A Rubuce Take Book 2Hausa Novels

A Rubuce Take Book 2 Page 30

Sponsored Links

Part 02

Page 30

Mummy ce dauke affan da yake faman tsala kuka,kukan nasa daya dinga shiga kunnuwan widad kamar a duniyar mafarki

“Karbeshi ki bashi yasha,kamar bacci yakeyi” mummyn ta fada tana miqa mata shi,saidai ko motsawa batayi ba bare tayi azamar karbarsa,abinda yaja hankalin mummyn kenan

“Ke widad…. widad lafiya?” A hankali ta ajjiye affan ta zauna tana jan widad din cikin jikinta gami da ambaton

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, Hasbunallahu wani’imal wakil” ganin kamar tana neman fita a hayyacinta,addu’o’i ta soma karantawa tana shafa mata a fuska,a hankali sai nutsuwarta ta fara dai daita,ganinta ya fara dawowa dai dai,ta zubawa mummyn idanu wasu hawaye masu zafin gaske suka fara zarya akan fuskarta.

“Meyake faruwa?,me ya sameki?”

“Mummy cikina ne yakemin wani irin ciwo”

“Ya subhanallah” ta fada wani sashen na zuciyarta yana mata wasi wasi,yanayin da taga ta shiga baiyi kama da yanayin ciwo ba,yafi kama da wanda yaga wani mummunan tashin hankalin

“Bari na kira saleem sai mu muje kiga likita,ai bai kamata a zauna ba” kama hannun mummyn tayi

“Aah mummy,addu’a zakici gaba da yimin,ko yanzun da kika yimin na samu sassauci” kai ta jinjina badon ta yarda da widad da abinda yake damunta ba,a haka ta sakata ta shayar da affan saita sake karbarsa ta fita,saidai fiye da rabin hankalinta yana kan widad din,duk bayan wani lokaci saita leqata tare da tambayarta ya jikin?,akwai abinda take buqata?,saidai tace babu.

A ranar yadda taga baqar rana haka taga baqin dare,baqin daren daya zame mata baqiqqirin,yayi mata kuma tsaho tamkar daren mutuwa,tayi dukka Wani qoqari na fahimtar da abbas abinda yake zato ba haka bane amma yaqi saurararta,ta kira har sau ba adadi,ta tura masa tex na bayanai har batasan yawansu ba amma ba abinda ya canza,kafin gari ya waye ta fige ta fita hayyacinta da tashin hankali,kamar yadda shima a nasa bangaren wani irin firgici tashin hankali da razani yaso da’ai d’aitashi,duk sanda ya tuna har lawal ya shaida fitar tata ya kuma bashi tabbacin zuwa take hotel din tana kuma kawo maza sai yaji kamar zuciyarsa ta fashe ya mutu.

Sanda mummy ta shigo da safen ja da baya tayi tana salati ganin yadda fuskar widad din tayi jajur da ita ta tasa

“Ke tashi,tashi ki gayamin gaskiyar abinda yake damunki” mummyn ta fada tan ajjiye kayan tea data shigo mata dasu,ta nemi gefanta ta zauna ta a nutse tana rutsata da ido.

Batasan ba zata iya daukan wannan tashin hankalin ba,batasan zuciyarta ba zata iya jure wannan al’amarin ba sai data dora kanta a kafadar mummyn,a sannan ta sake gasgata uwa rahamace da babu kamarta a doron duniya,tayi kuka tayi kuka,har sai data zagwanye dukkan wasu damuwoyi data jima tana dakonsu a ranta,sannan a hankali cikin wani irin ciwo da zuciyarta ke mata ta furta ma mummyn abinda ke faruwa

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” ta maimaita sau uku cikin mugun gigicewa tana daga widad daga kafadarta

“Da wannan abun kike boyewa?,wacce iri ce ke widad?,to ni kaina wannan abun yafi qarfina,yafi kuma qarfin jina da kunnuwana,bazan iya jin wannan abun ni kadai ba,maza tashi”ta fada tana dauko ruwan tea din data shigo dashi

“Tashi kisha wannan yanzun nan fita ta kamani,banga ta zama ba” haka ta dinga bata tea din,tana kurba tana jin kamar mutuwa takesha,mararta kamar zata fashe saboda tsananin ciwo,amma wannan ciwon bashi ke damunta ba,salama ne akan ciwon dake danqare cikin zuciyarta.

Mummy na bata tea din tana sake maimaita innalillahin saboda yadda batun ya daki zuciyarta,ta sani ta kare kanta da mutuncinta tsahon rayuwarta,dai dai da rana daya kuma bata taba hutawa da yiwa yaranta da jikokinta addu’a kan samun kariya daga zina ba,tayi imanin addu’arta ba zata tashi a banza ba.

Da cup din ta fice bayan ta sakata kwanciya sanda taga gumi yana yanko mata ko ina

“Ki cire damuwa a ranki,Allah yana tare dame gaskiya muddin kinsan kedin me gaskiya ce,komai daren dadewa Allah bazai bar gaskiya ta tozarta ba” da wannan kalamin na mummy widad ta samu nutsuwa kadan,saidai duk da haka hawaye baibar fita daga idanunta ba,yadda abbas ya rufe idanu kamar yau ya fara saninta,yaqi ji yaqi gani,yaqi tsaiwa ya saurari gaskiyar ta.

Shiryawa mummyn tayi tsaf suka fice zuwa gidan yayanta,tabarsu a gidan ita da affan da su saleem,tace su kula da ita su dinga yawan leqata,zasuje su dawo ita da usama.

Shi kansa uncle bashir ya kadu da jin batun da mommyn tazo dashi,yayi Shuru yana jinjina maganar cikin ransa

“Abinda nake gani,mu basu iska shida ita,shi din na tabbatar tunda jami’in tsaro ne bazai gaza bincike ba,zuwa sannan ya huce ba kamar yanzun da yake kan doron zargi ba,kuma wala’alla ya kammala bincikensa sai mu tuntubeshi muji daga gareshi,zan shigo naga widad din in sha Allah,kici gaba da tausarta komai zai dai daita in sha Allah” mummyn ta gamsu da shawararsa,da wannan kuma ta dawo gida ta shiga kula da widad din,dukkan qoqarinta ta sanaya akanta,bata barinta ta kebe kwata kwata saidai idan ya zama dole gudun kada ta shiga damuwa,saidai abar zuciya da abinda takeso,wata muguwar damuwa keta cin ranta ta can qasa,duk da tana ta qoqarin sakewa saboda yadda take ganin mummyn nata tana wahala da ita.

Komai nata mutanen gidan sun bashi muhimmanci,kowa qoqarin ganin ya nuna mata damuwa da kulawarsa yake,amma har yau al’amarin abbas yaqi sakinta,mamakinsa ke cikata a duk sanda ta tunashi,a kowacce rana tana duba wayarta sau babu adadi waiko zataga kira ko saqonsa,kozai bayyana mata ya gano qarya ne sharri ne,ya gano kuskuren fahimtarta yayi,a kullum dakonsa takeyo ko zataga saqon ban haquri,amma shuruuuuu kakeji,babu shi babu dalilinsa.

Idan tace zata kwatanta yanayin da rayuwarta ta fada a wannan tsukin ma bata baki ne,wata irin damuwa me cin gangar jiki da ruhi,duk yadda take wuni cikin jama’a idan dare yayi tazo bacci saita kasa,kuka kuwa ta yishi kamar hawayen idanunta zasu qare,wai yau ita uncle dinta ke tuhuma da laifin zina,zina fa?,saita rushe da kuka tana jin kamar ranta zai bar gangar jikinta ta huta.

*H A F S A T*

Duniya ta zame mata sabuwa,sai takejin kamar bata da sauran wata matsala kuma yanzun,duk sanda ta dubi sassan widad ta ganshi a garqame,ta tafi kuma ba’asan ranar dawowarta ba,tayi rawa tayi juyi duk ita kadai,ta kuma kira habiba tayi mata godiya mai yawa,tare da fadin zasu koma wajen malaminta nan kusa,amma abu daya dake damunta,irin yadda abbas din gaba daya ya canza,bashi da kuzari bare walwala, fara’a kam babu ita,tuni tayi nata waje,duk da qoqarin da takeyi taga ta gyaggara yadda widad keyi amma babu abinda ya canza,sai abubuwa suka fara mata wuya,ga qoqarin ganin ta dauki pattern din widad wanda dukka jiki da zuciyarta suka gaza saboda bata saba ba,ga sauyin yanayin abbas din.

Shikam kome baisan yana yi ba,duk yadda yaso ya manta komai ya cisge widad daga rayuwarsa amma ya gaza,abun ya masa tsaye a rai,ya tsaya masa fiye da duk yadda ya zata,ko mutuwar mahiafiyarsa ya dangana amma ya kasa dangana da widad din,ya tsaya a gaban mudubi ya kalli kansa da kansa ya yiwa kansa fada amma ko gezau,yasha rasa bacci cikin dare idan abun ya taso masa amma abu guda zuciyarsa keta nacin bashi shawara

“Ki saketa kawai ka huta,ka saketa zaka manta da ita” saidai sam hannuwansa sun gaza rubutu takardar sakin.

Irin wannan maganar hafsat din tayi masa,bayan sallar isha’i yana zaune a falonsa yana kallon labaran duniya a tv,ga mai zuzzurfan hankali duba daya zaiyi masa ya gane tunani yakeyi bawai kallo ba,ta turo qofar ta shigo idanunta a kansa,ta dauke kai tana jan tsaki qasan ranta

“Haka zakayita yi kazo kuma ka haqura,kun rabu kenan har abada billahillazi” kafin ta qaraso ta sauya fuskarta zuwa yanayi na tausayi

“Daddyn mimi,nifa banajin dadin ganinka a haka gaskiya,wannan abun tunda ya riga daya faru,kawai ka sawwaqe mata,saika samu nutsuwar zuciya idan aka rabu gaba daya,badai affan ne zai hada ba?,ka dauko yaronka,na maka alqawarin zan riqeshi tare dasu mimi” kamar wanda wuyansa ya sage haka ya daga kai yana kallonta,wani irin duba ne da yafi kama da duban baki da hankali,duk yadda zuciyarsa ke bashi shigen wannan shawarar amma ai bata taba ma kawo masa ya rabo affan da mamarsa ba,sai kawai ya ajjiye remote din hannunsa ya miqe tsam ya wuce bedroom dinsa.

Da kallo ta bishi cikin mamakin yadda abubuwan har yau suka kasa saitan mata yadda takeso

“Wai me yake faruwa ne?” Ta tambayi kanta,sai ta miqe tabi bayansa,saidai ta sameshi ya wuce toilet,da alama kuma alwala yakeyi,dole ta fito,ta wuce sassanta ta kirayi habiba ta tsegunta mata damuwarta

“Ai dama yace kibi a hankali,don har yanzu zuciyarsa na ga yarinyar,zuciyarsu guri guda take,rabasu sai anbi da nutsuwa da taka tsantsan,don haka kibi a sannu,a hankali komai zai shigeshi ya rabu da ita harma ya manta da ita ba tare da ya sani ba,a yanzun dai gidanne ta barshi har abada,malam yace bazai bari ta dawo miki ba” taji dadi tayi maya godiya,ta kuma koma sashen,saidai tana murda qofar ta jita a kulle,tayita knocking amma ba’a bude mata ba,abun ya mata ciwo yadda a yanzun yake banzatar da duk wasu al’amura nata fiye da yadda take gani a baya,to amma data tuna da zancan da suka gama yi da habiba sai taji zuciyarta ta wanke,ta juya tana cewa

“A juri zuwa rafi da tulu da diban ruwa,baqar matsiyaciya yadda kika fiddani daga rayuwarsa,kin bar gidan nan har abada,kuma saikin fita daga zuciyarsa kema haihata haihata” ta fada a fili a hankali kamar me sambatu.

Yana fitowa kira yana shigowa wayarsa,kamar bazai dauka ba amma sai ya koma saman sofa bed ya zauna yana daga wayar,daga can uncle bashir yayi sallama jin ya daga wayar,ya amsa masa da muryarsa data zama me sanyi sosai.

Gabatar masa da kansa yayi,sai suka sake gaisawa cikin mutuntawa,sannan uncle bashir ya sanar masa da dalilin kiransa.

Wani irin zafin tururi ya dinga ji yana taso masa a qirjinsa,ya dinga furzar da iska daga bakinsa,da qyar ya iya controlling kansa kafin ua fara magana

“Na sameta da laifin cin amanata ne,tana zuwa hotel tana kuma kawomin maza har cikin gidan aurena,yanzu haka ina da shaida a hannu na,kuma ita kanta ta amsa da bakinta taje”

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” uncle bashir ya dinga fadi

“Yanzu babu ta inda kake gani za’a gyara lamarin?”

“Sai nayi bincike shine abinda zan iya cewa” ya fada a taqaice,don gaba daya bai qaunar maganar,sai yaji numfashinsa yana riqewa.

A sanyaye uncle bashir ya kalli mommyn widad

“Ya kukayi dashi?” Bai boye mata komai ba ya gaya mata,ta sake maimaita innalillahin da tun zuwan widad bata bar bakinta

“Ina zaki?” Ya tambayeta sanda yaga ta miqe

“Kiranta zanyi naji waye din yazo kuma da gaske taje hotel din ita?” Daga haka tayi gaba,ta isa qofar dakin ta tura ta budeta, widad ta daha jemammun idanunta wanda ta manta rabon da suga kwalli tana duban mahaifiyarta,tana zaune saman abun sallah,ta hade tafukan hannayenta waje daya,da alama addu’a takeson yi amma ta rasa me zatace

“Taso” mommy ta fada tana yafitota,saita miqe tsam tabi bayanta.

A nutse ta amsa musu duk tambayar da sukayi mata

“Dama shi baisan abubakar ba?”

“Zuwansa na farko kenan shida baaba hamisu” duk sai sukayi shuru suna jinjina abun da yadda za’a warwareshi

“Bari nayi kiran mahmuda,dole yasan abinda ake ciki,don na fuskanci abun babba ne” uncle bashir ya fada,ya sake fidda wayarsa ya zayyanewa abban komai.

Shima dai kiran sunan Allah ya dinga yi

“Ku kawomin ita kano” shine abinda ya fada,a washegari mummyn da uncle bashir suka yi mata rakiya zuwa kano,a gidan ummu suka sauka,suna shiga kuma widad din ta fada jikin ummu tana sakin kuma me tsuma zuciya.

Wani mawuyacin hali ummun ta shiga,ta dinga goge qwalla zuciyarta fal tausayin widad din tata,ganin yadda tayi wata rama ta sake yin fari faaattt,hatta fatar bakinta a bushe take

“Tun yaushe kika shiga wannan yanayin amma ba’a sanar min ba?,kiyi haquri ki kwantar da hankalinki,Allah yana tare dame gaskiya,kuma zai fiddaki ko ba dade ko bajima” haka ummu ta dinga fada cikin tashin hankali da yanayi na tausayi,zuciyarta kamar zata tsaga qirjinta ta fito,tasa aka gyarewa widad din daki,sannan aka shirya mata abinci kamar yadda aka shiryawa mommy da uncle bashir,amma komai widad din ta kasa tabawa,saboda bata iya cin komai,daga ruwa sai lemo,na fata kona gora,ita kanta mummyn tayi tayi ta dinga cin abincin amma baya wuce mata,kota kwatanta ci baya ciyuwa sai tayi amansa.
[20/05, 8:46 am] +234 810 324 4136: *H U G U M A*
*Arewabooks:Huguma*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)

Back to top button