Category: Matar Makaho Hausa Novel

  • Matar Makaho 64-65

    Matar Makaho 64-65

    Page6⃣4⃣&6⃣5⃣
    Mafarki yake koh gaske, da idanun sa yake kallon duniya, wanda rabon sa daya gani yanzun ana neman shekara 13, Allahu Akbar Tsarki ya tabbata ga Allah, Alhamdulilah Alhamdulilah, shine abinda yake maimaitawa

    Mikewa yayi da sauri yana bin koh ida da kallo, kamar wani dolo, shi ganin abin yake kamar mafarki ne, an jima zaici gaba da ganin duhu,sai bin wajen yake kamar daji, haka ya ringa takawa a hankali yana tafiya cike da Al’ajabin abinda ke faruwa yau dashi, shine da kallo?

    Hango gonaki yayi a shimfide, gwanin sha’awa na kayan labbu, ga kogi babba yana gudana da gudu yayi saitin kogin da saurinsa ya shiga ruwan, don wallahi azababben kishi yake ji, ai yana shiga kogin ya tsoma hannun sa cikin ruwan ya iba yasha, ya sake tsoma wa ya iba yasha, kamar wasa yaji ruwa yana jansa daga bakin gaba, har tsakiya sai kokari yake ya fitoh amma ina abin yaci tura, salati ya fara yana innalilahi, wasa wasa ruwa ya fara nitsar dashi sai kokowa yake da ruwan, duk kokarin sa na fita, abu ya gagara, daman shi ba ruwa ya iyya ba, ina makaho ina rafi, koh lokacin tasowar sa baiyi yayin bin yara kogi ba.

    Sosai ruwa ya hadiye sa har wuya, sai kokari yake Amma ruwan yafi karfinsa, zuwa wani lokaci, shuuuuuuuu yaji ya burme cikin ruwa, da sauri yayi tsalle yafitar da kansa, sai kuma yaji ya sake komawa, kamar wasa Al’ameen ya fara shan ruwa, sannu sannu har yaji ruwan yaci karfinsa, tun yana gani dishi dishi har yaji bayanan ,

    Gid’ado ne tsaye da shanun sa, daya koro bakin gaba susha ruwa, kamar wasa yaga shanukan sa, na kuka a bakin gaba, Alamu dai wani abin suka gani.

    Da sauri ya karaso wajen don yayi tunanin kada ne, koh wani mugun abu, tsayawa yayi turus yana bin abinda yake gani shida dabbobin sa, mutum ne, kwance baya motse kamar gawa, da sauri ya kad’a shanunsa har ya juya zai tafi don gudu rigima, daman ba shiri suke da manoma ba kar ace shiya kashesa, ya shiga uku.

    Sai kuma ya sake dawowa, haka kawai yaji hankalin sa bai kwanta da tafiya yabar gawan ba, nade kafar fantalelen wandon sa, na kiwo yayi ya shiga ruwan, jawo Al’ameen yayi, kiiiiiiiiii ya fitar dashi a ruwan, ajesa yayi a kan tabon bakin kogi.

    Kurawa fuskar Al’ameen ido gid’ado yayi tabbas wannan ba kabila bane, duk da fuskar tayi irin na fulani,Amma ba fulani husul bane, kyaun sanan akwai mix,ganin Hakan yasaka sa ciccibar Al’ameen, ya d’aura a bayan wuyansa yayi Rugan su dashi.

    Tun daga mahadin rugan su ake binsa da kallo, ganinsa d’auke da gawa a wuya, kowa ya tare sa, cemai yake shima a ruwa ya gansa, sosai wasu ke zagin sa meye na kawo musu gawa salon ya jaza musu bala’i, Amma shi sam bai damu ba tafiyar sa kawai yake.

    Isarsa gida ya tarar da mahaifinsa zaune a gindin bishiyar tsada a tsakar gidan su, sai innar sa dake gindin murhu tana girki.

    Assalamu Alaikum

    Waalaikum…….sai kuma ta dakata, bata ma karasa amsa sallamar ba, hadde yan boni, gid’ado dun dume, miyiyata do ha bahoma?(me nake ganin nan a bayan ka)

    Shuru yayi yana kallon ta, ganin yanda gabaki d’aya tabi ta gigice, bappan sa dake zaune a gindin bishiya ne, yayi saurin tasowa jin abinda inna kece wa.

    Gid’ado d’obo?bappan sa ya tambaya, yana nuna Al’ameen dake kafadar gidado.

    Bappa, kuyi hakuri bara na sauke sa sai in muku bayani, duk cikin fulanci suke maganar.

    Wani irin mu kwantar da hankali?kawai ka ciccibo mutum baya motse a kafad’ar ka, ka shigo mana ruga akan me?

    Don Allah inna a wad’a muyal, nima ganin sa nayi a bakin gaba, alamu dai ruwane ya jasa, koh aka yardashi, gidado yace yana kallon matarsa data fitoh daga d’aki, d’auke da tsohon ciki tana nufosu.

    Kwantar dashi gid’ado, in yaso koh sallah Amasa tunda naga kamar musulmi ne, bappa yace.

    Sauke sa gidado yayi, sosai bappa ya kurawa fuskar muhammad ido, yana nazari sai kuma ya d’aga ido yakalli gidado, Ai ohmayai(ai bai mutu ba)suma yayi.

    Da sauri gidado ya kara maimaitawa suma bappa?

    eh, yi sauri ka d’auko mini kwaryar magani a bukka, yana maganar yana dukawa kusa da muhammad, danne masa ciki ya farayi, take ruwa ya fara fita, ta bakin sa duk da baiyi motse ba, amma dai ruwan na fita sosai, bappa ya mammatse masa ciki.

    Matar gidado kam kujera ta samu ta zauna a hankali daker, sai ga gid’ado ya fitoh bukan bappa, da sauri ya ajewa bappa magani a gefe, bappa da lenki mai.

    Maganin bappa ya d’auka a kwarya, yana shashafa ma Al’ameen a fuska, da wuya yana masa Tofi,yana gamawa ya d’aga ido ya kalli gidado, husumo ayara ha sudu(ka daukesa ka kaisa d’aki)

    Wai bappan gidado ban gane a d’auke sa akai sa d’aki ba, yadaga ganin mutum bamusan daga ina ba, mugune koh nagari?kawai mu d’auko mu aje a cikin gidan mu, ni gaskiya ban yarda ba.

    Talatu kena bani mamaki wallahi, yanzun ace mutun baya cikin hayyacin sa, ina kikeso mu kaisa?

    Koma ina a kaisa, amma dai gaskiya banda cikin gidan nan, taima ma mugune.

    Koh mugune, mu Allah zai dubi zuciyar mu, insha allah bazai basa ikon cutar damu ba, bare ma wannan yaro baiyi kama da mugu ba, daga ka gansa kasan akwai jinin fulani a jikin sa.

    Lantana matar gidado kam, mikewa tayi ta shiga d’aki ganin fad’an bappa da inna baya karewa in gari ya waye .

    Kai gidado d’auke sa ka kaisa d’akin kusa da gindin murhu.

    Toh bappa, yace yana ciccibar sa yakai d’aki, shanu kansa dake binsa a baya tunda ya d’auko Al’ameen har gida, suya kama ya d’ad’aure a turke…….

    **************************
    Ta bangaren sumayya yau satin ta d’aya a Hospital, har da kwana d’aya, Amma jikin dai za’ace Alhamdulilah, da sauki kad’an duk da baiyi kwari ba, sosai likitoti ke kula da ita, hatta Dr tana iyya bakin kokarin ta, ganin sumayya ta samu lafiya, Amma taki kwantar da hankalin ta sam.

    Khadija ma yau sati guda, rabon ta da makaranta,suna faman jinyan sumayya, Goggo ke zama a asibiti, ita kuma ke musu girki a gida ta kawo musu, duk da sumayya baci take ba, sai yan aikace aikacen gida duk ita keyi.

    Kamar yau ma, khadija ce ta kammala girki a kofar sumayya, zuzzubawa tayi a kula, tasa a kwando ga flask a hannun ta, ta fitoh gidan Adara, tsallaka titi tayi ta nufi shagon yayan ta, shagari ta samu zaune yayi tagumi gabaki d’aya yaron ya shiga damuwa ainu na b’atan Al’ameen, duk da shike kula da shagon yanzun, amma sai yanajin shagon kwata kwata baya masa dadi.

    Assalamu alaikum.

    Wa’alaikumu salam, khadija zaki wuce hospital in kenan harkin shirya?

    Eh na gama girki.

    Ok yace yana mikewa, laida ya d’auko ya zuzzuba ayaba da kankana mai yawa, ya rufe shagon, kwandon hanun khadija ya kamar ba, ya bar mata flask in yana rike da laidan kayan marmarin a d’aya hannun, suka kama hanyar FMC da kafa, don shagari duk da muhammad baya nan, amma baya masa Almubazza ranci da kudi, asalima tattalin sa na yanzun yafi nada, hatta kudin asibiti duk Abinda aka bukata shiyake biya, ya hana sumayya kashe koh sisi.

    Sunzo sharan kwanan doruwa, kawai suka ga anyi packing moter a gabansu, khadija kam koh duban motar batayi ba, kokarin kaucewa take ta gefe, ta wuce abinta, dayake shagari bai wani waye Ammar ba, yasa bai ma saurare saba yabi bayan khadija.

    Ke yar kauye, mai tafiya bata kallon gaban ta.

    Da sauri khadija ta d’ago jin muryar Ammar,ina kwana?tace.

    Kin Amsawa yayi ya dubeta, ina zaku kuma da abinci haka.

    Asibiti, ta basa Amsa.

    Waye ba lafiya?

    Aunty sumayya .

    Subhanallah, yayan naki nacan ne?nima yau na dawo da asuba, shine nace bara na biyo gunsa.

    Shuru khadija tayi bata basa Amsa ba, sai kaucewa da tayi taci gaba da tafiya.

    Da sauri ya fitoh a motar, yabi bayan ta, keee ba magana nake miki bane?kina tafiya?

    Kala batace ba, tana ta tafiyar ta.

    Hannun ta Ammar ya rike, da sauri ta juyo tana kallon sa, sakemin hannu?

    Naki na saken, ina miki magana kina manna mini hauka, ina wasa dake?

    Kuka khadija ta sake masa da karfi, ai da sauri Ammar ya sake mata hannu, ya juya yana kallon shagari, dake tsaye yana kallon su, fuskar sa A hade, haka kawai yaji ya tsani Ammar, ganin yanda ya wani rikewa khadija hannu.

    Kai meke faruwa ne?Ammar ya tambaye sa.

    Fuska a hade yace, An sace oga ne shiyasa daka mata maganar, ina yayan ta, take kuka.

    Sai a lokacin Ammar ya gane shagari, watoh shine wanda muhammad yace zai d’auko su zauna a shago, abu na biyu daya basa mamaki kuma wai an sace muhammad, sai kace kaza, ban gane an sace saba?

    Eh an sace sa, haka kawai wasu a mota sukazo suka d’auke sa, a bakin titi

    Tsabar razana har tuntube yayi, yau kwana nawa kenan?

    Sati d’aya.

    Amma har sati d’aya, police basu d’auki wani kakkauran mataki ba?mutum ya bata kamar wani kaza koh d’uriyan sa babu?

    Koh report bamu shigar ba, Shagari ya basa Amsa.

    What?? ba’a kai kara ba, akan me?

    Sumayya na asibiti, ni kuma tsoro nake ji, shiyasa ba wanda yakai.

    Amma ai koh baku kaiba, nasan labari zaije wa yan sanda, tunda kuna kusa da station, yaci su subibiye Lamarin.

    Shuru suka, masa.

    Ku shiga muje asibitin, yace yana karban flask in da khadija ta dongorar, yasa a mota.

    Shagari ma shiga yayi ya zauna a gaba, har lokaci tana tsungune a kasa, hannu kawai Ammar yasa ya fizgota, ya jefa a bayan motar, ya zagaya driver sit ya zauna, yaja motar suka nufi Hospital.

    Suna shiga hospital in, dashi da shagari ne suka d’auko kula da flask, harda laidan, khadija kam an kaikaya mata inda yake mata kaikayi, kuka har lokacin yinsa take, duk yanda shagari keta bata baki tayi shuru, amma ina.

    Keeee wallahi in na sake jin koh tarinki, a asibitin nan saina saba miki, banason shirme tun d’azun, sai cika min kunne kike nayi shuru, yanzun mun shigo asibitin ma bazaki rufe bakin bane? saikin tara mana jama’a.

    Shuru khadija tayi, harga Allah wannan Ammar in kamar mai Aljanu haka yake, zafi zafi sanyi sanyi.

    Shagari kam gaba ya kara, dayake yasan d’akin da sumayya take, bai saurare tahowar suba, yayi tafiyar sa, yana maijin haushi a ransa.

    Shiya fara shigowa d’akin, da sallama.

    Amsa masa sumayya tayi, wance ke zaune daga ita sai dogon rigan kanti, kanta koh d’ankwali babu, tana zaune a bakin gadon, rike da wayarta, hawaye nabin kumatun ta.

    Ina wuni Aunty, ya jiki?

    Kai kawai ta d’aga masa, ta mika hannu ta d’auki d’an kwalinta, dake gefen gadon ta yafa a kanta.

    Zama shagari yayi yana bin d’akin da kallo, ganin baiga goggo ba.

    Assalamu alaikum, Ammar ne yayi sallama a bakin kofar d’akin.

    Amsa masa shagari yayi, ba tare da ya d’ago yaga bakin kofar ba.

    itama sumayya bata d’ago ba, sanin wake sallamar, don ta shaida mai muryar.

    Shigowa Ammar yayi, idanun sa ya sauka akan sumaya, dake zaune gabaki d’aya ta chanja, ta rame sosai sai haske data kara a yan kwanakin nan, har yayi yawa,tayi fari kamar ka tabata jini ya fitoh.

    A hankali ya tako har inda take, hannu yasa ya amshe wayar, sai a lokacin sumayya ta d’ago ta dube sa, hade da mika masa hannu, Alamun ya bata wayar ta.

    Matsawa yayi gefe, ya kurawa screen in wayar ta ido, hoton tane da suka d’auka, ita da muhammad ranan sallah a gidan su.

    Sumayya ya kamata kima kanki fad’a, wannan abinda kike kara cutar dakan ki kike, kuka bashi ne magani ba, koh mafita, kin zauna kina kuka, gaki ba lafiya bane dake, ki dubi yanda kika koma fisabililahi.

    Gaya mata kam D’an nan, haka nake fama da ita, bansan me take gani a wayar nan ba, ta tura khadija ta d’auko mata, shikenan tamai dashi madubi, tana kallo tana kuka, goggo data fitoh a toilet na d’akin ne take maganar.

    Hoton mijin tane a ciki mama, Ammar yace yana latsa wayar sumayya, dake hannun sa.

    Au shiyasa take kuka?/lalle sumayya baki jiran kanki, kiga yanda kika zama gabaki d’aya kin koma, kashi da rai sai haske da kike tayi kamar mai ciwon far d’aya.

    Kyaleta mama, hotunan duka zan goge.

    Kuka sumayya ta sake, jin abinda Ammar yace wai zai goge hoton muhammad a wayar ta”ka bani wayata karka goge na rokeka don Allah”

    Ah ah bafa zan baki ba, in gaya miki, tunda zaki tasa wayar a gaba kina kallo kina kuka.

    “Allah nayi Alkawari zan daina” tana magana tana kuka

    Toh yanzun me kike in ba kukar ba?

    Don Allah ka bata wayar ta, sai kuka take tana maka magiya, kana wani ja mata rai, khadija ce tayi maganar cikin jin haushi ganin iyayin da yake ma Auntin ta.

    Wani kallo Ammar ya watsa mata, jin maganar da take masa kamar sa’arta.

    Bata sake magana ba, aje abincin tayi tana kallon sumayya, in zuba miki Aunty?

    “Ah ah banaci”

    Wani irin bakici?sumayya yau kwanan mu tara a asibiti, abinci kirki baki ciba ya za’ayi kiyi lafiya.

    Shuru sumayya tayi, ta koma ta kwanta bata kara magana ba, don ta fahimci bazasu gane abinda ke damun ta ba.

    Ammar kam kallon khadija yayi ya sake kallon, Goggo,meke damunta , sukace mama?

    Damuwa ce d’an nan, hawan jinine ya kamata, maimakon ta nutsu ta samu lafiya, Amma ina sai kara kwantar dakan ta take A gado.

    Allah ya bata lafiya, in ba damuwa mama, ina so zan fara bincike akan case in batar Al’ameen, in muna bukatar cikekken bayani zan tuntube ku.

    Ba kome yaro mun gode, Allah ya saka sai dai ban gane kaba?

    Abokin muhammad ne.

    Au koh dai kaine Ammar, da yake sanar dani ka bude masa shago?ai munga abin Arziki Allah ya biya ka.

    Ameeen mama.

    Sai a lokacin shagari da khadija, suka san Ammar ne ya bude ma Al’ameen shago.

    Fita Ammar yayi bai bawa sumayya wayar taba, ita ma bata sake magana ba.

    Ta bangaren Al’ameen kam har dare bai dawo hayyacin sa ba, gidado yayi ta zuwa dubasa yafi a kirga Amma shuru.

    sai da gari ya waye, ya farka jujjuyawa yayi sai kuma ya bude idanun sa, da sauri ya koma baya da mamaki, ganin yarinya budurwa zaune a gaban sa kyakky……………..🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

     

  • Matar Makaho 94-95

    Matar Makaho 94-95

    Page9⃣4⃣&9⃣5⃣
    Bayan ta ya rike sosai ga wani irin ciwo da taji a maranta lokaci d’aya ta gigice tana salata tunda take bata taba jin ciwo irin na yau ba, Ambaton Allah kawai take a ranta gabaki d’aya ta had’a gumi, jin wani abu na zuba babu control ya sata tsorata ruwa ne yake dundula, salati ta sake hade da kwalawa khadija kira.

    Khadija dake bacci kamar a mafarki taji muryar sumayya mikewa tayi ta nufi ban d’akin da sauri ta bude wazata gani? sumayya ce duke jikinta sai rawa yake gabaki d’aya ta had’a gumi a tsorace take tambayar ta haihuwa ne? sumayya bata samu Amsan bata ba, nuni kawai ta mata ta kira mata mota su tafi asibiti, ba musu khadija tad’au hijab tasa akan kayan baccin jikinta, ta ruga da gudu ta fita a falon, sakatan get in ta zare ta fita bakin kwalta, abinka da dare koh tsuntsu bata samu ba koh ina shuru, kuka ta sa da gudu ta dawo cikin gidan, kofar d’aya makwanciyar su ta wuce tana buga wa, amma basu bude ba gashi kaf gidan babu mai mota koh mijin laila ma ba motar bane dashi.

    Haka da dawo sashen su, tana shiga zuwa lokacin jikin sumayya ya kara tsanani sosai koh zama ta kasa har lokacin tana tsungune.

    Da sauri ta d’auki wayar ta layin kalamu ta kira, sai da ta masa kusan 4 miss call kafun ya d’aga cikin muryar bacci yake tambayar ta lafiya?

    Ai tana sanar dashi da sauri ya mike ya zura jallabiyar sa ya fitoh a d’akin sa, harya tura kofar falon su zai fita saiga nannen sa ta fitoh daga dakin ta, tambayar sa tayi ina zaije a daren nan?

    Sanar da ita yayi Auntin khadija ba lafiya tana labour, tambayar sa tayi mijin tafa,Amsa ya bata shidai bai taba ganin mijinta ba, yama ga alamu bata da miji, jin haka yasa nanne d’aukar hijab nata ta sanar da mijinta zasukai sumayya asibiti, suka fitoh tare dashi mota kalamu ya fitar suka shiga sai get insu sumayya, fita nanne dashi sukayi zuwa ciki.

    Zuwa lokacin sumayya tayi laushi sosai koh gane wake kanta bazata iyya ba, dayake dare ne nanne da khadija ne suka ririketa yayinda kalamu ya diauki akwatin ta, data jima da shiryashi a zaune, rufe musu kofar yayi suka tafi asibitin da sumayya ke awo.

    Suna zuwa aka karbesu nanne na zaune a waje ita da khadija, kalamu keta hidima na sayyan abubuwan da aka bukata koh zama bai samu, har 4 na asuba sumayya haihuwa ya gagara, gabaki d’aya karfin ta ya gama karewa sai da aka kira Assalatu kafun haihuwa yazo gadan gadan, cikin hukunci Allah sumayya ta haifi yaran ta guda biyu wanda koh sanin wani iri ta haifa bata sani ba, tsabar wahalar da tasha, tadai san ta haihu sau biyu, Alluran hutu aka mata bayan an kimtsata a take bacci ya d’auke ta.

    ******************
    Bugu d’aya Al’ameen ya d’auka a take Ammar ke sanar dashi anga wajen da khadija take, suna Abuja.

    Ai muhammad baisan lokacin da ya wantsalo daga kan kujeran falo, a take yayi sujjada akan tiles yana wa Allah kirari, goggo da mahmah dake zaune a kasan falo suna cin abinci da sauri suka mike suna tambayar sa lafiya?ai da sauri ya mike ya rungumi mahmah cikin farin ciki yake sanar da ita anga sumayya anga sumayya tana Abuja.

    Ai sosai suka nuna farin cikin su goggo harda kuka, a take Muhammad ya fitar da waya ya kira abie ya sanar dashi akan yanzun nan zai tafi gidan su Ammar zasu wuce abuja.

    Hanasa Abie yayi yace ya bari sai da safe sai subi fly zai sa a nema musu ticket sai su tafi tare da abie, ai a take goggo ma tace zata mahmah ma tace ita ma, dada dake kusa da abie tace itama baza’ayi ba ita ba, duk yanda abie da muhammad sukayi da tsofinnan su zauna a Taraba, su zasuje su dawo da sumayya amma kememen sukace kafar su kafar su abie, haka ba yanda abie ya iyya duka aka musu booking in fly tare da kiraye kirayen waya har nijar aka sanar dasu an samu wajen da suke, suma sun sanar dasu a cikin satin nan suna zuwa gabaki d’ayan su.

    Washe gari tun sassafe suka bar Taraba muhammad koh bacci jiya kasawa yayi, dada ma haka ta watsar da safina tace sai taje taga jikallen ta, Ammar ma tasa Abdul yayi a gaba tare zasu ya nuna musu gidan su kalamu.

    Karfe 9 su muhammad suka dira a Abuja, dayake yana da aboki, tun a taraba ya kirasa akan suna zuwa, tarba suka samu daga wajen abokin abie shiyazo ya d’aukesu a Airport, direct gidan su kalamu suka wuce, Amma abin haushi basu sami kowa ba wai Suna asibiti, haka mai ganin ya sanar dasu Alfarman ganin baban kalamu abie ya nema ba musu, mai gadi ya shiga ga sanar dashi, aiko sai gasa bayan sun gaisa ne sukace masa suna son sanin asibitin da kalamu sukaje in ba damuwa.

    Ganin girman su da kudin su, gashi kamar ba lafiya ba, hakan yasa baban kalamu yace musu bara ya bisu asibitin, shiga mototi sukayi ya kira nanne ya tambaye ta asibitin da number room nasu, da mamaki yake tambayar ta koh lafiya jin muryar ta ya dishe-dishe alamu dai ba lafiya ba, koh tayi kuka, ya tambaye ta lafiya tace masa ba kome, kashe wayar yayi ya sanar dasu abie ga asibitin da suke.

    Suna isa asibitin muhammad da gudu ya ruga bayan sanar dashi block inda suke koh kunyan su abie baiji ba da gudu yayi block in mutane sai kallonsa suke, da sauri sauri ya shiga d’akunan one by one yana dubasu, ana ukun ne ya shiga koh sallama babu ganin mace kwance akan gado ga yara sa’o’in juna zaune rike da jinjiraye a hannayen su, da sauri suma suka juyo jin mutun a d’akin babu sallama.

    Ai da sauri khadija ta mike ta kwala ihu yaya!!!!!!!! Da sauri kalamu dake kusa da ita rike da d’ayar babyn da sauri ya cafke wance ke hannun khadija, don saura kad’an ta buga jinjira, da gudu khadija tayi wajen muhammad batayi wata wata ba ta rungumi d’an uwanta tana fashewa da kuka yaya, kaine koh mafarki nake?

    Khadija nine nine khadija ina Aunty ki?

    Allahu akbar yaya kalli nan tace tana nuna masa kan gadon da sumayya ke kwance har yanzun tana bacci.

    Da sauri ya ware idanun sa yana kallon sumayya sai kuma ya juya ya kalli kalamu, ya sake kallon khadija?

    Gyada masa kai tayi tana murmushi, shima murmushin yayi sai kuma ga hawaye, tare da matsawa kusa da gadon da sumayya take kwance, dukawa yayi akan gwuwar sa hannu yasa a hankali yana shafa fuskar sumayya, dake kwance sanye da kayan asibiti, tayi kyau tayi fresh irin na masujego, wannan ce sumayyar tawa ashe haka take da kyau masha Allah?

    Itace yaya kaga wa’innan jarirai nakane.

    Da sauri ya juya yana kallon kalamu da sauri ya mike tsaye hannu yasa ya Amshi babies in yana kallon su, yarane mata masu tsananin kama da junan su tamkar An raba kunu a kofi, gasu masu tsananin kama dashi kome nashine a fuskar yaran, gasu farare tass, rungumarsu yayi ya fashe da kuka.

    Toh ragon maza baka da aiki sai kuka, mahmah da suka shigo cikin d’akin tun d’azun, amma basu ma san da su ba.

    Da sauri ya nufi mahmah yana ce mata, mahmah kalli yaran nan, wai yarana ne kallesu fa ga sumayya mahmah kyakkyawa fa sosai?
    .
    Sunkuyar da kai abie yayi yana mamakin surkin nan nasa yau koh dai ya mantasa a wajen ne, shima da sauri ya nufi wajen da yarsa ke kwance, zama yayi a bakin gadon yana shafa gashin kanta daya hargitse koh ribon babu.

    Mahmah ce ta karbi baby d’aya dada ma ta karbi d’aya goggo kam baki kawai ta sake tana bin kowa da ido, kalamu kallon babansa yayi dake gefe, ya gaidashi, amsawa yayi yana tambayar sa mai jiki.

    Matsawa kusa da abie muhammad yayi ganin sumayya ta fara motse, a hankali ta bude idanunta dalilin kukan da yaranta suka sake dukan su biyu.

    Tana bude idanunta bata sauke sa akan kowa ba sai muhamamd dake kanta a tsaye, kamar a mafarki haka ta kalli abin da sauri ta mike zaune har tana kokarin zamowa kasa, da sauri ya tarota, bi a hankali sumayya jikin ki ba kirfi.

    Ai jin abinda yace da sauri ta riko hannunsa gam tana kwalama khadija kira, Amsawa khadija tayi da sauri ta karaso wajen”khadija yayanki ke mini gizau na kamasa ”

    Aunty ba gizau bane yayane

    “Yaya kuma khadija mijina fa baya gani yau kuma naga wannan na gani”?

    Aunty ya warke ne.

    Ai sumayya najin haka ta sake dariya cikin farin ciki koh damuwa da jikinta batayi ba ta rungume mijinta, don ita sam hankalin ta vaikai wajen mutanen d’akin ba.

    Mikewa abie yayi dasu mahmah zasu fita a dakin su basu waje don sukam kunya ne zai kashe su.

    Nanne dake toilet tana wanke kayayyakin sumayya daya baci, tun d’azun take jin surutai a d’akin mikewa tayi tsaye da boket na kaya a hannunta ta bude kofar toilet ta fitoh, Wai khadija da kalamu anya kuna da hankali kuwa mara lafiya na bacci kuke surutai da wa……bata karasa ba tayi turus ganin jama’ar dake shirin fita a d’akin dasuka juyo suna kallonta.

    Dada ce ta kama salati tana tafa hanneye, wanake ganin nan?

    Abie ma da sauri yace Hafsa??

    Nanne kam bata wani nuna reaction ba, dayake tun daren jiya data gane sumayya tasan tabbas zata ga su abie, duk da saurin da take tabar asibitin kafun suzo don ita batasan sumayya gudu tayi ba, haka ma batasan itace Aunty khadija ba sai daren jiya.

    Nanne bata wani Amsa ba bare ma ta nuna tasan abie, sai tsayuwar da tayi tana kallon sumayya data sake muhamamd tana kallonta sosai irin kallon nan na kewa da soyayya, cikin kuka tace” ummi”?

    Sai a wannan karo nanne tayi magana, Na’am momcy?

    Da sauri sumayya ta sauka akan gadon tana takawa a hankali cikin dauriya tayi wajen mahaifiyarta fad’awa tayi jikinta tana kuka yau kam ta rasa ina zata sa kanta, murnan samun babies koh murnan ganin mahaifiyarta koh mijinta dole tayi kuka, ummi karan kanta hawaye ne ya cika a idanunta tana shafa kan sumayya ya isa haka momcy yi shuru kinga ba lafiya bane dake koma ki kwanta, tana maganar tana rike da hannun sumayya har ta kaita bakin gadon ta aje ta.

    Waini yau hafsa nake gani ne koh gizau idanuna kemin koh mafarki nake ne?

    Itace dada Abie yace yana dafe kansa cikin takaici da bakin cikin abubuwan da suka faru a baya.

    Mijin hafsa ne yace, Hafsa kin sansu ne daman nina d’auka koh iyayen yarinyar nan ce?

    Baban kalamu ne da kakarsa wannan kuma Addansa ce ta nuna sumayya.

    Daga sumayya har kalamu da Abie a tare suka jefowa Hafsa tambaya lokaci guda, baban kalamu wani kalamun?

    Da sauri abie yace hafsa ban gane ba wanene kalamu.

    Nuna masa kalamu tayi dake tsaye cikin shock na abinda nanne tace, yanzun wai sumayya Addansa, ta yaya kamar ya?baigane ba?

    “Ummi kina nufin kalamu d’an uwa nane”?

    Hafsa kina nufin wannan yaro, yaro nane?

    Kallon sumayya da abie hafsa tayi jin tambayar da suka jefo mata, eh kawai tace tana kama hanyar kofa zata fita tare da kallon mijin ta, yauwa Alan guburo mutafi naga dangin ta sunzo zasu zauna a gunta.

    Ah ah hafsa zuwan mu bazaisa ki daina hidima da yarki ba.

    Ah ah dada zan tafi , Allah ya sauwaka momcy.

    “Ameeen ummi in zaki dawo a kawo mini sabulun wanka”

    Toh momcy muje kalamu koh zaka zauna ne?

    Ah ah nanne muje yace yana kallon abie da mamaki wai wannan ne babansa, shi abin ma yajisa wani banbara kwai.

    Kokarin fita a dakin suke a hankali abie ya kama hannun kalamu daya wucesa zai fita a d’akin, kalamu bazaka ma abie magana bane?

    Murmushi kalamu yayi sai kuma yaji hawaye ya taro masa, abie ashe kanason na maka magana, shine zaka kyamace ni ka kyautata rayuwar yar uwata, amma ka wofantar da nawa rayuwar ka barwa uwata ni, na zauna a matsayin agola a gidan da, bana ubana ba ya maye gurbinka ina Amfani da sunan sa koh a makaranta, bai taba nunawa duniya bashi ya haifeni ba koni bansan bashine mahaifina ba, sai yau akan me zan maka magana ni bansan wani uba ba sai ……..

    “bai karasa ba sumayya ta mike ta wanke sa da mari cikin bacin rai ta soma magana, karka kuskura ka fara abinda zai dame ka wallahi kayi kad’an ka zagar min uba na barka,ni a haka nake son abina koma me zaimin bazan taba kinsa ba” sai kuma ta kama kuka.

    Da sauri nurses dake falo suka shigo d’akin, akan surutun dake tashi, hakuri aka basu akan za’a kiyaye magana ne mai muhimmanci ake, ganin kalarsu yasa su barinsu a dakin.

    Daker aka samu suka sassanta nanne ta koma gida dasu goggo yayinda mazan kuma suka koma hotel sumayya ma ita da dada kadai aka bari a hospital.

    Washe gari aka sallame ta saboda kyaun da jikinta yayi, don haihuwar duk da yazo da gardama amma tana haihuwa shikenan.

    Gidan nanne aka maidata bata koma gidan hayansu ba,sosai ake kula da ita muhamamd a rana sai yazo sama da sau hudu, sai da sumayya ta kwana hudu da haihuwa kafun suka koma shirye shiryen dawowa jalingo don anan ake son yin taron suna gashi yan nijar ma sunce suna shirin zuwa, duk yanda sukayi ta rokon nanne ta biyosu taki tace bazataki bin umurnin mahaifinta ba na raba kanta da zuriyar shugaba, saida mijinta ya nuna bacin ransa da nuna mata yaranta nada hakki akan ta, sannan kalamu bazaiji dadin hakan ba tunda shima so yake yaje yaga dangin babansa, daker dai ta Amince washe gari da sumayya ta cika kwanan biyar sukabi jirgi saijalingo.

    Muhammad murza idanunsa yayi yace a gidan sa da babansa ya sai masa a Amazon sumayya zata sauka, ba musu duk da abie yaso ta koma gida Amma ganin hafsa da Al’ameen basason hakan.

    Gidan sumayya ta sauka dayake babban gidane ga d’akuna shiyasa gidan ya d’auke su, duka harda su hafsa falmata su babayo muhamamd goggo dasu mahmah, kalamu kam shugaba family house ya sauka kuma ba karamin farin cikin ganinsa sukayi ba.

    Babu inda haihuwar sumayya bai bazu ba jama’a sai tururuwan zuwa dubata suke harda yan Abuja laila ma daga adamawa ta gangaro, a ranan yan nijar suka diro nageria gabaki d’aya yan uwan yusuf ne harda shi karan kansa ma, wannan zuwa harda lawiza da nabila, sosai gidan ya dad’a cika da yan uwa kota ina yan gidan shugaba ma tun a washe gari suna matan suka diro, yusuf a gidan sarki ya sauka dayake suma ana gobe suna suka zo, kai sumayya taga jama’a iyya jama’a ga wani irin lalle da aka watsa mata mai masifar kyau da ketson suna duka.

    Yau take suna yara sunci suna NA’IMA da NA’IFA , tun Asuba yan gidan Adara suka diro su inna asabe inna lami Ana gindin murhu a sauke wanshan a d’aura wanshan, shanu uku aka yanka da rago biyu, duk suna ta kan gyaran nama, ga abinci kala kala, gashi koh ina ka leka zakaga group group na mata kowa da angon su mai zafi, wanda abie ya d’auki nauyi duka, yan nijar nasu da ban haka dangin adara, yan shugaba family house ga yan gembu, ashan gefe naga MATAR MAKAHO FAN’S ansha anko na Atamfa mai ratsen flower green ana zazzaune ana dirkan shinkafa a manyan tireruka hhhhh.

    Sumayya dake sanye da wani hadedden material gown wanda yasha dinki ga sarka na d’anyen gwal da sarki ya bada aka kawo mata, sarkane da dankunne sai warwaro ga agogo mai zafi na mata duka, tasha heavy make-up sai d’aukan hotuna suke da kannen Ammar dake sanye da Ankon su, khadija da kalamu dake zaune a gefe suna cin shinkafa.

    Muhammad da Ammar harda su ramadan zulkiflu gidado badaru duk yanzun sun chanja kamar basu ba, suna zazzaune a kofar gida a rumfar da aka kakkafa abinci suke ci mairai da lafiya.

    Tun daga nesa suke jin ihun yara da mutane suna rugawa a guje, da sauri suka mike gabaki d’ayansu suna kallon abinda ke faruwa.

    Mutum suka gani kamar mace ne koh na miji bazasu gane ba, kadangaru manne a jikin sa tana gudu suna binsa wasu na jikin ginin unguwan suna rugowa suna binta sosai kota ina kadangaru ga wasu runduna na binta a baya, sai wata mata dake gefenta rike da sharbebeyar bulala tana kad’a mai kadangarun suna tafiya a haka.

    Da sauri su muhammad suka ruga cikin gida da gudu har ana rige rige, ganin wajen da suke suka nufo.

    Suna shiga suka rufe kofar gidan da karfi suna ji sai bugawa matar take akan don Allah abude mata, kiri kiri su muhammad sukaki budewa har abin yaja hankalin matan dake compound sosai, dada dake rike da jinjira zata kaiwa kawayen ta dake falo a zaune ssga dayar, itace taji hayaniya aje jinjiran tayi ta fitoh compound, ganin su muahmamd da jama’ar tsakar gidan a tsaye yasata karasawa bakin get in tana tambayar dalili, kafun ma su muhammad suyi mata bayani tuni tasa hannu ta zare sakatar get in, ihu Ramadan ya sake tsabar rikita yare ma ya fara.

    Dada na budewa idanunta ya sauka akan matar dake rike da bulala kwalalo ido tayi cikin mamaki tace wanake gani anan kamar Nafi………….

    kafun ma ta karasa maganar ta idanunta ya sauka akan wance ke tsaye mammanne da kadangaru ga bataliya a kasa, ai ihu dada tasa ta ruga ciki da gudu, da sauri inna lami tazo zata rufe get aida sauri wannan matar ta banke kofar ta kora mai kadangaru ta shigo, itama shigowa tayi, ai ana ganinta, ihu ne yake tashi abinka da mata atake masu Aljanu Aljanunsu ya soma tashi, gidan suna gabaki d’aya ya rikice ya zama gidan tsere kowa gudu yake yana burmuwa falo wasu kitchen masu Aljanu kam sun zuzzube…………..

    ✨Ruqeenjalal✨🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
    🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯
    ~ Na ~

  • Matar Makaho 60-61

    Matar Makaho 60-61

    Page6⃣0⃣&6⃣1⃣
    Da sauri ta d’ago kanta jin yanda yayi maganar a matukar sanyaye, kamar wanda zai nemi Alfarma itafa halaliyar sace,amma ga yanda yake had’ata da Allah, yayi matukar kokari, yanzun ana neman kusan wata uku da auren su, koh ma fiye da haka, ba tare da ya taba tilasta ta akan hakkinsa, kullum ya bukace hakan, zata saka masa kuka, koma hakan koh baya so yake kyaleta.

    Jin batace kome ba yasa sa lalubar fuskar ta,In baki Ra’ayi kiyi hakuri sumayya,na hakura.

    Da sauri ta kamo nasa fuskar hawaye na cika mata ido, “yayan khadija hakkin kane fa?kaima da kanka ka fad’a, kaga kenan ni bani da damar hana ka, tunda naka ne, duk abinda zaka bukata a gareni mallakin kane, na amince kayi duk abinda kake so dani, ta karasa maganar da fashewa da kuka.

    Jin ta fara kuka yasa muhammad, da sauri yace, sumayya kiyi hakuri nama hakura, shikenan tashi kisa kayanki mu kwanta.

    “Ba kuka nake ba”

    Hannu yasa ya shafo kumatun ta, toh me kike, kuma menene a fuskar taki?

    “Kayi hakuri”

    Fuskar sa ya had’a da tata fuskar, baki min kome ba sumayya.

    “Toh insa kaya koh haka xamu kwanta” ?

    Shikam ba karamin dariya sumayya ta basa ba harya kasa hakuri, saida ya dara, hhh menene haka kuma sumayya?

    “Toh ba tambaya nayi ba, koh tambaya laifine”?

    Ah ah ba laifi bane, yace yana d’aura fuskarsa a kafadar ta, yana goga mata gemunsa.

    A hankali sumayya ta manne masa gam a jiki, hannu tasa ta kama gashin kansa, jin kamar zai zautar da ita, jin bakinsa akan wuyan ta.

    Ahhhh, yace yana kamota, d’agota yayi gabaki d’ayan ta, yana lalube harya hau gadon, kwantar da ita yayi ya hau kanta, bakinsa ya jona cikin nata, sosai yake tsotsar bakin ta, jikinsa sai rawa yake.

    Sosai sumayya ke tare da farga ba, don yanayin muhammad kawai yau zai tabbatar maka, da gaske yake son Angon cewa.

    Washhh Ashhhhh sumayya tace, lokacin da taji muhammad ya yaye mata towel in jikinta, shima tuni ya watsar da nasa daga ita harshe babu sutura a jikinsu…….

    Zafafan Romance Al’ameen yake wa sumayya, da zafi zafi don A lokacin bazaka taba tunanin koh baya gani ba, aikin dake gabansa kawai yake.

    Sumayya dake kwance rumtsa ido tayi, jin Al’ameen na ware mata kafa, bakinsa d’auke da Addu’an saduwa da iyali

    Kara ta kwala da karfi, tare da ware ido, jin wani Al’amari mai girma daya ratso rayuwarta, a karon farko hannunta dake free, ta d’aga a zabure ta cakumo gashin kansa.

    Da karfi ya fizgo Hannunta, daga gashinsa ware hannun yayi ya danne da jikin katifa, sosai ya kara bada himma akan abinda yake, bai taba d’aukar zaiji wani d’adi ba tunda Abbajon sa ya barsu, wahalar rayuwa bai barsa ya tuna akwai wani dadin da zai iyya d’and’ana wa, maka mancin wannan dadin ba, sai gashi yau sumayya ke shayar dashi.

    Sumayya kam gumi ta had’a sosai, duk da an fara yayyafi, Amma daga ita har muhammad zufane ya jikasu, sosai sumayya ke kuka tana goga kanta da jikin pillow, ba zafin da Al’ameen ke d’and’ana mata bane yafi ratsata, wani irin sarawa taji kanta nayi kamar wance ake fisgar gashin kanta da karfi, haka takeji a kanta kuka tasa, don abin ya hade mata biyu, ga azaban da Al’ameen ke gana mata sosai, kanta ke bugawa ji take kamar kwakwalwarta zai fita, sai salati take tana murza kan da filo.

    Ta bangaren Al’ameen kam, yau ba’aji ba’a gani am amsa sunan MAKAHO yau, don koh kukan sumayya baji yake ba, hankali..sa na gefe, damuwar sa kawai yaji abinda yake gabansa.

    Sumayya jin wasu irin bugawa da kanta keyi akai akai jijiyoyin kanta takeji kamar zasu tsinke, koh gani bata iyyawa yanzun sosai, duk da a duhu suke Amma duhun da take kallo yanzun yafi karfin duhun d’akin.

    Sosai bakin ta ya bushe, sai shakuwa take, tana kiran ruwa da muryarta da baya fita sosai.

    Amma ina muhammad baisan tanayi ba abinda yasa agaba yake fama.

    Jan numfashi sumayya tayi da karfi jin wani irin wahalallen shakuwa, ya gudu da numfashin ta duka, sakewa tayi jagab ta koma jikin filo,

    Muhammad bai farga da halinda sumayya take ciki ba sai da ya gama samun nutsuwa, A hankali ya zare jikinsa a nata, aiji yayi kamar an watsa masa Allurai a idanun sa, soki yakeji a cikin kwayan idonsa, sunfi d’ari rumtsa idon yayi da karfi, yana kiran sunan Allah jin wani irin barkono da soki na cakansa, tunda yake bai tabajin azaba irin wannan ba, kansa ya had’a da jikin gado da karfi ya buga ji kake gauuuuu ………..ya sulale kan katifar baya motse.

    Har Asuba muhammad da sumayya suna sume, basu farfado ba, babu wanda yasan halinda suke ciki, sai mahallincin mu,

    A Hankali sumayya ta fara motse, a hankali take kokarin bude idanunta, sai kuma ta maida su ta rufe da sauri, jin wani irin nauyi daya mata, sai da tafi minutes 10 kafun ta sake bude idon, a hankali harta budesu duka, ware idon tayi tana kallo dishi dishi har idanunta suka sauka akan muhammad, dake yashe a gefe ga goshin sa a fashe.

    Cikin matukar razana ganin sa kamar wani matan ce, haftowa tayi da kuzari zata mike, kara ta sake tana Ambatan sunan Allah, ta koma ta kwanta jin wani irin rad’ad’i dake ratsata, ta kasa

    A hankali ta mike zaune, tana cije lebenta, ta fara rarrafawa zuwa garesa, matsowa tayi sosai ta tattabasa jin baya motse, yasata sake kara”innalillahi wa’inna’illahi raji’um nashiga uku, don Allah muhammad karka tafi ka barni wayyo nashiga uku, wayyo mijina na bonu,ganin kamar suma yayi, sai kuma ta rarrafa da sauri taja blanket in ta rufe masa jiki, da rarrafe ta sauka akan gadon, towel inta dake yashe a kasa ta d’auka ta d’aura.

    Firij ta wuce ta d’auki ruwa, haka ta rarrafa ta iso bakin gadon ta saitin da yake, hannu tasa ta bude bakin goran, ta tsiyaye ta wasa masa a fuska, Amma ina shuru muhammad bai tashi ba, kuka ta sake tana bulbula masa ruwan sanyin a fuska, Amma koh motse baiyi ba,”wayyo muhammad wayyo mijina, na shiga uku Allah ka taimake ni”

    A matukar gigice ta saka kunnen ta a kan kirjinsa, jin zuciyarsa na bugawa, yasa hankalin ta kwanciya don ta gane suma yayi.

    Tunawa tayi da number maimuna kanwar Ammar, a wayan ta koh ta kirata ne? ta had’ata da Ammar koh Zai taimaka mata mijinta ya tashi tunda itama, tana bukatn taimako, gashi bata san wazata kira ya tallafa musu ba.

    Da rarrafe ta isa kusa da wayan d’auka tayi jikinta sai bari yake, ta kira maimuna tanajin ta d’aga tace”Assalamu Alaikum”

    Wa’alaikumu salam Aunty sumayya ina kwana?

    “Lafiya maimuna don Allah Ammar na gida”?

    Lafiya kam aunty sumayya, naji muryan ki a dishe?

    ” nace miki Ammar na gida”?

    Ah ah wallahi yau yabar gari da asuba lfy?

    Kashe wayar in sumayya tayi, don bata da lokacin maimuna.

    Da sauri wani tunanin yazo kanta, ta rarrafa ta isa wajen kayan sa, budewa tayi tana ciro masa kaya, in yaso sai ta saka masa, ta fita ta kira keke su tafi asibiti, duk da ba lafiya bane da ita, koh da rarrafe zata fita ta taimake rayuwar mijinta.

    Kayan sa ta bude ta, dauko jallabiya tayi ta aje, tasa hannu zata d’auki gajeren wandon sa, taji hannunta ya taba wani abu mai karfi kamar gidan agogo, hannu tasa ta zaro abin, haka kawai taji hankalin ta bai kwanta da wannan karamin akwatin ba, hannu tasa ta bude.

    Da sauri ta rufe Idanun ta ganin wani irin haske daya kashe mata ido,A hankali ta sake bude ido ta kurawa sarkan ido, yayi haske yasa ke mutuwa farine sosai, mai kyau sai zanen zaki dake tsakiyar gaban sarka, sosai sarkan ke sheki yana komawa normal.

    Jiki na bari ta rike sarkan, indai bata manta ma Al’ameen yace baban shi ya basa sarka, koh dai wannan ne sarkan? menene dalilinsa na cirewa? a wuyansa, rarrafe tayi ta isa garesa, sarkan ta d’auka ta d’aura masa a wuya.

    Ai sarkan nan na shiga wuyan Al’ameen, ya wani irin haske sosai sai kuma ya koma normal bai sake hasken ba.

    Da rarrafe sumayya ta fita a kofar dikin”subhanallah”tace ganin har rana ya fitoh don lokacin ana neman, kusan karfe 8:00 na safe koh sallan asuba basuyi ba,da rarrafe ta shiga kitchen kittle ta jona a soket, tana zaune a wajen ya tafasa juyewa tayi a boket, ta sake saka wani saida ta juye kittle uku,sannan ta fara kokarin mikewa,don d’aukar boket in ta juye a band’aki, Amma ta kasa, kuka kawai ta sake, ta koma ta zauna.

    Muhammad kam tunda sumayya ta fita a d’akin ya farka, sosai idanunsa ke masa zoge kamar an kwakule masa su,tun d’azun yana kwance don duk jikinsa a sake yake.

    Da sauri ya mike zaune jin kukan sumayya ta window, sai yanzun tunanin abinda ya faru ya fado masa,take yaji tsikar jikinsa ya miki, hasbinallahu wani’imal wakin, yace yana mikewa zaune, dafa kansa yayi da karfi jin wani irin rad’adi a inda ya buge, a haka dai ya lallaba ya mike zaune, jin baida sutura a jiki yasa sa fara laluben gadon, ji kawai yayi hannun sa ya taba wani abu damshe damshe, ga karnin jini.

    Da sauri ya mike, sauka yayi ya d’auki wando a cikin kayansa ya saka, yana dafe da kansa har lokacin idanunsa a rufe suke.

    Sumayya!!!sumayya!! Menene?yace yana karaso wa kusa da ita.

    Ai barin kukan sumayya tayi, ta zare ido ganin Al’ameen akan kafafunsa, hannu tasa ta kamo nasa hannun”na kasa tashine, ga rana yayi bamuyi wanka ba, gashi ina son kai ruwa band’aki na kasa, gashi ka suma hankali na ya tashi”tana maganar tana kuka.

    Rungumar ta muhammad yai da karfin gaske, A hankali ya bude baki daker, kamar yanajin tsoron magana, sumayya ina sonki, sumayya ina tsananin kaunar ki, bazan taba mantawa da daren jiya a rayuwa ta ba, har abada kece cikon farin cikina, ina fatan har in koma ga Allah, karna miki butulci matata.

    Kara rungumar sa tayi sosai, taji wani sanyi a ranta da tausayin mijinta”nima babu abinda zance maka sai dai na mana fatan gamawa da duniya lafiya, mijina har abada bazan taba barin kaba harsai ranan da na daina numfashi in Allah ya yarda.

    Toh bakice kina sona ba?

    “143”

    Meyake nufi?

    “Kayi tunani mai zurfi, wanka nakeso nayi nayi sallah, rana yayi ka kaimin ruwa bayan gida”

    Toh yace yana saken ta, boket na ruwan zafin ya d’auka, yana tafiya har lokacin idanunsa zafi suke masa, kuma bai bude suba.

    Bayan ya aje ruwan, dawowa yayi ya ibi na sanyi a wani boket in daba.

    Sumayya dake zaune har lokacin a dakali”ga baf a kitchen ka kaimin ban d’akin”tace masa

    Haihuwa kikayi ne wai gimbiya?

    “Mutuwa nayi”

    Insha Allah ba yanzun ba, yace yana d’aukar boket in, kaiwa yayi band’aki yana fitowa, sumayya dake kan dakali ya ciciba yayi bayan gida da ita, ajeta yayi.

    “Toh ka fita mana, waima menene naga ka rufe ido yaukam kaki budewa”?

    Idanun ciwo suke mini, yau kamar borkono a ciki.

    Uhmm kawai sumayya tace tana had’a ruwan wanka, duk yanda taso muhammad ya rabu da ita ki yayi shiya taimaka mata tayi wanka, ya d’auko mata wani towel in, ta d’aura ruwa ya cika a buta ya bata tayi Alwala.

    Shima wankan yayi ya fita a d’akin har lokacin idanunsa a tamke, yayi Alwala yashiga d’aki, zuwa lokacin sumayya tayi sallah tana zaune tana lazimi.

    Bayan ya idar da sallan, a hankali yasa hannu ya shafo sarkan wuyansa da mamaki ya kalli sumayya, gimbiya yanaga sarka a wuyana kuma, ke kika d’auko koh?

    Da mamaki sumayya ke kallonsa, yau kuma gimbiya ta zama kenan”eh nina saka maka, kace babanka ne ya baka sannan baka sakawa, akan me”?

    Sumayya naki saka sarkan nan ne, dom sau biyu ana kokarin fizgesa a wuyana,shiyasa na daina sawa.

    “Kamar ya ban gane ba”?

    Wallahi barayi mana, kaje kasuwa xaka saida abu anki saya, Amma barayi na kokarin sata.

    “Allah ya kyauta , wai bazaka bude idon bane”

    Ba musu yad’an fara kokarin, bude idon a hankali a hankali harya budesu duka.

    “Ya illahih”sumayya tace lokacin da idanunta ya sauka akan kwayar idon muhammad, yayi jajazur kamar jini zai digo, inka ga idon zaka d’auka koh buga masa shi akai jini ya taru.

    Sumayya menene naji kina salalami?

    “Ba kome, yayan khadija kaga idanunka kuwa”?

    Taya zan gani, bayan ba gani nake ba, me idon yayi?

    Wallahi kamar jini zai digo jajazur”

    Kuma Nima rad’adin da nakeji sosai fa.

    Allah ya kyauta, bara naji sauki sai muje asibiti, Amma dai yanzun, kaje chemist ka siyo mini magani rage rad’adi, kaima saika sayawa kanka naga, har wajen ya kumbura”?

    Gaskiya ne, kannawa ciwo yake wallahi, gashi ma yunwa nake ji, kema nasan kinaji bara na had’a duka nasai mana.

    Nikam bazanci kome ba, ka biya shago kawai ka d’auko mini lemo, bakina d’aci, ka tura a kira khadja tazo tad’an gyara mini kofar, nikuma bara nayi sauri na fitar da zanin gadon ya baci sosai”

    Toh ki zauna kawai tunda tafiyar taki batayi kyau ba, bara na jika zanin gadon inna dawo zan wanke? yace yana fita a d’akin bayan ya d’auki zanin gadon, waje muhammad ya fita bayan yakai zanin gadon band’aki, tsallake titi yayi, yaro ya samu ya aika gidan goggo, a kira masa khadija, shikam ya wuce chemist in jambusko.

    Yana isa chemist yasamu layi dole ya zauna har akazo kansa, maganguna ya saya harda wanda zai diga a ido, yabi shagon sa lokacin har shagari ya bude, d’aukowa sumayya lemon yayi, yasai abinci duka yana rike da laidodin a hannunsa har lokacin idanunsa rad’adi suke masa.

    Yazo tsallaka titi kamar daga sama yaji mota yayo kansa gadan gadan da gudu ya fara kokarin kauce wa, Amma ina saida suka cin masa, kamar zasu kadesa, amma suna zuwa kusa dashi suka ja birkiii

    Sosai ya tsorata sai kiran sunan Allah yake, wasu kattai hannun su d’auke da bindigogi, suka fitoh a motar duk sun rufe fuskokin su da mask……..🍀

    🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
    🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯
    ~ Na ~

    🍃 *Rukayya* *Ibrahim* 🍃

    ✨Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za’a ga mistake Koh typing error Amin afuwa👌
    free book 🤧

  • Matar Makaho 40-41

    Matar Makaho 40-41

    Page4️⃣0️⃣&4️⃣1️⃣
    Yusuf ne kwance akan zainab suna dambe

    Salati dumbin Alumman dake wajen suka sake,zainab Kam da sauri ta sake Yusuf ta matsa gefe tana kuka da rawan jiki

    Yusuf Kam ya kasa magana sunkuyar da Kai kawai yayi don bazai iyya hada ido da ubangari ba

    Yusuf Ashe Kai Maci Amana ne Yusuf Ashe Kai mugune Yusuf shiyasa tsawon shikarun nan kake zaune Dani da fuska biyu azzalumi maha’inci kawai wallahih nayi Dana sanin zama dakai, Allah ya isan mini tunda ka rasa Wanda zakabi sai Yar cikinka,yace hawaye na taruwan Masa a ido,matasan samarin nan basuye wata wata ba suka rufe Yusuf da duka duk yanda yaso musu bayani Basu basa dama ba

    Aisha Kam ba karamin shock ta Shiga ba Daman Yusuf ba D’an uwan ubangari bane? shiyasa inta tambaye sa Ahlinsa sai yahau fushi Ashe baida gaskiya ne kwata kwata, Aisha Kam kuka take tana dana sanin Yusuf, ya zubar Mata da mutunci ya ha’ince ta

    Matar ubangari waya ta d’auka ta Kira police lokacin Amma Yusuf jina jina Koh tsayuwa baya iyyayi,ga matan sa da yaransa duk suna kuka, A lokacin yaran basusan me uban yayi ba Amma tabbas sunsan ba lfy

    Police na zuwa daker suka k’wace Yusuf ganin ana kokarin kisan kai, lokacin da police suka Kama Yusuf za’a fita dashi cikin tsananin azaba yake rokonsu su barshi yaga MATARSA zai Mata magana.

    Ba musu domin tabbas su kansu police a lokacin sunji tausayin sa sosai da sosai,wani ne a cikinsu ya taimaka Masa suka nufi wajen da Aisha ke duke tana kuka

    Yusuf na Isa dukawa yayi yasa gwuwarshi a kasa cikin galabaita ya fara magana, Aisha Koh kowa zai yarda akan abinda yafaru don Allah Aisha ke kad’ai ki yarda Dani, yardan ki kawai nafiso akaf fad’in duniyan nan bayan yardan Allah,don kece abokiyar rayuwa ta in kowa zai juyamin baya ke Kika rungumeni bani da kaito Aisha Ina neman Wannan alfarman. ya karasa maganar hawaye nabin fuskar sa

    Aishan ADARA Kam yau Hali ya motsa jikinta har bare yake cikin kakkauran murya ta mike ,Yusuf Yusuf wallahih nayi Dana sanin haihuwa da Kai Yusuf, nayi Dana sanin auren ka Yusuf ka cuce kanka ka cuceni Yusuf bana bukatar ka a rayuwa ta ni daga yau mijina ya mutu.

    Sosai Yusuf ya fashe da kuka maicin Rai Wai waye zai fahimce sane kowa bazai yarda dashi ba kawai don an gansa a d’akin yarinya Babu bincike sai kawai ad’au mataki, me yasa tunani bazaizo musu ba duba da cewa ya rasa inda zai nemi zainab sai a cikin gidansu?

    Yunkurin magana yafara ais……,da saure Aisha ta d’aga Masa hannu Yusuf Koh Babu Kai zamu rayu da yarana Koh bakai Zan iyya rayuwa Koh ba Kai rayuwar zata Mana Dadi,Amma zaman ka acikin mu shine kuncinta ka tafi bana bukatarka a yanzun,tace tana Mai kokarin baren wajen.

    Da sauri yusuf ya Kama hannun Aisha,bataye wata wata ba ta tsinka Masa Mari.
    Da sauri Yusuf ya sake Mata hannu

    Da sauri Al’ameen Yayi wajen babansa cikin kuka ya rungume sa,abbajo menene Kaye musu suke dukanka abbajo ga fuskarka duk jini,abbajo muje asibiti a maka treatment kaji abbajon mu ka bawa police hakuri karsu tafi dakai,kuka Yusuf ya sake hade da rungumar d’ansa Dayake Jinsa Kamar bugun numfashin sa, cikin su biyun yafi kaunar Muhammad sosai.

    Karka damu muhammad Zan dawo kaji laifin da ba nawa bane aka d’aura mini Wanda duniya kaf ni ake gani da laifin ,Yusuf yace ma d’ansa Yana Mai d’aukar sarkan dake wuyansa fari Mai azabebben kyau da walkiya ya d’aurawa Al’ameen a wuya, Muhammad ka kula da mamanku da kaninka kaji in mamanku ta haifi mace kace asa Mata khadija Inna mijine asa masa Shitu,Yana fad’a Masa hakan police sukazo suka Tisa keyarsa zuwa cikin mota

    Bayan an tafi da Yusuf, Alhaji ubangari da danginsa Koran Kare sukama Aisha da yaranta,sosai Aisha tayita kuka tana tattara kayanta zubawa tayi a ak’watin karfe ta d’aurawa Al’ameen da salim,suka Kama hanyar sintali.

    Gari gabaki d’aya ya d’auka zancen Yusuf yayi kokarin mawa Yar ubangidansa fyade,bayan isar Aisha gidan ADARA zuwa lokacin labari yazo kunnensu Dayake unguwan da suke da sintali ba nisa

    Bayan isar Aisha gida ta sake haduwa da wani tashin hankali shine mahaifinta yace sai ta mayarda yaran Yusuf gun danginsa kafun ta zauna musu a gida Dayake mahaifiyar ta tarasu tun kafun auren ta,yasa ba Wanda yayi yunkurin baiwa baban ta hakuri

    Aishan ADARA ta shiga tashin hankali ba kad’an ba na rashin sanin asalin Yusuf abin yayi mugun daga Mata hankali,ta rasa Ina zatasa kanta taji Dadi,don da ta koma gidan ubangari tunda shine waliyin Yusuf ya fad’a Mata inda dangin Yusuf suke Amma rashin mutunci da aka Mata a gidan Koh kyaun gani Babu,karshe dai wani abokin Yusuf ne Wanda sukaye mutunci sosai ya taimaki Aisha bayan Jin labarin abinda ya faru tabbas shima ya shiga tashin hankali Amma Sam Bai yarda Yusuf ne zai aikata wannan abinba, d’auko Aisha yayi ya Basu d’aki a gidansa duk da MATARSA ta tsani zaman su Aisha Amma ba yanda zata iyya Aisha ta koma gidan abokin Yusuf da zama.

    Wannan zaman gidan abokin Yusuf shine mafarin haduwar
    Al’ameen da kamila

    An Kai Yusuf kotu,Amma bashi da hujjan Kare kansa haka yanaji Yana gani,laifinda ba nasaba aka yanke Masa hukunci.

    Bayan Shari’a abubuwa sun ma Aisha yawa na rashin mijinta don abinda zataci ma gagaransu yake Dole karatun su Al’ameen a private ya gagara ta ciresu ta maidasu Government school, sukaci gaba da zuwa,itakam wankau take Koh daka take sama musu abinda zasuci sosai Aisha take fama da rayuwa ga bakin cikin_ abinda Yusuf ya aikata,ba karamin bakin jini ya shafawa yaransa ba

    Hankalin Aisha Bai Kara tashi ba Saida lokacin komawar Salim asibiti Amma Bata da Koh sisi haka ta d’aukesa sukaje asibitin Amma abin mamaki duk yanda suka Saba da zuwa ganin likita Amma yau kawai da basu da kudin magani haka suka dawo gida kayan sakawarta Aisha ta tattara da kayan dakinta take sayarwa a hakan ta ringa ma Salim jinya da kayyakinta don abokin Yusuf d’aki kawai ya Basu Amma abinci Kam sai dai ta nema musu,

    Ta bangaren zainab Kam tayi Dana sani Dana saninda har abada bazata daina yinsu ba sai yanzun take ganin wautarta na biyewa khairat harta aikata wannan mumunan kazafi wa Yusuf gashi abin Bai tsaya iyya Yusuf ba ta raba ma’aurata ta raba uba da yaransa ganin Yusuf da take taji Dadi yanzun Babu shi gashi Koh samarinta ma yanzun duk sun gujeta a dalilin labarin da suka samu

    Zainab rayuwa ta Mata zafi Koh baccin kirki Bata iyya wa taso sanar da iyayenta gaskiya Amma kairat ta kwabeta don hakan zai iyya zubar Mata da mutunci fiye Dana yanzun da take ciki.

    Al’ameen da kamila yaran makwanta ne gidansu kamila.na kusa da gidan bala abokin Yusuf,

    Kamila dalibar makaranta i private school ne Wanda ke kusa da goverments day da Yusuf ke ciki

    Farkon haduwar kamila da Yusuf a hanyar makaranta zai tafi itama zata fita.

    Tunda kamila.taga Al’ameen take yawan shige Masa har gidansu take zuwa tun Al’ameen baya kulata hardai ya fara kulata Aisha Karan kanta da farko bataso mu’amalar Al’ameen da kamila ba ganin Al’ameen lokacin shikara biyar ya bawa kamila Amma haka ta barsu ganin karatu Yusuf ke koya Mata kullum insun hadu

    Bayan wata uku lokacin cikin Aisha ya Shiga wata bakwai,zuwa lokacin Aisha Bata da kome a dakinta sai taburma sai sarkan wuyan muhammad sai tsummo karansu saboda duk kudin sun Kare akan kudin maganin Salim ga rayuwa dai anata gargarawa

    Yau ranan juma’a Al’ameen da Salim sun dawo makaranta bayan sun kara kamila gida don yanzun shakuwane Mai tsanani a tsakanin su wanda in kamila bataga Al’ameen ba zatazo gidansu haka shima, suna zaune dumamen safe da ya rage shine Aisha ta Basu itakam haka ta hakura saboda yau sun tashi bako sisi,zainab ce ta shigo gidan da sallama a bakinta

    Aisha ta amsa Mata Dan Sam bata Jin haushin family ubangari don Koh itane abinda Yusuf ya aikata saita Masa fiye da haka

    Kallon zainab take Wanda duk tabi ta rame kallo d’aya zaka Mata kasan Bata cikin hayyacinta,bayan sun gaisa zainab ta d’aga ido tana kallon Aisha Bata San ta Ina zata fara ba yau tayi Alkawarin zata Fad’i gaskiya Koh zata samu sassauci a rayuwan ta

    Hawaye ne ya cika idanun zainab ta bude baki a Hankali tace,maman Muhammad akwai wani magana da zanfada Miki bansan ya Zaki d’auki maganar ba Amma na g’wammaci na karbi Koh wani hukunci akan Wanda nake ciki

    Cikin mamaki Aisha kam ke kallon zainab a iyya zamansu da zainab Bata taba ganin ta Mata magana a mutunce ba Kamar yau,toh zainab Allah yasa naji alkhari

    Gaskiyan abinda ya faru maman Al’ameen babu ruwan Yusuf aciki,tace tana kallon Aisha

    Kamar ya bangane ba zainab?

    Eh tabbas Kamar yanda nace , Yusuf Babu ruwansa a ciki nice da khairat Muka had’a kome a tunanin mu Koh in aka Kama Yusuf xai mini fyade babana zai tilastashi ya aure ni Amma ban taba tunanin abinda na aikata ba daidai bane Saida Naga yanda na wargaza muku farin cikin na dasa muku bakin ciki, wallahih maman Al’ameen nayi nadama,Dana biyewa khairat ban tashi nadama ba Saida naji jiya tana Hira da kawarta a waya suna mini dariya, na tsokancin danayi harna yarda da abinda ta gayamin Ashe itama son Yusuf take,ta karasa maganar hawaye ya zuba akan fuskarta

    Aishan ADARA Kam daskarewa tayi a zaune itakam wace irin mace ce Mai mantuwa me yasa ta kasa yarda da Yusuf, namijin daya yarda zai rayu da ita Bai damu da tarbiyan gidansu ba Koh halinta ba ya aureta Koda Yusuf Zina yayi hukuncin da ta yanke Masa yayi tsauri,wani irin murdawa mararta yayi na tashin hankali atake jini ya balle Mata durkusawa Aisha tayi tana Kiran sunan Allah.

    Da gudu matar Bala dake tsaye tun d’azun tanajin bayanin da zainab keye tazo da gudu,tana kwalawa mijinta Kira da gudu ya fitoh su uku suka ciccibi Aisha zuwa asibiti

    Al’ameen Kam Kama hannun Salim yayi suka Kama hanyar gidan ADARA,suna Isa kakansu suka samu a kofar gida suka fad’a Masa mamarsu ba lfy an kaita asibiti, hankali baban Aisha ya Tashi matuka don shi Karan kamshi korinda Yama Aisha na haushin yaran Yusuf ne, Amma Yana son yarsa tura su Salim yayi gidan Amina (Goggo) shi Kuma ya wuce gidan Bala agun ya samu wa’inda ke zaune aka fita da Aisha, aka Masa kwatancen asibitin da aka Kai Aisha

    Bayan zuwansa ne yaji labarin abinda ya haddasa ma Aisha nakudar Dole abakin Matar Bala,shima sosai ransa ya baci duk da Bai gamu da zainab a asibitin ba Amma ransa ya matukar baci gida ya koma ya sanar da yaransa da yaran Yan uwansa akan suje su fara d’aukar mataki akan zainab kafun hukuma ta shiga

    Ayarin gidan ADARA daga Yan Mata har zaurawa da samari sukaye Ayari guda suka fasa unguwa da kafa suka taka har gidan ubangari.

    Zainab Kam gabaki d’aya ta rasa nutsuwarta Koh zama takasa waje Daya, tunda ta gudo daga hospital karshe dai Saida mamarta ta tambaye ta Koh meke damunta haka? tunda abinnan ya faru ta fahimci walwalar zainab ya d’auke, zainab Kam kin fad’a Mata gaskiya tayi

    Suna zaune dukansu a gida dayake yau Friday ne ubangari ya dawo aiki da wure haka Yan makaranta,ji kawai sukaye an bankado get in gidan an shigo ciki kafun ma su gama tantance suwaye ne har kanwar Aisha ta nufi d’akin zainab jawota sukaye har kofar gidan da gudu su ubangari suka Mara musu baya.

    Rufeta da duka ADARA sukaye, saiga khairat tafitob gida makwantan su, Aiko kamota sukayi suka Had’asu suna jibga duk yanda Yan unguwa da ubangari suke kokarin k’wace zainab da khairat abin ya gagara ganin zasuye kisan kai don zainab ta Suma Amma haka Ayarin gidan Adara Basu daina jibgarta ba Saida ta farfado da duka

    Police aka Kira lokacin unguwan ya cika makil day’an kallo, abinka da Friday kowa na gida,

    bayan zuwan police kafun aka samu aka k’wace su zainab anso Kama Yan ADARA Amma Ina abin ya gagara don fad’ane ya kusa zama na police da Yan gidan Adara,ganin jaraba irin na Yan gidan yasa polisawan tambayar musabbabin fad’an don dai sunyi sunyi su bisu station aye kome agun Amma sunki, D’aya daga cikin samarin gidan ne ya nuna zainab,ke don uwarki fada musu meya faru tsakaninki da yusuf mijin Aisha?

    Hakika zainab tayi mugun tsorata hakan yasa Bata boye kome ba ta fad’a duk abinda ya faru,atake Alumman suka fara Allah wadai da zainab da khairat ubangari Kam yanke jiki yayi ya Fadi hawan jininsa ya tashi, police ma tafiyarsu sukaye Basu d’auki kowa ba.

    Ta bangaren Aisha Kam ganin tana kokarin rasa Ranta yasa likitoti Mata operation aka cire baby girl bakwaini aka saka a kwalba,Aisha na farfadowa sunan mijinta ta fara Ambata tana sambatu,tunda ta farfado batada magana sai a kaita wajen Yusuf ta nemi gafaransa Amma ba’a barta ta fita a asibitin ba saboda yanayin jikinta Dana baby.

    Ta bangaren ubangari ma hakan take jinya ya kwanta har kusan sati baisan inda kansa yake ba abubuwa sun taru sun Masa yawa,Yana Jin sauki kad’an ya Tashi da kafarsa ya koma wajen Alkalin da yayi musu Shari’a,

    An nemi ganin Yusuf don a wankesa a kotu Amma abin tashin hankali shine, Yusuf a Randa aka kaisa prison Bai kwanaba ya fita tare da sa hannun kotsosin kasa

    Wannan magana ita tafi ko wace magana tashin hankali agun Aisha don anye iyya bincike an had’a hannu da masu kudin da Yusuf yayi mu’amalan kasuwanci dasu don binciko inda Yusuf yake Koh suwa suka fiddasa

    Duk Wanda aka tuhuma Mai hannun a cire Yusuf magana D’aya yake fad’a baisan Yusuf ba kawai umurni aka basa daga sama

    Wannan magana tayi mugun dagawa Aisha hankali atake ta sake kwantawa ciwo Wanda an rasa kansa kullum gaba gaba yake duk abinda babanta ke dashi ya kare a jinyar Aisha da Salim don shima zuwa lokacin zuciyarsa ta fara tashi.

    Tsawon wata biyar ana binciken case in Yusuf Amma shuru ba wani cigaba,yau dai jikin Aisha da sauki,bayan Salim da Yusuf sunzo duba mamar tasu ,don yanzun suna zaune a gidan Adara ne

    A hankali ta Kama hannun Al’ameen ta rike cikin nata ta fara magana hawaye nabin Gefen idanunta,Al’ameen ga kaninka nan da Yar uwarka khadija Muhammad ka kula dasu ka zama uba a garesu Koda kowa zai gaji dasu Kai ka zaman musu gata, jagora,Garkuwa,inaji a jikina wata Rana zaka Hadu da mahaifinka,kace Masa ni Aisha Ina neman afuwarsa ya yafe mini Koh Zan samu salama,ka zamo Mai hakuri kamar mahaifinka duk abinda zakaye a rayuwa ka ringa bincike karka yanke hukunci a cikin fushi don karshin sa Dana sanine.

    Al’ameen duk da yarone Amma hankalinsa in yayi dubu toh ya tashe in Bai manta ba haka abbajonsa yayi Masa, shikenan ya gudu ya barsu don shi har yanzun baisan takammamen abinda yake faruwa ba,

    Mami kema gudu zakiye kamar abbajo ki barmu?yace Yana kuka shida Salim dake kusa dashi

    Ah ah Yusuf ba gudu zanye na barku ba inda zanje kowa ma zaije in lokacin sa yayi sanan abbajonka Bai gudu ba wata Rana zai dawo kaji,ga kaninka na kuka ka rarrashesa karka barsa ya zubda hawaye kasan ciwonsa bayason damuwa Koh?ta tambaye sa muryanta na shakewa

    Kai muhammad ya gyad’a Mata hade da Kama hannun Salim Yana rarrashensa,

    Ji kawai yayi mamin su na wani irin shakuwa hade da Kiran sunan Allah,da sauri ya fita a d’akin yaje Kiran Doctor

    Suna shigowa dakin da sauri Muhammad ya matso gareta cikin matukar razana ganin maminsu Bata m……………….

     

    🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 *Albishirin ku Mata ku marmaso kuji sirrin,Koh kinsan mace sai da kamshi da gyara* 😉

    🍀🍀🍀🍀 *Turare suna d’ayace Amma sun banbanta kowanne da ingancinsa kamshinsa da aikin sa*

    🍀🍀🍀🍀 *Ina muku Albishir da UMSAD INCENSE Dan samun turaruka masu kamshi da* *gyara*

    🍀🍀🍀 *Tabbas Turare sirrine ga Koh wace mace*

    🍀🍀🍀 *Gamai bukatar turarukan UMSAD INCENSE*

    🍀 *Na tsunguno(habil)*
    🍀 *Na jiki (kwalaccam)* ( *khumra, black & white* )
    🍀 *Turaren turara jiki after birth* ,
    🍀 *Na d’aki(halud Al’oud)*

    *UMSAD INCENSE suna kofar waika wajen Ado bayaro layout Kano State* 💃🏼💃🏼

    🍀🍀🍀 *Suna bada d’aya Koh sare akan farashi Mai Rahusa*

    🍀🍀🍀 *Suna bada order kayansu Gamai bukata aduk jahar da yake a fadin Nigeria*

    Contact them vie
    🪀08028827241 or 09033791049
    IG @umsadincense
    🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
    🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯
    ~ Na ~

    🍃 *Rukayya* *Ibrahim* 🍃

    ✨Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za’a ga mistake Koh typing error Amin afuwa👌
    free book 🤧

  • Matar Makaho 44-45

    Matar Makaho 44-45

    Page 4️⃣4️⃣&4️⃣5️⃣
    Al’ameen ne ya yanke jiki ya Fad’i,sosai mutumin ya rikice yahau salati cikin kidema

    Hayaniyar sa shiya matashe samarin dake kwana a d’akunan kofar gida,Suma dai sosai mutuwar Salim ta shigesu ruwa aka watsawa Al’ameen Amma Ina Koh farfadowa baiyi ba Dole tasa wasu daga cikin matasan d’aukar sa zuwa asibiti

    Usman makwancinsu shiya d’auki gawar Salim zuwa gidansa

    Washe gari agidan malam Usman aka shirya salim.

    Al’ameen dake asibiti kam Yana farfadowa da asuba ya tashi hankalin kowa sai ya dawo ankai Salim tare dashi

    Haka aka kamasa g’wanin tausayi zuwa gidan malam usman,Yana shiga gida aka Kaisa Kan gawar D’an uwansa a hankali ya zauna Kan cafet in hannu yasa Yana lalube ya bude gawan jikinsa na bare yasa hannu ya shafa fuskar Dan uwansa murya na rawa hawaye nabin kuncinsa yake ma D’an uwansa Addu’a

    Salim sosai ya samu jama’a kamar me don duk wanda yasansa, kuma yaji mutuwarsa yazo,tare da Al’ameen aka kai D’an uwansa kabari.

    Bayan mutuwar Salim sosai kewa da kad’aici ke damun Al’ameen Koh bacci baya iyya wa saboda kewan D’an uwansa shikenan yanzun baida abokin Hira baida Wanda zai fad’awa damuwar sa baida Wanda zai kwana tare dashi sai Yar kanwarsa khadija ita Kuma mace ce

    Mai gidan Salim shiya bawa Al’ameen kudi Ya sari mangoro Koh a bakin kofar gidane ya fara saidawa don Bai dace Yana tsallake titi kullum zuwa kasuwa zaman shago ba

    Ba musu Al’ameen ya karbi kudin yad’an fara business dashi,Kuma Allah yasama abin Albarka Yana samun na abinci da biyawa Khadija D’an hidindimun makaranta

    Zancen kamila Kam baiyi fushi ba duk da Bata Masa ta’aziyar D’an uwansa ba haka ya sake Kama Khadija don lokacin ta d’anye wayo sukaje gidansu kamila.

    Kamila ce tsaye da kawayen ta a waje tare da wasu samari uku A bakin mota

    Al’ameen suna Isa kofar gidansu kamila,yaji hayaniyar maganar mutane Kamar harda ta kamila hakan yasa cikin murna yau dai zasu gana, tunda ya jima Yana zuwa baya samun ganin ta

    Da saurinsa yace wa Khadija suye wajen da Yake jin muryan mutane

    Ba musu Khadija na rike da sandar sa suka nufi wajen, Assalamu alaikum

    Waalaikumu salam D’aya daga cikin samarin ya Amsa Masa

    Ina wunin ku, Al’ameen ya gaidasu

    Lafiya samarin suka amsa d’ayan ya zare kudi a Aljuhunsa Yana mikawa Khadija,ungo Yan mata

    Khadija Kam kin karba tayi don bata Saba bara ba koma yayanta ya hanata roko Koh karban abin hannun Wanda Bata sani ba

    Karba Mana yarinya D’aya daga cikin kawayen kamila ta fad’a don Bata San Al’ameen ba

    Yayana ya hanani karban kudin Wanda ban sani ba, Khadija ta fad’a musu tana noke kafad’a

    Da mamaki samarin ke kallon su Al’ameen mutum ya fitoh bara abasa yace bazai karba ba,toh lfy meya kawo ku gun mu inba bara ba

    Am don Allah Ina da tambaya ne? Al’ameen yace

    Allah yasa mun sani

    Yauwa Kamar muryan kamila nakeji d’azun a cikin ku?

    Eh ganinan lfy?kamila ta basa Amsa

    Lafiya kamila in ba damuwa inason magana dake ne

    Ina jinka,tace tana Masa kallon banza

    Don Allah mu koma gefe

    Kai MAKAHO akan me zaku kebe da matar da Zan aura Kai asuwa d’aya daga cikin samarin yace

    Wani abune ya cake zuciyar Al’ameen shikenan kamilar ma ya rasata shikam yaushe zai samu farin ciki ne duk mai kokarin faranta Masa wata Rana gudu yake ya barsa

    Kamila aure zakiyi?yace Yana kokarin faduwa tsaban shock

    Eh aure zanyi Koh kana da matsala da hakan ne

    Kamila Ina Alkawarin mu?

    Alkawari kana nufin na aure ka kana MAKAHO Kuma talaka da wanne zanji da ciyar dakai Koh da ciyar da yaranka Koh da maka jakora Koh d’awainiya?Zan dai iyya auren ka a Talaka Amma banda kana MAKAHO kam.

    Sosai zuciyar Al’ameen ta tsinke

    Dariya matasan da Y’an Matan suka sake na shekeyanci,Kai kamila bakida mutunci wallahi 😒 soyayya ce fa saikuje kusha love da lalube D’aya daga cin Yan matan ta fad’a tana dariya

    Budurwar da ke gefe sanye da hijab itace kad’ai Bata ma Al’ameen tozarci ba

    Kama hannun Khadija taye hade tacewa Al’ameen su tafe

    A hankali Al’ameen ke tafiya Kamar k’wai ya fashe Masa a ciki Bai d’auka Koh nakasa zaisa kamila gudunsa ba Koda kowa zai gujesa

    Suna sharan kwanan nayin, kawar kamila ta dube Al’ameen,kaga bawan Allah don Allah Ina Mai rokon alfarma a gareka shine ka rabu da kamila Koda itace autar Mata ka barta duniyace ai Koda zata rabu dakai bada tuzarci Koh kushen halitta ba Amma ita Bata dube hakan ba y
    Ta wulakanta ka kaima ka barta bari na har Abada,Kaye hakuri Allah Yana tare da musu hakure.

    Insha Allah baiwar Allah na rabu da kamila Nima na hakura da ita Allah ya had’a kowa da rabonsa,

    Ameen ta basa amsa tana Mai komawa layinsu tabarsa tsaye da Khadija

    Wannan shine Ranar da Al’ameen ya fita a Rayuwan kamila.

    Bayan wasu shekaru karatu ya fara zama sai da kudi, a hakan yake ta faman ganin Khadija tayi karatu Koh ba kome zata tallah fawa kanta, Amma Ina kudi ya gagara don yanzun mangoron ma sai a hankali Bai wuce a Rana yayi cinikin 200 Koh kasa da hakan. Gashi a ciki Kuma yake ciwa cikinsa hakan yasa karatun Khadija tsayawa iyya Junior.

    *An dawo labari* ………..
    Khadija Kam kuka take kaman me,haka ma Sumayya Allah sarki Ashe haka rayuwar wa’innan bayin Allah yake, tasu kaddarar kenan,a cikin Yan watanni nan da mahaifinta ya juya mata baya taji kamar tafi kowa matsala,ashe itakam ma in an had’a kaddarar ta dana Muhammad nata ba kome bane tunda har tayi karatu ta tashi cikin kudi da lfyr ta Amma shifa ga maraici ga kuncin rayuwa da Talauci.

    D’aga ido tayi tana kallon Al’ameen dake zaune a kujera fuska tayi ja”yayan khadija baka bani lbrn auren mu ba”?ta tambaye sa

    Khadija tashi ki tafi kinji kukan ya isa haka, Al’ameen yace batare da ya amsawa Sumayya tambayar taba

    Mikewa Khadija tayi zata fita a d’akin cikin kuka abin g’wanin tausaye”Khadija”Sumayya ta Kira sunan ta

    Na’am Aunty

    “Khadija kiyi hakuri kome na rayuwan duniya Mai karewane Sannan Yana da iyyaka kinji”?

    Toh Aunty tace tana share hawayenta

    “Ki d’auki doyan nan ki tafi dashi gobe da safe sauki kawo mini ducuments naki kinji Khadija”

    Toh Aunty kawai tace tana d’auki laidan doyan ta fita

    “Yayan khadija na tambaye ka shine kaci no face”

    Sumayya nagaji wallahih ki barni nad’an huta Mana waima me zakiye da ducuments in Khadija ne?

    “Oho ba’a sani ba Ina maka magana kana tambaya ta Nima naki fad’an”

    Shuru ya Mata tare da lumshe idanunsa

    Itakam ganin ya Mata shuru tasan dai akwai abinda bayason fad’a matane,tashi taye a hankali ta Isa garesa faduwa tayi a kansa da gangan

    Washhhh yace yana gyara Mata kwanciya

    “Don Allah ka fad’amin Mana”

    Kinga Sumayya nifa banason na fad’a Miki abinda zaizo Yana d’aga Miki hankali.

    “Allah bazan d’aga hankalina ba kawai ka fad’a mini”

    Ok toh shikenan Amma sai da dare Zan fad’a Miki

    “Gaskiya Nina gaji da abinda kake minin nan wani irin sai dare Kuma Wannan ai Jan Raine”

    Banace Zan fad’a ba ki barni Mana zuwa Daren in ban fad’a Miki ba saiki Tuhume ni

    “Uhmm toh yanzun me zakayi”?

    Bacci,ya Amsa mata

    “Bacci a hakan”?

    Eh…..

    Tashi Sumayya tayi taje ta d’aura abincin dare ta barsa a d’akin

    Bayan fitarta sosai yake tunani akan ya fad’a matane Koh karya fad’a Mata karshe dai ya yanke shawaran ya fad’a matan kawai

    Bayan isha’i Sumayya ce da Al’ameen kwance akan gado Sumayya taye matashe da cinyar Al’ameen sunfi minutes 20 a haka,tunda sukaci abincin dare sukayi sallah, suke a haka Amma Al’ameen baice mata kome akan labarin ba abin sosai ya dame ta Amma ta danne tunda yace zai fad’a zata barsa ya fad’an da kansa.

    Sumayya!!ya Kira sunanta Yana Mai shafa gashin kanta mai tsawo da kamshi

    “Na’am”ta amsa Masa

    Sumayya banso fad’a Miki dalilin auren mu ga ganin cewa kece kikafi kowa sanin hakikanin gaskiya don bana tunanin har yanzun ana cikin zamanin da za’a ma mace aure batare da tasan miji Koh miji ya santa ba.

    “Me kake nufi”? Sumayya ta tambaye sa fuskar ta a hade Jin abinda yake fad’a Mata

    Yanzun masifa Zaki mini Koh Jin lbr zakiyi?

    “Aiba labarin kake bani ba sukata kake”Sumayya tace,tana kokarin sauka a gadon

    Sorry toh, yace Yana kamota

    “Nikam ka sake ni ”

    Kin saketan yayi yana rungume da abarsa, naki sakin kin in kajimin mata fa

    “Allah ni ka sakeni nace maka”tace tana kokarin xame kanta a jikinsa

    Fushi kikayi ne Gimbiya?

    ” waye Gimbiyar”?

    Sumayya mana.

    “Gimbiyar wa”?

    Al’ameen…

    Uhmmm kawai tace bata kara magana ba

    Kinga na miki Alkawari, zan fad’a miki gaskiyan abinda na sani akan auren mu?

    “Nima nafasa ji yau sai gobe”ta fad’a tana mai sa hannu ta d’auko wayarta dake gefen filo, airp inda ke makale a jikin wayar ta manna a kanne

    Sai magana yake baiji ta amsa masa ba hannu yasa yana tattaba ta, Gimbiya ina magana kin mini shuru

    Duk da sumayya taji Al’ameen ya taba ta Amma taki koh sauraransa

    Shikam gane fushi take yasa sa dagota sama daga jikinsa ya jefata gefen gadon

    Ihu sumayya ta sake bawai zafi taji ba don laushin katifar dana blanket bazai bari taji zafi ba tsorata kawai tayi don bata tsammaci hakan ba” wayyo wuyana ya karye”

    Nashiga uku sumayya inga wuyan da gaske kinji zafi dan Allah kiyi hakuri ban dauka zakiji zafi ba, yace yana matsowa kusa da ita

    Sumayya kam langobewa tayi wai wuya ya bugu”wayyo wuyata shikenan ya kasheni jama’i

    Don Allah kiyi shuru muga wuyan wallahi bada niya nayi ba

    Sumayya kam kara lafewa tayi jin ya cicibeta ya daura a cinya kamar wata baby

    Sannu sumayya koh muje asibiti ne?

    “Nidai goyona nakeso kayi”ta karasa maganar da make murya

    Jikinsa na rawa yace, toh… toh… hau, yana dukawa a kan gadon

    “Nika d’agani bazan iyya tashi zaune ba”

    Cicibar sumayya yayi ya goya haka ya ringa lalube yana zaga d’aki zuwa baranda da ita sai kusan 10:00 sumayya taji gyangyadi kafun tace masa, ” ka kwantar da ni bacci nake ji”

    Ai da sauri bawan Allah yayi d’aki da ita da lalube ya shimfid’ata a gadon duk ya gama gajiya ba kad’an ba shiyasa daya samu taye bacci ba karamin dadi yaji ba gudun fitina ma koh tabata bayyi ba a gefe ya kwanta yanata tunanin wuyan sumayya don harga Allah ya d’auka da gaske ne

    Da asuba ma hakan take sashi tayi ya d’auketa har waje tayi alwala ya dawo da ita d’aki kafun ya tafi masallaci.

    Misalin karfe 9:12 na safe Al’ameen ne ke bacci a d’aki bayan dawowar sa sallan asuba

    Sumayya data gama aikinta a nitse tayi girki duka don bata tashesa ba saida ta gama harda wanka tayi kafun a Hankali tashigo d’akin wayanta ta d’auka ta danna play in waka ta kara volume, ta saka Eirps kunnen Al’ameen ta mannawa

    Ai kam yana cikin baccinsa yaji abu tibbbtibb ga waka kamar a kwakwalwarsa, da sauri ya mike zaune hade da furta, innalilahi sumayya wuyank……..sai kuma yayi shuru jin dariyan sumayy a kusa dashi

    Hannu yasa sosai ya damkota kwantar da ita yayi a gefensa yahau kanta sosai yayi lamo yana daidaita bugun zuciyarsa har lokacin abin na kunnensa

    “Wayyo menene haka”?

    Shikam koh jinta bayayi, sai dad’a lumshe idonsa yake jin wakar da ke tashi a kunnensa sosai yatafi dashi

    Da sauri sumayya ta zare eirps in jin sai magana take baya kulata

    Da sauri ya bude ido, tare da kamo hannunta data cire masa abin kunnensa, mena cirewa? wakarfa bai kareba

    “Inata magana kamin banxa badole na cire ba”

    Toh mekike son na miki kenan guda daya? tunda jiya ma ai magana nake miki kika saka abinnan a kunnenki kika manna mini nima, duk wai akan maganar jiyanne kiketa fushi koh?

    Shuru sumayya tayi

    Dalilin auren mu…….
    nidai bazance Miki nasan kome akan auren mu ba illah dai bazan manta ba wata Rana wani mutum yazo ya sameni agun sana’a ta yasai Mangoro ya tafi bayan kwana biyu Kuma sai gashi ya dawo Amma baifita a motarsa ba aika yaro yayi ya kirani nakai masa mangoro bayan naje ne yace na Shiga motarsa, Yana da magana Dani,ni kuma naji tsoro gudun kar Amaimaita na baya(Randa aka makantar dashi) shiyasa naki Shiga motar duk yanda yayi Dani ki nayi,karshe dai agun mukayi magana,Kamar haka

    Ni sunana mamman Ina da yarinya Naga hankalinka da nutsuwarka shine nayi maka kwad’ayin Koh zaka Amince in baka auren ta?

    Sosai naji mamaki nida bana gani ad’auki yar Mai mota sukutum a bani gani Talaka haka kawai sainaji Raina Bai Kama zancen ba, shiyasa nace Masa bana bukata batare da Kuma sauraransa ba nayi tafiya ta

    Bayan sati D’aya kawai bappa sulaiman yakirani Wai za’a mini aure,sosai abin yaban mamaki za’a mini aure kuma kamar mace,bappa aure Kuma Kamar Yaya?na tambaye sa

    Kamar yanda kaji bappa sulaiman ya bani Amsa

    Duk Azana Yar gidan nan za’a bani Amma bappa yace Wai Yar shugaba family ne tunda naji haka kawai nasan lallai wannan aure mai dalili ne ba auren Angani anaso ba,da farko naso nunawa bappa illan auren nan Amma ya murza ido yace sai anyi daga karshe ma cemin Yaya Wai yarinyar tanada Wanda zata aura matsala aka samu bayan anyi test shine aka samu tana d’auke da c…………….

     

    🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 *Albishirin ku Mata ku marmaso kuji sirrin,Koh kinsan mace sai da kamshi da gyara* 😉

    🍀🍀🍀🍀 *Turare suna d’ayace Amma sun banbanta kowanne da ingancinsa kamshinsa da aikin sa*

    🍀🍀🍀🍀 *Ina muku Albishir da UMSAD INCENSE Dan samun turaruka masu kamshi da* *gyara*

    🍀🍀🍀 *Tabbas Turare sirrine ga Koh wace mace*

    🍀🍀🍀 *Gamai bukatar turarukan UMSAD INCENSE*

    🍀 *Na tsunguno(habil)*
    🍀 *Na jiki (kwalaccam)* ( *khumra, black & white* )
    🍀 *Turaren turara jiki after birth* ,
    🍀 *Na d’aki(halud Al’oud)*

    *UMSAD INCENSE suna kofar waika wajen Ado bayaro layout Kano State* 💃🏼💃🏼

    🍀🍀🍀 *Suna bada d’aya Koh sare akan farashi Mai Rahusa*

    🍀🍀🍀 *Suna bada order kayansu Gamai bukata aduk jahar da yake a fadin Nigeria*

    Contact them vie
    🪀08028827241 or 09033791049
    IG @umsadincense

    🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
    🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯
    ~ Na ~

    🍃 *Rukayya* *Ibrahim* 🍃

    ✨Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za’a ga mistake Koh typing error Amin afuwa👌
    free book 🤧

  • Matar Makaho 46-47

    Matar Makaho 46-47

    Page 4⃣6⃣&4⃣7⃣
    Wai yarinyar tana d’auke da ciki shiyasa sukeso na rufa musu asiri na aure ta

    Sosai nayi mamaki kuma zuciya ta takasa Aminta akan zancen cikine kawai ba, tunda yaran masu kudi da yawa suna cikin shege Amma ba’a bawa talakawa saini MAKAHO sam nakasa yarda.

    Dana matsawa bappa da tambaya ma cemin yayi koh naki koh naso sati mai zuwa d’aurin aure

    Harga Allah banso auren ba sam, don inaji a jikina ba batun ciki bane, imma cikin ne taya za’ayi a d’aura aure da ciki a jikin budurwan kenan, koh an zubar?karshe fa akafi karfine kafun sati d’aya ba wanda baisan zancen auren mu ba saidai sam ba wanda yasan dalili kuma duk wanda yaji batun auren saiya digawa auren ayar tambaya

    Amma ke sumayya menene dalilinki na aure na?

    “Auren ka, ina ma na sanka kajimin mutumi fa” ?ta fad’a cikin kuka sosai abin ya mata zafi watoh bayan auren kaskanci da akaso mata har b’atata akayi a wajen mijin don aga abinda yafi wanda suka sata😭muni

    Sumayya nifa tambaya kawai nayi kuma abinda nayita gujema kenan, kika ga nake gudun fad’a miki gaskiyar abinda na sani, ya karasa maganar da kara rungumarta jikinsa

    “Shikenan yanzun koh inada cikin sai ka yarda ka zauna dani” ?

    Indai har cikin babu a jikinki koda kin tabayene zan zauna dake a hakan ma naji dadi ai, na samu mata

    Kuka sumayya ta sake sakewa watoh duk zaman da suke da Al’ameen na kokonto ne tayi ciki koh batayi ba kai wai meta tsarewa dangin mahaifintane, na mahaifiyarta kamma bata sansu ba bare

    Kiyi shuru sumayya mundin bakece kika gaji da zama dani ba ni bazan taba juya miki baya ba a duniya, bayan khadija da ke sai goggo bayan ku banida mutanen da suke sona tsakani da Allah, ke kuma kin nuna mini tsantsar hallaci a rayuwa, don wata koh da gaske tayi ciki aka aura matani bazatayi hakurin zama dani ba bare ta taso cikin kudi yanzun kuma tana fama da rashi harsai ta nemi na kanta

    Da sauri sumayya ta rufe masa baki cikin kuka tace”karka kara fad’ar haka banaso nima a yanzun kaine kad’ai Garkuwa ta kaine bangon da zan jingina ya rikeni, insha Allah kome zai wuce kamar ba’ayi ba.

    Allah yasa toh yanzun ya maganar kamilar?

    “Bazan koya mata ba gaskiya kartazo tana shigewa mijina don yanzun kai ba tsaranta bane”

    Yanzun shikenan saboda ni saiki rasa makudan kudi haka?

    “Wani makudan kudi kuma bayan jiya ma na samu mutum uku da zasu fara zuwa, shiyasa yau zamu fita dakai muje bank zan bude Account maganar kudin koyar, shiyasa zan bude Account transfer zasu mini ta bank kuma yaran manya ne sosai fa, inaga anya ma bazan bude shago ba”?

    toh Allah ya bada sa’a, Amma banda maganar shago kam banyarda ba matar aure da shago kamar wata inyamura.

    “Ayya koh a shagunan kofar gida saina kama d’aya tunda bakin titi ne”

    Sumayya ban Amince ba, yace yana tashi akanta hade da karban eirps in hannunta ya mayar kunnensa kawai ya kwanta

    Ganin ya kwanta yasata tashi ta d’auko musu karyawa jejjerawa tayi, ganin bai sauko ba yasa a hankali tahau kan gadon agadon bayansa ta kwanta luf ta lumshe idanunta “breakfast is ready”

    Shuru taji bai amsa ba Amma dai yasa hannu ya tabata,hannun ta buge hade da cire masa abinda yasa a kunnen san ta makala a kunnenta wakar umar m shareef ke tashi a ciki

    Jin ta cire masa yasa sa mikewa da sauri ya Amshi abin a kunnenta, wakar dadi tamin don Allah ki maida mini, ya fad’a mata yana mai mika mata wayar hannun nasa jin wakar ta chanja

    Hhh”waikai kam anya ka taba saka eirps a kunnenka kuwa”?ta karasa maganar da sauka akan gadon

    Da sauri shima ya sauko had’e da cewa wallahi kamar kin sani inadai jin ana zancen sa Amma ni bantaba sawa ba ashe da dadi

    “Hhh toh zauna kaci abinci sai na baka bluetooth harda wa’azi da karatun qur’ani zakaji a ciki ba waka kawai ba”

    Menene bluetooth kuma, banda na waya?

    “Baka san ana posted a waya ba? toh ai yakamata kasan bluetooth da mp”

    Nasan mp mana, bluetooth ne bansani ba saina tura abu a waya inaji anacewa kai bude bluetooth naka na tura maka waka koh vedio.

    “Kayi kokari wannan kuma na yayi ne a kunne zaka makala ba tare da igiya kamar eirps ba ka gane”

    Eh na gane..yace yana zama

    Abincin sumayya ta zuba musu mika masa tayi bayan ta damka masa shukali a hannu, wai nikam me kika maidani ne? an gaya miki bazan iyya d’aukar shukalin bane?

    “Waya sani koh abincin ma saina fara baka”

    Kwafa yayi kawai ya fara ci

    Suna tsaka da karyawa sukaji sallamar khadija amsa mata sumayya tayi hade da bata izinin shigowa

    Khadija bataso shigaba ganin yayanta na d’akin, Amma ba yanda ta iyya haka ta shigo, ina kwana Aunty?

    “Lafiya khadija ya goggo”?

    Tana lafiya ina kwana yaya, tana maganar tana kokarin zama

    Lafiya khadija…ya Amsa mata

    ” khadija matso muci” sumayya tace wa khadija

    Ah ah Aunty nagode, daman takarduna ne na kawo miki duka kamar yanda kika bukata.

    “Lallai ma khadija bansan yaushe zanna baki abu kisa hannu ki karba ba tare da kin mini filako ba”tace tana mikawa khadija plate na abincin data zuba mata sabo

    Ba musu khadija ta karba

    “Yayan khadija”

    Na’am sumayya..

    Inaso zamu fita da khadija, zanje na sama mata makaranta tunda yanzun muna first time bazamu sha wahalar samun aji ba, Amma yakace ka Amince koh yaya”

    Sumayya bazance miki kume ba sai dai nace Allah ya biyaki, tabbas yau zaki cikamin d’aya daga cikin buru kana dana so cikawa amma kana naka Allah na nasa.

    Aunty makaranta zaki sani😳??khadija ta tambaya cikin zare ido fuska a washe

    “Insha Allah kanwata zaki shiga makaranta yau yau ma amma wani school kikeson shiga”?

    Koh wanne ma aunty nagode kin gama min kome arayuwa tunda zaki sani a makaranta bani da wani zabi koh wanne ki sani.

    Matsalata dake kenan khadija in mutum yace kaza sai kice kaza, yanzun ni in baki fad’amin makarantar da kike soba ina zansan makarantan da ya dace ki shiga”

    Nidai aunty na baki zabi

    “Shikenan bari yayanki ya zaba miki”

    Da sauri Al’ameen yace, nikam ba ruwana tsakanin ku nida ba idone dani ba ina nasan makarantu inba na gw’annati tada ba

    “Shikenan yanzun Art kikeso koh science”?

    Aunty science nakeso.

    “Shikenan sai muje GSSSJ ina ga makarantar tafi inganci a harkan science”

    Kai Aunty tsadane fa da school in kuma ga kudin registration mai yawa gashi wai sai anye Attitude test kafun abawa mutum gurbin karatu.

    Khadija kenan indai kin yarda da kanki Attitude test bazai baki tsoro ba maganan tsadan registration, kuma ai kyaunsa yasa kudin yayi yawa, duk da makarantar goverment ne”?

    Gaskiya ne sumayya kinsan koh lokacin mu ba makarantar da ta kaita inganci kyau da doka kuma sai wane da wane ne a ciki a kaf Taraba daga goverment har private Amma yanzun xamani ya chanja saidai a sata a lissafin goverment school mafi inganci

    “Yauwa bara na tashi in shirya kaima sai muje dakai yayan khadija zan bude account a bank da voter’s card naka”

    Nikam gaskiya ba inda zani tunda khadija tazo da National ID card nata sai a bude miki babban Account kawai.

    “Kace kawai bazaka ba shikenan”sumayya tace tana mikewa,kaya ta fitar zata saka ganin haka yasa khadija fita a d’akin ta bata waje

    Nifa kawai zuwanne banji shiyasa nace kije da khadija

    “Toh zamuje daga nan saina wuce bank in, nama manta ban fad’a maka ba nayi posted na vedio n make-up da lalle harda photos yanzun haka next week za’ayi bikin yar kanwar Deputy Govnor an bani kwangilan musu lalle da make-up kawaye kawai da Amarya”

    Duk sunzo gidan nan?Al’ameen ya tambaya da mamaki

    “Ah ah a online fa muka gama kome har balance na fad’a musu yanzun ma jiran Amaryar take na tura mata account numbar na”

    Wow Allah abin godiya Amma dai sunan ki da suka ganine yasaka su baki aikin hala?

    “Wani irin suna kuma?toh ni ban ma saka sunana ba wani sunan na saka”

    Wani suna kenan?

    “Basai kaji ba” tace tana yafa gyalenda ta d’auko sai jaka da takalmi data rike a hannu zata fita a d’akin sai kuma ta sake juyowa ta kallesa jin tambayar da ya mata

    Sumayya baki bani bluetooth in ba?

    “Ikon Allah”tace hade da nufar cikin kayanta, Allah yasa ma tayi charge insa, makala masa tayi a kunne ta saita da wayanta,” waka zan saka maka koh wa’azi”?

    Waka….

    Wakar ta kunna masa”ga wajen da zaka taba ta gefe in zaka danna next koh back koh stop koh play”tana fad’a tana kama hannunsa tana nuna masa gun

    Eh na fahimta, saikin dawo

    “Allah yasa zanbi kasuwa duka me zan saya maka”?

    Kasuwa kuma sumayya?

    “Eh mana koh bakason naje? na saima khadija uniform ne da kuma d’an cefene nakeso na mana na sati uku kafun a fara azumi”

    Saikun dawo Allah ya kiyaye hanya

    “Ameen baka fad’a mini abinda zan sai maka ba”

    Am waken Gembu(Red beans)nakeso inkin iyya dafawa yanda suke innan asa tarugun Gembu(yellow pepper) da ice fish, irin dafin.

    “Hhhh eyeee kaima har kasan hadin dadi haka bansani ba”

    Allah inason abincin sosai…

    “Shikenan zan saya maka sai mun dawo”

    Allah yasa…

    Ameen, sumayya tace tana fita a d’aki, suka nufi kofar gidan da khadija

    Sunje makarantan kuma Alhamdulilah khadija ta samu gurbin karatu a makarantar science bayan interview da aka mata don an riga anyi Attitude test tun bayan sati uku, sun bawa khadija class, sumayya ta biya kudin kome atake aka mata registration aka bata su textbook, notebook , da tarkacen kayan makaranta su rigan sanyi rigan house socks vaji da sauran abubuwa

    Bayan sun bar makarantar yau kam duk wanda yaga khadija koh ba’a fad’a masa ba yasan tana cikin farin ciki sosai bank sukaje sumayya tasa aka budewa khadija Account .

    Kasuwa suka wuce tasai ma khadija uniform jaka da takalmi don sune kawai ba’a basu ba, a kasuwar ta baiwa tailor ya d’inka musu kala ukune jibi khadija zatazo ta karba Turare ta saima khadija da mayuka masu kyau sai Dutsen guga karami na wuta.

    Cefene tayi mai yawa sosai ta sai harda su drinks, doya, dankalin hausa, harda na turawa, vegetables, kai abubuwa sosai sumayya ta saiya saida kudin hannunta ya kare na machine kawai ya rage musu da d’an abinda baza’a rasa ba

    Bayan sun dawo gida da sallama, suka shiga gabaki d’aya dan dazon yan gidan suka bisu da ido ga kaya niki niki kamar masu kaura suka wuce suka shiga kofar ga yara na rirrike da laidodi

    Wa’alaikumus sallam, sannun ku da hanya Al’ameen yace yana cire hannunsa daga cikin kwanukan da yake wankewa

    “Yauwa yayan khadija” sumayya tace tana bin kofar da kallo ganin kayansu daya wanke ga randa a cike da ruwa Alamu dai jido yayi

    Yaran na sauke kayan sumayya 10 10 ta basu da murna suka karba kowa na jin dadi suka fita

    Sallah khadija da sumayya sukayi kafun suka baje cefenen suna dubawa, khadija kam ganin yanda sumayya ta loda mata kayan sayayyanta a gabanta kuka kawai ta sake tana rungumar sumayya,yanzun aunty duka wannan nawane? yaya kaga kayan kuwa wai duka nawa😅, tana fad’a tana kamo hannun yayanta ta d’aura akan damin kayayyakin abin ma abin dariya da tausayi

    Shima karan kansa Al’ameen yayi mamakin kayan, sumayya abubuwan nan basuyi yawa ba kinje kin kashe kudi da yawa haka sumayya kina ga ba aiki nake fita ba bazaki tattala kudinki ba sai kina fashaka haka.

    “Allah zai kawo kuma maganar baka aiki bazai hana nayi walwala ba kaima insha Allah kafun d’aya ga azumi zaka daina zaman gidan nan”

    Allah yasa Amma dai sumayya kayan yayi yawa

    Babu wani yawa yar fa makaranta ce sai da guga da wanki da gyara, kema khadija duk safiya kina zuwa kafun ki tafi makaranta kizo ki karya,ki karbi kudin tara dana keke kinsan sunce sai 2 ake tashi kuma ana dukan letti

    Toh Aunty amma zanna karyawa a gida saina zo na karbi na kudin.

    “Shikenan monday zaki fara zuwa jibi, kije ki karbi uniform in ki gobe ki goge, gata sai school”😃

    Hhh hakane Aunty in tafi da kayan naje na nunawa goggo kona barshi Anan?

    “Ai yanzun kayanki ne ki tafi dashi”

    Toh aunty tace tana rungumar kayanta ta fita

    Khadija na tsananin farin ciki yau wanda rabon dana gansa har na manta, Al’ameen ya fad’a yana lalubar hannun sumayya ya kama

    “Insha Allah zaka yita ganin sa yanzun harka gaji”

    Allah yasa, kema Allah ya biyaki

    “Ameen, na sai maka waken Amma na gaji gaskiya bazan iyya dafawa yanzun ba kasan sa da wahalar nuna”

    Shikenan sumayya Allah ya kaimu goben

    “Ameen”, tace tana d’aukar wayanta dake neman agaji”Assalamu Alaikum”

    Shuru tad’anyi sai kuma yaji tace “toh bara na tura miki ta WhatsApp”

    “Ok shikenan”, tace tana aje wayan

    “Kasan waya kira”?

    Ah ah …

    “Yar kanwar deputy ne waina tura account number”

    Toh Allah ya bada sa’a

    Ameen, bara na tura musu

    Tashi Al’ameen kam yayi yaje ya cigaba da wanke wanken sa

    sumayya kam Account numbar ta tura musu koh minutes 10 ba’ayi ba taji Alert kudine ya shigo account in khadija dayake da layinta aka bude account in…..

    Khadija kam na fita a gidan yayanta da kaya niki niki sai sauri take kamar zata fad’i damuwarta kawai taga ta isa gida ta nunawa goggo abin Alkhari data samu, bata hankalta ba tazo tsallaka titi koh ganin gabanta batayi, ji kawai tayi jama’a na illalilahi keeee kalli gabanki

    Ai jiii kawai kake kiiiiiiiiiiiii kauuuuuuuuu………….

     

    🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 *Albishirin ku Mata ku marmaso kuji sirrin,Koh kinsan mace sai da kamshi da gyara* 😉

    🍀🍀🍀🍀 *Turare suna d’ayace Amma sun banbanta kowanne da ingancinsa kamshinsa da aikin sa*

    🍀🍀🍀🍀 *Ina muku Albishir da UMSAD INCENSE Dan samun turaruka masu kamshi da* *gyara*

    🍀🍀🍀 *Tabbas Turare sirrine ga Koh wace mace*

    🍀🍀🍀 *Gamai bukatar turarukan UMSAD INCENSE*

    🍀 *Na tsunguno(habil)*
    🍀 *Na jiki (kwalaccam)* ( *khumra, black & white* )
    🍀 *Turaren turara jiki after birth* ,
    🍀 *Na d’aki(halud Al’oud)*

    *UMSAD INCENSE suna kofar waika wajen Ado bayaro layout Kano State* 💃🏼💃🏼

    🍀🍀🍀 *Suna bada d’aya Koh sare akan farashi Mai Rahusa*

    🍀🍀🍀 *Suna bada order kayansu Gamai bukata aduk jahar da yake a fadin Nigeria*

    Contact them vie
    🪀08028827241 or 09033791049
    IG @umsadincense

    🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
    🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯
    ~ Na ~

    🍃 *Rukayya* *Ibrahim* 🍃

    ✨Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za’a ga mistake Koh typing error Amin afuwa👌
    free book 🤧

  • Matar Makaho 34-35

    Matar Makaho 34-35

    Page3️⃣4️⃣&3️⃣5️⃣
    Al’ameen ne, Sumayya ta gani zaune ya zuba tagumi Koh abincin Bai d’and’ana ba.

    Cikin mamaki ta karaso cikin dakin”yayan Khadija lafiya kuwa”? tace tana matsowa kusa dashi

    Firgigit ya dawo hayyacinsa, Sumayya har kun Gama kwalliyar?

    “Eh mun gama,Naga bakaci abincin kaba Allah dai yasa lfy Koh” ta Kara tambayar sa.

    Lafiya Sumayya jiranki nake in kuka Gama saimuci”ya Bata Amsa

    Da mamaki sumayya ke kallonsa”banace kaci ba”?

    Sumayya na kasaci ne, kece Kika nema Kika dafa Taya zanyi na rigaki ci bayan ke kina ta faman aiki.

    “Karka Kara fad’amin irin wannan magana daga yau”

    Don me?ya tambaye ta

    “Saboda duk abinda na baka ni gani nake kamar kaika bani mukeci banason Kara Jin irin maganar nan,Ina zaune itdakai ne badon kome ba sai don Allah,rufin asirin ka nawa ne nawa nakane”ta fada tana kallonsa

    Shikenan Sumayya nagode,

    “Bana bukatar godiyan ka ka gode Allah”tace tana matsowa kusa da abincin budewa tayi tasa shukali”Bismillah muci”tace tana iba

    Toh yace Yana laluben nasa shukalin

    Abinci sukaci Amma cikinsu Babu Mai magana kowa Yana cin abinci ne,bare Hajiya sumy

    Suna Gama cin abincin Al’ameen ne ya tattara Kwanukan yafita dasu waje

    Sumayya Kam wanka ta shiga,tana fita tayi Alwala,kayan bacci tasa ta kwanta

    Al’ameen Jin ta kwanta yasa shima fita wajen ruwa ya Iba yayi wanka.kamar yanda yazamo musu Al’ada wankan dare kafun su kwanta,Yana fitowa ban d’akin kofar shashen su ya rufe,ya shigo d’akin,rufewa yayi a hankali yake takawa Yana laluben gadon harya iso, Hawa gadon yayi ya kwanta a hankali,

    Sumayya Kam mamakine ya kamata ganin sa a hakan Sannan yahau gadon ma Bai Saba Mata yanda yake Mata ba, watoh son mannuwa kusa da ita.

    A hankali ta mirgina kusa dashi hannu tasa ta Kama NASA hannun”yayan Khadija”

    Cikin sanyin halinsan nan ya amsa mata, na’am.

    “Menene yake damunka ne Wai” ?

    Ba kome Sumayya me Kika gani?ya tambaye ta Yana Mai dagota ya d’aurata a jikinsa gabaki d’aya

    “Ba kome, yauwa nace kanada National ID card ne”?

    Sai dai voters card bani da National ID card

    “Ok shima zaiyi Daman inason na bude account a bank ne kasan banzo da details nawa ba”

    Toh shikenan Allah ya kaimu goben saina baki

    “Zaka rakani bank in? Koh naje da kaina”ta fada tana gyara kwanciyar ta akansa

    Duk yanda Kika gani goben ne Zaki bank in Koh yaushe?

    “Sai na Gama lallen da akayi booking innan”

    Toh shikenan Allah ya kaimu saina rakaki,in khadija taji sauki Kuma sai kuje tare kinsan me?ya tambaye Sumayya

    “Ah ah”

    Khadija na son zuwa bank Kamar me haka lokacin kudin covid 19 ta dameni Wai sai naje mun bude account muma,mun cika Koh zamu samu kudi,Amma da mukaje bank hanani Shiga sukayi security Wai ba’a bara a banki,Kuma su tsaya su saurare mu sunki Haka suka kuramu waje.

    Sosai naji maganar ta tabamin rai”aiko Insha Allah da ita zani taga bank,Amma kaima fa Dole zamuje tare tunda account Kai za’a budewa ba niba.

    Toh Allah ya nuna Mana yace Yana zura hannunsa a cikin rigan bacci dake jikinta

    Jin hannunsa a riganta unexpected yasa ta zabura sai Kuma ta koma ta kwanta a hankali ta lumshe ido Jin abinda yake Mata da hannunsa a cikin riga”kasan me”?

    Ah ah ya Bata Amsa

    “Nikam Ina ga Zan Saida laptop Ina da waya”

    Akan me Zaki saidasu toh?

    “Saboda Banga amfanin suba inba kallo ba me nake dasu shiyasa Zan sayar”tace. Tana taimaka Masa ganin Yana kokarin zare rigar Tata

    Umm umm Sumayya waike bazaki ringa d’aukar kwalliya kina sawa a media ba Koh Allah zaisa asamu location naki Kinga ai sai afi saninki sosai a Jala

    “Kasan ba kowa keson asa hotonsa a social media ba shiyasa ban fara posted ba,Nima nayi wannan tunanin”

    Eh ai tambayan su zakinayi Zaki d’aura hotonsu kiyi Tallah Amma fa Yan Mata banda matan aure, insun Amince shikinan,tunda wasu da yawa in sunyi kwalliyar ma post suke.

    “Gaskiya ne Amma waya fad’a maka ana d’aura kwalliya a online?
    Kuma ya akayi kasan ana Post”?Sumayya ta tambaye sa tana kakkama Masa gashin kai Jin wani magic dake bin jikinta a sanadin abinda yake Mata

    Uhmmm ai inaji ana Hira koma ni lokacin da na makance ma waya tayi araha a hannun kowa ba,Kamar yanzun

    Washhhh toh,uhmm tace tana zillewa daga kansa ta sauka a gefe.

    Jin ta zame yasa ya bita shima, tana kwanciya ya kwanta akanta rumfa ya Mata da kirjinsa,ya had’a fuskarsa da Tata fuskar yayi Yana tsintsinar bakinta,dake kamshi

    “Wayyo ka sauka nauye”tace tana mutsu mutsu tana damke damtsen hannunsa

    Shagwaba Koh bafa nauyina na d’aura miki ba

    “Nidai ka sauka,kawai tsoro nakeji”

    Tsoron me?ko ni dodone?ya tambaye ta Yana Mai Kara matsota garesa

    “Ka sauka”

    Naki,yace Yana Kara Danna kansa akanta

    “Nifa bacci nakeji kaji muye bacci”

    Nikam banajin bacci

    “Nikam ai inaji Koh”?

    Sai kiye ai na hanaki ne?

    “Amma ai ka tokareni”

    Shuru ya Mata yaki kulata sai bidirinsa yake a kanta jifa jifa tana taimaka Masa

    Jin abin NASA ya fara yawa yasa ta fashe Masa da kuka

    A tsorace ya mike a kanta sauka yayi gefe cikin tsoro,yake tambayar ta,ke Sumayya menene,Yana tattabata yaji Koh lfy

    Saura kad’an dariya ya kubucewa Sumayya Jin yanda duk ya tsorata dagajin kukanta kawai,ta rasa ma wani irin namiji ne Mai shegen tsoro haka

    “Toh ba Kaine ba nace maka inajin bacci sai matseni kake”ta fada da muryar kuka tana kallonsa tana Masa gwalo ganin yanda sai zazzare ido yake kamar kace kittt ya ruga

    Shine abinda ya saki kuka?

    “Eh Mana”

    Toh Yi hakuri kwanta toh.

    Dariyace ta subuce mata Jin abinda yace Yana kwanciya a gefenta baima mannu kusa da itaba

    Cikin mamaki ya Tashi zaune Jin tana dariya, Sumayya Anya lfy kuwa daga kuka saiki koma dariya?

    Shuru tayi gudun karya harbo jirginta”babu kawai ji nayi kamar jakulkule ake mini a ciki”

    Shuru yayi baice kome ba illah rufe ido da yayi Yana nazarin Rayuwa yau Wai shine da Mata,Ashe haka zama da mace yakeda Dadi duk halinda kake ciki muddin ka samu mace na gari ka Gama samun Jin dadi,duk halinda namiji zai shiga mundin dare yayi zata ga tayi kokarin kauda damuwar tasa Koh Bata cireba,zatayi iyya bakin kokarin ta taga ta d’auke Masa hankali

    Jin yanda Sumayya keta motse yasa shi kiranta, Sumayya!!

    “Na’am”ta amsa tana gyara kwanciya

    Bakiyi bacci ba?

    “Umm banyi ba”

    Saboda me?

    “Haka kawai”

    Jin Amsar da ta basa yasa a hankali ya matso gareta,lumshe ido tayi Jin yanda tsikar jikinta ke tashi,Jin gashin kirjinsa na goguwa da bayan ta

    Hannu yasa a hankali ya Kama waist inta d’an zabura tayi kad’an,yasa hannu ya maidata,watoh kukan shugwaba Koh?

    “Bawani shugwaba,Kuma ni ba shagwabebbiya bace atoh”

    Shugwabebbiyace Mana ai duk lukutaye akwai shagwaba

    “Waye lukutar”?ta tambaye sa tana juyowa suka fuskanci juna

    Daga Sumayya har Al’ameen wani yanayi sukaji a tare da junan su sosai kusancin su yayi yawa akwance da suken nan

    Kece Mana, lukuta kiga nan naki fa Kato,yace Yana Kama Mata bombs,
    Hannu tasa ta buge Masa hannu”ai naka yafi nawa girma”

    Zare ido yayi Kamar tana ganinsa,ai Dana shiga uku ai,sai wando Mai shape za’ana dinka min.

    Hhhhh Sumayya ta Kama dariya “Wai wando Mai shape waya ganka kana tafiya kana murgud’asu a cikin jallabiya”ta karasa maganar da kamo hannunsa dake Kan kirjinta don wallahih kirjin zafi yake Mata

    Shi Karan kansa Al’ameen abin sai da ya basa dariya,Amma yakiye, murmushi kawai yayi,Jin ta Kama Masa hannu kafarsa ya daura Mata akan kafa.

    Kokarin mikewa ta fara har lokacin hannunsa na rike a nata Wai don karya taba Mata inda bataso

    Jin tana kokarin tashi yasa sa tambayar ta,Ina Zaki Kuma dare fa yayi.

    “Rigata nake nema”

    Kiye me dashi?

    “Me ake da riga”

    Sawa, ya Bata Amsa

    “Nima sawan zanyi”

    Nikam gaskiya banso kawai mu k’wanta haka.

    “Jikinka Koh nawa?wato mu k’wanta haka ka karasani ba”

    Sorry zafi yake mikine?

    “Eh Mana duk ka mammasa mini jiki”

    Amma ai kinji Dadi

    “Banjiba”ta basa amsa tana mikewa zaune

    Ai da sauri yasa hannu ya rike Tata hannun,yana kwance Bai tashi ba,kiyi hakuri mu k’wanta haka ba abinda Zan sake Miki.

    “Ai kasan bakyau kwana ba Kaya”

    Menene a jikinki Koh tsirara kike yanzun?

    “Rigan fa”

    Ai nace bazan miki kome ba yace Yana jawota jikinsa matseta yayi a hankali ya jawo blanket inda ke Kan kadon ya rufe jikinsu.

    ***********

    Washe gari Kamar kullum bayan Al’ameen ya dawo sallan asuba, sunnah TV Sumayya ta kunna musu daga ita harshi in suna kwance suna sauraron wa’azi.

    Sai wajen 7:3pm Sumayya ta mike shara tayi yayan Khadija ya Mata wanke wanke, ruwan zafi ta jona abuta,Yana tafasa ta juye a boker tasawa yayan Khadija nasa, ta shiga ban dakin

    tana fita yayan Khadija ma wanka ya Shiga.

    Vayan sun Gama shiryawa kudi ta mika masa 1k”ka sai Mana egg’s guda biyar sai bread na 500 Mai kyau ka hada Mana da butter ”

    Karban kudin yayi,ya fita.

    Bayan ya sayo k’wai da bread, soya k’wai in Sumayya tayi ta hada musu cornflakes ga tie,jira musu tayi a kasan cafet,kamo hannunsa tayi suka zauna a kasa, bubude abincin tayi”karbi shukalinka”

    Toh yace Ya karba shukalin ,tattaba plates in yayi Jin plate biyu ne ga bowl d’aya ga cups biyu,wannene abincin nawa Naga Kwanukan da yawa?

    Duka zakaci d’ayan soyayyen k’wai ne d’ayan bread ne da butter a jikinsa sai Kuma bowl na cornflakes,sai cups na tie”nace Ina tura Masa plate in k’wai a gabansa”kaci kwai sai kana Had’awa da tie ga bread”

    Shikam Al’ameen ya kasa magana Wai karyawane da abinci Kala uku shi Al’ameen,ganin Al’ameen bai fara ci ba ita har tayi Rabin cup na tie inta yasa ta aje kofin,hannu tasa a cikin k’wai in ta yagi babba ta tura Masa a baki

    Shikam Jin abinci a bakinsa da Kuma yatsarta sai faman tura Masa take yasa sa cizon yasan kad’an,

    Ai Kara ta sake hade da yarfa hannun nata”wayyo yatsana jini jini yake na bunu tace tana duba hannun”.

    Da mamaki Al’ameen yace jinii ma Sumayya?

    “Eh gashi shikinan ya gusuramin yatsa”

    Mu gani

    “Bazaka gani ba sai kace idone da kai”

    Toh muji.

    Bazakaji ba din,tace tana daukar kofin shayen ta

    Jin tayi Shuru yasa sa gutsurar bread Mai butter,Wai zai Bata itama d’ayar hannun nasa yasa ya lalubo fuskarta,Jin fuskar Tata yasa ya fara lalubar bakinta da hannunsa

    “Kasan Allah Inka samin hannun hagunka a bakina ba”tace ganin Yana ta tattaba Mata baki da hannun nasa

    Kayya abinci Zan baki,yafada Yana Mika Mata gutsuren bread inda ke hannun damansa a baki,

    Rufe bakin tayi Taki budewa.

    Shikam sai goga Mata bread in yake a lebe gashi duk butter ya Bata Mata fuska

    “Kanata Bata mini fuska da butter”tace bayan ta rike hannunsa

    Toh ba kinki bude bakin ba sai kokari nake,

    Kaga kaci abincin kan, ka barni naci nawa,tace Masa tana goge fuskar ta

    Toh ki bare na baki wanann kawai kinji

    Ganin yanda ya nace Mata yasa ta bude bakin Yana saka Mata bread in da sauri ta datse hakorin ta,Wai don ta cije yatsarsa shima abin mamaki da sauri taga ya cire hannunsa kafun ma hakorinta ya Sauka akan yatsar,Yana dariya

    Ai Daman nasan saikince Zaki Rama shiyasa Nima nayi taka tsamtsam da yatsana.

    Shuru ta Masa Bata tanka masa ba.

    Haushi ya shigane bakutuwa?

    Kara ta sake tayi kansa “nice bakutuwa”

    Jin ta hafto, yasashi Kare kansa, hannu yasa ya tare fuskarsa.

    Ganin haka sai abin yayi mugun Bata dariya waishi harga Allah tunani yake wani abin zata Masa haryana tare fuska.

    Jin shuru baiji tayi Masa kome ba yasashi fara laluben ta Aiko ya jita a kusa dashi,da sauri ya rikota, sorry kinji

    “Ni……shuru tayi Bata karasa ba Jin sallama a kofarsu amsawa tayi ta mike kaci abincin kafun na dawo”

    Toh yace Yana saka hannunsa ya d’auki cup inda ta aje masa…

    Sumayya tana fita taga wata budurwa irin classic innan zata Kai kusan sa’ar ta kyakkyawace Amma baka Tasha kwalliya tana rataye da school back “sannuki da zuwa”tace Mata tana shimfid’a musu darduma”Bismillah ki zauna”

    Yauwa Ina kwana?bakuwar tace tana zama akan sallayar

    “Lafiya ykk ya gida”?

    Lafiya Alhamdulillah,ya aiki?

    Lafiya klau,Ina zuwa Sumayya tace tana mikewa d’akin ta shiga ta hada cornflakes da ruwa Daya a fijrij ta hada a tire ta kawowa bakuwarBismillalahih ka abin Kari ba nauye Kam”tace tana ajemata a gaba

    La d’awainiyane haka Allah dakin barsa yanzun na fitoh gida zanje school ne ma nace bara na biyu dai ta gidanki

    “Allah sarki Amma dai ki saka Koh albarkane yafi dai kikici bazanji Dadi ba”

    Shikenan bara dai NASA albarkan tunda kin Masa tace tana iban cornflakes in da shukali uku tayi tace Alhamdulillah

    “Badai harkin koshi ba”?

    Alhamdulillah wallahih ya isheni,suna na kamila Ina zaune a unguwan gadi,Daman nazone wajen ki in Babu damuwa inason zan fara Training in make-up,Naga wanda kika ma kanwata a auren Asma’u shine nace tamin kwatancen gidanki inyaso sai nazo inji.

    “Toh gaskiya ni bana koyarda make-up saboda bani da shago sai gidana Kinga Kuma Ina da ayyuka yau da gobe”tace Mata tana tunanin ta yarda ne Koh karna yarda

    Ba damuwa sister Nima Ina zuwa school Kinga saiki bani time inda zanna zuwa Koh ki ban number ki duk lokacin da kike free sai ki kirani Koh Kika samu Yan make-up.

    “Shikenan yanzun dai ki bare Inna ma mijina magaa in ya Amince xakiji daga gareni”

    Ok ba damuwa saiki bani contact naki Koh in ba damuwa sannan nawane kudin da Zan biyaki Kinga Inna koma Koh yaushe Kika kirani saina tawo dasu

    Toh, make-up dai kashi kashine sanann yanayin kwakwalwar mutum wata a wata D’aya zata koye make-up wata biyu wata fiye da uku ma Bata iyya ba so ni bansan ya yanayin d’aukar kwalliyarki ba Amma dai inso samune wata uku kina koya”

    Ok yanzun wata ukun nawa ne kudina

    “50k Koh wani wata kudinki na wata uku 150k kenan”

    Wai habba sister kudin nan yayi yawa Mana dubu dari da hamsin,

    Gaskiya kenan Kinga a cikin kudin Zan Saya make-up kit sabo duka,saboda bazaiyu Ina baki na aikina kina koya dashi ba, sanan infa kika iyya a kwana uku Zaki iyya samun sama da kudinda Kika biya na koyo”

    Hakane Kam Amma dai ki duba ki rage mini kinsan baban mu yace in zaiyu nida kanwata zai biyawa.

    “Shikenan Zan rage dubu goma”

    ok shikenan an gode saina jiki

    Shikenan bara na baki number,daidai lokacin Al’ameen ya fito d’akin hannunsa rike da cup inda yasha shaye

    What?? wa nake ganin nan Kamar Muhammad Al’ameen Yusuf bakuwar tace tana zare ido

    A matukar razane har bakin sa na rawa yace kamilaaaaa………..

     

    🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 *Albishirin ku Mata ku marmaso kuji sirrin,Koh kinsan mace sai da kamshi da gyara* 😉

    🍀🍀🍀🍀 *Turare suna d’ayace Amma sun banbanta kowanne da ingancinsa kamshinsa da aikin sa*

    🍀🍀🍀🍀 *Ina muku Albishir da UMSAD INCENSE Dan samun turaruka masu kamshi da* *gyara*

    🍀🍀🍀 *Tabbas Turare sirrine ga Koh wace mace*

    🍀🍀🍀 *Gamai bukatar turarukan UMSAD INCENSE*

    🍀 *Na tsunguno(habil)*
    🍀 *Na jiki (kwalaccam)* ( *khumra, black & white* )
    🍀 *Turaren turara jiki after birth* ,
    🍀 *Na d’aki(halud Al’oud)*

    *UMSAD INCENSE suna kofar waika wajen Ado bayaro layout Kano State* 💃🏼💃🏼

    🍀🍀🍀 *Suna bada d’aya Koh sare akan farashi Mai Rahusa*

    🍀🍀🍀 *Suna bada order kayansu Gamai bukata aduk jahar da yake a fadin Nigeria*

    Contact them vie
    🪀08028827241 or 09033791049
    IG @umsadincense

    🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
    🧑‍🦯MATAR MAKAHO 🧑‍🦯
    ~ NA ~
    🍃Rukayya ibrahim🍃

    ✨Tsokaci wanna shine novlel na farko Koh da z a ga mistake ko typing error Amin afuwa👌

    Free book🤧

    *🍀wanann shafin sadaukarwa ne gareki haj Aisha Ahmad Allah yabar kaina🍀*

    Page 3️⃣6️⃣&3️⃣7️⃣

     

    🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
    🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯
    ~ Na ~

    🍃 *Rukayya* *Ibrahim* 🍃

    ✨Tsokaci wannan shine novel na farko Koh za’a ga mistake Koh typing error Amin afuwa 👌
    free book 🤧

  • Matar Makaho 66-67

    Matar Makaho 66-67

    🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
    🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯
    ~ Na ~

    🍃 *Rukayya Ibrahim* 🍃

    Page6⃣6⃣&6⃣7⃣
    Kyakkyawa tana sanye da kayan fulani, ga wani kitso manya manya a kanta, ta kura masa ido, da sauri ya mike zaune keee lafiya?ya tambaye ta cikin Al’ajabi.

    Wallun hakkiloma, tace masa tana murmushi.

    Da mamaki yake kallon ta, kafun ma yayi magana yaga wani saurayi da bazai wuce shekara 21 ba ya shigo d’akin, baki ne kamar yarinyar sai dai yarinyar ta fisa kyau sosai, duk da shima ba mummuna bane.

    laaa ka tashi?yace da sauri yana karaso wa kusa da Al’ameeen.

    Al’ameen kam ya cika da mamaki wai inane nan? gashinan a cikin wani daki kamar akurkin kaza, haka yake kallon d’akin, sai dai jin fulatanci a bakin su yasa sa gane fulanine su, duk da gidan Adara fulani ne sai dai sam basa magana da harshen su, da hausa suke magana sai dai koh yaya ne indai mutum ya zauna a jalingo, zaiji fullaci koh bai iyya maida martani ba bare shida yake zaune a unguwan fulani, shima cikin fullaci yake tambayar su nan inane yake.

    Murmushi yaga saurayi yayi, sai kuma ya juya ya kalli yarinyar, indo wai har yanzun baki tafi tallah ba?kinsan in inna tazo ta samu baki wuce ba ranki zai baci koh,fita ki d’auki nonon ki kitafi.

    Ba musu ta mike duk da ranta baiso ba, ta fita a d’akin, juyawa gidado yayi yana kallon Al’ameen, sunnu ya jikin naka?duk da fulatanci yake magana.

    Sosai Al’ameen yake mamakin wannan Al’amarin, wai garin yayane ma yazo inda yake nan, yanaji gidado nata masa magana amma kala baice ba.

    Ganin yaki magana yasa gidado tashi yabar dakin,cikin gida ya shiga yaje ya sanar da bappan sa bakon ya farka, amma baya magana don shi ya d’auka koh wata matsala ce, ya hana muhammad magana.

    Al’ameen na zaune kamar gunki yana tunani abubuwan da suka faru dashi, a yan kwana kin nan, sai kuma tunanin sumayya ya fado masa, koh yanzun a wani hali take?lumshe idanunsa yayi yana kiyastata amma yagagara hasko kaman nin ta, yaso ace itace mutum na farko da zai fara gani, bayan dawowar idanun sa.

    Gidado da bappa da suka dade da shigowa, sai magana suke amma Al’ameen baisan ma sunayi ba, dafasa gidado yayi, da sauri ya zabura sai kuma ya d’aga ido yana kallon dattijon dake kusa dashi, ya zuba masa ido, sunkuyar da kansa yayi Amma baiyi magana ba.

    Akwai inda yake maka ciwo ne?

    A hankali y dago kai ya kalli mutumin, sai kuma ya basa amsa cikin fulatanci kamar yanda yamasa magana, babu abinda yake mini ciwo.

    tashi ka fitoh kayi Alwala ka biya sallan da ake binka, gidado zai kawo maka kaya ka saka da abinci kaci.

    Toh kawai Al’ameen yace, yana mikewa tsaye da taimakon gidado ya fitoh a d’akin, kasance war dakin a hanyar kofar gidane , yasa yana fita yaga inna zaune tana gyaran zogale a tsakar gida, ina kwana?

    Mtswww kawai inna Talatu tayi, tacigaba da abinda take ba tare da tabi takan gaisuwar saba.

    Sanin halinta yasa gidado d’aukowa Al’ameen buta ya mika masa,shima Al’ameen dayake ya saba ganin abinda yafi na inna yasa bai wani damu ba, don duk Abinda zata masa lafilane in an had’a da rashin mutuncin gidan Adara.

    gidado dakinsa ya shiga, kaya ya d’auko kala uku na fulani, sai nono da matar sa ta dama,ya had’a da dambu ya kaima Al’ameen a d’aki.

    Bayan muhammad ya idar da sallah, wanka yayi bayan gidado ya iba masa ruwa a rijiya, ya chanja kaya, abincin ya bude kasa cin dambu yayi, nono kawai yasha, kad’an duk yabi ya shiga damuwa halinda sumayya da kanwar sa zasu shiga a rashin sa.

    Sai bayan muhammad ya gama kimtsawa, kafun ya mike a hankali ya fitoh a d’akin bappa ne da gidado zaune a gindin bishiya, sai inna dake zaune a gefen su rike da fifita, karasowa yayi kusa dasu bappa a hankali, ya zauna a gefen su,duk da bansan tayaya nazo nan ba, amma dai nasan taimako na kukayi, nagode Allah ya saka da Alkhar, yace musu.

    Ameeen,bappa da gidado har suna had’a baki suka amsa masa, sai kuma bappa ya kara tambayar sa, yaro garin yaya babba dakai har ruwa ya jaka?koh wani abinne ya faru dakai?

    Shiga ruwan nayi zan sha, shine yajani, ya bashi Amsa.

    Kai bako ne hala koh?don ruwan mu bayason bako.

    Eh ni ban taba zuwa kauyen nan ba, baba

    A ina kake?

    Jalingo.

    Jalingo kuma?inane haka, nidai bantaba jin sunan wannan gari ba, gidado yace da mamaki.

    Bappa ma kara tambayar sa yayi inane jalingo kuma?

    Muhammad kam sai yanzun ya tuma ashe bafa a kasar NIGERIA yake ba, yanzun toh Amma a ina yake haka, gadai mutane kamar na kasan sa fulanine musujin yare, wani kasane wannan, dan uwa?yayi maganar yana kallon gidado.

    Gidado ya juya ya kalli bappa, shima bappan gidadon ya kalla suka had’a ido, sannan suka sake maida kallonsa kan muhammad, Cameroun.

    A hankali yace musu ba’a kasar nan nake ba.

    Kamar ya ba’a kasar nan kake ba?

    Eh baba ba’a nan nake ba, a nigeria nake.

    Nigeria, a ta ina kasar take? gidado ya tambaya da mamaki, don shikam baisan wata kasa nigeria ba, murmuahi bappa yayi yana kallon gidado, nigeria ai na sha zuwa, lokacin da muke cikin ganiyar kuruciya, har kasar muke zuwa kiwo tun daga Cameroun, har nigeria.

    Wai bappa kasan kasar ne?inji gidado

    Sosai ma nasan jahohin kasar, kai yaro a wani jaha kake?ya tambaye muhammad.

    Taraba, ya basa Amsa yana kallon inna dake ta zabga masa harara tun daga inda take.

    Allah sarki ai naje jaharma dashi, da gombe harda Adamawa, amma tunda kace a taraba kake kenan ta Gimbu ka shigo kasar cameroun?

    Nima ban sani ba baba kawoni akayi.

    Kamar ya yaro aka kawo ka, ban gane ba?

    Shuru muahmmad yayi yama rasa ta ina zai fara.

    Dafasa bappa yayi, kaga yaro ka fad’amin gaskiya, mu bazamu cutar dakai ba sannan haka muke fata agunka.

    A hankali muhammad ya gyara zaman sa, ya fara bawa bappa da gidado labarin sa, har Auren sa da sumayya, da batar mahaifin su , har zuwa sanadin zuwarsa kasar nan, ya kara dacewa, sannan baba ina so na koma kasata koh don ganin halinda na tafi nabar mai d’akina a ciki.

    A hankali bappa ya d’aga ido yakalli muhammad da kyau, ya sunan ka?

    Muhammad Amma anfi sanina da Al’ameen.

    Ashe sunan baba nane dakai, Zan fad’a maka gaskiya, akwai asiri a jikin ka har yanzun, sanan bakai aka ma asirin ba, an ma wasu asirin ne a jikin ka, anyi amfani da tauraren ka anyi asiri da kai, dole kana bukatar ka zauna ka nutsu, komawar ka gida yanzun matsala ne duba da abinda mutanen da suka kawo ka sukace, zaka bata musu aiki sanan kwangilar kisan kai aka basu, watoh kaga yanzun an daina Amfani da boka, da zahiri ake son ganin bayanka, ka zauna anan zan maka jinya da izinin Allah duk asirin dake jikin ka zai karye, wa’inda akama asirin ma zasu dawo hayyacin su, sannan zan taimaka maka da maganin kariya babu wani asiri da zai sake cinka bi’izinillah,kaima ka dage da Addu’oin neman tsari a wajen Allah, don yawan ibadan ka shiyasa har yanzun basu gama cin nasara akanka ba.

    Shuru muhammad yayi amma sam ransa baiso ba, baiso hakan ba, yaso ace ayau innan ya koma gare ta, yaje yaga halinda take ciki ya kalleta da idanun sa, yaga wani irin farin ciki zatayi yau idan taga yana kallo, amma babu hali, sannan maganar mutumin nan bai kwanta masa ba, don shi ba mutum bane mai bin maganganu irin wannan na magani magani, aa tsari tsarin nan sam basu ransa.

    Ka kwantar da hankalin ka babana, ni magani zan baka don nema maka lafiya, sannan mu sama ma wasu lafiya, domin samun lafiyar ka, warakan wasu ne, karkaji kokonto ni bana aiki da Aljanu koh wani shirka, magani nake bayarwa wanda Alllah ya hure mini sani akan ganyen itatuwa da sassaken su, tunda na ganka nasan Akwai sihiri a jikin ka, Amma inga sarkan da mahaifinka ya baka.

    Hannu yasa ya kunce sarkan ya mikawa bappa, kurawa sarkan ido yayi nad’an wani lokaci sai kuma ya mike ya dauko ruwa a kwarya ya saka sarkan, ya zuba magani kad’awa yayi sai kawai ruwan maganin ya zama fari tas, wannan sarka d’ayan biyu ne Amma bazance maka kome ba Akansa, bappa yace.

    Shuru Al’ameen yayi sai kuma ya gyada kai a hankali alamun ya amince,ya karbi sarkan ya makala, kamar kwana nawa ne zamuyi baba?

    Murmushi bappa yayi sai kuma yace,ka kirani da bappa haka yarana ke kirana, sannan maganin ka bana kwana bane, na wata ne.

    Kamar wata nawa kenan bappa?

    Kamar wata uku, kuma kasan inka gama magani dole sai kunje cikin cameroun asai da shanu mu baka kudin mota.

    Shuru muhammad yayi kamar ya fashe da kuka, yanzun har wata uku yana zaune a wannan kauyen, ba tare da sumayya ba ai sai kewan ta ya kashe sa, tun lokacin sa baiyi ba, toh nagode bappa Allah ya saka,mikewa yayi a hankali ya nufi kofar da yake hango fili ta waje , alamu dai kofar gida kenan.

    ina zaka?Gidado daya mike yake tambayar sa don ya d’auka tafiya zaiyi

    Waje nake son fita, ya basa Amsa.

    Kanason zaga gari ne?

    Eh ina so, yace cikin ransa yana dariya wai wannan kauye ne gari.

    Toh jirani barana kunce shanu mu fita kiwo, saina nununa maka wajaje, yace yana tafiya tirkensu domin kunce shanun.

    Da sauri Al’ameen ya biyo sa wai zai tayasa kuncewa, ai yana saka hannu a kafar shanun da sauri yaja baya, ganin yanda shanun ta hafto kamar zata tunkudesa da kahon sa.

    Dariya gidado yayi, kai kaja baya fa shanun nan saimu, yana maganar yana kunce su .

    Matsawa muhammad yayi gefe yana kallon gidado yagama kunce su yana kad’asu yayi waje bayan ya karbi guzirin sa a wajen matar sa, muhammad na binsa a baya yana mamaki wai d’an yaron nan ne da mata.

    A haka suke tafiya gidado sai hira yake masa, duk inda suka wuce saiya ringa masa bayani, ga gonan wane, ga shanun su wane, ga kogin kaza a haka har suka nausa daji, wuni sukayi suna yawo sosai Al’ameen ya gaji bayan gidado ya kunce boronsa daya rataya, abinci ne a ciki sai goran ruwa, bayan sunci ne suka kamo hanyar gida basu suka iso ba sai goshin mangari ba, suna isa suka samu har an kira mangariba da sauri sauri gidado ya d’aure shanun suka tafi masallaci.

    Sosai jama’ar garin suke bin muhammad da kallo, ganinsa ras dashi kamar ba gawan jiya ba, gashi kyakkyawar bafulatani, suna idar da sallah, gida suka koma suna shiga muhammad yaga yarinyar d’azun da safe zaune a gefe tana cin tuwo, kai koh d’an kwali babu.

    d’aga ido tayi ta kalli Al’ameen da sauri kuma ta mike, cikin fullaci tace, laa bako kaine ka tashi, ya jikin naka yau sai sauri nake nono na ya kare na dawo gida, Amma bai kare da wuri ba.

    Shuru Al’ameen yayi baiyi magana ba, yana nazarin yarinyar kenan khadijar sa zatafi yarinyar nan a yanzun, Allah sarki yaci burin ganin su duk da bai taba tunanin ganin sa zai dawo ba, Amma yaso ganin sa na farko yafara dasu, ganin yanda ta bata fuska alamu dai bataji dadin shurun da ya mata ba, gashi gidado na kusa dashi, yasa a hankali yace eh na tashi.

    Washe baki tayi sai kuma da sauri tace, nakai maka abincin ka d’aki bappa yace na kai.

    Kai ya fahimce yarinyar nan yar damuwace, fadi ba’a tambaye taba, kamar ya sata, rijiyar dake tsakar gidan ya nufa jan ruwa yayi a kwalla ya wuce bandaki, bayan ya d’auko kayan da zaisa, bai wani jimaba ya fitoh Alwalan isha yayi jin ana kiran sallah ya wuce masallaci.

    Bayan an idar da sallan gida ya nufa a hankali ya shige dakin da aka ware masa, zama yayi akan gadon kaba da aka saka A dakin, ya buga tagumi abin duniya ya dame sa, tunanin matarsa kawai yake, adaidai wannan lokacin ne suke cin abinci, shin itama abincin take cine koh me take yanzun?

    Gidado ne ya shigo dakin da sallama.

    Amsa masa muhammad yayi, tare da gyara zaman sa.

    Har yanxun bakaci abincin ba tsoho?

    Da mamaki muhammad ke kallon sa, tsoho kuma?

    Eh man tunda ka haifi bappa aikai tsohone, yace yana aje agushin hannunsa.

    Murmushi muhammad yayi sai yanzun ya tuna, ashe fa bappa yace sunan baban sa garesa.

    Abinci na kawo mu had’a muci, yace yana bubude agushi.

    Hannu kawai muhammad yasa a kwanon bawai don yana kwadayin cin abinda ke ciki ba, loma uku yayi ya tsame hannun sa, da mamaki gidado ke kallon sa, wai harka koshine koh me?

    Wallahi gidado bazan iyya ciba, gabaki daya na saba ci da mata na, muna ci muna hira gabaki d’aya yau dai ina jina wani iri.

    Hhh dayake kabar hannun wa’inda suka kamaka ba har kana zancen kewa .

    Dariya shima muhamad yayi yana kallon gidado, wai ni ya akai nazo gidan kune?

    Nine na tsintoka a ruwa, na kawo ka gida.

    D’agani kayi koh shanunka ne ya kawo ni?

    Nina d’agaka, mana.

    Da mamaki Al’ameen yace, kaika d’agani fa kace, yana mamakin yaron nan ne ya dagasa.

    Hh ka raina karfina kenan koh?

    Shuru yayi sai kuma ya girgiza kai

    Toh kaci abincin mana, in bazaka ciba sai nasa indo ta kawo maka nono.

    Kai na koshi, nagode gidado

    Haka gidado yaci sauran abincin, bayan sun fita waje muhammad ya wanke hannunsa yana kokarin koma wa daki don sam zaman gidan baimai ba, bayason zama a gidan da akwai mata, haka shi kuma yana tsakiyarsu gashi ba’a kewaye dakin sa akayi ba, babana!!!!yaji bappa ya kirasa.

    Na’am ya amsa yana nufo bappa, bayan ya zauna ne bappa ya mika masa maganguna, wannan na hayaki ne wannan na wanka, yanxun zaka d’auki kwalla ka jika zuwa safiya, zaka fara amfani sai wannan gadaline zaka, shiga daki da kanka zaka nika da duste zansa gidado ya kawo maka, ga mai saika zuba gadalin a ciki, kana shafawa safe da rana, sosai bappa ya had’awa muhammad magani karba yayi, yayi godiya.

    Kamar yanda bappa yace haka yayi, ya jika maganin ya had’a nasha, yana gamawa ya shiga ya kwanta abinsa, sai kuma kewar sumayya duk yabi ya cikasa ji yake kamar yayi tsuntsu ya gamsa a nigeria, koh hankalin sa zai kwanta sosai yake kewan gadon su, kewan jikin ta, abincin ta, fadar su,kamshin ta kome nata kewan sa yake, a haka daker bacci ya d’auke sa.

    *********************
    sumayya fa jiki ya fara sauki kad’an duk da ba kwari yayi ba, Amma da sauki, sosai take samun kulawa a wajen mutanen nan guda uku, goggo Ammar da khadija duk da ba kula Ammar take ba, amma kullum sai yazo kuma inzai zo haka zai kawo mata abubuwa, su tsire koh kaza, sai dai su khadija suci, itakam bata iyya ci sam.

    Makwanta dayan unguwa, harda yan gidan Adara, sunzo dubata sosai ta cika da mamaki, haka customers nata ma sunzozzo kuma sosai suke rike wani abu in zasuzo, lallai sana’ar mutun nasa aga kimarsa,tunda lokacin da bata sana’a babu wanda ya lekota a asibiti, Amma yanzun kowa zuwa yake yana mata ya jiki, da jajen batar mijin ta, gashi yau satin ta biyu a gado, amma haryau zuwa ake, iyayen Ammar ma sunzo da kannen sa, baban sa ne kawai baizo ba.

    Kamar kullum yauma hakan take, da sallama ya shigo d’akin, hannunsa d’auke da laida jikin laidan duk raba da alamu dai wani abin mai sanyi ne.

    Khadija dake gefe ne ta Amsa masa tana tashi daga kan kujeran da take, ta koma gefen gadon ta zauna.

    Sumayya dake kwance, koh d’ago kai batayi ta dubesa ba, don tun akan wayanta ta daina bi takan sa.

    Sannu hajiya ya jikin?

    Shuru ta masa taki magana, sai khadija dake gefen tane takece masa jikin da sauki.

    Bude laidan da yazo dashi yayi, goran kunun ayane mai sanyi harda raba a jiki, gashi fari tass, ya mikawa khadija, gashi ki bata koh zata sha?

    Kaidai yaya Ammar baka gajiya wallahi, kullum ka kawo abu baci take ba, amma koh yaushe sai ka saya.

    Mom ina cefa tayi kunu, shine nece ta zubamin a gora guda biyar, zan kawowa sumayya tun jiya na aje a firij.

    Karba khadija tayi tana kallon sumayya dake kwance tana jinsu, Amma har lokacin bata d’ago ba, Aunty ga kunun aya mai sanyi.

    Shuru tayi sai kuma taji tana jin kwad’ayin sha, mikewa tayi a hankali ta karbi goran.

    Tsaya ta tsiyaye miki a kofi, Ammar yace ganin tana kokarin bude marfin.

    Koh magana sumayya batayi masa ba, tana bude goron a hankali tasa hancin ta mai tsayi a bakin goron tana tsuntsuna kunun, tare da lumshe ido, kunun sosai yake mata wani irin masifeffen kamshi, dake fita a ciki na aya da dabino.

    Habba sumayya menene haka?abinci kike tsuntsunawa hakan bai dace ba, babu kyau fa, yace yana mamakin abinda tayi kamar wata tababbiya.

    Kafa goran tayi da bismillah, ta fara sha shatake kamar yar kokowa da sauri sauri, tunda ta kafa goran sai da yayi rabi ta cire a bakinta tana hutawa,kafun ta sake kafa bakin ta akai sai gora ya rage babu kunu.

    Ammar da khadija tsakake sukayi suna kallon sumayya, ita da tafi sati biyu ana binta taci abinci, taki sai d’aura mata ruwa ake, duk an bubula mata jiki, Amma yau ba lallama ba banbaki, da kanta tasha kunu har goran faro medium.

    Sumayya kam ta kammala da gora d’aya, rike take da gora empty a hannu, tayi shuru amma fa har ranta kari take so, saidai tanajin kunyar tambayar wani,ganin Ammar in baibar d’akin ba.

    Bude laidan Ammar yayi ya fitar da wani goran kunu, tashi yayi da kansa ya mika mata, hade da karban empty na goran, ba tare da yayi magana ba ya koma ya zauna.

    Ba kunya sumayya ta bude goron ta kama sha, wannan karon kam a hankali take sha tana kurba kad’an kad’an har tayi rabin goran, kafun ta aje sauran a hankali ta koma ta kwanta.

    Ammar mikewa yayi ya kalli khadija, ke tashi muje waje zanyi magana dake, yana maganar yana fita waje.

    Tashi khadija tayi tabi bayansa, samunsa tayi tsaye a baranda yana jiran ta, karasowa tayi ta tsaya a gefen sa fuska ba walwala, kamar yanda taga yayi.

    Shin yayan ki nada abokan hammaya ne?

    Babu yayana baida wani abokin fad’a, asali ma yanda na tashi ban taba ganin yayana yayi koda cacan baki bane da wani.

    Ok toh akwai wanda yake nuna masa kii koh kyama haka?

    Gaskiya babu.

    Ok shikenan kawai, yace yana barin wajen ya nufi packing space, khadija ma cikin d’akin ta koma .

    Sumayya kam da tafiyan Ammar koh minutes 30 batayi ba, ta sake mikewa da sauri ta d’auki sauran kunun ayan ta shanye wanda ta rege a gora, kafun dare sumayya ta gama da gora biyar innan tas sai fitsari da take akai akai.

    Goggo data dawo karan kanta tasha mamakin kunun da yau sumayya tasha, amma batace kome ba.

    Da misalin karfe 2 sumayya ta farka da sauri ta mike zaune, jin wani irin azabebben yunwan kunun aya daya farkar da ita, sauka tayi a gadon ta nufi wajen empty in gorunan, bubudesu tayi tana kale a marfi tana sha, tsaban yanda take ji kamar bazata iyya bacci ba in bata sha ba.

    Da yake asibitin ba’a barin mutane fiye da d’aya da mara lafiya, yasa goggo barin khadija da sumayya a dakin ita ta koma wajen block in ta shimfida taburma ta kwanta, kamar yanda sauran yan uwan majinyata keyi, shiyasa buruntun sumayya, khadija ya tayar mikewa tayi a hankali tana kallon sumayya, Aunty lafiya?

    “Khadija kunun ayannan nake so, kuma ya kare”

    toh kiyi hakuri Aunty, zuwa da safe sai inje in sai miki, kinga yanzun dare yayi.

    Sumayya kam ji take yanzun in bata sha kunun nan ba zata mutu, mikewa tayi ta d’au hijab tanufi kofa.
    Aunty ina zaki kuma?
    “Neman kunu, ta bata amsa”
    A daren nan ina zamu samu wani kunu , don allah ki dawo bara nafita ni naje na saya miki.

    Dawowa sumayya tayi ta zauna a bakin gadon, ta d’auki goran kunu tana shinshinawa.

    Fita khadija tayi tun sumayya na tsammanin ganin ta har ta fara gajiya, ta jira kusan awa d’aya bata dawo ba, mikewa kawai tayi ta fita a dakin,ba tare da ta damu ba don yanzun damuwar ta kunu ne, ba dare ba,bakin get ta nufa daga ida sai hijab, data d’aura akan zanin ta sai takalmi koh kudin kunu ma bata d’auka ba a hakan ta nufi get.

    Security ne suka tare ta da mamaki, ganin zata fita da uwar daren nan, duk yanda taso su barta, ki sukayi itama taki koma wa ciki, tana tsaye a bakin get in harta gaji ta koma gefe ta zauna, ta had’a kai da gwuwa.

    Tsayawar mutun taji a kanta, da sauri ta d’ago ta dubesa sai kuma ta mike da sauri cikin mamakin ganinsa a wannan lokacin……………..🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
    🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯
    ~ Na ~

  • Matar Makaho 54-55

    Matar Makaho 54-55

    Page5⃣4⃣&5⃣5⃣
    Akan ibada don naga d’an changen rayuwa da kuka samu haryasa kuna sanyi da ibadan koh, toh bari kuji irin wannan daman makiyan ku suke jira sumu ku mai gabaki d’aya in kukayi sake da ibadah toh tabbas zasuga bayan ku sarkin yawa yafi sarkin karfi, watan da muka shiga wata ne mai Albarka ni’ima da falala ku dukufa wajen neman tsari da kariya a wajen mahaliccin mu.

    Sake baki sumayya tayi tana kallon matar da bata santa bama gashi dare ne ba nepa bare ta mata kallon sap”malama wani irin magana ne haka sannan suwaye makiyan mu”?

    Baki bukatar ji nidai na fad’a miki tace tana fita a kofar

    Sumayya kam kamar doluwa haka ta kuma sai bin hanyar da matar ta fita kawai take tana Al’ajabi”yayan khadija kaji wani magana kuwa”?

    Uhmm sumayya maganar matan nan koh bamu gaskata ba, Amma tunda ibadah tace toh mu dage koh ba makiyi Addu’a makamin mumini ne

    “Gaskiya ne” sumayya tace duk jikinta yayi sanyi sosai abincin ma kasa cigaba daci tayi

    Al’ameen dake cin abinci tsayawa yayi jin sumayya shuru hannu yasa ya tabata sumayya yadai?

    “Uhmm babu kome kawai dai ina mamaki ne”

    Mamakin me kuma? inna matan nan ne ai ba abin mamaki bane don duniya da fad’i kika san menene Alakarta da su kedai mu rike ibadah hannu bibiyu insha Allah ba Abinda zamu gani sai Alkhari kici Abinci pls?

    Toh tace tana cigaba dacin abincin”yayan khadija me zan dafa mana na sahur”?

    Me kike so?

    “Uhmm aikai na tambaya koh”?

    Nima saina tambaye ki

    “Toh ai mata ke tambayar miji abinda za’a dafa”

    Au yanzun kam an yarda ni mijine kenan?

    “Oho dai nikam ka fad’a mini abinda zan dafa so nake mu kwanta da wuri samun mu tashi da wuri”

    Ki mana tuwon shinkafa miyan shuwaka

    “Nama koh kifi”?

    Duk wanda ya dace ki saka

    “Ok” kawai tace tana tashi kitchen ta shiga ta barshi zaune akan taburma

    Girki sumayya tayi sai kusan 10:30 ta kammala aikin girki juyewa tayi a kula takai d’aki tayi tatan kamu da khadija ta karbo mata a inji tana gamawa tattara taburman tayi, ta rufe kofar su zuwa lokacin Al’ameen yayi bacci tuntuni itama kwanciyar tayi bata tashesa ba don bacci takeji itama

    Misalin karfe 1:30am Al’ameen ya farka jin sumayya ajikinsa yasa sa tata bata, sumayya!! sumayya!!

    “Menene”?

    Ki tashi mana

    “asuba yayi ne”?

    Baiyi ba sallah zamuyi tashi maza kinji

    “Uhum”tace tana mikewa sauka tayi akan gadon ta kamo hannunsa suka fitoh waje bayan ta kunna hasken wayan ta Alwala sukayi suka tada sallah

    Sai karfe uku suka sallame sosai suka dukufa suna Addu’an neman tsari wajen mahallincin mu da neman gafaran sa

    3:41 sumayya ta d’auko musu tuwon ta bude da zafin sa kamar yanzun akayi zuba musu tayi sukayi sahur basu koma bacci ba sai data cika ruwan randa a laida fari ta d’add’aure ta cika firij nata bayan asuba suka koma bacci

    Dayake Cikin Ramadan ba’acika sayan kaya da safe ba sai yamma yasa Al’ameen yabiye wa sumayya suka cigaba da bacci basu suka tashi ba sai kusan 9 Al’ameen ya tafi masallaci tafsiri sumayya ma islamiyar unguwan taje wata babbar malama ke tafsir wa matan aure a ciki

    sai bayan Azahar Al’ameen ya fita shago, sumayya kam sallah tayi ta shiga kitchen abinci ta dafa dankali ne da kwai ta soya sai ruwan tie ta musu macaroni da miya duk ta zuzzuba a kula ta zuba wasu goggo ma a manyan kula guda biyu, kiran yaro tayi ya kira mata khadija bayan ta dama kunu cikin bokatin penti fari babba, wanka ta shiga kafun ta fitoh saiga khadija ta shigo bayan sun gaisa ta bata boket in da cups na roba wanda ta saya jiya ta had’a mata takai masallaci sadaka sai ruwan da tasa da asuba a firij sunyi guda shima boket ta cika ta d’aurawa Almajiri yabi khadija

    Rarra bawa khadija tayi a masallaci sosai jama’a ke sawa abin Albarka don koh masu kudin unguwan basa kawo kome a azumi sai talakawa ke kokarin ciyar da masu azumi (Allah ya kyauta)

    Bayan khadija ta dawo da bokata yen, kulan abinci sumayya ta bata ta kaima goggo suyi bud’a baki

    Al’ameen ne ya had’a kankana da dabino sai sweet milo, yasa a laida biyu ya rike a hannunsa barin shagari yayi a shago hade da basa kudi yasai abin bud’a baki shima

    Gidan goggo ya wuce ya bata laida d’aya ya kamo hanyar gida

    Tun akan hanya ake ta masa godiyan kunu da kankara sosai yayi mamaki wani kunu kuma amma baiyi magana ba amsa musu yayi ya shiga gida daidai lokacin aka kira sallan mangari ba

    Assalamu Alaikum

    “Wa’alaikumu salam”

    Jin bakin sumayya cike da abinci ta amsa sallamar yasa sa da mamaki yace toh yau koh jira babu hajiya har an kai loma?

    “Ai a azumin nan ba jira kaji in gaya maka ana kiran sallah sai ci yaushe zan jiraka kuma”

    Uhmm yayi kyau yace yana zama akan dakalin da take, mika mata laidan yayi ganin yau koh karba batayi ba sai jin karan shukali kawai yake

    Amsa tayi ta bude dabino ne guda biyar ta damka masa a hannu sai ruwan shayi a kofi

    Karba yayi ya bude baki da addu’a bayan yaci dabinon ruwa ya kurba kawai yayi Alwala ya tafi masallaci

    Sumayya kam sai da ciki ya d’auka kafun ta zakud’a itama sallar tayi bayan ya dawo masallaci shima yaci nasa Abincin sauran kayan marmari da ya rage ta saka a firij

    Da misalin karfe 11 bayan ta gama aikace aikacen girkin asuba yake tambayar ta akan kankara da kunu

    “Yanzun don zanyi aikin lada saina fad’a maka yayan khadija watan azumi ne fa”

    Allah ya karbi ibadun mu

    “Ameen, FATAN MU(next novel)kenan insha Allah”

    Ta bangaren kamila Alhamdulilah jiki yayi sauki sosai harma an sallame ta sai dai fa fatar hannu kam ba kamar nada ba
    Yau dai gidan kawarta ta nufa
    Assalamu Alaikum
    Wa’alaikumu salam wanake gani anan koh dai idanuna ne kemin gezo lallai kamila duniya ashe ana iyya tunawa damu

    Ke matsalar ki kenan Harira daga mutum yazo gunki koh wajen zama baki bani ba kin kama mini korafi

    Ai dole na miki kamila tun auren ki na sake saki a idanu na? koh wayarki na daina samu sai dai inji a gari kinzo kin koma yar buru uba har zaki ce ban baki mazauni ba

    Yanzun dai kiyi hakuri ki zauna wata magana ce ta kawo ni

    Aikam sai ta kawo ki badai kika kawo kanki ba

    Kee habba don Allah jarabar ta isa haka

    Naji meke tafe dake kamila

    Yauwa zancen dai na muhammad ne

    Wani muhammad in?

    Ki jiki da wani banzan tambaya muhammad nawa nake dashine wai

    Nidai nasan tsohon mijinki dai ba muhammad bane

    MAKAHO…

    Kwal uba yanzun kuma tsohon zuma aka koma

    Ai daman tafi magani, ke Harira kinsan meya kashe min aure?

    Ah ah

    Toh rashin biyamin bukata ne bayayi, don bana gamsuwa shiyasa na kashe aure na don ni yanzun duniya kaf in dai zan samu namiji gwarzo ba ruwa na da talauci koh kyau kin gannin nan don nabisu banga da kyau ba

    Amma ke dai kamila akwai shirme kece miki akai shi Al’ameen in jarabebbe ne kamar ki?

    Hhh habba Harira ido fa ba mudu bane amma yasan kema

    Hhhh shegiya ta faso gari, ta karasa maganar da bawa kamila hannu suka tafa, toh yanzun me kike so ayi ne

    Yauwa MAKAHO fa aure yayi kuma wata yar iska ya aura family shugaba

    😳shugaba fa kikace?

    Eh nima nayi mamaki auren nan yar iska in kika ganta sai gaban ki ya fad’i tsabar kyau

    Kema dai kamila aikin san zuriyan gidan daman kyawawane sai dai na wani yafi na wani

    Gaskiya ne in gaya miki wai dana gama bibiyar muhammad na tataro kome nasa na samu cikeken bayani akansu shinefa naje da sunan koyan kwalliya wajen ta yar iska kinga duka da suka mini karshe ma acid inda zani makaranta dashi zamu shiga lab zuciya ya ebeni na d’auko zan watsa ma yar banza kawai in gaya miki abin mamaki muhammad ya zabi matar sa akaina da kansa ya hankad’a ni har acid ya zube a hannuna, ta karasa maganar da nunawa Harira hannun

    Cap wani mataki Dad ya d’auka akansa?

    Ai ban fad’a masa gaskiya ba cewa nayi ita ta zuba mini

    Aiko kinyi wauta

    Ai ma abin ba inda yaje don bata kamu ba

    Kema ai kinsan bazata kamun ba, yanzun dai me kike so ayi

    Yauwa Harira wajen malaman nan naki nake so ki kaini akan maganar nan

    Hhhh yar iska ba kullum fad’a kike mini akan malamai ba angaya miki ana zama hakane ai kikace zaki zauna haka toh bone ya sameki

    Gaskiya kam don akansa babu abinda bazan aikata ba ke so nake inga koh kaunar ganin sumayya baya so yaji kaf duniya ba wanda yaki jini irin ta, ba wanda yake so irina

    Shegiya ba kome tashima kiga bara na d’auko mayafi muyi gaba kinsan har kauyen mutum biyu ne in bamu tafi yanzun ba sai kuma gobe saboda hanya ba kyau ga dare

    Amma harira haka zaki tafi naga mai gidan baya nan gashi yara daga su sai yar aiki

    Kee waya gaya miki sai na jira sa ai wallahi sai abinda nace

    Uhmm kai nima fa za’ayi tafiyar nan naku dani

    Amma dai kin taho da kudi kam koh ?

    Karkiji kome akwai kudi akwai mota sai ki tukamu tunda ke kika san hanya

    Ok muje

    haka kamila da Harira suka d’auki hanyar mutum biyu wajen boka a watan azumi koh tsoron Allah babu

    Sai la’asar suka isa cikin mutum biyu dole tasa suka faka motar su a bakin titi suka hau machine mai kafa biyu zuwa ciki cikin kauyen bayan sun iso ma sai da suka tsallake ruwa

    Wani dutse ne baki kiren hayaki na fita akai tunda suka nufo wajen wani irin wari ne yake bugan hancin su da sauri kamila ta tushe hancin ta

    Cikin gaggawa Harira ta buge hannun, kamila ke kamila ki rufa mana asiri kar muje ciki a haka kin tushe hanci wani irin iskanci ne wannan?

    Amma Harira baki jin wari da doyi na tashi ne?

    Ina ji amma rufe hancin ki daidai yake da rasa aikin ki

    Kamar ya?

    Kamar haka tace tana kama hannun ta su koma baya

    Ke Harira menene haka?

    Bakin ce baki gane ba shine zan ganar dake

    Yi hakuri muje

    Haka suka nufi cikin kokon kamila kamar zata mutu tsabar wari ai bata gama ganin tashin hankali ba sai data shiga kokon taga tashin hankali mutum ne a zaune kamar an sassaka sa jikinsa duk kuraje sunyi ruwa sun cika sai doyi yake dagashe sai fata kawai ya d’aura a Gabansa ga gashin kansa sa tsitsige kamar shaid’an gashi jikin kokon kadangaru ne sunfi dubu a mamman ne koh ta ina bazama kaga jikin kokon ba tsabar yawansu gasu a shure waje d’aya

    Kai ku dakata ku dakata nace, yafad’a da muryarsa mai amoi gata muryar yar irin jarirai cikin tsawa yayi maganar

    Sosai kamila ta razana da gudu tayi hanyar fita

    Karki kuskura ki fita a nan ba tare da an gama da bukatun ki ba Tabbas zaki sami Muhammad MAKAHO…….

    Aijin ya ambace zata samu muhammad yasa ta dawo da sauri jiki na rawa ta tsunguna kamar yanda Harira tayi

    Kallon ta bokan yayi sannan ya rufe idonsa yana wani irin magan ganun tsibbo na d’an wani lokaci kafun ya bude idanunsa kallon cikin kwaryar yayi nad’an wani lokaci kafun ya d’aga ido yana kallon kamila

    Tabbas zaki samu muhammad amma fa rabasu da sumayya babban Had’ari ne saboda kaddarar su a manne take dana juna akwai makiya sama dake idanunsu kullum na kansu sannan asirin dake yawo akansu yafi wanda kike so a saka musu Amma akwai mafita d’aya

    Jiki na rawa kamila tace kamar ya kenan Allah gafarta malam

    Wani irin tsawa ya daka mata, keee ba’a kira mana Allah Anan kinsan akwai sane kika zo neman biyan bukata wajen mu(Wa iyyazubillah)

    Tuba take na kan dutse sabuwa ce Amata afuwa

    Ammata Harira amma ta kiyaye nan bama son shirme

    Zan…z..nkiyaye..takara sa maganar cikin tsoro harga Allah mutumin razana ta yake

    Yanzun ana tsaka da ibadan watan Azumi kuma sun tsaya dakyau wajen ibadah basu bada wani kofa da Za’a kawo musu farmaki ba sai dai akwai dama, nan da sati biyu zata Fara jini mundin tayi sake da ibadah zamu farmata

    Kamar ya malam?kamila ta tambaye sa

    Ranan juma’a 17 ga azumi da misalin karfe 1 na rana zata fara jini a lokacin zuwa kwana biyar kina da daman da maganin zai cita mundin tayi sakaci da ibadan da suke yanzun

    Ok toh malam ni yanzun wani mataki koh ince wani aiki d’aya za’a mini

    Akaf asirin da za’a musu don ganin yakita, bazaici ba don an musu bakin asiri na zama tare da juna abu d’aya zan miki shine Ama sumayya kurciya tabar kasan gabaki d’aya ta manta da NIGERIA a rayuwar ta kwata kwata da rayuwar da tayi a ciki,
    Wannan damar xaki samu na auren muhammad, duk da hakan zai batawa wasu shirin su da suka dade sunayi

    Na Amince wallahi na yarda ayi mata koma menene

    Shikenan zaki kawo bakar tinkiya da jan tatabara sai rakuma biyar masu ciki

    Malam ina zan samu wa’innan abubuwan sai dai in b
    Da hali na bada kudin sai a nema asaya

    Ba damuwa ki kawo

    Nawa ne?

    Bama yanke kudi biya kawai ake

    Kudi kamila ta basa kusan 500k

    Kije ki dawo gobe in mun had’a aiki sai kizo ki karba

    Toh mungode

    Fita sukayi da Harira sosai taji dadin jin za’a mata maganin yar iska

    **************
    Sosai sumayya da Al’ameen suka dage da ibada sallan dare ga sadaka duk yamma sai sumayya tayi kunu da kankara shi kuma muhammad yayi sadakar lemo ma Almajirai koh dabino

    Khadija kam haryau basu kara haduwa da Ammar ba bata kuma san shiya bude ma yayanta shago ba taci gana da zuwa makaranta har azumi yakai 17 sumayya batayi sakaci da ibada ba kwanciya da Alwala in Muhammad ya tashi da dadare yana tada ta itama ta zauna tana lazimi sosai suke ibada Awatan koh bacci yanzun basu da lokacin sa sai bayan asuba

    Ta bagaren kamila sun koma wajen boka washe gari a idanunsu ya kamo wata katuwar mujiya ya fade mata ciki layoyin da ya rubuta sunan sumayya ya saka ma mujiyar a cikin da Allura da zare yasaka ya dinke cikinta ya baiwa kamila tayi ta kula da ita a keji ta mata jinya nan da kwana 16 ranan da sumayya zata fara Al’ada kenan kuma ana son karta sake azumi daga ranan sai randa sumayya ta fara Jini saita saketa da tsakar dare tana mai Ambaton sunan sumayyar kafun gobe da safe zataji kyakkyawar lbr

    Duk da kamila na tsoron mujiya Amma dayake shaid’an ya buga mata ganga haka ta cici a kwando tayi jalingo

    Yau aka kai azumi 20 a daren ranan sumayya ta samu tsarki bayan isha’i tayi wanka

    Al’ameen kam bayan ya dawo daga Ashan kwanciyan sa yayi don yau Tahajjud zasu shiyasa yake son kwantawa da wuri

    Sumayya kam abincin asuba tayi sai kusan 9:39 ta kwanta

    Da misalin karfe 12:10 Al’ameen ya farka Tada sumayya yayi sukayi Alwala kaya suka chanja daga na bacci zuwa jallabiya ita kuma tasa dogon riga sai hijab sallaya ya d’auka suka rufe kofar suka fita

    Gidan goggo suka wuce don khadija tayi ta rokon su zata bisu itama bayan sun isa sumayya ce ta shiga gidan da sallama jin shuru yasa ta buga kofar d’akin khadija

    tashe tayi Itama Alwalan tayi suka fita a gidan

    Haka su uku suka kama hanya koh ina ka wuce group group ne na Al’umma musulmai suna tafiya manyan masallatai kamar rana ne ba dare ba

    Sumayya da khadija da Al’ameen da kafa suka taka har macilin babban masallacin juma’a na Dr Ibrahim jalo jalingo

    Sai 3 aka tashi Ana fifita a masallacin, ture ture tsabar yawan jama’a cunkoson ne yaraba sumayya da khadija

    Bayan khadija ta fitoh daker tsaya tayi tana dube duben sumayya Amma bata ganta ba A haka ta fitoh bakin SINTALI GIOBAL ta tsaya saiga yayan ta don daman sunyi agun zasu hadu in An tashi

    Bayan isarsa da mamaki jin muryar khadija kad’ai banda sumayya ya tambaye ta, ke khadija ina Aunty taki?

    Wallahi yaya banganta ba tunda muka…………..

    🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
    08146017245 *hohoho wani Kaya Sai amale shin kunsan kayatattun magungunan Mata na maman haidar*
    *Kayan maman haidar basuda matsala domin traditional medicine ne Kuma anahadasu da ingantattun itatuwa masu karfi da Basu da illah*

    🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

    *1 Gumbar kankana da ayu* 🍀🍀
    2 *Gumbar ayu zallah* 🍀🍀
    3 *Gumbar Madara da kwakwa*🍀🍀
    4 *Kaza mekwai* 🍀🍀
    5 *Zabo me zuma*🍀🍀
    6 *Kaza me allurai🍀🍀 sahihiyar mallaka ba boka ba malam*🍀🍀
    7 *Kwallin idonka inadona*🍀🍀🍀
    8 *Tauwadar mata*🍀🍀🍀
    9 *ketar larabawa magani me kankarowa mace kima da daraja*
    10 *Maganin sanyi me fatattakarsa duk kuwa nacinsa Koda bakya haihuwa indai matsalar sanyice gwada wnnn*
    11 *Maganin nono. Sahihi*
    12 *Maganin hips and bobbs*
    13 *hodar. Ni I’ma koramar mata*
    14 *nakasan Mara babban sirri*
    15 *kafi jijjibi*
    16 *daga Sha Sai wanka kasaitacce magani*
    17 *Dan kwankwalati namata da mazajensu Kevin Mata*
    18 *matsin kinfi budurwa dubu ko haihuwa nawa kikai Babu magana*

    🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
    *Maman haidar Bata tsaya anan ba*
    *takawomuku hadaddan sabulun gyaran jiki da hadin dilka Mesa sheki da laushin fata gaman kitso Wanda laraba ke amfani dashi inkin gwada saikin dawo kudai kunemeta awannan number* 08146017245
    🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

    🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
    🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯
    ~ Na ~

    🍃 *Rukayya* *Ibrahim* 🍃

    ✨Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za’a ga mistake Koh typing error Amin afuwa👌
    free book 🤧

  • Matar Makaho 48-49

    Matar Makaho 48-49

    Page 4⃣8⃣&4⃣9⃣
    Da karfi khadija ta watsar da kayan hannunta tsungunawa tayi jikinta na bari ta kama kai, gabaki d’aya ta gama sadakar wa yaukam sai Ta Allah

    Cikin zafin nama da haushi mai motar ya fitoh da fad’a fad’a,kee wace irin wawuyace wai kina tafiya koh ganin gabanki bakyayi da yanzun na kadeki fa baki jawo mini matsala ba gashi yanzun kinsa na buge keke napep innan da sai dai me zan buge? nosense kawai stupid

    Khadija kam har yanzun bata dawo daidai ba ga kuma tsawar da ake buga mata, d’aga kanta tayi tana kallon mutumin don Allah kayi hakuri wallahi bangan ka bane

    Da mamaki mutumin ke kallon ta sai kuma yayi murmushi, ke bakece kanwar Al’ameen ba?

    Eh…..eh..nice

    Murmushi kawai yayi hade da dukawa a tsakar titin yana tattara mata kayanta,saiki taso ai inba so kike wani motar tabi ta kanki ba

    Khadija kam cikin had’a fuska don sai yanzun takejin haushin zagin da ya mata, mikewa kawai tayi ta koma gefen titin

    Kizo ki shiga mota na kaiki gida?

    Bazan hauba, kuma ka bani kayana nikam.

    Kinji haushine khadija?

    Da mamaki take kallonsa toh a ina ya santa gashi itama tun d’azun sai tunanin inda tasan wannan fuskar take

    Ke yar Kauye bar kallona

    Naki dainawa kuma miko mini kayana, ta karasa maganar da kai hannu zata karbi laidodinta

    Da sauri ya kauce hade da cewa, ke khadija nifa yau gidan yayanki zaki kaini yau kusan wata biyu ina sintiri a sintali kowa na tambaya Al’ameen mijin sumayya sai ace ba’a gane saba yau ma Allah ne yasa zamu hadu shiyasa na biyo ta bakin kasuwa.

    Aikuwa bazan nuna maka ba, ba zagina kake ba

    Yi hakuri haushi naji Shiyasa yanzun muje ki nuna mini gidan yayan naki

    Gaskiya ni yanzun gida zan koma ba gidan yaya ba sauri nake

    iyeee nace ki nunamin gidan da nafi wata biyu ina nema shine zaki wanice kina sauri

    Kaga malam ni yanzun ma haka gidan na fitoh gaskiya bazan koma ba saidai nama kwatance

    Toh shikenan yi mini, kuma ga kayanki karki shiga motar inkin ga dama

    Oho maka dai, inka tsallaka titin nan sai ka mike kaga lungun shan kana shiga zakaga babban titi da yayi barade ka tambaye masu shagunan wajen, gidan Adara za’a nuna maka saika aike yaro kofar MAKAHO

    Ok toh shikenan naji, yace yana komawa wajen mai keken biyansa yayi asaran da ya masa, ya shiga motarsa yaja

    Khadija kam da ido ta bisa ta kasa tuna inda tasan bawan Allah nan Amma tabbas akwai inda ta sansa.

    **************
    “Yayan khadija gaskiya nifa yau bazanyi girki ba wallahi na gaji wanka zanyi na kwanta ”

    Kidaiyi wanka amma banda kwanciya kinsan bakyau bacci bayan la’asar koh?

    “Gaskiya ne amma dai zan d’an taba kafun goshin mangariba saika tashe ni”

    In ance abu ba kyau sumayya ki gujesa don Allah kidai kwantan koh waya koh TV ki kallah Amma banda bacci kam.

    “Toh shikenan akwai kudi a purse nawa anjima ka sayo mana abinci”

    Ah ah zan dafa…

    “Zaka dafa kuma yayan khadija, kaji mini kaudi”🤕

    Nine mai kaudi?😳

    “Eh man in ba kaudi ba ina kai ina girki, salon kaje ka kone koh ka yanke ba”

    Amma dai wallahi sumayya kin gama raina mini wayo me kika maidani ne wai?

    “Sorry toh me zaka iyya girkawa”

    Oho…..

    “Yi hakuri mana wasa fa nake maka”

    Ba wani, ya karasa maganar yana zama a bakin dakalin

    “Banace kayi hakuri ba, habba danejo Am heedee Am buddi Am yafannam lee”ta karasa wakar da kamo hannunsa ta nufi kitchen in dashi

    Kinga sakeni nafa fasa girkin bara kiji karma ki kama mini wani waka wai ma tsaya ke bafulatana ne daman?

    “Bororoje ce ba bafulatana ba, kuma girki sai kayi ehen”

    Ke wai ana girkin dole ne?

    “Yau sai kayi ai duk wanda yayi niyar aikin lada sayya karasa”

    Toh nace na fasa koh

    “Nikuma nace sai kayi” ta karasa maganar da dokarasa akan kujeran kitchen in

    Kin zama yayi inta dosana sa saiya cije”wai kai kam menene haka kasan Allah yau saikayi girkin nan”

    Zama yayi ba yanda ya iyya

    “Me ka iyya girkawa”?

    Me kikeso na girka miki?

    “Iyeee lallai ma watoh am bani zabi kenan irin ga k’wareren nan”

    Eh fad’a mini me zan girka miki?

    “Waken gembun jiyan nan zaka girka”

    Ah ah gaskiya banda shi don nidai ban iyya ba, don ni ba d’an gembu bane.

    “Hhhhh bakar magana koh”?

    Kema Aishi kika fad’amin

    “Shikenan yanzun me ka iyya dafawa maganar gaskiya nafa gaji da tsayuwa kwanciya nake son nayi fa”

    Doya na iyya soyawa da indomie, kwai, harda taliya dafa duka sai Tie

    “Doya Da k’wai ka iyya soyawa ko daban daban”?

    Soyayyen doya,kwai ma soyawa na iyya, da dafawa

    “Ok sai ka soya mana doyan da salt daban saika soya kwai shima daban akwai yaji a roba ka hada mana da ruwan bunu”

    Sannu hajiya,😒 yace yana kokarin lalubar bojuwa(tukunya)

    “Waye hajiyan kadaiji dashi”bojuwan sumayya ta wanke ta d’aura akan hot plate tasa masa mai Amma bata kunna ba Albasa ta yanka a ciki, doya ta d’auko da kwai tarugu Albasa lawashi maggi gishiri ta aje masa a kusa dashi koh wanne a roba koh tire koh gwangwa ninsa ruwa ta iba a boket tasa kofi ta aje masa duka don ya huta da tashi koma ransa innan” ga kome a zaune Allah yasa yayi dadi”tace tana fita a kitchen in

    Baiyi magana ba kawai wuka ya d’auka yafara feran doyan

    Ruwa sumayya ta iba tayi wanka kaya tasa ta kwanta duk da Al’ameen ya hanata amma baccin tuni ya sace ta

    Al’ameen na tsaka da feran doya yaji salaman yaro, amsa masa yayi

    Wai ana sallama da MAKAHO

    Inji wa?

    Nima ban sansa ba yace dai in masa sallama dakai

    Ok kaje kace masa ina zuwa

    Toh, yace yana fita a kofar

    Tashi Al’ameen yayi ya wanke hannun sa ya shiga d’akin, sumayya!ya kira sunanta jin shuru bata amsa ba sai numfashin ta dake sauka akai akai, girgiza kai kawai yayi ya d’auki sabon riga da wando da sumayya ta sai masa ya saka ya cire 3quiter dake jikinsa, waje ya fita yana mamakin waye yazo gunsa yau haka

    Waje ya fita yana tattaba jikin ginin kofar gidan don jin ina mai sallama dashin ya tsaya jin baiji motsen saba ya sakasa, kara maimaita sallamar

    Wa’alaikumu salam Al’ameen

    Laiiiiii wana kejin muryarsa kamar Ammar?

    Baka mantani ba Al’ameen ka rike sunana baka manta ba.

    Habba Ammar wanda ya maka hallaci irin wanda kamin ai ba mutumin da zaka manta dashi bane

    Hakane Ya mai jikin?

    Da sauki sosai Ammar, ya aiki ya gida?

    Lafiya kasan yau kusan wata biyu da dawowa na ina zuwa unguwan nan ban gane kaba wallahi har Hospital in na koma sukace ai an mata tiyata ma har an sallame ku tuntuni

    Eh kam satin mu d’aya aka sallame muma tuni.

    Allah sarki yamai jikin toh?

    Da sauki fa sosai kamar ma ba’a taba yanka taba, na barka a tsaye muje bakin dakali

    Ok toh in ba damuwa naga dakalin da rana kazo mu shiga cikin mota mana?

    Tsakake Al’ameen yayi yana nazari kutt anya zai yarda ya shiga motar mutun da bai sansa ba(lokacin da ya taimake ka ka sansa ne) Am daman ina d’an aikine a gida nama manta na d’aura tukunya

    Murmushi Ammar yayi watoh har yanzun Al’ameen bai yarda dashi ba kenan, toh ba kome nima bara na wuce naga yamma tayi sai na sake zuwa

    Toh shikenan nagode da ziyara Ammar

    Toh aje a cigaba da aiki mijin hajiya hhhhh

    Hhh Ammar kenan, ya fad’a yana mikama Ammar hannu sukayi musabaha a karo na biyu

    Bayan tafiyar Ammar cikin gida Al’ameen ya wuce yana tunane tunane sai kuma yaji bai kyauta ba da Ammar nason cutar dashi da randa ya d’auke sa da sumayya ya cuce su, ta wani bangaren kuma sai yaji gwara masa hakan babu ruwansa da mutanen duniya sai mutunci yanzun bai yarda da kowa ba haka zalika tsoron shiga mota ne dashi tunda masu mota suka makantar dashi, kauda tunanin yayi ya cigaba da aikinsa, daya ya gama fere doyan ya zuba a roba wankewa yayi ya tsame a kwando ya zuba gishiri kunna hot plate in yayi ya kama Aiki.

    Bayan kammala girkin Al’ameen juyewa yayi a kula ruwan shayi koma a flask wanka yayi yashiga d’akin, har lokacin sumayya bacci take, hawa yayi kan gadon a hankali ya kamota d’agata yayi cak yayi waje da ita ajeta yayi a kan dakali

    Ido sumayya ta ware jinta a sama kafun ma ta gama nazartar inda take taji an ajeta a dakali”menene haka”?

    Mangariba ake kira baccin ya isa haka, watoh bakiji bakisan baccin mangariba akwai matsala bako

    “Baccin kwasheni yayi ai”

    Sai kiyi Alwala nikam na tafi masallaci, bai saurare abinda zatace ba ya fita abinsa

    Itama samayya Alwala tayi ta shiga d’aki…

    Bayan sallan isha Al’ameen ne ya shigo kofar su, kitchen ya wuce ya d’auko kulan da 🍽 ya shige d’aki

    Sumayya dake kwance fuskarta sanye da glass ta d’aura system inta akan cikinta tana daddan nawa,d’ago kanta dake kan fillo tayi tana bin Al’ameen da kallo ganinsa d’auke da kula sosai tayi mamaki matuka, don ita harma ta manta da zancen zaiyi girki” ikon Allah wai da gaske kake kayi girki”?

    Idanunki zai nuna miki, yana magana yana fita a d’akin bayan ya aje kulan hannun sa da plate da shukula, sai kuma gashi ya dawo dauke da flask da cups, ajewa yayi a hankali akan cafet ya zuzzuba doyan da kwai sai yaji a gefen plate ya tsiyaye tie a kofuna

    Itakam sumayya sai ido kalala take kallonsa dashi”wai duk wannan kaika soya”?

    Eh man bakin raina ni ba an gaya miki in mutum baida ido shikenan sai akace bazai iyya abinda masu ido keyi ba, ai harma yafi namasu ido muna iyyawa

    “Ah ah kwadai kwatanta Amma badai yafi ba malam”

    Au karya zan miki kenan?

    “Bance ba,ina nawa doyan naga ka zuba plate d’aya”?

    Eh namu ne yau tare zamuci a plate d’aya

    Sumayya batayi magana ba sauka kawai tayi akan kujeran hannu kawai tasa ta fara cin doyan ” kai maggi yayi yawa”

    Kiji tsorin Allah fa sumayya

    “Toh da tsoron ka zanji”

    Amma dai k’wan nan babu maggin da yaji inba sharri ba

    “Nikam naji, k’wan maggi ga Albasa doyan kuma bai soyu ba, tie in kuma sugar baiji ba”😕

    Hannu yasa ya d’auke plate in gabanta da cup in tie in ya rike a hannunsa

    “Yaya haka kuma”?

    Ki miko mini kudi inje in sai miki abinci amma badai wannan zakici ba kowa ma ya hakura Almajiri zan kira na bawa, karasa maganar yayi yana shirin fita a d’akin

    Da sauri sumayya ta biyosa hade da kamo rigansa”dan Allah yayan khadija ka aje abincin mana waikai bakasan wasa bane?wasa fa nake maka”

    Wasa koh?toh ni da gaske nake kuma sakar min riga karki yaga

    “Habba don Allah yaga riga sai kace wata mai farashunan mayu”

    Toh waya sani

    “Yasan me”?

    Sakarmin riga hajiya

    “Ayya ka bani abincin mana wallahi wasa nake doya yayi d’adi haka tie ma k’wai innan inda kasan dafin Turai”

    Mika mata plate in yayi shima ya koma ya zauna abinci suka cigaba daci

    Bayan sun kammala ci yaukam ita ta d’auki kwanuka, bayan ta kaisu waje brush tayi shikam Aswakin sa ya d’auka ya goge bakinsa d’akin suka koma kayan bacci sumayya ta saka rigane da wando cotton mai laushi da socks na sanyi a kafarta, jin an fara yayyafi yasa Al’ameen fita waje ya tattare musu ruwa
    shima kayan baccin sa da sumayya ta sai masa ya yasa

    Sumayya gado tahau iyafis ta d’auka ta jona da wayan ta ta manna a kunne tana kallon film a ciki

    Shima bayan ya gama shiryawa d’akin ya rufe ya hau kan gadon, tattaba kan gadon yake har yaji ya tabota kwanciya yayi kusa da ita yasa hannu ya zame hular kanta

    Hannu tasa ta cire kunne d’ayan ta makala masa a kunne

    Kwanciya yayi akan filon da take gabaki d’aya ya nutsu yana sauraron abinda ke kunnensa, sai kuma yasa hannu ya taba sumayya hade da kiranta, sumayya!

    “Na’am”

    Uhmm Amma wannan indi’an film ne koh?

    “Eh..ya akayi ka gane”?

    Muryansu mana duk da Turanci suke magana amma dai sai kiji suna maganar sari koh bauta

    “Gaskiya ne kasan sunan film in”?

    Ah ah

    “this is fate, watoh kaddarar Rayuwa na Arewa 24”

    Oh film in karam koh?

    “Eh shine ma ke magana yanzun”

    Ai da sauri ya zare abin kunnesa tare da sa hannu ya zare na sumayya, kinsan Allah bazaki kalli film innan ba

    “Ikon Allah akam me bazan kalla ba”?

    Nidai kawai bazaki kalla bane.

    “Toh me kakeso na gani”?

    Wani film banda wannan

    “Uhmm nikam gaskiya shi nakeson kallo” tace hade da karban abinta ta mayar kunne

    Da sauri ya fizgo abin gabaki d’aya ya had’a da system in yana kokarin sauka akan gadon

    Da sauri sumayya ta cakumosa baya hade da kokarin karban system in

    Duk yanda taso kwatar abinta abin yaci tura duk inda tayi saiya zillar da hannunsa karshe ma hakura tayi takoma gefe tana maida numfashi

    Tashi yayi jin ta kwanta, zuwa yayi ya aje system in akan kujera, ya dawo ya kwanta abinsa

    Ganin ya aje yasa ta saurin mikewa zaune cikin azarbabi take kokarin sauka ta gefen kadon a hankali, tana sauka saboda matsen d’akin yasa dole saita biyo ta bangarensa kafun taje kan kujera, a hankali take tafiya

    Shikam tun tashinta zaune da saukarta duk a kunnensa shuru kawai yayi yana son ganin gudun ruwanta

    Tazo daidai dashi har zata gifta a bazata kawai taji ya fisgota baya ta fad’a kansa

    Kokarin tashi take, ya sake maidata, wai sumayya meyasa ne bakijin bari sam

    “Me nayi kuma”?

    Yanzun ina zaki?

    “Waje zan fita”

    Me zakiyi a wajen?

    “Fitsari mana koh an hana fitane in aka kulle kofa”

    Jin amsar da ta basa ya saka hannu ya mannata da jikinsa sosai kamar zai maidata ciki

    Karan shagwaba ta sake da karfi”wayyo”

    Ke menene haka saikin tara mini jama’ane

    “Toh ba kaine ka matseni ba”

    Toh ai ke ince bakiji koh kad’an kannan naki taurine dashi fa

    Eh naji kaina taurine dashi kuma ni ka sakeni fit………

    Bai bari ta karasa ba kawai ya manna bakinsa da nata sosai yake kissing inta yana dad’a matsota garesa kamar zai maidata ciki

    A hankali tasa hannu ta kama kansa da karfi ta danke gashin kansa masu yawa sosai, hade da ajiyar zuciya

    Washhh ashhh kawai Al’ameen yace bayan ya zame bakinsa a nata, hannu yasa ya kamo hannunta data rike masa gashi ya d’aura a kirjinsa, da sauri ya maida bakinsa cikin nata

    Sosai yau sumayya da Al’ameen suka farantawa junansu duk da tafiya tayi nisa sumayya ta copsa Shi kuma Al’ameen tsoro.

    *RANAN MONDAY*
    Yaune fa hajiya khadin Goggo zata makaranta jiya koh baccin kirki bata iyya ba, da sassafe ta tashi tayi wanke wanke shara kafun 6:00 har tayi wanka dumamen da goggo ta duma shi taci, uniform nata tasa fari kal wando da hijab harda riga duka farare ne socks ta saka fari ta d’aura bakin d’an kwali(kallabi)ta zura hijab, sandal inta da Aunty ta tasai mata kala biyu d’aya 👟 ne d’aya sandal, 👟in ta d’auka bakine shima don a dokar makarantar baki da fari suke so, tasa a kafarta sai agogo shima baki turare ta fisa fuskar nan washe kamar gonan Auduga takema goggo sallama hade da d’aukar school back nata shima baki mai kyau, ta fita a gidan

    Sumayya da Al’ameen ne a kitchen suna girkin karyawa kamar kullum yauma hakan take watoh ana aiki ana fad’a

    Assalamu Alaikum

    “Wa’alaikumus sallam, yan makaranta”

    Kai Aunty ina kwana?

    “Lafiya khadija harkin shirya gaskiya ne Allah yasa hakan ya d’aure banda littin”

    Ameen Aunty, ina kwana yaya?

    Lafiya khadija harkin shirya?

    Eh yaya na shirya

    D’aki sumayya ta shiga naira 200 ta d’auko sai drinks d’aya da goran faro d’aya ta fitoh “ungo khadija wannan kudi yayanki ne ya bada na baki koda zaki zo ya fita ashe da rabon zaku hadu ma kihau keke sauran d’arin saiki rike a hannunki ga wannan kuma kisa a school back naki kinji, banda kawayen banza banda abota da maza kinga makaranta ne da Christian sukafi yawa sosai kuma benchi d’aya ake had’a maza da mata don haka babu ruwan ki da yaran Christian abinda ya kaiki shi zakiyi kinji ki maida hankalin ki akan abinda ya kaiki Allah ya tsare mana ke”

    Hannu khadija tasa ta karbi kudin da drinks in hade dama sumayya godiya, yaya na tafi

    Al’ameen kam ya rasa ma me zaice da sumayya sumayya Alkhari ce garesa matar rufin asiri, toh khadija saikin dawo kindaiji abinda Auntin ki tace miki koh?

    Eh yaya..

    Adawo lfy

    Bayan fitar khadija sumayya kam kitchen ta koma taci gaba da aikin ta Al’ameen na tayata

    Assalamu Alaikum

    “Wa’alaikumu salam” sumayya ta amsa tana fita a cikin kitchen in da sauri jin muryar wance ke sallamar

    Aiko itace da mamaki sumayya ta bita da kallo,
    Al’ameen ma da sauri ya fitoh a kitchen in jin muryar me sallamar

    “Lafiya” sumayya ta tambaye ta

    Eh lafiya daman n…………….

     

    🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 *Albishirin ku Mata ku marmaso kuji sirrin,Koh kinsan mace sayanzunshi da gyara* 😉

    🍀🍀🍀🍀 *Turare suna d’ayace Amma sun banbanta kowanne da ingancinsa kamshinsa da aikin sa*

    🍀🍀🍀🍀 *Ina muku Albishir da UMSAD INCENSE Dan samun turaruka masu kamshi da* *gyara*

    🍀🍀🍀 *Tabbas Turare sirrine ga Koh wace mace*

    🍀🍀🍀 *Gamai bukatar turarukan UMSAD INCENSE*

    🍀 *Na tsunguno(habil)*
    🍀 *Na jiki (kwalaccam)* ( *khumra, black & white* )
    🍀 *Turaren turara jiki after birth* ,
    🍀 *Na d’aki(halud Al’oud)*

    *UMSAD INCENSE suna kofar waika wajen Ado bayaro layout Kano State* 💃🏼💃🏼

    🍀🍀🍀 *Suna bada d’aya Koh sare akan farashi Mai Rahusa*

    🍀🍀🍀 *Suna bada order kayansu Gamai bukata aduk jahar da yake a fadin Nigeria*

    Contact them vie
    🪀08028827241 or 09033791049
    IG @umsadincense

    🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
    🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯
    ~ Na ~

    🍃 *Rukayya* *Ibrahim* 🍃

    ✨Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za’a ga mistake Koh typing error Amin afuwa👌
    free book 🤧

    *HAPPY INDEPENDENT DAY* 🇳🇬