Arubuce Ta Ke Hausa NovelHausa Novels

Arubuce Ta Ke 68

Sponsored Links

Page 68

A farfajiyar gidan ya cimma yaran suna wasa,ya tsugunna suka dafeshi gaba daya ya miqe dasu,yau din ba yabo ba fallasa,basuyi datti ba amma kuma bai samesu fes yadda yakeso ba,dukkansu kansu a tsefe yake a daure da band,yana rungume dasu a jikinsa suka sanya kai cikin falon dake sassan hafsat din.

Shima yau dai falon babu laifi,saboda babu dattin,amma bawai kar kar yake ba,yaji dadin hakan har qasan ransa,ya kuma tsinci kansa da fatan samuwar canji daha gareta da kuma dorewar dabi’unta.

Bata parlor din,don haka ya zarce bedroom din nata kanshi tsaye,har yanzu yaran suna kafadarsa suna masa surutu,ya tura qofar dakin,dai dai sanda ta waiwayo suka hada ido,tana tsaye gaban mudubi,saita dauke kanta tana amsa sallamar,jikinta sanye da wata koriyar atamfa riga da fallen zani

“Sannu da zuwa” ta fada cikin careless,kamar wanda yaje qofar gida ya dawo,bai amsa mata ba sai daya sauke yaran a qasa,ya saka hannu a aljihunsa ya fidda chocolate ya miqa musu

“Ku jiremin falo maza mimin daddy” da gudu suka falla sukayi falon kuwa,sai ya maida dubansa gareta,har kullum idanuwansa ba zasu gaji da gayawa zuciya da kwanyarsa yadda yakeson ya ganta ba haka ya ganta ba,kamar yanzun,kai zaka ce matar qauye ce,koriyar atamfar da aka tashi aka yima wani sungul dinki,ba wani abun jan hankali a jikinsa nare style din zamani,daurin kanta kamar na matar qauye,amma duk da haka baiji ya wani tunzura ba,ko tsananin buqatar da yake ciki ce ta kauda duk wani aibu daga idanuwansa?,idanma hakanne harda tasiri ‘yar tsaftar daya isketa a ciki.

Duk duniya ta shaida auren soyayya sukayi da hafsat din,amma dabi’unta nata nesatata daga zuciyarsa,ya taka a hankali yayi tsaye a bayanta yana goye da hannayensa

“Tsakani da Allah haka akewa miji maraba?,mijin da yafi wata guda baya tare da iyalinsa?” Waiwayowa tayi ta watsa masa wani kallo,a yau taci alwashin gwada mishi amfaninta,tunda kare ma ai yana da ranarsa,tasan a buqace zai dawo,zuciyarsa cike fal da tarin buqatun da babu wadda zai dosa da nufin saukewa idan ba ita ba

“Bayan marabar daka samu daga wajen wadda ta fini?,ina cewa bani kadai bace iyalin naka”

“Na fiki sanin hakan,amma yanzun taki marabar nake da buqata” ya fada yana rungume ta ta baya,saita fara qoqarin tureshi amma ya hana mata wannan damar,har ta gaji ta haqura,sannan ya saketa don kanshi

“Kome zakiyi ki dinga qoqari kina zurfafa tunaninki,ina yawan gaya miki,ki dinga sanya hankalinki a gaban fushinki”

“Eh ai dama kullum ni nake da laifi,kaikam baka aikatamin komai,duk wani rashin kulawa da kake nunamin ina hadiyewa baka gani ba”

“It’s okay…..na sameku lafiya?”

“Gamu lafiya lau” ta fadi kamar wadda aka cusawa tsumma a baki

“Ma sha Allah” ya fada yana shafa sumar kansa sannan ya juya zuwa falon,don sam tarbar da yake da buqata ma bata iya taba har kwanan gobe.

Abinda ya fara dawo masa akai yadda widad tayi welcoming nasa,duk da cikin quruciya take komai…..amma komai nata burgeshi yakeyi,yaga zallar kewarsa a idanunta,irin kewar daya rufe mata idanu ta gaza ganin koda hajiya da take kunya da kuma marmarinta,kewar data gaza boyuwa daga idanunta……irin yanayin da yayita begen samu daga hafsat tsahon shekarun da sukayi a tare amma abun ya faskara.

Wannan tunanin ya haifar da murmushi saman fuskarsa,bai zauna a falon ba ya dauki yaran suka wuce zuwa sashensa,can dinma ba laifi an dan gyarashi,duk da dama sashensa baya barinsa yayi datti.

Ba jimawa ta shigo da kayan abinci,ta zuba masa ta koma gefe ta zauna tana danna waya,fuskarta kadaran kadaham,amma bata tsoma bakinta a hirarsa da yaransa ba,sai daya ci rabin abincin,taga babu alamun widad tare dashi sannan ta magantu

“Ina ka baro antyn tasu?” Hankalinsa nakan zarema yaran uban qayar dake jikin kifin data dafa,bata damu data tsaya ta gyarashi da kyau ta cire qayar ba ya amsa mata

“Na barta gidan hajiya” haushi ya cikata,saboda ba qaramin aiki ne yake jiran yarinyar ba,taci buri sosai wannan karon,don ta dauki alwashin daga shi har widad din saita fito musu da sabon taku,zuwa weekend din da ya dinga yi babu ita kafin tafiyarsu ta taso ba qaramin qona mata rai yayi ba,saboda ta riga ta saba da ayyukan widad din,wani lokacin tun ranar laraba zata fara hada dalar qazantarta ta jirayi zuwan widad din,tasan idan tazo kamar anyi ruwa an dauke ne,fes ko ina yake komawa.

Bata sake tambaya ba don kada ya ramfota,amma cikin ranta addu’a take Allah yasa kada tace zata kwana,a badini ji taje kamar ta tafi gidan hajiyan ta janyo widad din tayi mata shegen duka.

Suna qoshi suka bigire da bacci a wajen,dama kusan lokacin baccinsu ne,hannunsa riqe da yatsar nawwara ya saki ajiyar zuciya sannan ya kalli hafsat

“Ki kaisu dakinsu kizo ina son ganinki” yayi maganar a tausashe yana duban tsakiyar qwayar idanunta,dauke kai tayi,don batason ya karya mata zuciya kwata kwata,taja tsaki qasan ranta sannan ta yunqura zata miqe wayarta ta dauki tsuwwa,saita dakata ta daga wayar ta sanyata a kunnenta

“Hello…..kin qaraso?,kina falo?, okay gani nan” sai ta katse wayar,ta sunkuya ta dauki mimi ta fita a falon.

Miqewa yayi ya shige bedroom dinsa ya zarce toilet,yayi brush ya sake alwala,sanann ya fito ya rage kayan jikinsa ya dawo falon,har a sannan bata dawo ba,bai dauka zata dauki tsahon lokaci haka ba,sai ya kunna tv ya kama labarai ya fara kalla,duk kuwa da cewa hankalinsa baya wajen.

Kusan minti talatin ba ita babu labarinta,kamar ya shareta sai ya fasa,ya koma ya dauko jallabiyya mai santsi saqar qasar oman ya zuba,ta masa masifar kyau ta qara fidda wannan sirritaccen kyansa,ya dawo ya dauki nawwara suka baro sashen.

Ba kowa a falon,amma da alama anyi baquwar ta tafi,dakinsu ya kai nawwara sannan ya dawo ya wuce dakinta.

A gaban mudubi ya sameta tana hada kudi,suka hada ido,tasha jinin jikinta amma ta basar,ya zube hannayensa a aljihun jallabiyyar jikinsa yana mata duban da yasan yana ratsa qashinta da kyau

“Gani na biyo sahu” ya fada cikin wani salo,ta lumshe idonta, muryarsa ta tabata da kyau,amma girman kanta sai ya motsa

“Baquwa nayi,kuma yanzun ma wata baquwar gareni tana hanya” bai sauraren ta ba ya taka zuwa bayanta ya kuma rungumeta da kyau ta bayan,baiyi qasa a gwiwa ba ya fara aike mata da wasu saqonni masu nauyi da tsuma zuciya,sun isketa da kyau kuwa,ita kanta tasan waye abbas din fiye da kowa a duniya,ta wannan fannin idan ana taron bada award…..ba award ba idan akwai abinda ya fishi ya cancanci a bashi,tun tana dojewa har sai da ya zaqulo dukka wani qwarin gwiwarta yayi watsi dashi,ya gigita tunaninta da kyau ya kuma yi mata masauki saman gadonta ba tare data ankara ba,sadai tafiya nayin nisa,yana gab da kaiwa inda yake da muradi hudubar shaidaniyar zuciyarta ta dawo mata,ta tattara qarfinta gaba daya ta tureshi ta koma gefe tana cika tana batsewa.

Da qyar ya daga kansa ya kalleta,idanunsa sun canza launi sosai,a sannan idan ka kalleshi zakayi tsammanin barkono aka watsa masa

“Me kikeyi haka?” Baki ta turo masa

“Sai yanzu kasan ina da amfani?,bakasan fushina ba balle damuwata ba”

“Kinsan me kika aikata?,kinsan matsayin yin hakan har a wajen Allah?” Qeya ta juya masa tana kada qafa,tana jin itama a yanzun lokacinta ne da zata murza kambunta,batasan ma me ta tsaya jira ba da har yake mata haka take daga masa qafa,bayan tasan tana da wannan makamin a hannunta

“Kai bakasan naka hukuncin ba saini?,meye naka hukuncin tukunna” shuru ne ya biyo baya,yayi qas da kansa yana dafe da mararsa data fara yi masa ciwo,hafsat itace musababbin samuwar ciwon mara a wajensa,a baya kafin yayi aure bashi dashi,duk da yana da qarfin sha’awa,to amma a lokacin baisan meye aure ba,bai kuma qwallafa ransa akan mata ba,hasalima basa cikin tsarinsa kwata kwata,har sai daya samu halalinsa.

Shurun da taji bai sanyata ta juyo ba,abu daya take jira ya roqeta ya lallasheta,tana jin a sannan ne zata iya haqura ta san masa,shima saita shimfida masa dokoki ya kuma tafe mata kudin da take so wanda zata qara jari a business dinta,duk da zuciya da ruhinta suna d’ar d’ar, zuciyarta na gaya mata zaiyi wuya abbas din ya roqeta.

Wata babbar ajiyar zuciya ya fidda,kamar zai hada da zuciyarsa,ya motsa ya miqe ya jawo jallabiyyar sa ya maida jikinsa,tayi tsit tana sauraren motsinsa,a yadda ya kamu da yawa bata dauka zai iya motsawar bama,ya tsaya qyam saman qafafunsa,cikin mamaki ta waiwayo tana dubansa.

Kallo daya ta yiwa fuskarsa gabanta ya fadi,tayi hanzarin dauke kai tana gayyato dakiya

“Ina da qarfi da ikon da zan iya danneki nayi dukkan yadda naga dama dake…..amma bazan aikata hakan ba,bawai don kinfi qarfina ba…… a’ah,saidai dalilai guda uku,na farko auren soyayya mukayi dake ba qiyayya ba,na biyu ban haquri da lallashi kikeso daga wajena……wallahi wallahi muddin wadan nan dabi’un naki zaki ci gaba dayi,ba zaki taba samun wannan daga gareni ba har abada…..abu na uku kuma…….bake kadai bace Allah ya halattamin ba,sannan kuma bake bace autar mata,ki jiqa abinki ki shanye,indai abbas ne na haifu,kuma dan halak ne ni gaba da baya” daga wannan ya fara takawa a hankali yana ficewa daga dakin,yana tafiya yana cije labbansa saboda yadda yakejin mararsa kamar zata tsage.

Gaba daya maganganunsa sun gigita ta,babu zance mafi gigita kuma a ciki daya ce mata ba ita kadai Allah ya halatta masa ba……yana nufin widad?,shi yanzu sai ya kusanceta?,bazaiji kunya ba?,yarinyar da ya kusa haifarta?,zumbur ta miqe,tana jin kamar taje ta dawo dashi yayi abinda yayi nufin yin…..don da ya aikata abinda yake nufi a zancansa gwara ta bada kanta ta dawo dashi,amma kuma tana taku uku wata zuciyar ta dawo da ita

“Zaki zubda mutuncinki da ajinki a wajensa” sai taci gaba da gamsar da kanta cewa abbas din bazai iya ba,yarinyar tayi quruciya da yawa,bazata taba iya gamsar dashi,kai ba zata daukeshi bama,ko ita da yaya suke qarewa bare widad din dako qasusuwanta basu gama yin qwari ba,ta tabbatar bashi yiwuwa

“Namiji nefa,idan komai bai kawoshi ba buqatarsa zata dawo dashi,basu da haquri ta wannan fannin” ta sake tabbatar wa da kanta,sai taja tsaki ta koma tayi zamanta,har fana tuhumar kanta

“Kin faye rawar kai akan abbas din nan,shi yasa ya rainaki,ya kasa ganin kimarki” wata zuciyar ta sake gaya mata,da wannan taja mugun tsaki ta miqe ta dauko wayarta dake ringing tana duba me kiran,baquwarta ce da zata kawo mata biyan bashi,saita aje wayar ta shiga bandaki tayi tsarki da alwala ta fito,saidai har a sannan itama tana ji a jikinta,don ba qarya tayi missing abbas din,sannan tarkon daya dana mata banda akwai wani quduri a ranta…..ta kuma yi da gaske ta dace da zuciya mai tauri bata isa ta tsallake ba,a ranta taji tana fatan tattaurar zuciyarsa ta sauko da wuri ya karyo ya nemeta,don itama a buqace take.

Tunda ya zube a dakinsa bai iya tashi ba,a nan yayi sallar magariba ya kuma yi isha’i ya koma ya kwanta saman abun sallar,rub da ciki yayi tun tsahon awannin yana fatan ya samu sassauci na zuciya da kuma gangar jiki,gaba daya ya manta zaije dauko widad,sai da yaga kiran hajiyarsa.

Bayaso yace mata baya da lafiya,yanzu zata daga hankalinta,kuma yasan babu driving din da zai iya,sai yace mata yana zuwa.

Number k’aninsa umar wanda daga shi sai auta ya kira yace yazo ya karba key din motarsa ya kawo widad din,idan hajiya ta tambaya ya gaya mata baqi yayi,a ladabce ya amsa masa,ya katse kiran,ya aje wayar yana cusa hannunsa cikin fuskarsa.

Ita kuwa hakimar tana falonta a zaune,duk sanda taji wani motsi saita leqa taga waye,so take taga shigowar widad din ta tsareta da ayyuka,idan da hali ma yau kwanan dakin su mimi zata sakata yi,taso acema key din part dinta yana wajenta tace mata ya bata,batasan me yasa bata saka mata dokar ajeshi a wajenta ba,amma daga wannan zuwan abinda zatayi kenan,ta dinga barinsa a hannunta,idan suka dawo ta dinga karba.
[3/15, 9:35 PM] +234 704 440 6400: *H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)
*Arewabooks:Huguma*

Leave a Reply

Back to top button