Hausa NovelsNoor Al Hayat Hausa Novel

Noor Al Hayat 61

Sponsored Links

Khadijah tace “Ya dangartakar ku da su Deejah?” Ya d’an yi shiru yana tunani kafin yace “Wacece Deejah kuma?” Ta kallesa tace “Deejah ce baka sani ba?” Buda ido yyi yace “Ohh wai warce kika tarar gida ranan da na kai ki kike nufi, kawar Maryam” Khadijah tace “Ehh” yace “I think, noo they are just family frnds kawai, Dad din Maryam da dad dinsu are just good frnds, childhood frnds if I am not mistaken, that’s just it” Khadijah tace “Toh Maryam fa?” Ya shafa kansa yace “Her mum kanwar Abbana ce, dad dinta kuma was once under my dad, so Maryam is my cousin” Khadijah tace “Ohk” yana kallonta yace “But why did you ask?” Wani kallo tayi masa tace “Is there anything wrong with me asking?” Murmushi yayi yace “Not at all, yaushe xa ku fara exams?” Tace “Nan da 3wks” yace “Ohk Allah ya kai mu” tace “Ameen” daga haka ta kama hannun Shureim dake tsinkar flowers ta nufi cikin gida, Aliyu ya bi su da kallo Shureim na daga masa hannu har suka shiga cikin gidan. Da daddare Khadijah na bedroom tana karatu bayan Shureim yayi bacci taji an danna bell, sosai gabanta ya fadi ta kalli agogo, a lokacin ma takwas yayi, ta mike a hankali ta isa gun kofar ta tsaya tace “Waye?” Jin muryar mace ta bude kofar, Safeenah ce tsaye bakin kofar tace “Khadijah I want to spend the nigh here if it’s ok by you” Khadijah tace “Oh you are welcm” daga haka ta bata hanya ta shigo parlorn tana cewa “Su Anty Deejah na takura ni shi sa na yo nan, da dare bai yi ba gidansu Maryam dama xan tafi” Khadijah tayi murmushi tace “To mu shiga ciki” bin bayanta Safeenah tayi har suka isa bedroom dinta, Safeenah na kallon Shureim dake bacci tace Woaw brothern ki ne wannan” Murmushi Khadijah tayi bata ce komai ba, can kuma tace “Ki hau saman gadon” Safeenah ta hau kan gadon xuwa daya side din tace “Hope baxan takura ku ba” Khadijah ta xauna gefen gadon tace “Haba dai ba wani takura” Safeenah tace “Kin san har na fara ba Abban mu labarin ki” Khadijah tayi dariya tace “Haba dai” Safeenah tace “Ehh mana, Ko mijin Jawahir Dr Ayman ya din ga kallona jiya da muka xo, da yake bai san ni ba dama tunda ba gida daya muke da jawahir ba, she is my cousin, My father and her mother are having same parent” Khadijah tace “Ayya that’s nyc” Safeenah tace “Ke karatu kawai ya kawo ki kasar nan kenan” Khadijah ta gyada kai tace “Na ma kusa gama wa” Safeenah tace “Ayya, a Nigeria wani state ku ke da parent din ki?” Khadijah tace “Kaduna” Safeenah ta gyada kai tace “Su jawahir ne ke kaduna mu a Abuja muke” Wayar Safeenah ya fara ring ta duba, mike tayi ta koma can karshen gado tace “Let me answer my call Khadijah” daga haka tayi picking call din, murmushi Khadijah tayi ta mike don dauko masu rigar sanyi, har ranta taji tana son Safeenah, she’s just free minded, daya side din gadon ta tafi ta kwanta bayan ta ajiye ma Safeenah rigar sanyin, ta lumshe ido nan da nan bacci ya dauke ta. Da asuba bayan sun idar da sllh Safeenah ta koma ta kwanta, Khadijah ta fita xuwa kitchen tana tunanin abinda xata yi na breakfast ta kai ma su Deejah, Irish tayi deciding ta soya da kwai ta dafa masu ruwan shayi don ita iyakar abinda take ci kenan gidan sai indomie ko shinkafa… Gaba daya cimar kasar bai dameta ba shi yasa ko siya bata yi, ta fi ga abincin Nigeria, har ta gama abinda take a kitchen Safeenah bacci take, daukan Shureim tayi ta fita daga dakin xuwa wani dakin tayi masa wanka ta dauko Uniform dinsa ta shiryasa ta sa masa kayan sanyin sa sannan ta basa Breakfast, wankan tayi ita ma kafin ya gama ta shirya cikin abaya ta yafa mayafinsa ganin da sauran lokaci yasa bata kai masu breakfast din ba ta tafi kai Shureim makaranta, tana dawowa ta tarar da Safeenah a parlor, Tace “Har kin tashi?” Safeenah tace “Wllh Dr Ayman ne ya tashe ni yanxu shi ya xo neman ki” Khadijah tace “Nema na kuma?” Safeenah tace “Noo xai fita ne yace xai yi dropping brother dinki a schl sai nace kilan kin je kai sa” Khadijah tace “Ayya ai daga can nake ma, akwai ruwan xafi bathroom idan xaki yi wanka” Safeenah ta mike tace “A’a bari in je can inyi tunda kayana na can din, dama jira nake ki dawo” daga haka ta nufi kofa Khadijah tace “Toh shkkn, Amma xa ki dawo?” Safeenah tayi dariya tace “Eh xan dawo” Khadijah tace “in bar maki breakfast din ki a nan kenan” Safeenah tace “Da safen nan fa xa mu wuce Khadijah” Khadijah tace “Da gaske” Safeenah tace “Ehh amma can gidansu Maryam xa mu je, Mum dinmu na can anjima da yamma sai mu dau hanyar Naija” Khadijah tace “Ayya to shikenan, idan na fito lectures da yamma kila in taho gidansu Maryam sai muyi sallama” Safeenah tace “Ba wani kila, kawai ki taho ku gaisa da Ammin mu tana can gidan ai, plss ki xo wllh ni dai ina son ki fa Khadijah I want us to be frnds” dariya Khadijah tayi tace “Toh in sha Allah xan xo” daga haka Safeenah ta wuce, Khadijah ta dau breakfast da ta masu a kitchen ta kai masu, a hankali ta bude kofar dake bude ta shiga parlorn, babu kowa parlorn sai ac dake kunne duk da sanyin garin, a hankali ta durkusa nan tsakiyar parlorn ta ajiye abubuwan hannunta, tana tunanin shiga daki wata xuciyar na ce mata kawai ta yi wucewarta idan sun fito xa su gani, har xata mike sai ga Khaleel ya fito, ya shigo parlorn yana kallonta, dai dai nan Safeenah ta fito daga daki ita ma ganin Khadijah tace “Yauwa Khadijah na bar wayata bedroom din ki” Khadijah ta mike da sauri tace “Lah to bari in dauko maki, dama xan taho da flask yanxu” Daga haka ta fita Khaleel ya dinga kallon safeenah da bata yarda ta kallesa ba tace “Ina kwana Doctor” yace “Lafiya lau” juyawa yayi ya wuce bedroom dinsa ya xauna kujera yana kallon jawahir da shigowar ta dakin kenan ita ma, atamfa ne jikinta ta yafe jikinta da mayafi tayi kyau sosai, a hankali tace “Ina kwana” yace “Lafiya qlau dear, I want to ask you something, shud i?” tana kallonsa tace “Ina jin ka” yace “Safeenah naji kamar ake kiran ta koh?” Jawahir na kallonsa tace “Ehh, what about her?” yace “Ya ku ke da ita pls?” Jawahir tace “She is my cousin sis, My mum and her father are having same parent, me ya faru?” Kallonta ya dinga yi kafin yace “Where do they stay?” Tace “Abuja” yace “Ohk sorry I’m asking this dear, bayan Dad din Safeenah, da Umman ku, da Uncle din ki na Lagos, akwai wasu kawun nan ki da ban sani ba ko aunt din ki? ta bangaren mumy fa nake tambayar ki” jawahir ta d’an yi shiru, sai kuma tace “Dama su biyar ne kawai gun maternal grand parent dina, kawun mu na Lagos ne babba, sai Abbansu Safeenah, sannan kawu Abdul, sai Ummata da kuma autarsu, but she is late, ta rasu” Khaleel dake ta kallonta yace “Since when?” Ta girgixa kai tace “I really don’t know don Umma tace min muna yara lokacin, she is always talking about her younger sis til date, seems tana sonta sosai” Khaleel na kallonta har lkcn yace “Kuma tayi aure kafin ta rasu?” Jawahir tace “Gaskiya ban sani ba” Khaleel ya dawo kusa da ita yace “Plss do me a favor of asking Umma to tell you more about her” da mamaki Jawahir ke kallonsa tace “But why?” Ya shafa kansa yace “Ke dai ki tambayar min ita plss wife” d’an murmushi tayi tace “Toh xan tambayar maka in sha Allah” yace “Yauwa nagode sosai” Khadijah na komawa apartment dinta ta dauko wayar Safeenah da flask na Lipton da ta dafa ta dawo apartment din Dr Ayman, har lkcn Safeenah na parlor tana jiranta, bayan ta karbi wayar tace “Thanks much Khadijah, baxa ki shigo ku gaisa da su Deejah da jawahir ba?” Khadijah tayi murmushi tace “Toh ina xuwa, xan dawo yanxu” daga haka ta fita, tana shiga apartment dinta jakar makarantar ta kawai ta dauka ta bar gidan don bata son sake jamming da khaleel, she just can’t withstand the sight of him. Kamar yanda tace ma Safeenah suna gama lectures karfe uku da yan mintuna ta tafi gidansu Maryam tunda ta mata alkawari, Hajiya Mariya taji dadin ganinta haka mahaifiyarsu Safeenah, Khadijah na ganinta ta ganeta don ita ce suka yi vid call kwanaki, Safeenah tace “Ammi kin ganta koh” Ammi tayi murmushi tace “Ae kam na ganta, ya iyayen naki Khadijah” Khadijah tace “suna lafiya…” Ammi tace “A kaduna ku ke da xama?” Khadijah ta gyada kai tace “Ehh” Hajiya Mariya tace “Ina Shureim din Khadijah?” Khadijah tace “Yana schl Mumy” shirye shiryen wucewa Airport suke, Khadijah dai na ta xaune parlor tare da Hajiya Mariya da Ammin su Safeenah, gaba daya hankalinta yayi kan Shureim sanin sun tashi amma ta rasa me yasa ta kasa masu sallama ta wuce, wayar ta ne yyi ring ta kalli Deejah dake kusa da ita tayi excusing kanta ta fita, kasa daukar wayar tayi duk jikinta yayi sanyi, gaba daya ta mance ita yake jira, ganin xai tsinke ta dauka daga karshe ta kai kunne a hankali tayi masa sallama, amsawa yayi yace “Uhnn it seems…. Amira ni kadai nake hauka na koh?” Da damuwa tace “Am very sorry barrister, I wanted calling you na mance, but kasan me duk wanda kaga ya maka kyau Wallahi ina so, I want ur choice” jin yayi shiru a hankali tace “Ka yi shiru barrister” yace “Ohk then…” Marairaicewa tayi tace “You are still angry koh?” Yace “Sure” tace “But nace fa kayi hakuri” yace “Amira if I am important to you baxa ki ce kin manta ba, am still in dubai because of you but kuma kice min kin mance” jikinta yayi sanyi tace “Don Allah kayi hakuri…” Yace “Nayi” daga haka yayi mata sallama ya katse wayarsa, tana ta tsaye duk bata ji dadi ba don tasan bata kyauta masa ba aka shigo gidan da mota, bin motar tayi da kallo har yayi parking ya fito, kallonta ya dinga yi sai kuma ya karaso inda take yace “Iman, when did you come?” Tace “Yanxu” yace “Good evening” tace “Same, pls kace ma su mumy na tafi Shureim yana schl har yanxu” ya kalli agogon wrist dinsa yace “Har yanxu? This is after 4” tace “Na xo sallama da su Safeenah ne” ya kara kallon agogo yace “Ohk to mu je ki daukesa in kai ku gida dama airport xan kai su…” Tace “A’a don’t worry ka kai su airport din, tnxx” daga haka ta juya ta fita gidan, tana isa makarantar su Shureim ya samu an xo an daukesa, wucewa gida tayi, tana bedroom ta cire kaya ta daura towel xata shiga wanka aka bude kofa da sauri ta juya shureim ya shigo da sallama ya wara ido yace “Anty yau ma na riga ki dawo wa” Tace “Wa ya dawo da kai?” Yace “Uncle mana” jawosa tayi ta xauna gefen gado tace “Da kuka dawo mai Antyn dake gidan tace maka?” Yace “Nothing, she only gave me food with juice, shine yanxu tace in xo in cire uniform” Khadijah ta tabe baki tace “Shi uncle din me yake?” Ya buda ido yace “Yana daki…” Ta kuma tabe baki ta cire masa uniform dinsa ta fara yi masa wanka tasa yayi alwala suka fito ta shirya sa sannan tace yayi sallah, wanka ta shiga tayi ta fito ita ma ta shirya, Shureim na assignment dinsa kan gado ta dau wayarta, text ta shiga rubuta ma Barrister na ban hakuri tana gama rubutun ta tura masa, dai dai nan aka danna bell ta mike ta dau gyalenta ta fita.

Back to top button