Author: Novels

  • Arubuce Ta Ke 98

    Arubuce Ta Ke 98

    Page 98

    “Matsa daga gurin nan hafsa tun raina bai baci ba” ya sake fada cikin kausashiyar murya,shammatarsa tayi sai kawai ga hannunta jikin widad,ta shaqeta sosai tana dura mata ashar,kai zaka dauka mahaukaciya ce sabon kamu.

    Cikin qasa da second biyu,cikin wani irin bacin rai fushi da kuma qarfin hali itama widad ta shaqetan

    “Ya salam” abbas din ya fada da qarfi yana kama hannun hafsat ya fincike daga jikin widad,sannan ya janye widad din gefe yana riqe da hannunsa tsam cikin nata

    “Wuce cikin gida tun kafin raina ya gama baci!” Ya fada a tsawace

    “Bazan wuce ba,ba inda zani, wallahi wallahi yau saina koyawa yarinyar nan hankali don ku****mar ubanta,ni za’a dinga rainawa hankali ana cin amanata?”

    “Ba ubana kike zagi ba,naki kika zaga wallahi” widad ta fada cikin bacin rai,tana jin kamar abbas ya saketa ta sake komawa kan hafsat din.

    Sake yunqurawa tayi a zafafe jin raddin da ta mayar mata

    “Ni kike gayawa haka?,ka barni nayi mata dan banzan dukan da ba zata sake magana ba” kafin ta qaraso ya buda qofar bayan sashensa ya sanya widad wadda itama takeson qwacewa ya maida qofar ya rufe sannan ya juyo yana kallon hafsat da idanunsa da suka canza launi saboda bacin rai,ranshi a mugun bace yace

    “Ki shiga hankalinki, banason rashin mutunci da hauka”

    “Nice mara mutunci?,nice kuma mahaukaciya?,ai dole ka fadi haka,kun hada kai kuna cin mutuncina,kuna cin amanata,Allah ya isa wallahi ban yafe ba,Allah ya isa na” ta fada da qarfi,saidai……tun kafin ta kammala rufe bakinta ya kwasheta da wani kyakkyawan mari a kuncinta.

    Cak wuta ta dauke mata,yayi mata mugun ba zatan da bata taba tunanin zai iya aiwatar wa ba,itace yau abbas ya daga hannu ya mara saboda widad?

    “Stupid!” Ya fada yana huci,wani irin fincikar jikinta tayi tana dosar qofar

    “Wallahi yau sai na daketa naga abinda zakayi” dab da zata qarasa ya isa gabanta yana nuna mata hanya,amma burinta ta qarasa ta bude qofar ta fiddo widad

    “Ka matsa ka bani waje azzalumi kawai”

    “Kibar wajen nan hafsa na gaya miki”

    “Saina shiga,saina shiga azzalumi” wani lafiyayyen marin ya sake sauke mata hagu da dama,gaba daya sai wuta ta dauke mata,taci burki tana kallonsa kamar wata zararriya riqe da kumatunta

    “Don kina iskanci da rashin mutuncinki kina ganin kamar bazan iya daukan mataki a kanki ba kin yaudari kanki,sassauci na da dauke kan da nake miki inason na zama mafi alkhairi ne ga iyalinsa,amma ke gaba daya tosashiyar kwanyarki ta kasa gano miki hakan,to wallahi wallahi kinyi na farko kinyi na qarshe,bazanci gaba da dauka ba,ki bacemin daga wajen nan tun ban bi ta kanki ba!!!” Ya fada da wata irin rugugin tsawa,ba hafsat dake tsaye a wajen ba,hatta da widad dake daga cikin falon saida cikinta ya juya, tsoron sosai ya kamata,ta koma ta zauna saman daya daga cikin kujerun dake dab da qofar,karin farko da taji sautin fushi da bacin rai daga gareshi kenan.

    “Ko meye zaka ce, kuma ko me zakayi bazan fasa fadin cutata da kakeyi da cin zarafina ba,yarinya qarama ta mallakeka sai yadda tayi dakai,sai abinda tace,kanata zalunta ta,bazna yafe ba wallahi,sai Allah ya sakamun,kai da ita dukanku bazan yafe muku ba” cikin fushi ya sake daga hannu sai kuma idanunsa suka sauka kan cikinta,ya janye hannun yana qoqarin hadiye fushinsa,bai taba dora hannu a kanta ba sai yau,sai ya kama hannunta ya saita mata hanya yana gaya mata cikin tsawa ta bace masa a wajen.

    Jinta take kamar ba’a tsaye take saman qafafunta ba kamar akan iska take haka ta juya ta fara barin wajen, hannunta har yanzu akan kuncinta,idanunta na malalar hawaye masu zafi da quna,yau ita abbas ya mara?,wannan shine mummunan abun tarihi na farko daya faru a iya zamansu da ba zata mance dashi ba.

    Ido ya zuba mata cikin fushi har ta bace a wajen,sannan ya juya ya bude qofar,wanda tuni widad dake zaune saman kujera ta miqe tana dakon isowarsa,saidai zuwa yayi ya wuceta abinsa yana wani irin huci,kaman zai zauna akan kujera amma sai ya kasa,ya dinga kai komo widad din tana kallonsa tana kuka qasa qasa

    “Shut up” ya fada mata da wata irin tsawa data sakata qanqame jiki waje daya hadi da runtse idanunta,bayason jin kukanta ne kwata kwata,tana qara hasala masa zuciyarsa ne ba tare data sani ba,a cikin yanayin da yake kuma a yanzun bazai iya lallashinta ba,sai kuma ya koma ya zauna bayan ya sakar mata tsawar,jikinsa yana mutuwa,qaramin sautin kukanta yana sake ratsa falon.

    Kusan minti talatin suna a haka,ta kasa shuru shi kuma ya kasa lallashinta,sai da suka doshi minti arba’in sannan ya miqe ya fice,ba jimawa ya dawo dauke da hijab dinta da wayarta ya miqa mata,sannan ya isa gaban freezer dinsa ya ciro ruwan gora mai sanyi ya bude ya miqa mata,tasa hannu ta karba tana satar kallonsa,idanunsa ba’a kanta yake ba,wani gurin daban yake kalla,sai takai ruwan bakinta ta fara sha,ya fara sauka cikin cikinta yana ratsa qirjinta dake suya,yana kuma rage mata radadin da takeji.

    Kusan rabi tasha sannan ta miqa masa,sai ya sake saka hannu ya karba ba tare daya kalleta ba,bakinsa yakai ya shanye sauran yana yin gaba,ya cillar da robar yana cewa

    “Wuce muje” bayansa tabi ba tare da tasan ina suka nufa ba,motar sa ya bude tun kafin su qarasa da remote control,ya isa seat din gefan driver ya bude mata ta shiga ya mayar ya rufe,sannan ya zagaya shima nasa bangaren ya shiga ya tayar da motar suka bar gidan.

    Lamo tayi cikin motar,ta kwantar da kanta a makarin kujerar tana ‘yar sheshsheqar kuka,idonsa ya dinga runtsewa,sautin kukanta yana qonashi da yawa,basarwa ya dinga yi yana zaton zai iya daurewa amma sai ya kasa,tausayinta ya lullubeshi,yadan daki kan motar,sai ya gangara gefan hanya yayi parking ya juyo sosai ya zuba mata ido yana hadiye bacin ransa da qyar

    “Why widad…..why…….me yasa kika biye mata?” Idanunta dake jiqe da hawaye ta daga ta kalleshi

    “Amma uncle…..itace ta fara fa” kai ya jijjiga

    “Na sani,amma kina zaton zan tsaya ne a wajen ina kallo ta cutarmin dake?” Kai ta kada a hankali alamun a’ah

    “So kike ki koyi irin abinda takeyi?,kinaso na daina samun walwala gaba daya?” Kai ta girgiza nan ma sabuwar qwalla na sauko mata

    “Kayi haquri uncle……am sorry” a hankali ya lalubo hannunta da hannunsa guda daya ya hadesu waje daya yana hadiye wani bacin rai daya tsaya masa

    “Am sorry too baby,na miki tsawa,it was not intentionally…….hankalina ne a tashe,raina a bace,banason kema ki koma wani abu daban”

    “Bazan sake ba uncle” ta kuma fada hawaye na sake balle mata

    “Kina qonani baby doll,kina qona zuciyata,ki daina wannan kukan” ya fadi yana kamo fuskarta cikin hannunsa,tare da zaro handkerchief dinsa ya soma goge mata fuskar cikin wani irin salo na tausasawa da nuna zallar qauna,hausawa sukance gaida mai gaidaka ko bazai amsa ba,ko meye zai mata idan tana cikin bacin rai bai fadi ba,widad ce kadai ke fahimtar ransa a bace yake ko yana fushi,saita tabbatar tayi abinda zai samu sassauci kota saukeshi daga fushinsa,duk da kusan ba itace sila ba.

    Saida suka shiga unguwar ta fahimci gidan hajiya ya kawota,bashi da wani solution illa hakan,saboda yasan kwana zatayi kuka ita kadai,babu lallai ta saki jikinta,a nan ne kawai zata sake tayi baccinta.

    Mamaki ya kama hajiya lokacin data gansu tare,baice ma hajiyan komai ba ya barta a nan ya koma setting room din qofar gidansu suka shiga meeting din da suka shirya yi din.

    Itama batace komai da hajiyan ba,saidai hajiya ta fuskanci sanyi jiki kadan tattare da ita,tanata kallon widad din,canzawar da tayi tayi yawa,ta kasa cinyewa wannan karon bayan sun gama meeting din ya shigo gidan,widad din ta tafi kawo masa abincin da bai samu ci ba tace dashi

    “Anya abbas ba juna biyu yarinyar nan take dashi ba?” Ido yadan lumshe yana sakin qaramin murmushi,hasaso ‘yar rigimar tashi da ciki kawai yakeyi,inda hakan zata kasance da yafi kowa farinciki,amma fa yasan daru ne za’a shashi

    “Banjin haka hajiya”

    “Bata amai bata yawu,ba zazzabin dare?” Dan jim yayi sannan ya girgiza kansa

    “Babu hajiya”

    “To ma sha Allah,Allah ya kawo nagari masu albarka”

    “Ameen ameen” ya fada cikin dan jin nauyi.

    Muneera ya nema yace ta gyara daki daya widad din zata kwanta a ciki,ba jimawa muneera ta gyara din,don dama ba dakin da hajiyan ke barinsa da dauda.

    Yana zaune ta wuce dakin,hajiya tace taje ta kwanta,taga kamar tana alamun bacci a idanunta,ta yima hajiya sai da safe,ta juyo zata masa sallama suka hada ido,sai ta basar tace

    “Sai da safe”

    “Allah ya bamu alkhairi” ya amsa ta yana binta da kallo,inda suna kaduna waye zai shiga tsakaninsu a irin wannan lokacin,kaf rayuwarsa yana qaunar dare yayi,saboda lokacine da zai rabi jikinta sosai ya kuma kwana yana jin duminta hadi da shaqar tattausan qamshinta.

    “Ba yanzu zaka wuce bane” hajiya ta tambayeshi ganin goma da rabi na neman gotawa,agogo ya kalla sannan yadan dubi hajiyan

    “Wannan program din nake jira su gama saina wuce” ya bata amsa yana maida dubansa ga tv din,saidai a zahiri gidan ne baya qaunar komawa,idan ya tuna abinda hafsat din tayi sai yaji ransa ya baci,yana so ya sake hucewa ne kafin yakai ga shiga gidan,bayason komawa da zafinsa shaidan ya ingizashi ya yanke mummunan hukunci.

    “To bari na shiga na kwanta nidai” sukayi sallama da hajiyan,amma yace idan ya gama zai wuce zai mata magana.

    Ido yabi hajiyan dashi har ta shige daki,sai yayi zumbur ya miqe yana zuba hannuwansa a aljihun rigarsa ya wuce dakin widad.

    Tunda ta shiga dakin tana kwance ne kawai amma bacci bai zowa idanunta ba har sannan,har yanzu zuciyarta a bace take kan abinda hafsat din tayi mata,tunda take ba’a taba yi mata makamancin abinda hafsat din tayi mata ba,gaba daya kimarta babu ita a idanunta,duk wani sauran mutunci nata da take gani a yanzu babu shi,to me tayi mata da har take yunqurin dukanta?, tabbas inda ta dora hannunta a kanta babu abinda zai hanata ramawa kowa kuwa gemunta na jan qasa ne saboda girma da shekaru,tunda ai bataga abinda tayi mata ba.

    Sallamarsa tasa ta daga idanunta zuwa fuskarsa,ta zuba masa ido na wasu sakanni,haka kawai taji tausayinsa ya kamata,tausayin da batasan na meye ba,ya tako a hankali zuwa gaban gadon,sai ya matsa jikin switch na fankan yana rage gudun fankan dakin,sannan ya dqwo gefan gadon ya zauna yana cewa

    “Wannan iskan ai tayi yawa”

    “Zafi nakeji” ta fada muryarta qasa qasa,ya waiwayo yana dubanta cikin mamaki,don garin a sake yake da iska, baice komai ba yakai hannunsa jikinta ya taba,da gaske gumi takeyi,sai yasa hannu ya dagota gaba daya yana zare mata rigar jikinta,ya barta daga ita sai farar vest me siririn hannu, idanunsa suka sauka a qirjinta da suka cika suke a tsaye kyam,sai tayi hanzarin jan bargo zuwa qirjin nata ta koma da sauri ta kwanta tana boye fuskarta.

    *H A F S A T*

    Kuka ta zauna tana yi sosai kamar zata fidda zuciyarta,ba zafin marin ne yafi damunta ba,wadda aka mareta ta sanadinta ne damuwarta,hannun abbas yau da yakai fuskarta ya daketa saboda widad din?,takai ta kawo,ta kasa zama tana jin kamar abinda yake cikinta zai fito a yau.

    Tana tsaka da wannan taji tashin motarsa,da sauri ta daga labulenta tana leqensa har ya fice, zuciyarta ta dinga qissima mata abubuwa da yawa,shi da waye?, abinda yafi tsaya mata a rai kenan,sai kawai kuka ya qwace mata,ta dauki wayarta da hanzari ta danna wa mamanta kira,tana jin baqinciki kamar zai kasheta,ba zata iya hadiyar wannan bacin ran ita kadai ba.

    Ashar mamanta ta dinga zundumawa

    “Saboda baisan darajarki da mutuncinki ba?,cikin daren nan,da tsohon ciki a jikinki zai kamaki ya daka?”

    “Ni umma anya wannan hanyar tana aiki kuwa?”

    “Bana shakka akai,saidai kice wani abu da ya kawo tasgaro ya faru,amma koma meye ki daga waya ki gayawa uwarshi abinda yayi miki,yadda yasa kika tasheni a bacci itama ki tasheta” akan wannan suka rabu,ba tare da wani dogon tunani ba kuwa ta laluba number hajiya ta kirata.

    Dai dai lokacin da dattijuwar ke saman abun sallah tana shafa’i da wuturi taji qarar waya

    “Subhanallah” ta furta bayan ta gane number wadda ke kira,tabbas matsala ce ta faru ta tabbatar,don ba zata iya tuna sanda taga kiran hafsat din a wayarta haka siddan ba tare da komai na matsala ya faru ba.[3/22, 9:37 PM] +234 813 343 4840: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*

  • Arubuce Ta Ke 93

    Arubuce Ta Ke 93

    Page 93

    Widad kuwa sabgarta take a sassanta,don ko leqowa batayi ba bare ma su hadu,su mimi suna wajenta,sukaci lafiyayyen abincinta suka qoshi,daga qarshe ma bacci a nan ya dauki mimi,nawwara kawai ya dauka sanda yazo yi mata saida safe,tace yabar mata mimi din ta kwana a nan.

    Uwar bata wani damu ba,a lokacin kawai kallon raguwar hidimarsu bisa wuyanta takeyi,bayan ta kwantar da nawwara ta cimmasa a bedroom,ya gama shirinsa cikin kayan bacci,sassanyan qamshinsa ya cika dakin,yana zaune yana amsa waya hankalinsa kwance,saita bude closet dinsa ta duba doguwar riga cikin kayan baccin da yakan ajjiye a dakin,ta tube rigar lace din jikinta ta aza kayanta tayi fuska,babu batun sake wanka,tunda dai an tsira da wankan safe,ta dawo ta zauna,lokaci lokaci tana kallonsa har ya gama wayar ya aje yana dubanta

    “Ya akayi?” Ya fada yana kallonta, don yasan halinta,ungulu ce bata jewar banza,zaman da tayi lallai akwai magana a bakinta

    “jari nake buqata ka bani,jari na yayi qasa” yana daga kwancen yake kallonta,ya rasa me takeyi da kudi,ashana baya barin mace ta siya masa,ko yaushe cikin tura mata kudi yakeyi,suttura har wardrobe dinta baya rufuwa saboda yawansu kuma gashi ba sanyawa akeyi ba,hakanan ba bayar dasu akeyi ba,bata taba cikakken sati ba tare data nema kudi a hannunsa ba,sai ya lumshe idonsa sannan yace

    “Kamar nawa?”

    “Fice hundred thousand only”

    “Only?” Ya maimaita zancanta na qarshe,ba tare da ya jira amsarta ba yace

    “Allah ya hore” wani kallo tayi masa sheqe qe,amfanin da zatayi da kudin ta gama kasafta zasu fita ne a jikinsa,don ba zata iya fiddasu daga cikin kudinta ba,amma zaizo mata da wannan zancan

    “Allah ya hore,saidai idan ba zaka bayar bane?” Miqewa yayi ya zauna sosai yana kallonta cikin idanu

    “Kullum me yasa babban burinki da jin dadinki ki kawo sabani a tsakaninmu?,me yasa zaman lafiya baya miki dadi?” Maganganunsa sai taji kamar gugar zana yake mata,take ta cika tayi fam ta fara zubda maganganu

    “A hakanne banason zaman lafiya?,duk da tarin haqurin da nakeyi kai baka gani ba?,ina cewa makaranta ka maida waccan yarinyar kana kashe mata kudi,ko ka dauka bansan private ka kaita mai tsada ba?,itama taci kudinka ballantana ni,ita din da duka duka kwananta nawa a rayuwarka,duk kawaicina baka ganshi ba kenan tunda ni dama a wajenka babu abinda na iya na alkhairi”

    Ido ya maida ya rufe kamar me shirin bacci,saidai ba baccin zaiyi ba,yana sauraren bugun zuciyarsa ne da duk bugawa take bugawar da zallar qaunar yarinyar tare da ambato sunanta,she means alort to him,batasan wace widad cikin rayuwarsa ba,yana dai qoqarin dannewa ne kawai,bai baiwa soyayayyarta kaso daya cikin goma damar fitowa ba saboda kada ya bada kafar barna ko baraka a tsakaninsu,a wannan yanayin yasan duk bayanin da zaiwa hafsat din a banza,ba zata fahimceshi ba sam,idan idanunta suja rufe kan abu kamar cin qwan makauniya,burinta kawai ayi mata abinda ranta yakeso,yana jinta tana ci gaba da zayyano dalilai marasa tushe bare makama,da ya gaji da jinta sai ya miqe tsam kawai ya dauki pillow ya yada a qasa ya kwana abinsa,abun da ya sake tunzurata kenan,ta miqe ta cire rigar baccin jikinta ta maida rigar lace dinta data cire,ta buda qofar tayi ficewarta,yadan bude idanunsa a hankali yabi bayanta da kallo harta fice,sai ya gyara kwanciyarsa yana rufe idanunsa,sam baiji wata damuwa ba don ta fita din,tun yana tunane tunane har bacci yayi gaba dashi.

    A ranar kwanan kuka tayi ta godewa Allah,gaba daya tsanar widad ta gama cika mata zuciya,abubuwa da yawa basa faruwa saita sanadin zuwanta,gaba daya ta hargitsa mata gida ina dalili?,cikin ranta da zuciyarta takejin matakin data dauka shine dai dai, hukuncin data yanke kuma yayi dai dai,domin a yanzun babu wani abu da zai saurin sadata zuwa ga cimma burinta idan ba ta wannan hanyar ta biyo ba.

    Washegari widad din ta shirya ita dasu mimi,tun da safe tayi musu wanka,ta cire kaya cikin wadanda abbas a taho musu dashi ya manta su cikin kayanta tayi musu kwalliya da kyau suka wuce gidan hajiya.

    Taji dadin ganinsu matuqa,ta rasa inda zata sanyasu,a nan akayi mata jan lalle har bayan hannunta,hatta hajiya sai data yaba, idanunta na buye da Widad din tana ji a ranta anya ba juna biyu widad din ke dashi ba?, quruciya ta hanata ganewa,shi kuma uban gayyar hankalinsa baikai ba?,amma da yake hajiyan bata cika sanya baki a lamuran surukanta ba duk da tana jin widad sosai cikin ranta,kamar diyar data haifa a cikinta,duk da haka sai tayi shuru,cikin ranta ta bisu da addu’a.

    Da yamma tace masa zata koma taje tayi girki,suna shirin tafiya sai gashi,tayi mamaki don bata tsammaci zaizo ya dauketa ba,haka kawai yaji duka gidan babu dadi bayan fitarsu,amma hakanan dai ya daure suka wuni da giwar tasa a haka😂,duk da babu abinda ya tsinta a zaman,don gaba daya babu fara’ar arziqi a tattare da ita bare hirar arziqi,to dama yaya lafiyar kura bare tayi hauka?.

    Tunda ya shigo shima yake binta da kallo,lallen ya sake fito da ita sosai,ya kasa daurewa har sai daya bita kitchen yasha dumin jikinta sannan ya samu nutsuwa,suka tattare sukabar gidan hajiyan suka wuce gida.

    Tare yau sukayi girki kamar yadda suka saba a Kaduna,gaba daya yau sai takejin kasala,har yana tsokanarta

    “Kindaiyi qiba baby kawai” saita hau bubbuga qafa

    “Niba wata qiba,Allah banaso” dariya mai taushi ya saki,ya dauketa cak ya dorata saman kantar kitchen din

    “Ni kuwa bakiga yadda kikayimin kyau ba,komai ya fito yadda nakeso…..fiye ma da yadda nakeso,sannan kin qara dad…….” Hannu tasa ta toshe masa baki,don tasan qaarshen zancan,kalmar tana matuqar bata kunya,amma taga shi kansa tsaye yake fadarta.

    A daren ya same tantancewa,ya kuma sake nutsuwa da gamsuwa da cewa Allah ne kawai ya dubi zuciyarsa ya bashi widad din a lokacin da bai shirya ba,zuciyarsa kuma bata taba kawo masa ya aikata hakan ba.

    *W A S H E G A R I*

    Tunda sukayi sallar asuba tace masa tana son zuwa saloon,daga can zata wuce gidan uncle muhsin,kallonta yayi

    “Baby…..salon yawo ko?,kinsan banason kina yawan fita,jiya me yasa baki gayamin an hada duka ba?” Kai ta langabe gefe,kwata kwata batason zaman gidan,sannan haka kawai takejin haushin hafsat duk sanda ta kalleta,shi yasa batason ma hada waje da ita,bare yau tasan can zai kwana,may be tana kallonsa zaua tafi can ya barta ita kadai a sassanta,sai mimi dake tayata kwana,ta narke fuska

    “Don Allah uncle,na dade fa banje ba” ido yadan zuba mata,sai kuma yadan saki murmushi

    “Shikenan” qanqameshi tayi tana fadin

    “Thank you uncle” ido ya lumshe yana murmushi,jikinsa na amsawa saboda yadda ta manna masa jikinta sosai,hannunsa yasa ya dagota yana duban qwayar idonta,kamar me rada yace mata

    “In dan qara?” zamewa tayi tana dariya hadi da boye fuskarta cikin hijabinta,duk sanda ya buqaci kadaicewa da ita a fargaba yake sakata,har yanzun bata saba da abun nan ba

    “Ni uncle….banason nayi ciki,mutuwa zanyi idan nayi ciki fa” ta fada a shagwabe,tattausan hannunta ya kamo ya riqe,duk da qarancin shekarunta amma yasan tana da matuqar juriya dashi,shi kansa baisan me yasa baya gajiya da ita ba

    “Bana gaya miki ba wannan abun ne yake sawa a samu ciki ba?,sai kinsha ruwa kin qoshi sosai idan aka gama shine ake samun ciki” kai ta gyada a hankali alamun gamsuwa,ya bita da kallo can qasan ransa yana danne dariyar daketa cinsa,yana mamakin yadda ta yadda da wannan dabarar daya shirya mata,quruciyarta tana bala’in tafiya dashi,wani abune da yake kallonsa na musamman tattare da ita,don tana debe masa damuwa sosai,tana barinsa a nishadi duk sanda ta tafka wani babbar wautar da quruciyar.

    Tada da himma sosai,duk da tana danjin kasala da nauyin jiki amma sai data gama gyara gidan tsaf,ta shirya breakfast sannan sukayi wanka,tare suke wanka daman,indai ba wani babban uzurin fita bane ya taso masa,wannan yasa suka gama da wuri ya rigata fita parlor ya fara yin break din,ita kuma tana ciki tana qarasa shiryawa.

    Cikin baqa wul din abaya mai wani irin aiki da stones masu sheqi ta shirya,wani irin kyau tayi mai daukar hankali saboda yadda abayar tabi lafiyayyar farar fatarta ta kwanta da kyau,ita kanta sai data kalli kanta har sau babu adadi,ta juya gaba da baya sannan ta rola mayafin sama kanta,ta dauki wata ‘yar mitsitsiyar hand bag mai hade da takalmi ta jefa wayarta a ciki sannan ta fito.

    Mug din da yayi niyyar kaiwa bakinsa ya sauke,ya bita da kallo tamkar yau idanuwansa suka saba ganinta

    “Ma sha Allah!” Ya furta yana kallonta,yana ji kamar ya buda zuciyarsa ya sanyata ya huta da radadin sonta da yake ji.

    Sama sama tayi break din,yanata tsokanarta da zumudin zuwa gidan uncle ya hanata cin abinci,suka fito tare

    “Bari na sallami antynki” ya fada yana buda mata motar ta shiga,sannan ya wuce sasssn hafsat din,tadan bishi da kallo saita dauke kanta zuwa gaban motar,ta jawo wani littafi ta soma buda shafukansa don ta ragewa kanta damuwar da take ta ji,da kuma wata irin faduwar gaba data tashi da ita tun dazun da safe.

    Suna zaune da yaran suna breakfast suma,wanda ba komai bane sai ruwan tea da tsurar bread,ya dauki yaran ya musu wasa yayi kissing dinsu sannan ya ajjiyesu,ta gaidashi fuska a cunkushe ya amsa mata,har batason kallonsa musamman idan ta tuna daga inda ya fito,wajen waye ya kwana,ya ajjiye mata kudi yadda ya saba,zai fita mimi tace ya tsayata zata gurin anty weedad

    “Antynku fita zatayi” jin haka yasa hafsat din tasha jinin jikinta kan tare zasu fita,don haka ta miqe sa nufin masa rakiya,abun yadan bashi mamaki don ba sabonta bane,amma.bai hanata ba,suka jero tare suka fito.

    Cikin jikinta taji kamar yana tahowa,ta daga kai sai ta hangosu a jere da juna,tashin farko taji wani abu ya tsaya mata a wuya ganin yadda suka jera din,ta maida dubanta kan fuskar hafsat din,wani haushinta ya cikata,saita dauke kanta ta mayar kan littafin tayi kamar bata gansu ba.

    Har suka iso wajen idanun hafsat din na kan widad,wani irin zafi me tsanani takeji a ranta game da yarinyar,kyan da tayi ya tsaya mata a rai,ta fito sakkk balarabiya,to amma tana samun sassauci ta wani fannin idan ta tuna gab take da yin maganin matsalarta,kowanne lokaci ne daga yanzu,don haka tayi masa a dawo lafiya tan juya zuwa ciki ranta yana mata suya da yadda yarinyar ta nuna halin ko in kula da ita,gaisuwar ma da take mata yau bata sameta ba,lallai ta yarda raini ne yake ci gaba da tsirowa a tsakaninsu,sai kuma ta saki wani irin murmushi tana jan qwafa

    “Zakisan ni ban sa’ar yinki bace yarinya” ta furta tana shigewa sassanta.
    [3/21, 3:59 PM] +234 813 343 4840: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)
    *Arewabooks:Huguma*

  • Arubuce Ta Ke 87

    Arubuce Ta Ke 87

    Page 87

    Wayar anty ummee ta sake kira cikin mugun rudani da tashin hankali tafara gaya mata yadda ake ciki,ita kanta abun ya bata mamaki sosai

    “Wannan maganar bata waya bace,ki daure ki cinye komai kiyi masa duk abinda yakeso,zuwa jibi in sha Allah zamu dawo daga bikin ‘yar yayar babansu khadija(mijinta),gaata in sha Allah da wurwuri zaki ganni,idan ban samu fita bama zan miki magana saiki shigo mu hadu.

    Wannan maganar ta tayar da hankalin hafsat din sosai,ganin jibi take tayi mata mugu mugun nisa

    “Don Allah ki katse bikin nan anty ummee,kizo mu samu mafita,ina cikin mugu yanayi,ji nake zuciyata ba zata iya dauka ba,kamar zata fashe nakejinta”

    “Indai bakiyi juriyar dana gaya miki ba kikace zakibi son zuciyarki to komai zai lalace miki ne” abinda tace da ita kenan.

    Tayita kwatanta yadda zata fuskanceshi da fuskar komai ba komai ba amma ta kasa,kwata kwata zuciyarta bata da irin wannan juriyar da jarumtar irin ta anty ummee din,ta gama cusguna ma rayuwarta kuma tayi masa abinda yakeso?,babu abinda idanunta ke hango mata sai sanda suke fitowa daga dakin,yau hannun abbas dinta ne cikin na wata macen?,turakarsa da duk duniya ita kadai tasan kalarta yau sai ga wata mitsitsiyar yarinya ta fito daga ciki?,wa yasan ma me suka aikata suka ajiye mata yarinya a falo?.

    Duk yadda ta juya ta kasa aiwatar da komai,kawai saita kulle kanta a dakin ita kadai,saqa da warwara ba irin wadda batayi ba akan yadda zata bullowa al’amarin,kota kan yaranta ba ma bata bi,suma yaran dawowar widad yasa basu sake nemanta ba,suna can wajenta,wadda bayan ta gama hada masa tea din ta koma yin wanka ta wuce dasu,ta sake yiwa nawwaran ma wanka,don ita kanta ba cikakkiyar tsafta a jikinta.

    Zamansa a sassan nasa sai zuciyarsa ta kasa jurewa rashin ganin gilmawarta,ta saba masa da qamshinta,girkinta da a yanzu duk duniya babu girkin da yakejin taste dinsa idan ka dauke na hajiyarsa bayan nata,ya dinga qoqarin danne xuciyarsa,don a qa’ida awannin na hafsat ne,bayason kuma ya fara sabawa jiki da zuciyarsa da aikata wani abu da zai jagoranceshi ga zamowa kasashen namiji mara adalci,dole yayi wanka ya shirya ya biya ta sashenta don a qalla cikin su biyun ya kamata wata a ciki tasan inda zashi kada a nemeshi,hafsat ya dace ya soma fadawa,amma yaci alwashin bazai shiga sashenta ba,zai mata horon da zata sake shiga hankalinta.

    Tana tsakiyar su mimi din suna assignment,ta dora abinci a kitchen,gown ce a jikinta na chiffon material butter color da zanen green flowers qananu

    “Zan fita amma bazan dade ba zan dawo” ya furta jikinsa na amsawa,don daga inda yake tsayen yana iya jiyo qamshinta mai dadi,ga kuma qamshin da sashen kansa yakeyi wanda ya cukude da qamshin girkinta.

    Marairaice fuska tayi tana kallonsa da farare sol din idanuwanta

    “Uncle…..don Allah kada ka dade” murmushi ya subuce masa, ya jinjina kai yana kallo labbanta

    “In sha Allah” kusan a tare sukayi masa a dawo lafiya,har ya isa bakin qofa yaji bazai iya wucewa ba,ta gama kashe masa jiki,yana qishirwar lausasan labban nan nata,sai yadan waiwayo ya mata sign din tazo.

    Miqewa tayi tana sakin murmushi,tana kaiwa bakin qofar ya jawota cikin labule yadda yaran ba zasu iya hangosu ba,baiyi wata wata ba ya mannata da qirjinsa yana sauke ajiyar zuciya,ya dago fuskarta yana dubanta,idanunsu suka sarqe waje daya,sai suka hau yiwa juna kallon kallo,cikin zafin nama ya hade bakinsu waje daya.

    Da qyar yayi controlling din kansa,ya zareta daga jikinsa yana sake kissing goshinta

    “Allah yayi miki albarka,take care” ya fada yana ficewa a hankali,sai ta kasa motsawa ta bishi da kallo,yayin da wani lafiyayyen murmushi ya dinga fita daga fuskarsa,yana ji a jikinsa kallonsa take,wannan dalilin ya hanashi waiwayo,don ya bata damar kallon nasa sosai yadda ranta yakeso,ya hangi wasu abubuwa sosai daga zuciyarta,wanda ba lallai ita din ta fahimci shigarsa rayuwarta ba.

    Sai data daidaita kanta sannan ta koma cikin yaran tana tana labbanta da yatsunta, batasan me yasa duk sanda yayi mata irin wannan abun take tsintar kanta a wani yanayi ba

    “Kema kin zama yar iska ko?” Ta tambayi kanta da kanta,sai ta bushe da dariya ita kadai,har yaran suna kallonta dukansu,mimi ta tambaya

    “Mene ne anty” dan zubawa yarinyar ido tayi har yanxu murmushin dake saman fuskar ta bai bace ba,sai ta kama kumatunta

    “Babu komai mimi,kawai inason daddy uncle….” Ta furta maganar ba tare data shirya ba.

    Farinciki ya kama yarinyar,ta washe bakinta tana dariya

    “Shima yace yana sonki” ido ta fidda

    “Yaushe?”

    ” rannan dinnan” murmushi ta kuma saki,tana juya maganar yarinyar a ranta,saita miqa mata pencil din sukaci gaba da rubutun,zuciyarta wasai cike da tunaninsa,abinda bata taba tsintar kanta a ciki ba akan wani halitta.

    Dole saboda yunwar cikinta ta fito ta shiga kitchen,ta fara tunanin me ma zata dafa musu?taja tsaki yafi a qirga,ta rasa dame zata fara,saita matsa ta window gaban window din kitchen din nata ta zugeshi saboda iska ta shigo.

    Tana gama budewar iska me dadi mai hade da wani hadadden qamshin abinci ya cika mata ciki,ta hadiyi yawu da kyau tana tunanin ta inda qamshi kala kala yau yake cika mata gida,tabi wajen da kallo tana qaramin nazari,sai ganinta ya tuqe a sassan widad.

    Gabanta yadan fadi,kada ya zamana yarinyar ke girkin dake bada irin wannan aroma din,kai ta kada,ko jikinta kunne ne ba zata yadda da haka ba,yarinyar da aka kawo ko ruwan zafi bata iya dafawa ba,yaushe akayi dare har garin zai waye ta iya girki haka?.

    Tun tana aikin tana basarwa har ta gaza,sai ta ajjiye abinda takeyi ta juyo ta baro sassan nata ta doshi sashen widad din,tana kusantar part din iska da kums hancinta suna tabbatar mata daga can ne qamshin abincin ke fitowa,sai tayi tsaye daga bakin qofa yatsanta a baki,ya akayi haka ta faru?,bata da abinda zatayi,dole haka ta juya ta koma gwiwa a sanyaye,amma kuma ta cika da mamaki tare dason gano yadda akayi haka ta faru.

    Tana girkin amma gaba daya tunani ya cika mata kanta,ranta a jagule yake,bata qaunar ganin wani ci gaba sauyi ko walwalar rayuwa daga yarinyar gaba daya.

    Sallama taji da muryar mimi,a mamakance ta waiwayo tana kallon yarinyar

    “Mommy kizo inji daddy”

    “Ke…..waye ya koya miki sallama?” Daria ta saki cikin jin dadi

    “Anty amarya ce,tace duk inda za’a shiga sai anyi sallama,ba kyau shiga guri idan ba’a yi sallama ba” haushi takaici da kuma baqinciki suka cikata,wanne irin sanabe ne haka za’a fito mata dashi akan diyarta,sai taha qwafa

    “Shi kuma me zanyi masa,har ya gama fushin nasa ne?” Ta fada tana kallon yarinyar kamar itace zata bata amsa,ita dai batace komai ba,sai taja tsaki ta kashe gas din ta fito zuwa dakin baqi da tace yana can.

    Tunda tayi sallama taga kawunta gabanta yayi mummunar faduwa,saboda tasan cewa lallai ruwa baya tsami banza,ta saci kallon abbas dake zaune daura da kawun nata suna taba hira,wadda duka akan abinda ya shafi security na qasa ne,baiko dubi sashenta ba,haka ta daga kai ta isa ga kawun nata ta zube tana gaidashi kanta a qasa.

    Shuru tayi ta nutsu sosai kamar da gaske tana sauraron kawun nata sanda yake mata fadan tsafta,iya abinda yafi abbas din yakai qorafinta akai kenan,amma ji take gaba daya ya gama tozartata ya wulaqantata,hausawa sukance wai wanzami bayason jarfa.

    “Nifa kawu kawai baya ganin qoqarina ne,amma ai inayin duk abinda naga zan iya bakin gwargwado”

    “Oh…..qarya yake miki kenan?,nace qarya yake miki,to ko ni da nake namiji ai gashi ina gani” ya fada yana nuna dakin baqin da ya hada qura sosai,sai kawai ta saki kukan takaici,kawun ya qara da cewa

    “Duk qoqarin da abbas yakeyi babu wanda bai san dashi ba,don bai taba kawo qararki ba tsahon zamanku tare sai yau,kuma bazai taba tiwuwa ace shekarun duka da kuka kwashe ke dashi baki taba yi masa laifi ba,saidai kece d baki gani”

    “Nima kawu ai yana yimin”

    “Rufen baki,me ya hanaki ki fada” ta inda yake shiga bata nan yake fita ba,yayi mata fada sosai ya kuma tursasata ta bashi haquri.

    Kamar wadda aka cusawa tsumma a baki kanta a qasa haka ta furta kayi haquri,gaba daya ma abun sai ya jishi banbarakwai,don zaiyi mugun mugun wahala kaji kalmar ban haquri daga bakinta,daga qarshe dukansu kawun ya hadasu yayi musu nasiha sannan ya wuce gida,abbas ya fita ya rakashi har bakin mota sannan yayi masa alkhairi,duk da cewa da qyar ya karba.

    Daya dawo tana ta kumbure kumburenta sai ya watsar yayi kaman bai gani ba,ya tattara ya fita sallah,bai kuma dawo ba sai bayan isha’i,don ya tsaya ya saurari karatun da ake a masallacin duk bayan sallan isha’i zuwa qarfe tara na dare.

    Silk sleeping dress ce a jikinta baby pink mai gajeran hannun net,duka tsahonta iya qaurinta yake,ta lullube kanta da wata qaramar hular net mahadin kayan,ta cusa duka gashinta aciki,idan kayi mata kallon farko saika dauka batasan ko zo na kasheka da hausa ba,dakin babu wadatar haske sosai,sai na screen din wayarta dake hannunta.

    Gaba daya bata jin dadin chart din da takeyi,zuciyarta duka babu dadi,wani irin kewarsa ce take taba zuciyarta a hankali,tun dazu daya shigo yace zai fita bata kuma ganinsa ba,kuma dazun taji shigowar motarsa,taji mimi tana masa oyoyo,amma bai shigo ya sake ganinta ba?,wani abune da bata saba dashi ba,duka sai taji qirjinta da zuciyarta sun quntata,wayar ma ta fita a kanta,ta maidata gefa ta ajjiye tana zamewa ta kwanta,idanunta suna hada ruwan hawaye.

    A gajiye yake jinsa,don haka ya nufi sashen widad yayi mata sai da safe,ya murda qofar ya jita a kulle

    “Sarkin tsoro” ya fadi yana sakin murmushi,ya saka nasa key din ya bude ya shiga.

    Falon nata neat kamar ba’a zauna ba,qamshinsan nan yana nan,amma akwai qarancin haske,da alama ta gama shirin kwanciya.

    Lumshe idonta tayi sanda taji sallamarsa,sai taji wani abu da ya tokare mata a qirji yana sauka,ta bude idonta tana amsa masa sallamar,dai dai sanda ya shigo dakin,ya saka hannu ya kunna fitilar haske ya gauraye ko ina.

    A kanta idanunsa suka fara sauka,suna hada ido sai taji zuciyarta ta karye,ta sake narkewa tana jin idanunta suna tsatstsafo da hawaye

    “Bakiyi bacci ba?” Ya tambayeta yana takowa inda take,maimakon ta amsa masa saita cusa kanta cikin pillow tana sakin kuka,yaji a jikinsa kukan take,saboda haka ya tako da sauri ya iso inda take

    “Wuud(qauna/soyayya,sunan da ya kuma fara kiranta dashi kenan)” sake cusa kanta a pillow din tayi,sai ya haura gadon gaba daya,ya birkitota jikinsa yana leqen fuskarta

    “Me ya faru?,kuka?” Gaba daya ta saki kukanta,ta kuma qanqameshi tana saka kanta a qirjinsa,cikin narkakkiyar muryar kukan tace

    “Ba kaine ba?”

    “Nine?,nayi me?” Ya fada tana fidda idanunsa

    “Tunda ka fita baka sake shigowa ba kayi tafiyarka,kuma daka dawo ka shiga wajen mommyn mimi ni kuma sai yanzu ka shigo,bayan ma a can zaka kwana”

    “Kishi?!” Ya fada a zuciyarsa yana zaro idanunsa waje,wani lafiyayyen murmushi kwance saman fuskarsa,maganarta dai dai take da albishir a gareshi na rainon da yakewa zuciyarta ya fara kaiwa ga gaci,albishir ne a gareshi na zai fara tarbar sabuwar rayuwar daya raina,sabuwar zuciya da jaririyar soyayyar data fara ginuwa.

    Rungumeta yayi gaba daya a jikinsa,cikin taushi da laushin harshe ya fara gaya mata wasu kalamai da suka sata jin kunya,tun tana ya bari yana qi har kunya ta sakata ta shige jikinsa gaba daya,sai daya tabbatar ta nutsu sannan ya sakata ta kwanta,ya rufeta da duvet da kyau,ya saita mata sanyin ac dana fanka guri daya,ya kuma rufe mata dukka windows dinta dama sashen gaba daya.

    Tana jinsa yana fita kamar tace masa ya dawo,to amma ta samu dakiyar zuciya tunda ya gaya mata goben a nan zai kwana,ta rufe idonta tana sake bawa kanta qwarin gwiwa,duk da zuciyar dai babu dadi.
    [3/19, 5:44 PM] +234 808 711 8630: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)
    *Arewabooks:Huguma*

  • Arubuce Ta Ke 95

    Arubuce Ta Ke 95

    Page 95

    Tayita qoqarin motsa wata gaba ta jikinta amma ta kasa,wata mummunar shaqa taji an yiwa wuyanta,abinda ya sabbaba mata numfashinta ya soma wahalar fita kenan,cikin gigita firgici da kuma tsoro ta soma bude idanunta a hankali tanason ganin waye a dakin?,waye yayi mata wannan aikin.

    Wayam……babu kowa a dakin,daga ita sai kayan gado labulaye zuwa frames a dakin.

    Idanunta ta wulga gefe,sai ya sauka ga bangon dakin da take fuskanta,wani irin motsi taga yana yi,yana kuma darewa a hankali,wani dogon hannu yana ratsowa har zuwa inda take kwancen,ta motsa bakinta da nufin addu’a amma komai ya gaza fita,idanun nata yana kan hannun da yaci gaba da ratsa bangon dakin yana qara shigowa hadi da ci gaba da shaqe mata wuya.

    Ci gaba tayi da kokawa da numfashinta tare da qoqarin ganin ta kira sunan Allah,tsahon wasu mintuna kafin ta samu ta fusgo addu’a da qarfi daga bakinta

    “Ya Allah….. innalillahi wa inna ilaihi raji’un” ta fada da qarfi,kalmar da tayi sanadiyyar yankewar komai,jikinta ya sake, bangon dakin ya koma dai dai,motsin da dakin yakeyi ya tsaya cak,ta miqe da mugun hanzari,ta nufi qofar dakin da gudu tana sake kiran sunan Allah da mabanbantan sunaye.

    Kai tsaye ta fada dakin abbas din ta maida qofar ta rufe sannan ta zube a wajen tana tokare bayanta da qofar kamar me shirin hanawa wani shigowa dakin,ya sulale ta zube a wajen tana riqe da wuyanta,saita fara karanta ayatul kursiyyu da qarfi,ko ina na jikinta yana wani irin rawa kamar me shirin ficewa daga hayyacinta.

    Ta jima a wannan yanayin tana karanta ayatul kursiyyu da dukkan addu’ar tsari da tazo bakinta,har sai da dukka yawun bakinta ya dauke,Allah ya saukar mata da wata nutsuwa,saidai har yanzu jikinta rawa yakeyi,tsoron dake tattare da ita ya ragu sosai,saidai a firgice take qwarai da gaske.

    Kusan awa guda kenan kafin ta samu kuka yazo mata,ta tattare guri daya cikin wani irin yanayi na tashin hankali,tana jinta ne tamakar a tsakiyar wani daji da babu gida gaba babu gida baya,ita daya qwal a sashen,ta ina zata iya fita tabar sassan?,ta baro wayarta a dakin da batajin zata iya taka koda qofar dakin ne bare tayi kiran abbas,cikin wannan yanayin taci gaba da zama a bakin qofar dakin,rabi kuka rabi addu’a,a haka ta qare darenta tsaf a zaune dungurgur har aka kirayi sallar asuba.

    A jikinsa ya dinga jin tunaninsa ya karkata a kanta,don haka ana idar da sallar asuba ya baro masallaci ya wuce sassanta.

    Kamar numfashinta zai tsaya haka taji sanda taji motsi yana buda sassan nata da key dinsa,ta qanqame jikinta guri daya tana sakin kuka sosai tana kiran sunan Allah,har ya buda ya shigo falon ya kuma duba dakinta bai ganta ba tana zaune a wajen ta kasa motsawa,mamaki ya cikashi ganin har bandaki ya duba,babu ma alamun ta shiga,don a bushe bandakin yake,sai tunaninsa ya bashi ya duba dakinsa,don haka ya fito ya nufi qofar dakin.

    Daya murda handle din yaji alamun a kulle take sai hankalinsa yadan kwanta,cikin ransa yana murmushin ya akayi ta canza daki ta koma nasa dakin?,sai ya gyara tsaiwarsa yana rayawa a ransa lallai yau zaiyi mata tsiya.

    Knocking yayi,widad dake zaune jikin qofar ta runtse idanunta tana jin kamar numfashinta zai dauke,ya sake qwanqwasawa murya can qasa ya kirayi sunanta,abinda ya bata qwarin gwiwar miqewa da hanzari ta bude qofar,batayi wata wata ba ta fada jikinsa,ya tareta da sauri cikin mamaki da tashin hankalin jin irin kukan data fashe dashi.

    A rude yake ta jero mata tambayar me ya sameta?,me ya faru?,menene?,amma ta gaza amsa masa tambaya ko guda daya,sai sake riqeshi da tayi da kyau kamar mai tsoron kada ya subuce mata,a haka tana jikinsa ya jata zasu koma dakin amma ta turje taqi,dole sai parlor suka dawo saman kujerar tana kwance a jikinsa tana gurzar kuka.

    Kusan minti talatin suna a haka sanann ya soma lallabarta,yace tayi sallah?,tace a’ah

    “Kije kiyi sallah sai kizo ki gayamin abinda ya faru” ko motsawa daga jikinsa qi tayi,sai a sannan ya sake experiencing tsoron dake tattare da ita,mamakin abinda ya haifar da irin wannan tsoron daga wajenta ya saukar mishi,duk da ya sani ita din matsoraciya ce,to amma tsoron nata baikai haka ba,hasalima ta fara sabawa da gidan,ta rage tsoron sosai.

    Sai shine da kansa ya rakata bandakin ya kuma tsaya tayi alwalar ta kuma yi sallar,ta hanashi motsawa ko ina,tana kwance a jikinsa wani irin zazzabi ya fara saukarwa jikinta,dole yaja duvet ya lullubesu ita dashi, hankalinsa gaba daya ya tashi,gashi tambayar duniya ta gaza ce masa komai,sai dan uban kukan da take masa..

    Wani irin tsoro ke dawainiya da ita shi yasa ta kasa gaya masa,tana ji kamar idan ta fada masa abun zai sake dawo mata,don haka ta kasa cewa komai sai kukan,hankalinsa dukka a tashe yake,yayi lallashin duniya tayi shuru tunsa taqi fadin abinda ya faru amma ta kasa yin shurun,sai hawaye da taketa fitarwa,a haka har rana ta fara fitowa tana kwance a jikinsa saman gadon,a haka yayi azkar dinsa yana duban fuskarta wadda a sannan bacci ya fara fusgarta,wani irin zazzabi yana sake lullubeta.

    A hankali bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita,sai a sannan ya samu ya zare jikinsa ya tula mata pillows yadda zata tsammaci shine,ya miqe ya soma bincike gidan wai ko wani abun ta gani,tun daga dakinsa zuwa nata dakin,bandakunansu qasan gado kitchen ventilation dinta dako ina amma baiga komai ba,dole ya haqura ya wuce kitchen ya hada ruwan zafi yasha zuciyarsa cike da wasu wasi da tunane tunane.

    Sanda ta farka zazzabin ya riga yayi qarfi a jikinta,dole ya zare mata rigar jikinta ya jiqa towel ya soma rage mata qarfin zazzabin,ba yadda bai lallabata tayi wanka ya kaita taga likita ba amma taqi,yace zai kira Dr gida nan ma tace bataso,sai kukan da taketa masa,wanda ya qarasa rudashi gaba daya.

    Ta bangaren hafsa hankali kwance take hidimarta,ta gama shirya breakfast suka ci abinsu da yara,tana ta kai kawo tsakanin falonta zuwa farfajiyar gidan hankalinta na sassan widad din,har sha daya na rana bataji motsinsu ba,don ta tabbatar yana sassan widad din,tunda ga motarsa ba fita yayi ba,saita koma ciki ta dauki wayarta tayi kiransa.

    A lokacin ya sanya widad din a gaba yana bata tea,da qyar take karba sai sharar hawaye take,sai da yayi da gasken ma ya samu take amsa din

    “Naji shuru daga sallah baka dawo ba,ga kuma break dinka” ido ya lumshe yana jin zuciyarsa babu nutsuwa gaba daya,a yanzun ma shi baijin wata yunwa,bare ma yasan ba wani break din arziqi ta tanada ba,idan tayi wutar duniya……ta qure adaka ta soya chips da fried egg

    “Ina cikin gidan,widad ce bata jin dadi” baki ta tabe,ranta fes ba tare da taji wani abu ya dameta ba

    “Inason fita ne,umma bata jin dadi xanje na duba jikinta”

    “Ki gaisheta” kawai ya fada a taqaice ya katse wayar,yasan dama kiran bawai don baici abincin bane main purpose ba,ya ajjiye wayar gefansa ya sake maida hankalinsa ga widad din.

    Ido ya zuba mata,gaba daya dare daya duka ta fada ta birkice masa,ya lumshe ido yana jin wani abu yana taba ransa

    “Me ya faru baby….. please tell me ko raina zai nutsu” kamar ko yaushe sai hawaye suka fara taruwa,ya tareta da sauri

    “Ya isa, shikenan” ya miqa mug din bakinta yana cewa

    “Qarasa shanye wannan” cikin ransa yana tunanin yadda zai lallabata taga likita,bazai iya zama yana ganin uban zazzabin nan a jikinta ba.

    Wayarsa ta sake qara,sai yaga hafsat ce,ya sake daga wayar ya sakata a handsfree

    “Na tura mimi ka bata kudin mai zan saka mai a motata” takaici ya cikashi,ya lumshe idanunsa yana qoqarin hadiye bacin ransa

    “Kada tazo,ba kudi a jikina,kije zan tura miki ta account idan kinje gidan man kya basu ATM dinki su cira”

    “Tom” ta fada hankalinta kwance yana ajjiye wayar,ko kunya sam.bataji ba,ita dashi duka sun dani full tank yakewa motar tata,bama motarta kadai ba,hatta motar da zaya bari a gida idan zai koma kaduna.baya barinta haka,yaja qaramin tsaki qasan ransa yana fadin

    “Astagfirullah” sau tari idan hafsat din tayi masa abu,sai yaga istigfari kawai ya dace yayi,wala’alla yayi wani laifi ma Allah ne daya kasa gane me ya aikata din.

    Wunin ranar gaba daya tana maqale a jikinsa,duk inda zai motsa zata bishi,kwata kwata tsoron gidan ya kamata matuqa da gaske,tana jin kamar ta bude ido ta ganta a kaduna,ga zazzabin da ya hanata sukuni wunun ranar,taqi yarda kuma taga likita sam,sai gige mata jiki daya dinga yi da ruwa mai sanyi,ya bata paracetamol tasha sannan aka samu sassaucin sa,sai daga baya ya sake dawowa.

    zuwa dare ta dinga masa kuka saboda yadda wata muguwar tsanar gidan ta shigeta,ta dinga kuka sai sun koma kaduna,ba shiri cikin daren ya soma hada musu kayansu,bai kwanta ba sai daya gama shirin tafiyar tasu.

    Da safen ta tashi da ‘yar walwalarta saboda jin zasu tafi,kafin ya gama nasa shirin ita tuni ta gama,sanda ya kammala shiryawar kuwa zaije ya sallami su hafsat farfajiyar gidan ta fito ta zauna tana jiransa,sam bata doshi wajen hafsat din ba,haushinta takeji musamman duk sanda zasu kebe da uncle din nata,ko zata ganta kusa dashi,idan wani abu ya kawo ga ta tabashi kuwa saidai tabar wajen tana goge qwalla,ita kanta batasan manufar hakan ba,batasan kuma abinda yake kawo mata jin hakan a zuciyarta ba (kishi😄, Allah sarki,quruci dangin hauka,ta fara kishin uncle din nata ba tare data sani ba).

    Tana tsaye daga bakin window din falonta tana hangensu sanda ya gama sallamarta ya fice,bayan ta gama mita da qorafin akwai sauran kwana daya daya rage ai bai cika shi ba,bai biyewa qorafin ta ba,don koma yaya yayi dai sai ta yishi,ya zama kamar cikin jininta abun yake.

    Murmushi ta sauke sanda suka fice din,cikin wata walwala da jin dadi ta fada saman kujera tana tunano abubuwa masu yawa a zuciyarta,lallai a baya ita taso har aka kai wannan matsayin ma da ake kai yanzu kamar yadda ummanta ta gaya mata,ashe wannan hanyar itace hanya mafi sauqi da sauri ta maganin matsalar ta ta tsaya tana biyewa hasashe da hanyoyin anty ummee masu tsauri?.

    Assalamualaikum

    Yanzu an wuce lokacin da za’a dinga novel na qaryar soyayya tsura kawai a ciki da uban tarin dukiya daga qasa zuwa qasa,dole mu fuskanci reality na abubuwan da suke faruwa yanzu suke damunmu,akwai darasi sosai da nakeso mu cimma cikin labarin nan,kuyi haquri muje harmu cimma gaci
    Sannan tun asali duk wanda ya sanni labaraina ba gajeru bane,daga bayan nan ne nake gajeru,to wanann salon labarin yazo a haka ne,sanann raguwar tsahon pages din yasa numbers din sukayi yawa,amma in sha Allah i will try my best naga pages din sun dan qara tsaho ta yadda numbers din zasu ragu, thanks for choosing me.
    [3/21, 3:18 PM] +234 813 343 4840: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)
    *Arewabooks: Huguma*

  • Arubuce Ta Ke 91

    Arubuce Ta Ke 91

    Page 91

    Sassanyan qamshi parlor din yake fitarwa baya ga wani kwantaccen yanayi da duk wanda ya shigo ciki sai ya burgeshi,awa guda kenan da gama dukka aikinta,ta kuma shirya kanta cikin wata gown ta yadin chiffon mai qaramin hannu,plain ne black babu digo ko adon komai a jiki,ta matse gashinta da jiyan abbas ya kaita da yammaci aka gyara mata shi,yana daya daga cikin abinda yakeso,shi yasa shima yake bashi kulawa har fiye da yadda ita ke kula da sumartata,duk sanda take kwance a jikinsa zaka samu hannunsa saman kanta yana yamutsa sumartata mai tsaho da santsi,abinda yake yawan haifar mata da kasala,saita lafe a jikinsa.

    Hankalinta ya dauku ga wayarta sosai,tana karanta wani hausa novel mai suna HANGEN DALA,labarin ya tafi sosai da hankalinta,ya kuma fara ankarar da ita matsayin hafsat a wajenta.

    Ya dauki mintuna kusan uku tsaye a bakin qofar yana qare mata kallo ba tare data sani ba,hancinsa kuma yana shaqar daddadar iskar da parlor din yake fitarwa.

    Tayi masa wani mugu mugun kyau,cikin kwanakin gaba daya wani kyau take qarawa,ga wani irin fari data sakeyi kamar ka sanya hannu jini ya fito,ta kuma qara qibar data sakata murjewa,alamun hankali da girma sun fara nunawa a jikinta,qibar tayi mata wani irin kyau dake dimauta masa tunani,shi kansa wani lokaci yakan tuhumi kansa

    “Abbas anya baka zauce akan yarinyar nan ba?” Bai sani ba ko zaucewar yayi,amma shi kansa yasan yana mata wani irin so da bazai misaltu ba,baya gajiya da kallonta,baya gajiya da ganin shirmenta,baya gajiya da sauraren hirarta,ko ba komai zai samu nishadi irin wanda duk duniya idan ba wajenta ba babu wajen wanda yake samunsa.

    Yaga alamun hankalinta yayi nisa sosai,don haka ya sanya qafarsa cikin tattausar muryarsa yayi mata sallama,suna hada ido ta miqe da sauri bayan ta watsar da wayar gefe,ta kuma tako da sassarfa yadda ta saba yi masa ta dane shi,ya sanya dukka hannayensa ya tarbeta,ya kuma dauke abarsa cak ya aza a jikinsa yana aika mata kisses ta ko ina,laushin fatarta da qamshinta kamar zai zautashi.

    Kamar ko yaushe ta sunne kanta tana jin kunyarsa,ya saki qawataccen murmushi yana shiga cikin falon sosai da ita hadi da cewa

    “Gayamin…..me zanyi na qarasa cire kunyar nan baby……tana qwarata wani lokacin fa” ya fada murya qasa qasa kamar su da wani ne a falon,saita sakar masa murmushi tana shigewa jikinsa.

    A hakan yana dauke da ita suka shige bedroom dinsa tana masa sannu da zuwa

    “Yau anyi zafi,wanka zan fara yi baby,ba wani abinci yau” dariya ta sakar masa,sannan ta wantsalo daga hannuwansa zuwa qasa,ya tareta da sauri yana cewa

    “Yi a hankali,wai bakiga kin fara zama ‘yar lukuta ba?,inajin na kusa fara kasa daukarki” baya taja tana bata fuska

    “Ka kusa daina daukata kuma uncle?” Ta fadi tana bubbuga qafa a shagwabe,yasan yanzun zai ballowa kansa ruwa,sai yayi saurin yin kwana

    “Wasa nake miki fa babyn uncle…..amma fa wait…. seriously kin fara zama ‘yar lukuta,ban yarda ba akwai abinda yake faruwa,me kike ci bakya sanmin?” Siririyar dariya ta saki

    “Uncle ka fini ci fa,saidai wanda nake ci da daddare kana bacci” kai ya gyada yana dariya

    “Harda rabona kike ci ai,kuma ban bayar ba,saina fanshe abuna,zo nan” ya fada yana takawa gabanta idanunsa a narke a kanta,ta saki dariya taa fadawa toilet da gudu.

    Tsayawa yayi ya bita da kallo har ta shige,qugunta ya bude sosai,qirjinta ya fara cika irin yadda yakeso,abinda yake sake dimautar dashi a kanta koda yaushe,saidai har yau ‘yar shagwabar tasa kukan amarci takeyi bata daina ba,hakan baya damunsa,hakan ma burgeshi yakeyi,ya zauna ya lallashi kayarsa.

    Gaban mudubi ya taka ya zuge jakar daya shigo da ita yana duba takaddun daya shigo dasu,ya sake sakin murmushi yana tunanin irin yadda zataji idan ya gaya mata komai na tafiyar ta saudiyya ya kammala,yana tsaka da dubawar kuwa ta fito tana goge ruwan hannunta da qaramin towel

    “Uncle ka shiga na hada” ajjiye su yayi,ya matsa zuwa gabanta,a tausashe ya kamo qugunta ya hade da nashi yana duban qwayar idanunta,itama shi take kallo,tana samun kanta cikin wani irin yanayi a duk sanda irin hakan zata faru,tana ji da ganin wani abu na musamamn cikin idanuwansa

    “Amma dai na gaya miki,indai kina yin wankanki bakya jirana,zaki dinga wanka biyu ko?” Fuska ta narke masa sannan ta turo masa dan qaramin bakinta

    “Uncle saina zauna ka dawo kaga qazantata?” Bin siraram lips dinta daketa qyallin lip gloss yayi da kallo tsigar jikinsa na zubawa,sannan ya dauke ya maidasu cikin manya kuma fararen idanuwanta,har cikin zuciya da ruhinsa yana yaba mata,yadda bata qaunar ya ganta ba wanka,naturally haka take,sometimes kafin ya dawo daga salla tayi wankanta

    “Okay,tunda haka ne zaki biya ladan qin jin maganar uncle” bai barta ta samu damar cewa komai ba ya hade bakinsu waje daya ya shiga aika mata da wani zazzafan kiss da ya sanya taji kwanyarta tana yamutsawa,cikin lokaci kadan ya sauke mata wani saqo mai nauyi daya sanya jikinta saki gaba daya,yayin da ilahirin nashi jikin ya dauki rawa gaba daya,kusan ta saba da wannan yanayin nasa,tun tana tsoro harta saba gani,ta saba ganin wannan romance din mai zafi daga wajensa,fice mata a hayyacinsa yakeyi cikin lokaci qalilan,wannan yake rudata itakuma tayita masa kula,kukan da baya samun damar lallashinta sai bayan komai.ya kammala.

    Yau dinma daga bata ladar rashin jin magana ya zarme,shi kamsa baisan me yakeyi ba,illa dai zuciyarsa da qwaqwalwarsa yaji sun kasa jurewa,bai kuma barta ba sai daya isa ga muradinsa duniyarsa qarshen farincikinsa.

    Tana a jikinsa tana masa ‘yan koke koken data saba,hannunsa cikin sumarta yana yamutsata,idanunsa a rufe,lips dinsa kawai ke motsawa suna fidda sautin wasu kalmomi masu zaqi da kwantar da rai,yayin da zuciyarsa tayi nisa wajen son gano iya matakin matsayin da widad ta tsaya a ransa,ko yaushe yana jin kamar a ranar ya fara saninta,tana da wata irin baiwa da bai taba tsammanin za’a sameta jikin kowacce diya mace ba,a duk sanda ya kasance da ita burinsa na sake kasancewa da ita baya raguwa saidai ya qara hauhawa

    “Uncle wayo” ta fada a shagwabe da siririyar muryarta, murmushi ya kubce masa,hakan take yawan gaya masa duk sanda irin hakan ta faru

    “Kiyi haquri dani babyn uncle,na jarabtu dake har bansan iyaka ba,am sorry….but I have something special for you,muje muyi wanka ki gani”.

    Tare sukayi wankan duk da tana dan zuzzulle masa,suka shirya ta gabatar masa da abinci yaci cikin nutsuwa da kwanciyar rai,best taste for ever a wajensa.

    Bayan ya kammala ya jingina bayansa da kujera qafafunsa a miqe harde wajen guda,yatsun hannunsa ma a hade yana dubanta,kamar cin abincinta yadan ragu,tun ranar nan ya gani,amma kuma bai sakashi damuwa sosai ba,ganin bata canza ba,saima murjewa da jikinta yakeyi,hannu ya miqa mata alamun ta taho,saita maqale kafada

    “Uncle wayo” ta fada tana dariya,bai shirya ba dole shima dariya ta kubce masa,a baya yakan jima baiyi dariya irin haka ba,amma a yanzu.widad ta maidata abu mai sauqi a wajensa idan yana tare da ita,dukka tsare gida shan kunun nan da kamewa sun koma office da sauran guraren aiki

    “Kizl ki karba albishir din naki,ba wayo bane yanzu” matsawa jikin nasa tayi,ya kuwa riqeta gam yana fidda takaddun ya fara mata bayani.

    Ruqunqumeshi tayi da kyau cikin farincikin da batasan yawansa ba tana sake tambayarsa

    “Uncle da gaske?”

    “Na taba yi miki qarya?” Kai ta girgiza

    “Baka taba uncle” ta fada hawayen farinciki yana sauko mata,saiya bata fuska kadan

    “Kuka?,noo baby,don’t cry mana” ya fada yana janta jikinsa hadi da dan bubbuga bayanta alamun lallashi.

    Irin godiyar data dinga masa sai daya ji qwalla ta sauko masa,godiya ce da bai taba jin irinta daga bakin hafsat ba,duk kuwa da ya kaita gurin da yanzun widad din zata je a qalla sau uku kenan,sai ya saka hannuwansa yana sake lullubeta cikin jikinsa da kyau,yana sake jinta tana shiga rayuwarsa da gasken gaske.

    A ranar ta dinga kira waya tana shaidawa kowa,ummunta mommynta da abbanta sune farko,sannan uncle muhsin anty madeena anty deena dasu hajja,kowa yaji dadi ya kuma yi farinciki da wannan labari,ya kuma tayata murna qwarai, uncle muhsin ya kirashi yayi masa godiya,kai kawai ya girgiza

    “Bakasan wacece widad a wajena bane muhsin,she meant alort to me,bansan ya zan fasalta maka ba” yayi furucin tun daga qasan zuciyarsa.

    Murmushin jin dadi uncle muhsin ya saki,amma a fili sai yace

    “Easy sir…..surukinka nake fa kaketa fallasamin sirrin zuciyarka” sai suka sanya dariya a tare.

    Cikin satin yace ta shirya zasu wuce bauchi,batajin son zuwa bauchin sam,amma tana son ganin hajiya dasu mimi,don ta kwana biyu bata je ba,bata nuna masa komai ba,cikin karsashi ta shirya musu dukka jakankunansu,ta kuma siyawa su mimi da hajia tsaraba,bayan tace ya turo rose ko samuel su kaita kasuwa,sai gashi ya kashe aikinsa da kansa yazo ya kaita ta siya duk abinda takeso,don yanzun ba kasafai yake bari wani ya kaita wani waje ba,idanma ta kama to saidai ya turo mace.

    **********Tunda sale ya bude gate din gidan ta gane motarsa ce,amma data fahimci bashi kadai yazo ba saita ci gaba da zamanta saman plastic chair din da take zaune a kai,ta jibge kayan da take siyarwa tana faman lissafi,gefenta su mimi ke wasa kamar ko yaushe futu futu abinsu,kai bakace akwai interlock cikin gidan ba.

    Widad dake bacci abinta cikin motar ko shigowarsu cikin gidan bata san dashi ba,ya waiwaya yana mamakin nauyin baccin da takeyi a ‘yan kwanakin nan,fuskarta tayi wani mugun fresh hasken fatarta ya kashe masa idanu,ya daga hannu da nufin tashinta,saidai mimi da nawwara sun rage masa aiki,don tuni suka fara kiran sunanshi suna rige rigen isowa,muryarsu ta sakata bude idanunta a hankali,ta saki murmushi tana kallon yaran har suka iso garesu.

    Ita dashi aketa rige rigen tarbarsu,tayi nasarar riqe mimi shi kuma ya dauki nawwara,daga inda hafsat din take kamar zuciyarta zata fado,ta janye idanunta tana jin kamar zuciyarta xata fashe,ta gaji da jiran da anty ummee tace tayi,sai take gani kawai ta soma gajiya da lamuranta,tunda ta nemi aron dubu dari biyu bata bata ba.
    [3/20, 8:54 PM] +234 813 343 4840: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)
    *Arewabooks:Huguma*

  • Arubuce Ta Ke 96

    Arubuce Ta Ke 96

    Page 96

    Wata wawiyar ajiyar zuciya ta saki tana samun nutsuwar ruhi da gangar jiki sanda taga sun dauki hanyar kaduna,duk da jikinta babu wani qwari sosai saboda zazzabin daya gallabeta,amma at least ta samu wani sassaucin.

    Dan waiwayo yayi kadan ya dubeta,sannan ya cire hannunsa guda daya daga kan motar ya kama dogon hancinta yadan ja

    “Hankalinki ya kwanta ko?” Saita sakar masa murmushi, murmushin da yayi masifar kewarsa,yaketa kuma struggling na ganin tayi shin amma bai sameshi ba sai yau.

    Tun basuyi nisa ba ta soma bacci,wani irin nannauyan bacci da shi kansa abbas din ya dinga kallonta,ko sau daya baiyi.marmarin tashinta ba,baccin ma datayin dadi yayi masa,aqalla yasan zata rama bashin baccin da batyi ba kwana biyu,sai ya kunna radio station yana sauraren labarai,da sauran programs da suka jibanci harkokin tsaro,da ya gaji ya maida karatun qur’ani,wanda ya qarawa baccinta dadi sosai,baccin da bata farka ba sai da suka isa kaduna.

    Tun daga wannan ranar bata sake binsa bauchi ba,don ko cewa yayi zasu weekend yanzu zata rage walwala,gaba daya garin ya fita a ranta,shima bai takurawa, don asalinsa ba mutum bane mai takura da tsanani akan abu bane,sai ya barta yaje yayi kwana biyu ya dawo,har kusan watanni uku.

    Cikin hakan bikin diyar yaaya bara’atu ya taso,ya gaya mata,duk da bataso amma ta gaza nuna masa,yana da tsananin kirki da karamci,yana mata kyautatawar da duk duniya baya ga ummu bata ganta a wajen kowa ba,wannan ya sanya duk wani abu da tasan bayaso ko zaiji babu dadi take nisantarsa(bawai don tasan muhimmancin hakan ba,kawai saboda yadda kyautatawarsa taje da nauyi a idanunta).

    Kaya ta fitar ta bayar akayi mata dinkuna masu kyau, zuciyarta duka babu dadi,cike da tsanar bauchin amma haka ta dinga shirya,duk da tana boyewar amma ya karanci akwai abinda ke faruwa,don kuzarinta ya ragu,a sanyaye take komai.

    Ana gobe zasu tafi da daddare,yana zaune kan sofa bed yana shan black tea din data hada masa ita kuma tana rufe wata qaramar jakarta data zuba qananun abubuwan amfaninsa da tasan zai buqata,duk inda ta gifta idanunsa yana biye da ita,baya gajiya da kallonta,barin yau din da tayi kwalliya ciki wani mini skert da wata riga da sukayi matuqar karbarta,zuwa lokacin komai nata ya cika yayi yadda akeso ya zamana a jikin diya mace,ta zama wata ‘yar duma duma da ita,haske da laushin fatarta ya qaru,hakanan tsahon gashinta cikarsa dama baqinta,lips dinta ya qara zama pink sosai haka idanunta sun sake fitowa,ta fannin mu’amalarsu ya sake zama wani mayenta,shi kansa baisan yadda akayi ya sake horancewa ba,baiqi duka dare ya dinga kasancewa da ita ba,baya gajiya da ita,wata baiwa ke gareta ta musamman mai dimauta tunanin mutum,saidai widad din tashi har yanzu raguwa ce,batayi qwarewar da yakeso tayi ba,kullum hakan ta kasance sai yayi zaman lallashi,shagwabarta da sangarta take zube masa,shima sai ya biye mata.

    Ajjiye mug din hannunsa yayi yana fakon isowarta,aikuwa tana zuwa giftashi ya sanya hannu ya fincikota jikinsa,yayi mata kyakkyawan masauki saman cinyarsa dake bayyane a waje cike da gargasa,hannuwansa ya saka ya zagaye qugunta dasu ya sake matso da ita sosai,ya saka fuskarsa a tsakiyar dukiyar fulaninta yana shaqar qamshin dake fita a wajen.

    Hannu ta saka ta riqe kansa,tana jin tsigar jikinta tana tashi saboda yadda labbansa suka sauka a wajen,ta saki dariya tana janye jikinta baya,ya daga idanunsa da suka fara sauya launi yana murmushin shima ya kalleta

    “Kamar baki shiryawa zuwa bauchin nan ba” kanta ta langabar gefe,a zahiri batason zuwan,amma bai kyautu ta nuna masa ba,saita girgiza kai

    “Aah,kawai kasala nakeji kwana biyun”

    “Nayi noticing canji da yawa,kin koyi bacci,sannan ga overdose kyau baby da kike qarawa,overdose dad……” Hade bakinsu tayi waje daya yau da kanta,don batason ya qarasa fadin kalmar,bala’in sakata jin kunya takeyi,hakan da tayin saita tafi dashi wata duniyar ta daban,tasa ya dimauce ya mance dukka maganar da zai fada din,sanda zata qwace kanta kuma yace baisan zance ba,sai da ya cimma gaci sannan ya samu nutsuwa.

    Washegari da wuri suka isa,don sha biyun rana ma a can tayi musu,sassanta ta wuce kai tsaye,gidan duk bai mata dadi ba saboda su mimi basa nan,hajiya tasa anzo an daukesu,an musu kitso da qunshi kamar yaran kowa,an kuma dauki kayansu sai bayan biki zasu dawo.

    Wannan karon hafsat din bata hana ba,bata ma isa ta hana din ba don tasan abbas din ko zai jure komai banda wannan,kuma kai tsaye shi yayi kiranta yace ta bada yaran,ta hada musu tarkacen kayansu,gasu dai a ido masu kyau da tsada ne,amma dauda da rashin kula duk sunci mutuncinsu.

    Tsaye hajiya tayi kawai cikin takaici tana qarewa kayan kallo,banda ma gidan yana samun feshin maganin qwari da kuma gyaran da uban kewa dakin nasu duk sanda ya samu chance….ta tabbatar ba za’a rasa wani qwaron a ciki ba,hajiyan nada masifar tsafta,sai tattara kayan tasa akayi aka bayar,banda ma masu tsada ne da kuma sauran qwarinsu qazanta ce ta cinyesu,a wajen hajiyan bola ce tafi kamata dasu.

    Har ta fitar da kudi ta bayar za’a sake musu sabuwar siyayya mimi tace akwai wasu kayansu a wajen anty widad.

    Hajiyan da kanta ta kira widad din tace mimi tace suna da kaya a wajenta,ta fiddo musu dasu umar zaizo ya karba,tana shiga sassanta kayan ta fara hadawa,a killace a tsaftace a kuma goge,umar din ya karba ya tafi dasu.

    Tunda ta sauka gidan ranta yayita baci,gaba daya kamar an tattaro dukka bacin rai an aza mata,haka ta dinga dannewa,ta hau gyaran sashen nata,sai data tabbatar komai yayi neat din ta sake wanka ta canza kaya,ta dauki wayarta ta kira abbas don tanason zuwa saloon da qunshi,na qafafunta duka sun fita,kuma batason shiga mutane haka,abinka da farar fata, babban adon hannayensa da kyan ganinsu ayi musu qunshi.

    Lokacin yana tsaye a qofar toilet yana amsa wayar Jasmin yana jiran hafsat dake ciki ta gama wanke masa zai shiga saboda dan uban qurar daya hada,bata damu ta shiga ta gyara ba,sai ya bawa Jasmin excuse ya katse kiran nata ya daga na widad din.

    Cikin shagwabar nan tata dake sake narkar dashi tace

    “Uncle”

    “Babyn uncle” ya amsa mata tattausan murmushi yana subuce masa,sunan da hafsat taji ya kira saita miqe tsaye dafe da cikinta ta kasa kunne tana sauraren hirar

    “Zanje saloon da qunshi,kaina da hannuwana duka ba dadi”

    “Ba laifi,amma baby……ina kishi fa gaskiya,ki zaba duk inda kikeso zan sa a kira miki su har gida special services mana” kafada ta noqe,ita zaman gidan ne bataso har ga Allah

    “Don Allah uncle,yaushe rabon da nazo bauchi” ta fada da wata irin narkakkiyar shagwaba da har data sakashi lumshe ido ba tare daya shirya ba

    “Shikenan,ki shirya zan fita headquarter yanzu,sai mu biya”

    “Thank youuuuuuu” ta fada tana dariya

    “You are welcome” ya amsa yana sauke wayar sannan ya sake kiran Jasmin yace mata zai shigo nan da minti talatin.

    Sauri sauri tayi ta gama wankewa ta fice ta bashi waje,ya shiga ya hada ruwan wankansa da kansa,abinda bai sani ba kenan muddin suna tare da widad.

    Sassanta ta nufa tana sakin ashar cikin zuciyarta,ita ta dauka ma wannan karon shi kadai yazo,ashe sai data sake biyoshi,akwai sauran rina a kaba kenan?,saita jinjina kai,ta buda wardrobe dinta ta fiddo kayan sawa,sannan ta buda bandakinta ta shiga ta fara kwaskwarima.

    Cikin wata doguwar rigar atamfa da tayi mugun budewa daga qasa ta shirya,brown ce mai adon blue black,tayi amfani da blue black hand bag veil da kuma takalmi,kalar ta haska farar fatarta da kyau, daurin da tayi wanda ta kawoshi gaban goshi ta fidda gashinta ta qasan daurin ya qara mata wani irin kwarjini,ko yaya ta motsa jikinta qamshi yake fitarwa.

    Saboda saurin da take ta fita a gidan ta rigashi isa parking lot,tayi tsaye jikin motar tana jiran fitowarsa,wayarta sabuwa da ummu ta aiko mata da ita a hannunta suna hira da bilkisa ta watsapp,tana ta kwasan dariya,don bikisa din ba daga baya ba,ko yaushe qoqarinta taga ta dora widad din kan hanya,ta kuma ganar da ita wace hafsat.

    Cikin wasu lafiyayyun indian blazers ya shirya blue black din shima,tamkar yasan color din da zata saka kenam,tun daga nesa kwalliyarta ta tsone masa ido,ya zuba mata dukka idanun nasa yana takowa a hankali,ko qifta idanunsa a kanta qyashin yi yakeyi.

    Cikin jikinta taji yana wajen,saita daga kanta ta sauke a kansa,kamar shi,itama kwalliyar sa tatafi da ita ainun,yayi wani mugun kyau,ya koma yaro sosai da bai wuce sha tara zuwa ashirin ba,murmushi ya subuce mata,bakinta ya dinga motsawa tana jiran ya qaraso ta tsokaneshi,saidai dab da zai qaraso din hafsat ta bayyana,ta kwaso sauri cikin baqar abaya data saka ta yafa baqin mayafi wanda ya kasa zama a kafadarta saboda sauri dason ta cimmasu kafin sukai ga fita.

    Ganinta sukayi kawai tana kiciniyar bude gaban motar tana cewa

    “Banajin dadi abban mimi,ka miqa ni asibiti don Allah” tayi maganar tana shigewa gaban motar.

    Da kallo dukkansu suka bita,widad ce ta fara dauke kanta kamar bata ga abinda tayi ba,sai ta matsa ta dauke handbag dinta dake saman motar ta juya zuwa cikin gida

    “Ina zuwa kuma?” Dan dakatawa tayi da tafiyar

    “Na fasa zuwa ne” iska ya furzar

    “Aah,kizo Muje na fara sauketa saina qarasa dake” kai ta girgiza

    “Um um…..naje ko gobe ko jibi” ta fada tana qoqarin boye damuwa sa fushinta,kawai ba zata iya hada mota da hafsat din ba,kallo daya tayi mata tasan neman rigima ya fiddota,dazun da umar yazo karbar kayansu mimi taji yana wayar jiya yakai hafsat din asibitin awo

    “No….,wuce muje” ya fada yana takowa inda take tsaye,yana karbe jakarta daga hannunta

    “Uncle…..”

    “Wai ba magana ake dake ba!…..yara suyita musu da na gaba dasu,kaga abban mimi just leave her mu tafi kawai” hafsat ta fada cikin tsawa,bayan baqincikin yadda taga yana lallabarta hadi da riqe mata jaka ya saukar mata ya tsaya mata a qirji.

    A sukwane widad din ta waiwayo tana jin wutar dai dai take da ita a yau tana tashi cikin kanta,fes ta kalleta ido cikin ido,cikin lallausar muryarta a nutse ta amsata

    “Sorry mommy….bafa dake nake ba……da uncle dina……au mijina na,da mijina nake magana”[3/22, 8:25 AM] +234 813 343 4840: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)
    *Arewabooks:Huguma*

  • Arubuce Ta Ke 88

    Arubuce Ta Ke 88

    Page 88

    *W A S H E G A R I*

    Ture plate din da ya gama cin chips din yayi gefe guda bawai don ya qoshi ba,a’ah sai don babu wanu taste a tattare da dankalin,salam dashi,yakai dubansa ga yaransa daketa cin abinsu hankali kwance,saboda rashin sabo da kuma rashin sanin dadin bakinsu.

    Kallonta yayi itama tana ta cin abinta kamar yaran,tun kayan daren jiya ne a jikinta,duk da tayi wanka a hakan,ya danyi gyaran murya

    “Yau din ba sai kinyi shirin komai ba,zan kwana wajen qanwarki,jibi sai na dawo wajenki,idan mun koma jibin shikenan,idan bamu koma ba sai a dora da haka” maganar taxo mata a mugun ba zata,ta daga kanta da sauri tanason ganin da gaske abbas ne ke mata zancan rabon kwana tsakaninta da widad din,tsabar mamaki da tsorata sai kuwa ta qware,dankalin ya shaqe mata wuya,tahau tari babu qaqqautawa,take idanunta duka suka firfito,ya tsiyaya ruwa da sauri ya miqa mata yana mata sannu.

    Ko data gama shan ruwan numfashinta ya dai daita sai taji kamar ta kurma ihu,abbas din yayi wani mugun baqi a idonta,duk qoqari da jarumtar da tayi a jiya bai gani ba?,shine da safiyar Allah zai zo da wani zancan na daban,banda rainin wayo da rainin hankali,su gama satittikansu a can,sannan a nan ma a cinye mata weekend dinta?.

    Bala’i ke cinta sosai tana kuma son ta saukeshi akan abbas din,amma kuma batason tayi wani abu da anty ummee zata ce ta bata plan din gaba daya,duk da haka ta kasa haqura,ta kafeshi da ido sosai tana kallonsa

    “Abban mimi…..ni kake cewa zaka yiwa rabon kwana da widad diyar cikina?” Cikin second uku kacal ya gama qare mata kallo,a nutse ya jingina jikinsa da kujerar da yake kai sannan ya gyada mata kai yana lumshe ido hadi da budesu,sai ta janye nata idanun,ranta yana qoqoluwar baci,daya daga cikin yanayin da zaka gane hankalinsa a kwance yake,kuma ransa bai baci ba kenan idan yayi maganarsa,kuma sign dake nuna tabbatacciyar magana ce da babu canzawa,sai kawai ta miqe da sauri ta nufi daki,batason hawayen da suka taso mata su zubo a gabansa yaga rauninta.

    Tana kuka tana kiran anty ummee,wadda tuni ta saba da ganin kiranta,kiranta babu alkhairi kamar yadda kiran nata ba samuwa bace damuwa ce,haka siddan idan bata da matsala ba zata taba nemanta ba,tana dagawar kuwa taji sautin kukanta

    “Anty ummee ni yau abbas ke gayawa wai kwanan widad ne?”

    “Abbas din?” Anty ummeen ta fada abun yana girgiza ta itama

    “Eh,shifa” shuru tayi mamaki na ratsata,wanne irin kafaffen namiji ne abbas din,duk hanyar da aka bullo masa sai ta warware?,tsahon minti biyar suna kan wayar hafsat na mata kuka,taja dogon numfashi tana cewa

    “Kinga,kiyi shuru da bakinki,inaso kiyi kamar baki damu ba,kada ma ki bari ya gane kinyi kuka,amma yau bai isa ya kwana a dakin yarinyar nan a gaban idonki ba,ke har su koma wallahi,ki kwantar da hankalinki,indai kinbi abinda zan gaya miki yanzu” sosai taji qunci da takurar da zuciyarta ta shiga yana warwarewa,ta goge hawayenta fes tana sakin dariya

    “Bansan wacce irin godiya zan miki ba ‘yaruwa,bansan dame zan saka miki ba”

    “Ni dubu hamsin ma nake nema,inda zaki bani ita da komai lafiya lau”

    “Ki bari zamuyi maganar kawai anty ummee” ta katse zancan

    “Shegiya uwar son abun duniya,duk bala’in son abun duniyar taki wallahi Allah sai naci dake,duk wayon amarya sai an sha manta” anty ummeen ta fada a zuciyarta

    “To shikenan,sai na jiki” daga haka sukayi sallama,saita miqe ta shiga bandaki ta gyara fuskarta,ta dawo tahau gyaran dakin nata,cikin ranta tsanar widad na sake shigarta,gyaran dakin da a baya saita manta ma ya akeyinsa,don ita ke komai,koda brassiere dinta ta yasar duka zata kwashe ta kuma wanke,amma gashi cikin qanqanin lokaci komai yana shirin canzawa?,ba zatayi sake ba kuwa,ba zata bari haka taci gaba da faruwa ba cikin gidanta,zata bi kowacce hanya don ganin komai ya dawo bisa kan tsari yadda ta shirya.

    ************washegari wajen sha biyu na rana saiga nujood ita da sauran qannenta,dadi ne sosai ya kama widad,ta rungumeta kana taja baya tana cewa

    “Hajjaa fa?” A shagwabe,nujood daketa baza hanci ta dubi widad din batace komai ba,har sai da widad din tadan daki kafadarta

    “Kina jina ina tambayarki don wulaqanci”

    “Aina kasa magana ne,wani shegen qamshi kikeyi widad,ke bakiga ma yadda kika canza ba gaba daya,kinga wani shegen kyau da fatarki tayi?,wai dama haka auren yake amma naji abba na maganar saina gama secondry na shiga university ki higher institute?” Harara widad ta watsa mata,tana ji a ranta nujood din bata da hankali

    “Ke kike ganin haka dalla malama” dariya suka saki a tare,sannan suka zauna saman kujerun falon,suka hau surutu har wani bayajin muryar wani.

    Nan suka wuni a tare,saidai rabi da rabin hankalinta yana kan abbas din,yace mata zaije yakai hajiya dubiya,idan sun wuce ziyarce ziyarce zataji shuru,idan kuma sun gama da wuri he promised her zai dawo gida da wuri.

    Zuwa azahar ta gama yanke abinda zata dafa masa,taja nujood kitchen din,nujood nata tsokanarta

    “Uhmmm,kaga matan aure,Allah har mamakin girkinki nake widad,yaushe kika qware haka?” Murmushi tayi

    “Online classes ne dani sun kusa guda goma,kuma kowanne da irin abinda suke koyawa,dukkansu kuma expert ne,idan suna miki classes kamar a gabanki akeyi”

    “To ya girkin mutuniyarki?,har yanzu yana nan jiya iyau,hala kina dan sanmata idan kika dafa?” Nujood ta fada tana dariya,saboda tuna girkin da aka tarbesu dashi ranar da suka kawo widad din.

    Shuru widad din ta danyi tana nazari,sai kuma ta tuna,da sauri ta daki bayan nujood tana dariya kafin ta tsagaita

    “Oho,da yake ni bacin girkinta nakeyi ba”

    “Ah dole uncle abbas yaji dake wallahi,irin wannan delicious haka,lallai kwanan nan mommyn mimi za’a shiga uku” ta fada tana feshewa da dariya,tana kunna gas ta kalleta

    “Kaman yaya?,saboda girkina yafi nata sai uncle yafi ji dani?” Harara nujood ta balla mata

    “To zauna nan,ke bakisan maza mayun abinci bane?,ki dinga kula daga yau,yadda yakecin abincinki da yadda yakecin nata” nan kuma sai hira ta balle.

    Nujood tadan girmi widad da kadan,ta kuma fita wayo da shiga cikin jama’a,don takanje gidajen qannen hajjaanta hutu,kuma dukansu yaran mata ne,wasunsu suna da abokan zama,tana ganin yadda suke abubuwa,uwa uba qawayenta na makaranta suma kusan suna da yayye aurarru,kuma suma suna zuwa gidajensu,to idan aka hadu hirarsu bata wuce ta aure da gidan miji,musamman yanzun da suka shiga ss,kowacce tana ganin kamar ta zama senior.

    Shuru widad tayi tana biye da hirarrakin nujood,mamaki ya dinga kamata, zuciyarta ta dinga kawo.mata abubuwa da yawa game da hafsat,kenan matsayinsu daya da ita duk da qarancin shekarunta?,duk da ta girmeta amma matsayinsu daya kenan?,duk da bata tambayi nujood komai ba,amma ta tsinci abubuwa da yawa cikin hirar da sukayi.
    Nujood ce ta kama mata aikin,ta shurya lafiyayyar wainar shinkafa da miyar agushi data zuba naman rago wadatacce,don da safiyar abbas din ya aiki yaron office dinsu yayo cefane na duka kayan buqata na gidan,ita dama yawanci idan yasa akayi irin wannan siyayyar kadan yake diba mata,tunda basa wuce kwanaki hudu a bauchin suke komawa,saidai idan wani abunne ya taso.

    Ta taba ganin ya aika an siyo masa wainar,saita gwada yi masa sau daya,duk da bata tashi ba amma tayi dadi ba laifi,ya kuma ci sosai,data tambaya muneera sai taji ashe tana cikin favorite foods dinsa,yanzun kuma ikon Allah sai bata bata kunya ba,ta tashi tayi kyau sosai,tayi saqa saqa a ciki,ta kuma yi laushi,anty madeena ce ta bata wannan recipe din ta gwada,ta kuma sake tambaya a classes din da takeyi.

    Bayan ta gama suka gyare gidan fes tare, nujood ta soma hada kan yaran

    “Yamma tayi yanzun zakuga bala ya iso daukarmu” fuska widad din tadan bata

    “Haba mana nujood,ku bari zuwa magriba” baki ta kama

    “Waaa….niiii?, rufan asiri bazan iya.kallon love din da za’a balle yau ba, bakiji wai irin qamshin daya cika gidan na ba?,har waje wallahi,ina ganin kishiyarki yau saita hadiya yawu ya kusa sau saba’in” ta sheqe da dariya,hakanan maganar nujood ta bawa widad dariya

    “Ki daina sharri wallahi,ba lallai ma ta jiyo qamshin ba kike abunki” ido nujood ta zaro

    “Lallai yarinyar nan bakisan kishiya da kishi ba” harara widad ta watsa mata

    “To yaya babba” sai suka saka dariya.

    Kayan makeup ta hadawa nujood da sauran qannenta,sannan ta bata turare tace ta kaiwa hajjaa,ta rakasu farfajiyar gidan,saida drivern ya iso suka shiga mota sannan ta juya zata koma ciki.

    Kacibus sukayi da hafsat din,ido ta zubawa widad,itama saita zuba mata nata idon,dauke kai widad din.tayi ta wuce abinta,abun da ya qara daurewa hafsat din kai,tabi da kallo mamaki yana cikata,sai kuma ta ja qwafa cikin ranta tana sakin murmushin mugunta

    “Yaro man kaza,yaro baisan wuta ba sai ya taka” ta fada a fili,nishadi yana cika Zuciyarta.

    Ganin duhun magriba ya kawo jiki sai ta lafe a falon tanata duba agogo,sanda taji shigowar motarsa saita narke cikin kujerar tana tsumayin shigowarss,ba jimawa kuwa yayi knocking,ta taso a hankali tana tura baki gaba ta bude masa.

    Ko gama buduwa qofar batayi ba ya shigo ciki,cike da zaquwa ya sanya hannu ya dagata cak ya rungumeta cikin jikinsa yana sansanar kowanne sashe na jikinta,idanunsa a lumshe kunnuwansa na karbar daqon shagwabarta,ya tattara dukka qarfin halinsa ya taka zuwa ciki da ita,suka zube saman kujera,muryarsa na rawa yace

    “Me ya faru baby doll?,kukan na meye?”

    “Uncleeee……” Ta kirashi a narke

    “Ba kai bane,baka dawo da wuri ba,tun da rana nake jiranka” muryarta har tsakiyar kwanyarsa,tattausan murmushi ya subuce masa,ya cusa kansa cikin gashin kanta bayan ya zame dankwalin

    “Uhnnn……inda na dawo me zaki bani?” Ba zato yaji bakinta a kunnensa,da zazzaqar muryar ta din nan ta rada masa wani abu da ya sakashi qanqameta cikin jikinsa

    “Wayyo Alla na” ya fada cikin taushi,saita qyalqyale masa da dariya cikin matsananciyar kunya tana boye fuskarta,hannuwansa duka biyu ya saka ya daga fuskartata yana kallonta cikin tsakiyar idanunta da nashi idanun da suka canza launi

    “Gani na dawo,ko yanzun baby banyi late ba,don Allah kada ki fasa” ido ta lumshe sosai tana sake sakin murmushi,cikin hirarsu da nujood ta tsinci wannan,ashe haka uncle din nata keso yaji ta furta hakan?

    “Naje nayi sallah na dawo?” Ya tambayeta a narke shima,kamar qaramin yaro,saita gyada masa kai,ya miqe cikin qarfin hali yana dubanta

    “Bari nayi alwala.na fito”

    “Na rakaka uncle?” Ido ya zaro

    “Bakyason alwalar tawa ta tsaya kenan?” Saita saki qaramar dariya tana kwantar da kanta a hannun kujera.

    Kafin ya dawo ta gama sallarta itama,haka kawai yau ta tsinciki kanta cikin zumudin kasancewa tare dashi,wani irin sabo kullum zuciyarta ke sake yi dashi,saita miqe ta hada masa ruwan wanka,ba’a dade da.idar da sallar isha’i ba ya sake shigowa.

    Zaman cin abincin yayi bayan ya gama wankan,ya shaqi daddadan qamshin da miyar ke bayarwa,take tsohuwar yunwarsa ta tash,sanda yakai abincin bakinsa kansa qarasa kuncewa yayi,kamar kullum qarawa hannunta zaqi akeyi

    “Ki zabi dukka tukuicin da kikeso na baki na dafa min abinda nafiso da kikayi” murmushi ta saki

    “Kace Allah yayimin albarka,haka ummu ke yimin idan nayi mata wani abun kirki” kai ya jinjina yana sake samun gamsuwa da yarinyar a ruhi da gangar jikinsa gaba daya,tun daga tarayyarsu zuwa yau ya tabbatar ta samu cikakkiyar tarbiyyar da irinta tayi qaranci ga yaran yanzu,shikam zai iya cewa ya tsincik diamond ne a cikin tarin duwatsu marasa daraja can can.

    Cikin lallausar muryarsa data karye ya fara mata addu’a,addu’ar data dinga amsawa tana murmushi,saboda da gaske tayi mata dadi sosai.

    Karar sautin wayarsa ya katse musu daddadan yanayin da suke ciki na wata irin hira me tafi da hankali da tunani,daya duba sai yaga hafsat ce,ya danyi mamaki kadan,duk da dazun daya shiga ya sameta tana sallah,sai kuma bai qara komawa ba,ya bari sai yazo rufe gidan,ransa bai kawo komai ba ya jawo wayar ya daga.
    [3/19, 5:44 PM] +234 808 711 8630: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)
    *Arewabooks:Huguma*

  • Arubuce Ta Ke 83

    Arubuce Ta Ke 83

    Page 83

    “wait…..amma fa da matsala” saita tsaya tana kallonsa da idanuntan nan dake cike da quruciya da rashin wayau a wasu lokuttan,muryarsa ya sassauta sosai

    “Eh mana,wannan abun da gani zai haifar da tashin hankali…….idan nasha ya zamemin matsala babu me saukemin hayaqin da zai tashi a kaina,gashi kedin raguwa ce,first night saida kika ziyarci asibiti” curewa tayi guri guda tana cewa

    “Wayyo Allah ummu na”

    “Wayyo Allah hajiyata,sonta zai kashe miki danki” ya fada cikin murya mai taushi qasa da tata jikinsa yana saki gaba daya.

    Kasa jurewa tayi,saboda bugu da zuciyarta keyi,saita zane ta fice da sauri,ya bita da kallo hade da murmushi,haka auren me quruciya yake da dadi?.

    Wayarsa dake ringing ce ta dawo dashi daga tunanin da ya lula,sai ya daukota yana duba me kiran.

    Suraj ne,yadan shafi kansa kadan kafin ya daga,don yasan sai yasha qorafi.

    Suna gama gaisawa qorafin kuwa ya biyo baya

    “Ban san ko widad din ce ke boye ka ba kuma,tunda dai daa ba haka kake ba” murmushi ya saki yana kurbar smoothie din

    “Yanayin aiki ne kawai”

    “Anyway,next week zamu shigo kadunan da madam”

    “Yayi,aikin ya biyo ta garinmu kenan” abbas ya fada,sai kuma suka fada wata hirar.

    Ranar bai bar gidan ba sai bayan magariba,yana isa unguwarsu ana sallar isha’i,ya tsaya a masallacin layinsu yayi sallar sannan ya isa gidan.

    Kamar ko yaushe,koda meye tayi masa baya fasa shiga sassanta idan ya dawo,ba don komai ba sai don yaransa,ya samesu kwance qasan carfet bacci yayi awon gaba dasu,ya tsallaketa tana zaune tana waya yasa hannu ya kwashesu ya kaisu dakinsu,duk da dakin ba’a kintse yake ba,amma kuma yafi falon data barsu,ya gyara zanin gadon ya kwantar dasu,ya duba laundry basket dinsu da yake cike taf da kaya da uban bedsheet dinsu masu kyau da tsada,amma sunyi datti kuma bata da lokacin da zata tsaya ta hadasu ta zagaya baya inda washing machine yake ta wanke ba,ko ta bayar wa sale yaron gidan ya wanke su ba

    “Allah ya sawwaqe” ya fada a fili,yana raya a ransa gobe zai zauna da kansa ya gyara musu dakin nasu ya fidda kayan ya bayar a wanke musu kafin ya koma,don yaci alwashin ya daina mata gyaran sashe,tunda abun nata sake ci gaba yakeyi.

    Kafin ya fito ta hattama wayar,saita sauke qafafunta dake saman center table tana fadin

    “Sannu da zuwa”

    “Yauwa” ya amsa sama sama yana zama hannun kujera,yayi imanin zaiyi wuya ya zauna cikin kujerar baici karo da danshin ruwa lemo ko fitsari ba

    “A kawo maka abinci?” Ta tambayeshi tana danna waya,sai ya girgiza kai sannan yace

    “Ajjiye wayar nan zamuyi magana” dan kallonsa tayi sannan ta aje wayar tana kallonsa

    “Nace shekararmu nawa yanzu da aure?” Dan jim tayi sannan tace

    “Kamar shida cikin ta bakwai”

    “Good……me yasa har yanzu kika kasa fahimtar zahirin rayuwa hafsa?,me yasa har yau kika kasa gane kina tafka kusakurai da hankalinki ya kamata ace yakai kai kin kuma gyara” fuska ta bata sosai

    “Wanne kuskure kuma nayi?,wai don Allah me yasa bakason zaman lafiya abban mimi?” Da ido ya tsareta,saita kauda nata idon daga kansa,ta sani nashi idanun yafi nata kaifi nesa ba kusa ba,ta hade rai sosai,ya janye idonsa yana miqewa hadi da saka hannunsa a aljihun wandonsa yana kallonta,baisan me yake damun kanta ba,gidadanci ne ko rainin wayo?,komai ka gaya mata ba zata gane ba, batasan maslaha ba batasan fada ba,duka dai dai take daukan kowanne,tunda taqi fuskantar alqibla,bari ya bita da zafi zafi tunda ya fahimci tafi ganewa hakan

    “Tunda baki ganewa kuskure ko laifi……fine,gobe banason na tashi na samu wannan tulin qazantar dake sassan nan,idan ma ke tana miki dadin zama ne a cikinta,to karki sake na samu daki da jikin yarana a yadda na sameshi yau” ya qarashe maganar a zafafe,sannan ya juya da dan hanzarinsa ya fice daga sashen.

    Kamar idanunta zai fado saboda kallon data bishi dashi,kallon da inda yana tsaye ne a gabanta bata isa tayi masa shi ba,taja dogon tsaki kamar zata tsinke harshenta,ta rasa wanne kalar miji Allah ya hadata dashi,taurin kai kafiya da kuma tsatstsauran ra’ayi,dole ta tattare komai.nata ta wuce daki,gwara ta kwanta da wuri ko ta samu ta tashi da wuri ta gyara iya abinda take ganin zata iya,a goben ma idan widad din bata dawo ba to tabbas zata dauki mota taje ta daukota da kanta ta dawo da ita cikin ruwan sanyi da kwantar da kai,ta yadda babu wanda zai fahimci manufarta.

    **********Ranar lahadi,ranar daya zamana saura kwana guda suraj da matarsa suzo,yana gida ranar,don haka duk wasu ayyuka shi ya kama mata sukayi tare,suka gyara kowanne daki yadda zai dace da zaman kowa a cikinsu.

    Dakinta ne na qarshe,sun gama komai tare,ta tsaya hannayenta riqe a qugunta tana kallon yadda ya sauya fasalin dakin tana murmushi.

    Sanda take kallon dakin shi kuma ita yake kallo,wani short rubber wando ne a jikinta,wanda da kadan ya wuce gwiwarta,sai kuma rigar kayan mai gajeran kayan data fidda shape dinta sosai.

    Da wani siririn rubber band kalar kayan jikinta ta daure gashin kanta,hakan ya baiwa doguwar jelarta mai santsi damar reto a bayanta.

    Kusan yaune ranar farko data fara irin wannan shigar saboda aikin da zasuyi,amma iya yau din gaba daya ta hanashi sukuni,duk inda ta motsa idanuwanta suna biye dashi

    “Finished uncle” ta fadi tana dubansa tana murmushi,sai ya mayar mata da murmushinta,yanason ya gaya mata ta debi wasu kayan nata da zatayi amfani dasu ta maida dakinsa amma kuma bayason plan dinsa ya rushe,gwara ya barta a hakan,sannu sannu bata hana zuwa.

    *W A S H E G A R I*

    K’arfe uku na rana su suraj suka iso kaduna,bilkisa matar suraj akwai fara’a kirki da kuma saurin sabo,tun ba yau ba suna hira sosai da widad din ta watsapp,wannan yasa ba wani baqunta can me yawa a tsakaninsu ba.

    A nan falo suka zauna bayan abbas ya shiga musu da kayansu ciki,suka koma balcony din sashen suka zauna sukabar su widad din a falo.

    Basu rufa mintuna ashirin ba aka kira sallar la’asar,saida dukkansu suka bada farali sannan suka zauna zaman cin abinci,su suna balcony din saman lallausan carfet,ita da bilkisa suna zaune a falon,suna ci suna taba hira.

    K’arfe takwas na dare ta shigo dakin da bilkisa ta sauka,rigar bacci ce a jikinta wadda ta sauka har kusa da idon sawunta,saita dora hijabi a kai wanda bai wuce qugunta ba.

    Da murmushi bilkisa dake gaban mudubi tana fa shafe shafen turaruka ta waiwayo tana amsa mata,widad ta qaraso tana hayewa saman gadon gami da jan pillow

    “Na zaci har kin kwanta” kai ta girgiza

    “Ina ni ina bacci mai gidana bai dawo ba” qaramin murmushi widad ta saki tana rayawa a ranta

    “Kamar wani qaramin yaro” duk da cewa ita dinma tun dazu take leqawa ta window idan taji motsi taga ko uncle din nata ne,tunda suka fita bayan sun gama cin abinci basu dawo ba.

    Duk da sun sha hira sosai da balkisa,ta kuma debe mata kewa amma sai takejin gidan gaba daya wani iri babu dadi

    “Nima har na fara jin kamar bacci bacci” ta fada tana maida pillow din saman gadon zata kwanta,sai bilkisa ta juyo da sauri tana dubanta

    “Aah…..shi kuma abbansu ahmad din na kaishi ina?”

    “Zasu kwana tare da uncle fa” ta fada adan shagwabe

    “Aah wlh ban gayyato ki ba,haka kawai kisa nayi baqinjini wajen yallabai yana ganin mutuncina?,daga zuwana na rabashi da amaryarshi”

    “Mom Ahmad wallahi kema kin faye tsokana” widad ta fada tana gyara kwanciyarta,bilkisana qoqarin saka wandon sleeping dress dinta tace

    “Banda quruciya dake dawainiya dake….. yaci ace kin karanci irin kallon da yake binki dashi duk sanda kika gifta ta gabanshi,ina tsoro nan gaba kada yallabai ya fara tafiya yana kiran sunanki,idan haka ta faru kam hafsat inajin hadiyar zuciya zatayi ta mutu”

    “Kai mom Ahmad kai anty bilkisa” widad ta fada tana dariya sosai,don ita dariya ma maganar ta bata

    “To ita kuma mommy hafsat me zai sakata mutuwa don kawai uncle na kiran sunana?” Tambayar data sanya bilkisa maida dubanta sosai ga widad,da alama dai har yau batasan wace kishiya ba,batasan kuma kishi ba,uwa uba batasan wace hafsat sani na badini ba,kallon zahiri take mata

    “Kishiya irin hafsat ba zasu taba son suga miji irin uncle dinki.yana sonki ba,ba zasu taba so suga kina masa wani abu da zaiji dadi ba”

    “Amma mom ahmad,ni bata taba nunamin komai ba” kallonta sosai ta sakeyi

    “Ta gama yi miki komai din ai ba tare da kin ankara ba,saboda tasan ba lallai tunaninki ya kawo miki komai ba a kai” Shuru widad tayi tana juya maganar,zancan da suka taba yi da anty madeena ya dawo mata sanda take gaya mata ba gaskiya bane abinda hafsat din ta dinga gaya mata tana tsoratar da ita,to me hakan ke nufi?,wannan shine kishin?,idan kuwa shine yafi kama da HASSADA kawai

    “Idan kina tantama daga yau ki sake mata dukkan aikin da kike mata…..ki kula da uncle dinki,don nasan har yanzu idan ta samu dama sakaki aiki takeyi” maganar bilkisa ta saka widad a tunani sosai,kafin tace komai muryoyinsu sun bayyana a falon alamun sun dawo.

    Tare suka fita da bilkisa din,saidai suraj din kawai suka samu yana shirin shigowa ciki,dole widad ta yiwa bilkisa sallama ta wuce nasu dakin.

    Ta tura dakin ta shiga,baya ciki amma ga kayanshi nan saman gadon,sai ta qarasa a hankali ta debesu,ta ninkesu sannan ta zubasu a laundry basket,takalman ma tayi musu waje,sai ta koma kan sofa bed ta zauna ta kunna data dinta ta shiga watsapp tana duba saqonni.

    Qofar bandakin ya bude ya fito,daure da towel da ya daurashi daga qugunsa,duka duka tsahonsa kuma iya gwiwa,duk wata qirar jikinsa ta bayyana a waje sosai,qaqqarfan jiki daya ginu da excercise.

    Bata zaci a haka ya fito ba….wannan yasa ta daga kai,saidai suna hada ido tayi saurin maida idanunta kan wayar tana raba idanu.

    Karamin murmushi ya saki,har cikin zuciyarsa yana jin dadin yadda ta kasance,amma a fuska bai nuna ba,yadan basar duk da yadda taketa fusgar hankalinsa,don already ta cire hijabin ta ta ajjiye don tasha iska,yadda ta nannade gashinta yayi masifar jan hankalinsa.

    Sannu da zuwa tayi masa tana ta babbasarwa,ya amsa mata yana janta da hira,yayi kaman bai gane ba,ya tsaya gaban madubi yana shiryawa yana satar kallonta ta ciki,cikin dace ya dinga kamata itama tana satar kallonsa,amma duk sanda ya gani din saita bagarar,abin ya dinga bashi dariya sosai,amma ya dinga cinyewa cikin miskilancinsa,har ya gama shirinsa tsaf cikin dakin ya kuma zauna ta zuba masa abinci ya soma ci.

    Yana cin yana kallonta da lumsassun idanunsa har ya kammala,cin abincin da da wankan sun ja masa kusan awa biyu,zuwa sannan jikinsa ya gama saki,gaba daya muradinta yakeyi,sai ya miqe,ya zare kayan jikinsa,yabar iya boxer kawai,ya koma saman gadon ya kwanta rub da ciki yana lumshe idanunsa.

    Shuru ya ratsa dakin,sai ya bude idonsa a hankali ya zube a kanta,daga yadda take zaune yasan itama kwanciya takesonyi amma tana shakkar rabarsa

    “Baby….” Yayi kiranta a tausashe,muryarsa can qasan maqoshinsa,saita daga fararen idanuwanta ta kalleshi, idanunsu suka gauraya waje daya,wani abu taji ya taba zuciyarta sosai

    “Am very tired……..zo kiyimin tausa please baby” ya fada yana narkewa hadi da yin fuskarsa tausayi,idanunsa suna lumshewa saman fuskarta,yana jin kamar yakai gareta ya fusgota.
    [3/18, 4:01 PM] +234 813 343 4840: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)
    *Arewabooks:Huguma*

     

  • Arubuce Ta Ke 80

    Arubuce Ta Ke 80

    Page 80

    Tsaye yake gaban mirror yana taje kansa,shirye yake cikin mulberry silk da ya kwanta sosai a jikinsa,ya kuma fidda kyan fatarsa data wadata da tsafta da kuma hutu,jikinsa na fidda sassanyan qamshin turarensa.

    A nutse take takowa zuwa qofar dakin nasa,tura qofar a hankali saita tsaya tana kallonsa ta cikin madubin ba tare data saki hannun qofar ba,hakanan bata koma ba bata kuma shigo dakin ba.

    Idanu ta zuba masa sosai tana kallonsa,yayi bala’in yi mata wani sassanyan kyau,a yau din quruciya kyansa da haduwarsa sun sake fito mata muraran fiye da ko yaushe, shigar ta karbeshi,duk da dama zaiyi wuya ya saka kaya a jikinsa basu karbeshin ba,ta’ammali da uniform saboda yanayin aikinsa ya sanya yafi mu’amala da manyan kaya akan qanana,saita saki qofar a hankali ta goye hannunta a qirji taci gaba da kallonsa.

    A nutse ya sauke idanunsa a kanta,shi dinma shigarta ta yau ta fusgi hankalinsa sosai,abaya ce a jikinta ruby color,saita dora dan qaramin Vail a kayanta dusty rose,dan siririn pink lips dinta na fidda qyallin lipstick data shafa musu, fuskar ta ta kwanta da color din powder din data shafa

    “Ma sha Allah” ya fada ta hanyar motsa labbansa,ya ajjiye comb din hannunsa a hankali,yana so yau ne ya kamata real tana satar kallonsa,abinda ya lura fa koya kenan cikin satin nan,idan kuma ya fada saita waske harda qananun hawayen ita ba kallonsa take ba.

    Batayi zato ba taga ya waiwayo gaba dayansa,idanunsu suka sarqe cikin na juna,kunya ta kamata,tayi taku biyu baya zata koma ya dakatar da ita

    “Don’t move baby” yayi maganar muryarsa nadan sarqewa,ganin da yayi mata a yanzu da idanu sai yake ganin kamar madubin ashe ya rage kyan da tayi,turarenta da ko yaushe yake tsaye masa a rai ya iska na kadoshi kadan kadan yana cakuda da nasa yana bayar da wani kalar qamshi na musamman,sai ya cira qafarsa ya soma takawa a hankali zuwa inda take, qafafunsa na nutsewa cikin lallausan carfet din daya malale dakin dashi,bazai iya kauda kai ba a yanzun,yana qishirwa wadan nan labban nata,yanason yaji duminta sosai…….wanda rabonsa da hakan tun randa ya maidata tasa halak malak,duk kuwa da cewa gado daya suke kwana,amma bai sake neman komai daga gareta ba, saboda yana son fidda duk wani sauran tsoro nasa dake ranta.

    Qugunta ya kamo da dukka hannayensa biyu ya matso da ita jikinsa sosai har jikin nasa yana gogar nata,gabanta ya fadi sosai ta lumshe ido tana son hadiye tsoronta

    “Bude idon na gani….. please my baby” ji tayi ba zata iya tsallake umarninsa ba,sautin muryarsa gaba daya ta kashe mata jiki,ta bude manyan idanuntan fes a kansa,sai yaja numfashi da kyau,yasa yatsunsa biyu ya kama kumatunta yadan ja kadan

    “Inason wadan nan idanun,inajin kamar na hadiyesu” ido ta fidda fuskarta na washewa

    “Ana cinye idon mutum uncle?” Ta fada a sakarce,sai ya saki murmushi kawai yana tunanin yaushe widad din tashi zata gama girma ne,ya girgiza kansa a hankali,yana jin komai na jikinsa yana amsawa

    “Ba’a cinye ido,amma ana iya lasheshi,ana lashe kunne,ana lashe baki ana lashe harsh……..”

    “Stop uncle,wallahi kunya nakeji” ta fada a narke kamar zata sanya kuka,yadda fuskarta tayi ta sake tafiya da imaninsa,mitsitsin bakinta data turo gaba ya kalla,zuwa yanzun gaba daya burinsa ya tattara a kai,a tausashe yace

    “Bari na nuna miki ki gani” bai qara ko second biyu ba ya hade bakinsu waje daya,cikin wani irin lallausan salo da kuma qwarewa yake aike ma qwaqwalwarta saqo ta hanyar bata zazzafan french kiss daya birkita tunaninta gaba daya,ya kuma zare mata kowanne kuzari da qarfin hali da take jin tana dashi.

    Ba inda bai aika da harshensa cikin bakinta ba,ya lasheshi tsaf ciki da waje sannan ya saketa yana jan numfashi.

    Taga taga tayi zata fadi saboda yadda jikinta yayi laushi gaba daya,yayi hanzari da sauran nasa kuzarin ya tarota yana kallon qwayar idanunta,sai ya jinginata da jikinsa,hakan kuwa ya mata,don boye fuskarta tayi a qirjinsa,wata kunya tana dawainiya da ita.

    Qaramar dariya mai hade da ajiyar zuciya ya sake

    “Good baby…..da alama kin fara daukan haske ko?” Ya fada yana leqa fuskarta,saita kebe masa baki ta soma ‘yar sheshsheqar kuka,har cikin jininsa ta aike masa da wani saqo daya huda zuciyarsa,sai ya dinga jij sheshsheqar tata kamar da manufa,yadan janye jikinsa kadan don bayason abun yaci gaba da tafiya,amma saita riqe hannunsa tana sake neman wajen buya a jikinsa,don gaba daya ya gama aza mata nauyinsa,amma ta lura shi ko a jikinsa,abinda yayi mata a yanzun tana jin kamar ba zata iya sake kallonsa ba har abada

    “Ohhh…..kina buqatar qari kenan?” Kai ta girgiza da sauri,saita sakeshi taja da baya tan lalubar qofa ta fice da sauri.

    Da kallo ya bita kamar wani sakarai harta fita din,ya koma da baya ya zube gefan gado,wannan din wani dadadden mafarkinsa ne da a yau ya cika,he loves kisses sosai,yana bala’in so body contact da iyalinsa qwarai,amma hakan bata samuwa sam sam a gareshi,saidai yayita fama da hakan a tarin mafarkansa,yayi loosing abubuwa masu yawa da yasha tsarawa kansa a tsarin rayuwar gidansa,saidai da daya da daya komai yake rugujewa ya rushe,tsarinsa da ra’ayinsa yayi nisa qwarai dana hafsat,wasu abubuwan ma tana kallonsu as bata lokaci,ko kaiwa maqura,yana jin kamar a yanzun zai gina dukka mafarkansa ya kuma rayasu in reality.

    Gaba daya ta saka jikinsa yayi laushi,bayajin zai iya driving dinsu daga kaduna zuwa bauchin,bashi da wannan qarfin kwata kwata,don haka ya ciro wayarsa ya kira samuel yace yazo zasu wuce bauchi yanzu yanzu.

    Minti goma kacal samuel ya kirashi kan ya iso,already motar dama a wanke take,hakanan dukka kayansu suna ciki,sai ya miqe yana gyara rigarsa,ya dauki agogo da hularsa duka ya sanya,ya sake fesa turarensa,sannan ya kwashi wasu documents dake cikin wata folder ya fito.

    A gaban fridge ya sameta tsaye tana shan ruwa,ya taka a hankali ya tsaya a bayan nata yana dora hannunsa saman nata hannun da ta riqe ruwan dashi tana sha,hannun ya qawatu sosai cikin wasu siraram banguls kusan guda goma ruby color da duka haska farar fatarta datayi wani fresh.

    Qwarewa tayi, saboda gaba daya bata ji takunsa ba,ya sanyata a kafadarsa yana dan dukan bayanta harta daina tarin sannan ya janye jikinsa kadan

    “Ki dauko komai?,samuel yazo xamu wuce” kai ta jinjina masa alamar eh,sai ya miqa mata document din hannunsa,ya ja mayafin dake kanta ya soma nada mata shi.

    Baya ya danja ya kalleta,she looks very gorgeous,sai yaji kishinta yayi bala’in kamashi,har yaji kamar dama bai kira samuel ba.

    Hannunta ya kama ya isa da ita gaban wani dan fashion mirror dake maqale cikin falon, murmushi ya subuce mata,ya akayi ya iya rolling haka?,ta cikin idanunta ya karanci tambayar dake cikin zuciyarta,sai ya saki murmushi

    “Mimi da nawwara” a taqaice ya amsa mata amma ta gane,saita kauce gefe daya saboda kallon da yake jifanta dashi ta madubin yana mata nauyi da yawa.

    Kafin su fita ya kira samuel ya masa aiken dole,wai fita dan kantin dake kusa da gidan ya karbo kasa biro,kafin ya dawo suna cikin motar,yana isowa yace ya aje masa wajensa zai karba,don kada ma.ya juyo har ya ganta,ya amsa masa a ladabce ya kunna motar suka fice daga gidan.

    Tun basuyi nisa ba bacci ya soma fusgarta,sai yayi mata majingina da kafadarsa sosai,ya lalubo hannunsa ya sanya a tafin hannunsa ya hadesu waje daya.

    Kusan awa biyu ta kwashe tana bacci,sanda ta farka saita janye jikinta daga nasa cikin jin nauyi,ya murmusa kadan yana dubanta

    “Kin more min kafada,sai naci tararki” kafada ta noqe tana dariya cikin jin kunya.

    Awa biyu da rabin suka shiga garin bauchi,sai tadan dubeshi har yanzu hannunsa yana cikin nata

    “Gidan hajiya zaka saukeni” ta fada qasa qasa,don sam sai taji bata qaunar zuwa gidan.

    Waiwayowa yayi ya zube mata manyan fararen idanunsa yana kallonta qasa qasa,cikin zuciyarsa yake son qiyasta yadda hakan zata faru,sai kuma ya girgiza kansa a hankali kafin ya dauke idamunsa a kanta

    “Ba yau ba” ya fadi kansa tsaye,don baya jin zai iys nesa da ita

    “Don Allah uncle” ta fada a mugun shagwabe kamar zata saki kuka

    “No,Baby” komawa tayi ta lafe jikinta a sanyaye tayi shuru,tafison gidan hajiyan,tafi qaunar zama a can,saita fara sharar hawaye kafin ta sake masa siririn kukanta.

    Idonsa ya lumshe yana jin wani abu mara dadi yana taba zuciyarsa,irin abinda bai tana jin kamarsa ba,duk da dama shi din kusan weak point dinsa kenan

    “Is okay” ya fada yana sanya hannunsa cikin nata,sannan ya bawa samuel umarnin canza titi zuwa titin da zai kaisu unguwar gida dubu.

    Ajiyar zuciya ta sauke,ta sake lafewa tana dan sakin murmushi

    “Na gode” waiwaya yayi a hankali ya kalleta,sai ya sanya hannu yaja hancinta

    “Karkiyi saurin godemin,don idan munje ba lallai bane na barki ki kwana ba” baki ta tura gaba,sai ta kwantar da kanta ba tare da tace masa komai ba,ya sake sakin qaramin murmushi yana kallon hanya hadi da matse hannunta sosai kuma a tausashe cikin tafin hannunsa,can qasan zuciyarsa yana jin wani abu mai qarfi a kanta yana sake ginuwa.

    Ita ta fara shigewa gidan hajiyan cike da karsashi, zuciyarta fal farinciki,don kusan wata guda kenan bata zo ba,zuwanta na qarshe har suka koma batazo gidan ba.

    Su biyu ne falon,ita da gwaggwo fanteka suna taba hira,sun gama cin abinci kenan tayi sallama,sosai farincikin dake fuskar hajiyan ya bayyana,ta amsa sallamar tana cewa

    “A’ah,mutan kaduna…..irin wannan ba zata haka?”

    “Aiko dai,haka amaryar abas din ta fara canzawa,ah lallai yarinya taji kiwo” gwaggwo fanteka data kama haba cike da jin wani abu a ranta me kama da qyashi qyashi ta fada,maganar da ta yiwa widad din nauyi,karon farko da kunyar hajiya ta kamata,musamman da ta tuna abinda ya wanzu tsakaninta da abbas din,sai take ganin kamar ma kowa yana iya karantar hakan,don haka tun daga dan nesa dasu ta zube tana gaidasu.

    Cikin kulawa hajiyan ta amsa, gwaggwo fanteka kuwa ta zuba mata ido tana kallonta,sosai widad din ta canza,ta fara cika ta kuma yi kyau abinta,ta amsa tata gaisuwar tana sauke numfashi hadi da gyara zamanta

    “Kundai tafi kunbar uwar gida da jiran gida ko?” Ta jeho widad da batasan ma kan asalin abinda kae faruwa ba tambaya

    “Uhmmm,ina ruwan widad,ita da batasan komai ba akai” hajiya tayi saurin karbar zancan

    “To ai shikenan,Allah ya kyauta” ta sake fada tana gyara zamanta,dai dai sanda abbas yayi sallama ya shigo parlor din,qaninsa muneer yana biye dashi da babban ledar da muddin da ransa da lafiyarsa baya gaza shigowa da hajiyan tashi ita.

    Washe baki gwaggwo fanteka tahau yi tana sake gyara zama,lallai yau din ta shigo a sa’a,tasan cewa shar da ita zata fita,harda ita wajen marabtar abbas din,ya duqa ya gaidasu cikin girmamawa sannan ya koma ya zauna sosai daura da hajiyan tasa.

    Miqewa gwaggwo fanteka tayi tana cewa

    “Ni bari na wuce gida,naga la’asariya ta kusa”

    “Ki tsaya mana ki karbi tsarabar taki?”

    “A’ah haba,kya dai aiko muneera ko muniru ya kawomin,yallabai Allah ya huta gajiya” hannu abbas ya sanya a aljihunsa ya fidda sabbin ‘yan dubu dubu ya miqa mata,tasa hannu kuwa ta amshe babu tayi tana zuba godiya.

    Nan falon hajiyan yayi zamansa suna hirar yaushe gamo,duk danda widad dake kitchen tare da muneera ta gifta sai taji ranta ya mata sanyi,ta kuma sake godewa Allah,kallo daya ta yiwa abbas din harma da widad din ta karanci akwai wani gagarumin sabon canji cikin rayuwarsu,walwalar abbas din ta qaru,idan ma ba idonta bane ke mata gizo har ‘yar qiba taga yadan qara,abinda bata taba gani a tare dashi ba,sannan duk sanda widad din zata gifta idanuwansa suna biye da ita,kamar yadda itama duk sanda ta ratso ta falon saita saci kallonsa.

    Ana idar da sallar la’asar yayi shirin wucewa gida,yace ta fito su wuce,amma saita sakar masa darunta tana maqale wuya,idan zata shekara tana masa wannan shagwabar yanason gani,ba kuma zai gaji ba,tilas ya haqura ya barta bayan hajiya ta sanya baki,ya wuce gidan shi kadai,amma cikin jikinta da zuciyarsa duka sai yakejin wani iri babu dadi,kamar ya baro wani b’ari ne na zuciyarsa a wani waje.
    [3/18, 3:06 PM] +234 903 685 1413: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)
    *Arewabooks:Huguma*

  • Arubuce Ta Ke 92

    Arubuce Ta Ke 92

    Page 92

    Kasa ci gaba tayi da lissafa kudin,idan tayi gaba sai ta dawo baya,dole ta zube kudin tana jin kamar ana sukar zuciyarta da mashi,ta miqe tana gyara daurin zaninta da dan qaramin cikinta wanda ya fara fitowa kadan,duk da duka duka bai wuce wata uku ba,amma saboda tana da tumbi har ya fara bayyana kansa.

    Tana doso su tana qare musu kallo,dukkansu daga shi har ita sun canza,kamar wadanda ke rayuwa a wajen nigeria ba

    “Hafsatu kina me?,kina me kika zauna kina gadin gida?,kina meye kika zauna?” Zuciyarta ta fara raya mata,take taji ranta yayi mugun baci,kamar ma kada ta isa inda suke,tunda tun tsaiwarsu babu wanda ya fahimci wanzuwarta a wajen.

    “Sannu da zuwa” ta fada ciki ciki,qamshin turaren widad wadda ta tsaya daura da ita na cika mata hanci yana kuma qara iza wutar kishinta a zuciyarta.

    Waiwayawa yayi ya dubeta,har ya daga hannu zaiyi welcoming nata kamar yadda suka saba da widad,sai kuma ya tuna yanzun zata ce yara,ko ta canzawa abun akala,yayi qoqarin sakin qaramin murmushi yana kallon yadda ta canza,cikin tun baiyi nisa ba ya fara birkitata

    “Sannu mom mimi,ya gida ya jikin?” Ya tambayeta,duk da kullum sai ya kira yaji jikin nata

    “Alhmdlh” ta furta tana qoqarin saisaita kanta,saboda wani mugun muzanta da taji tayi tsaiwar da tayi kusa da widad din,ta glass din motar da suke tsayen take satar kallon mugun tazarar banbancin dake tsakaninsu da ita,saita zama kamar wata mai aikin gidan,don haka ta janye jikinta a dabarance zuwa gefe sanda widad din ke gaidata,gaisuwar data qona mata rai,don duka hankalinta nakan mimi tana janta da wass,ta amsa mata ciki ciki.

    Motar ya rufe yana ci gaba da riqon nawwara a hannunsa,ya juya zuwa sassansa yana yiwa naawara waqar da ya saba yi mata hafsat din tabi bayansa da sauri

    “Uncle” widad tayi kiransa da narkakkiyar muryarta,ba abbas da aka kira sunan shi ba,hatta da hafsat sai da ta tsaya cak,yaji kiran har jikinsa duk kuwa da ya saba,amma yau sai yaji kamar muryarta ta qara zaqi

    “Kayana please uncle,nagaji part dina zan shiga na huta”

    “Hutu” hafsat ta fada a ranta

    “Bai kamata acena qyale ta har tana samun damar hutawa cikin gidan nan ba”hafsat din ta fada a ranta,batasan ya akayi ta barta harta ajjiye dukka wani aiki da take mata ba

    “Munyi haka ne dake?” Ya fada yana narke mata shima da salon da ita ta koya masa,sai hafsat din ta daga kai da sauri ta kalleshi cike da mamaki,abbas din ke abu kamar wani qaramin yaro?.

    Baisan me akeyi ba,don idanunsa na ga widad

    “Alqawari ne zan cika Allah uncle” ta fada tana maqale kafada

    “Alright” ya amsa mata yana miqawa hafsat nawwara da nufin ta riqeta

    “Ajjiyeta mana” ta fadi cikin zafin zuciya, ganin yadda ita yakewa maganar,amma duka hankalinsa na kan widad din,baice komai ba ya juya da nawwara a kafadarsa ya daukar mata luggage din yana biye da ita a baya har zuwa sassanta.

    Da idanu ta rakasu,wai me yake faruwa ne?, yaranta ma farinciki suke da zuwan yarinyar ne?,ga wani abu me girma data lura yana gilmawa cikin idanuwansu shi da ita.

    Ko kafin ya dawo tuni ta tsufa cikin falonsa,tunani yayi mata katutu,koda ya shigo falon ta daga kai ta dubeshi sai taji gaba daya ta raina kanta,ga laulayi daya sanyata ta kwantsame ta fita hayyacinta,gefe guda rashin gyaran da bata daukeshi a bakin komai ba shima ya taka rawa wajen lalacewar tata.

    Kusan yinin ranar cikin qunci ta yishi,tana aikace aikacen da ba kasafai ta fiya yinsu ba sai abbas din yazo tana fama da qunci,itakam widad koda ta isa sashenta zagewa tayi ta gyarash fes,yaran na biye da ita har ta gama,ta kama yaran bisa radin kanta tayi musu wanka,tana jin dadin yadda yaran ke qaunarta,a nan falonta ta barsu bayan ta dora aninci mai sauqi,ta shiga itama ta sake wanka.

    A gaban madubi ta tsaya daure da towel tana kallon kanta,ko ina na jikinta ya fara cika,abinda yaketa bata mamaki kenan,hasken data qara ya ninka nata nada,tasan bata canza mai ko sabulun wanka ba bare tace ko sune suka saka,don kanta ta gaji da kallon kan nata,bata kuma gano dalilin wannan canjin ba saita tabe baki kawai taja manta ta fara shafawa.

    Hafsat din na gyaran sashen shi kuma yana gyaran closet dinsa,duk da yasan zaiyi wahala gobe widad din bata gyara ta ba,amma kuma yana tausayinta,yana ganin kamar aikin yana mata yawa,don sanitation irin wanda yakeso take a sassan nasa bayan hafsat ta gama jiqa jiqarta.

    Baisan ma ta gama ta fice ba sai daya gama wanka yana neman wasu qananun kaya nashi,ya tuna suna cikin akwatin widad din,dole ya dora jallabiyya saman towel din dake daure a qugunsa ya wuce sassan nata don ya ciro kayan.

    A falo ya tambayi su mimi antynsu,sukace tana ciki,ya wucesu bayan ya sake canza musu channel zuwa mbc 3.

    Sanda ya buda qofar dakin nata ta zame towel dinta tana saka brassiere,tsaf ya qare mata kallo ta cikin mudubin yana jin numfashinsa yana sauyawa,don komai ya fito masa muraran,komai na widad din sake daukan hankalinsa yakeyi kowacce rana,sai yaji ya kwadaitu da son jin duminta cikin jikinsa,don haka ya taka a hankali har ya isa gareta,yayi caraf ya riqe towel din sannan ya fincikota a tausashe zuwa jikinsa.

    Tare suka sauke ajiyar zuciya shi da ita,ya zaci zata nema qwacewa ko zame jikinta,sai yaji tayi luf cikin qirjinsa,qamshin sabulun wankansa yana mata dadi sosai har zuciyarta,wannan ya bashi damar aiwatar da abinda zuciyarsa ke kwadaita masa hankali kwance,har sai da taji yana niyyar zarmewa sannan ta zare jikinta tana tuna masa su mimi dake parlor.

    Da jirkitattun idanunsa da suka sauya launi yake dubanta tare da tayata daura towel dinta da ya zame,daurin gaba yayi mata,ya cukuikuye towel din a tsakiyar qirjinta yana duban wajen,sai tasa hannunta guda daya ta rufe,daya hannun kuma ta jawo hijab dinta dake gefe ta soma yunqurin sakawa,ya saki siririyar dariya yana cewa

    “Please mana,minti kadan fa zan dan kalla saiki rufe”. Ya soma kicin kicin qwacewa ita kuma tana nade kanta a ciki tana dariya,da wannan har ta sake komawa jikinsa.

    Ganin aikin take kamar zai kasheta,ga laulayi gaba daya jikinta babu cikakken qwari,don haka ta tsame hannunta daga yankan salad da takeyi ta nufo sassan widad din.

    Tun a hanya take kwatanta da yadda zata fuskanceta do kada ma taga sassauci a fuskarta ta nema kawo mata wargi.

    Bin ko ina na falon ta dinga yi da kallo,ko ina fes kamar yadda abbas yakeso,ya koya mata kenan,tsinanniyar tsaftar nan tasa,taja mugun tsaki tana tambayar su mimi widad din

    “Tana daki,yanzu abba ya shiga kiranta” wata mummunar faduwa gabanta yayi,abbas kuma?,me yakeyi a dakin?,bayan yau din kwananta ne?,ta gama masa wahala daga kaucewarta har ya baro sassan?,cikin mamaki zafin zuciya da kuma kishi ta doshi dakin,batayi wata wata ba ta murza handle din ta tura da qarfi ta shiga,shigar da batayi mata dadi ba sam,shigar da sai da taji kamar kanta zai tarwatse,abbas dinta widad din kwance a jikinsa suna qyalqyala dariya,duk sun yiwa shimfidar gadonta squeezing.

    Tare suka daga kai suka dubeta,saita kasa jurar ganinsu ta soma girgiza kai,ga widad kuwa mo gezau batayi ba,tadai ci gaba da janye hijab dinta daga hannunsa tana cewa

    “Laaa,mummyn mimi wallahi bamuji sallamarki ba,uncle ne,yana nan yana…….” Ido ta runtse da sauri taja baya,ta kuma buga qofar da kyau,gudu gudu sauri sauri ta fice daga sassan kuka yana kubce mata.

    “Yana nan yana me uncle din?” Abbas ya fadi yana jefa mata hararar tsokana,can qasan ransa a bace na yadda ta kutso mata har bedroom dinta ba tare da sallama ko neman izini ba, dariya ta qyalqyale dashi,duk.da qasan ranta taji haushi,ta riga ta saba da dabi’ar yin sallama kafin ta shiga waje,amma ita hafsat din qatuwa da ita batasan tayi ba?

    “Ba komai” ta amsa masa tana dariya,saiya tsaya kawai yana kallonta yanajin wani farinciki yana wanzuwa cikin rayuwarsa,tsahon seconds sannan ya miqe yayi kissing goshinta,ya qarasa akwatin ya dauki kayansa yana tsokanarta ya fito.

    Yana dosar dakinsa ya jiyo sautin kukanta,ya girgiza kai kawai yanajin takaicin hafsat din,yana saka kansa cikin dakin ta daga kai tana dubansa,idanunta sharkaf da hawaye,tasan halinsa sarai,miskili ne na qin qarawa yaso,ganin yayi.kamar.bai ganta ba ya nufi dressing mirror dinsa saita buda baki a zafafe

    “Na gode,na gode sosai da cin fuskar daka yimin,yau kacal amma harka fara satar kwana na kana kai mata?” Kamar bazai.amsata ba har ya gama fesa turarensa bayan ya fidda jallabiyyar jikinsa,sai a sannan taga towel kawai yake daure dashi, zuciyarta ta sake fusata qwarai,ya juyo ya dubeta

    “Ina kwanan yake?,ina cewa rana ce yanzu?,da kika shiga kuma wani abun kikaga munayi?” Tambayoyin nasa sai taji gaba daya na rainin wayo ne

    “Kayi laifi amma kana yin kamar bakayi komai.ba abban mimi?” Ta fadi tana nuna qirjinta da yatsanta,zare towel din ya qarasa yi yana sanya kayansa,sai da ya gama tsaf har sannan tana zaune tana dubansa,ya dawo gabanta ya tsugunna yana kallon qwayar idonta,ya sauke idanunsa zuwa ga hannuwanta da farcenta ya dan soma taruwa,ga ‘yan qananun datti nan sun fara shiga qasan farcen,sun nuna kansu ne saboda yadda hannun da farcen suka kode dalilin rashin digon lalle ko kadan a jikinsu,abinda yafi tsana kenan ya gani,shi yasa sanda yake bauchi da kansa yake daukarta ya kaita gidan qunshu ya ajiyeta ya kuma bar mata kudi masu dan yawa akan ayi mata,amma da wahala idan ya kaita sau goma ayi sau uku saita kawo uzuri tace layi yayi yawa bata samu ba,wani lokaci ma kafin yazo daukarta ta hayo motar haya ta dawo gida,yasan kuma tabbas kudinta kawai take karbewa daga wajen mai qunshin,a yanzun yanason kama hannun nata amma yanajin wani iri,tun daga ranar da widad ta fuskanci me son lalle ne bata sake zama hannunta haka ba,hasalima bata rabo da sargen da take sawa yatsunta idan bata samu lallen ba,abinka da farar fata,mugun kyau yakeyi mata,wani zubin har tukuici sai ya ajjiye mata.

    Duk da haka ya kama yatsun hannun nata yadan ja kadan yadda zata fahimci zancan yace

    “Dani dake waye yafi wani laifi?,Allah da kansa fa cikin qur’ani yake cewa ‘yaku wadanda kukayi imani,kada ku shiga gidajen da ba naku ba har sai kun nemi izini kunyi sallama akan ahalin gidan,wannan shine mafi alkhairi a gareku,idan ma baku samu kowa ba a cikinsu gidajen kada ku shiga har sai an muku izini,idan kuma akace ku koma ku koma’ kinga anan kin sabawa koyarwar qur’ani da sunnah” tunda ya fara maganar ta zuba masa ido tana hawaye,yau gidanta ake cewa ba zata shiga duk inda taso ba saita nema izini saboda ya ajjiye wata

    “Yanzu abbas gidana kake kafamin wadan nan sharuddan a kansa?”

    “Ya salam”ya fada yana lumshe ido takaici yana kamashi,wacce irin qwaqwalwa take da ita,yana gaya mata Allah da annabi tana gaya masa molanka da son zuciyarta, kafin ya buda idanun ta dora

    “A jikinka fa na sameta,ranar kwana na,kaci amanata kanason juya laifin kaina,wallahi sai yanzu na gane dalilin da ya sanya yarinyar nan ta fara rainani,kana raba mana kwana,kana duk abinda kakeyi dani da ita,tana shirme kana biye mata shi yasa take kallon kowa a banza…..”. Tsam ys miqe

    “Excuse me”ya fada a taqaice yana rabata ya wuce,don bazai iya ci gaba da daukar rainin hankalinta ba,kamar yadda ya fuskanci gaba daya ba zata taba gane abinda yake nufi ba.

    Gaba daya ranar ta bata ta da kuka da takaici,taji a ranta ta riga ta gama yin sake,saidai har yanzu akwai sauran dama da zata nunawa yarinyar ita ba kanwar lasa bace.[3/21, 3:59 PM] +234 813 343 4840: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)
    *Arewabooks:Huguma*