Arubuce Ta Ke Hausa NovelHausa Novels

Arubuce Ta Ke 61

Sponsored Links

Page 61

Kiran farko aka gaya mata user busy,tadan dakata na wasu mintuna sannan ta qara kiranta,cikin sa’a kuwa ta shiga

“Aah,kaga amaren kaduna” anty deena ta fada cikin tsokana,da yake idan taso tsokanarta haka take ce mata,dariya ta danyi ta gaidata tambayarta yaranta,ta amsa mata da suna lafiya,suka dan taba hirar data shafi gda sannan daga bisani shuru ya biyo baya,sai anty deena dince tace

“Kina bibiyar kuwa karatun da ake a groups din nan,kinsan kudi na biya kada ki sakani nayi asarar kudina” dariya ta danyi

“Inabi Allah anty,a ciki ma naga wani abu,nayi kuma to mommy hafsa tanata fada,nace anty ko banyi dai dai bane?” Ta qarasa fada a shagwabe

“Me kikayi kuma?” Antu deena ta tambayeta,bata boye mata ba ta gaya mata komai,anty deena tayi shuru tana nazarin maganar cikin ranta,zuciyarta na hasaso mata wani abu,amma kuma nataso ta dora nata tunajun ko tunanun yarinyar akan hakan,tunda dukka dan adam ajizine,zai yiwu ajizanci ne da kuma yanayi ma kishi da zai iya motsawa kowacce mace a kowanne lokaci

“Bakiyi abu mara kyau ba widadun ummu…”

“Ba wani widad din ummu yanzun fa anty deena ta daina sona,su Aafiya tafiso,kullun mukayi waya sai tace zatazo amma taqi zuwa” murmushi ya kubce mata

“Zatazo weedad,kullum ummu cikin zancanki take,amma kafin sannan…..inaso kome kika gani ance ayi kiyi qoqarin yinsa,zaki yi?” Ta tambayeta,saita gyada kai

“Eh anty deena”
“Yauwa widad dinmu,sannan ko meye kika gani baki gane ba ko ya faru ki kirani,koni ko anty madeena ki tambayemu,ba komai ne idan mommy hafsa tace kiyiwa uncle din naki zaki dinga yi ba kinji ko?”

“Tom anty deena” sun dan jima suna waya tana sake wayar mata da kai a fakaice sannan sukayi sallama,koda suka gama wayar litattafan ta debo ta sake zabo wasu a ciki ta dora da karatunta,itama tama manta d batun mommy hafsa da duk matsalolinta.

Rai bace hafsat din ta goge kiran da widad din tayi masa,sannan ta koma dakin ta maida wayar ta ajjiye ta kamar yadda ta ganta taci gaba da zaman jiransa,amma kuna qasan ranta a quntace yake da abinda ya farun,tana zargi da kuma tuhumar kanta,kwana biyu ta watsar da kiran yarinyar bare taci gaba da saita mata hanya,amma fa tana tsoro,kada ya zamana ta hadu da gogaggu kima wayayyun da zasuyi mata karatun da yafi nata shiga,tunda kaduna badai hadakar gamayyar mutane daga gari da qabila kala daban daban ba,amma zata kira ta binciki hajiya amina taji dawa dawa take hulda.

Koda ya fito daga wankan baisan anyi kiranshi ba,saboda qarar shower ta hanashi jin ringtone din,yana goge ruwan jikinsa tana binsa da kallo,jikinsa luwai luwai, fatarsa mai santsi da taushi sai daukar idanu takeyi, muscles din a hade alamun ya samu kyakkyawan training,ta hadiye wani abu da qyar saboda kishinsa daya tsarga mata.

Waiwayawa yayi suka hada idanu da ita,saiya dauke kansa yana cewa

“Ya akayi?,me yake faruwa?” Qaqalo murmushi tayi sannan tace

“Har yanzu banji kace na fara hada kayana ba”

“Zuwa ina?” Yayi mata tambayar bayan ya isa gaban madubi yaja lotion dinsa zai fara shafawa,wani abu ya tsarga mata amma ta dake

“Umara mana” sai daya kalleta ya kuma ci gaba da shafa mansa sannan yace

“Ban shirya wannan zuwan dake ba,babu kudi a hannuna,ina cewa ma ko wata shida bamuyi da zuwa ba ko?”

“Eh amma ai musulmi baya gajiya da zuwa” kai ya gyada

“Haka ne,amma yanxun bani da kudin da xamu iya tafiya mu duka,ke ni da hajiya” ranta ya baci sosai, zuciyarta tayita qissimata mata abubuwa da yawa da zata gaya masa,a fakaice dai hajiyan kusan duk shekara saiya kaita kenan,tunda itama ai baara iwar haka taje

“Aure ya cinye maka kudin kenan?” Ta tambayeshi tana tsareshi da ido,ya sake waiwayowa ya kalleta,ya kuma karanci yanayinta cikin sakanni,sai ya kuma dauke kansa ya maida ga abinda yakeyi,bayason doguwar magana,hakanan baya qaunar mita da qorafi

“Idanma hakanne ba mamaki bane” tofa,baki yasan me zai fada amma baisan me za’a mayar masa ba,saita miqe a mugun fusace

“Allah yayi mana arziqin da zamuyi ta zuwa babu mai hanamu” sai tayi waje fuuuu kamar zata tada iska.

Ransa ya sosu,amma ko iskar data kwasota bai kalla ba,yaci gaba da shirinsa,kafin ya sanya kayansa ya tsaya ya tsaftace sassansa,ya kuma dafa coffee yasha sannan ya qarasa shiryawa ya fice abinsa,yasan bazai rasa abinci gidan hajiya ba.

Tun daga wannan maganar ta dauke masa wuta gaba daya,shima kuma ya tattarata ya watsar ya baiwa banza ajiyarsa,yana ganin guga koda baiyi tsiran komai ba yayi na igiya,ta yaya zatayi kishi da mahaifiyarsa ko nawa kuwa zai kashe mata?,ita din ai ba tsararta bace.

Duka kwanakin da yayi kowa sabgarsa yake,amma hafsa din ta fishi damuwa,saboda tana da buqatar kudi a wajensa,baya ga haka tanason ya dawo da widad din har su dawo daga tafiyar,a wata dayan da zasuyi tasan zata moreta sosai,zata kuma dora mata karatun da zai zauna daram a kwanyarta,amma girman kai da jin tafi qarfin tayi qasa yasa taji gwara tayi shuru duk abinda ma ya yanke shikenan.

Ta bangaren widad kuwa cikin kwanaki qalilan karatun hausa novels ya shigeta sosai,idan tana karantawa tana jinta ne kamar a wata duniyar ta daban,yana debe mata kewa,tana kuma ganin abubuwan da suke bata mamaki,duk kuwa girki ko drinks din data gani saita gwada,a lokacin kitchen dinta yaga rayuwa,saidai duk abinda ta gwada din idan taga yayi farinciki cikata yakeyi,mai aikin maama(hajiya amina) ke tayata wani bin,tana ganinta kamar latifa saboda kirkinta.

Ranar da zai baro kadunan zai biya ta gidan hajiya ya daukota su wuce,har ya kammala shirinsa tsaf a sassansa tana nata sashen tana baccinta,don tun daga waccan ranar basu qara hada makwanci ba,tana sashenta yana nasa,yaci alwashin ko meye zatayi badai shi da qafafunsa ya bita yayi begging nata ba,yasan abinda takeso kenan.

Tare dasu mimi suka fito,a wajensa yaran suka kwana,tsaf dasu don su kansu sai daya shiryasu ya kuma gyara sasssan,suna riqe da hannunsa ya tura ya shiga,falon a hargitse kamar wanda aka tashi taron biki,harsa pampers din nawwara da yayi imanin idan bana shekaran jiya bane na jiya ne

“Ku zauna nayi sallama da mamanku” ya fada yana kallonsu,sai suka amsa suna hayewa saman kujerar,ya ajjiye luggage dinsa ya nufi qofar bedroom dinta,don ko takalminsa bai fidda ba saboda tsaftar tiles din ma bata gamsheshi ba,duka yayi rod’i rod’i kamar an watsar da ruwan tea ya fara bushewa samansa.

Sau uku yana knocking sannan yaji ana tambayar waye da cunkusashiyar muryar bacci,gyaran murya kawai yayi,ta taso tana turbune fuskarta daya kacame saboda bacci ta buda qofar.

Ido hudu sukayi, doguwar rigar wata kodaddiyar atamfa ce a jikinta da aka yiwa adon net,net din har ya soma bubbulewa alamun dake nuna ya fara gajiya da aikinsa,kanta gashinta ne him daya hautsine kamar ciyawar da aka tara za’a ciyar da dabbobi,abinka da baqar fata idan bai shafa mai ba….duk jikinta yayi fari fari,dakin yana fidda irin abinda jikinta ke fiddawa,da alama ya kama ko ina.

Kansa ya dauke,don takaicinta bazai kasheshi ba,ya fara gajiya da al’amuranta da kullum babu gyara sai gaba da abun yakeyi,ya sanya kai cikin dakin,dole ta kauce masa ya rabe ya shige,sai ya kasa zama,yana kallonta ta tsince pant dinta da bra dake watse a qasa

“Ina kwana?” Ta gaisheshi murya a cushe

“Lafiya….mu zamu wuce” ya bata saqo a gaggauce,saboda qagauta da yayi da wanzuwarsa cikin dakin,ya zura hannunsa a aljihu ya fiddo rafa na kudi ya matsa gefanta ya ajjiye mata yana cewa

“jibi zamu tashi,zamuyi sati uku idan ta kama har hudu ma,saboda inaso zamu tsaya egypt hajiya zataga likita,duk yadda ta kama dai….shikenan babu wani abu?” sai a sannan ta dago ta sake kallon sa

“Daa ka sani ma baka shigo ba,inda wucewarka kayi da hakan yafi” tsareta yayi da idanunsa yana mamakin furucinta

“Hafsa…..magana nake miki ta zanyi tafiyar da babu lallai na sake dawowa fa” gaba tayi tana qoqarin komawa cikin bargonta

“Allah ki yaye hanya” ta fada cikin nuna halin ko in kula taja bargo ta rufa abinta,saidai tuni idanunta sun cika da hawaye,banda qin Allah,da kudin da zataga likitan basai ta haqura ba a biya musu tare,idan suka dawo taga likitan a nan ba,ai duka daya ne,to amma a’ah,wai dole sai an nuna maka iyakarka.

Sai daya bata kusan mintuna a tsaye yana kallonta ta cikin bargon,zuciya na hasalashi amma ya hadiye ya juya a hankali ya soma fice daga dakin.

Wuf tayi ta yaye rufar ta kuma sauko daga gadon,da gudu tasha gabansa

“Au tafiyar zakayi?” Ta fada hawaye yana layi kan fuskarta,kallo daya yayi mata ya kauda kansa,saboda yadda zuciyarsa ke azalzalarsa

“Tun ba yau ba nasan baka damu da damuwata ba dama,ba abinda ya shafeka da baqinciki na ko walwalata,to kaje,amma ka sani akwai hisabi tsakanina dakai,Allah bazai taba yafe maka ba idan ka zalunceni” ido ya runtse yana jin zafin maganganunta,ya budesu a hankali sai suka kan yaransu,mimi da nawwara suna tsaye daga bayanta sunyi carko carko,da alama sun fahimci wani abune mara dadi yake faruwa.

Maganganu ne da yawa a ransa da amsoshin da zai bata,amma sai ya hadiye,muryarsa a sarqe yace

“Naji,Allah ya saka mikin,matsa ki bani hanya” jagale tayi tana kallonsa,sai kuma ta saki qofar ta koma ciki da gudu ta fada gado tana sakin kuka,baiko waiwayeta ba ya matsa zuwa gaba,ya sunkuya yayi kissing goshin yaran sannan ya kama hannunsu zuwa falo ya kunna musu cartoon yayi musu dabara ya fice.

Har suka kama hanyar kaduna ransa a bace yake amma yaketa dannewa saboda kada hajiya ta fahimta,yasan yanzu zata gaza nutsuwa.

Sai da suka shiga garin kaduna sannan ya fara tunanin yadda zasu samu widad ita kuma,abinci da zasuci da sauransu,yau dai ba makaranta yasan tana gida,to amma abinci bashi da tabbacin zasu samu,tunda ga wadda a haife ta haifeta ma bata da wannan tunanin,ina ga ita?,ya yanke kawai idan sun isa yana kai hajiya ciki ya koma ya siya musu abinda zasuci ya hada musu da order din abincin dare,gobe kuma ya samu time yayi musu,da wannan tunanin suka shiga unguwarsu.
[3/13, 12:54 PM] +234 813 343 4840: *H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)
*Arewabooks:huguma*

Leave a Reply

Back to top button