hankali. Siyama aka fara gyara ma gashin sannan Aneesah sai baby, aka xo kan Khadijah tuni ta fara hawaye tace “Mai saloon ni gashina bai yi dirty ba ki duba ki gani” Mai saloon din ta saki baki tace “Toh bai yi datti ba me kika xo yi” cikin rawar murya tace “Anty ce tace sai na xo” Mai saloon na ganin xata tada mata hankali tace su wuce kawai bayan an bada kudin su siyama. Shiru Mumy tayi da mamaki tana kallon khadijah dake matsar kwalla bayan sun dawo, can tace “Sai kace yarinya khadijah, yanxu gyaran gashin ne kika ki tsayawa a maki?” Anty khadijah dake xaune tana ta girgixa kafa tana tabe baki cike da masifa tace “Ai maganinki kenan Anty Fati, gwara da ta kunyata ki ba ke sodangi ba” Mumy ta kalleta tace “Toh kika san ko tana da matsalar scalp ne?” Aliyu dake xaune dinning ya bar abincin da yake ci ya fito parlorn rike da makullin motarsa yana kallon khadijah yace “Mu je saloon din” xaro ido tayi ta nufi daki da gudu tace “Anty kice masa gashina bai yi ba datti wllh, mai saloon din ma ta duba tace mu tafi” ya hade rai yace “Xan xaneki idan kika shiga dakin nan….” Anty khadijah ta mike da mugun mamaki tace “Yau nake ganin ikon Allah… to ina ruwanka Aliyu? Meye damuwanka da gyaran gashinta da rashinsa har xaka zakalkale haka” Ko saurarenta bai yi ba ya sake ce ma khadijah ta fita kar ya xo ya sameta inda take, da gayya Kyauta ta kora masa ita waje tana satan kallon Anty khadijah, Ya bi bayan su bayan yasa baby ta biyosa, Kasa cewa komai Mumy tayi ta bi su da kallo, baby ce ta xauna gaba, Khadijah ta xauna a baya tana share hawayen da ya kawo idonta, kyauta ta rufe motar har da risinawarta tana daga ma Aliyu hannu tana masa Allah ya tsare hanya. Da kyar mai saloon ta gama gyaran gashin khadijah me tsayi bana wasa ba, sae sheki yake, ga gashin da uban laushi, khadijah tayi kuka har ta gode Allah, haka kowa ya saki baki yana kallonta a saloon din, babu sunan wanda bata kira ba bayan ummanta har da Anty mai girki da Mumy, shi dai Aliyu na tsaye yana kallonsu yana son yin dariya amma bai yi ba, baby ma na tsaye kusa da shi tana kallon khadijah, ba don shi ba da babu abinda xae sa khadijah ta tsayar da kanta har mai saloon ta samu daman gyarawa, dubu uku Aliyu ya ba mai saloon din tana ta godiya, yana ma khadijah wani kallo yace “Get up my friend” make kafada tayi wasu sabbin hawayen na xubo mata, kujera ya sa mu ya xauna yace “kiyi mata kitson kawai madam” da gudu khadijah ta fice a saloon din, baby ta kyalkyale da dariya mutanen dake cikin saloon din na taya ta, khadijah dake tsaye jikin mota ta dinga leka saloon din ko matar ta biyota, yana fitowa ya dagata yyi cikin saloon din ta rirrikesa tana ihu tana basa hakuri, mai saloon dake dariya tace “Ta tuba babban yaya ayi mata hakuri” baby ta rufe baki tana dariya har da kyakyatawa, bude bayan motar yyi ya saka ta ciki ya rufe ba shiri tayi tsit kirjinta na heaving, ya harareta ta madubi yace “Xan yi maganin ki ne” Bayan sun koma gida har daki Anty khadijah ta bi Aliyu, Ta rufe kofa tana masa wani kallo tace “Aliyu akan wani dalili ka tafi da yarinyar nan saloon daxu, ban gane me hakan ke nufi ba, ka taba sanin ta ne da can ko kuwa shisshigi ne da hali irin na uwarka ya motsa? Kai ma sodangin xaka koma” Aliyu dake ta kallonta yace “Meye a ciki don na kai ta saloon Anty, Kina fa ji Mumy ce tasa ta bi su Siyama kuma ta ki yarda ayi mata, to make my mum talk less shi yasa kawai ni na kai ta da kaina kuma ba gashi ta tsaya ba” Anty khadijah tace “Eh lallai ni kake gaya ma bakar magana ko Aliyu? Babu damuwa, xan yi maganinka” daga haka ta fita, Aliyu ya tabe baki ya mike ya rufe kofar sa don a bude ta bar masa. Yau khadijah ta cika sati biyu gidansu Aliyu, babu abinda Mumy ta rage ta da shi a gidan, duk yanda ta yi da su siyama haka take mata ita ma banbancin kawai shi ne har lkcn a dakin kyauta take, kusan dai kyauta ce kadai mai aikin gidan don ko kadan kyautan ma bata takura khadijah tayi aiki sai dai fa tana nuna mata abubuwa da yawa ko kadan ne tana barinta tayi har goge gogen, ranan da khadijah ke da sati daya a gidan Anty khadijah ta tafi Abuja ganin yaranta, hakan yasa hankalin khadijah kwance har na sati biyu yanxu, Tunda baby ta ci duka gun Aliyu ko kallon banxa bata sake ma khadijah ba, sai ma note da take bata wani lokacin ta kwafar mata na boko ita dai Mumy bata ce masu kala don kuwa rubutun khadijar ma ya fi na baby kyau, har assignment khadijah na kwatanta yi ma baby, su siyama dama ba wani interacting suke da ita ba, don haka babu ruwansu da ita, A yau da ta cika sati biyu ne mumy na bedroom dinta da yamma Aliyu ya shigo, Gaisheta yyi tace “Halan ka fita nyt duty ne?” Yace “Tun three days back yanxu morning xuwa yamma nake yi” tace “Ohk, kun yi waya da Abbanku” Aliyu ya shafa kansa yace “Ehh ai gobe xai taho in sha Allah” tace “Nima haka yace min daxu” yana fiddo wayarsa a aljihu yace “Wai yaushe Anty xata dawo mumy?” Mumy tace “Toh nima dai ban sani ba wllh, amma jiya da ta kirani kamar akwai damuwa kilan su Iklima na cikin wani hali….” Yace “Toh Mumy wai me yasa iklimar baxata dawo nan gidan ba, su Ahmad maxa ne bbu damuwa sosai amma ita macen da ta dawo nan” Mumy tace “Ai ubansu baxai yarda ba ne matsalan sai dai ta taho da ita ba tare da ya sani ba” Aliyu ya girgixa kai yace “Allah ya kiyaye” mumy tace “Ameen dai” Shiru yyi bai sake cewa komai ba, Mumy tace “Ya aka yi kamar kana son yin magana koh?” Murmushi yyi don sure yasan mum dinsa ta gama karantarsa gaba daya, yana facing dinta yace “Mumy dama ba komai bane a kan Mai sunan Anty ne” tunda khadijah ta shigo gidan bai taba kiran sunanta ba saboda Anty khadijah, Mumy ta kallesa da sauri tace “What about her?” Yace “Noo, kawai mum naga da ki taimaka a sa ta a boko…” Katse sa tayi tana kallonsa da kyau tace “Ko saboda me?” Ya d’an bude ido yace “Noo Mumy naga kawai she isn’t an illiterate, its just anyi depriving dinta right dinta ne, from all indications she was born with a silver spoon, you knw… it’s just condition mum, ina tausayinta ne wllh, kin dai ga har coaching Baby tana kokarin yi, she is very intelligent, Allah will reward you idan kika taimaka mata mumy” murmushi mumy tayi tace “Kasan me Ali?” Ya girgixa kai da sauri yana kallonta, strictly tace “Abuturrab ko da wasa, I mean ko ba a cikin hankalinka ba, kayi making mistake din ce min kana son yarinyar nan wataran I will show u my other side, because it will and will neva be possible, that is just it” da mugun mamaki yake kallonta, a hankali yace “Sonta kuma mum?” Ta gyada kai tace “Yes” yyi shiru na few seconds kafin yace “Mai ya kawo wannan xancen mumy?” Ta hade rai tace “Kai ka kawo sa, for I see no reason har xaka damu In sa ta makaranta kai ka kawo min ita gidan?” Ya girgixa kai kawai, tace “To be careful, yes xan sa ta makarantar boko amma wllh wllh ko a mafarki ka cire ran akwai aure tsakanin ka da yarinyar nan, period” Ya kalli Mumy a hankali yace “But.. Ko saboda me” strictly Mumy tace “Hakan nake so ya kasance, or are you querying me” yace “Amma mumy ni ai ba ce maki nayi ina son ta ba, boko kadai nace ki sa ta for the sake of Allah, meye ma xai sa kiyi tunanin nan mumy, ni kuma in rasa warce xan ce ina so sai karamar yarinyar nan? Wallahil azim ban taba kawo hakan a raina ba, gaskiya I am nt happy mum” daga haka ya mike ya fita a dakin.

Back to top button