Arubuce Ta Ke Hausa NovelHausa Novels

Arubuce Ta Ke 89

Sponsored Links

Page 89

Sallama yayi sannan yayi shuru na wasu seconds

“Okay’ taji yace,ya sauke wayar yana sakin ajiyar zuciya sannan ya kalli widad

“Baby…..ina zuwa” kawai sai taji ranta yayi mata babu dadi,a sanyaye ta gyada kai,ya sunkuya a hankali yayi kissing goshinta sannan ya fice.

Tashi tayi ta tattara kayan abincin da ya gama ci,ta gyara wajen sannan ta dawo saman kujera ta kwanta tana maida idanunta ga tv,saidai kuma fiye da rabin hankalinta yana kan abbas,ko yaya taji motsi sai ta daga kai taga ko shine.

Tun tana kallon agogo da marmari har ta sare,tun tana danne zuciyarta har ta kasa ta fara sharar hawaye ganin sha daya ga sha biyu itama ta gota an tafi qarfe daya na dare,saita fashe da kuka tana curewa cikin kujera,tsoro haushi da takaici hadi da baqinciki suka mamayeta,me yasa uncle zaiyi mata haka?,daga cewa gashinan yanzu yanzu?.

Hada kai da gwiwa tayi tsakanin cinyoyinta ta saki kuka sosai,zuciyarta na wani irin tafasa,ya tafi wajen mummyn mimi ya barta ita kadai?,bayan shi yayi mata alqawarin a nan zai kwana yau.

Tun tana kukan da qarfinta har ta soma jin babu dadi,zuwa uku na dare kukan ya isheta ita kanta,a hankali kuma wani wahalallen bacci mai hade da bacin rai ya dauketa nan cikin kujerun falo.

Cikin mamaki yake saka kanshi cikin falon,wayam babu kowa,sai tarkacen kwanukan da suka gama cin abinci da sauran datti wanda dama falon baya rabo dashi,haka ya dinga tsallake shirgi har yakai qofar dakinta.

Yana murda handle tana sakin wani irin nishi,abinda ya sanyashi buda qofar da dan hanzari ya saka kai ciki.

Male male ya sameta,kwance qasan tiles tana juyi daga wannan bangon zuwa wancan,tana ganinsa ta dago masa hannu,idanunta jagab da hawaye.

“Subhanallah” ya fada yana qarasowa da sauri inda take kwancen,ya saka hannu yana dagota,gaba daya jikinta sharkaf yake da gumi,ya dorata saman cinyarsa yana tambayarta

“What’s going on?,me yake damunki?”

“Cikina abban mimi……cikina zai fashe…..wayyo Allah” ta sake fada da qarfi tana wani irin murdewa.

“Relax,ya isa” ya fada yana riqe hannunta dake saman cikin nata

“Mutuwa zanyi,mutuwa zanyi,ciwo yakeyimin” ta sake fada tana riqeshi da kyau

“Ba abinda zai sameki,ki nutsu,bari na fiddo mota sai mu wuce asibiti” gan ta riqe hannunsa cikin nata

“Don Allah kada ka tashi,wallahi kana fita zan iya mutuwa”

“Just a minute……yanzu zan dawo,saina kira widad ta kwana da yaran kafin mu dawo” kai ta jijjiga masa tana fashewa da kuka

“Don Allah nidai kada ka tafi,ka mayar dani kan gado,sanyin wajen nan kamar zai fasamin qashi” duk yadda zai motsa ta hanashi,ko waya da yakeson kira taqi bari,haka ya miqe ya dauketa ya azata saman gadon,tana ajjiyeta ta kanainaiyeshi da hannuwanta tana ci gaba da matagugun ciwo.

Da qyar ta bari ya saka hannu ya kade shimfidar gadon saboda datti datti da yake ji akai,ya jawo mata pillow dinta da pillow case din ta gaji da haduwa da dattin dauda,sai tasa hannu ta kare

“Ka barni a jikinka please,ina samun relief” ta fada tana hawaye,hakanan ya zauna jingine da makarin gadon yana fatan ta samu sauqi,duka hankalinsa akan agogo yana mamakin yadda lokaci yaja haka,widad na ransa,ya dauki wayarsa ya fara kiran layinta.

Har wayar ta qaraci ringing dinta ba’a dauka ba,ya sake kira nan ma ba’a daga ba,ya danji relief,saboda ranshi ya bashi cewa bacci ne ya dauketa.

Jin shuru abun ya lafa sai yadan motsa da nufin sa mata pillow yaje ya duba yaran ya wuce sassansu,ji yayi tayi caraf ta riqeshi,cikin kuka kuka tace

“Yanzu ba zaka iya zama dani ba daddyn mimi?” Tayi maganar tana sake riqeshi d kyau

“Ya isa shikenan,yara zan duba,kuma.nabar qanwarki batasan me ake ciki ba” banza tayi taci gaba da sharba kukanta kamar ma bataji abinda yace ba.

Duka duka baccin minti arba’in yayi aka qwala kiran sallar asuba,ya zame jikinta ya kwantar da hafsat dake baccinta sosai,har ya buda toilet dinta yaji bazai iya shiga ba,ya koma ya buda dakin yaran.

Sai daya duba lafiyarsu sannan ya shiga nasu bandakin dake da sauqin qazanta yayi alwalar ya wuce masallaci idanunsa akan sassan widad.

Tun kiran sallar farko ta tashi,ta farka tana sauke ajiyar zuciya na kukan data sha,ta kalli agogo saiga wasu hawayen,ranta ya motsu qwarai,kawai sai ta miqe ta wuce dakinta tana jin bacin rai yana cikata.

Alwala ta daura,ta dawo cikin dakin ta jawo akwatinta guda daya ta fara sauke kayanta kaf tana lodawa a ciki,tana yi tana sharar qwalla,itakam yau ta gama kwanan bauchi.

Akwati biyu ta shirya cike da kaya,ta jawosu falo sannan ta koma dakin tayi sallah,sai ta shiga wanka kawai,bayan ta fito ta shirya cikin atamfa dinkin riga da skert,ta zabi hijabin daya dace da atamfar jikinta ta dawo falon riqe dashi tayi zaune kusa da akwatunta tana share qwalla lokaci bayan lokaci,jiran shigowarsa kawai takeyi.

A gurguje ya kammala azkar dinsa ya baro masallacin,gaba daya hankalinsa yana kan widad din,key dinsa yayi amfani dashi ya bude qofar falon,ya tura a hankali yana mamakin ganin qwan wutar falon a kunne

“Subhanallah” ya fadi sanda yayi tuntube da akwatin widad,sai yaja baya yana kallon akwatunan guda biyu dake maqare da kaya,sannan ya maida dubansa ga widad din.

Fuskarta a dinke tsaf,sai qananun qwalla da take sharewa,ta dauke kanta daga gareshi gaba daya,sam taqi yarda su hada ido,ya fahimci laifi ya tafka a jiyan,kuma da alama laifin babba ne a wajenta,ya zube hannayensa a aljihun rigar jikinsa yana qare mata kallo gami da sakin murmushi,wata qauna da soyayyarta mai kaifi tana hudashi,sai ya fara takawa a hankali zuwa gabanta.

Yana isa ya tsugunna saman qafafunsa yana qoqarin leqa fuskarta,amma kuma ta hana hakan faruwa,mamakin hawayen dake kwance saman fuskarta ya kamashi

“Is that serious?,kuka take da gaske?” Ya tambayi kansa

“Assalamualaikum” ya fada a tausashe,amma maimakon ta amsa saima hade rai data sakeyi tana share qwallar dake kwarara

“Ya salam,baby kuka kuma?” Shuru nan ma tayi masa

“kinga,ya isa,yi shuru ki gayamin menene?” Sai ya miqa hannunsa a nutse ya kamo hannuwanta,saita zame hannuwan nata ta fashe da kukan da take dannewa

“Ba kai bane, kayimin alqawari,shine kuma ka tafi can ka kwana”

“Ya salam……kishi?” Ya tambayi kansa cikin mamaki hadi da tsareta da idanu,saidai kuma wani abu mai sanyi na kwarara cikin zuciyarsa

“He won…….ta fara sonshi” ya bawa kansa amsa yana jin duniyarsa na cika da farinciki,ya gyara tsugunnon da yayi a gabanta zuwa zama sosai yana sake kama lallausan hannunta

“it was not intentionally…….naje na sameta bata da lafiya ne,i called you ki duba wayarki” sam ji tayi bata nutsu ba,gaba daya garin ya gama fice mata aka,sai ta sake zame hannuwanta

“Ni tafiya zanyi” ido ya fidda cikin fargaba,ya kuma tambayeta cikin hanzari

“Ina?”

“Kaduna,bazan sake kwana a nan ba” ta fadi tana sake sakin kuka.

Ajiyar zuciya ya sauke yana kama kunnuwansa da kyau

“Am sorry please forgive me”

“Allah ni tafiya zanyi,bazan sake kwana a nan ba”.

Duk yadda zaiyi yahi mata akan tayi haquri su qarasa weeknd dinsu amma ta tubure tace sam,itafa a yanzun saiya shirya sun wuce,daga bisani yace mata ta bari zuwa yammaci nan ma ta tubure masa,sam taqi zama suyi magana da nutsuwa da fahimta dashi,gaba daya ta birkice masa,saiya sauke ajiyar zuciya yana kallonta yadda take kuka riris,zuciyarsa na wani irin suya,kukanta a yanzun shine abu.mafi girma da zuciyarsa bata qaunar ji,ba kuma zata iya jurewa ba,sai ya sanya hannu ya jawota cikin jikinsa yayi mata kyakkyawar runguma yana shafa bayanta a hankali cikin sigar lallashi.

Da qyar yadan shawo kanta ta tsaida kukan,dole ya soma hada kayansa sannan ya wuce toilet ya fara shiri.

Ta bangaren hafsat kuwa yau ranta fes ta tashi,anty ummee ce mutum ta farko data soma kira ta zayyana mata komai,sunci dariya abinsu kamar ba gobe

“Na gaya miki indai zaki iya jura wannan yarinyar juyata ba wani babban aiki bane,nawa take gaba dayanta?,da kanta zata ja qafafunta ta koma gidan ubanta”.

Sun jima suna hira da ita sannan sukayi sallama,tanaso tadan sake gyarawa kodon abbas din amma kuma tana tunanin idan tayi hakan kamar zaiyi saurin dago plan dinta,don haka ta narke taci gaba da kwanciyar ta.

Tsaf ya gama shiryawa yau din cikin qananun kaya,trouser da shirt na kamfanin Armani masu asalin tsada da aji,ya waiwaya a hankali cikin kamewa da nutsuwa ya dubi widad da har yanzun ranta yake a hade,suna hada ido ta sake dauke kai,dariya ta taso masa,ya saki qaramin murmushi yana girgiza kai

“Am done qanwata” kalmar qanwar tawa daya fada ta sakata waiwayowa tana kallon idanunsa,dama abinda yake da muradi kenan,abinda kuma yayi kewa kenan,ya lumshe idanunsa tsigar jikinsa na zubawa,yayi missing nata har baisan adadi ba

“Zan iya zuwa nayi sallama dasu mimi?” Ya fada da wata kasalalliyar murya,saita gyada kanta a hankali,har ya taka zuwa gaba ta bude baki a hankali

“Kada kuma ka sake zama irin ta jiya” cak ya tsaya yana dariya qasa qasa,wow……at her age amma ta iya kishi haka?,what if idan ta sake girma da wayo?,haka yayi gaba yana murmushi shi daya bayan ya amsa mata da

“Yes ma’am I will be back quickly” cikin ransa yana raya girman mulki irin na diya mace,banda haka widad din da ya haifeta amma kai tsaye take bashi command,kamar ba shine ke bawa manyan zaratan police order ba kuma subi cikin hanzari da gaggawa

“Mace ta wuce haka” wata zuciyar ta raya masa,ya jinjina kai yana sake sallamawa lamarin mata.

Da murmushin da ya jima bai gani ba saman kuncinta ta tarbeshi

“Ina kwana?” Ta gaidashi tana kallonsa da kyau,yayi mata kyau over,sai taji wani kishinsa yana ratsata,abbas din ba daga nan ba,mutum ne mai wani irin class da iya ado da gayu,ko yaya ne sai ya dauki hankalinki idan yayi kwalliya,sassanyan qamshinsa ya cika dakin gaba daya

“Lafiya alhmdlh,ya jikin naki?” Sai ta sake sakin murmushi tana cewa

“Da sauqi,naji dadin jikin”

“Ma sha Allah,Allah ya qara lafiya”

“Ameen” ta bashi amsa tana ci gaba da qare masa kallo

“Su nawwara fa?”

“Basu tashi ba……kayi kyau daddynsu” da dan mamaki ya kalleta,don kalma ce baquwa a kunnensa da bakinta,har widad da tazo daga baya bayanta ta fita iya fadinta,har baisan adadin sau nawa ita din ta fada ba

“Thank you,na gode”

“Amma wannan kwalliyar da safen nan fa?” Gyara tsaiwarsa yayi,don gaba daya bayajin dadin wanzuwarsa cikin dakin,iskar da take kaikawo a dakin bata masa ba at all

“Inajin zamu wuce Kaduna ne” cikin mamaki ta qanqance ido

“Kaduna kuma fa kake cewa,yanzu yanzu?” Yasan dole sai taja magana,bai kuma san sanda zasu gama ba,don haka ya taimaki kansa ya matsa window din dakin ya yaye labulen ya kuma bude glasses din Windows din ya bawa iska damar shigowa,kafi ya gama aikin ya amsa mata ta sake sakin qorafi,har qasan zuciyarta bata gamsu da wannan tafiyar ba ta gaggawa irin haka

“Amma dai gaskiya daddynsu wannan tafiyar……kalli fa qarfe nawa gaba daya?”

“Uzuri ne na gaggawa ya taso,so dole a tafin yanzu” shuru ta danyi har zuwa sanda ya ajjiye mata dukka kudaden da ya saba aje mata idan zai tafin,sukayi sallama tana daga kwance bata motsa ba,ya saba da wannan idan da sabo,don haka ba wani damuwa ya wuce dakin yaran,sunta bacci ya tofa musu addu’a ya fito,ga mamakinsa sai ya sameta zaune hannun kujera a falo,ta dubeshi sannan tace

“Muje na rakaka mota” baice komai ba ya juya yayi gaba tabi bayansa.*H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)
*Arewabooks:Huguma*

Leave a Reply

Back to top button