Hausa NovelsNoor Al Hayat Hausa Novel

Noor Al Hayat 15

Sponsored Links

Shekaru shiddah baya…..

A hankali ta karashe shanye shayin dake hannunnta ba tare da ta bi ta kan soyayyen kwan dake gabanta ba ta ajiye cup ta mike tace7 “Umma to idan Kawu ya tafi da ni baxan sake dawowa ba?” warce ta kira da Umma dake duke tana goge mata takalmanta masu tsada tana xuba su a wani jaka ta juyo da rinannun idonta tana kallon ‘yar yarinyar warce da kadan ta haura shekara sha uku tace “Xa ki dawo Khadijah in sha Allah” Khadijah bata sake cewa komai ba tana dai tsaye, tsadaddun ready made ne jikinta da cover shoe mai kyau sai kyalli yake, da farin hijab karami, kunnuwanta dauke da dankunnen zinari ‘yan kanana, Khadijah tace “Toh Umma me yasa ke baxa mu je da ke ba” Umman bata kalleta ba tace “Nima gidanmu xan je Khadijah” Khadijah ta durkusa kusa da ita a hankali tace “Umma ni bana son gidansu Kawu ki tafi da ni gidanku don Allah” Umman bata ce komai ba har ta gama rufe jakar ta daura kan babban jakar dake dauke da kayan Khadijah, jin Umma bata ce komai ba Khadijah ta dau remote xata kunna TV, Umma ta jefa mata wani kallo tace “Xaki fara ko, ni dai na gaya maki kar kije gidan mutane kina masu irin wannan kallon da kike kamar wawuya, kashe TV din nan yanxun nan” Khadijah ta kashe tvn ta koma ta xauna kan kujera, dai dai shigowar kawunta, kuma wan mahaifinta, har ya karaso parlon idonsa na kan soyayyen kwan da Khadijah ta bari a plate, ya dau plate din ya xauna yace “Tsabar almunbazzaranci dubi abinda aka yi ma lafiyayyen kwai, karshen komai ya xo in sha Allah” ita dai Umma bata ce komai ba ta wuce daki don fiddo nata sauran kayan da ya rage a gidan, Kawu ya dinga cin kwan kamar his life depends on it, har dai ya gama daga karshe ya ajiye ya na kallon Khadijah dake ta kallonsa yace “Toh ki tashi ki fita ga adai daita can ki shiga ki jirani a kofar gida” ta xaro ido tace “Kawu ba da mota xa mu je ba” dakuwa ya mata yace “Tashi ki ban waje” mikewa tayi tayi hanyar kofa tana waigosa, shi kuma ya dau katon jakar ya bi bayanta, Umma ta fito da nata kayan waje ta dau plate da cup ta shiga kitchen ta wanke su ta ajiye, ta kuma sake tabbatar da komai a kashe yake sannan ta bi bayansu, Khadijah na tsaye jikin adai daitan Umma ta jawo ta, a hankali tana kallon eyeballs dinta tace “A duk inda kika tsinci kanki ki xamo mai hakuri kin ji Khadijah, nasan ki da shi, komai kuma aka sa ki kiyi, sannan most important of all banda kallon TV don Allah…” Khadijah tayi murmushi da ya bayyana beauty point dinta tace “Umma I can’t do without watching tv fah” Umma ta hade rai tace “So u won’t heed to what am saying koh?” A hankali ta sauke idonta tace “Am sorry mum” Umma ta ja kumatunta tana murmushin karfin hali tace “That’s my girl” a hankali kuma a sanyaye ta kara da cewa “And always pray for daddy, kullum kika yi sallah ki masa addu’ar Allah ya masa rahama” Khadijah ta gyada kai tace “Toh Umma” Umma ta shigar da ita adai daitan tace “Safe trip dear, I will always pray for you” Khadijah ta gyada mata kai trying hard to control her tears, Tuni Umma ma ta juya ta nufi main road da jakarta ba tare da ta bi kan kawu Jibril dake kokarin maka ma gidan kwado ba, Khadijah ta bi stepmother din ta da kallo hawaye na sakko mata, a haka kawu ya shigo adai daitan, yana mata wani kallo yace “Kukan uwar me kike ma mutane” cikin rawar murya tace “Umma ta” Dungurinta yyi yace “Uwar ki ba Ummar ki ba” Khadijah ta sunkuyar da kai, mai adai daitan ya dau hanyar park, hannu Khadijah ta daga ma stepmum dinta ganin sun wuceta, ita ma ta daga mata tana goge hawayen idonta. Tasha mai adai daitan ya kai su, kawu ya sauke kayan Khadijah ya bai ma mai adai daitan kudi sannan ya biya masu kudin mota xuwa katsina, da kyar ya yarda ya biya seat biyu wai xai dauketa a kafa, sai da yan motar suka sa baki, bayan kusan minti goma motar ta cika suka dau hanyar katsina, tunda Khadijah take bata taba shiga motar haya ba, rabonta kuma da katsinan tun tana da shekara bakwai da suka je tare da Abbanta, kai kana ganinta kasan she is restless, matar da ke kusa da ita tace “Yarinya me ya faru?” Kamar xata yi kuka tace “Amai….” Kawu ya kwalalo ido yace “Me?” Tace “Amai” dungurinta yyi yace “Ke yarinya ce xaki ce ma mutane kina jin Amai cikin mota” matar tace “Haba bawan Allah, sai yara ke Amai idan suna tafiya” dakatar da ita yyi yace “Ke… Learn to mind ur business while in public, ‘yar ki ko tawa” matar tace “Aa ba yar ka bace wllh, don da yar ka ce baxa ka yi mata abinda kayi mata ba yanxu” Bala’i kawu ya fara kamar mace a motar, ana haka Khadijah ta toshe bakinta jin aman xai taho mata, matar bata bi ta kan kawu ba ta sa driver ya tsaya, ta sauke Khadijah, nan kuwa ta dinga kwara Amai, matar na tsaye kanta, shi ko kawu yana cikin mota sai fada yake yana kumfar baki, kowa ya xuba masa na mujiya bbu wanda yace ci kanka, wani mutumi a motar ya ba matar ruwa ta mika ma Khadijah, ta wanke bakinta da fuska sannan suka dawo cikin motar ana mata sannu, wata mata ta bada leda ta rike a hannu idan ta ji wani aman, har suka isa katsina kawu bai yi shiru ba, Khadijah tayi Amai yyi sau biyar, dunguri kam ta sha sa gun kawu duk da ba a kusa da shi take ba, bbu wanda yace masa ci kanka cikin passenger din motar, a dai dai ta ya samu da xai kai su har gidansa.. Karfe biyu da kusan rabi suka shigo gidan, bungalow ce mai kyau, wanda Abban Khadijah Alhaji Muhd ya mallaka ma yayan nasa a lkcn yana da rai, sai dai ba lallai wanda ke nan lkcn da aka ba Kawu gidan ya yarda Cewar gidan ne a ynxu ba, don yyi mugun tsufa ga dattin bala’i, kuma dudu gidan bai yi shekara shidda ba, Duk matan Alhajin guda biyu suka fito jin shigowar mai gidan nasu suna masa sannu da xuwa, kawu dake kokarin bude jakar kayan Khadijah bayan ya xauna parlor yace “Toh ga ta nan, gida kuma ni da Isiyaka mun rufe an sa a kasuwa, ga ta nan ban san gun warce xata xauna ba cikin ku” Matarsa ta fari Hajiya Salaha tace “Toh ni dai yara sun yi yawa a gu na, ban san dai ko Maimuna ba” warce ta kira da Maimuna tace “Ni kuma sai nace maki yaran basu min yawa ba koh?” Kawu yace “A’a bbu xancen tada jijiyoyin wuya taje dakin ki Maimuna kayanta kuma a kai dakin salaha, shkkn” daga haka ya dinga fiddo da tsadaddun kayan Khadijah, daga shi har matansa bbu mai cewa komai sai kallon ikon Allah suke, Kusan set takwas ya cire ya ajiye gefe yace “Wannan siyar da su xa ayi in sha Allah, domin kuwa baxata xo nan ta dinga saye sayen kaya ba kamar wata er gote ta janyo ayi tunanin shi gareni…” Takalman ma duk ya ware kusan biyar, golds dinta na dankunni da awarwaro kuwa dama suna aljihunsa, Khadijah dake ta tsaye jikin kujera tana waiga ko ina na parlorn da idonta tana neman remote ta kunna TV amma bata gani ba, ganin kawu xai xuba duk kayan da ya ware a wani jaka ta karaso da sauri tace “Kawu ina son wannan takalmin, da shi nake xuwa makaranta” Dungurinta yyi da karfi ya kunduma mata ashar, ta koma baya a tsorace yace “Ki shiga hankalinki da ni fa xan xane ki wllh” xata mike ya fixgota ya cire dankunnin kunnenta, Hajiya Maimuna tace “Toh idan ba fitsara ba ita har xata gaya maka abinda xaka yi” mikewa yyi ya dau jakar yace “Ku shiga da sauran, ni na tafi kasuwa kan yamma yyi” daga haka ya nufi kofa” bayan fitarsa Hajiya salaha ta sake fiddo kayayyakin ta dau kusan kala biyu da panties da kayan bacci, Hajiya Maimuna ma ta jawo jakar ta dau huluna da kaya kala daya da dogon rigar kanti da safunayen hannu da kafa, Hajiya salaha xata sake jawo jakar Hajiya Maimuna ta rike tace “Tsiyace jakar xa ki yi” Hajiya salaha ta jefa mata wani tace “Ke ai arxiki kike karama jakar, abu baxa ayi sa da hankali ba, ita sai ta sa uwar me?” Hajiya Maimuna ta rufe jakar ta tura tana kallon Khadijah dake ta tsaye tana kallonsu tace “Dauka ki kai dakin can dake kusa da wancan kofar, kin wani tsaya ma mutane kememe” Khadijah ta karaso da sauri ta dau jakar ta bi hanyar da Hajiya Maimuna ta nuna mata, kafin ta fito sun dau takalma kala daddaya ta dau jakar takalmin ma ta kai dakin. Uban wanke wanken dake tule gun pampon da aka tanadar don yin wanke wanken Hajiya salaha ta nuna mata taje tayi, a hankali Khadijah tace “Ina jin yinwa” Hajiya salaha tace “Can baki ci abinci bane kafin ki taho, ki je bakin pampon akwai tukunyar taliyar da ta rage ki ci sannan kiyi wanke wanken” Fita khadijah tayi xuwa gun pampon, ta yi kusan minti daya tana kallon taliyar da kudaje ke bi, ta turo baki ta rungume hannayenta, Dawowa parlon tayi kamar xata yi kuka tace “They are flies perching all over the food, ni baxan iya ci ba” sakin baki suka yi gaba daya suna kallonta, can suka kwashe da dariya Hajiya Maimuna tace “Toh baturiyaa jikar mongo park….” Hajiya salaha tace “Kin wuce kin ba mutane waje ko sai na mike.. Ina ruwan ki da k’uda idan ba rainin wayo ba, ki bar abincin kar ki ci, kuma maxa ki tafi ki wanke kwanukan yanxun nan” juyawa khadijah tayi ta bar wajen, Hajiya Maimuna tace “Idan ba ma tsoron Allah ba har Alhaji xai yarda ya rike er Muhammad, uwar me ya tsinana sa yana raye” Khadijah dake ta turo baki ta dau omon da ta gani da sosan wanke, tsaye tayi ta rasa ta inda xata fara wanke wanken, can dai ta dauko babban bahon da ta gani ta tari ruwa ya kusa cika sannan ta xaxxage d’an omon, muryar wata mata da shigowarta gidan kenan taji tana cewa “Ke ya haka, da uban ruwan nan xaki kada kumfa?” Khadijah ta kalleta kamar xata yi kuka tace “Toh ban sani ba” matar ta karaso baki sake, nan ta rage ruwan ta kara mata omon sannan tace “Haka ya isa” parlor matar ta shiga wajen su Hajiya tana cewa “Ku kuma ina kuka samo wancan Ajebon” Karfe kusan hudu da rabi Hajiya Salaha ta fito bayan tafiyar bakuwarta, sakin baki tayi tana kallon Khadijah dake durkushe bakin pampo har lkcn, kwanuka ta ko ina, duk ta hade gumi ta jike kayanta jagab, kai kana ganinta kasan bata taba ba ne, Hajiya ta kwalo ma kishiyarta kira ta fito da sauri, ita ma ta xaro ido tace “Me xan gani ni Maimuna, wanke wanken awa biyu?’ Khadijah dake kallonsu kamar xata yi kuka tace ” plates din sun bushe, ya ki ya fita” Hajiya Maimuna ta rike ha6a tace “Ehh lallai muna da aiki, yanxu tsalelliyar budurwa kamar ki baki iya wanke wanke ba shekara sha uku sa’ar Murjata” Hajiya Salaha da ita ma ta bude baki ta kalli kishiyarta tace “kina da aiki dai, don ba ni aka kawo ma ita ba, mutum yaji da nasa ‘ya yan mana, shima Alhaji wllh, da ba sai ya bar ta gun kishiyar marigayiyar uwarta ba” Juyawa Hajiya Maimuna tayi tace “Toh Allah ya kyauta” daga haka ta shiga ciki, Hajiya salaha ta mata tsawa tace “Tashi mana kan kwanuka yar banxa kawai, ke ga yar masu kudi ko, to xa ki ci kwakwa a gidan nan don bbu shegen da xai dau iskancin ki, kawai kin bi kin ma mutane asarar omo, maxa kuma ki dau tsintsiya ki tattare gaba daya gidan nan idan shima kuma baki iya ba sai in ga” khadijah da ta bata fuska xata yi kuka ta karasa ta dau tsintsiyar da take nuna mata ta fara sharan, takaici ya rufe Hajiya ganin gwara ma ta shekara a tsugunne bakin pampon da wannan sharan da take na yan iska, juyawa tayi ta bar gun daga karshe tana cewa “Xaki san inda kika xo yarinya” da daddare Khadijah na rakube jikin kujera gaba daya hankalinta da soul dinta na kan kallon cartoon da kananun yaran kawu Jibril suka sa a TV, an kirata ya fi sau uku amma inaa, hauri Sajida er Kawu ta biyu ta kai mata tace “Yau naga mayyar kallo ana magana bata ma san ana yi ba” a firgice ta mike sai dai har lkcn idonta na kan TV, Hajiya Maimuna dake lekosu daga kitchen don ita ke kiran khadijar ta xo ta karbi abinci, ta karaso a fusace ta kai mata dundu, firgita ta juyo Hajiya Maimuna ta murda kunnenta tace “Gafara shegen kallon nan xai maki ne hala, ka ji min yar kaza kaza” sunkuyar da kai khadijah tayi kamar xata yi kuka, Hajiya Maimuna ta turata kitchen tace “Ga tuwon ki can a kitchen ki dauka, gayyar tsiya kawai” tafiya kitchen din tayi tana yi tana waiwayo TVn ta dauko tuwon a wata yar roba an ya6a masa miyar kuka koriya shar, sai kallon miyar take kamar idanuwanta xa su fito, ta dawo parlon ta xauna cikin yara dake cin abinci su ma ta ci gaba da kallonta Hajiya Salaha ta shigo parlon tace “Wato kinsan idan mutum ba ayi masa tarbiya ba sai na kallo, kinga saura kadan ta xubar da tuwon tana kallo” da sauri khadijah ta kalli tuwonta taga ba daidai ta ajiye sa ba, Hajiya salaha ta fixgota a fusace ta juyar da ita tana kallon kofar kitchen tace “Duk kika sake juyowa sai na kashe ki” Khadijah dai bata ce komai ba ta kai hannu a hankali cikin tuwon ta mintsili kadan ta kai baki, yamutsa fuska tayi tana hadiyewa da kyar sai kuma ta kalli Er Kawu ta uku mai suna Rabi tace “Anty akwai indomie?” Yarinyar ta fashe da dariya sannan ta gaya ma Uwarta Hajiya Salaha, Hajiyar tace “Ehh akwai wanda ubanta ya kawo mana daga kabari” Khadijah dai bata ce komai ba, haka tayi ta kallon tuwon ta kasa ci, daga karshe haka ta mike ta kai kitchen ganin kowa na kai kwanonsa can, Hajiya Maimuna ta kwalo ma kishiyarta kira ta nuna mata tuwon da ta bari tace “kin dai ga koh? To wllh har in fita girki sai dai yunwa ya kashe yarinyar nan”

*Haske Writers Association*💡

07087865788 Contact me here.

✨ *Noor-Al-hayat*✨

Back to top button