Arubuce Ta Ke Hausa NovelHausa NovelsHausa Novels

Arubuce Ta Ke 58

Sponsored Links

Page 58

Tsakanin shi da itan zamu iya cewa wasu irin mutane ne da miskilanci yake gudana a jininsu,saidai duk da wannan hakan bai hana sabo da sakewa a tsakaninsu ba,kamar ko yaushe,safiyar ranar juma’a ce,suna kitchen ita dashi,tana sanye da abaya mai santsi peache color me turuwa kadan,wanda daga cikinta riga da wando ne straight leg,duk da basu matseta ba amma sun fidda aihinin shape nata,shi yasa ya dora abayan a kai,haka kawai tayi sha’awar sanyasu,taga hotunansu cikin wayar wata ‘yar ajinsu yayarta ke sayarwa,data duba kayanta taga tana da irinsu,kaf ire iren wadan nan kayan nata suna hade ne a waje daya,bata taba gwada sakasu ba,tana ganin kamar kayan ‘yan iska ne.

Manyan kalba da aka yi ma kanta guda hudu masu kauri da tsahon jela,biyu suka zubo gefe da gefen fuskarta,suka kuma sauka mata har kafada,sauran biyun kuma suka sauka a gadon bayanta.

Yau din abbas na saman cupboard a zaune kawai yana latsa waya,saboda tunda suka tashi da safen tana gaidashi tace,saita langwabe kai gefe guda tana wasa da yatsun hannunta

“Yau babu abinda zaka koyamin,I want to surprise you” she is always like a baby,haka take maganarta cike da quruciya,daya daga cikin abinda yasa yakeson yaga tana magana,kota dake da gasken gaske tana zuba wautarta,amma ita a nata ganin a dai dai take komai.

Yadda ta ritsashi da idanu bayan ta gama maganar ya sanya dole murmushi ya qwace masa,irin miskilin murmushinsa da ko haqoransa baka fiya gani ba,ya dage girarsa dukka biyun sama yana kallon tsakiyar qwayar idanunta

“Really?”
“Yes” ta amsa da amsa amo cike da qwarin gwiwa,sai ya girgiza kai yana qaramar dariya

“Zamu gani,in zauna yau abina kenan?”

“Eh mana,na baka hutu” ya fidda sauti kadan,yayi tsalla daya ya haye sama yayi zamansa,saita bishi da ido tana fidda manyan idanunta waje,wasu irin fararen manyan zagayayyun idanuwa da suka dauki hankalinsa a karon farko,har baisan yayi subutar bakin tambayar ta

“What?” Ya fadi yana jin wani abu nason masa tasiri,qaramar dariya mai cike da sakalci tayi

“Tsallae daya fa kayi uncle ka haye?” Murmushi ya sake subuce masa,ya girgiza kai

“Shine kika bude dukka wadan qwala qwalan idanun naki zaki cinyeni dasu?” Baki ta tabe kamar yadda qaramin yaro keyi idan zai saki kuka,abinda ya sake shagaltar dashi da kallonta kenan,siraran labbanta kamar ta shafa musu jambaki

“Qwala qwala fa kace uncle”

“I don’t mean qwala qwala marasa kyau,u have a beautiful eyes dear” ya fadi yana duban qwayar idanunta,kawai sai taji wani irin kunya ta kamata,ta saka tafukan hannayenta ta rufe fuskarta,hirar ‘yan ajinsu ta fado mata,daya daga ciki dake basu labarin yadda saurayinta yake kodata,haka akeji dama data taba ce musu kunya takeji?.

Zara zaran yatsuntsa data rufe fuskarta dasu yabi da kallo,farare tas,hatta da farcenta fari ne qal babu digon komai a jiki

“Me kike tunani?” Taji ya sake fada

“Ba komai” ta amsa masa da sauri tana sauke hannuwanta daga fuskartata,gani take kamar zai karanto abinda ke cikin zuciyarta

“Kin manta am a police,da tsalle daya muna iya hayewa saman gini dake da tsahon da yafi na wannan,kin tuna?” Kai ta gyada tana murmushi,saita kasa ci gaba da cewa komai saboda yadda yake kallonta tsakiyar idanunta yana sanyata tana jin wani iri.

Shuru kitchen din ya dauka,yayin data buda wayarta tana duba recipe na abinda zata dafa din,tana daukowa daya bayan daya tana ajjiyewa,har ta kammala ta fara aikinta.

Haka kawai ya samu kansa da daga kai time to time yana kallonta,hakan ya sanya duk kai kawonta take yinsa cikin idanunsa ba tare data ankara ba,aiki yayi aiki,taja igiyar rigar ta daureta don tafi jin dadin yin aikin,saidai abinda bata sani ba,gaba daya ta fidda shape na mazaunanta qugunta da kuma qirjinta.

Ya sake dagowa yaga a inda girkin ya tsaya idanunsa sukayi kyakkyawan gani,yaso janye idanun nasa amma sai ya kasa,karon farko kamar an zare masa laka daga jikinsa,yaso ya maida kai ga wayarsa amma sai yaji ya kasa,dole ya kashe abinda yakeyi din,ya aje wayar a gefe,ya jingina da bango ya harde hannayensa a qirjinsa ya zuba mata idanu.

Sam batasan yana kallon ta din ba,saboda ta bada hankalinta gaba daya ga abincin,tanason yayi dadin da zai yaba mata,ta waiwayo zata dauki chopping board har ta juya ta fara yanka albasa jikinta ya bata kamar kallon ta yake,tana juyawa sukayi ido hudu,sai gabanta ya fadi,ta juya da sauri ta saki igiyar rigar tata,ta koma shapeless kamar yadda take idan ba igiyar a jiki,jikinta yadan dauki rawa kadan,ta sunkui da kanta tana yankan da sauri sauri.

Bata son kallo ko kadan,bare shi da a duk sanda ya kalleta sai taji nashi idanun kamar sun banbanta dana kowa,ta fara nisa a tunani,don haka har ya sauko daga inda yake zaunen,ya tako a hankali ya tsaya a bayanta bata jishi ba.

Sosai ya zuqi qamshin splash da jikinta ke fitarwa kadan kadan yana kadawa hagu da dama gaba da bayanta,taku biyu ya qara ya sake rage kusancin dake tsakaninsu,sai a lokacin taji kamar iskar dake bayanta ta canza da wani kalar qamshi na body mist na daban.

Cikin hanzari ta waiwayo,ta manta da wuqar dake hannunta tana datsa albasa,tariga ta dora ashe saman yatsanta ne,tayi wurgi sa wuqar tana yarfar da hannunta gefe daya,saidai duk da zafin da taji kusancin shi da ita yafi daga mata hankali,ta kafeshi da idanu qirjinta na wani irin bugawar da bai taba yiba,ta kuma ja baya sosai har ta qure da jikin kitchen cabinet din.

Kallon kallo aka shiga yi tsakanin shi da ita,a hankali ya sanya hannunsa ya lalubo hannunta data yanke din ba tare daya janye idanunsa daga cikin nata ba,sai daya sanya hannun cikin tafin hannunsa sannan ya maida dubansa akai.

Kusan lokaci daya suke duban hannun shi da ita,sannan suka kalli juna

“Kinga abinda kikayi ko?” Ya tambayeta da wata shaqaqqiyar muryar,kamar jiransa dama takeyi sai ga hawaye ya cika mata idanu

“Kaine fa ka bani tsoro” dariya taso bashi amma ya dake,saiya langabe kai kamar yadda yaga tayi

“Banda ke banga wadda take tsoron mijinta ba” kamar ya tunzurata,don batason kalmar miji,sai ta fara qoqarin zame hannnunta daga cikin nashi

“Ni ba mijina bane kai”

“To waye ni?” Ya tambayeta yana dage girarsa sama

“Uncle” kai ya girgiza kawai yana sake sakin boyayyen murmushi

“Riqe uncle dinki,banaso,let me treat your wound first” ya fada yana sake kamo hannunta.

Kujera ya saka mata ta zauna akai,sannan shima ya jawo wata ya zauna,har gwiwoyinsu suna haduwa da juna,ya bude first aid kit din ya fada wanke jinin,yana yi tana rintse idanu,ya daga idanunsa ya kalleta,idanuwansu suka hadu waje daya,sai taji hakan ya mata nauyi sosai,ta kauda nata idanun numfashin su yana gauraya da juna.

Har ya gama mata babu wanda ya sake cewa komai,ya sakar mata hannun yana hade kayan waje daya

“Jibi idan Allah ya kaimu zanje bauchi” kallonsa tayi da sauri,hakanan kwanakin nan sai ta dinga jin batason zuwa garin

“Zanje nayi one week,zamu taho da hajiya,the next day zamu wuce umara ni da ita in sha Allah” zuwan da yace hajiyan zatayi taji yayi mata dadi,har zumudinta ya bayyana a fili

“Amma wata daya ya kamata tayi,ko ka dawo da ita nan kawai” ta fada tana langabar da kanta,cak ya tsaya yana kallonta,yaji mamakin jin furucin daga bakinta,abinda bai taba ji daga bakin hafsat ba tsahon zamansu da ita

“Hajiya ba zata zauna ba” ya amsa mata yana miqewa riqe da kit din.

Koda ya dawo sai ya fara rolling hannun rigarsa zuwa sama,tana daga zaune tana kallonsa har ya gama,idanuwanta suka sauka kan lallausar gargasar dake lullube da hannunsa,abar da take yawan burgeta ba tare da tasan dalilin ko kuma amfaninta

“tell me what you are cooking sai na qarasa” idanu ta narke

“Zan iya qarasawa uncle,don’t spoil it” girarsa ya daga ya watsa hannayensa

“I will finished it anyway idan ma baki gayamin ba” ya fada yana qarasawa,ya bubbada tukwanen

“Kin kusa gamawa ai” ya fada ba tare daya juyo ba,yana mamakin qoqarin da tayi,kai ta gyada masa.

A nutse yake ci gaba da aikin,har ya kammala,duk inda ya motsa idanunta suna biye dashi,yana ankare da ita amma bai nuna ya ganta ba,har ya kammala,zata karba gyara kitchen din shima ya hada ya gyara komai,mamakinsa sake cikata yakeyi kullum,shi kam baya jin aiki ne?.

************Tana nade saman kujerar falon,tayi lamo kamar ‘yar magen data samu waje mai laushi,sanye take da atamfa dinkin riga da skert na atamfa,ta yane saman kanta da dankwalin atamfar,jikinta na fitar da tattausan qamshin turarenta,daga gaba kadan kujerar ta uku daga gefanta,abbas ne a tsaye yana qarasa zuge jakarsa ta tafiya,yanayi yana amsa waya daga office,har ya kammala,ya kashe wayar ya sanyata a aljihu,ya dauki jakar ya rataya a kafadarsa.

Sai a sannan ya waiwayo inda take zaunen,yadan zuba mata idanu yana karantar yanayin fuskarta,duk sanda zayaje bauchi indai bada ita bane sai yaga wannan damuwar a tare da ita,saidai a wannan karon damuwar kamar tafi ta kowanne lokaci.

Yadda tayin kamar wata marainiya ya bashi tausayi da kuma dariya,ya taka a hankali ya tsaya a gabanta,ya miqa mata dogayen lausasan hannunsa.

Hannun tabi da kallo kafin ta mayar saman fuskarsa dake dauke da wani irin haiba da wani sirritaccen kyau da ba kasafai kake iya hangensa farat daya a fuskarsa ba,har cikin zuciyarta takejin wani iri babu dadi,saboda wannan ne karon farko da zaije yayi sati daya,kwana biyu rak yake ya dawo duk sanda ya tafin,idan da itane ma suke kwana uku.

Sake miqa mata hannun yayi,saita noqe hannun nata tana lumshe idanunta hadi da kwantar da kanta tsakanin cinyoyinta.

Murmushi ne mai sauti ya kubce masa,cikin taushin murya yace

“Get up,tashi muyi sallama” curewa tayi waje daya,saita saki kuka kawai

“Ya rabb”ya furta yana sauke jakarsa daga kafadarsa ya ajjiyeta a qasa,sannan ya duqa saman gwiwarsa a gabansa

“Na gayawa hajiyane baki barni inje na daukota ba?,ko na gayawa maman mimi baki amince naje muyi sallama ba?” Furta sunan mommy hafsat da yayi ya sakata zabura,ta kuma daga kanta da sauri,sunanta kawai na sanya gabanta faduwa,hajiya kuwa tana jin nauyi da kuma kunyarta fiye da yadda baki zai furta,dukkansu babu wanda zataso ya gayawa abinda yace zai gaya musun.

Kai ta girgiza masa da sauri,ya lumshe idanunsa ya kuma budesu duka a tare

“Wipe your tears” hannu biyu tasa ta goge hawayen yana kallonta, cikin ransa yana jin wani irin yanayi daya gaza tantance wanne iri ne,a yau apart from hajiyansa,yau ga wata halitta dake amsa sunan matarsa tana jin babu dadi wai don zaiyi nesa da ita,a wajen mutum guda yake ganin hakan….. hajiyan sa,babu na biyun sai a yanxun da yake gani daga wajenta.

Sai daya hilaceta ta dan saki jiki,sannan ya miqe ya dauki luggage dinsa yayi mata sallama ya fice,tana tsaye a jikin window har motarsu ta tashi suka fice daga gidan.

KI KULANI miss xoxo

DAUDAR GORA Billynabdul

RUMBUN K’AYA hafsat rano

IDON NERA Mamuhghee

A RUBUCE TAKE huguma

_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_

_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

0022419171
Maryam sani
Access bank

Saiku tura shaidar biya ga
+234 903 318 1070

*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
09166221261

*Al’ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
+227 96 09 67 63

*Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥[3/12, 9:02 PM] +234 813 343 4840: *H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)
*Arewabooks:Huguma*

Leave a Reply

Back to top button