Author: Novels

  • Arubuce Ta Ke 68

    Page 68

    A farfajiyar gidan ya cimma yaran suna wasa,ya tsugunna suka dafeshi gaba daya ya miqe dasu,yau din ba yabo ba fallasa,basuyi datti ba amma kuma bai samesu fes yadda yakeso ba,dukkansu kansu a tsefe yake a daure da band,yana rungume dasu a jikinsa suka sanya kai cikin falon dake sassan hafsat din.

    Shima yau dai falon babu laifi,saboda babu dattin,amma bawai kar kar yake ba,yaji dadin hakan har qasan ransa,ya kuma tsinci kansa da fatan samuwar canji daha gareta da kuma dorewar dabi’unta.

    Bata parlor din,don haka ya zarce bedroom din nata kanshi tsaye,har yanzu yaran suna kafadarsa suna masa surutu,ya tura qofar dakin,dai dai sanda ta waiwayo suka hada ido,tana tsaye gaban mudubi,saita dauke kanta tana amsa sallamar,jikinta sanye da wata koriyar atamfa riga da fallen zani

    “Sannu da zuwa” ta fada cikin careless,kamar wanda yaje qofar gida ya dawo,bai amsa mata ba sai daya sauke yaran a qasa,ya saka hannu a aljihunsa ya fidda chocolate ya miqa musu

    “Ku jiremin falo maza mimin daddy” da gudu suka falla sukayi falon kuwa,sai ya maida dubansa gareta,har kullum idanuwansa ba zasu gaji da gayawa zuciya da kwanyarsa yadda yakeson ya ganta ba haka ya ganta ba,kamar yanzun,kai zaka ce matar qauye ce,koriyar atamfar da aka tashi aka yima wani sungul dinki,ba wani abun jan hankali a jikinsa nare style din zamani,daurin kanta kamar na matar qauye,amma duk da haka baiji ya wani tunzura ba,ko tsananin buqatar da yake ciki ce ta kauda duk wani aibu daga idanuwansa?,idanma hakanne harda tasiri ‘yar tsaftar daya isketa a ciki.

    Duk duniya ta shaida auren soyayya sukayi da hafsat din,amma dabi’unta nata nesatata daga zuciyarsa,ya taka a hankali yayi tsaye a bayanta yana goye da hannayensa

    “Tsakani da Allah haka akewa miji maraba?,mijin da yafi wata guda baya tare da iyalinsa?” Waiwayowa tayi ta watsa masa wani kallo,a yau taci alwashin gwada mishi amfaninta,tunda kare ma ai yana da ranarsa,tasan a buqace zai dawo,zuciyarsa cike fal da tarin buqatun da babu wadda zai dosa da nufin saukewa idan ba ita ba

    “Bayan marabar daka samu daga wajen wadda ta fini?,ina cewa bani kadai bace iyalin naka”

    “Na fiki sanin hakan,amma yanzun taki marabar nake da buqata” ya fada yana rungume ta ta baya,saita fara qoqarin tureshi amma ya hana mata wannan damar,har ta gaji ta haqura,sannan ya saketa don kanshi

    “Kome zakiyi ki dinga qoqari kina zurfafa tunaninki,ina yawan gaya miki,ki dinga sanya hankalinki a gaban fushinki”

    “Eh ai dama kullum ni nake da laifi,kaikam baka aikatamin komai,duk wani rashin kulawa da kake nunamin ina hadiyewa baka gani ba”

    “It’s okay…..na sameku lafiya?”

    “Gamu lafiya lau” ta fadi kamar wadda aka cusawa tsumma a baki

    “Ma sha Allah” ya fada yana shafa sumar kansa sannan ya juya zuwa falon,don sam tarbar da yake da buqata ma bata iya taba har kwanan gobe.

    Abinda ya fara dawo masa akai yadda widad tayi welcoming nasa,duk da cikin quruciya take komai…..amma komai nata burgeshi yakeyi,yaga zallar kewarsa a idanunta,irin kewar daya rufe mata idanu ta gaza ganin koda hajiya da take kunya da kuma marmarinta,kewar data gaza boyuwa daga idanunta……irin yanayin da yayita begen samu daga hafsat tsahon shekarun da sukayi a tare amma abun ya faskara.

    Wannan tunanin ya haifar da murmushi saman fuskarsa,bai zauna a falon ba ya dauki yaran suka wuce zuwa sashensa,can dinma ba laifi an dan gyarashi,duk da dama sashensa baya barinsa yayi datti.

    Ba jimawa ta shigo da kayan abinci,ta zuba masa ta koma gefe ta zauna tana danna waya,fuskarta kadaran kadaham,amma bata tsoma bakinta a hirarsa da yaransa ba,sai daya ci rabin abincin,taga babu alamun widad tare dashi sannan ta magantu

    “Ina ka baro antyn tasu?” Hankalinsa nakan zarema yaran uban qayar dake jikin kifin data dafa,bata damu data tsaya ta gyarashi da kyau ta cire qayar ba ya amsa mata

    “Na barta gidan hajiya” haushi ya cikata,saboda ba qaramin aiki ne yake jiran yarinyar ba,taci buri sosai wannan karon,don ta dauki alwashin daga shi har widad din saita fito musu da sabon taku,zuwa weekend din da ya dinga yi babu ita kafin tafiyarsu ta taso ba qaramin qona mata rai yayi ba,saboda ta riga ta saba da ayyukan widad din,wani lokacin tun ranar laraba zata fara hada dalar qazantarta ta jirayi zuwan widad din,tasan idan tazo kamar anyi ruwa an dauke ne,fes ko ina yake komawa.

    Bata sake tambaya ba don kada ya ramfota,amma cikin ranta addu’a take Allah yasa kada tace zata kwana,a badini ji taje kamar ta tafi gidan hajiyan ta janyo widad din tayi mata shegen duka.

    Suna qoshi suka bigire da bacci a wajen,dama kusan lokacin baccinsu ne,hannunsa riqe da yatsar nawwara ya saki ajiyar zuciya sannan ya kalli hafsat

    “Ki kaisu dakinsu kizo ina son ganinki” yayi maganar a tausashe yana duban tsakiyar qwayar idanunta,dauke kai tayi,don batason ya karya mata zuciya kwata kwata,taja tsaki qasan ranta sannan ta yunqura zata miqe wayarta ta dauki tsuwwa,saita dakata ta daga wayar ta sanyata a kunnenta

    “Hello…..kin qaraso?,kina falo?, okay gani nan” sai ta katse wayar,ta sunkuya ta dauki mimi ta fita a falon.

    Miqewa yayi ya shige bedroom dinsa ya zarce toilet,yayi brush ya sake alwala,sanann ya fito ya rage kayan jikinsa ya dawo falon,har a sannan bata dawo ba,bai dauka zata dauki tsahon lokaci haka ba,sai ya kunna tv ya kama labarai ya fara kalla,duk kuwa da cewa hankalinsa baya wajen.

    Kusan minti talatin ba ita babu labarinta,kamar ya shareta sai ya fasa,ya koma ya dauko jallabiyya mai santsi saqar qasar oman ya zuba,ta masa masifar kyau ta qara fidda wannan sirritaccen kyansa,ya dawo ya dauki nawwara suka baro sashen.

    Ba kowa a falon,amma da alama anyi baquwar ta tafi,dakinsu ya kai nawwara sannan ya dawo ya wuce dakinta.

    A gaban mudubi ya sameta tana hada kudi,suka hada ido,tasha jinin jikinta amma ta basar,ya zube hannayensa a aljihun jallabiyyar jikinsa yana mata duban da yasan yana ratsa qashinta da kyau

    “Gani na biyo sahu” ya fada cikin wani salo,ta lumshe idonta, muryarsa ta tabata da kyau,amma girman kanta sai ya motsa

    “Baquwa nayi,kuma yanzun ma wata baquwar gareni tana hanya” bai sauraren ta ba ya taka zuwa bayanta ya kuma rungumeta da kyau ta bayan,baiyi qasa a gwiwa ba ya fara aike mata da wasu saqonni masu nauyi da tsuma zuciya,sun isketa da kyau kuwa,ita kanta tasan waye abbas din fiye da kowa a duniya,ta wannan fannin idan ana taron bada award…..ba award ba idan akwai abinda ya fishi ya cancanci a bashi,tun tana dojewa har sai da ya zaqulo dukka wani qwarin gwiwarta yayi watsi dashi,ya gigita tunaninta da kyau ya kuma yi mata masauki saman gadonta ba tare data ankara ba,sadai tafiya nayin nisa,yana gab da kaiwa inda yake da muradi hudubar shaidaniyar zuciyarta ta dawo mata,ta tattara qarfinta gaba daya ta tureshi ta koma gefe tana cika tana batsewa.

    Da qyar ya daga kansa ya kalleta,idanunsa sun canza launi sosai,a sannan idan ka kalleshi zakayi tsammanin barkono aka watsa masa

    “Me kikeyi haka?” Baki ta turo masa

    “Sai yanzu kasan ina da amfani?,bakasan fushina ba balle damuwata ba”

    “Kinsan me kika aikata?,kinsan matsayin yin hakan har a wajen Allah?” Qeya ta juya masa tana kada qafa,tana jin itama a yanzun lokacinta ne da zata murza kambunta,batasan ma me ta tsaya jira ba da har yake mata haka take daga masa qafa,bayan tasan tana da wannan makamin a hannunta

    “Kai bakasan naka hukuncin ba saini?,meye naka hukuncin tukunna” shuru ne ya biyo baya,yayi qas da kansa yana dafe da mararsa data fara yi masa ciwo,hafsat itace musababbin samuwar ciwon mara a wajensa,a baya kafin yayi aure bashi dashi,duk da yana da qarfin sha’awa,to amma a lokacin baisan meye aure ba,bai kuma qwallafa ransa akan mata ba,hasalima basa cikin tsarinsa kwata kwata,har sai daya samu halalinsa.

    Shurun da taji bai sanyata ta juyo ba,abu daya take jira ya roqeta ya lallasheta,tana jin a sannan ne zata iya haqura ta san masa,shima saita shimfida masa dokoki ya kuma tafe mata kudin da take so wanda zata qara jari a business dinta,duk da zuciya da ruhinta suna d’ar d’ar, zuciyarta na gaya mata zaiyi wuya abbas din ya roqeta.

    Wata babbar ajiyar zuciya ya fidda,kamar zai hada da zuciyarsa,ya motsa ya miqe ya jawo jallabiyyar sa ya maida jikinsa,tayi tsit tana sauraren motsinsa,a yadda ya kamu da yawa bata dauka zai iya motsawar bama,ya tsaya qyam saman qafafunsa,cikin mamaki ta waiwayo tana dubansa.

    Kallo daya ta yiwa fuskarsa gabanta ya fadi,tayi hanzarin dauke kai tana gayyato dakiya

    “Ina da qarfi da ikon da zan iya danneki nayi dukkan yadda naga dama dake…..amma bazan aikata hakan ba,bawai don kinfi qarfina ba…… a’ah,saidai dalilai guda uku,na farko auren soyayya mukayi dake ba qiyayya ba,na biyu ban haquri da lallashi kikeso daga wajena……wallahi wallahi muddin wadan nan dabi’un naki zaki ci gaba dayi,ba zaki taba samun wannan daga gareni ba har abada…..abu na uku kuma…….bake kadai bace Allah ya halattamin ba,sannan kuma bake bace autar mata,ki jiqa abinki ki shanye,indai abbas ne na haifu,kuma dan halak ne ni gaba da baya” daga wannan ya fara takawa a hankali yana ficewa daga dakin,yana tafiya yana cije labbansa saboda yadda yakejin mararsa kamar zata tsage.

    Gaba daya maganganunsa sun gigita ta,babu zance mafi gigita kuma a ciki daya ce mata ba ita kadai Allah ya halatta masa ba……yana nufin widad?,shi yanzu sai ya kusanceta?,bazaiji kunya ba?,yarinyar da ya kusa haifarta?,zumbur ta miqe,tana jin kamar taje ta dawo dashi yayi abinda yayi nufin yin…..don da ya aikata abinda yake nufi a zancansa gwara ta bada kanta ta dawo dashi,amma kuma tana taku uku wata zuciyar ta dawo da ita

    “Zaki zubda mutuncinki da ajinki a wajensa” sai taci gaba da gamsar da kanta cewa abbas din bazai iya ba,yarinyar tayi quruciya da yawa,bazata taba iya gamsar dashi,kai ba zata daukeshi bama,ko ita da yaya suke qarewa bare widad din dako qasusuwanta basu gama yin qwari ba,ta tabbatar bashi yiwuwa

    “Namiji nefa,idan komai bai kawoshi ba buqatarsa zata dawo dashi,basu da haquri ta wannan fannin” ta sake tabbatar wa da kanta,sai taja tsaki ta koma tayi zamanta,har fana tuhumar kanta

    “Kin faye rawar kai akan abbas din nan,shi yasa ya rainaki,ya kasa ganin kimarki” wata zuciyar ta sake gaya mata,da wannan taja mugun tsaki ta miqe ta dauko wayarta dake ringing tana duba me kiran,baquwarta ce da zata kawo mata biyan bashi,saita aje wayar ta shiga bandaki tayi tsarki da alwala ta fito,saidai har a sannan itama tana ji a jikinta,don ba qarya tayi missing abbas din,sannan tarkon daya dana mata banda akwai wani quduri a ranta…..ta kuma yi da gaske ta dace da zuciya mai tauri bata isa ta tsallake ba,a ranta taji tana fatan tattaurar zuciyarsa ta sauko da wuri ya karyo ya nemeta,don itama a buqace take.

    Tunda ya zube a dakinsa bai iya tashi ba,a nan yayi sallar magariba ya kuma yi isha’i ya koma ya kwanta saman abun sallar,rub da ciki yayi tun tsahon awannin yana fatan ya samu sassauci na zuciya da kuma gangar jiki,gaba daya ya manta zaije dauko widad,sai da yaga kiran hajiyarsa.

    Bayaso yace mata baya da lafiya,yanzu zata daga hankalinta,kuma yasan babu driving din da zai iya,sai yace mata yana zuwa.

    Number k’aninsa umar wanda daga shi sai auta ya kira yace yazo ya karba key din motarsa ya kawo widad din,idan hajiya ta tambaya ya gaya mata baqi yayi,a ladabce ya amsa masa,ya katse kiran,ya aje wayar yana cusa hannunsa cikin fuskarsa.

    Ita kuwa hakimar tana falonta a zaune,duk sanda taji wani motsi saita leqa taga waye,so take taga shigowar widad din ta tsareta da ayyuka,idan da hali ma yau kwanan dakin su mimi zata sakata yi,taso acema key din part dinta yana wajenta tace mata ya bata,batasan me yasa bata saka mata dokar ajeshi a wajenta ba,amma daga wannan zuwan abinda zatayi kenan,ta dinga barinsa a hannunta,idan suka dawo ta dinga karba.
    [3/15, 9:35 PM] +234 704 440 6400: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)
    *Arewabooks:Huguma*

  • Arubuce Ta Ke 74

    Arubuce Ta Ke 74

    Page 74

    Tana zaune saman kujerar dake fuskarta qofa yana kada qafartaranta cunkushe da tunani kala daban daban,warmer dinta da abbas ya bayar yafi komai bata mata rai a yanzun,don bata dauki widad din a wata matsala da zata kasa saitata ba,wannan kuma sai yazo ya hadu da rashin shigowar widad din ya qara tunzurata.

    Widad din nayin sallama ta watsa mata wani irin kallo mai hade da harara

    “Sai yanzu kikaga damar zuwa?” Ido widad din ta dauke yana qarasowa cikin falon

    “Gefen uncle na fara gyarawa tukunna” miqewa zumbur tayi,har batasan ashar ta subuce mata ba

    “Kina nufin dakinsa kika shiga kika gyara?,waye ya baki wannan izinin?” Kallonta take danyi da mamaki,sai kuma ta janye idanunta,saboda bata saba kallon babba haka kai tsaye idan yana mata fada ba

    “Shi yace nazo na gyara” maganar ta sake tunzurata,ba bata lokaci ta nufi qofa ranta na suya,wannan wanne irin zubda mata da mutunci yayi shirin yi?,me ya hanashi kiranta ita tazo ta gyara masan,kawai sai ya kama ya kira yarinya taga makwancinsu?.

    Har takai qofa kuma ta dakata,saboda tunawa da tayi ita din me laifi ce,sai tayi qwafa ta dawo ta zauna,koma meye akan widad din yau zata saukeshi

    “Me kika tsaya kina kalla da baki wuce kin kama aikinki ba?,ki fara da kitchen idan kin gama ki wanke bandakina,akwai kayan nawwara data bata a toilet dina,saura kiyimin ha’inci” idonta ta bude a hankali daga rufesun datayi tun sanda tayi mata tsawar farko,bata ce mata komai ba ta doshi kitchen,tana jin wani abu me kama da bacin ran da bata taba ji ba yana son fara tana zuciyarta,me tayi mata da zata dinga binta da irin wannan tsawar?.

    Tana ta cika tana batsewa ita daya a falon tayi baquwa,baquwar kaman customer a wajenta,tana siyan pieces na laces da hafsat din ke kawowa daga Lagos tana siyarwa,dadewarsu tare ya haifar da qawance a tsakaninsu,ta jima batazo gidan hafsat din ba,saboda dama ba kowa bane yakejin dadin ziyartar gidanta ba,saidai idan cikinka a cike yake da abinci,hakanan baka da qishirwa.

    Already ta gaya mata idan ta shigo bauchin zata qaraso taga wasu lace,tasan kudi zata samu a jikinta,wannan yasa ta karbeta da fara’arta,ta kuma ajjiye duk wani bacin rai dake damunta.

    Suna tsaka da gaisawa talatu ta dawo dasu mimi ta koma

    “Ma sha Allah,mimi ta fara girma” baquwar me suna hajiya habiba ta fada

    “Wallahi,aikin kwana biyu baki shigo ba,saidai aike”

    “Bari kawai,abubuwa ne suka cushemin” daidai lokacin da mimi ta matso kusa da hafsat din tana gaya mata zatayi toilet

    “Sarakan saka mutane aiki,baiwar taku ai ta dawo” sai ta sanya baki ta qwala kiran sunan widad din har sau uku.

    A lokacin tayi nisa cikin tunanin dabi’un hafsat din,me yake damunta da take tara wanke wanke haka ba zata iya kintsawa ba?,ko ina na gidanta bashi da dadin shaqar qamshi har sai sanda tazo?,muguntar zatayi mata ne?,ko haka dabi’arta take?,itadai tunda ta taso a rayuwarta bata tana ganin kalar qazanta irin wannan ba.

    Yadda take kiran sunan nata ya fargar da ita,ta ajjiye plate din hannunta da sauri,garin saurin wuqar dake ajiye a wajen tadan yanketa a dan yatsa,ta runtse ido tana jin zafin yankan yana ratsata,ta yarfe hannun tana bude idon nata sanda muryar hafsat ta sake iskarta cikin wani amo na gigitar kira.

    Dukkansu su biyun suka zuba mata idanu,hafsat din ta jifanta da wata muguwar harara,yayin da hajiya habiba ke mamakin ganin widad a gidan,tunda bata santa ba

    “Me kikeyi kina jina ina kiranki?” Ta fada cikin nuna isa taqama da gadara,tanaso ta yarfata sosai gaban hajiya habiba

    “Banji ba sai daga baya”

    “Kin fara canza hali ko?,indai kuwa hakane zakisha mamakina,zaki kuma sha wahala ne kawai,ki dauki mimi ki dorata a poo tayi toilet,kafin sannan ki kawowa baquwa ruwa” batace mata komai ba sai kama hannun mimin da tayi,tuni dama yarinyar ta iso wajenta tana mata sannu da zuwa,ita kanta yarinyar cikin walwala take,saboda me basu kulawar da mahaifiyar data haifesu ma bata iya basu ta dawo,surutan mimi ya rage bacin ran da a yau taji tana jinsa har cikin zuciyarta.

    Sai data dorata a poo din sannan ta shirya ruwan da lemo a tray ta dora cup a kai ta fito Parlor din.

    Sai da widad ta bace hajiya habiba ta dauke kallonta daga kanta sukaci gaba da cinikinsu,amma kuma maganar dake ranta tana ta cinta,har ta kasa Shuru

    “Wai nace ba…..me aiki kikayi ne?” Ta jefawa hafsa tambayar,dai dai sanda widad ke fitowa dauke da tray din.

    Duban widad din hafsat tayi,bata kuma tashi bada amsar ba sai data iso tsakiyarsu tana ajjiye tray din

    “Tayi kama dame aiki ko?” Ta fada a wulaqance tana tabe baki,amsar hajiya habiba shine ko daya babu kama da ‘yar aiki a tare da ita,amma data fuskanci akwai magana a bakin hafsat din sai bata amsa mata ba,har zuwa sanda tace

    “Wai nan haka kishiyace aka yimin”

    “Kishiya?!” Ta amsa da amo mai qarfi tana sake bin widad data juya zuwa kitchen da kallo

    “Wallahi hajiya”

    “Kan ubancan….ah banga laifinki ba,amma ke kuma kina meye har aka miki kishiya?” Wannan shine iya abinda widad din ta iya ji.

    Ko data koma dakin hafsat din,tsaye tayi a gaban mudubi kalmar ‘yar aiki tana dukan ranta,meye tayi da tayi kama da ‘yar aiki?,tasan meye ‘yar aiki,amma har yanzu bata fuskanci ainihin ma’anar kishiya ba,a cikinsu wanne yafi zafi?,ta samu kanta da tambayar kanta da kanta,kunnuwanta na iya jiye mata yadda hajiya habiba ta maimaita kalmar kishiya da wani irin nauyi da girma,me yasa kalmar kawai tayi girma haka?.

    Kallon hafsat hajiya habiba taci gaba dayi tana sauraren bayanin da take mata,da irin qoqarin da tayi take bautar da widad din

    “Kinyi qoqari qwarai,amma kuma ina jiye miki ranar da maigidan zai fuskanci bautar da ita kikeyi,ina mai tabbatar miki yana son kayarsa,saidai wala’alla yana ganin tayi qanqanta ne kawai shi yasa.mautara bata fito fili a kanta ba,ke…..baya ga haka ma mijinki me kamewa ne,idan wani ne ko jaririya ce yadda take da wannan mugun kyau wallahi tuni aikin gama ya gama,waima kina kallon fuskar yarinyar nan da kyau kuwa?”tayi tambayar tana kama haba,idanunta akan fuskar hafsat data bawa hajiya habiba dukka hankalinta

    “Girma ya fara zuwa mata fa,duk da dai ban santa a sanda aka kawota ba,kuma ke kin sani,ko makaho idan ya shafa ki ya shafata yasan ta fiku kyua nesa ba kusa ba,ta fiki diri,ke koni bazan yarda mijina ya dinga kallon wannan surar ba wallahi tallahi…..”

    “Yanzu me kikeso kice?” Hafsat ta katseta daga yadda take kuranta kyan widad,saboda a yanzun a duniya babu abinda ta tsana irin taji an fada ko an yabi kyanta,ko tunawa ta fita kyau bataso tayi tsakanin ita da zuciyarta bare har a furta mata

    “Yauwa,idan kana da kyau ka qara da wanka,kudi zaki saka ki shiga malamai su sake kauda idonsa da zuciyarsa daga kanta,sannan a sake kama miki ita sai abinda kika ce” shuru hafsat tayi tana nazari,nan fa daya,an kuma zo wajen,ita indai zancan ta fidda kudi ne to babu ita a wajen,sannan ma kuma me take da buqata wai,komai da anty ummee ke tsara mata yana tafiya yadda ya kamata,ko canzawar da widad din ta fara yi hakan baya rasa nasaba da raga matan da takeyi kwana biyu qila shi yasa ta fara sakewa,kuma ko yadda anty umnee ke gudanar da gidanta ya isheta ishara,babu boka ba malam,amma ko meye ta fada ya zauna,kowa juyashi take a cikin gidan ta ruwan sanyi.

    “Gaskiya banajin a yanzu ina da buqatar wani malamin tsubbu hajiya,saidai ban sani ba ko nan gaba bana ma fata” jinjina kai kawai hahiya habiba tayi,tana ganin ta gaya mata iya abinda zata gaya mata,sauran dabara ta rage game shiga rijiya

    “Yanzun nawa ne balance dina a hannunki?” Hafsat din ta dawo dasu kan maganar kudi,abinda tafi qauna kenan.

    Gaba daya ta dinga jin sassan kamar a kanta yake,sai taji batason qara koda minti biyar a cikinsa,akwai tambayoyin da take da buqatar amsoshinsu,saboda haka sauri sauri ta gama mata duk abinda zatayin ta fito,sai mimi ta maqale zata bita,dama neman kai hafsat din take dasu tace su bita,amma sai nawwara taqi bin nata

    “Sai kiyita zama ai”ta fadi tana jifan yarinyar da harara,so take tadan samu ta dafa ma abbas wani abun,kafin yazo yahau kanta da qorafi.

    Ruwa me zafi ta hada tayi wanka,ta yiwa mimi ma,take walwalar yarinyar ta qaru,don har gashin kanta ta wanke mata.

    Cikin abaya ta shirya kamar yadda take zabinta,zataso shiga kitchen ta dafama yarinyar wani abu,to amma a gajiye take jinta,sai ta fidda snacks din da tayi ta zubo a jaka,ta zuba mata ta hada mata da lemo,sai gashi tana ci hannu baka hannu qwarya,don yafi mata indomie din da ta zame musu ‘yar kullum safe rana dare,sai randa Allah ya cishesu suka fita unguwa ko taso ta dafa wani abun.

    Snacks kuwa irin haka ba samunsa sukeyi ba,muddin ba daddyn nasu bane yazo bauchin ya fita dasu wasu gureren ba.

    Tana saman kujera a zaune tana sauraren hirar da mimi ke mata,gaba daya kuzarin jikinta babushi,sunayen da hajiya habiba ta kirata dasu su suketa mata yawo akai

    “Kishiya/’yar aiki”,so take yamma ta qarayi ta kira anty deena ko anty madeena ko hajjaa tayi musu tambaya.

    Tare da sallama ya tura qofar falon nata ya shigo,ya canza shiga zuwa wasu qananun kaya da sukayi masifar karbarsa,suka kuma fidda zatinsa sosai.

    Idanunsa a kanta sanda mimi ta kamo hannunsa tana cewa

    “Daddy zo muci,anty ce ta bani,yayi dadi sosai daddy,kace mommy ta dinga yi mana irinsa” biyewa yarinyar yayi,yaje ya tsugunna gaban plate din ya dauka ya gutsura yana yaba dadinsa,wasa wasa sai gashi yana ta ci,ya daga kai ya kalli widad dake zaune gefe tana kallonsu

    “Ya akayi?,yau babu sakalcinne?” Ya tambayeta da sigar tsokana, murmushi ya kubce mata,itadai batasan me yasa yake mata kallon quruciya sosai da sosai ba,itakam tana gani zuwa yanzun ma ai ta isa mace

    “Ga wayarki da kika manta” ya.miqa mata wayar yana kallonta,hannu biyu tasa ta karba,tama manta da ita

    “Adan qara mana snacks din mana baby doll” sunan da ya fara kiranta dashi kenan,tun last week da akayi wani taro na matan police,rose ta kawo me kwalliya har gida tayi mata,ya dinga tsokanarta wai ta zama kamar ‘yar tsana,da wayo da wayo ma ya hanata zuwa taron,yace tayi kyau da yawa,bazai barta taje ba,data saka masa kukan shagwabarta sai yace

    “Wa yace kiyi kyau haka?,bazan iya barinki ba kije,but i promised you zan fita dake anjima kiga gari” da wannan ya fanshi kansa.

    Koda ta zuba musu snack din ta dawo zama tayi shuru,baice mata komai ba amma yaci gaba da karantar ta cikin qwarewa ta gefan idanu,ya fahimci kamar damuwa ce da ita,sannan tana yawan taba yatsarta

    “Me ya samu hannun?” Ya tambayeta a tausashe bayan ya miqe yana kallonta,kai ta girgiza da sauri

    “Ba komai” ta amsa masa tana dunqule hannun nata,baice komai,ya taka a hankali ya isa gabanta,ya kama yatsan yana dubawa,yanka ne,ga wajen yayi ja abinka da farar fata,sai ya daga kai ya kalleta

    “A ina kikaji wannan?” Shuru ta danyi sannan a hankali tace

    “Kitchen”

    “Me ya kaiki kitchen daga dawowarki?” Rasa amsar da zata bashi tayi,saita zabi tayi shuru

    “But na shigo sau biyu ban sameki ba kina wajen maman mimi”

    “Eh na dan shiga ne” shuru yayi yana tattara maganganunta guri guda,ya fahimci tana yawan zama a wajen hafsat din,to amma a idanunsa na zahiri baiga wani hali ko wani abu da take mata da zai sanya ya hana ko ya tuhumi zuwanta ba,sannan yafi ta’allaqa zuwan nata can akan su mimi,yasan halinta sarai nason yara,saidai sauyawar yanayin nata a yau yasa yaji bai gamsu da yadda ya ganta ba

    “Zanje na dawo indai da qarfe kika yanke sai an miki anti tetanus” narai narai tayi da.idanunta jin batun allura,yayi murmushin gefan baki,idan ya biyewa wannan sakalcin nata tabbas yasan ba za’a yi ba.

    Har yakai qofa ya waiwayo yana kallonta,idanunsa qasa qasa,kasa jurewa kallonsa tayi tadan kauda kallonta gefe

    “Ko zaki rakani,gidan suraj zanje na dubashi” kai.ta girgiza alamun a’ah,yau din tana jin gajiya sosai a jikinta,bugu da qari ma kuma tana son yin waya.

    Kai ya mirgina hagu da dama sannan yace

    “Alright,take care” yayi maganar yana aza mata nauyin kallon nan nasa,saita jinjina masa kai,ya juya ya fita.
    [3/17, 1:28 PM] +234 813 343 4840: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)
    *Arewabooks:Huguma*

  • Arubuce Ta Ke 78

    Arubuce Ta Ke 78

    Page 78

    Bakinta ya mutu murus,sai rawa da jikinta kawai yakeyi,abun ya bashi tausayi sosai,baiyi experiencing haka daga wajen hafsat ba a wancan lokacin,shi yasa a yanzu yake ganin komai daban,amma daya tuna banbancin shekarun sai ya fahimci dole a samu irin hakan,widad din yarinya ce sosai,dole tafi hafsat shan jiki.

    Sau uku yana sauya musu ruwa mai dumi sosai,kusan duka dashi akeyin gashin,har sai daya kintaci lokaci sannan ya canza ruwa me kyau

    “Zaki iya wankan da kanki?” Duk.yadda takejin nauyin ganinta da yayi a haka bata jin zata iya wankan da kanta indai toilet din takeso bari,don ko ina na jikinta rawa yakeyi,saita girgiza masa kai.

    Da kansa ya wanketa tas kamar su mimi,ya nadota a towel ya fito da ita,wajen shiryawa ne ta riqe towel din tace zata iya da kanta,ya saki boyayyen murmushi,don dariya ta bashi,abunda take fa boyon a yau ya gansu ya ta kuma taba halalinsa son ransa,saidai inda ta bashi damar da haka zaiso,don bai gaji ba,yana jin kamar ma ba’a yi komai ba.

    Bai matsa da yawa ba ya dauko mata komai ya aje mata kusa da ita ta yadda basai tayi tafiya me yawa ba sannan ya fice.

    Kitchen ya wuce da kansa ya fara hada musu breakfast,duk bayan sakanni sai wani murmushi ya subuce masa,ya koma kamar wani zautacce shi kadai,wani irin wasai yake jinsa tamkar angon da yayi kwanan farko a gidansa,ji yakeyi kamar an canzashi,kamar ba shine abbas ba.

    Lafiyayyen breakfast ya hada,ya shirya komai saman tray abun sha’awa kamar ba girkin namiji ba,ya jima da koyawa kansa girki,tun bai iya ba har dolen dole ta saka ya koya din,banda ya iya din ya tabbatar da tuni yunwa tayi masa illa indai don ta hafsat ce.

    A cure waje daya ya sameta tana ta rawar sanyi,ya ajjiye tray din ya isa inda take ya fara qoqarin dagota cikin damuwa,sai ya samu kuka takeyi

    “Ya rabb…..” Ya fada cikin tsananin damuwa,gaba daya jikin nata ya rikice da zafi,ga complain na ciwon da takeji

    “Kiyi haquri kici.wani abu,sai muje kiga likita” ya fada a tausashe cikin sigar lallashi,gaba daya yayi wani mugun laushi.

    Kafada ta maqale cikin salon rigima hawaye ya ziraro mata,sai da ya murde ya koma ainihin abbas dinsa sannan ta yarda ta tsaya,ya hada tea ya zuba komai a plate ya saisaita zafinsa,sannan ya matso kusa da ita hannunsa dauke da mug din

    “Ehennnn…..oya,take it” da kadan da kadan take kurba bakinta yana rawa,bata wani sha mai yawa ba ta fara kelaya amai,sai data dawo da komai na cikinta.

    Tsaf ya gyara wajen da kansa,sannan ya dauki waya yayi kiran samuel yace ya bincika asibiti mafi kusa dasu yayi musu booking,idan so samu ne asibitin Dr jessica

    “Yes sir….zanzo na daukeka ne?” Sasssan da widad ke kwance ya kalla,sai ya girgiza masa kai hadi da cewa

    “Nob,idan ka gama abinda nace maka shikenan,you can go”

    “Yes sir” ya sake fada cikin girmamawa,wayar ya ajjiye ya soma takawa zuwa inda take kwance,ba samuel ba,koma waye bazai iya bari yayi driving widad din ba,yana jin kamar tsokar zuciyarsa ce ke rayuwa a wajen jikinsa.

    Gaban gadon ya koma,a tausashe ya duqa gabanta,ya saka hannu ya nutse ya janye gashin kanta daya rufe rabin fuskarta baya,idanunsa a kan fuskartata daya wani taushi ta kuma canza lokaci guda.

    A hankali ta bude idonta suka sauka cikin nashi,sai tayi saurin maidasu ta rufe,wani mugun kyau yaga ta qara masa a hakan

    “Zaki iya tashi muje asibiti?” Fuska ta narke,ita kam gaba daya bata qaunar abinda zai sanya ta motsa,amma hakanan yayi mata dabara cikin lallabawa ya sanyata tashi ta saka hijab dinta suka fito.

    Yana driving amma duk bayan wasu sakanni sai ya juya ya kalleta,ta tattare gu daya cikin seat din motar,sai ya miqa hannu ya kashe ac din motar,yadan qara speed don su isa da wuri.

    Already samuel ya gama komai,dr jessica ce da kanta,cikin girmamawa ta nuna musu seat,ya zaunar da widad wadda taketa bi da kallo,cikin zuciyarta tana ta yaba kyanta,shi kuma ya tsaya daga bayanta kamar wani bodyguard.

    Akwai sanayya tsakaninsu,don haka ta fara gaidashi cikin girmamawa,ya amsa mata tare da tambayarta aiki

    “me yake damunki madam?” Dr jessica ta tambayi widad tana murmushi,idanu a narke ta maida dubanta ga abbas,saboda batasan kalar amsar da zata bata ba,sai ya share kamar bai gane tana kallonsa ba

    “Uhmm,inajinki madam,fell free,kiyi bayani” ta fada tana jan takardar dake gabanta.

    Bai ankara ba sai sheshsheqar kukanta da yaji,ya daga kai da sauri daga danna wayar da yakeyi yana dubanta,sai yaja kujerar kusa da ita ya zauna har gwiwoyinsu na gogayya dana juna

    “Listen widad?,me kuma ya faru?” Muryarta a shaqe a kuma shagwabe qwarai tace

    “Kaine” sosai sound dinta ya taba zuciyarsa,ya saki murmushi

    “Okay,to ya isa,dr……she had her first night,she feels that the place is hurting her” kai dr jessica ta gyada sannan tace

    “Muje na duba” bata gane me take nufi ba sai data hau gadon da take duba marasa lafiya bayan abbas ya taimaka mata,nan ta fara raba idanu,ta kuma narke masa tana hawaye sosai,don kunya takeji ta buda gurin kuma a sake gani?.

    Da qyar yasha kanta yana riqe da tafin hannunsa cikin nata ha dr jessica ta gama dubawa ta koma kan kujerarta

    “It’s bruises,you hurt her a lot sir,but ba damuwa,she will recover in a few days” ta fada tana jan takarda

    “Saika qara haquri sir, she’s too young,dole ta samu ciwuka haka musamman idan ya zamana anyi gaggawa,but with time zata saba” tura baki widad tayi gaba,itama dr din nan bata da kunya,zata saba dame?,yayin da abbas yadan saci kallonta ya saki boyayyen murmushi

    “Allah yasa” ya fadi qasa qasa,cikin ransa yake hasashen lokacin da widad din zata sallama masa ruhi zuciya da kuma rayuwarta,lallai da ya shiga jerin maza mafi sa’a a duniya.

    Magunguna ta rubuta mata masu kyau,sannan ta basu wasu shawarwari har hakan yasa widad din tadan sake,saidai kunya kamar qasa zata tsage ta shige,tana ganin kawai abbas din ya gama kunyatata.

    Ko a hanya da wani irin nutsuwa da takatsantsan yake driving din,dukka hankalinsa da kulawarsa yana kanta,haka da suka koma gida,ya sanyata gaba da tambayar abinda takeson ci,saidai taqi sawa bakinta komai don bata da appetite,gaba daya taste din bakinta ya gama daukewa,tana ta faman koke koke,ta narke masa qwarai,dama hausawa sukace mai neman kuka ne aka jefeshi da kashin awaki,tsohuwar rigima da kuma shagwaba gaba daya ranar bawan Allah abbas aka juyewa,shi kuwa ya sanya hannu bibbiyu ya karba,saboda a yanzun jinta yake dai dai da ruhinsa.

    Girki kusan kala uku yayi mata amma tace bata ci,daga qarshe sai daya hade girar sama da qasa ya zaunar da ita ya dinga bata da kansa sannan ya samu taci,ya bata maganungunan tasha bayan ya tilasta mata ta shiga ruwa.

    Saman cinyarsa ya dora kanta,taso ta zame amma ya hanata,yanason kawo kusanci sosai a tsakaninsa da ita,ya kuma fidda dukka wani tsoro nasa daga zuciyarta daya dasu a daren jiya,sai tayi likimo ta lumshe ido tana sauke ajiyar zuciya,ita kanta tana matuqar son kwanciya a jikinsa,bata taba jin wani guri da take jin wani nutsuwa da kwanciyar hankali idan tana gurin ba irin cinyar tasa,amma for now tsoronsa takeji, tsoronsa takeji sosai,gani take kamar idan tayi bacci zai sake maimaita mata abinda ya aikata mata jiya.

    Sannu a hankali bacci mai dadi yayi awon gaba da ita,ya sauke ajiyar zuciya yana gyara mata kwanciya sosai yana kallon fuskarta, murmushi ya sake subuce masa,yakai.hannu zai shafi lips dinta sai kuma ya janye hannu da sauri gudun kada ya tasheta.

    Wuni guda ranar suna tare cikin gidan,kwata kwata ma ya manta da wani batun aiki,sai da aka nemeshi a gurin aikin sannan ya bada excuse din yana da patient.

    A daren duk yadda taso bijirewa kwana dakin haka ya mata dole ta kwana a dakin kuma cikin jikinsa,dukkansu shi da itan wani irin ni’imtaccen bacci ne yayi awon gaba dasu.

    Ko cikin duniyar baccinsa ya tabbatar da cewa wani gagarumin ci gaba da sauyi ne ya tunkaro rayuwarsa,sauka da shigar numfashinsa cikin wata irin nutsuwa.

    Washegari bayan sun idar da sallar asuba,dukkansu shi da ita suna saman abun sallah,kowanne jinsa yake kamar a wata sabuwar duniyar,musamman abbas da yakejin jiki da qirjinsa wasai,babu komai a ciki sai wata irin mahaukaciyar soyayyar widad din.

    “Ina kwana?” Ta fada qasa qasa kanta a qasa tana murza tafin hannunta.

    Gaba dayansa ya waiwayo,sai ya saki murmushi,ya cira hannunsa a nutse ya miqa mata yana cewa

    “Zo nan mu gaisa da kyau” manyan idanunta da suka dan fada kadan ta daga ta kalleshi,sai ta noqe kafada,don gaba daya tsoronsa takeji

    “Please mana baby doll” ya fada da wata irin kwantacciyar murya,qas ta sakeyi da kanta tana tuna kalaman mommynta,sai ta miqe a hankali ta fara takowa zuwa gabansa.

    Da idanu ya bita,yana jinta tana tsarga masa har cikin jinin jikinsa,yabi takunta da kallo,akan tsari take ajiye qafafun nata kamar wadda ake qirga ma adadin takunta.

    A gabansa ta tsugunna tana watsa masa qamshin jikinta,lumshe idonsa yayi zuciyarsa na bugawa,duk yadda taso daurewa ya kauda kai ya gaza,sai yasa hannunsa ya fusgota a tausashe yayi masauki a jikinsa.

    A tausashe ya maida hannuwansa ya rungumeta

    “Kin tashi lpy my baby?,ya jikin?” Ya rada mata a hankali cikin kunnuwanta,har sai da duk wata tsiga ta jikinta ta tashi,ta lumshe idonta gabanta yana bugawa da sauri da sauri

    “Da sauqi”

    “Ma sha Allah……haka nakeson ji,Allah yayi miki albarka” har cikin zuciyarta taji sanyin addu’ar,ya motsa bakinsa zaiyi magana,kafin yace komai wayarsa dake gefe ta dauki ringing.

    A nutse ya sauke idanunsa yana duba mai kiran,hafsat ce,sai ya tsaya yana kallon wayar kamar mai son karanto dalilin kiran nata ta cikin wayar.
    [3/18, 3:05 PM] +234 903 685 1413: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)
    *Arewabooks:Huguma*

  • Arubuce Ta Ke 85

    Arubuce Ta Ke 85

    Page 85

    Yau din tunda suka tashi daga kaduna basu tsaya ba,don bata jima ba bacci ya dauketa,don dama yawanci saboda ita yakan tsaya din,ya samar mata wani abun da zataci,to har suka je inda yakan tsaya din suyi sallah da sauransu tana baccinta,don haka ya wuce abinsa kai tsaye,lokaci lokaci yana waiwayawa ya kalleta,yana monitoring baccin nata.

    Bata farka ba sai da suka shiga unguwarsu,tadan kalleshi,suka hada ido,yasan me takeson cewa,gidan hajiya takeson zuwa,to amma bayajin zai iya barinta,tunda duka duka kwana hudu zasuyi su juya,suya saki murmushi kawai ya shafi gefan fuskarta

    “Ba kwana gidan hajiya wannan karon,i need you by my side” shuru tayi kawai,ta langabar da kanta gefe guda ba tare data ce komai ba,duk da ba haka taso ba cikin ranta.

    Yana gama parking kusa da motar hafsat din data dauki qura mimi na shigowa ita dame daukota daga makaranta,ganin motar babanta ya sanyata tahowa da gudunta tana kiran sunansa,ya dagata ya rungumeta yayi kissing dinta,saita zame daga jikinsa ta koma wajen widad.

    Ta yima widad din nauyi,amma saita riqe hannunta tana tsokanarta hadi dayi mata waqar ‘yar makaranta,tana ta dariya,dadi ya cika yarinyar,ko banza tana samun nishadi kulawa da kuma canjin rayuwa a duk sanda baban nata da antyn nata sukazo.

    Kamar sama sama take jiyo muryar mimi din tana kiran sunan baban nata,sai taja tsaki ta share,a ranta tana jin haushin yadda yarinyar keda qulafucin ubanta,tana tsoron gaba kadan ma zaiyi wahala idan batafi sonta akan uban ba,saita ci gaba da lissafin kudinta,amma kuma jin shiru bata ji motsin mimin ba,saita ajjiye wayarta da take lissafin a ciki ta miqe tana gyara daurin zaninta,ta sako kai zuwa harabar gidan.

    Dai dai sanda sale ke cire kayansu a booth din motar,abbas din yana gaya masa kada yayi nisa zai kaishi kasuwa.

    Cikin wani mugun mutuwar jiki ta sauke hannuwanta data tokare bakin qofa dasu

    “Kanbun bal bala’in bala’i!” Bakinta ya furta duk da batasan yaushe hakan ta faru ba,daga inda take tsaye tana iya hangen widad wadda ke riqe da hannun mimi,fuskarta kwance da murmushin daya qarawa fuskar tata kyau da kuma kwarjini

    “Wanne irin girma ne haka cikin wata guda kacal?” Ta tambayi kanta da kanta,har yanzu idanunta na saman fuskar widad din,ko sau daya ma bata waiwayi inda abbas din yake ba.

    Takawa ta soma yi zuwa inda suke tsaye a hankali tanason sake gasgata abinda idanunta ke nuna mata,saidai duk taku daya idan tayi bugun zuciyarta sai ya qaru,kyau da yadda girma ya fara nunawa a jikin widad din suka soma bata mamaki.

    Qaramar jakarta abbas ya dora mata saman mota bayan ya kulle motar

    “Keda mimin banga marabarku ba” yayi maganar yana kafeta da idanu hannayensa duka biyun cikin aljihun rigarsa.

    Dariya ya bata,tadan juya ido cikin irin nuna mamakin nan,saidai hakan batasan mugun kyan da ya qara mata ba

    “Uncle kace na girma fa?” Har tsakiyar zuciyarsa ta aike da saqo,bayason yayi saurin bada kai tun yanzun,tunda dai nan ba kaduna bace

    “Yes…..amma ga jakarki nan,ki dauka sai mu gani” ya fada tsadajjen murmushin nan nasa yana fita daga fuskarsa.

    “Uncle itama wannan din da nauyi don Allah…..” Widad ta fada cikin shagwabar data saba yi masa

    “Ya salam” ya fada yana miqa hannu hadi da dauke jakar,yayin da hafsat taji tana shirin faduwa,sai takai hannu tana neman abinda zata riqe gudun faduwa,hannunta ya sauka kan kyakkyawar luggage din widad guda daya da tayi saura sale bai dauke ba.

    Hannunta ta janye,mamaki yana sake kasheta,gata kusa da wajen amma cikinsu ba wanda yama lura da wanzuwarta a wajen,wani tunani yazo mata,tayi qoqarin saita kanta ta hanyar yin gyaran murya kadan,abinda yasa duk suka waiwayo

    “Sannu da zuwa,saukar yaushe?” Tayi maganar tana tsare gida hadi dayin kicin kicin da fuska,sannan ta miqa hannu tana son karbar jakar widad dake hannunsa a zuwan tasa ce

    “Yanzu ne,ko kayanma ba’a gama daukewa ba”

    “Fitar wuri kukayi kenan” ta sake fada tanason calling attention dinsa,sai ya dan gyada kai,abun nata nayau yana dan bashi mamaki

    “Ina wuni” widad ta fada ba tare data dubi sashenta ba,haka kawai takejin wani abu mara dadi yana dan taba zuciyarta,taji kuma.ba zata iya gaidata yadda ta saba ba,sai hafsat din ta waiwaya tana kallonta,sai a lokacin ta sake ganinta sosai

    “Oh….. amarya lafiya lau” can qasan ranta tana dan mamakin yanayin data gaisheta dashi,ba haka ta saba gaisheta ba dashi,ta saba ta gaisheta tana fara’a bayan ta rusuna mata,sa’an nan idan tayi kamar bata ji ba sai ta sake maimaitawa

    “Ba jakata bace ta qanwarki ce” ya fada yana kulle motar sanda yaga tana nufar sashensa da jakar

    “Oh, okay” ta fada tana dawowa baya inda widad ke tsaye da mimi,kai tsaye ta miqa mata jakar,don dama abinda takeso kenan ta karba kayarta.

    Ba tare da nufin komai ba ta kalli abbas din a shagwabe

    “Allah uncle da nauyi,kuma kace zaka kaimin fa”

    “Bance na fasa ba ai” ya fada yana miqawa hafsat hannunsa,kamar sakarya ta sakar masa jakar,xallar mamaki yana cikata,ta bishi d kallo sanda yake cewa

    “Muje na ajjiye miki”
    Su ukun suka juya zuwa sassanta,mijinta….. diyarta ta bisu da kallo,me yake shirin faruwa ne wai?,ko kuma tace meye ne ya farun?.

    Kamar wadda aka tsikara saita kasa tsaiwa,ta daga qafarta da hanzari tabi bayansu,ta cimmasu ya karba keys din ya saka yana bude mata qofar sassan nata,sai ya waiwayo yana duban hafsat din da tayi tsaye a bayansu,ta kasa ta tsare tana dubansu,ya dauke kai ya qarasa buda qofar ya matsa mata gefe ta sanya kai ta shige ita da mimi da suketa surutunsu ko a jikinsu.

    Cikin falon ya ajjiye mata jakar,sannan ya juya ya fice daga falon yana tsokanar mimi,a sannan hafsat din tana qifar parlor din bata shigo ba,saidai tana jin zuciyarta na mata wani iri,ta kasa tuna komai bare tayi tunanin me ya kamata tayi,jikinta yayi mugun sanyi,zuciyarta kuma tana bata akwai wani abu.

    Kallonta ya sakeyi sanda ya fito,tana tsaye qyam kamar wadda aka bawa gadin qofar falon,yadan kalleta sai kuma ya wuce,ta taka ta bishi a baya,zuciyarta kamar sata fito daga qirjinta,tanason masa qorafi to amma kuma tace masa meye?,haka taci gaba da binsa a baya har zuwa sashen nasa.

    Sanda ya bude waiwayowa yayi yana kallonta,qura fal sashen,wannan abu yana masa ciwo,baisan sai yaushe zai fara dawowa yana samun sassan nasa a tsaftace ba,suna hada ido ta kauda kai,tasan qorafi yakeson yi,amma ba zata bashi dama ba,zata gyara tunda ga widad tazo,wasu ayyukan zasu ragan mata ai,sai ta karba jakarsa ta wuce bedroom dinsa da ita.

    *_BAYAN AWA BIYU_*

    Yana zaune saman kujera take gyaran falon,tana aikin tana gyara daurin zaninta dake kwancewa,fuskarta sam babu walwala,tunani ne cunkushe fal a ranta.

    Nawwara na zaune saman doguwar kujerar da yake kai,yanata bare mata chocolate tana sha tana masa surutu,lokaci bayan lokaci yakan daga kai ya dubeta,tun daga tsefaffen gashinta da yayi cibiri cibiri har zuwa qafafunta dake cike da kaushi,babu digo lalle ko kadan bare su samu arziqin suturta kaushin qafartata,brassiere dinta ta saki sosai,don kana iya hangota ta gadon bayanta.

    Ya lumshe idon takaici yana cikashi,duk wani abu da diya mace zaga gyara a jikinta ya bada sha’awa hafsat din ta kauda shi da kanta da mugun qazanta da rashin sanin ciwon kanta,tattausan qshin widad ya tuna,babu sanda zata giftashi bakaji tashinsa ba daga jikinta,sabanin hafsat din da saidai yaji wani na daban bawai qamshi ba.

    Ta gama gyaran tana jin tayi wani gagarumin aikin azo a gani,gaba daya qugunta har ya riqe,saita taka zuwa qofar fita,tanason kiran widad din tazo ta gyara mata kitchen hade da kayan miya zata dora girki,sannan ta kama sauran gyaran falonta zuwa sassan part din nata

    “Zo mana” ya kira hafsat din yana sauke lallausar qafarsa a qasa tsigar jikinsa nadan xubawa,haka kawai yake ji gyaran data yiwa sassan nasa bai gamsar dashi ba,saboda ya riga ya saba…..muddin widad din tayi gyara to sai ka rantse da Allah wani engine akasa aka kauda qazantar waje.

    Dan jim tayi don ta qagu ta kira yarinyar,tanason jin abubuwa da yawa daga bakinta ko zata samu haske kan zarginta,amma ganin ya kafeta da idanu yasa ta kasa bashi uzurin cewa tana zuwa din,ta juyo ta dawo ta samu waje ta zauna

    “Meye da meye a kayan amfaninki ya qare?” Ya tambayeta yana hada hankalinsa sosai a kanta with seriousness,don shikam Allah ya sani,bayason ya zalunceta,amma muddin za’a ci gaba da tafiya a haka komai zai iya faruwa,zuciyarsa zata gaza daurewa hada waje da ita.

    Sosai ta kalleshi,saita girgiza kai

    “Babu komai” shuru yadanyi yana jinjina amsarta,sai ya miqe ya kama hannun nawwara

    “Ban yarda ba,muje na gani”, kamar zata fasa kuka haka ta miqe,shigarsa sassanta tasan ba abinda zai dadeta dashi wani bacin rai,bata da damar musu,haka ta miqe tabi bayansa.

    Suna fitowa daga sashen sukaci karo da wata iska mai qamshi dake kadawa dukka ilahirin harabar gidan,yaja iskar sosai cikin hunhunsa ya fesar,a wajen mutum daya yakejin wannan qamshin,kuma ko yanzun ya tabbatar yana fitowa ne daga sassanta,kewarta yaji ta saukar masa,tamkar sun dauki wani lokaci mai tsaho ne basu tare,yayin da hafsat ta dinga shaqar qamshin itama,tana tunanin daga ina yake haka?,da bata gane ba saita watsar,ta raya a ranta qilan daga maqota ne.

    Suna ratsa falon yana qare masa kallo,yadda dukka yabi ya haukace,harda kayan wanki zube saman kujera,ko meye ya kawo.kayan wanki falo oho,suna isa bedroom dinta ta qarasa tsinkewa da al’amarinta,anya hafsat bata da ciwon qazanta?,wani lafiyayyen zani da bashi bashi ne yake fitowa daga bandakinta yana baiwa dakin wani irin yanayi mara dadi,katifarta gayanta ce kawai,babu zancan bedsheet akai,dukka qofofin wardrobe din nata a bude suke hanhai,ga kaya wasu a qasa wasu a ciki.

    Iska ya shaqa ya fesar yana lissafa yadda zai kutsa kai bandakin,yaja iska sosai cikin hunhunsa sannan ya saka kai tana biye dashi,ranta dukka a bace,inda ya bari widad ta gama gyarawa ai kome zai shigo yayi sai yayi.

    Da daya da daya yake bude kowacce locker dake bandakin,dukka kayan da yake siya da sunanta na gyara kama daga shaving cream,shower gel, mouth fresh,relaxers,hair mist hand and foot cream dukka gasu nan jibge,wasu har ya manta daya siyesu ma saboda tsabar dadewa da sukayi,da ya saka hannu ya dauko da yawansu ma sun gaji da zama sun bushe a ciki,wasu sunyi expire,haka ya dinga tarkatosu gaba daya ya zuba a wani qaramin bucket ya fito dasu daga bandakin.

    A bedroom din ya tsaya,ya sake wangale qofofin wardrobe din nata yana duba kayanta daya bayan daya,yanaso yaga ta inda ya gaza,yanason yaga ko daga shine,saidai dukka sutturunta suna nan danqare,ya buda bangaren kayan baccinta dake jibge masu uban yawa,kasancewarsa ma’abocin son nighties baya rabo da siyansu komai tsadarsu,su dinma suna nan kar kar dasu,wasu ma a cikin ledarsu bata bude ba,sai ya juyo yana dubanta,idanunsa fal bacin rai da kuma soma gajiya da halayenta

    “Ta ina ne na gaza hafsat?,me kikeso nayi miki ne?,wanne hakki naki ne ban sauke ba?” Yaune kadai ta danji nauyi,amma girman kai da qi fadi yasa taqi hari hakan ya fito,sai ta bata ranta kadan tana cewa

    “Nifa bance ka gaza ba,sannan kuma nima ya kamata ana dubawa anamin uzuri,aidai kasan ba haka ka auroni ba,kuma ba haka nakeyi ba tun farko ba,yanxun yarane da hidimar gida ta yimin yawa” ransa ya baci sosai,a qalla tunda taga laifinta quru quru ko accepting ai ya kamata tayi ko?.

    “Ina yaran suke?,ni ban gansu ba,yara qwaya biyu kacal?” Ido ta fidda

    “Aikai raina hidimarsu kekeyi?”

    “Eh na raina,tunda koni ija iya hidimarsu,meye bana iya musu?” Baki ta tabe tana riqe qugunta,shikam ya fiya jidali da daga hankali,batasan meye damuwarsa ba da rayuwarta,yanzun nan ta gama gyaran sashensa ko hutawa batayi daga wahalar aikin ba ya tasota a gaba yana son tozartata.

    Wani bacin rai dake taso masa ya hadiye,cikin danne fushinsa yace

    “Am tired…..na gaji da wannan halayen naki hafsat,anzo gabar da dole ki gyara,bazan ci gaba da lamuntar haka ba” maganarsa ta farki zuciyarta ta kawo mata fassararta,zuciyarta na sake qarfafa mata gwiwa ba shakka akwai wata a qasa,bai taba gaya mata wannan kalmar ba sai yanzu,anya yarinyar can kuwa bata fara zamewa rayuwarta barazana ba
    [3/18, 4:01 PM] +234 813 343 4840: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)
    *Arewabooks:Huguma*

  • Arubuce Ta Ke 82

    Arubuce Ta Ke 82

    Page 82

    Qwafa taja sanda ta gama parking motarta kusa da tashi,ranta ya quntata sosai,duk sauri da taga yana yi dama nan ya nufa,tafison hakan dama,gwara ayi komai a gabansa,ta kashe motar, saidai kafin ma ta zare key din daga jiki tuni mimi ta bude murfin motar ta fice abunta.

    Da harara tabi bayan yarinyar,ta tsani yadda take rawar qafa akan wannan tsohuwar,amma tana qara wayo zataci ubanta ne,ba zata dauka wannan ba.

    Da gudunta yarinyar ta fada falon tana kiran sunan anty widad da hajiya,abbas ya bita da kallo yana hade ransa

    “Koma kiyi sallama” da sauri ta koma tayo sallamar ta sake shigowa,saidai hakan bai rage mata karsashinta ba,tana shigowar ta fada saman cinyar hajiyan,kafin su sake cewa komai hafsat tayi sallama ta shigo

    “Ikon Allah,ashe tare kuke” hajiya ta fada tana ma hafsat din sannu da zuwa.

    Idanunta akan kwanukan daya gama cin abinci, qamshin abincin yana nan daram a falon,kana shigowa kuma zai buwayi hancinka,haushi da kishi suka cikata,abind aya sassauta ma abinda takeji a ranta rashin ganin gilmawar widad din kwata kwata.

    Saman kujerar dake daura da hajiyan ta zauna,a maimakon zama a qasa kamar yadda ta samu abbas din

    “Hajiya ina kwana?” Ta gaidata tana sake qarewa falon da kwanukan abincin kallo,a mutunce ta amsa mata cikin nuna kulawa gami da tambayarta yara da kuma gida,duka ta amsa mata da lafiya lau,sai kuma shuru ya biyo baya,dai dai lokacin da baba usaina tayi sallama ta sako kai

    “A’ah yau kece a gidan?” Baba usaina ta fada tana zama itama,fuska hafsat din tadan saki,saboda saboda alaqar dake tsakaninsu ta amsa mata tana gaidata,suna tsaka da gaisawan mimi ta dami hajiya da batun anty widad

    “Tana daki,leqa kice idan ta gama tazo su gaisa da umminki,a kwashe kayana abincin nan ma a wajen” ta kuwa falla da gudu tayi dakin,abbas yabi yarinyar da kallo,yana jin shima kamar yabi bayanta.

    Sauke idanunsa yayi yana miqewa tsaye hadi da daukar wayarsa dake aje gefe

    “Kada ka fita fa,inason zamuyi magana ne ai” aninda ya dauke wutar magana cak a falon,kowa yayi shuru sai sautinta daya fita dake yawo,da mamaki ya kalleta,wacce magana ce da basuyita ba kafin ya fito sai a nan?

    “Hajiya wajenki nazo akan abbansu mimi”

    “Tooo…. ikon Allah,koma to ka zauna” hannuwansa ya sauke,ya koma hannun kujerar daya tashi a kai ya zauna,can qasan zuciyarsa nason darsuwa da bacin rai amma yana kaudarwa,tunda har yanzu baisan dalilin zuwan nata ba,saidai kwanyarsa nata son hakaito masa abinda ya faru da zai sanya tayi tattaki qafa da qafa har gaban mahaifiyarsa ta kawo qararsa,duk da bawai yau aka fara ba.

    Kafin takai ga cewa komai widad ta fito,riqe da hannun mimi sunata dariya abinsu,cikin wani lace sky blue da ratsin farin zare da aka yiwa dinkin tea bubu,bata daura dankwali ba sai siririn mayafi data dora a kanta mara nauyi kalar sky blue din.

    Idonsa ya lumshe ya kuma budesu yana sake zubesu a kanta,yaji wata nutsuwa na maye gurbin abinda keson motsawa daga zuciyarsa.

    Tare da qamshin nan nata ta iso,ya buwayi falon kuwa gaba daya,cikin ransa yake raya tabbas itama da qaunar turare cikin jininta,ta duqa cikin girmamawa ta gaida baba hassana.

    Kadaram kadaham ta amsa mata,tana qare mata kallo a fakaice

    “Tirqashi” ta fada qasan ranta ganin yadda yarinyar take sake juyewa,kyakkyawar siffarta da kuma kamanninta suna sake ninkuwa da bayyana kansu,idan akace za’a hadata da hafsat ko a yanzun ratar me yawa ce,balle kuma ace nan gaba?,ai sai abinda idanu suka gani,ita kuwa lami(mahaifiyar hafsa) tana aikin me?.

    Sanda widad din take gaida hafsan sai data tattaro dukkan qarfin halinta sannan ta iya amsa mata,gaba daya yarinyar tayi mata ba zata,tsahon wata dayan da bata ganta ba sai taga ta cika sosai,ta kuma fara zama cikakkiyar mace,gabanta yayi.mugun bugawa sanda zuciyarta ta laqana mata tambayar shin me zai kawo wannan sauyin?,ita kadai ta girgiza kai,bata yarda komai zai faru ba,a yadda abbas din yazo mata a zafafe jiyan ta tabbatar bai samu komai daga gareta ba,inda ya samu din ta tabbatar bazai zo mata a birkice haka ba,bataga wani sauyi daga wajensa ba duk sanda yayi mata zuwa irin wannan,saima qaruwa da abun yayi,duk da cewa taga wasu qananun sauye sauye,kamar mitar rashin shaving da turare a jikinta,saidai basukai mizanin da zata dorasu a komai ba,tunda batasan da zuwansa ba ai,ganinsa tayi katsam,bai kuma gaya mata yana da buqata ba ballantana ta shirya,kai koda ya gaya matan ma iya abinda zata iya shi tayi shi kuma zata ci gaba da yi.

    Motsawa baba usaina tayi

    “Bari na baku waje,naga kamar magana zakuyi”

    “Haba,kiyi zamanki,duka ba ‘ya’yanki bane” hajiya ta fada da kyakkyawan nufi,dama haka takeso,don haka ta koma ta zauna din tana cewa

    “Hakane,ia bakaqi ba,kada aga kamar bakasan matsalar kowa ba sai taka,d’a ai na kowa ne, bare abbas da kowa yakecin moriyarsa?”.

    “Ina jinki hafsatu,mene ya faru?,ina fata ba matsala bace” fara matsar hawaye tayi sannan ta magantu

    “Matsala ce hajiya, matsalar kuma abban mimi ne da kansa yakeson haifar da ita cikin gidansa”

    “Tofa!,tirqashi!” Baba usaina ta fada da madaukakin sauti bayan ta kama haba,yayin da abbas ya bude dukka idanunsa a kanta yana kallonta,tare da sauraren wanne kalar sharrin kuma zatayi masa

    “Mene ne ya faru?,gayamin” gyara zaman

    “Hajiya,kwata kwata abban mimi bambanci yake nunawa tsakanin da widad muraran,bayason huldarmu ni da ita,qiri qiri sai suzo weekend har su gama bazanga fuskarta ba bare ta zauna a gidanta ba,wasu ma basai suyimin sharrin na hanata zama ba?”

    “Laahhhh,da gudu kuwa,mutumin yau da baka iya masa?,tabdi” baba usaina ta karbe zancan

    “To bama haka ba,ta yaya zamu shaqu mu fahimci juna da ita hajiya tsakani da Allah,sannan su kansu yaran nan bakiga yadda sukeson zama da ita ba,amma gaba daya basu samun ganinta,a haka kan iyalinsa zai hadu?” Shuru hajiya tayi tana jinjina kai,maganarta ta qarshe ce kawai taja hankalinta,har takega tayi magana me ma’ana,baba usaina nason tsoma bakinta tace wani abu,amma kuma kwarjinin abbas din ya hanata,banda

    “Gaskiya ya kamata a aduba,saboda gobesu dana yaran” shi taketa maimaitawa

    “Kinzo da magana me kyau da ya kamata a duba,ki kwantar da hankalin ki, za’a gyara lamarin in sha Allah, Allah yayi muku albarka,ya qara hada kanku,ya wanzar da zaman lafiya a tsakaninku”

    “Ameen ameen…. yauwa,hakan dai yafi gaskiya,ta nan ne zasusan darajar juna,ita tasan darajar uwargidanta”.

    Taso ta sake qirar wani abun,amma hada idon da sukayi dashi yasa ta kasa cewa komai,sai kawai ya miqe ya fice afalon ransa yana masa suya,fita yasoyi amma sai ya kasa,yana daya daga cikin kujerun dake harabar gidan ya zauna kawai,qafarsa daya kan daya yana dan jefata a hankali,bacin ransa yakeson dannewa,ba kasafai ya fiya son barin bacin rai yana masa tasiri ba.

    Ba jimawa baba usaina ta fice,daga bisani hafsat din ta fito yaran suna biye da ita,hajiya a bayansu tana rabawa yaran alawa da manyan biscuits data saba basu,daga inda yake zaune yana kallonsu,yasan babu lallai su ganshi,har suka fice daga gidan ya kasa motsawa sai rakiya da yayi musu da idanu.

    Sai da aka kira azahar ya fita masallaci yayi sallah,daya dawo sai ya bude setting room din gidan dake farfajiyar gidan ya kwanta,har yanzu abun yana masa yawo a zuciya,shi har yanzu baiyi girman da za’a daina kawowa hajiya da kawunnansa qararsa ba?,har yanzu baiyi girman da kunnuwan hajiya zasu daina jin matsalarsa da damuwarsa ba?,har yanzu hafsat batayi hankalin da zata zauna dashi su fahimci juna su warware matsalarsu ba shi da ita ba tare da duniya taji ba?,kansa ya kada a hankali yana kiran sunan Allah,ya rasa yadda zai rabata da wannan halin,bayan shi din har yau bayajin zai iya tuna wata rana da ya taba kai qararta gidansu ba.

    Wayarsa dake saman kansa ya dauko,ya lalubo number dinta dake rubuce da sunan BABY DOLL ya kira, ringing daya aka daga,muneera ce,ta gaya masa sallah takeyi,yace idan ta idar ta gaya mata ta sameshi a setting room,ya ajjiye wayar yana gyara kwanciyarsa.

    Minti biyar cikakku qamshinta ya fara marabtarsa,ya rufe idanunsa yana budesu,suka sauka a kanta,hannunta dauke da madaidaicin tray data dora wani glass jug akai da qaramin cup guda daya.

    Ido ya zuba mata yana qare mata kallo son ranshi,kamar kowanne lokaci sai yaji damuwarsa tana raguwa,a nutse ta iso ta sunkuya a gabansa tana ajjiye masa jug din,sai ya fara yunqurin tashi,ta miqe zata ja baya ya samu nasarar riqota,yayi mata mazauni saman cinyarsa,kunya ta sanyata boye kanta a kafadarsa,taqi yarda su hada ido

    “Ki kalleni please baby…….zuciyata ba dadi,nasan zan samu relief” har cikin zuciyarta taji wani abu ya tabata da fadin hakan,saita daga kanta da sauri,kodai qarar da mommy hafsat ta kawowa hajiya ce ta bata ransa?,ta tuna kalaman mommynta na qarshe

    “Banda kai miji qara,abune mara kyau,koni bance ki kawomin qararsa ba,idan ya bata miki rai ki gaya masa ku fahimci juna” sannan ta tuna da kalaman ummunta

    “Kome mijinki yayi miki ya isa ne,banason qorafe qorafe dakai qara” sannan tana tuna yadda take sanya yayyensu a gaba da fada duk sanda kika kawo mata qorafi akan mijinki,musamman idan bai gamsheta ba

    “Kayi haquri” ta furta da tausasan labbanta da ko yaushe suke burgeshi,har baisan sanda murmushi ya subuce masa ba,ya rabb……ba ita tayi laifi ba,amma ita take bada haquri,ya tabbatar idan zai dige indai ba wuya ce tayi wuya ba zaiyi wahala wannan kalmar ta fita a bakin hafsa

    “Zan haqura,amma saikin yarda na taba nan” ya fada yana mata nuni da qirjinta da yadan sake cika,da sauri ta kama hannunsa da yayi mata nunin dashi tana fidda ido waje,saidai kafin tace wani abu ya langabe mata kai kamar ba shine babansu mimi ba

    “Don Allah,kiji tausayina mana” kafada ta noqe masa itama tana shagwabe masa

    “To na kwanta agun ko na minti daya ne,idan kikace aah fa zanyi kuka” dariya yaso bata,amma tsoro tsoron da takeji ya danneta,kafin ta bashi amsa ya kama dukka hannayenta biyu ya riqe cikin nasa,ya kuma cusa fuskarsa da kyau tsakanin qirjin nata.

    Sosai ya zuqi numfashi ya kuma fesar,ta lumshe idonta tana jin yadda dumin numfashin yake ratsa ta tun daga rigarta zuwa brassiere dinta,ya kuma tarar da fatar wajen.

    Wani irin abu data kasa daurewa ya zarce dayi mata yana sake cusa kansa a wajen,ta zame hannuwanta daga cikin nasa ta riqe kansa da kyau,sai ya tsaya cak jin yadda jikinta ya dauki rawa,ya kuma zare fuskar tasa,ya sauke idanunsa da suka kada sukayi jaa saman fuskarta.

    Sai daya dauki wasu sakanni yana kallonta sannan ya motsa bakinsa cikinn shaqaqqiyar muryasa yace

    “Ina da buqatarki baby…..ina da buqatarki gaba dayanki,rayuwata na da buqatarki fiye da yadda ruhi yake da buqatar numfashi” kalaman sun mata nauyi sosai,saita kifa kanta kawai a qirjinsa bugun zuciyarta na qaruwa.

    Sun jima a haka kafin ta zame jikinta ta sauka qasa ta bude jug din,smoothie ne na banana da yasha madara data jefawa qananun ice cube a ciki yayi madaidaicin sanyi,ta tsiyaya ta miqa masa a cup.

    “Na gode” ya fada yana karba,kunyarsa tasa ta sakin murmushi kawai,ya kurba ya lumshe ido,dadinsa yana ratsa kunnuwansa

    “Yaushe kika koyi wanann?”

    “Jiya,yayi dadi” sai daya jijjiga kai sannan yace

    “Over!” Yadda ya fada din ya bata dariya
    [3/18, 4:01 PM] +234 813 343 4840: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)
    *Arewabooks: Huguma*

  • Arubuce Ta Ke 79

    Arubuce Ta Ke 79

    Page 79

    Kaman wanda aka yiwa hani da daga wayar har ta katse sannan ya miqa hannu ya dauki wayar,yana shirin binta kiran ya sake shigowa,sai ya gyarawa widad zama a jikinsa sosai,yana sake riqeta a jikinsa cikin wani taushi da salo

    “Ina ka shiga ne inata kira” abinda kunnuwansa suka fara jiye masa kenan,sai ya lumshe idanunsa ya kuma bude lokaci guda

    “Assalamualaikum” ya furta a nutse,a tunaninsa zata ankara da kuskurenta ta kuma gyara

    “Wa’alaikumus salam……inata kiran wayarku baku daga ba duka ku biyun” ta sake maimaitawa tare da amsa sallamar duka guri guda.

    Danne zuciyarsa yayi kadan,idan da sabo yaci ace ya saba da duk wata dabi’a ta hafsat din,to amma kullum baqin halayenta sake qaruwa sukeyi

    “jiya gaba daya ko ka nemeni,sannan itama inata kiranta bata daga ba” ta kuma fadi cikin azalzala da ci da zuci

    “Tana ina ka bani ita” ta kuma fadi dai still,sai ya buda idanunsa gaba daya kamar tana gabansa

    “Wai me yasa koda yaushe ki bakisan abinda ya kamata ba?,da sassafen nan kin kirani kina jeramin tambayoyi kamar wani yaronki?,me yake damunki ne?,baki ji ya na kwana ya na tashi ba?” Fuska sosai ta bata,ita ba wannan bane ya dameta,hidimar bikin qanwarsu da suka fada kwana biyu bata kirata ta jaddada mata jan kunnen data saba mata ba shine damuwarta,uwa uba yadda ra’ayoyin mutane da kuma hirarrakin da aka sha akan kishiya gidan bikin ya dugunzuma mata lissafi gaba daya

    “Jiya kadai ban kiraki ba kinji babu dadi….kinyi tunanin yadda nakeji?,ke da sam idan ban kiraki ba saidai a zauna a haka idan ba buqatar kanki bane ya taso?”

    “Nidai don Allah,kai me yasa ba’a yi maka abun arziqi?,yanzu gashi dana kiraka ka hauni da qorafe qorafe?, widad nace ka bawa tunda naji muryarka ai nasan lafiya lau kake”

    “Bacci takeyi” ya amsa mata kai tsaye,zuciyar hafsat ta buga,bacci a dai dai wannan lokacin?,ya akayi ma yasan tana bacci idan dai ba tare suke kwana ba?

    “Bacci kuma kamar tare kuke kwana?” tayi subutar bakin fada,sai tambayar tayi masa banbarakwai,kulata sam bashi da amfani,don haka ya sauke wayar kawai ya kashe.

    Sosai hankalinta ya daga,ta saka lalubo number dinsa da tayi saving da abban mimi ta soma.kira ba qaqqautawa,har abun ya sake daure masa kai,daga baya sai ya kashe wayar ma gaba daya,ya sauke ajiyar zuciya yana sake gyarama widad kwanciya cikin jikinsa.

    Sau tari idan hafsat din tayi wani abun….sai ka rantse da Allah bata da maraba da masu tabin hankali idan ta aikata wani abun,kuma a wajenta wannan dai dai ne?.

    Kasa zama tayi,ta dinga kai kawo a dakinta,tana ganin kamar ta fara sakewa fa da yawa,kamar abbas din yana son canza hali da dabi’a,indai hakanne bai kamata taci gaba da sakewa yarinyar ba,bai kamata taci gaba da ganin haqorinta a waje ba,lallai dole tasa tsananin rashin wasa da rashin sakin fuska a tsakaninsu,amma ta ina zata fara?,duk shi ya cuceta da haramta mata zuwa kaduna,tasan halinsa kuma,yana da wahala kaga fushinsa,amma a duk sanda ya taurare lallai babu mai sakashi ya sauko,sai wata zuciyar ta bata shawarar ta kaiwa hajia ko kawu hassan qorafinta,to amma kuma hakan bamai yiwu bane,tasan babu abinda hakan zai haifar sai tashin tashina,abun qarshe yazo ya juye a kanta,amma kam tabbas ba zata dauki wannan dokar nashi taci gaba da tafiya a haka ba.

    Qarfe goma na safe ta motsa,ta bude idanuwanta a hankali ta zubesu kan fuskarsa,ta lumshe su tana sake budesu,wata bala’e’iyar kunyarsa tana saukar mata,sanda ya motsa yana ajjiye magazine din hannunsa ta maida idanunta ta kulle ganin yana niyyar fahimtar ta farka,batasan ya akayi ya gane ba,tadai ji fitar murmushinsa sannan ya sukunya yayi mata rumfa,ya sakar mata lallausan kiss saman tausasan labbanta dake matuqar jan hankalinsa

    “Good morning baby doll” cusa kanta tayi cikin cinyarsa cikin wani yanayi najin kunya,yaja numfashi mau nauyi saboda yadda ta sanya kan nata tana sauke masa numfashi mai dumi yana ratsa fatar cinyoyinsa ya tabashi sosai, hannuwansa ya saka ya dagata gaba daya ya sauketa cikin jikinsa,ya mamayeta da hannuwansa duka ta shige jikinsa sosai cikin wani lallausan riqo.

    Kasa kasa yake mata magana cikin kunne,kamar wani na a wajen zai iya jinsu

    “Yanzun ke babba ce babyn uncle,don Allah ki daina kunyar nan,tun jiya uncle dinki baiji muryarki ba,mommy tace banda musu…… mommmy tace ni mijinki ne……mommy tace ki kula dani kin manta?” Kai ta gyada a hankali,karon farko qaramin murmushi ya qwacewa fuskarta daya tuna mata da mommyn nata

    “That’s good mommy’s girl,say something please,i wanna hear your sweet sweet sweet voice”

    “Ina kwana uncle?” Ta fada a mugun shagwabe,zaka dauka tana sane tayi hakan,saidai ko kusa,kawai sound din ya fita a haka ne.

    Hannunta guda ya riqe cikin nasa tana murzawa a hankali

    “Lafiya lau baby…..ya jikin?,hope kin warware?” Kafada ta maqale masa a narke tana mele baki kamar yadda qaramin yaro keyi duk lokacin da yake shirin sakin kuka,hakan ya bashi damar ganin baby face dinta da kyau,ta sake wani fresh sossaaii,ko wannan shi ake kira da qyallin amarcin da ake fada?,ya raya hakan a ransa

    “Har yanzu gurin da ciwo”

    “Sosai?”

    “Ba sosai ba” ta amsa mishi tana kallon qwayar idanunsa,abinda ya haifar masa da wani sabon feeling mai qarfi a kanta

    “Kinsan me za’a yi?” Ya sake fada yana gyara mata zama sosai a jikinsa

    “A sake guda daya zaki warke” wani shagwababben kuka daya tasheshi a aiki ta saka,ta fara tuttureshi tana shura qafafuwa,irin yadda takewa ummunta duk sanda rigimarta ta tashi

    “Iyeeee,eh lallai babyn uncle ta warke,let’s try again” shigewa jikinsa tayi ta qanqameshi tana sake sakar masa kuka,irin wannan shagwabar yakeso ya gani…..irinta yake da buri…..a matsayinsa na police…..He knows hardship,he knows hardness,duk wani nau’i na tsawa bada umarni da seniority shi ya sani yake gani, at least a gidansa yana buqatar soft and cool attitudes which can make him peaceful and calm.

    Shuru yayi ba tare da ya lallasheta ba,ya lumshe ido yana jin yadda muryarta ke fita da da wani irin taushi sakalci da kuma quruciya,har sai da yaga bata da niyyar tsagaitawa da gaske ta tsorata,sai ya saki murmushi,ya sunkuya a hankali,ya cusa fuskarsa ta gefan fuskarta ya lalubi kunnenta,cikin rada yake gaya mata wasu.maganganu da suka sanyata jin kunya

    “Uncle….. uncle” abinda ta fara fada kenan tana riqe gaban rigarsa da kyau wai zata boye fuskarta a ciki,sai ya saki siririyar dariya ya dagata gaba daya yana cewa

    “it’s bath time”.

    Sai da sukayi wanka gaba dayansu ya hada musu breakfast a gurguje sannan ya bata magungunanta tasha.

    Komai ya hanata yi,tana daga kwance tana kallo,saidai duk giftarawar da zaiyi saiya bar mata abinda zai sanyata dariya,inda zaka ganshi a lokacin,zaka rantse ba ASP abbas bane,miskilin da ganin haqorinsa ko murmushinsa ke zama wani babban aiki,zaka zaci wani mutum ne can na daban mai kama da abbas din.

    Cikin kwanaki biyun gaba da babu inda yaje,suna tare cikin gidan,komai na gidan ya dauke mata,yayi wani irin mugun sakewa da ita matuqa gaya,ya kuma jata jikinsa sosai,a yanzun babban burinsa ya gina rayuwa mai.inganci ya gina rayuwar da zata zame masa madubin gobensa,duk wani abu da yasan tana so,ya kuma fuskanci yana sakata nishadi da walwala shi yakeyi,wani irin tattali da kula yake nuna mata,wani abunma baisan yanayi ba,don yana tasowa ne daga qasan zuciyarsa komai yake tasowa,wani irin yanayi dashi kansa baisan a ina zai ajjiyeshi ba.

    Kudi yake zuba mata sosai a waya,tana daga zaune tayita kiran ‘yan gida tana shan hira,musamman ummunta da mommynta,kusan ko da yaushe maganar mommyn tabi mijinta,banda musu ko taurin kai,sabawa umarninsa da sauran dukka abubuwan da bayaso,koda yaushe tana gaya masa

    “Ki kula dashi,kiyi masa dukkan abinda yakeso,banason na sake jin kowa yaji wani abu da yake gudana a tsakaninku,ko meye zaiyi miki ko ke zakiyi masa,mai dadi ko mara dadi,sirri ne tsakaninku,ki zauna kiyi tunani ki koyi warwarewa da kanki,idan kin gaza ki nemeni” kusan rabi da rabin hirarsu da ita kenan cikin hikima.

    Hutun satin ya dauka ganin ba wasu tarin ayyuka sosai a office,saidai lokaci lokaci ya leqa office din yayi awa daya ko biyu ya dawo gida a daddafe,don baya iya haura hakan,sai yaji gaba daya nutsuwarsa da hankalinsa sunyo gidan.

    Ita dinma komawa take kamar wata mara lafiya muddin xai fita ya barta a gidan,saidai idan ta fita makaranta,wanda zuwa yanzun da kansa yake jigilar kaita da daukota,bai sake yarda wani ya kaita koya dauko masa ita ba,bayajin zuciyarsa zata iya dauka wannan.

    Cikin sati guda ta warware,ta warware da wani irin soyayya da shaquwa dashi sabuwa data ginu a ranta,ya bar mata wani babban tambari da ya kame ilahirin zuciyarta gaba daya ba tare data ankara kota fuskanci meye ba,tasan dai a wannan lokacin tana matuqar son kasancewa tare dashi,tana jin wani farinciki duk lokacin daya zamana yana kusa da ita,suna hira aikin gida ko kuma assignments,tana jinta sukuku cikin rashin sakewa da walwala a duk lokacin da ya zamana ya nesanta da ita.

    _cikin wannan yanayin sati biyu da suka biyo baya ya shirya ma zuwa gida weekend,yace ta shirya su wuce tare,don baya jin zai iya barinta har tsahon kwanaki uku ba tare da tana kusa kusa da rayuwarsa ba_

    *_muje zuwa dai masu karatu,yanzu takun zai fara daukan zafi_*
    [3/18, 3:05 PM] +234 903 685 1413: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)
    *Arewabooks:Huguma*

  • Arubuce Ta Ke 76

    Arubuce Ta Ke 76

    Page 76

    Tunda akayi sallar magariba bai motsa ba a masallacin,yaci gaba da zama yana sauraren masu karatu dakeyi tsakanin magariba da isha’i,idanunsa a lumshe amma ita yake hangowa a ciki,yasan dai yau zaisha daaru da qorafi,to amma hakan yafi masa sauqi akan abinda zaije yazo,a yanayin da yake ciki yasan ko hafsat saidai idan zata nuna juriya ne kawai,bawai don qarfinta zai iya dauka ba.

    Har aka gama karatun aka yi sallar isha’i ba abinda ya canza,ya kalli agogo tara saura na dare,yasan a yanzun tana shirin kwanciya saboda akwai makaranta gobe,sai ya tashi yayi Shafa’i da wutiri sannan ya baro masallacin,bai koma gidan ba sai daya biya ya siya fruit.

    Tana lafe cikin kujera tana qananun hawaye,ga kukan mage daketa zarya yau tsakanin sassansu da ainihin main gidan,ya tura qofar da qaramar sallama maqale a bakinta,ga mamakinsa sai ya hangeta cikin kujerar,yayin da ganinsa ya bata qwarin gwiwar miqewa da gudu tayo wajensa,tana zuwa ta fada jikinsa ta sakar masa kuka

    Lips dinsa ya cije,ya dora hannunsa saman sumarta dake tsole masa idanu tun shigowarsa ta dazu yana shafa sumar daga saman kanta har zuwa inda jelar kalbar ta tsaya,bakinsa ya kasa furta komai,sabosa yadda komai ya dawo masa sabo bayab kasancewarta cikin jikinsa.

    Sun jima a haka,yanata karbar feelings yana mazewa har zuwa sanda ta lafa da kukan

    “To mene na kukan?” Cusa kanta tayi a qirjinsa,itama qamshinsa yana qayatar da ita,sai data tura baki gaba kamar yana kallonta sannan tace

    “Ba kaine ba,na dade inata shan wahala,nayi maka girki kuma daga shigowa saina nemeka na rasa”

    Murmushi ne ya subuce masa,ya hadiyi yawu da qyar sannan yace

    “That’s all?” Kai ta gyada masa a hankali

    “To ya isa,yanzu bari nayi wanka nazo naci abincin,ai bance bazanci ba ko?” Hakan daya fada yayi mata dadi,ta rakashi dakin ta hada masa ruwan wankan da kanta,amma sanda taga ya fara balle botiran rigarsa saita miqe zata gudu.

    Hannu daya yasa ya dawo da ita gabansa,ya futa tsaho sosai,saiya sake janyota zuwa jikinsa suka hade waje daya,ya bata saman qafafunsa ya taka,hakan ya qara mata tsaho,yana riqe da ita da hannu daya,daya hannun kuma yana cire maballan.

    Saura hudun na qasa,saiya saki,ya kamo hannunta a tausashe ya dora akan qirjinsa

    “Qarasamin” ya fada yana saka daya hannun nasa ya zagaye bayanta dasu,hakan ya bata damar tsaiwa sosai,saidai dukka hannayenta biyu rawa suke,fatanta kawai ta cika umarnin mommmy data gaya mata duk abinda yace yanaso daga yau ta tabbatar tayi.

    Fuskarta yaci gaba da qarewa kallo sanda taje cire masan,tun daga cikakkiyar girar idonta,qaramin lallausan kabbanta,tana da wani irin kyau me sanyi da tsayawa a rai,duk da har yau yaga alamar batasan wannan baiwar da take da ita ba.

    Duk second daya da zasu qara a haka sake qayatar dashi tsaiwar take,rawar da hannunta keyi yasa ta dauki lokaci kafin ta gama,duk da cewa saman qafafunsa take a tsaye,amma hakan baisa yaji gajiya ba ko kadan

    “N…..na gama”ta fada muryarta tana dan rawa,saiya sukunya gishinta yayi kissing dinta,zuciyarsa nata tunzurashi ya zarme amma yana mata waigi,two step back yayi yana sauketa sannan yace

    “Thank you” ya furta hade da wani siririn murmushi ya wuce ta saman labbansa,saiya fara zare rigar,ta juya da hanzari ta fita a dakin, murmushi ta qara saki yana girgixa kai,ya dauki towel da widad din ta yiwa waje na musaman ya rataya ya shiga wanka,wannan ya bata damar guduwa daga dakin.

    Komai ta shirya masa a table mat,sai data tabbatar komai yayi sannan ta wuce daki ta debo books dinta na makaranta da aka basu assignment ta dawo dasu parlor din,don dama kusan ko yaushe tare sukeyin assignment,saita koma koma ta zauna saman kujera tana jiran fitowarsa,wayarta na hannunta tana chart.

    Ba jimawa sassanyan qamshinsa ya soma isowa parlor din,ta daga kai a hankali tana dubansa,yayi kyau cikin wasu light blue din kaya,fuskarsa tayi fayau kamar wanda yayi aikin wahala,saidai yayi fresh ya kuma yi kyau.

    Tana murmushi ta miqe tana cewa

    “Kazo kaci uncle please” tayi maganar tana karyar da kai gefe,sai ya sakar mata murmushi,komai nata burgeshi yakeyi,duk da tana komai ne ita bilhaqqi da gaske,ya tako a hankali har yanzu jikinsa babu qwari ya zauna.

    Tana serving dinsa tana zuba masa surutu, yana daurewa ne kawai yana biye mata, saboda yadda gaba daya qamshinsa ke tafiya da hankalinsa,uwa uba rigar ta mugun fidda surar qirjinta da suka fara cika suna bin girma da jikinta ya fara yi,ta gama zuba komai ta tura masa tana cewa

    “Aci a bani mark” kai ya jinjina ya fara diban abincin yana ci,shuru yayi yana jinjina dadin taste dinsa,baisan sunan abincin ba saboda bana hausa fulani bane,amma tako ina ya tafi dashi.

    Itakuwa tana zaune gabansa ta tsira masa ido tana jiran jin abinda zai fada,kusan minti biyar shuru,saita fara bubbuga qafafunta

    “Uncle….. uncle…..baiyi dadi bane?” Idanunsa ya zube mata ya lumshesu kadan sannan ya jinjina mata kai

    “what a wonderful taste!…..na kasa magana ne don kada nayi shirme,I have never eaten food that tastes like this” dadi sosai ya cikata,dariyar farinciki ta kubce mata,saita matso tana dauko pillow zata saka masa a baya tana cewa

    “Bari na fara da saka maka waigi kada ka fadi” hakan da tayi ya bawa tudun qirjinta damar gogar jikinsa,nan take ya qware da abincin da yake qoqarin hadiyewa yahau tari.

    Da sauri ta tsiyaya ruwa ta bashi tana masa sannu,duk fuskarta ta nuna damuwa qwarai,idanunta sukayi narai narai da hawaye,tayi tsai tana kallonsa gami da jero masa sannu har tarin ya lafa

    “Sannu uncle,ko na qaro maka ruwan?” A tausashe ya dubeta,wani kimarta da mahaukaciyar soyayyarta tana ratsashi,he never thought that she would care about him so much duba da qananun shekarunta da kuma yadda wadda ta girme mata ta ninka shekarunta ma ba haka take masa ba.

    He wonders how she shows concern for him,ko yaya yayi dare ko ya gaggara cin abinci duka sai tabi ta damu kanta,bare taga alamun bashi da lafiya,saita zauna ta dasa masa kuka har sai yayi da gaske wajen qarfafa jikinsa da nuna mata ya warke,ko iya wannan kulawar ya samu alhamdulillah,ko iya haka ya fuskanci manufar hajiya akan yarinyar…..ko haka aka tsaya ya samu tarin abubuwa da yawa daya rasa daga wacce suka debi shekaru tare,ko a iya wannan ya samu abubuwan da ada baisan namiji yana samu daga wajen matarsa ba,saidai yana buqatar qari…..zuwa lokacin ya fara gano muhimmancinta me girma cikin rayuwarsa,yana son ya maidata tashi…..halak malak……yanason su sake zama.abu daya,yana son dandana mata soyayya mai zaqin da dandanonta bazai iya fita daga halshenta ba,yanason ta zama tasa ta har abada.

    Sai data tabbatar ya nutsu sannan ta debe kayan abincin,ta kuma gyara wajen tas yana daga zaune cikin mutuwar jiki yana kallonta,daya daga cikin abinda yake burgeshi da ita,bata yarda tabar waje a hargitse ba.

    Dab dashi ta zauna har cinyarta tana gogar tasa,cikin jikinsa ta aike masa da wani saqo me nauyi ba tare data san tayi ba,a kwanakin nan da sabo ke sake shiga tsakaninsu haka take masa,ko meye zatayi tana maqale da jikinsa kamar mage,ya fuskanci ta saba ne tun a gida,tana da son jiki,kuma hakanan dama takewa ummu.

    Saman cinyarsa ta dora littafin da hannunta duka,sannan a shagwabe tace

    “Uncle….. assignment fa” jikinsa gaba daya ya dauki rawa,yasa hannu cikin zafin nama ya janye hannayen nata duka biyu daga jikinsa,tsoro yadan shigeta ganin yadda ya sauya lokaci daya, muryarta a narke kamar zata saki kuka tace

    “Uncle bazaka yimin ba?”kai ya girgiza muryarsa na dan rawa

    “No”

    “Amma shine ka ture ni?” Ta sake fada hawaye na cika mata idanu,zuba mata ido yayi wani abu na zaga jininsa,tana sake shiga rayuwarsa da wani mugun gudu da kuma gaggawa,bayason tana shige masa a irin wannan situation din da yake ciki,idan taci gaba kuwa bashi da tabbacin abinda zai iya biyo baya

    “Banaso kina hawa jikina” kunya ta saukar mata,itace ma ke hawa jikinsa?,sai ta miqe da sauri har tana zubar da litattafan cikin borin kunya tana hawaye ta shige daki.

    Da kallo ya bita har ta bace,sai.ya dawo da dubansa nan inda ta tashi yana sauke wawiyar ajiyar zuciya hadi da rufe idanunsa,bazai bita ba don kusancinsu da ita zai iya haifar da komai,ya miqe a hankali ya wuce dakinsa yana jin yadda komai na jikinsa ya daddaure.

    Saman pillow ta kifa fuskarta kunya na cikata,me yasa take yawan zama a jikinsa?,itama bata sani ba, yawancin lokuta ma batasan tayi ba banda yanzu daya fada,ta jima a haka tana jin kunyar kanta da kanta kafin ta miqe ta shige toilet,tayi brush ta dawo gaban madubi ta fara shirin kwanciya.

    Haka kawai ta zauna ta bata lokaci tana duba duka turarukanta,na gefen kunne na gabobi na matse matsi da sauransu,tana karantawa tana shafawa

    “Bari dai na gwada naga da gaske da qamshi” ta fada a sakalce,ita kanta da kanta sai data dinga bin jikinta tana shanshanawa ta lumshe ido

    “Hmmmm,aikuwa kullum saina shafa,ashe dai da gaske da qamshi” duka ta gama wannan,saita wuce cupboard dinta ta bude tana ‘yan waqenta,leda ce ta biyota ta fado,a dan tsorace taja baya ta zubawa ledar ido,saita tuna ledar da matar gidan da suke ciki ta bata kyauta ce ranar data fara shiga,ta dauka ledar ta bude tana zazzage kayan ciki.

    Murmushi ya subuce mata sanda ta tuna abinda ta cewa abbas randa aka bata kayan,ya zuwa yanzu ta karanta amfani da muhimmancin kayan

    “Bari dai na gwada mu gani” ta furta tana dauko daya daga ciki,wine color ce mai wani matsiyacin ado na fararen furanni a jikinta,ta net ce mai wani irin sulbi kamar silk net,ta zura rigar harda pant dinta,sannan ta isa gaban madubi tana canza tafiya.

    Dan ihu ta saki tana fidda ido ganin komai nata ya bayyana muraran,ta rufe bakinta za hannayenta tana sake kallon kanta da kanta tare da jin kunyar kanta,saidai ta dade bataga abinda yayi mata maqurar kyau irin rigar ba.

    Wani abu ya darsu a ranta,gata gaban uncle abbas,saita fara jujjuyawa yadda ta taba gani a wani littafi tana gwada shine a gabanta.

    Kamar jira maqalalliyar magen gidan takeyi ta soma kuka tana kusur kusur jikin window glass dinta,mummunan faduwa gabanta yayi,ji tayi kamar ma ta shigo dakin saboda daya side na window din a bude yake,sai net kawai,ai bata tsaya tunani karo na biyu ba ta kwasa da gudu ta fita a dakin,bata kuma nufi ko ina ba sai dakin abbas cikin mugun tsoro.
    [3/17, 1:28 PM] +234 813 343 4840: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)
    *Arewabooks:Huguma*

  • Arubuce Ta Ke 86

    Arubuce Ta Ke 86

    Page 86

    “Ka gaji?,ka gaji dani kenan kake nufi?,saika dauki mataki ai k…….” Kafin ta qarasa ta daka mata tsawa,dukkan yadda yakeson ya taushi kansa haqurinsa ya gaza

    “Kada ki gayamin maganar banza da wofi,kin dauka ina tsoronki ne da bazan iya daukan mataki a kanki ba?,to ki shiga hankalinki wallahi,saboda idan nace hukuntaki zanyi abun bazai miki da kyau ba” yana kaiwa nan yayi gaba abinda har yana yin ball da botikin daya ciko da tarkacen kaya masu tsada daya wulaqantar.

    Da kallo ta bishi zuciyarta na suya,mamaki kuma ya cikata,wai yau ita abbas yakewa haka?,sai zuciyarta ta karye qafafunta sukayi sanyi,hawaye ya fara sauka daga idonta,ta koma ta zauna gefan gadonta tana share hawaye.

    Zuciyarsa na zafafe sosai sanda ya baro mata sashen,ya isa sashensa kai tsaye ya wuce bedroom dinsa,wannan karon bazai qyaleta ba,ko yaya zaiyi magana da wani magabacinta ko za’a samu sassaucin wani abu,yana tsoron faruwar abubuwa da yawa a nan gaba daga gareshi,baisan me zamansu zai zama ba a gaba,ga yara mata da yake dasu da yasan dolen dole wataran gidan wani zasu je,uwa uba kuma yanayi na lafiya,ta yaya muhalli babu cikakkiyar tsafta za’a samu ingantacciyar lafiya?.

    Saman sofa bed dinsa ya zauna yayi waya ta a qalla mintuna goma,koda ya gama wayar riqeta yayi a hannunsa yana jin banbarakwai babu dadi,yau ya aikata abinda bai taba aikatawa ba wato kai qarar hafsat din, tsahon zamansu tare na wasu shekaru.

    Ta bangaren widad tuni ta gama tsaftace sassanta, hankalinta bai kwanta ba saida ko ina ya dauki qamshi,ta fiddawa mimi uniform dinta ta sake mata wanka,akwai ragowar kayanta a sassan tun wancan zuwan da tayi,ta saka mata su,saita tsaya tana kallonta.

    Yarinyar kyakkyawace,kawai rashin tsafta da gyara ne yake dakushe duk wani kyau nata

    “Anty ki kaini wajen daddy yaga kwalliyata,dama inata cewa mommy tayimin tana cewa bata da lokacin wannan” murmushi ta sake

    “Wanka zanyi nima,ki bari idan nayi saina kaiki” marairaicewa tayi

    “Don Allah anty,nidai yanzu” ba yadda zatayi,dole haka ta dora qaramin mayafinta ta kama hannun mimin suka fice tana cewa

    “Duk chocolate din da daddyn ya baki kin yarda zamu raba?” Tana dariya ta gyada mata kai.

    Babu shi a parlor din sanda suka shiga,saita cewa mimi

    “Bari na duba shi a daki” ta gyada kai yarinyar ta zauna saman kujera cikin zaquwa.

    A nutse ta tura qofar dakin,daidai lokacin da yake zaune cikin sofa bed din,ya kwantar da bayansa sosai a jikin sofa din,idanunsa da suka rusuna ya daga yana kallon fuskarta sanda ta tsaya daga bakin qofar tana riqe da handle din tana kallonsa kamar yadda shima.ya zuba mata ido,duk sai taga kamar ya sauya daga zuwansu bauchin.

    Hannunsa ya daga yayi mata nuni da tazo,ta saki qofar ta soma takawa a hankali kamar mai tausayin qasa,ya zuba mata ido yana jin nutsuwa tun gabanin ta iso gareshi.

    Hannunsa ya bata sanda ta iso kusa dashi,ta saka nata hannun a ciki,sai ya fincikota cikin jikinsa a tausashe,ya mata kyakkyawan masauki a qirjinsa,yasa labbansa masu taushi yayi kissing goshinta,sai ta dan saki ajiyar zuciya

    “Mimi na rako zata nuna maka kwalliyarta” ta fada a shagwabe kamar yadda ta saba yi masa magana,birkitota kadan yayi yana kallon fuskarta

    “Ina taki kwalliyar…..ita tafi muhimmanci” kunya ta kamata ta sauke fuskarta a qirjinsa tana shaqar daddadan qamshinsa

    “Banfa yi wanka ba,aiki na gama yi,gurin duk yayi qura” girarsa ya dage sama duka biyun

    “Iyyee,abun ‘yar haka ne?,shine kika share iya wajenki banda nawa ko?” Kai ta girgiza da sauri tana ‘yar dariya

    “Ba haka bane uncle,nasan mummy hafsat ta gyara maka fa” kai kawai ya jinjina

    “Yanzu yaushe ne za’a yimin kwalliyar,ta musamman nakeso,i will pay” dariya ta saki,tanajin dadin yadda yake yaba komai nata

    “Za’a yi maka uncle” ta furta tana rufe fuskarta da hannunta

    “That’s my baby doll” shima ya amsa mata yana jan dogon hancinta

    “Muje naga mimi’ ya sake fada yana dagata a jikinsa,gaba daya sai ya rasa kaso hamsin na bacin ransa, shigowarta kawai ya tafi da komai,ta miqe ya sanya hannunsa cikin nata ya riqe gam suka fara takowa xuwa falon.

    Babu irin abinda bata saqa a ranta ba sanda take tsaka da kukan,sai datayi me isarta sannan ta dauraye fuskarta,bata da wata mafita,komai ya tsaya mata cak,batasan me ya kamata tayi ba,saita dauki wayarta ta soma lalubar number anty ummee ko xata samu wasu shawarwari.

    Abun takaicin tana kira taji suna sanar mata kudinta ya qare,dama already taci bashin mtn na kusan dubu uku,duk kuwa da cewa duk wata sai abbas din ya saka mata kudin credit ta account dinta bama credit din ba,taja tsaki ta sauka ta koma bank dinta ta sakawa layin bashin da suke binta,bonus din da suka bata tayi amfani dashi ta kira anty ummee din.

    Shuru tayi har ta gama bayaninta sannan ta dora

    “Ina tsoron kada yarinyar nan ta fara shiga rayuwarsa anty ummee,ni zuwan nan da sukayi ma sai naga kamar ta fara budewa ta zama mace,harda kai mata kayanta sashenta fa,duk da na sanshi bashi da girman kan wannan wa iyalinsa,amma yarinyar ai bata cancanci wannan kulawar ba” baki anty ummee ta tabe,tana jin kamar ta jawo hafsat din tayita jibga

    “Nidai da farko saidai nayi miki addu’ar Allah ya yaye miki wannan baqar qazantar,bansan irin ribar da kike samu da ita ba” maganar ta bata ran hafsat,don duk yadda kake da ita kace mata qazama ce to sai an ganku a rana

    “Meye haka anty ummee?,nifa ba akan wannan na nemi shawararki ba,tunda dai ni ina iya bakin qoqarina,abubuwane sukeyimin yawa,kuma nayi nayi ya daukon mai aiki yaqi,to bazan kashe kaina ba” kai anty ummeen ta jinjina,gwara ta bita a yadda suka soma,kada ta yiwa kanta rasa rasa

    “Ke gaskiya ce baki so,na daina kuma gaya miki,amma indai kansa kike san shawowa dole kidan gyara inda idanunsa zasu ganki tsaf,tunda da tsafta aka jarabceshi ke kuma ea qazanta…..muddin kinason ganin dai dai dole ki sauko daga ra’ayinsa kibi nasa ko yaya ne,koni da kikaga ina yadda nakeso,wasu abubuwan ra’ayinsa nake bi kafin na murda idan naga ya biyu yadda nakeso na koma kan nawa ra’ayin” sun dan dauki lokaci suna fafatawa ma kafin hafsat ta fahimci abinda anty ummee take nufi,dole ta yarda tadanyi gyara a ranar ko zata cimma manufofinta ta ruwan sanyi.

    Suna gama wayar ta miqe tana tunanin ta inda zata fara,sai ta yanke ta shiga da kanta ta kira widad din,can qasan ranta tana mamakin yadda ko motsinta bata sake ji ba bare ta shigo taga abinda ya kamata tayi mata.

    Tun bata qarasa ba taga sassan nata a kulle,ta juya cike da mamakin ina taje?,ko gidan hajiyan da aka rufe babinsa ta koma?,harta dawo da baya…..amma tana kallon sashen abbas din akalar tunaninta ya canza,saita nufi can,duk da zuciyarta na gaya mata bata ciki,to amma mafi rinjaye na tunaninta yana rinjayarta ga zuwa sashen nasa.

    Tana buda qofar falon abbas dake riqe da hannun widad yana bude ta bedroom din,idanunsa na kallon gefansa yana magana da widad din,cak hafsat din ta tsaya kamar an dasata,qirjinta yana harbawa,ta zuba masa ido tana son ganin waye yake biye dashi.

    Wani mugun ashar ne taji ya taso mata,saidai abinda yazo ya tsaya mata a wuya ya hana kowanne kalma fita daga bakinta,widad fa take gani,widad yau a dakin mijinta?,riqe da hannunsa?,baqar zuciya da kuma fushin dake cin zuciyarta ya sanyata cikin zafin nama ta harbo zuwa cikin falon.

    Takunta yaja hankalinsa sanda yake tsokanar mimi tayi kyau,ya tashi daga durquson da yayi,ya zuba mata idanu,don kallo daya yayi mata zuciyarsa ta bashi akwai wani abu na daban.

    Kafin ta qaraso idanunsu suka sarqe cikin na juna,wani irin baiwar idanu gareshi masu tsananin kwarjini,abinda yayi mata tasiri kenan,kallonsa ya ratsa zuciyarta ya karya duk wani zafi data debo da kima qissime qissime da zuciyarta keyi mata na irin abinda zata aiwatar,saurin data kwaso ya canza zuwa nawa.

    Kallon kallo suka ci gaba da yiwa juna,sai taji zuciyarta kamar zata fashe idan bata ce komai ba,a sannan ta tuna ita din me laifi ce,ta kuma tuna gargadin da anty ummee tayi mata

    “Kissa saida kwantar da kai”maganar data gaya mata ta qarshe kenan

    “Nace me za’a dafa maka?” Ta maye gurbin dukka wani bala’i daje qasan zuciyarta da wannan tambayar,tambayar da yaji sam bata dace da yanayin da ya ganta a ciki ba,to amma koda ta tambaya dinne da gaske,yanajin ya zuwa yanzu ya kamata ya nuna mata fushinsa,saiya dauke idonsa daga kanta ya maida kan ‘yarsa

    “Bana buqatar komai” ya amsa mata a dake yana duqawa yana gyarawa mimi kwalar rigarta.

    Wasu irin hawaye ne masu dumi suka cika mata idanu,ta zubawa widad ido,wadda sam idanunta baya wajen,ta tattareshi akan tv,haka kawai takejin wani irin itama cikin ranta, yanayin gidan a yau ya sake mata rashin dadi,ta tabbatar a lokaci irin wannan a kaduna ita dashi din suna kitchen tare suna girki,ko suna backyard dinsu suna wankin undies,ko suna karatu ko kallo.

    Qwafa taja can qasan ranta tana danne hawayen,batason ta zubdashi a gaban widad din,ta juya tana barin falon,kamar zatayi bindiga ta fashe haka takejin kanta,nadama da dana sanin ma tambayarsa me za’a girka din ya cika Zuciyarta,gashi ya yarfata a gaban qaramar yarinyar da a haife ta haifeta.

    Hanyar data fita yabi da kallo,yaja dan qaramin tsaki sannan ya koma ya zauna kusa da mimi

    “Hadamin coffee ko black tea” ya bata umarni yanason danne shima nasa fushin,tadan kalleshi da wani irin yanayi,cikin zuciyarta takejin akwai wani abu dake damunsa,don ba haka yake ba,kamar zatayi magana saita fasa,ta miqe tana nufar qofa.

    Tana sanya qafarta a falonta taji an biyo bayanta,ta tsorata sosai,taja da baya tana dubanta,sai data gane hafsat dince saita saki ajiyar zuciya tana lumshe idanunta hadi da budesu tana kallonta.

    Wani irin kallo take bin widad dashi,tana jin kamar ta fincikota ta rufeta da duka,yarinya qarama amma tana neman dagula mata lissafi,tanaji a jiki da zuciyarta abbas ya sake canzawa ne sosai ta sanadin aurenta,a baya idan ya fiya cika masa ciki tattarawa yake ya koma inda ya fito,sanda suna gari guda kuma saidai ya tsiri zaman gidan hajiya,ko kadan bata damuwa,saboda tasam ba wani wajen yaje ba,kuma shi din ba mai kula kulen mata bane,asalima sam basa cikin tsarinsa,don haka ba kasafai ta fiya damuwa,idan ya qare fushinsa zai dawo yaci gaba daci abincinsa ko yaya ta dafa kuwa,idan yaji bai masa bama zai shiga kitchen ya dafa da kansa
    (Hmmmm,duk a lokacin bata taba kawowa miskilanci bane irin na mijinta,ta aza hakan akan babu yadda zaiyi da itane,kamar dole yayi duka abinda yakeyi din).

    “Uban me kika shiga yi dakin abban mimi” kamar daga sama furucin yazowa widad,mamaki ya kamata,for now dai ta fahimci matsayinta daya da hafsat din,ta kuma fahimci me kalmar aure take nufi,indai haka ne bataga muhallin wannan tambayar ba,duka wannan ba damuwarta bane,abinda yafi bata mata rai kalmar UBAN WA data fada,wanda dai dai yake da zagi a wajenta

    “Dake nake!” Ta sake fada cikin tsawa kamar zata kai mata duka,amma ga mamakinta sai taga widad din ta tsireta da manyan idanunta

    “Ai ba haramun bane tunda kema naga kina shiga” ta fada a sakalce abunta tana dubanta.

    Zallar mamaki ya saukowa hafsat din,tayi sakato tana kallonta

    “Ni kike gayawa wannan maganar?” Ta fadi tana jin wani zafi har cikin ranta

    “Me nace mommy?” Ta tambayeta kanta tsaye,a karo.na biyu ta sake shiga mamaki,anya kuwa?,anya abinda take tunani bai faru ba?,yaushe yarinyar tabfara fahimtar abubuwa haka?.,da tayi wani qaramin tunani sai tabar wancan maganar tace

    “Ki wuce kije kiyi aikinki,suna can suna jiranki”

    “Tom,bari na dafawa uncle tea” tea?,har tea yake sakata dafa masa saboda zallar jawo mata raini?,wanne girki ta iya da zai buqaci tea daga wajenta

    “Ni kike.maidawa magana widad?” Juyowa tayi tana kallon hafsat din,ita gana daya sai taji ta sire mata daga zuciyarta,tunda ta fahimci akwai qaryayyaki da yawa data taba gaya mata,a dabi’arta kaifi daya ce,ko meye za’a yi mata bata qarya haka ta taso tun quruciyar ta,dalilin da ya sanya ta sake shan wahala kenan sosai a wajen ‘yan uwanta da cousins dinta

    “Me nayi mommy?,aikinsa shine gaba da kowanne aiki fa,ba kyau miji ya saka kaqi” zuwa lokacin gaba daya hafsat din ta gama sarewa,lallai qaryarta ta fara qarewa,tund har yarinyar ta fara sanin ma’anar kalmar miji,ta kuma fara tantance bin umarnin wata a gaba da nata umarnin,basu taba musayar magana da ita ba koda da sau daya,amma yau da ita suke musu?,tana ce mata ga yadda za’a yi itama kuma tana fadin nata,ah wannan babbar musifa da babbar guguwar canji ce ta tunkarota,wadda take buqatar zama na musamamn da shawarwari don sanin meyenmatakin dauka na gaba,daga wannan sai bata sake cewa komai ba,ta juya tana barin wajen tana jin kamar duniyarta tazo qarshe gaba daya.

    Tsakin da batasan yazo bakinta ba shi ta fitar,tadan harari hanyar data wuce din

    “Kawai kawai ni….”sai kuma tayi shuru tana quna quni,ita tunda taga yadda taketa wani tsare mata uncle dinta da kallo taji tana jin haushinta,bata taba ma kula da haka take zuba masa ido ba sai yau din,haka ta shiga kitchen din,ta fara duba kayan hada tea din da tasan yana matuqar so ta fara hada masa,lokaci lokaci tana dan jan tsaki.[3/19, 5:42 PM] +234 808 711 8630: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)
    *Arewabooks:Huguma*

  • Arubuce Ta Ke 89

    Arubuce Ta Ke 89

    Page 89

    Sallama yayi sannan yayi shuru na wasu seconds

    “Okay’ taji yace,ya sauke wayar yana sakin ajiyar zuciya sannan ya kalli widad

    “Baby…..ina zuwa” kawai sai taji ranta yayi mata babu dadi,a sanyaye ta gyada kai,ya sunkuya a hankali yayi kissing goshinta sannan ya fice.

    Tashi tayi ta tattara kayan abincin da ya gama ci,ta gyara wajen sannan ta dawo saman kujera ta kwanta tana maida idanunta ga tv,saidai kuma fiye da rabin hankalinta yana kan abbas,ko yaya taji motsi sai ta daga kai taga ko shine.

    Tun tana kallon agogo da marmari har ta sare,tun tana danne zuciyarta har ta kasa ta fara sharar hawaye ganin sha daya ga sha biyu itama ta gota an tafi qarfe daya na dare,saita fashe da kuka tana curewa cikin kujera,tsoro haushi da takaici hadi da baqinciki suka mamayeta,me yasa uncle zaiyi mata haka?,daga cewa gashinan yanzu yanzu?.

    Hada kai da gwiwa tayi tsakanin cinyoyinta ta saki kuka sosai,zuciyarta na wani irin tafasa,ya tafi wajen mummyn mimi ya barta ita kadai?,bayan shi yayi mata alqawarin a nan zai kwana yau.

    Tun tana kukan da qarfinta har ta soma jin babu dadi,zuwa uku na dare kukan ya isheta ita kanta,a hankali kuma wani wahalallen bacci mai hade da bacin rai ya dauketa nan cikin kujerun falo.

    Cikin mamaki yake saka kanshi cikin falon,wayam babu kowa,sai tarkacen kwanukan da suka gama cin abinci da sauran datti wanda dama falon baya rabo dashi,haka ya dinga tsallake shirgi har yakai qofar dakinta.

    Yana murda handle tana sakin wani irin nishi,abinda ya sanyashi buda qofar da dan hanzari ya saka kai ciki.

    Male male ya sameta,kwance qasan tiles tana juyi daga wannan bangon zuwa wancan,tana ganinsa ta dago masa hannu,idanunta jagab da hawaye.

    “Subhanallah” ya fada yana qarasowa da sauri inda take kwancen,ya saka hannu yana dagota,gaba daya jikinta sharkaf yake da gumi,ya dorata saman cinyarsa yana tambayarta

    “What’s going on?,me yake damunki?”

    “Cikina abban mimi……cikina zai fashe…..wayyo Allah” ta sake fada da qarfi tana wani irin murdewa.

    “Relax,ya isa” ya fada yana riqe hannunta dake saman cikin nata

    “Mutuwa zanyi,mutuwa zanyi,ciwo yakeyimin” ta sake fada tana riqeshi da kyau

    “Ba abinda zai sameki,ki nutsu,bari na fiddo mota sai mu wuce asibiti” gan ta riqe hannunsa cikin nata

    “Don Allah kada ka tashi,wallahi kana fita zan iya mutuwa”

    “Just a minute……yanzu zan dawo,saina kira widad ta kwana da yaran kafin mu dawo” kai ta jijjiga masa tana fashewa da kuka

    “Don Allah nidai kada ka tafi,ka mayar dani kan gado,sanyin wajen nan kamar zai fasamin qashi” duk yadda zai motsa ta hanashi,ko waya da yakeson kira taqi bari,haka ya miqe ya dauketa ya azata saman gadon,tana ajjiyeta ta kanainaiyeshi da hannuwanta tana ci gaba da matagugun ciwo.

    Da qyar ta bari ya saka hannu ya kade shimfidar gadon saboda datti datti da yake ji akai,ya jawo mata pillow dinta da pillow case din ta gaji da haduwa da dattin dauda,sai tasa hannu ta kare

    “Ka barni a jikinka please,ina samun relief” ta fada tana hawaye,hakanan ya zauna jingine da makarin gadon yana fatan ta samu sauqi,duka hankalinsa akan agogo yana mamakin yadda lokaci yaja haka,widad na ransa,ya dauki wayarsa ya fara kiran layinta.

    Har wayar ta qaraci ringing dinta ba’a dauka ba,ya sake kira nan ma ba’a daga ba,ya danji relief,saboda ranshi ya bashi cewa bacci ne ya dauketa.

    Jin shuru abun ya lafa sai yadan motsa da nufin sa mata pillow yaje ya duba yaran ya wuce sassansu,ji yayi tayi caraf ta riqeshi,cikin kuka kuka tace

    “Yanzu ba zaka iya zama dani ba daddyn mimi?” Tayi maganar tana sake riqeshi d kyau

    “Ya isa shikenan,yara zan duba,kuma.nabar qanwarki batasan me ake ciki ba” banza tayi taci gaba da sharba kukanta kamar ma bataji abinda yace ba.

    Duka duka baccin minti arba’in yayi aka qwala kiran sallar asuba,ya zame jikinta ya kwantar da hafsat dake baccinta sosai,har ya buda toilet dinta yaji bazai iya shiga ba,ya koma ya buda dakin yaran.

    Sai daya duba lafiyarsu sannan ya shiga nasu bandakin dake da sauqin qazanta yayi alwalar ya wuce masallaci idanunsa akan sassan widad.

    Tun kiran sallar farko ta tashi,ta farka tana sauke ajiyar zuciya na kukan data sha,ta kalli agogo saiga wasu hawayen,ranta ya motsu qwarai,kawai sai ta miqe ta wuce dakinta tana jin bacin rai yana cikata.

    Alwala ta daura,ta dawo cikin dakin ta jawo akwatinta guda daya ta fara sauke kayanta kaf tana lodawa a ciki,tana yi tana sharar qwalla,itakam yau ta gama kwanan bauchi.

    Akwati biyu ta shirya cike da kaya,ta jawosu falo sannan ta koma dakin tayi sallah,sai ta shiga wanka kawai,bayan ta fito ta shirya cikin atamfa dinkin riga da skert,ta zabi hijabin daya dace da atamfar jikinta ta dawo falon riqe dashi tayi zaune kusa da akwatunta tana share qwalla lokaci bayan lokaci,jiran shigowarsa kawai takeyi.

    A gurguje ya kammala azkar dinsa ya baro masallacin,gaba daya hankalinsa yana kan widad din,key dinsa yayi amfani dashi ya bude qofar falon,ya tura a hankali yana mamakin ganin qwan wutar falon a kunne

    “Subhanallah” ya fadi sanda yayi tuntube da akwatin widad,sai yaja baya yana kallon akwatunan guda biyu dake maqare da kaya,sannan ya maida dubansa ga widad din.

    Fuskarta a dinke tsaf,sai qananun qwalla da take sharewa,ta dauke kanta daga gareshi gaba daya,sam taqi yarda su hada ido,ya fahimci laifi ya tafka a jiyan,kuma da alama laifin babba ne a wajenta,ya zube hannayensa a aljihun rigar jikinsa yana qare mata kallo gami da sakin murmushi,wata qauna da soyayyarta mai kaifi tana hudashi,sai ya fara takawa a hankali zuwa gabanta.

    Yana isa ya tsugunna saman qafafunsa yana qoqarin leqa fuskarta,amma kuma ta hana hakan faruwa,mamakin hawayen dake kwance saman fuskarta ya kamashi

    “Is that serious?,kuka take da gaske?” Ya tambayi kansa

    “Assalamualaikum” ya fada a tausashe,amma maimakon ta amsa saima hade rai data sakeyi tana share qwallar dake kwarara

    “Ya salam,baby kuka kuma?” Shuru nan ma tayi masa

    “kinga,ya isa,yi shuru ki gayamin menene?” Sai ya miqa hannunsa a nutse ya kamo hannuwanta,saita zame hannuwan nata ta fashe da kukan da take dannewa

    “Ba kai bane, kayimin alqawari,shine kuma ka tafi can ka kwana”

    “Ya salam……kishi?” Ya tambayi kansa cikin mamaki hadi da tsareta da idanu,saidai kuma wani abu mai sanyi na kwarara cikin zuciyarsa

    “He won…….ta fara sonshi” ya bawa kansa amsa yana jin duniyarsa na cika da farinciki,ya gyara tsugunnon da yayi a gabanta zuwa zama sosai yana sake kama lallausan hannunta

    “it was not intentionally…….naje na sameta bata da lafiya ne,i called you ki duba wayarki” sam ji tayi bata nutsu ba,gaba daya garin ya gama fice mata aka,sai ta sake zame hannuwanta

    “Ni tafiya zanyi” ido ya fidda cikin fargaba,ya kuma tambayeta cikin hanzari

    “Ina?”

    “Kaduna,bazan sake kwana a nan ba” ta fadi tana sake sakin kuka.

    Ajiyar zuciya ya sauke yana kama kunnuwansa da kyau

    “Am sorry please forgive me”

    “Allah ni tafiya zanyi,bazan sake kwana a nan ba”.

    Duk yadda zaiyi yahi mata akan tayi haquri su qarasa weeknd dinsu amma ta tubure tace sam,itafa a yanzun saiya shirya sun wuce,daga bisani yace mata ta bari zuwa yammaci nan ma ta tubure masa,sam taqi zama suyi magana da nutsuwa da fahimta dashi,gaba daya ta birkice masa,saiya sauke ajiyar zuciya yana kallonta yadda take kuka riris,zuciyarsa na wani irin suya,kukanta a yanzun shine abu.mafi girma da zuciyarsa bata qaunar ji,ba kuma zata iya jurewa ba,sai ya sanya hannu ya jawota cikin jikinsa yayi mata kyakkyawar runguma yana shafa bayanta a hankali cikin sigar lallashi.

    Da qyar yadan shawo kanta ta tsaida kukan,dole ya soma hada kayansa sannan ya wuce toilet ya fara shiri.

    Ta bangaren hafsat kuwa yau ranta fes ta tashi,anty ummee ce mutum ta farko data soma kira ta zayyana mata komai,sunci dariya abinsu kamar ba gobe

    “Na gaya miki indai zaki iya jura wannan yarinyar juyata ba wani babban aiki bane,nawa take gaba dayanta?,da kanta zata ja qafafunta ta koma gidan ubanta”.

    Sun jima suna hira da ita sannan sukayi sallama,tanaso tadan sake gyarawa kodon abbas din amma kuma tana tunanin idan tayi hakan kamar zaiyi saurin dago plan dinta,don haka ta narke taci gaba da kwanciyar ta.

    Tsaf ya gama shiryawa yau din cikin qananun kaya,trouser da shirt na kamfanin Armani masu asalin tsada da aji,ya waiwaya a hankali cikin kamewa da nutsuwa ya dubi widad da har yanzun ranta yake a hade,suna hada ido ta sake dauke kai,dariya ta taso masa,ya saki qaramin murmushi yana girgiza kai

    “Am done qanwata” kalmar qanwar tawa daya fada ta sakata waiwayowa tana kallon idanunsa,dama abinda yake da muradi kenan,abinda kuma yayi kewa kenan,ya lumshe idanunsa tsigar jikinsa na zubawa,yayi missing nata har baisan adadi ba

    “Zan iya zuwa nayi sallama dasu mimi?” Ya fada da wata kasalalliyar murya,saita gyada kanta a hankali,har ya taka zuwa gaba ta bude baki a hankali

    “Kada kuma ka sake zama irin ta jiya” cak ya tsaya yana dariya qasa qasa,wow……at her age amma ta iya kishi haka?,what if idan ta sake girma da wayo?,haka yayi gaba yana murmushi shi daya bayan ya amsa mata da

    “Yes ma’am I will be back quickly” cikin ransa yana raya girman mulki irin na diya mace,banda haka widad din da ya haifeta amma kai tsaye take bashi command,kamar ba shine ke bawa manyan zaratan police order ba kuma subi cikin hanzari da gaggawa

    “Mace ta wuce haka” wata zuciyar ta raya masa,ya jinjina kai yana sake sallamawa lamarin mata.

    Da murmushin da ya jima bai gani ba saman kuncinta ta tarbeshi

    “Ina kwana?” Ta gaidashi tana kallonsa da kyau,yayi mata kyau over,sai taji wani kishinsa yana ratsata,abbas din ba daga nan ba,mutum ne mai wani irin class da iya ado da gayu,ko yaya ne sai ya dauki hankalinki idan yayi kwalliya,sassanyan qamshinsa ya cika dakin gaba daya

    “Lafiya alhmdlh,ya jikin naki?” Sai ta sake sakin murmushi tana cewa

    “Da sauqi,naji dadin jikin”

    “Ma sha Allah,Allah ya qara lafiya”

    “Ameen” ta bashi amsa tana ci gaba da qare masa kallo

    “Su nawwara fa?”

    “Basu tashi ba……kayi kyau daddynsu” da dan mamaki ya kalleta,don kalma ce baquwa a kunnensa da bakinta,har widad da tazo daga baya bayanta ta fita iya fadinta,har baisan adadin sau nawa ita din ta fada ba

    “Thank you,na gode”

    “Amma wannan kwalliyar da safen nan fa?” Gyara tsaiwarsa yayi,don gaba daya bayajin dadin wanzuwarsa cikin dakin,iskar da take kaikawo a dakin bata masa ba at all

    “Inajin zamu wuce Kaduna ne” cikin mamaki ta qanqance ido

    “Kaduna kuma fa kake cewa,yanzu yanzu?” Yasan dole sai taja magana,bai kuma san sanda zasu gama ba,don haka ya taimaki kansa ya matsa window din dakin ya yaye labulen ya kuma bude glasses din Windows din ya bawa iska damar shigowa,kafi ya gama aikin ya amsa mata ta sake sakin qorafi,har qasan zuciyarta bata gamsu da wannan tafiyar ba ta gaggawa irin haka

    “Amma dai gaskiya daddynsu wannan tafiyar……kalli fa qarfe nawa gaba daya?”

    “Uzuri ne na gaggawa ya taso,so dole a tafin yanzu” shuru ta danyi har zuwa sanda ya ajjiye mata dukka kudaden da ya saba aje mata idan zai tafin,sukayi sallama tana daga kwance bata motsa ba,ya saba da wannan idan da sabo,don haka ba wani damuwa ya wuce dakin yaran,sunta bacci ya tofa musu addu’a ya fito,ga mamakinsa sai ya sameta zaune hannun kujera a falo,ta dubeshi sannan tace

    “Muje na rakaka mota” baice komai ba ya juya yayi gaba tabi bayansa.*H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)
    *Arewabooks:Huguma*

  • Arubuce Ta Ke 81

    Arubuce Ta Ke 81

    Page 81

    Kamar ko yaushe a harabar gidan ya cimma yaran,sunata wasan qasa sunyi futu futu dasu,qasa har saman kansu,amma hakan bai hanasu murnar ganin juna ba,ya tsugunna ya kwashe abinsa sunata masa surutu yana kerbewa.

    Dab da zai shiga sashen nata ta fito,sanye da atamfa dinkin doguwar riga,tayi daurin ture kaga tsiya,duka gashinta da ba kasafai ta fiya son kitso ba ya fito abinsa ta qasan daurin,hannun brassiere dinta daya fito ta kafadarta ya sake muzanta shigar tata,atamfar anko ce da sukayi biki tun shekaran jiya,kuma tun shekaran jiyan take jikinta bata cire ba,sam batayi tsammanin zuwansa a yau din ba,shi yasa ta saki jiki ya sheqi baccinta,bata jima da tashi ba ta biyo sahun su mimi jin shuru ba motsinsu tun dazun.

    Tare hanya tayi tana masa sannu da zuwa hadi da karbar jakar hannunsa,bata son ya shiga sashen nata,saboda ita kadai tasan irin badaqalar daya kwasa ba,don hatta da uniform din mimi yana zube a falon da school bag harma da tsadajjen lunch box dinta daya siya mata

    “Mu qarasa sashen naka,dama fitowar da nayi gyarawa zanje nayi” ta fada tana sake kankane hanyar.

    Bai musa mata ba,don a yadda takeyin din yasan zancan gizo baya wuce na qoqi,bataso ya shiga yaga ba dai dai ba ya gyara mata ko yayi mata fada,ko shi din yasan idan ya shiga babu lallai ya samu sashen a yanayin da zai iya zama,so no need ya matsa sai ya shiga din,don haka ya juya da yaran suka wuce sashen nasa.

    Tun daga qofa yaga abinda aka saba,a yau dinma sashen nasa babu gyara,yadda ya barshi kusan wata guda haka yake a yanzun,sai ya basar,ya ajjiye yaran ya zauna shima saman kujerun falon,ta yiwa jakarsa mazauni sannan ta juya tana kallonsa

    “Bari na fara dora maka wani abun sai nazo na gyara nan din” manyan fararen idanunsa ya daga ya kalleta

    “No,a bani abinda kuka dafa kawai da rana”.

    Da sauri tadan kalleshi,sannan cikin yanayi na rashin gaskiya tace

    “Ba zaka iya ci ba,infact ma inajin sun cinye…..”

    “Eh daddy,indomie ce mommy ta dafa mana,kuma saida nawwara ma tace tana jin yunwa s……” Yarinyar bata qarasa ba saiji kake fafff ta doke mata baki,take kuwa bakinta ya fashe

    “Shegiyar maganar tsiya,muna magana uban waye ya sako bakinki a ciki?” cikin bacin rai abbas ya kama leban yarinyar yana dubawa,sai da ya gama ganin iya wajen da ya fashe din,ya goge mata wajen ya dorata kan cinyarsa yana lallashi sannan ya dubeta cikin bacin rai

    “A gabana zaki fasawa yarinyata baki?,kece me abun duka ba ita ba,amma waye ga dakeki?,na rantse da Allah kinyi na farko kinyi na qarshe,bance kada ki hukuntasu ba,amma ba ta irin wannan hanyar ba”.

    Ranta ya baci sosai,ta dinga jefawa yarinyar harara,tanason bata mata budget gaba daya,amma tasan maganinsu,tattarasu zatayi kaf kwanakin wajen widad.

    Saboda tana da plan sai bata tanka masa ba,illa bata fuska sosai data yi,ta juya tana ficewa daga sassan ranta a bace.

    Kai tsaye ta nufi sassan widad,gwara ta fito da ita tun yanzun ta kama mata ayyukan,saboda yau aikin nata suna da yawa,ko gyaran sassansa zuwa abuncinsa aiki ne babba a wajenta,ga nata sashen da tasan zaici tsintsiya ruwa da klien,saidai tun kafin ta qarasa taga kaman babu mutum a sassan,kasa gasgata idanunta tayi,ta dinga ganin kamar gizo,har dai data taba qofar,takuma yi knocking taji shuru.

    Sak tayi,ta tsaya yana jinjina kanta,baizo da ita bane?,ko kuma ta wuce gidan hajiyarsa yadda ta tsiri wannan iskancin wani lokacin?,bata da amsa,don haka sai ta wuce sassanta,ta dauki wayarta ta kira muneera.

    Tambayar farko tace mata gatacan ita da hajiya a falo suna hira,ta zuqi iska ta fesar,lallai kan yarinyar ya fara wayewa,ita za’a mayar ‘yar iska?,aqalla wata guda da wani abu kenan bata saka yarinyar a idonta ba,ko zuwanta na qarshe kwana guda kwata kwata tayi a gidan suka koma.

    Sake fitar da iska me zafi tayi daga bakinta,maganganun anty ummee suka dawo mata,ai kuwa ba zata bari hakan ta faru ba,tare ta karantawa yarinyar karatun manya,dole tabi da ita,dole tabi hanyarta,dole ne kuma ta fara gane banbancinta da ita,sai ta fara dora abinci sannan ta kwashi kayan shara ta wuce sashen nasa tana sake saqa abubuwa da yawa da take da shirin aiwatarwa.

    *_W A S H E G A R I_*

    Karfe goma na safiya ya fito tsaf dashi,cikin lallausan yadin filtex na maza mai asalin kyau da tsada,komai yana yinsa ne a wani kasalance da rashin kuzari,duk kuwa da cewa a jiyan ya samu yadda yakeso daga hafsat din,to amma sai yakejin wani irin mugun banbanci mai tazarar yawa,banbancin da zai iya kiransa kwatankwacin nisan dake tsakanin sama da qasa,gaba daya ma zai iya cewa wani irin bacci yayi mara dadi cije da kewar widad din,duk juyin da zaiyi sai ya dinga ganin kamar itace a gefansa,amma dole ya tattara dukka wadan nan ya danne can qasan zuciyarsa da qarfin gaske gudun shiga hakkin me hakki.

    Yana daura links a hannunsa tayi sallama ta shigo dakin,hannunta dauke da plate din data soya plantain wadda ta qone tayi baqi abinta,yadan bita da kallo kadan,tana nan gayanta,bayan wankan ibada da tayi kafin sallar asuba babu wani abu data qara,koda da turare kuwa,wanda zuwa yanzu zamansa da widad hancinsa ya saba da shaqarsa.

    Yana yiwa turare wani mugu mugun so,amma ita nata ra’ayin sunyi hannun riga da ta’ammali dashi,sai randa ranta yaso,ko kuma aka taki sa’a ranar tana da ra’ayinsa.

    “Fita zakayi kenan” ta fada tana zama gefan gadon da har yanzu ta kasa gyarashi,don tuni dama yayi sallama da kwana a sashenta

    “Eh,akwai wani abu?” Ya fada yana takawa gaban mudubi,ya dauki cup din coffe din da yace ta hado masa dashi yakai bakinsa.

    “Aah,inason zuwa gidan hajiya ne” dire mug din coffe din yayi saman madubin bayan daci ya ziyarci bakinsa,sannan ya zarce da dubanta yana nazarinta.

    A ka’idarta zaiyi wahala taje gidan hajiyan haka siddan,shi yasa maganar ta bashi mamaki ko a yanzun ma,amma taqi yarda ta kalleshi bare ya karanto gaskiyar abinda ke cikin zuciyarta,har ya gama kallonta,ya jawo qonanniyar plaitain din ya fara kokawa da ita

    “Saikin dawo” ya amsa mata daga baya,yana tsame hannnunsa daga plate din,yaja tissue yana goge maiqon daya bata masa hannu.

    Sarai taga yadda ya cakali abincin,abu na farko da ya kamata tayi taji dalilin da yasa bai maida kai yaci ba,tunda fita zaiyi,amma inaaaa,ba wannan bane a gabanta,sai kawai ta kwashe kwanukan bayan fitarsa,ta hada da kudin cefanen daya ajiye mata,duk da babu abinda zasu siya,ta soke a lalitarta,sannan ta shiga bandaki tahau shiryawa a gurguje,don tana da tabbacin zaiyi wuya idan ba gidan hajiyan ya nufa ba,tanason kuma ta cimmasa a can ayita ta qare.
    [3/18, 4:01 PM] +234 813 343 4840: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)
    *Arewabooks:Huguma*