A Rubuce Take Book 2Hausa Novels

A Rubuce Take Book 2 Page 17

Sponsored Links

Part 02

Page 17

Sallamar anty ummee ce ta tsinkar mata da zuciya,a sanyaye ta amsa mata,anty ummee din ta shigo idanunta na dan shawagi cikin falon,cikin ranta tana Allah wadarai da halin qazantar ummeen da har yau ta gaza rabuwa dashi.

“Ya naji gidan shuru,ina yaran?” Ta tambayeta bayan sun gama gaisawa,kamar jira takeyi sai kawai ta sakewa ummeen kuka

“Ke meye haka?,ai sai a dauka wani abu nayi miki daga shigowata” kamar zuciyarta zata fito daga qirjinta sanda take gayawa anty ummeen damuwarta,sai data gama tsaf sannan ta tabe baki

“Ai wallahi yanzu yadda kissa ke ci asirin bai isa yayi wannan aikin ba,ke ko masu asirin aida kissar suke hadawa bawai ki tsaya haka sungungum ba,ni ai tunda umma ta gwasaleni saina tsame hannuna,yanzu ki yiwa kanki hisabi,da lokacin da muke kan takunmu da yanzu wanne lokaci ne kikafi samun yadda kikeso?” Shuru tayi tana nazari,ko ba’a gaya mata ba tasan amsar,a wancan lokacin ta samu dukka wata dama da rashin haqurinta yasa ta gaza kaiwa ga gaci ta koma bin malamai,duk da suma nasu aikin tana samun biyan buqata duk kuwa da bamai yawa bace,amma babu jinkiri a hanyarsu,sha yanzu magani yanzu ne(wa’iya zubillah).

“Nasan kin riga da kin baiwa kanki amsa,to koda zakibi malamai saikin hada da kissa,saboda haka idan kin shirya bismillah,duk da dai yanzun bani da lokaci isashe,muna shirye shiryen tashi zuwa sabon gidanmu,idan na hada hankalina waje daya saimu tsara yadda zamu gyara komai,muga kuma yadda Allah zaiyi”.

A ranar saita samu walwala sosai,daga ganin anty ummeen sai taji kamar matsalarta tazo qarshe,ta dan jima a gidan,wanda bata fita a gidan ba sai data yagi wani abu daga jikin hafsat,bata hanata ba,don itama yanzu taimakonta take nema,daga qarshe ma sai data bawa dan riqon gidanta dan yayan abbas din key din motar ta ya maida anty ummeen gida.

Sau biyu tana fitowa tana shige kitchen amma tana ganinsa a zaune inda ta barshi,kusan awa guda kenan yana zaune a wajen,yaran suna kwance daga gefansa sunyi barci.

Tunda ya dawo ya watsa ruwa ya zauna zaman cin abinci,ta dire masa abincin ta qara gaba,don tun ranar da widad ta haihu haka take masa,zafinsa takeji,saidai ko.sau daya bai taba nuna mata ma ya gane wai fushi take ba,don shidai kaf a abinda ya faru baiga abin yiwa fushi a ciki ba,shi yasa ya tattara ya bawa banza ajiyarta.

Cikin zafi yake amsa wayar tsahon awa gudan kenan da gurbataccen turanci (brooking),da alama yana magana da wasu cikin yaransa ne akan abinda ya shafi aikinsu.

Fitowarta ta qarshe daga kitchen din ya sauke wayar a kunnensa bayan yaja tsaki,sau da yawa ire iren abubuwan dake janyo musu bacin suna kenan daga wajen al’umma suke musu kallon abu daya,yanzun ya zama dole ya tafi kaduna a gobe

“Zoki dauke yaran nan ki kaisu daki” kakkausar muryarsa da amonta babu wasa kwata kwata a ciki ta ratsa kunnenta,saita ratso ta tsakiyar kujerun ta fara daukesu daya bayan daya,shi kuma ya buda warmer din abincin yana qare ma abincin kallo.

Bacin ransa ya sake daduwa sosai,ya maida murfin ya rufe,ya koma.ya jingina da kujera yana sauke ajiyar zuciya,ya dade da sanin irin muhimmancin widad cikin rayuwarsa,amma nisan da tayi dashi a yanzu ya sake haska masa girman da muhimmancin da take dashi ga rayuwarsa.

“Idan kinkaita ki dawo” saita tura baki gaba tana cure fuska kamar wadda aka yabawa kashi,tana tsammanin yana buqatar wani abune daga gareta,indai.kuwa hakane yau a jikinsa zata fanshe abubuwa da yawa da ta qudirta,don haka koda takai nawwara sai da taja lokaci sannan ta dawo cikin falon,zuwa sannan ma har ya shiga kitchen ya hada coffe da kansa,don ya gwammace ya shashi ya kwanta akan yaci wannan qaddararren abincin nata.

Gefe ta zauna tana hada rai, baice komai da ita ba sai daya gama sha ya dire cup din,ya jawo system dinsa dake cike da rubutu yayi saving ya kasheta,sannan ya bude briefcase din gefansa ya ciro kudade ya ajjiye mata.

“Nasan hajiya ta gaya miki gobe zaku wuce kano suna,gashi nan,kudin transport ne dana amfanin gida,nasan zasu isheki harda ragowa ma” ya qarashe maganar ba tare daya dubi fuskarta ba,sai jakarsa da yake rufewa

“Ni ba inda zani fa,saboda haka sai sun dawo” wani kallo ya watsa mata bayan ya miqe yana kallon cikin idanunta

“Ba shawararki nake nema ba,umarni ne na baki, bijirewa magana ta kuma bazatayi miki dadi ba,banason doguwar magana,gobe zaku kano period” ya juya a nutse yana tafiyar nan tasa majestically kamar bashi da sauran damuwa,duk kuwa da cewa qasan ransa bacin rai ne fal,ga na shirmen da aka masa a office ga matsalar hafsa din da har yau babu alamun gyaruwa ko nutsuwa a tattare da ita sam sam.

Dakinsa ya wuce ya ajjiye jakar sannan ya fara hadawa kansa ruwan wanka a mugun gajiye,abinda baisan dashi ba muddin kwanan widad ne,koda ya gama gado kawai ya haye,sannan yaja wayarsa ya kira widad din don ya tabbatar zai samu relief.

Ya samu har fiye da yadda yakeso ma,ta sauke masa dukkan wani bacin rai dake ransa,daga qarshe ma video call sukayi ita dashi,ta nuna masa duk wata kwalliyar suna

“Wannan ai tsomo ni kawai zakiyi,nayi missing……nayi missing sosai,ina da aiki amma banda haka ya kamata nazo naga kwalliyar sosai”

“Za’a yi maka wadda tafi wannan,kada ka damu,ka maida hankali ga aikinka,wanda na tabbatar muhimmncin da kake bashi shine mabudin dukkan wannan nasarorin da kake samu”

“Sirrin kuma nasarorin kece ba……nutsuwar da kike bani widad…….I don’t know how to explain it to you,you become part of me”.

Irin wadan nan hirarrakin dake qara dasa kowanne cikin zuciyar dan uwansa su sukaci gaba da gudana,daga qarshe yace a karbo masa muhammad zai ganshi,dole ta ajjiye wayar duk da yadda takejin kunya don yana hannun ‘yan suna,ta samu nujood ta lallabata ta karboshi.

Ya jima yana kallon yaron ta cikin video call din sannan ya sauke ajiyar zuciya

“Bazan iya hana wannan taron sunan ba,amma don Allah….. please na roqeki,ki kulamin da kanki,ki kuma kularmin da yaro na,kada ayita wannan shige da ficen da shi” dariya ma ya bata yadda ya marairaice,kuma yake maganar da gasken gaske

“Oh…… dariya ma na baki?, seriously madam……am in pain na yadda za’a kallemin ke a gobe,don Allah ki kula”

“Nifa taka ce,mallakinka ce ta har abada,infact ma saboda kai Allah ya halicci widad,no need ka damu,kayi aikinka hankalinka kwance don Allah” maganganu tayi masa masu kwantar da hankali,dole daga bisani sukayi sallama saboda yadda aketa kiranta daga falo.

Suna gamawa ya ajjiye wayar yayi addu’ar kwanciya barci,yaja duvet abinsa ko takan hafsat baibi ba.

Sanda ta gama baqin ran nata tana zaton zai biyota taga bai biyota ba saita shirya ta taho,koda ta iso tuni ya jima da yin baccinsa,abinda ya qara mata baqinciki da takaici,ta kasa kwanan dakin ta rufe masa qofa ta koma nata dakin.

********Tun asuba ya shirya ya fice abinsa,bai sake tada mata zancan zuwa kano ba alamun zabi kenan ya rage nata.

Duk abinta tasan iya lokuttan da take iskancinta,ta sani sarai idan ya kafe bashi da dadi sam,dole ta fara shirin tafiya,bayan ta kira muneera taji qarfe nawa ne tafiyar.

A ranar sai data fidda kayan sawarta daga cupboard dinta gaba daya amma ta rasa wanda ya dace ta saka,kowanne akwai nashi illar,sutura iya sutura masu tsada,don abbas baya siyan abun banza,saidai idan ita ya bawa kudin ta siya na banza ta soke sauran kudin,wannan kuwa ko ta kanta baya bi.

Wata rigar tasha squeezing,wata bata ga dan kwalinta ba,wata na buga tsami,saboda an saka an maidata cikin kayan ba tare da an wanke ko an barta tasha iska kafin a maidata din ba.

Bata taba jin haushin irin abun ba sai yau,so takeyi tayi shiga ta kece raini,amma maimakon taji haushin kanta sai haushin ya tattara akan widad da abbas,kamar dole sai taje sunan?,amma kuma data tuna maganar anty ummee da tace gwara taje ta ganewa idanunta barnar kudin da yayi musu sai taji babu case,taci gaba da bincikawa,da qyar ta dace ta tsamo wata ABC england dark blue,itama a yamutse take,saidai atamfa ce mai laushi cotton sosai,don haka ta fesa mata ruwa ta zauna akai ta samu tadan miqe.

Duka mayafanta masu tsada da abbas ke siya sanyasu takeyi cikin kayan siyarwarta ta saida,a nan ma da qyar ta samu wani baqi ta dora,sanann ta laluba jaka da takalmi duka ta yamutsa abinta.

Idan kika ganta zakiyi tsammanin amaryar ‘yar talla ce daga wani qauyen ranar fitowa daga gidan miji na farko,ga jambaki ja ya kama ya haska baqar fatarta data rasa gyara bare tayi kyan da masu duhun fata keyi idan ta samu kula ba tare da canza launin fata,to amma da yake ba saban bace ta fannin ado da kwalliya,sai take ganin ta gama qure adaka,qarfe goma na safe motar da abbas ya sanya ta kaisu kanon ta iso ta dauketa suka wuce.

Daga ita sai gwaggwo mero qanwar hajiyarsu,sannan muneera yaaya bara’atu,sai gwaggwo fanteka da gwaggwo hassana matan uncles dinsa,da kuma qanwar abbas wadda take binsa nasma.

Tunda suka dau hanya babu wanda ta kula a cikinsu,saboda kowa fuskarsa babu alamun damuwa ko bacin rai sai ita kadai,har gwara gwaggwo hassana da yake suna da alaqa da ita,takan tabe baki lokaci lokaci ko tayi magana qasa qasa akan tafiyar.

A can kano kuwa ko cikin family ranar kowa yasan sha lelen ummu ta haihu,gata tako ina a ranar ya nuna kansa,ba daga wajen mommy mahaifiyarta ba,ba kuma daga wajen ummunta ba,ba daga wajen tsoho mai ran qarfe alh salim ba ko mahaifinta Alhj mahmud da Allah ya dorama son jikan nasa,kamar a kansa aka fara masa haihuwar jika ba,ga kuma mai dungurungum din wato DSP abbas turaki.

Wani kalar suna ake gudanarwa,irin sunan da tsiya da babu suke gudu da qafafunsu, komai a wadace,hatta da almajirai da mawadata ranar sun shaida sunan,tun da sassafe widad ke sanya sutura tana canzawa harta fara gajiya,qarfe sha biyu saiga motarsu hafsat tayi landing cikin tsakiyar harabar gidansu widad??????

_to mai karatu,ya zata kaya ne?,anya kuwa hafsat ayau zata iya cinye kishinta?,kuzo dai mu rakasu ciki mu gani_??????????????????????????????????????????????
[13/05, 9:33 am] +234 907 874 7031: *H U G U M A*
*Arewabooks:Huguma*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)

Back to top button