Arubuce Ta Ke Hausa NovelHausa Novels

Arubuce Ta Ke 70

Sponsored Links

Page 70

Duk da cewa baikai ga cimma gaci ba,duk da cewa buri da muradinsa bai cika ba……amma ta kaishi wata duniya data sake haukata tunaninshi,ta sake ninka burinsa……ta sake kwadaita masa ita,ta kuma haifar da wani yanayi da kai tsaye zaka kirashi da ZAZZAFAR K’AUNA a karon farko,cikin jininsa ya dinga ji cewa eh weedad din ta dabance,zata iya zamowa ta musamman cikin mata….. za’a iya kiranta da ‘yar baiwa,ya samu wani irin nutsuwa da tarin ni’imomin dake hutar da zuciya su kuma sanya ma ruhi nutsuwa tattare duka a iya jikinta kadai,tun baikai ga afkawa waccar duniyar ba.

Wani irin ciwo yakeji har cikin zuciyarsa sanda take rera wani irin kuka,ciwo ciwo takeji daga can qasanta duk da baiyi yawa ba,saidai hankalinta a mugun tashe yake,me ya aikata mata kenan?,da wanne fuska zata kalli mutane?.

Yayi lallashi yayi ban bakin amma a banza,har sai da bacci ya taimakeshi ya dauketa,sai ya zareta daga jikinsa a hankali ya shimfidar da ita,ya kunna bedside lamp ya matso da ita kusa da fuskarta sosai.

Kallo na haqiqa ya zauna yana qare mata,baisan da wanne suna zai kirata ba,baisan kuma a wanne matsayi zata iya tsayawa cikin zuciyarsa ba daga ranar da ya maidata tashi,a yanzun Allah ne kadai yasan me yakeji a kanta,qauna soyayya tausayi da kuma shauqi gaba daya, mintuna qalilan amma sun canza matsayinta daga wani bigire zuwa wani bigiren na daban.

Ya jima zaune kamar mai karanta littafi yana kallon baby face dinta da tayi jazur da ita,sannan ya sauke ajiyar zuciya,ya zura qafafunsa ya sauka daga saman gadon ya shige bandaki.

Tsarkake kansa yayi sannan yayi wanka,ya fito ya tsane jikinsa da kyau ya sauya kaya sannan ya koma saman gadon,bai jishi dai dai ba har sai daya jawota jikinsa,tunane tunane ne masu tarin yawa ke masa yawo a kai,shi kansa idan yace ga dai dai lokacin data ma zuciyarsa wannan muguwar illar yayi qarya,wani abu mai qarfi akanta ya dinga shigarsa,sai ya dinga jin gaba daya duniyarsa ta ta’allaqa da ita.

Kiran sallar asuba ne ya tasheshi,har ya gama shirinsa na fita masallaci bata ko motsa ba,bacci take sosai tana kuma sauke ajiyar zuciya lokaci bayan lokaci,har sunkuya saman kanta zai tasheta yaji ya kasa tashin nata,yaja mata bargon ya rufeta bayan yayi kissing goshinta,ya fita yana waiwayawa kamar wanda akace za’a dauketa kafin ya dawo.

Sanda ya fita sallar yayi mamakin ganin cunkoson jama’a a layin nasu,ya qarasa a hankali ya fara musabaha da mutanen dake wajen

“Munyi tunanin baka gari ai yallabai” daya daga cikin dattawan layin ya fada yana duban abbas

“Me yake faruwa alhaji audu?” Abbas din ya tambaya yana dubansa

“Wallahi daren jiya ‘yan fashi suka shigo gidan maqocina alhaji isah”

“Subhanallah” ya fada cikin alhini

“Kusan kowa yaji abun,don tun wajen karfe daya na dare suka shigo unguwar,basu fita sai qarfe uku”

“Ya salam,Allah bai sa naji ba,amma aka rasa wanda zaiyi kiran koda wayata?”

“Wallahi Allah ya daukewa kowa wannan tunanin” matsawa gaba ya fara yi zuwa gidan alhj isah din,inda mutane suka fara dandazo

“Badai wanda suka raunata ko?”

“Eh to,sun harbi yarinyar sa,suna hanyar kaita asibiti”

“Kun kira jami’an tsaron?” Cikin alhini alhj audu ya girgiza kai

“Kusan awa guda kenan amma babu su ba dalilinsu” sosai ran abbas din ya baci,ya tambayi police din wanne area dinne alhaj audu ya gaya masa,sai ya fidda wayarsa yayi kiran dabai wuce na minti uku ba cikin bacin rai

“you must be there before thirty minutes” abinda ya fada kenan ya kashe wayar ya mayar aljihu

“Kada kowa ya shiga cikin gidan,sannan suma mutanen gidan a gaya musu su nisanci inda abun ya faru…. alhaji muje muyi sallah tukunna” tare suka rankaya da alhaji audu zuwa masallacin suna sake tattauna yadda abun ya faru,bashi da nauyin bacci sam,kamar yadda bai saba dogon bacci ba,amma yayi mamakin yadda jiya har akayi aka gama abun baiji ba,lallai da gasken gaske ‘yar qaramar yarinyar ta gigita masa rayuwa da kyau a jiyan,ta kuma shirya janshi zuwa wata rayuwa ta daban,baisan sanda wani siririn murmushi ya kubce masa ba.

Wannan case daya faru a unguwarsu ya hanashi komawa gida da wuri,sunata bincike kan abun har sai da suka samu nasarar tracking barayin cikin taimakon Allah da kuma qwarewar da yake da ita,sai wajen qarfe daya na rana sanann ya gama nasa aikin,ya danqawa wadanda alhakin kula da area din yake a hannunsu,ya zare safar hannunsa ya miqawa daya daga cikin police din,gaba daya hankalinsa yana kanta tun dazun,dauriya kawai yakeyi.

Sama sama ya amsa gaisuwar yaron gidan nashi ya wuce zuwa cikin gidan,kai tsaye sashensa ya wuce,ya tura qofar falon ya shiga,bata falon bata bedroom din,sannan bata toilet,sai zuciyarsa ta raya masa ko tana sashenta,don haka ya juya akalarsa zuwa can.

Kaf ya gama dubawa bai ganta ba,sai abun ya shiga bashi mamaki,baya da niyyar shiga sashen hafsat din yau gaba daya,amma dole ya shiga ya gani ko tana can.

Dukkansu suna falo ita da yaran,tuni falon ya koma ‘yar gidan jiya,tana saman kujera zaune abinta,ta cika tayi fam da fushi,daga abbas din har widad din kowanne da nasa laifin a wajenta,donme yarinyar zata tafi gidan hajiya tayi zamanta?,uban waye zaiyi mata aikin da tafi kowa sanin itace zata yishi?,sannan abbas din me yake nufi da ita?,har azahar tayi amma ya kasa leqowa yaga lafiyarsu?,jikinta ya soma sanyi amma wani sashen na zuciyarta yana qarfafa mata gwiwa,tare da sake kambama mata laifukansa,duk da haka ta soma rasa qwarin gwiwarta,tasanshi….yana da danne zuciyarsa da hanata saurin fushi,amma kuma idan yayi fushin bashi da dadi sam.

Boyayyar ajiyar zuciya ta sauke sanda taga shigowarsa,ya tsugunnawa yaran suka haye bayansa,fuskarsa na fidda murmushi,zuciyarsa dauke da tausayinsu,da babu alamun an musu wanka

“Ina antynku?”

“Daddy ta dawo?,ka kaini wajenta” mimi ta fada,abinda ya tabbatar masa kenan bata shigo ba kwata kwata

“Ina kwana?” Ta fada ganin yana niyyar miqewa ba tare daya kalleta ba

“Lafiya”

“Ga breakfast dinka har ya huce baka ci ba”

“Na qoshi” ya amsa mata yana ficewa riqe da yaran.

Hankalinsa yadan tashi,ina ta tafi to?,ya tambayi kansa,sai ya jawo wayarsa ya kira layinta,a kashe layin yake,ya sauke wayar yana fidda iska daga bakinsa,gidan hajiya ta koma?,wata zuciyar ta gaya masa,har ya danna kiran layin hajiya sai ya kashe,idan ta tuhumeshi dalilin komawarta baisan me zaice mata ba,don haka ya kira layin umar.

“Kana gida ne?”

“Eh hajiya za’a baka?”

“Weedad tazo?”

“A’ah yaaya,tun jiya dai dana kawota gida”

“Okay,karka cewa hajiya ga abinda na tambayeka”

“To yaaya” umar din ya fada ,kafin ma ya qarasa abbas din ya katse kiran,sai yaji hankalinsa ya sake tashi.

Muhsin ne ya fado masa,baiyi qasa a gwiwa ba yayi kiransa bayan sun gaisa kafin abbas dinma yace komai ya rigashi magana

“Jiya jiya muke zancanku,inajin madam fa gobe ko jibi zata shigo ganin diyarta,nace ban da tabbacin kunxo weekend wannan satin”

“Jiya mukazo,amma kuma banajin zamu jima zamu koma,yanzun ban fiya sakewa a bauchi ba,ayyuka sunyi yawa a kaduna” hira kadan suka taba sukayi sallama,don shima muhsin din fitowarsa kenan daga gida yana kan hanya yana driving.

Wayar ya ajjiye,ya koma gefen gadon ya zauna hannuwansa cikin sumarsa yana murzata a hankali,yanason qwaqwalwarsa ta hasaso masa mutum na gaba da zai kira ya bincika ko can taje,ya akayi ta iya fita daga gidan har ta fita ba tare da wani ya ganta ba?.

Kasa zama yayi,sai kawai ya miqe ya dauki key din motarsa,tsoronsa daya kada yarinyar mutane ta bata cikin garin daba nasu ba,don yana da tabbacin zaiyi wuya ace shigowa akayi aka dauketa,don ya duba duk wani abu da zai iya bada alamun hakan bai gani ba,sai ya fita da yaran ya zubasu a motar suka fice daga gidan.

Layi layi titi titi ya dinga bi yana dubata amma sam babu ita ba alamarta,har wajen azahar,ya tsaya a wani restaurant ya siyama yaran takeaway,ya dawo cikin mota ya zauna kenan wayarsa ta dauki tsuwwa,ya duba me kiran sai yaga muhsin ne

“Kasan matarka ta tafi kano?”

“Kano?” Ya tambayi muhsin din cikin mamaki qwarai,duk da dama yana cikin dimuwar son sanin ina tayi

“Eh,yanzu muka gama waya da ummu,ta kirani tace na shaida maka,don tafiyar batayi mata kama data nutsuwa ba” qatotuwar ajiyar zuciya ya sauke yana jin wata nutsuwa na saukar masa

“Alhamdulillah” ya fada a fili

“Ka ganni a gefan hanya,tun dazun nake checking ko batayi nisa ba,ina shirin kira headquarter ma su bani mutane muyi aikin tare”

“Subhanallah…….wanne irin sakarci ne wannan?,halan bata gaya maka ba bakasan da tafiyar tata ba” qaramin murmushi ya subuce masa,yasan sarai muhsin ba wasa,yanzun nan idan yace zai gaya masa gaskiya sai yace zai taba masa mata,shi kam a yanzun a yadda widad takai har cikin ruhinsa,baya jin ko ruwan sama zai lamunce masa ya taba masa ita

“Me na tone tone?, tunda ka isar da saqon ummu shikenan,zan kirata”

“Please abbas……kada kace zakayi kawaici,ka gayamin gaskiya”

“Amma dai kasan indai kace zaka shiga tsakanin miji da mata zakaji kunya ne ko?”

“I know…..but…..”

“But what?,shikenan kawai,ka qyalemu tsakaninmu ne”

“Alright,Allah ya sawwaqe” daga wannan sukayi sallama ya aje wayar.

Mamaki ya sake kamashi,yayin da qaramin murmushi ya subuce masa,rigimammiya ce yarinyar ta ajin qarshe,ya akayi har ta iya kai kanta kano?,da gaske batasan wannan rayuwar ba,batasan meye ma’anar aure ba at all

“I will teach her……bazan bari ki subuce min ba,zan koya miki abubuwa masu zafin da zuciyarki zatayimin riqon tsauri da kyau” ya fada shi daya kamar me sambatu,abinda yake ji a ransa game da ita yafi qarfin a kirashi so,saidai wata irin zazzafar qauna da bai taba jin kamarta ba.

Aje wayarta ummu tayi tana sauke dubanta ga widad data cusa kanta cikin pillow tana ta sheqa kukanta,kukan da tunda ta iso kano take kwararashi,tayi tambayar duniya amma taqi daga kai ta kalleta ma bare akai ga amsawa.

Abu daya ne yasa hankalin ummu bai wani daga ba,widad din tata tayi fes tayi fresh,ta sake murjewa,ga kuma girma data qara,ta fara zama budurwa sosai,aure ya kwarzantata

“Widad” ta sake kiran sunanta,shuru bata amsa ba sai kuka,tana tsoron su hada ido da ummun,tana ganin kamar zata gane abinda yayi mata a daren jiyan

“Kinga idan ba zaki amsa min ba,ki daina kukan kada kanki yazo yayi ciwo” ummu ta fada tana miqewa

“Ki samu waje ki kwanta” ta sake fadi bayan ta isa gaban wardrobe dinta ta fidda hijab,tayi sallar azahar sannan ta dauki wayarta ta fita tabar mata dakin,cikin ranta tana juyayin abinda ya faru,kodai ita da kishiyarta ne?,tunda muhsin ya sake kiranta yace abbas din yace babu komai,amma kishiya kuma……nawa widad din take da har kishi zai hadasu tayi wannan tafiyar afujajan.

Da wannan tunanin ta isa falonta,ta iske latifa tana aje abincin rana

“Batace komai ba ummu?” Latifan ta tambaya cikin damuwa

“Uhmmm…..bata ce ba,nifa banga wani alamun damuwa tattare da ita ba,nafi zaton shirmenta ne kawai ya motsa,idan kuwa haka ne zataci qaniyarta,ta yaya zata dauko qafa daga bauchi ta taho kano ba tare da izinin mijinta ba?,baya ga haka kuma ita kadai a wannan rayuwar da muke ciki?” Ajiyar zuciya latifa ta sauke

“Ayi mata dai a hankali ummu,ai ruwa baya tsami banza”

“Kin manta widad din ne ashe” ummu ta amsa mata,wanda tana rufe bakinta momma tayi sallama

“Barka da rana ummu” ta fada tana ‘yar fara’ar da batakai zuci ba,da kallo ummu ta bita

“Ke kuma daga ina da rana haka fatsar fatsar?” Murmushi ta danyi tana wuwwulga idanunta wai ko zataga himilin kayan widad din da akace an ganto ta shigo ita kadai

“Zan fita ne nace bari na leqo,idan kina da canji ki aramin”

“Canji?” Ummu ta maimaita cikin mamaki,saboda irin wannan ita baya hadata da surukanta

“Eh….eh” dan shuru tayi tana karantar momma din,sai kuma tace

“Allah ya kyauta,shiga kitchen ki yiwa latifa magana ta baki” amsa mata tayi sannan ta nufi kitchen din tana kalle kalle a falon ta gefan idanunta.[3/16, 11:09 AM] +234 704 440 6400: *H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)
*Arewabooks: Huguma*

Leave a Reply

Back to top button