A Rubuce Take Book 2Hausa Novels

A Rubuce Take Book 2 Page 15

Sponsored Links

Part 02

Page 15

Parlor din kuwa cike yake da surukan ummu da jikokinta,saboda wasu a nan zasu kwana sai ranar suna ko washegari zasu tafi,duka kowa baida matsalar wajen da zai sauka,don gidan nasu badai girma da yalwar masaukin baqi ba.

Cikinsu ta zauna latifa ta kawo mata abinci akaci gaba da hira da ita,bataci mai yawa ba ta ture tana yatsina fuska,don ciwon mara da bayan kamar ma yafi na baya.

Ummu dake ankare da ita tace

“Lafiya?,mene?”

“Baya na ne yaketa ciwo ummu”

“Ehaan,kaji ba,shi yasa nace kiyi zamanki kika qi,saiki tashi ki shirya bari a yiwa wani cikin yaran nan magana ya dauko mota kuje asibiti” kai ta girgiza

“Aah,kawai a bani man zafi na shafa har qafafuwana ma”

“Basai taje asibiti sun jagulata ba ummu,tunda naga cikin kamar bai isa haihuwa ba ai,a bata.man ta shafa,zai ware,idan bai ware bama sai suje” anty halima ta fada cikin kulawa.

Ummu da kanta ta shafa mata ta kuma tasata a gaba kan ta wuce daki ta kwanta ta huta hakanan,a hadu gobe,tunda hirar tasu bata qarewa,dole badon taso ba ta wuce dakin tayi musu sallama,su kuma suka rakata da sannu.

To abu kamar wasa maimakon ciwo yayi baya sai yake qara gaba,tun tana daurewa daga kwance harta miqe ta zauna sosai,kafin wani lokaci mararta ta dauka itama,ta hada gumi sharkaf duk da ac din dake aiki a dakin.

Cikin ikon Allah ummu ta leqa dakin da kanta ganin nujood da zasu kwana dakin tare bata gama tata hirar ba bare ta shiga,da sauri ummu ta qaraso tana mata sannu

“Bayan ne?”

“Harda marata ummu” ta fadi muryarta na karyewa tana dafe da marar saboda wani irin ciwo da take mata.

Daga nan inda take bata matsa ba ta fara qwalawa latifa kira,kiran da yaja hankalinsu anty halima suka shigo.

“Amma fa kamar mai naquda,kuma cikin kamar baiyi girman da zata haihu ba”

Mmn muhassana matar uncle dinta ta fada

“Shine nima abinda na gani,inaga ki shirya keda halima ku bita,kome mene zasu fada,Allah ya sawwaqe” ummu ta fadi tana dafe da widad din,kamar ta cire ciwon daga jikinta,ba jimawa naadir yace ya fidda motar,anty madeena na riqe da ita suka fice kowa na mata sannu.

Babban private hospital ne daya hada qwararrun ma’aikata a cikinsa,kai tsaye sukayi amfani da file din mommyn muhassana tunda a nan suke ganin likita,kuma family file ne dasu,aka turata labor room bayan sun gama nata gwaje gwaje da tambayoyi.

Idanu ta dinga rarrabawa sanda sukayi maganar ta cire pant dinta,bata fahimci me za’a yi ba,ta cire ta tsaya suka buqaci ta kwanta ta kuma bude su gwadata.

Qwalla ta dinga yi sosai,ga zafin ciwon mara dana baya ga kuma budetan da nurses sukayi

“Labor kikeyi,kuma nan da asuba zuwa wayewar gari zaki iya haihuwa,don yanzun haka kinkai 4cm” abinda suka gaya mata kenan,abinda ta gayawa su anty halima.

Mamaki sosai suka dinga yi,don duk kowa kallon cikin suke baifi watanni biyar ba,tunda bai fito ba sosai,ba jimawa suka bata gado da daki,anty madeena kuma tayi waya gida ta gayawa su ummu,nan da nan saiga ‘yan gidan sun fara zarya zuwa,itakam widad batasan ma me akeyi ba,don tana labor room private room da aka bata,basu sukabar asibitin ba sai sha biyu na dare,aka bar anty halima da anty deena.

*_A R U B U C E T A K E_*

K’arfe takwas na safiyar ranar Allah ya bawa widad ikon haifo santalelen d’a namiji mai kama da abbas SAK!,tamkar yayi kakin yaron ya ajjiye,ko kuma photocopy dinsa akayi yana yaro aka ajjiye,wannan kusan itace kalmar da kowa yaga yaron ke fada

“Tabdi,wai don Allah a wanne waje wannan yaron yaje ya boye kansa?” Tambayar da anty haleema ta yiwa mommyn muhassana kenan

“Kin rigani ne a fili,na rigaki a zuci halima,ciki a ido dan qarami amma yaro tubarkalla ma sha Allah?,wacce addu’a kikeyi ne widad?” Widad dake jingine da jikin gado idanunta a lumshe murmushi kawai ta saki cikin jin nauyi,babu abinda take tunawa sai iein gwagwarmayar da tasha,wai dama hakan kowacce mace keji a sanda tazo haihuwa?,amma duk da hakan duniya cike take da ‘ya’ya?.

A safiyar ranar asibitin yayi wata irin cika da ‘yan uwa da abokan arziqi,duk wanda ke asibitin a ranar ya fahimci lallai haihuwa ce me kima da daraja aka yiwa wannan family,bata wani jima ba suka sallameta bayan sun tabbatar da komai nata lafiya.

Ita a cikin jikinta take jin wani banbarakwai,idan ta dubi kyakkyawan jaririn mai fuskar uncle abbas dinta taga wai a yanzun danta ne itama,mallakinta.

*A B B A S*

Yana tsaye sakiyar parlor din yana saka links din hannun rigarsa,yanayi yana duba agogo gami da dubansu mimi da nawwara da suka sanya yusra a gaba suna mata wasa,su a lallai ga manyan yayye.

Lokaci lokaci yana kallon qofar kitchen dinta,ya danja tsaki yana yarfe hannuwa,shikam gaba daya yayi dana sanin sanyata aikin ma,da yasan haka zata jawo masa yayi late da da kansa zai shiga ya hada breakfast dinsa yadda ya saba wasu lokutan,ta sani fa yau din zaiyi tafiyar,amma ta kwanta tana bacci abinta babu abinda ya dameta har sai da ya tasheta, just ruwan baqin shayi da soyayyen qwai amma ya gagara ta kammala masa,a lokacin widad ke ransa,yaji wata muguwar kewarta ta saukar masa,sai yake tunanin zaiyi wuya idan bai biya ya taho da ita ba idan ya tashi dawowa daga sokoto.

Wayarsa dake aje saman briefcase dinsa ta dauki tsuwwa,ya sunkuya ya dauki wayar yana duba me kiran,ya dan saki fuska ganin muhsin ne,jiya jiya suka gama waya dashi,ya danyi mamakin kiran,to amma maybe wani abun ya taso ne,saiya daga wayar ya saka a kunnensa.

Agurguje suka gaisa ya sanar masa da saqon kiran

“Ni zan tayaka murna….ko kaine zaka tayani?,…ko duka mu taru mu taya juna?” Dan murmushi ya sake,fararen jerarrun haqoransa suka bayyana

“Eheen……me ya faru?”

“Kayi d’a,ni kuma nayi jika,widad ta haihu” unexpected maganar yazo masa,sai ya fidda idanu waje

“Bama haka dakai muhsin”

“Kuma yau ba zamu fara ba,ka samu d’a na miji alhmdlh”

“Allahu akhbar,Allahu akhbar,Alhamdulillah, Alhamdulillah” shine abinda bakinsa kawai ya iya maimaitawa cikin wani irin yanayin madaukakin farincikin da shi kansa baisan adadinsa, uncle muhsin yayi masa barka don tabbas yasan ya fishi cancantar ayi masa barka,ya kuma ce yana jiran goron albishir dinsa sanann ya katse wayar don ya barshi yayi sharing farincikin wa danginsa.

Wayar kamar zata fadi a hannunsa haka yaji,ya rasa da wa zai fara sharing wannan abun farincikin,sai kawai ya kamo.su mimi ya rungumesu cikin jikinsa yana ta maimaita hamdalar da tun dazu taqi barin bakinsa

“Daddy menene?” Mimi ta tambayeshi tana kallon fuskarsa

“Antynku ta haihu yanzu” wani irin tsalle ta buga cikin farinciki tana kallon nawwara

“Nawwara mun sake samun baby,anty ta haihu,yanzu mun koma mu haka ko daddy?” Ta fada tana daga yatsunta guda hudu,kai ya jinjina mata murmushi yaqi barin fuskarsa,bakinsa kuma ya gaza rufuwa

“Bari naje na gayawa mummy” tayi maganar tana zame jikinta daga na abbas din,ta kuma ruga kitchen da gudu.

Ta gama zuba ruwan tea a flask kenan mimi ta fado kitchen din,ta juyo ta zabga mata harara

“Ban hanaku wannan guje gujen ba?,saikun fadi ku ishi mutane da koke koken banza”

“Anty ce ta haihu mummy” da sauri ta juyo tana dubanta

“Wacce antyn?”

“Antyn nan gidan,anty widad” wata mummunar faduwar gaba da tunda take zata iya cewa bata taba jinta ba banda randa abbas ya sanar mata qarin aurensa ba taji,ta zaro dukka idanunta tana kaiwa bakin mimi bugu

“Kijimin yarinya da shegen jawowa kai masifa,shashasha wadda batasan ciwo da matsalar ‘yan uba ba,baku da ‘yan uba a cikin gidan nan,kada na sake jin kinyi wannan maganar” dafe bakinta yarinyar tayi duk da Allah ya taimaketa bata sameta da kyau ba

“Wallahi mummy d……..” Tsawa ta daka mata ba tare data barta ta gama fadin abinda zatace din ba

“Fitarmin a kitchen masu shegen surutun da zai halakaka idan bakayi wasa ba”(subhanallah,yana da kyau mu dinga iya bakinmu akan yaranmu,komai qanqantar kalma mu kiyayeta mu guji fadarta akan yara saboda tsanani girma da kuma saurin tasirinta a kansu).

Bin yarinyar tayi da kallo harta fice sannan taja tsaki kamar zata tsinke harshenta,ta kuma juya tana ci gaba da rufe flask din,saidai har a sannan qirjinta bugawa yakeyi.

Komai ta shirya kan tray,duk da ba wani abun azo a gani bane,amma.bataso takai masa wani abun yace babu kaza ya sake sakata tashi

“Maimakon ya wuce ya samu eatery akan hanya yayi breakfast dinsa shima” ta fada cikin ranta tana gunguni,har yanzu zuciyarta ba dadi idan ta tuna abinda mimi ta fada,dole ta kwabi yarinyar don kada ma ta sake magana irin wannan,kada wataran ta fada da bakin mala’iku,’yan ameen suna kusa su amsa.

Cikin tray din ta dauko flask da cups din ta fito daga kitchen din,dai dai sanda suke waya da yaaya bara’atu bayan sun gama waya da hajiya

“Yanzun ina shirin tafiya sokoto muhsin ya kirani ya gayamin” shuru ya danyi fuskarsa daukr da wani irin murmushi da zai fayyace maka farincikin dake zuciyarsa bazai misaltu ba,ya sake murmusawa sanann yace

“Eh wallahi…..an samu baby boy”.

Cak komai nata ya tsaya da aiki na wucin gadi,kunneta yayi toshewar data kasa jiyo abinda yaci gaba da cewa,kalamansa zuwa ga yaaya bara’atu sai taji kamar ba hausa bane wani yare yake daban,sai ta dinga jinta kamar a duniyar mafarki ko kuma daga bacci ta tashi,daga bisani kuma kamar wadda babbar mota tazo ta daka haka taji kowanne sashe na jikinta ya saki,har kwanukan hannunta suka zame suka tarwatse a wajen,qarar faduwarsu da kuma fashewar flask din mai cike da ruwan zafi yaja hankalinsa daga wayar kan wayar da yakeyi,ya miqe da sauri yana katse wayar hadi da furta
[11/05, 2:59 pm] +234 810 324 4136: *H U G U M A*
*Arewabooks:Huguma*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)

Back to top button