A Rubuce Take Book 2Hausa Novels

A Rubuce Take Book 2 Page 18

Sponsored Links

Part 02

Page 18

 

Tun daga harabar gidan ta fara fahimtar daga wanne irin gida widad din ta fito,daga yadda taga abubuwa suna gudana tun daga farfajiyar gidan da aka cika da rumfuna jikinta ya fara sanyi,wani irin kishi da bacin rai yayi mata tsaye a wuya,a haka dai ta daure,ta fita a motar,suna biye da hajjaa data zame musu jagora cikin gidan.

Tarba ta girma akayi musu bisa jagoranci anty deena,ta shirya komai yadda zai qawatar da baqin cikin girma da karamci,komai kasa cewa tayi,sai idanunta dake biye da komai na gidan,tun daga falo zuwa wani falon da aka tanada don su kadai,ko da mutum guda bata gaisa ba,sai ido da takebin mutane dashi,sannan ta watsar kamar babu ita a wajen.

Komai dake gudana gwaggwo mero na ankare dashi,har zuwa sanda suka kadaita a falon,aka kuma turo musu widad dake shirye cikin wani dandasheshen lace da mummyn ta ta dinka mata,wanda kudinsa yakai dubu sittin.

Lace dim shine abu na farko daya fara tsone ma hafsat din idanu,tasan kudinsa sarai tunda sana’arta kenan,wani tashin hankali ya rufto mata,har ta gaza dauke idanunta daga kan lace din,tana jin kamar ta tashi ta yageshi daga jikin widad.

Duk yadda taso ta tausa zuciyarta ta amsa gaisuwar da widad din ke mata,ranta fes fuskarta cike da walwala amma ta kasa,daga qarshe ma sai tayi bandaki kamar wadda wata buqata ta kama.

Kasa riqe kukanta tayi,sai data matsi hawaye sosai sannan ta fito bayan ta waske da dauro alwala,ta riga kowa tayar da sallah tun farkon muhtarin sallar azahar.

Tana kan abun sallah ba tare data waiwayo ba,tana jinsu suna yaba yaron da aka shiryashi cikin wasu irin kaya masu asalin kyau da tsada na qasar saudiyya,kowa ya daukeshi sai ya fadi kyau da kuma tsantsar kamannin dake tsakaninsa da babansa,abinda ya sake dagula mata lissafi kenan.

‘yan awannin da sukayi ta shiga quncin da sai data gwammace bijirewa zuwan tayi koma meye suyi da abbas din,idanunta sunga abubuwa kala kala,wadanda da wannan bacin rai tayi guzurinsu zuwa gida.

Taro ya watse lafiya cike da tarin alkhairi da yaron ya zoma iyayensa biyu dashi,widad kuma ta shiga ci gaba da samun kulawa irin ta tsaffin da sukaga jiya sukaga yau,gefe guda ga gudunmawar yayyen zamani irinsu anty deena anty madeena,da matan abokai na qwarai irinsu fanna da sha’awa.

*_DUKKAN ME RAI MAMACI NE_*

Cikin sati biyu kacal muhammad da suke kira da affan ya fara wayo da wani irin girma dake alamta qiba zaiyi,daga shi har mamansa widad fatarsu ta qara gogewa,sunyi wani irin kyau na samun nutsuwa da kulawa,jegonta take hankali kwance,kulawa da soyayya tako ina,kusan ko yaushe suna manne a waya ita da abbas din,sukan shafe lokuta sosai suna hira,irin hirar dake debe kewa da sawa zuciya nutsuwa.

Kwana biyu kacal yin wayarsu yadan ja baya,data tambayeshi yace hajiya ce bata jin dadi a kwanakin,a ranar sau biyu tana kiran hajiyan taji jikinta,cikin dauriya da murmushi take amsa mata

“Da sauqi fa,kawai abbas ya tashi hankalinsa ne” kiran data mata a washegari da safe wanda shine kiran na kusan biyar hajiyan ta daga suka gaisa,ta tambayi dan jikallen nata wanda yake kamar shi daya ne jika a wajenta saboda yadda takejinsa a ranta

“Allah yayi miki albarka widad,ya dafawa al’amuranki,kiyi haquri,kiyi juriya,Allah ya baki ikon kula da mijinki da dukka abinda ma zaki haifa a gaba” bata kawo komai a ranta ba,saima nauyin addu’ar hajiyan ta qarshe,duk da haka saita samu kanta da cewa

“Ameeen” suka dan sake gaisawa sannan sukayi sallama da hajiyan.

A ranar duka basuyi waya da abbas ba,tadan shiga damuwa amma daga baya ta bayar wataqila yanayin aiki ne,wanda wasu lokutan dama idan ya sakasu a gaba basu da wani sauran sukuni har sai sun gama sannan suke samun sauqi.

Washegari affan yana saman cinyarta tana shayar dashi cikin dakinta,ita dashi dukkansu sunyi wankansu fes,sai qamshi suke fitarwa,so take ta gama bashi ya qoshi ta kaiwa latifa shi ta goyashi,kamar daga sama sai taji muryar uncle muhsin daga falo,cikin zumudi ta zare maman daga bakin affan ta sanyashi a kafada tana shafa bayansa,don yana shirin fara rigima ne,don da alama bai gama qoshi ba,tayo falon dashi.

A tsaye ta sameshi shi da tsoho me ran qarfe da kuma ummu,yadda dukkansu suka bita da idanu haka kawai sai taji ta tsargu,saboda basu taba yi mata irin wannan kallon ba,duk sai taji qafafuwanta sunyi laushi,ta daure ta qarasa falon tana masa sannu da zuwa,ya miqa hannu yana cewa

“Bani takwara na,shiga kitchen ki yiwa latifa magana ta tayaki hada kayanki zamu wuce bauchi” sosai maganar ta daketa,ta dubeshi da kyau

“Bauchi kuma uncle?,ina cewa yanzu ka shigo?” Kai ya gyada mata

“Eh,rakani zakiyi,flight zamu bi,kuma yanzun haka da nasa a siya mana ticket saura awa daya duka duka lokacin tashinmu yayi” kasa ci gaba da tambayarsa tayi,kawai saita juya tayi abinda yace din,saidai ko latifa dake hada mata kayan batace komai ba,bata tambayi ba’asin irin wannan tafiyar ta gaggawa ba,sai ta sake jin cewa lallai akwai wani abu dake faruwa.

Samun kanta tayi da gwada wayar abbas don ta tambayeshi yasan wani abu akan tafiyarta?,ta kuma shaida masa tahowarsu amma amsa daya computer ke bashi wayar a kashe take,dukka.layukansa,da personal da na aikin gaba daya,saita jefa wayar jakarta kawai ta dauki mayafin abayarta ta roller ta fito.

Sallama ta dinga yi da mutanen gidan,duk da tana gaya musu zata dawo sai tayi arba’in zata koma,ba wanda yace mata komai daga uncle muhsin har ummu,a haka suka fice a gidan ta cikin motar daya daga cikin samarin gidan da zai saukesu a airport.

Tun saukarsu a garin bauchi taji gabanta yana wani irin faduwa mai tsanani,nutsuwarta tana neman barin gangar jikinta,ta dauka irin yanayin da take tsintar kanta ne duk sanda sukazo bauchin,amma saita karancin yanayin ya sha bambam da wannan da take tsintar kan nata a ciki,tayita kokawa da zuciyarta har zuwa sanda taga sun doshi hanyar gidan hajiya.

Waiwayowa tayi tana duban uncle muhsin

“Na dauka gidanka zamu sauka?”

“Aah” ya fada a taqaice,daga haka shi da ita ba wanda ya sake magana,har zuwa sanda suka gangara gefan titi suka shiga faffadan layin dake malale da kwalta.

Mummunar faduwa gabanta yayi lokacin da taga jama’ar dake zaune a qofar gidan,qarqashin rumfar tempol,qofar gidan cike yake jama’a,haka ta dinga ratsa mutanen qafafunta kamar ba’a jikinta ba, zuciyarta na wani irin bugu,ta kuma kasa tambayar uncle muhsin komai,burinta kawai ta isa cikin gidan ta gano abinda yake faruwa.

Bata tsaya ba har sai data isa falon hajiya da shima yake tanqam da jama’a,sai surutai kadan kadan da kuma koke koke,kamar wata mutum mutumi ta tsaya tana qarewa kowa dake falon kallo,bakinta ya gaza cewa komai

“Kamata ki zaunar da ita” taji muryar Gwaggo mero tana fada,sai a sannan ta samu qwarin gwiwar kallon hajja dake sama mata wajen zama bayan ta karba affan ta miqawa yaaya bara’atu

“Waye ya rasu hajjaa”

“Kiyi haquri ki zauna,hajiya ce Allah yayi mata rasuwa” kamar an qwala mata qarfe haka taji,kunnuwanta suka daina ji na wasu sakanni kafin su dai daita, bakinta da dukka ilahirin jikinta ya fara rawa,Allah ya taimaketa ta kama kalmar

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” kuka mai tsananin qarfi ya qwace mata,sai kuma numfashinta ya fara sarqewa,ta fara kokawar qwatarsa,daga haka kuma saita daina gane komai.

Sanda ta farka cikin setting room ta samu kanta ita da hajjaa nujood da bilkisa matar suraj,suna mata sannu amma sake tanbayarsu take da gaske hajiya ta rasu ko kuma mafarki tayi?.

“Allahn da ya fimu sonta ya dauki abarsa,addu’a ce kawai zata nuna zallar soyayyar da muke mata ba koke koke ba” nasihar da suka dinga mata kenan cikin kwantar da kai, saita fashe da kuka sosai tana jerawa hajiya addu’o’i har kamar ba zata tsaya ba,a haka suka miqo mata affan daketa rigima ta soma shayar dashi,amma hawayen fuskarta yaqi tsayawa,duk sanda ta kalli affan din sai taji zuciyarta ta sakeyin rauni,yayi rashin kaaka,kuma masoyiyarsa,wanda tun yana ciki take qaunarsa da begen ganinsa amma Allah bai qaddara hakan ba.

Ba shakka hajiyan ta dace,domin dukkan wata siffa dake alamta kyakkyawan qarshe hajiyan ta sameshi,kama daga yanayin yadda ta mutu da cikakkiyar kalmar shahada a bakinta,zuwa yabo data dinga samu daga wajen mutane,gidan kamar xai tsage da jama’a,har maqwafta a cike yake babu masaka tsinke.

Ta idar da sallar la’asar tana zaune saman abun sallah,har a sannan qwalla bata bar fita daga idanunta ba,tuni kanta yake sara mata da matsanancin ciwo,husna ‘yar nasmah qanwar abbas ta shigo mata da abinci,ta kalleta ta kalli abincin

“Ina abbansu mimi ne?”

“Ni tun safe ban qara ganinsa ba” hankalinta sai ya qara daukuwa a kansa,tasanshi sarai,tasan irin soyayyar dake tsakaninsa da hajiyan,ya kamata a duba halin da yake ciki,itama tunda tazo bataji an ambaceshi ba,don haka ta miqe ta goyawa husna affan sannan ta canza hijabin jikinta zuwa babban daya saukar mata har qasa ta fita a dakin.

Da qyar aka gano mata shi a dakin su umar,sanda tayi sallama ta shiga dakin kasa ganinsa tayi saboda duhun da dakin yake dashi,ta laluba makunnin fitilar dakin ta kunna,haske ya wadaci ko ina,mamaki ya kamata ganinsa zaune saman abun sallar, idanunsu suka hadu waje guda,sai taji wani rauni ya ziyarceta,kuka take da muradin yi amma kuma zuciyarta na gaya mata ba haka ya kamata tayi ba.

Takowa tayi a hankali zuwa inda yake zaunen har yanzu idanunsu na manne da junna,fuskarsa ta fada wuni guda,sai wani irin jigata da idanunsa sukayi,dab da zata iso ya shafa addu’a sannan ya miqa mata hannunsa,ta dora nata hannun akai,zai mata masauki saman cinyarsa ta zame ta zauna daga gefansa tana kallon qwayar idanunsa dake cike da wani irin tashin hankalin da ba kowa bane zai iya karanta,tsananin jarumtarsa ya boye komai

“Yaushe kukazo?” Ya tambayeta da wata irin murya dake cike da sanyi da jigata,ta danyi gyaran murya kadan don kada ta fashe masa da kuka

“D’a…..d’az……” Kasa qarasawa tayi,dukkan wata jarumta ta qare,saita fashe masa da kuka harda sheshsheqa,baice komai ba illa rungume kanta da yayi a qirjinsa yana shafa bayanta,yadda kanta ke qirjinsa haka take jiyo yadda Zuciyarsa ke wani irin bugawa a hagunce.

Mintuna kusan biyar ta dauka a haka sanann ta fara qoqarin saita kanta,ta daga kai tana dubansa da idanunsa da suka sauya kala,hannu biyu yasa yana goge mata hawayen sanann yace

“Nasan ba wannan ne kukan da kika fara ba,pls karki qara yin wani kukan,hajiya bataso,kiyi mata addu’a” kai ta jinjina cikin aro jarumta,ta gaidashi tare da yi masa gaisuwa,don ya fita cancantar ayi masa gaisuwa,duk kuwa da cewa itama kallon uwa takewa hajiyan,ba zata taba mantawa da gudunmawa da soyayya qauna da kariya data baiwa rayuwarta ba.

“Amma uncle,me kakeyi a nan kai kadai a duhu?”

“Sallah nayi,baki gani ba sanda kk shigo?” Kai ta jinjina

“Na gani,amma idan ka shiga cikin jama’a kamar sai yafi,a nan din tunani zaiyi maka yawa ne” kai ya jinjina kawai

“Kaci abinci?” Ya sake girgiza mata kai,saita ajjiye masa affan ta shiga cikin gida ta samo masa abinci me kyau,saidai gaba daya ya kasa ci,ya ture plate din yace

“Samomin coffee kawai ya isa” haka ta koma ciki ta hado masa coffee din,a hanya ne suka hadu da hafsat tana shigowa goye da yusra,yadda ta dauke mata kai itama haka ta bawa banza ajiyarta ta shige.

Coffee din ya shige cikinsa da qyar,ya kama hannuwanta ya riqe cikin nasa yana cewa

“Allah yayi miki albarka” don badon tazo ba yanajin azumin yini biyu zaiyi,don shidai ko qyallin hafsat bai gani ba,duk da ya tabbatar tana gidan,don suna gaban gawar hajiya ta shigo gidan tana runtuma ihun da sai da akayi mata magana.

Bata barshi shi kadai ba sai data sashi gaba ya fito daga dakin ya koma cikin mutane,duk bayan wasu lokutta kuma tana sawa ana duba mata shi da yadda yake.

To rashin mahaifiya wani rashi ne mai mugun ciwon da fadin radadinsa bazai misaltu ba sai wanda Allah ya jarabta dashi, rasuwar hajiya rashine na dukka dangi dama mutanen unguwa,kowa yaga tsananin jarumtar abbas,don ba wanda baisan irin shaquwa da qaunar dake tsakaninsu ba.

A gidan yake kwana shi da widad din,amma daki daban daban,hafsat kuwa yaran take diba su wuce gidan iyayenta su kwana,sai kusan azahar take zuwa har akayi kwana uku.

Randa akayi sadakar ukun da safe ne tsananin ciwon kai na rashin bacci da kuma damuwa suka sanya abbas a gaba,dole ya buqaci tafiya gida don ya kwanta ya huta,duk da bashi da tabbacin yiwuwar baccin.

Farko hafsat yasa widad ta nemo masa su wuce tare,don yasan gidan kansa yayi qura,sanann widad din tana jego ga kuma mutuwar itama yadda ta bugeta tilas tana buqatar hutu,to amma sama da qasa babu hafsat din ba alamarta,dole yasa widad ta shirya suka wuce gidan.

Sosai ta gyara masa bedroom dinsa irin yadda tasan yana so,sannan ta shirya masa dan abinda zaici mai dadi da ruwa ruwa,ta kuma hada masa ruwan wanka mai dumi sosai da qamshi,yayi ya canza kayan,ta sashi a gaba yaci abincin ya kwanta sannan ta baro masa dakin bayan ta sanyashi yayi addu’a.

Falon ta dawo taci gaba da gyaranshi,tanayi tana duba affan dake kwance yana watsal watsal da qafa,ya cusa yatsunsa biyu a baki.

Doko qofar falon akayi lokaci guda ba zato ba tsammani,har affan dake kwance yadan firgita

“Subhanallahi” widad ta fadi tana duban bakin qofar.
[14/05, 12:25 pm] +234 810 324 4136: *H U G U M A*
*Arewabooks:Huguma*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)

Back to top button