Blog

  • Duk karfin Izzata Book 1 Paga 2

    Duk karfin Izzata Book 1 Paga 2

    Episode 2*

    Khalid rike da hannu zahra suka fito daga part ɗin,Ammi suka nufi part ɗin Ummi suna tafiya suna hira kamar wasu friend, a dai dai kofar da zata sada su da part ɗin Ummi, su kayi karo da yusuf fiskar nan a daure kamar bai ma san menene dariyaba, nan take jikin zahra ya hau kerma, murya na rawa tache “inawuni yaya yusuf,bai bai amsa ba ya ra ɓa ta gefen su zai wuche, da sauri Khalid ya damki dam tsen hannun sa, juyowa Yusuf yayi yana kallan chikin idon Khalid ɗin “me kuma kake kallo na eh idan bazaka amsa gai suwar Zahra ba ni ba yayan ka bane dazaka raɓa gefe’na ka wuche ” a kule Yusuf yace sorry ykk “ban sani ba Khalid ya faɗa yana sakin hannun Yusuf ɗin,aiko kamar jira yake Khalid yasake sa da sauri ya wuche ya barsu tsaye, dawo da kallan sa Khalid yayi kan Zahra dake tsaye kamar zatayi fitsari a wando saboda tsoro”menene Auta,chikin rawar murya Zahra tace,”yaya Khalid shiyasa fa nache maka kai da Aunty farida da Aunty mardiya ne kawai kuke sona sai Aunty salma, kana ganin yaya Yusuf ko gaisuwa ta bai amsa ba bare ma ya tambayeni ko ina lfy,ta karisa maganar kamar zatayi kuka, kakalo murmushin dole Khalid yayi dan ko shi kansa Yusuf ya ɓata masa Rae “karki damu Auta muje mutafi hai ki rabu dasu tun da ni ina son ki kinji yayi maganar yana shafa kanta “to shike nan yaya Khalid muje, chiki suka nufa a kofar balon Ummi sukayi sallama kafin su shiga komai na chikin palon Ummi irin na Ammi ne har colour komai iri ɗaya

    Wata kyakkyawar mata che zaune saman sofa mai zaman mutun 2 a gaban ta kuwa sofa table ne dake ɗauke da kwan dan fruit mai kyan gaske a hankali take gatsar Apple ɗin take hannun ta fara che itama tas kaman nin ta ɗaya da yusuf a kallan zata kai 36 years, da gudu Zahra ta tafi ta faɗa jikin ta tana faɗin Aunty “farida na dawo “kai Auta zaki balla ni ai, dari Zahra tayi tana faɗin to Aunty na tashi, karisa shigowa chikin palon Khalid yayi ya zauna saman sofa mai ma zaunin mutun 3 yana faɗin “Aunty babba barka da hutawa,murmushi Aunty farida tayi kafin tace ai kune manya yanzu na bar muku girman, da sauri Zahra ta miƙe zaune tana faɗin “Aunty farida harda ni, ki kabawa girman “eh Auta har dake mana,tsalle Zahra tayi, tana faɗin nima na zama babba yan zukam, murmushi kawai Khalid da Aunty farida keyi suna kallan irin farin chikin da kanwar tasu ke chiki

    Wayar Aunty farida dake zaune kusa da Zahra yafara kara alamar shigowar kira,da sauri Zahra ta ɗau wayar tana faɗin ni zanyi picking call ɗin ni zanyi picking call ɗin,” to Auta yimana chewar Aunty farida tayi maganar tana kokarin ajiye Apple dake hannun ta a chikin kwandan fruit ɗin, takawo wayar Zahra tayi dai dai sai tin fuskar ta zatayi picking call ɗin, a sukwane tamiƙawa Aunty farida wayar ta hannun ta har kema yake, ansar wayar Aunty farida tayi tana kallan Zahra da mamaKi, dariya Khalid yayi kafin yace Auta lfy irin wan nan riki chewa haka DON ko Aryan ne suka kira wayar ko, Zahra dai shiru tayi bata che komai ba, zai faman zazzare ido take
    Picking call ɗin Aunty farida tayi takara wayar a kunen’ta “hello Aryan ykk, daga ɗayan ɓangaren Aryan yace lfy lau Aunty babba ykk “ina lfy y prince, bai bata amsa ba sai dai yace “kinyi magana da Abba ne “aa bamuyi ba lfy dai koh ta tambaya a ɗan ruɗe “eh to lfy kedai in kinyi waya dashi sai muyi magana ” aa Aryan wlh ban yar daba za kasa nashiga tunani pls kafa ɗa min da wata matsala ne “aa Aunty farida babu komai ke dai ki kula mana da kanki kinji, bai jira amsar taba ya katse kiran, dagowa Aunty farida tayi tana kallan Zahra”Auta lfy kika nitsu haka “turo baki Zahra tayi tace ba komai, Khalid kuwa sai dariya yake musu dan yasan dalilin nisuwar Zahra, dawo da kallanta Aunty farida tayi tana faɗin lfy, bro kake kallan mu haka,” lfy lau kawai ina mamakin irin son damuke miki ne, duk zafin ran DON da Aryan in zasuyi magana dake sas sauta murya suke, idan ran DON ya ɓachi gaba ɗaya gd kai bama gd kawai ba gaba ɗaya family mu ba mai iya tin karar sa sai ke komai ɓachin ran da yake chiki inya ganki sai ya sas’sauta zuchiyar sa kike ɗai kike sashi ya chan za magana inyayi abun yana bani mamaki, murmushi Aunty farida tayi kafin tace kasan meyasa gaba ɗayan ku kuke kau nata “aa ban sani ba “saboda nima ina matikar kaunar ne, duk da ba iyayen mu ɗaya ba narike ku da zuchiya ɗaya “da sauri Zahra tace Aunty farida daman ba Abba bane ya haifi su yaya Khalid “eh Auta ba Abba bane marigayi bappa usman ne baban su yaya Khalid yaya Ahmad dakuma Aunty Salma, “kai Aunty farida to ya akayi haka ni ban san bappa usman ɗin bama chewar Zahra tafaɗa da mamaki a fuskar’ta “kai Auta kiche dai tarihi kike son sani to matso nabaki tarihin a gurguje dan zanje wajen Abba,kara matso kusa da Aunty farida Zahra tayi ta kasa kunne, Aunty farida ta gyara zama tafara magana kamar haka

    *Abba su uku ne awajen baban su sarki khalid awan chan lokachin, Abba shine babba sai bappa usman sai bappa Aliyu ne ƙarami kakan mu shi ya haɗa auren Abba da Ummi na alokachin, baban Ummi shine sarkin katsina ansha biki sosai, bayan auren ummi na da Abba da shekara ɗaya Allah ya albarka che da samun Aihuwa ɗiya mace kuma bakowa bace face ni, ina da shakata biyu a duniya Ummi na ta haifi Mardiya, an haifi Mardiya da wata uku Abba yace zai kara Aure da farko Ummi na taki yar da amma daga baya sai ta aminche Abba ya auro yar sarkin gombe kuma itace Aunty amarya, bayan auren su da wata 10 Aunty Maryam ta haifi ɗiya mace Abba yasa mata suna maryam,alokachin ne kuma bappa usman yayi Aure ya Auri umma’n su Khalid itama data zo ya mace ta haifa, Abba ya shiga tunani da damuwa dan yana son ɗa namiji gashi shiru shiru daga Ummi har Aunty amarya ba wan da yasake Aihuwa, wani taro dasu Abba sukaje da kakan mu garin yola a chan yaga Ammi ya dage sai ita Ammi ba fulatanan ruga che iyayen ta sunki bawa Abba auren ta amma Abba yana che haka suka hakura suka bashi Auren Ammi a kasha biki auren Ammi da wata uku tasamu chiki a tare suka samu chiki da Umma’n su Khalid chikin Ammi na da wata 3 Aunty Amarya ma tasamu chiki chikin Aunty Amarya na da wata 4 Ummi na ma tana mu chiki kamar abun haɗin baki rana ɗaya Ammi da Umma’n Khalid su aihu Ammi ta haifi ɗa namiji Umma’n su Khalid ta haifi yan biyu namiji da mace, bappa Usman yayiwa kakan mu takwara yawa ɗan sa na mijin suna Khalid,macen kuma salma, Abba kuma ya sawa prince Safras musha murna sosai a satin da a ka haifi khalid da prince a satin kakan mu mace ta rasu musha kuka da bakin chiki sosai, kakan mu tana da wata uku da rasuwa Aunty Amarya ta haifi yan biyu Abba yasa musu suna Aryan da Aiman, Aryan suna da wata uku Ummi na ta haifi yusuf daga nanne basu sake hai huwaba, Khalid da salma na da shakara biyu Umma’n su ta haifi Ahmad, shiyasa kikaga da yaya prince yaya khalid yaya Aryan yaya Aiman yaya Yusuf dakuma yaya Ahmad sun taso kamar wasu ta gwaye dan dukkan su banda Ahmad ba wan da yabawa ɗan uwan da full 1 year, shiru shiru su Safras na da shakara uku Ammi ta haifi Fahad, Fahad na da shekara uku Ammi da Aunty Amarya suha aihu a tare kuma dukka ƴaƴa maza suka haifa, Abba yasa musu suna Umar da Haidar Umar na koyan zama kakan mu da bappa Usman sukayi haɗari a kan hanyar su na dawowa daga wani taro dasuka je maiduguri munji mutuwar bappa usman wan da har gobe ma inajin mutuwar bazan taba daina jin mutuwar bappa usman ba har nakoma ga Allah, tun lokachin da aka sanar da Umma bappa Usman ya rasu ta faɗi bata sake lfy ba har itama takoma ga Allah, Ammi ta ɗauki su Khalid ta haɗa su dasu prince tariƙe, Abba ne ya karɓi sarauta bayan mutuwar kakan mu sarki Khalid Abba ya karɓi sarauta wajen da shekara 5 Ammi ta haife ki tun daga kanki ba wanda yasake Aihuwa har yanzu to kinji ta kai chan chen tarihi idan idan kina san jin komai kine kisamu Ummi taba ki lbr Aunty farida ta karisa maganar tana sauke ajiyar zuchiya*

    Ji su kayi daga bayan su ana faɗin ae basai tazo waje naba wan nan lbr dakika batama ya isa, murmushi sukayi gaba ɗayan su Khalid yace “ina wuni ummi “lfy lau baba saukar yau she Ummi tayi maganar tana kokarin zama saman sofa mai zaman mutun 1 “ɗazun mu kazo Ummi “to ina sauran ko kai ka ɗai kazo “Aunty farida tace aa Yusuf ya shigo kina bar chi ai daman shida yusuf ɗin da Aiman da Ahmad ne sukazo ƴa’ƴan basu zo ba,Aunty farida ta karisa maganar tana dariya, murmushi nasu irin na manya Ummi tayi tana faɗin ” kawai Ummi tayi batare datayi magana ba “Aunty tashi kije ki kiramin Haidar da Umar kinji chewar Aunty farida, miƙewa Zahra tayi jiki ba kwari ta fice daga palo, fita tayi daga ɓangaren Ummi gaba ɗaya, ta ɗan yi tafiya kafun tashiga ɓangaren su Haidar, da sallama a bakin ta ta shiga palon, babu kowa, shiru ta tsaya tana waswasin taje betroom na su ne, kokuma tajuya taje tachewa Aunty farida bata gansuba kamar daga sama taji anche “what are you doing here ɗago ido,tayi tana kallan sa yana sanye chikin 3cuter wando ruwan kasa da farar riga mara nauyi, saurayi ne dan shekarun sa zasu fi 25 ba kyakkyawar gaske ne kaman nin sa ɗaya da DON ban ban chin sa da DON shi idan sa fari ne DON kuma light green, murya na rawa Zahra tafara magana “Aunty farida che tache nakira mata yaya Haidar da Yaya Umar “daman Aunty farida ta zone ya tambaya yana chiro waya daga aljihun sa “eh tazo tana part ɗin Ummi, shiru yayi bai sake chewa komai ba, itama Zahra shiru ta tsaya almost 10 mnt a hankali ta ɗago kai dan taga wai ya tafine ko yana nan, yana tsaye a jikin stair case ɗin yana latsa wayar sa chikin tsoro da fargaban amsan da zai bata tace “yaya Fahad ina su yaya Haidar ɗin, shiri yayi bai tanka ba kamar ma bai san akoi mutun awajen ba ko sai latsa wayar sa yake, chikin tsoro Zahra ta sake mai mai ta tambayar “tayi yaya Fahad ina su yaya Haidar, wani dogon tsaki Fahad yaja chikin tsawa yake faɗin “wai kin bani ajiyar sune abeg get out, tun bai kai karshen maganar ba Zahra ta fita da gudu dan daman kamar a kan kaya take

    Da gudu tashiga palon Ummi kan chin yar Aunty farida ta faɗa tana Kuka “subhanallah Auta meyafaru wa ya taɓaki chewar Aunty farida Zahra dai kukan ta take batayi magana ba “ai kema Aunty farida kinsan halin su banso kika aiki Zahra wajen suba, yanzu kilama ta haɗu da Yusuf ne a hanya ya daka mata tsawa, chewar Khalid Aunty farida tasa hannu tana shafa kan Zahra tana faɗin “sorry my lovely Auta kyalesu duk abun da suke miki kitara saiki rama akan ƴa’ƴansu in sunyi aure sun aihu kinji koh share hawayen ki,
    dariya khalid yayi sosai san nan yace wai wa yaga yara, tab waƴan’nan akoi zan chen aure ma a’lamarin sune, ai wlh ko zan chen mace ban taɓaji sun yiba, mutane kamar dutse basu da shauki ƴanzu haka maganar danake miki friend mu hisham zai yi aure bakin san Hisham ba Aunty farida ta gyaɗa kai alamar eh “to Hisham dan yayi Aure Aryan da DON suka raba gari dashi “what? Kana nufin saboda Hisham yayi aure ne DON da Aryan zasu raba gari dashi, abotar kufa tun yarinta kai ina hakan ba zai yuba ” to gashima yayuwu kuwa dan ba yadda bamuyi dasu ba akan suzo bikin sunki zuwa,shima Aiman damuka samu muka lallaɓashi yazo yaki halaktar daurin auren, shi kuma Yusuf ɗaurin aure kawai yaje yaki zuwa wajen walimar ” tab to wlh basu isaba dolene su zauna tare da Hisham kilama sanadiyar zaman nasu suma sufara sha’awar auren yanzufa kusan 30 years kuke dashi kun zauna ba abunda kuka iya daga mai rike bin diga sai mai rike sirin jin Allura sai mai fama da laptop wai da sunan zane, Khalid ya dukar da kai kasa dan anzo kansa shima dan shine mai fama da laptop, aunty farida tachi gaba da chewa “sai mai fama da rigar lauyoyi gamasu tasowa nan yanzu duk kun lalata musu tunani dan suma ba mai wani maganar aure chikin su, duk kun chika mana gida, to mun gaji da ganin ku ƴaƴa muke san gani, su Ammi suna bukatar jikoki gashi ni tunda nayi aure ɗa 1 Allah yabani karamin Safras har yanzu shiru kakeji ban samu kariba to gwaranima, mardiya ko ɗayan bata samuba dan haka muna bukatar ƴaƴa agidan nan, yanzu haka Fahad shekarun sa inban mantaba zasukai 25 ga Haidar da Umar suma sun kai 23 ga Zahra Auta an zama yan mata yanzu haka Zahra nada 16 years to mekuke bukata dayawuche aure Allah ya hore muku komai,to yazama dole kuyi aure yan zu kam takarisa maganar da alamar ɓachin rai a face ɗinta, Ummi dai ido ta zuba musu tana kallon su dan ita ba mai yawan magana ba che ” laaa ni Aunty farida kin tunamin ma inasan muyi wata magana, chewar khalid ɗin “ok to inzo muje waje ke nan, Khalid ya ɗan sachi kallan inda Zahra da Ummi suke san nan yace eh to muje palan Abba zai fi tunda nasan yanzu baya nan yana fada “to muje amma kafin nan bari nayi waya da yan uwan kan nan dan inasan gabaɗayan mu muhadu a palan Abba bayan sallar issha “to kawai Khalid yace tare da mikewa yanufi hanyar fita “Ummi tache adawo lfy Baba tunda abun sirri ne “murmushi yayi yana shafa kansa batare da yache komai ba yafiche daga palon

    To

    (Garin yola ✈️🛬

     

    kyakkyawar yarinya che fara tas ga dogon hanchi har baka doguwa che amma ba sosai ba bata da kiba duk da tana sanye chikin hijabi, hakan bai hana gashin dake kwanche a gaban goshin ta fito waba dark black ne gashin very smooth gata da manya manyan blue eyes, laɓɓan’ta ɗan karami pink colour bazata wuche 14 years ba sanye take chiki wata ko ɗadɗiyar atamfa ta koɗe tayi fari ga wata je mam miyar hijabi baki ne amma saboda koɗewa sai da ya dawo ash colour tsaye take tana riƙe da bokiti irin na penti almost 5mnt tana tsaye chikin fushi tafara magana da harchen fullanchi “hiyana idan bazaki fitoba wlh tafiyata zanyi na barki, tayi maganar tana kallan kofar wani gida
    Gida ne ɗan ma dai dai chi kofar gidan ansa masa buhu an rufe a matsayin labule,irin gidan fulanin nanne masu kiwon shanu ke waye gidan yake da zana, daga chikin gidan hiyana ta da wata murya mai daɗin gaske tana faɗin adin kai diyana ina zuwa ina dubawa amrat hijabi ne “to wai waya chemaki amrat zata bi mu ne, zamuɗebo har da rabonta dan haka ta zauna a gida taƙarisa maganar tana yamutsa fuska ” yaye labulen buhun hiyana tai tafito, subhanallah sarki ya tabbata ga ubangiji da yayi wan nan halittar hiyana tafi diyana kyau sosai ta ɗan fita fita tsawo, kuma da alama zata ɗan fita shekaru dan hiyana zata kai 16 years farache sosai tafi diyana haske idon tama yafi na diyana girma da shiga colour idon ta yayi blue sosai kyakkyawa che ajin farko, rike take da hannun wata yarinya wadda bazata wuche 11 years ba yarinyar tana kama da diyana sosai sai dai ita idon ta baki ne manya manya, karaso’wa wajen da diyana ke tsaye su kayi hiyana na faɗin kiyi hakuri diyana kinji “haba hiyana ke che babba amma keche ke ja’mana duka kullun “to shike nan diyana kiyi hakuri zan gyara kinji muje to “aa bazamu tafi da amrat bafa ki mai data gida “diyana kibari mutafi da ita mana babu kowa fa a gidan bappa kuma yayi barchi kin sani bansan mu barta a gd ita kaɗai “nikuma Allah hiyana bansan amrat tabi’mu rafin nan akoi wahala Allah “to yanzu kam tun da mun fito muje kawai mu daina ɓata lokachi, juyawa diyana tana tura ɗan karamin bakin tan nan suka jera su kasa amrat a tsakiya

    Wani dan siririn hanya suka nufa mai chike da dogayen chi yayi tsakiyar chi yayin suka kutsa tafiya sukayi mai nisan sosai kafin su isa wani rafi mai girma gefe gefen rafin chike yake da gona’ki da shuke shuke, ruwa suka ɗiba a buket ɗin dasuka riƙe hiyana ta ɗora’wa diyana nata buket ɗin chike da ruwa san nan da kyar itama ta ɗora nata ta kamo hannun amrat suka fito daga rafin suka kama hanyar gd, tafiya suke ba wan da yace da ɗan uwan sa ko kala, a dai dai wata katuwar bishiyar mangoro wani saurayin da bazai wuchi 24 years wani ɗan dotti dashi pusu pusu kamar an kwato shi daga bakin Kura ba yasha gaban hiyana birki suka ja suka tsaya suna kallan sa, ɗaure fuska diyana tayi tana faɗin “buba me haka dan Allah kabamu hanya mu wuche, wani kallan uku 10 buba ya watsawa diyana kafin yace “ke ba take nake ba tukun nan kibari nagama da hiyana zan dawo kanki “chikin sanyin murya hiyana tafara Magana buba kayi hakuri kaji kabar mu,mutafi wlh ruwan nan akoi nauyi kabari in muka dawo ɗiban na biyu sai mu tsaya muji me zakache “ke ni sa’ankine dazaki che na jira ku to baku isa ba yanzu nake san yin maganata idan ruwan yamuku nauyi,sai ku sauke kasa ku ajiye idan nagama maganan da zanyi sai ku ɗauki ruwan kutafi, diyana sarkin rashin hakuri a kule ta juye’wa buba ruwan dake kanta ajikin sa tun daga kansa har kafa yamike shar’kaf ta watsa a guje tanufi hanyar gida, dafe kai hiyana tayi tana faɗin “kayi hakuri buba..bata kai karshen maganar ba buba ya buge ruwan dake kanta ya faɗi kasa ya zube ɗaukar boket ɗin buba yayi yafara bugawa da katsa yana kokarin fasawa, hiyana kuwa ganin hankalin buba ya koma kan yana san fasa musu boket ne yasa ta kama hannun Amrat suka kwasa aguje sukayi hanyar gd, sai buba ya gama fashe musu bo’kitan gaba ɗaya san nan yabi bayan su a guje

    Da gudu diyana ta faɗa gd wani ɗakin buk’ka tashiga,sai haki take tana numfashi da kyar, wani bawan Allah dake zaune chikin ɗakin, a kan gadon chiyawa, daka gan shi kaga ka mannin hiyana duk da tsufa da wahala dake tattare dashi ba zai hana ka gane kyan sa ba “diyana lfy kika shigo kina haki haka meyasaki gudu wani kika tso kana ko “bappa wlh buba ne shine zai bugeni na gudu kuma ba abun dana masa, bappa zaiyi magana sai ga hiyana tashigo rike da amrat dukkan su sai haki suke suna numfashi sama saman “hiyana har dake yau kuma bappa ya tambaya yana kallan hiyana, chikin sar’kewar murya hiyana tace “aa bappa laifin diyana che ta shafe ni, “ya Allah ya kawo muku mafita ƴa’ƴana, har suna haɗa baki wajen chewa ameen bappa, basu gama rufe baki ba aka ba paɗo ɗakin babu ko sallama wata mata che baka mai ƙaton hanchi, damkoh wuyar hiyana ta jata zuwa tsakar gd ta hau bugu matar nan tsaka nin ta da Allah take bugun hiyana, ta ko ina ihu hiyana keyi tana faɗin “dan Allah inna kiyi hakuri, “au kinsan da hakuri ke nan koh har buba zaku jiƙa da ruwa kuma ku zage’shi koh to wlh yau sai kun yabawa aya zakin ta, komawa ɗakin tayi ta damkoh diyana da gudu Amrat tayi bayan bappa ta buye, inna kuwa jan diyana tayi har tsakar gd ta ɗaukoh wani itache ta hau bugun hiyana da diyana dashi bugun su take sosai duk inda ta samu take sauke musu itachen, tun kukan su na iya fita har sautin kukan ya daina fita,duka sosai inna tamusu sai da ta faffashe musu jiki, san nan ta kyalesu takoma gefe kan wani dutse ta zauna tana mai da numfashi, su kuma suka dun kule waje ɗaya suna kuka, sai da inna ta gama hutawa san nan ta ɗago ta dube su tafara magana, “ke hiyana ko kina so ko baki so buba zaki aura dan kin samu ma zai rufa miki asiri, kuma kutashi tun da kun fusata buba ya fasa buket ɗin ɗiban ruwan to da kofi zaku koma ɗiban, wlh kutashi ku ɗauki kofi kutafi kufara ɗiba min ruwa yanzun nan, ku chika komai na gd san nan ku chika durum na dabbobin nan,kutashi tun ban zo na karai’raya kuba ta karisa maganar chikin tsawa, da kyar suka miƙe har suna tangal tangal suka sufi wani ɗan ki chin suka ɗaukoh kofi kowache ta ɗauki cup 1 suka fito suna kuka suka nufi waje

    Bappa na zaune chikin ɗaki yana hawaye Amrat ta fito daga buyan datayi a bayan sa tafara goge masa hawayen tana faɗin bappa ka daina kuka kaji, rungume ta bappa yayi yachigaba ga kwalla

    Su hiyana kuwa han yan rafin suka nufa suna rike da kofin suna kuka, “chikin kuka hiyana tace yanzu diyana bakin ga irin abun danake faɗamiki ba, kullun ina faɗamiki komai buba zai mana muyi hakuri dan in mu kache zamu biye masa wlh mu zamu sha wahala komai kan mu zai dawo amma ke bakiji,bansan wani irin kai ne dake ba “share kwallan fiskar ta diyana tayi tana faɗin yanzu hiyana haka zamu chigaba da rayuwa ni gaskiya bazan iya jure wa ba, yazamuyi mu ɗebo ruwa da kofi kuma a che mu chika abuba dake gida da ruwa har dana dabbobi nidai bazan iyaba “to duk bake kika jaba da zaki che bazaki iyaba kin nafa sane da kyar bappa yasamu yaje chikin birni ya sawo mana buket ɗin nan, yanzu gashi kinsa buba ya fasa bappa kuma ba takawa yake ba yanzu bare ya sawo mana wani ai dole ma mu ɗebo ruwa da kofin tun da dai kin san inna in tayi magana ba wan da ya isa yasa ta chanza, shiru diyana tayi bata sake chewa komai ba harsuka kai bakin rafin suka ɗebo ruwa a kofin suka juyo suka kama hanyar gd
    *DUK ƘARFIN IZZATA*

    _💖Story And Written💖_

  • Duk karfin Izzata Book 1 Page 6

    Duk karfin Izzata Book 1 Page 6

    💫STAR LADY💫*

    https://chat.whatsapp.com/Cx1u7E8LUUX1XY8pJeHfMO

    *DUK ƘARFIN

    💖Story And Written💖
    ⬇️
    *Star Lady*

    Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

     

    *

     

    Pls more like comments and share

    *DUK ƘARFIN IZZATA*

    _💖Story And Written💖_
    ⬇️
    *Star Lady*

    💖The talent troupe writer’s 💖

    Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

    *
    ⬇️
    *Mrs BMB*

    💫New team 💫
    ⬇️
    💖The talent troupe writer’s 💖

    Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

    *

    *

    *DUK ƘARFIN IZZATA*

    _💖Story And Written💖_
    ⬇️
    *Star Lady*

     

    💖 The talent troupe writer’s 💖

    Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

    * ⬇️
    *Star Lady*

     

    Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawa

     

    *Episode 6*

    Malam Audu yace na..bai karisa ba sakamakon wasu If gudu Shahram da Abdol suka fito suka fara buɗe kofar motochin sai da suka bi kowani mota suka buɗe kofar san nan,suka dawo jikin motar su DON suka tsaya, a nitse Ammi ta sako kafarta waje kafin ta fito gaba ɗaya,sanye take chikin wata ɗankareriyar yace pink colour ɗinkin bubu wuyar ta da hannun ta sanye yake da ta sanya musu wani ɗankareren gold mai matikar kyau da tsada wani bakin al’khabba, mai shegen kyau an masa kwalliya da duwasu fari masu kyalli ta sa a kanta a mai makon mayafi bakaramin kyau tayiba inka ganta kache bata wuche 25 years ba a hankali kamar bata son taka kasa tanufi hanyar gidan su hiyana tazo dai dai zata shiga gidan sai kuma ta tsaya ta juyo tana kallon su malam liman, chikin ladabi ta gaida malam liman san nan tace “malam taron me akene haka, murya na rawa malam liman yace aure zamu ɗaura, to Allah yaba da zaman lfy ta kai karshen maganar tana shigewa chikin gidan tana tunani a ranta yanzu Ahmad zai kara Aure ne ko yasanar dani, zan haɗu dashine wlh, da sallama a bakinta tashigo chikin gidan nanfa kallo yadawo kanta gaba ɗaya matan dake chikin gidan suka zuba mata ido “sannun ku dan Allah ina habiba Ammi ta tambaya tana kallon fuskokin’su
    inna na daga gefe a ɗan tsorace tamike tana fadin “gani nan lfy wacece ke,gyra tsayuwa Ammi tayi tace “Aisha che yar Ahmadu, baki inna tabuɗe “laaaa indo keche a lallai kinzo a sa’a yau ake bikin ɗiyar taki hiyana,daure fuska Ammi tayi tafara magana “hiyana kuma Ahmadu hauka yakene da zai aurad da hiyana yanzu kwata kwata nawa au shine naga jama’a a kofar gida, to bazai yuba wlh baza’a aurad da yarinyar nan nan zuba ina Ahmadu yake yazo ya mai da musu da sadakinsu dan wlh baza’a ae wan nan Aure ba Hons ni tafiya ma nazoyi dasu gaba ɗaya yaran, chikin tsawa inna tace “ke Indo kishiga hankalinki wlh banga uban daya isa ya hana a ɗaura Aure’n nan ba, Ammi chikin ta kai chi maganganun da Inna tamata ta kalli Inna daga sama har kasa kafin tafara magana “ke habiba ko Ahmadu bazai tsaya yana faɗamin magana ba amma yanzu zan nuna miki na isa bama a kan ƴa’ƴan Ahmadu kawai na isaba har, a kan shi Ahmadu da kansa ke, bintu fita waje kiche da Safras wan nan umarni’ne su watsa jama’a nan su dakatar da ɗaurin Auren nan,ta karisa maganar chikin fushi tana kallon kuyangun daƙe gefenta, da gudu bintu ta juya tanufi waje dan ta isar da sakon Ammi, wani tsalle Inna tayi ta damko wuyar rigar Ammi tana faɗin “lallai Indo kin manta wacece ni ke nan wlh kibar ganin kinyi Aure a birni yanzun nan sai namiki mugun duka, chikin fushi Ammi tace “habiba ki sakarmin wuyar riga habiba “Indo bazan sakiba wlh yau sai namiki mugun duka a gidan nan dan kin shiga abun da bariwan’ki, da gudu kuyangar dake gefen Ammi tafita waje dan ganin abun da Inna ke kokarin yi, hannu Ammi tasa tana kokarin chire hannun Inna daga wuyar rigar ta,

    Kamar daga sama aka ɗauke Inna dawani gigitatcen mari wadda yasata faɗuwa kasa bashiri, da sauri Ammi ta ɗago tana kallonsa tsaye yake idon san nan ta sauya tayi jaa jijiyoyin kansa duk sun miƙe gaba ɗaya fuskar sa ta sauya sai wani huchi yake,kamar wani maƴinwachin zaki gadan gadan ya tin kari Inna dake baje a kasa tana ihu, da gudu matan dake gidan kowace ta kama kanta mace ɗaya che ya rage zaune bata gudu ba gudu ba, wani bugu ya kaiwa Inna a wuya nan taƙe numfashinta ya ɗauke hannu yasake ɗagawa a zuchiye zai kara kai mata wani bugun, da sauri Ammi tache “a’a Fahad ya isa tayi maganar tana karisa wajen da Fahad ke tsaye ganin Fahad na kokarin karawa inna bugune yasa Ammi tayi saurin shiga tsakanin su tana faɗin ya isa haka Fahad ka kyaleta, “Ammi pls ki kyaleni na bugu matar nan kina gani fa wuyar rigan ki ta riƙe wai ma wacece ita ? yayi maganar chikin matsanan chiyar ɓachin rai “aa Fahad ka kyaleta haka nan baka ganin ta sumane matar kawun ku che “Ammi idan matar kawun mu che sae ta riƙe miki wuyar riga “ya isa Fahad jike ka kiramin su Safras kaji a zuchiye ya juya yafita sai huchiyake,
    Juyowa Ammi tai tana kokarin taɓa inna karaf idon ta ya sauka kan su diyana dake tsai tsaye a bakin kofar dakinsu sunyi chirkoh chirkoh da sauri Ammi tafasa taɓa Inna tanufi wajensu tana faɗin “ina Ahmadu hiyana jin an amba chi ina Bappa yasa ta fashe da kuka, turus Ammi ta tsaya murya na rawa tache “hiyana me kikewa kuka Ahmadu nache kuka hiyana tache “Bappa yarasu satin daya wuche
    Nan take Ammi tayanke jiki zata fadi da gudu hiyana tai kanta tana kokarin tareta dai dai lokachin su DON suka shigo da sauri DON ya karaso yasa hannu shima yana kokarin rikoh Ammi har karo sukai da hiyana bai ma bi ta kantaba ya rungumo Ammi ajikinsa yana kiran su nan ta da sauri su Fahad dukayi kansa suna kiran Ammi, Ammi
    ganin haka yasa hiyana tai baya

    Chikin tsawa Fahad ya ɗago ya kallo su hiyana yafara “meyasa Ammi waya mata wani abun, yanzu nafita na barta lfy lau,
    murya na rawa Hiyana tache “ta tambayeni Bappa ne shine nafaɗa mata ya rasu shine zata faɗi..bata karasaba maganar ba, ya daka mata tsawa ya isheni haka shiru hiyana tayi jikinta sai kerma yake
    DON kuwa kwantar da Ammi yayi a kan tabarman dake wajen yaɗago ya dubi su Fahad dake tsaye a kansa “kai kubani ruwa kafin DON yakai karshen maganar ma, Fahad ya nufi waje chikin mota yashiga ya dauko ruwan faro da sauri yadawo chikin gidan ya mikawa DON Aryan dake duƙe kusa da DON ya karbi ruwan ya bude ya tarfa a hannunsa ya shafawa Ammi a fuska, wani dogon numfashi taja tare da sauke nauyayyar ajiyar zuchiya sai kuma tamike zubur kamar wadda akawa allura tana faɗin “ina bahaka bane kunne nane bai jimin dai dai ba DON ya matso yarike ta a nitse yache “Ammi meke faruwane lfy “ba lfy ba dan naji kamar hiyana na faɗamin wai Ahmadu na yarasu “kiyi hakuri Ammi kinji ya karisa maganar tare da sakin ta, juyowa Ammi tayi tana kallansu hiyana ta musu alama da hannu akan suzo, ba musu suka miƙe sukanufi inda take gaba ɗayan su suka zauna kusa da ita
    Ganin Ammi ta dawo chikin hayya chinta sosai yasa Mikewa DON miƙe yanufi waje, Fahad da Aryan suka rufa masa baya

    Riko hannun hiyana Ammi tayi tafara Magana “yaushe Ahmadu ya rasu, chikin shesshekar kuka hiyana tache “juma’ar data wuce juma’ar data wuche Ammi ta mai mai ta da mamaki to amma “shine kuma ko sadakar 7 ba’ayiba za’ayi taran biki saboda me ? Hiyana zatayi magana Diyana tai saurin chewa “duk shirin inna che hakan ban gane duk shirin Inna ba che Ammi ta tambaya tana kallan fiskar diyana, sai yamzu matar dake zaune awajen tun dazun wadda kowa ya watse yabarta tafara magana, tashiga bawa Ammi lbr duk abun da yake faru,duk irin a’zabbatar da Inna ke wa su hiyana, Ammi sai hawaye take wani na bin wani chikin muryan kuka tafara magana “duk laifin Ahmadu ne ba yarda banyi da shiba akan yadawo kano kusa dani yaki wai bazai bar garin iyaye da kakanniba, bayadda na iya dole na kyalesa na sai waya mai kyai na bashi dan murinka gai sawa da juna amma yaki ansa wai baya so yanzu har Ahmadu ya kamu, da chiwo akafa ya daina takawa duk ban saniba, innalillahi wainna ilaihir rajiun gaskiya rashin zumunchi bai yiba wlh nima ina da laifi duk dachewa ba zaman kaina nakeba a kar’kashin wani nake, amma yakamata ko wani ne inrinka ai kowa yana dubamin shi yanzu me amfani haka shekara 7 rabona da dan uwana wanda shi kadai yaragemin aduniya yanzuma babu shi wayyo ni Aisha gaskiya auren nesa Auren gidan sarauta bai yiba mutun ba zaifita yaje yasada zumunchiba hakadai, Allah sarki bayin Allah marayun Alla tayi magana tana shafa kan amrat da kyar ta miƙe ta dubi hiyana tache “ina zuwa ku jirani tana kaiwa nan tanufi waje

    Kai tsaye wajen motarsu tanufa jakarta ta ɗauka ta chiro wayar ta ta danna kira takara wayan a kunne kana takoma daga gefe chan ta tsaya tana magana Almost 30mnt tana waya bayan ta gamane tazo tasamu su Doyn achikin motarsu tace “kai kujuya motochin zamu koma ta kai karshe maganar tana juyawa, batare da tajira amsar su ba ta nufi chikin gidan su hiyana
    In data barsu awajen tasamesu “kutashi mutafi abun datache dasu ke nan ba musu kuma basu tambayeta ina zasujeba dan ita hiyana tasan Ammi yar Bappan,sune su diyana ne basu san taba mikewa sukayi jiki ba kwari, Ammi takama hannu amrat sukayi gaba su hiyana sukabi bayanta sukabar inna abaje a kasa
    Suna fita suka samu an juya kan motochin kai tsaye motar ta tanufa, buɗe motar tayi san nan tache da su hiyana “kushiga bamusu suka shiga ita kuma ta juya tanufi motarsu DON
    DON naganin Ammi tsaye jikin marfin motan da kansa ya buɗe mata motar tashiga ta zauna kusa dashi
    Har anwa motochin key zasu tafi Ammi tache su tsaya bayan sun tsayane tache wa sojan da zai tukasu yashiga gidan su hiyana yakira mata maman bello, da sauri sojan yafita yanufi chikin gidan bajimawa yafito maman bello na biye dashi a baya har suka isa wajen motar
    Ammi ta kalli DON dake zaune yanata latsa wayarsa hankalinsa ma ba akansu yakeba “kai idan akoi kuɗi ajikinka bani shiru ya ɗanyi kamar mai tunani sai kuma yasa hannnu ya buɗe wani dan karamin waje dake manne da jikin kujerar baya na motar ya zaro rapa rapan 1k Kowani rapa kuwa zai kai 100k rapa uku yamikawa Ammi, ansa tayi ta sauke glass ɗin motar ta mikawa innar bello ta ɗora da chewa “kibawa bello rapa 2 ke kuma ki ɗauki 1, innar belli ta washe baki sai zuba godiya take, Ammi batache da ita komai ba sai ma ɗaga glass ɗin motar datayi ta bada umarnin sutafi da sauri suka tada motochin suka bar kauye kai tsaye Airport suka nufa.

    Innar bello kuwa ta juya ta koma chikin gidan su hiyana ta ɗebo ruwa ta zubawa inna a fuska, a’razane inna tafarka tana faɗin zanga uban da zai hana auren nan idan an isa ache menake, innar bello tache “to ni dai natafi sai anjima tajuya tayi fichewarta, inna kuwa tafara waige waige taga bakowa a gidan duk sun watse mikewa tai ko mayafi babu tayi waje kai tsaye gidansu buba tanufa

    Zaune suke dukkansu a tsakar gida har da bello inna tashigo ko sallama babu nan tasamesu ga buba sai faman ihu yake yana fadin aradun Allah bazan barsuba nine zanzama ajalin hiyana indai baayi auren nanba to aradu saina mata asiri ta mutu saina mata sanda
    Inna tache meyasamishi
    Inna larai maman buba tache mutanen dasuka zo din nanne dasukache kowa yawatse bazaa daura aurenba shine shi buban yache basu isaba sai wani daga chikinsu ya daga buban yabugashi da kasa kana ya kama kafarsa ya karya
    ” karaya tayi maganar tana zaro ido
    Inna larai tache “karaya kuwa shine yanzu malam yatafi kiran mai dauri

    Mikewa inna tayi tana faɗin “zomuyi magana tana tana kai karshen maganar tashige ɗakin innar buba, inna larai tatashi tabi bayanta tana shiga inna habiba tache “kinji meyake faruwa koh kuma kinsan idan yaran nan basu mutuba a dokar kauyen nan ban isa intaba koda kafar kazane a chikin dukiyarsu bakoh
    Inna larai tache kwarai kuwa yanzu me abunyi
    Inna tache wajen malamin chan na bayan dutse zamu sake komawa mana yasan yadda zaiyi ya kashemanasu a chan ko dai a haukata manasu komaidai me ma amusu dan wlh bazan barsuba
    Inna larai tache to kina da kudine ” Inna tache zannemo ai zuwa nan da sati mai zuwa sai muje
    Inna larai tache yauwa kiyi kokari dan allah
    To kawai inna tache mata kana tafito daga dakin tayi waje

    Kano ta dabo

    Aunty amarya zaune take a gefen gadanta ita da hajj sadeeya
    “sadiya yanzu tafiya Enugu ya kamaki dan bazan taba barin wani yayi mulkiba idan ba danaba
    Sadiya tache gaskiyakam amma bayanzu zanjeba sai wata mai kamawa dan kuwa wlh inada tafiya dayawa a gabana
    Aunty amarya tache wata daya baiyi nisaba kinfasan bayan sallah za’a dorasa a mulki nikuma danaga wan nan rana gwanda namutu
    Sadiya tache karki damu ai da dan sauran lokachifa abunda idan najema sha yanzu magani yanzu zaamin dankuwa a wajen zansa gagara ba dau ya kashe Safras din kowama yahuta
    Aunty amarya ya tache amma sadiya bansan bakida kwakwalwaba sai yanzu kifadamin idan muka kashesa muna da gadansane kina ganinfa yafi kowa kudi a gidan nan ai bakashesa zamuyiba sawa zamuyi gagara badau ya chusa mashi sun yar wajenki kinga dayafara san zulaihat shike nan insunyi aure sai sun haihu sai mukashesa inmun kashesa kinga a lokachin muke da gado
    Washe baki sadiya tafarayi tana fadin ashe kinasona har haka bansaniba wayyo allah tayi maganar tana kokarin rungumar aunty amarya
    Aunty amarya tache inasanki mana sosaima ai fin hakama yanzu dai kiyimana kokari akan afasa bashi sauratan nan daga nan kuma sai muzo muyi aikin zulaihat da murna hajiya sadiya tamike tana fadin to shike nan ai dolenema ayi aikin nan da gaggawa yanzu dai kawo kudi zanwuche
    Wani akwati aunty amarya ta bude ta zaro rapa rapan yan dari biyar biyar 300k tamukawa hajiya sadiya tache inbasu isaba saiki min magana sai nakaro
    Karba sadiya tai tanafadin saikinjini kana tafiche daga dakin tai waje
    Aunty amarya kuwa kwanchiya tai tana fadin ai dukkanku sai nayi maganinku wlh shima yusuf din ba kyalesa zanyiba aiyana da kudi sosai shima dan haka yarinyar hajiya binta zansa gagara badau ya hadasu dan mukwashe kudin dukka haka dai aunty amarya tai ta surutanta har barchi ya daukesu

    Aban garen su Ammi kuwa suna barin kauye airport suka nufa nan suka hau jirginsu sai kano
    Suna isa kowa yanufi part Ammi ma ta kama hannun amrat tache su hiyana su biyota part nata suka nufa suna shiga Ammi ta kira zahra a waya tache tazo tasameta a dakinta san nan tachewa su hiyana su zauna
    Zama sukayi a kasa Ammi tache aa kutashi ku zauna a kujera bamusu suka tashi suka koma kan kujerar Ammi tache amrat tazo ta zauna kusa da ita ba musu amrat taje ta zauna kusa da ita su diyana kam sai kalle kalle ake
    Da sallama zahra tashigo da gudu tatafi tafada jikin Ammi tana fadin harkundawo
    Ammi tache tashi ajiki nikam mutun ne sai shegen san jiki ” turo baki zahra tayi tache kai Ammi to niba yar auta bache Ammi tache duk bawan nan yasa nakirakiba
    Kibani hankalinki da kyau kinutsu ki saurareni wayan nan dakike gani yayan kawunkine damukaje wajensa a yola sai yanzu zahra ta dago ido tana kallonsu dan shigowarta bata lura da mutane awajenba
    Tache laaa Ammi kingasu kyawawa dasu wlh wanchan tana kama da yaya prince sosai
    “kinga zahra bansan shirme ki saurari abun da zanfada miki yanzu a gidan nan zasu zauna
    Zahra tabuga tsalle tache wayyo allah dadi Ammi dan allah kusasu a school namu danna na nunawa freinds dina su tunda suna da kyau sosai Ammi dai baki sake take kallan zahra mikewa zahra tai takoma kusa da Hiyana tamika mata hannu wai suyi musabaha
    Bamusu hiyana ta mikamata nata hannu zahra ta kama hannunnata sukayi husabaha tache sunana zahra kefa ” hiyana chikin gurbatatchen hausarta tache nikuma sunana Hiyana ” zahra ta mai mai ta sunar Hiyana tache nice name kekumafa tayi maganar tana mikawa diyana hannu
    Itama diyanar hannu tabata suka gaisa tache nikuma sunana diyana zahra tache hiyana an diyana wow su nan yayi to dayanfa tayi maganar tana nuna lamrat ” diyana tache sunata lamrat zahra tajuyo da kallanta kan amra dake kusa da ammi da sauri tamike takoma kusa da Ammi tana fadin kai kaga yar india a naija gata karama da ita ga kyau kamar me to amma itakuma wlh da yaya haidar take kama amma tafishi kyau gaskiya
    Ammi dai yau taga ikon allah wajen zahra mutunne sai kaudin tsiya tache zahra’u zakizo kizauna kiji abun da zanfada mikine kodai sai na batamiki rai
    Sai lokachinma zahra tatuna ashe magana ammi kemata komawa tai wajen zamanta ta zauna
    Ammi tachigaba da chewa yanzu dake da hiyana da diyana dakinku ɗaya ammi zata sake magana taji Zahra na fadin eyeeeee wayyo dadi Ammi ta daka mata tsawa zaki tsaya ki saurarenine ko saina saba miki shiru zahra tayi tanitsu
    Ammi tachigaba dachewa lamrat da amrat dakinsu daban dakin dake kusa da nakin nan shine nasu yanzu abun danakeso dake kitashi kuje dakin ki suyi wanka kibasu kayanki susa san nan suyiwa su amrat ma wanka zansa a kawomusu kaya tunda su naki yamusu yawa kuyi sauri dan inasan muje wajen mai martaba mikewa zahra tayi da sauri tache kuzo muje wani dan korrido suka shiga san nan suka dan tafi kadan sai suka shiga dakin zahra
    Nanfa zahra ta nunamusu toilet hiyana ne tafara shiga saikuma tafito tache aunty zahra bansan yazanyi amfani da abubuwan chikin toilet din ba ” zahra tache dukkansu su biyota san nan tamike tanufi chikin toilet din nanfa tafara nunamusu yadda zasuyi amfani da abubawan dayake suna da kwakwalwa sosai nan take suka gane zahra ta nunawa hiyana towel dake makale awajen tache tayi amfani dasu san nan taja hannun amrat sukayi waje
    Diyana da lamrat ma sukabi bayansu ” hiyana kuma tafara kokarin chirekaya danyin wankar
    Suna fitowa Zahra tafara kokarin fiddo musu kayan hadaddun dogayen riguna abayas tafitar musu masu kyau ta ajiye a kan gado san nan taje ta daukoh musu plat shoe masu kyau
    Hiyana nafitowa wanka diyana tashiga nanfa zahra tache saitawa hiyana make up hiyana bata hanataba
    Zahra tafara yimata make up mai kyan gaske bayan ta gamane tachewa hiyana ta dubi kanta a mirrow
    zubur hiyana tamike lokachin data ga kanta taba fuskarta tashiga yi tana fadin anya aunty zahra niche kuwa kodai chanzamin fuska kikayi
    Zahra tache aa hiyana kedai zauna bari nabaki kaya aike din kyakkyawa gaskene kyankine kawai aini simple make up ma namiki dan na lurama make up din rage maki kyau zaiyi shiyasa banmiki dayawaba
    Doguwar riga sky blue zahra ta dauko daga kan gadan tamikawa hiyana hiyana ta karba zatasa ” zahra tache to aibakisa bra ba
    Hiyana tache me kuma bre ” zahra tache breziya mana
    Hiyana tache bansanshiba zahra tache to kina nufin baki taba sawaba kai to aiyakamata kirinka sawa bari na daukoh miki nawa
    Lokachin da zahra ta daukoh bra ta mikawa hiyana damamaki hiyana ke kallan bra din tache to aunty zahra aina akesa wan nan kuma taya zansashi
    Zahra batasan sanda dariya ya kubche mataba saida tayi dariya sosai san nan tashiga yiwa hiyana bayani akan bra
    Hiyana nagane menene bra nantake taji kunya yakamata tayi kasa da kai zahra tache aa karmufara haka dake nidakefa kinganmu kamar yan biyu shekarunmu ma ƙila dayane dan haka karkisake chewa zakiji kunyata juya na daura miki bra
    Hiyana tache nifa shekaruna 15 zuhara tache kai shekara 15 kuma shine breast naki sukayi girma haka kinfini komaifa nikuma shekarata 16 amma kingani kam bawani auki tako ina
    Hiyana dai shiru tai bata sake magana ba har zahra tagama taimaka mata tasa kayan Zahra tache yabaki wanke kanki ba ingani
    Chirewa hiyana dankwalin kanta zahra tai a rude tache kai inna lillahi kinga gashinki har baya wayyo dama niche amma yanaga kannakima ba datti
    Hiyana tache jiya anwankemin kai din ai zahra tache mamanku hiyana tache aa makwanchiyar mu che innan bello ta wankemin mukam bamuda mama da baba duk sun rasu
    Zaro ido waje zahra tayi tache allah sarki sannu kinji allah yajikansu da rahma
    Hiyana ta amsa da ameen
    Ribons da mayuka masu kanshi na gashi zahra ta daukoh tazo tafara gyarawa hiyana gashin kannata da kyar ta tara gashin nata ta daure mata a tsakiyar kanta zuba mata gelar gashin tabaya wadda yakai har kan boos din ta san nan zahra ta daukoh mayafin rigar ta mikamata kana tasamata manya manyan dankunne masu raun sai kyalli suke
    Diyanama tana fitowa zahra ta dau yimata kwalliya saidata gyarasu tsab san nan tache ita zatayiwa amra wanka dan daga yau amrat yar tache
    Kama hannun amrat zahra tai sukashiga toilet tamata wanka san nan tache lamra tazo tayi wanka da kanta
    Sungama shiri tsab Ammi ta kawowa su lamtar blaus mai shegen kyau black colour
    Zahra ta karba tasamusu bakaramin kyau sukayiba
    A palo suka samu Ammi ” Ammi ita da kanta ta tsorata daganin kyan da sukayi dan sunhadu tache to kuzo muje palan mai martaba dan mukadai ake jira sukache to zahra ta kama hannun amrat Ammi kuma tarike lamrat sukayi gaba su Hiyana na binsu abaya
    Da sallama suka shiga palan gaba daya mutanen gidan suna palan har da mai martaba ma yana zaune shiru wajen babu mai magana kowa da abun dayake sunajin sallama suka dago kai amma banda Don Aryan Fahad Yusuf Aiman duk sauran su dago suna kallan Ammi
    Wuchewa Ammi tai ta zauna kusa da mai martaba zahra kuwa taja hannunsu sukaje suka zauna kusa da aunty farida ” kasa kasa aunty farida tachewa diyana tazo kusa da ita ta zauna mikewa diyana tai ta koma kusa da aunty faridan ta zauna
    Mai martaba yayi gyaran murya saida kowa yadago kai amma banda wayan nan jarumai guda 5 din sudai har yanzu suna duke da kai suna daddan na wayoyinsu
    Mai martaba ya nuna amrat da hannu yache tashi kizo mikewa tai tanufi wajensa gyra zama yayi san nan ya dorata a gefensa ta zauna yana shafa kanta yache yasu nanki
    Shiru amrat tayi bata amsaba mai martaba yasake mai mai ta mata tambayar
    Sai sukaji diyana tanachewa chikin gurba tatchen hausarta tache itakam batajin hausa mune kawai mukeji
    Dukka palan saida sukayi dariya banda Don, Aryan,Aiman,Fahad,Yusuf ”
    Khalid ne yache to kema kina ganin kinajin hausake nan
    Ummi tache yata rabu dasu hai ai kinyi kokarima dakika iya wan nan hausar abunda ba yarenkaba kuma katasowa kayi a inda ake magana da yarenba kuma a haka har kika iya fadin hakan ma ai masha allah
    Zahrane ta matso kusa da diyana tafara mata magana da fullanchi dayake zahra najin fullachin sosai Ammi ta koya mata
    Magana take mata a kan idan mai martaba yana nagana baa magana har saiyagama wani mugun kallo umar ke wurgawa Zahra hakan yasa tayi shiru ta daina magana

    Mai martaba ya dubi diyana chikin harchen fullanchi wanda bai taba magana dashiba yache to yasu nanta ai basu aunty amarya kawaiba harda jarumai 5 saida suka dago suna kallon mai martaba hankalinsa kwanche yake fullanchinsa
    Ammi kam ko ajikinta dan tasan ita ta koyamasa fullanchi
    Chikin harche fullachin diyana tache su nanta amrat
    Mai martaba yafa ra bayani nan yafadawa yan gidan matsayinsu Hiyana yakara dachewa daga yau sunzama yayansa kuma a nan zasu zauna bayan yagama maganarne yache koh akoi mai magana
    Aunty farida tadanyi gyaran murya alamar tanada magana ” mai martaba yache to ina jinki
    Aunty farida tache dan allah Abba inasan abani wan nan natafi da ita ta zauna awajena tayi maganar tana nuna Diyana
    Mai martaba yache aa bazaki rabasuba ki kyakemin yayana anan babu inda zasuje

    Nantake aunty mardiyama ta hadiye maganarta jin amsar da mai martaba yabawa Aunty farida daman itama tanasan taroka abata lamrat amma jin Aunty farida da kanta an hanata yasa tai shiru

    Aunty amarya kuwa tunani tashigayi ta yadda zata bullowa al amarin dan wlh bazata taba yarda su Diyana su zauna a gidan nanba dan kuwa yaddasuke kyawawan nan karsu Safras sufara sansu domin Safras zulaihat kawai zai aura

    Mai martaba yache to kutashi kutafi Khalid kai kuma ranar monday kaje kamusu registration a makarantar su Zahra
    Khalid yache to da ɗai ɗai mazan suka fara fita daga palan

    Ummi ne tachewa Ammi yamukaji da hakuri
    Ammi tache hakuri yazama dole ” Ummi tache allah yajikansa Ameen Ammi tache san nan su Aunty farida ma kowa yafarayiwa Ammi taziya

    Amrat na zaune kusa da mai martaba suna ta hira dashi da harchen fullanchi
    Aunty amarya kuwa afusache tamike tafita daga palan kai tsaye part nata tanufa
    Tana shiga ta kira hajiya sadiya tache ke aiki yakarufa domin kuwa mai martaba yana neman rusa mana shiri
    Hajiya sadiya tache mekuma yafa ” Aunty amarya tache Aisha che taje kauyensu ta daukoh wasu yara wai yayan kaninta daya rasu to wlh idan kikaga yaran nan kamar susukayi kansu dan kyau gasu da diri da komai kuma biyu daga chikinsu yan matane,yanzu fargabana ɗaya a nan shine kar matasan gidan nan sufara sansufa
    hajjiya Sadiya tache wayache maki zasu fara sonsu
    Aunty amarya tache ke wlh koke kikaga yaran nan sai kinsosu saboda kyau ni tsoran danake jima karfa Safras da Aryan su fara son su idan hakan yafaru wlh angama dani
    Hajiya sadiya tache angama dakene kokuma angama dani nida har na fadawa zulaihat Safras zata aura yarinya sai murnatake ai yazama dole mutashi tsaye
    Aunty amarya tache to yanzu me abunyi
    Hajiya sadiya . tache aiki gagarabadau zai mana ya koresu daga gidan kokuma ya haukata mana su kowa yahuta
    Aunty amarya tache wlh hakan kawai za’ayi zankaramiki 500k achikin account naki yanzu ayi aiki mai karfifa wanda idan suntafi suntafi ke nan sufita daga rayuwar kowa sukoma rayuwa a bula
    Hajiya sadiya tayi dariya tache karki damu aikinsan aikin gagarabadau badaga nan ba kedai kawai kizuba ido watan nan nakarewa muka shiga wata zanje enugu
    Aunty amarya tache ai shiyasa nake sanki kawata sai munyi waya kekam anjima da daddare zan kiraki bata jira amsar Hajj sadiya ba ta katse kiran ta ajiye wayar a kan gado tanufi toilet

    Pls more comments an like
    *💫STAR LADY💫*

     

    *DUK ƘARFIN IZZATA*

    💖Story And Written💖

     

  • Duk karfin Izzata Book 1 Page 9

    Duk karfin Izzata Book 1 Page 9

    *💫STAR LADY💫*

     

    *DUK ƘARFIN IZZATA*

    💖Story And Written💖
    ⬇️
    *Star Lady*

    Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

    *Episode 9*

    Rike take da cup ɗin coffee datahaɗa masa tafiya take, itakanta batasan ina tanufaba dan bata san part nashiba tazo dai dai,zata fita bangaren Ammi tachi karo da Fahad ” baya taɗan koma kaɗan kana tache ina wuni yaya Fahad ” bai amsaba kuma bai ko kalletaba yazo yawucheta ” da sauri ta tache yaya Fahad dan allah inane bangaren yaya Aryan ” banza yayi da ita yayi wuchewarsa chiki yabarta tsaye ” tayi kwafa tana faɗin wlh dani kake zanyi maganin kane tajuya tachigaba da tafiya, sai sauri take kamar tasan inda zata

    kai tsaye palan mai martaba tanufa da sallam tashiga babu kowa awajen dan haka tanufi betroom kai tsaye sallama tayi a bakin kofar betroom ɗin tunba’a amsa sallamar kuma ba’abata izinin shigowaba tashige abunta ” zaune tasamu Mai martaba da Ummi a kan gado suna hira ” mamakine yakama Ummi ” Mai martaba kam bai damuba dan yasan halin diyana sosai ” Ummi che tache diyana lfy kika shigowa mutane ɗaki babu sallama ” turo baki diyana tayi tana faɗin dakin yaya Aryan nake nema, natambayi yaya Fahad yaki faɗamin ” Ummi zatayi magana, mai martaba yarigata dachewa ” idan kika fita nan kibi pangaren hannun damanki a nan part nasa yake ” to ai kofa biyu’ne awajen wanene nashi chewar diyana ” na biyun shine mashi mai martaba yabata amsa ” to kawai tache san nan tafiche abunta ” dawo da kallansa mai martaba yayi kan Ummi data sake baki take kallan ikon god ” ya akayine mai martaba yatambayeta ” hmmm su diyana manya mamakin tabani ne itakam ko ajikinta kawai tafaɗowa, mutane daki chewar Ummi ” murmushi kawai mai martaba yayi kana ya girgiza kai

    Tura kofar part ɗin tayi tashiga tana tafiya tana wakarta chikin harchen fullachi ” (fullo daru midarata fullo daru midarata) ” har tashiga palan babu kowa, dan haka sai tanufi kofar datagani a chikin palo kai tsaye tashiga babu ko sallama ” jin mutun yashigo yasashi ɗago kai yana kallanta tachikin mirrow, daure,yake da towel a kugunsa da alama wanka yafito, gawani gashi mai tsantsi bakinkirin a kwanche akan faffadar kirjin’sa, damtsen hannunsan nan kamar zai fashe saboda karfi,tamkar wani zaki, ga gashin kansan nan kuwa ajike, yake da’alama ya wanke kanne, gashin kwanche yake har kafaɗarsa, zuba mata wan nan ash eyes ɗin nashi yayi ” sai waige waige take da alama bata magansaba ” shiru ta tsaya kamar mai sauraron wani abu” “zuba mata ido yayi sosai yana kallanta ” sanye take chikin doguwar riga abaya still dai kanta babu ɗan kwali,” “juyawa tayi zata fita karaf idanta ya sauka chikin nashi ta chikin mirrow, tsabar tsorata, wani kara tayi kana tayi wurgi da cup ɗin coffee dake hannunta ta watsa aguje zata nufi waje amma ina, taku biyu yayi ya tamki kugunta ” saboda tsabar tsoro nunfashinta ɗaukewa yayi ” sai dai kawai yaji tasake jiki zata faɗi da sauri yariketa da kyau,

    Kallan fuskarta yayi yaga alamar kamar suma tayi, yasa hannu ɗaya ya ɗauke ta Chak sai kan makeken gadansa ya kwantar da ita ” san nan yakoma gaban miro yachigaba da abun dayake, bayan yagamane
    yanufi dressing run nashi, saida ya dauki kusan 10 mnt kafin yafito sanye da kayan barchi a jikinsa doguwar wando da riga mai dogon hannu masu laushi farare tas ” kai tsaye freij yanufa ya daukoh ruwa, yazo ya zauna a gefen gadan yabuɗe bakin rubar ruwar ya tarfa a hannunsa, ya shafa mata a’ fuska ” wani nauyayyar ajiyar zuchiya ta sauke haɗe da jan dogon numfashi,
    batare da tabuɗe idoba tafara sambatu ” don Allah kayi hakuri wlh bansan bakaya ajikinka bane nashigo kuma kaikache nazo dan allah karka bugeni ” ke kimin shiru chewar Aryan ” da sauri ta buɗe ido tana kallan inda take, mikewa tayi da sauri ta saukoh daga gadan tanufi hanyar fita ” kamar daga sama taji yana faɗin ” inazakije konache kitafine? ” Da sauri ta juyo tana in ina a’a ” to zo nan ki zauna yayi maganar yana nuna mata kasan carpet ɗin ” da sauri takoma ta zauna ” wayache kizubarmin da coffee ” ɗago kai tayi tana kallansa taga bama ita yake kalloba wayarsa yake latsawa ” kayi hakuri zankawo maka wani tabashi amsa ” kinsan meyasa nakiraki ” aa bansaniba ” wlh wan nan shine last worming na karshe da zanmiki idan kikasake yimana maganar wan nan shegen kauyen a gidan nan saina babballaki kinajina ” murya na rawa diyana tache eh naji ”

    kuma inasan kibuɗe kunne ki saurareni idan kika bari nasake ganinki babu ɗan kwali saina aske gashin nan gaba ɗaya ” da sauri diyana tache yauwa yaya dan allah ka askemin inka iya wlh banaso daman ” mamakine yakama Aryan tunani yashigayi idanfa yabiyewa yarinyar nan to tabbas zaiya babballata ” dan haka sai yache ke yanzu kitashi kije kikawomin wani cofee ɗin san nan kuma kullum dasafe karfe 7 dai dai kikawomin coffee haka da daddarema karfe 9 dai dai shima inabutar coffee idan kika kuskura kika wuche time dana baki,sai jikinki yafaɗa miki kuma banche wani yahaɗa , coffee ɗin ba kezaki rinƙa hadawa kinaji, tashi kije kikawomin wani yanzun nan yayi maganar a kausashe ” da sauri tamike tanufi kofar fita har takai bakin kofa kuma saita juyo tana faɗin yaya Aryan to yabatun askin zaka askemin gashin ” wani mugun kallo ya wurga mata waddayasata fita a’ aguje ”

    gyara konchiyarsa yayi a kan gadan yana kokarin ɗaukar wayarsa saiyaji kira tashigo, saida wayar takusa katsewa tukun nan yayi picking call ɗin ” hello akache daga ɗayan bangaren ” ykk hisham chewar Aryan ” lfy y gd, wai meyasa innakiraku Aryan baku san daukar call na chewar hisham ” Aryan yache au kakirane ka tambaya, to ra’ayi yanzuma kayi sa’a ne dan inachikin farinchiki badan hakaba bazan daukaba ” haka zakachemin koh Aryan to waima menamukune ” kara daure fuska Aryan yayi kamar hisham na kallansa yache kaga hisham mufa duk wanda yahaɗa hanya da mace to bamatare, dashi dan yazama mai rauni, mukuma bamasan mai rauni kusa damu ” wani mahaukachin dariya hisham ya kwashe dashi yana faɗin inshaa allah Aryan kaine mutun na farkoh a chikinku dazai fara faɗawa soyayya kuma inshaa allah yadda kuka wahalar da soyayya itama saita wahalar,daku, wahalarma ba.. “Aryan baijira hisham yakare jawabansaba yakatse kiran yayi wurgi dawayar gefe ” dai dai lokachin diyana ta dawo hannunta ɗauke da cup ɗin coffee bakinta dauke da sallama ” wani mugun kallo ya wurga mata a kausashe yache get out ” da sauri tajuya dan yadda taga fuskarsan nan kamar wani zaki ” kichin tanufa ta ajiye coffee ɗin a kan table san nan tafito kai tsaye sashen Ammi tanufa abunta ,

    Tana shiga tayi ɗakinsu tasamu su zahra har sunyi barchi hayewa saman gadan itama tayi ta kwanta abunta bajimawa barchi ya dauketa

    Washe gari misalin karfe 7 sungama shirinsu chikin uniform naso sunyi kyau sosai abunsu
    Diyana sarkin aiki dachikawa bata daure gashin gantaba tasa hijabi, wutsiyar gashin yalekoh sosai saboda gashin,yafi hijabin,tsawo

    Kai tsaye palan mai martaba suka nufa dan yin breakfast da sallama suka shiga ” kowa nagidan yana zaune kan table suna breakfast ” mai martaba dakansa ya amsa musu sallamar yana faɗin wow yan matana kunyi kyau gaskiya ” Ummi da Ammi ma sai murmushi suke suna yaba kyansu auntu amarya ko sai harararsu take ” yusuf kuwa chewa yayi kai sweet sis yanzunema asalin kamanninki da don kekara bayyana ” asukane don ya ɗago kai yana kallan yusuf ” yusuf baimasan yanayiba saima karachewa yayi ammafa kinfi don kyau gaskiya, domin kuwa blue eyes yafi green eyes kyau ”

    a,fusache don yamike yayi yana faɗin zama danake inachin abinchi,dakuma yafara kawo raini, kana yadawo da kallansa kan Ummi yana faɗin daga yau arinka kaimin, abinchi na bangarena, dagahaka yayi waje ” murmushi kawai Mai martaba keyi yana girgiza’kai kana yadubi su diyana dake tsaye, to tsayuwar me kuke kuzo kuzauna kuchi abinchi kutafi karkuyi latti ” wuchewa sukayi suka zauna kan kujerun table din ” bintu sufara sarving nasu, nantake sukafara chin abinchin ”

    ke banache karfe 7 dai dai kirinka kawomin coffee ba yayi maganar kansa na duke yana danna waya kamar bashike maganarba ” chikin sanyayyiyar murya diyana, tafara magana, kayi hakuri yaya Aryan wlh nayi tunanin kafasane dan naga jiya kache nafita maka a ɗaki ” mai martaba dai baki buɗe yake kallan wan nan ikon allah, Ammi da Ummi ma ba abarsu a’bayaba kowa na falon, mamakine yakamasa ” Aunty amarya kuwa bakinchikine kamar zai kasheta tanasan magana tana tsoron mai martaba ” Khalid kam sai murmushi yake abuns, ” basu gama mamakinba sukajiyo , . muryansa yana faɗin to kitashi kikawomin yanzu ” bamusu tamike tanufi hanyar fita ” shikuma yadago kai kome zai kalla karaf suka haɗa ido da yusuf daya buga tagumi ya tsaresa da ido ” harara ya watsawa yusuf kafin nan yamike shima yafiche daga palan ” wani mugun dariya yusuf ya kwashe dashi yana tafa hannu ” Aryan najiyo dariyar Yusuf amma bai tsayaba kuma bakaramin haushi hakan tabashiba haryasa yajima yatsani coffee ɗin, baima san sake kallan yarinyar ”

    Aiman ne yamike yabi bayan Aryan ɗin batare dayache komaiba ” Ahmad naganin Aiman yamike yafita shima yabi bayansa ” Khalid kuwa kallan yusuf yayi kasa kasa yache baka kyautaba kuma ina da magana dakai anjima kasameni a daki ” to kawai yusuf ya amsa dashi ” mikewa Khalid ma yayi yafita daga palan”

    Dawo da kallansa kansu hiyana Yusuf yayi yana faɗin kuyi saurifa time na tafiya yau nizanma kaiku da kaina ” tsabar mamaki zahra batama san lokachin da tache wai anya yaya yusuf ne wan nan kuwa ” sai dataga yana wurga mata mugun kallo tukun nan ta dawo kan hanya ” a’gurguje suke chin abinchin dan kar time yakure ” suna gama chin abin suka mike yusuf yace muje koh san nan yayi gaba, sukabi bayansa

    Su hiyana na fita mai martaba yadubi su haidar yache kubamu waje zamuyi magana ” da sauri suka mike sukayi waje, palan ya rage daga Aunty amarya Ammi dakuma Ummi sai mai martaba ”
    calmly mai martaba yafara magana alhadulillah alhadulillah wan nan rana nake jira arayuwata a’che yau Aryan da Safra da Aiman, naga sunfara yiwa wata yamace magana to yau burina yafara chika, nasan yusuf Ahmad Khalid su masu saukin kaine, to maganar danakesan nayi ana shine kar wanda ya kuskura a chikinku yayiwa yaran nan, wata magana dan da alama addua ta a kan Aryan tafara karɓuwa , ” Ammi tache ranka yadaɗe ban fahimche kaba ” zaki fahimta amma bayanzuba mai martaba yabata amsa ” mikewa aunty amarya tayi a fusache tabar palan ” binta da ido kawai mai martaba yayi achikin zuchiyarsa kuma yana faɗin nasan zaayi hakan ai amma sai dai kinmakara dankuwa baki isa kihana abun da allah yahukunta ba, a’fili kuwa chewa yayi zaku iya tafiya ” mikewa Ammi da Ummi sukayi suka nufi waje.

    Da sallama diyana tashiga palan nashi baya nan kai tsaye chikin betroom din tawuche “da sallama tashiga ” zaune yake kan kujera yana aikin chikin laptop ” gabansa tazo ta duka kana tache gashi nan yaya Aryan ” a’fusache yache bana bukata ” mikewa tayi tafita da coffee ɗin a hannunta ta maida kichin abinta,san nan tafito tanufi harabar gidan, tsaye tasamu su hiyana suna jiranta tana zuwa suka shiga mota kamar yadda suka saba, da gudun gaske motochin suka fito daga gidan, dan yusuf ne yache suyi gudu sosai su diyana zasuyi latti,

    Karfe 10 na’safe

    Zaune suke suna fuskantar juna akan sofa Khalid ne yafara magana gaskiya yusuf baka kyautaba meyasa zakayiwa Aryan dariya haka kasanfa abun da muke buri ke nan muga Aryan da don yau sunkula wata ya mace,kuma kafi kowa sanin halinsufa, yanzu dariyar nan daka masa zai iyasawa wlh yakoma ruwa munfara farinchikin yafara dawowa kanhanya, kana’neman rusamana farinchikin, kuma gashi niɗin nan tun ranar da aka haifi Zahra nake mahaukachin santa amma na bar abun araina saboda’su don dan bansan wata matsala a tsakaninmu Aunty farida kawai na iya faɗawa yanzu ganin abun daya faru a palo ɗazun haryasa nafara ganina a matsayin angon zahra gashi yanzu kanane’man karusamin hakan gaskiya baka kyautaba wlh ”
    dogon nunfashi yusuf yaja san nan yache hakane yaya Khalid nasan nayi kuskure dankuwa nikaina burina naga sun chanza amma wlh abunne yabani dariya yanason abu, amma yana wani chicchijewa yananuna halin ko inkula ”
    Khalid yache yanzufa Aryan bazai taɓa fahimtar yanasan yarinyarba saboda shi baisan soyayyaba kuma inbanda aunty farida da iyayenmu mata kasan ba wata macen dayake magana da ita Koh, koh zahra datake kanwarmu bamaga da ita yake ba tunda kaga yayiwa yarinyar nan magana har yache takawo masa abu yachi wlh ba banzaba yana mahaukachin santa amma bazai gane hakanba yanzu , tunaninsa bazata taba bashi yana santaba kuma karkayi kuskure faɗa masa yana santama, kabari zuchiyarsa zata faɗamasa, dan inkache zaka faɗa masama hakan zaisa yadaina yiwa yarinyar magana, yakuma tsaneta ka kyalesa kawai ”
    ” murmushi Yusuf yayi kana yache tabbas zan haɗa masa tarko kuwa wanda zaisa yafaɗa son ta gadan gadan batare daya saniba ” hannu Khalid yamikawa Yusuf yana faɗin good idea idan kana bukatar taimakoh na a shirye nake ” darisukayi gaba ɗayansu suka tafa hannu san nan yusuf yamike yana faɗin saikajini zanzo na faɗamaka plant ɗin idan nagama shiryawa ” to kawai Khalid yache” sannan Yusuf yafiche daga ɗakin.

    Kuka take sosai kamar wata karamar yarinya tana waya ” wai inba gagarabadau ba bakisan wani malami bane kitausayamin sadiya wlh suna shirin kasheni idan Aryan yafara son yarinyar nan wlh yakasheni nashiga uku ” hajj sadiya tace kidaina faɗin hakan kiyi hakuri nan da 2 month ɗin kinji koma yafara sonta idan akamata aiki dole zai tsaneta karki damu pls kidaina kukan haka, toma wayache maki yana sonta ” sadiya inasan kisan wani abu Aryan fa ko Zahra datake kanwarsa bai taba mata maganaba amma yayiwa yarinyar nan magana kuma hardachewa tarinka kawomasa coffee kullum, ” karki damu nidai dan allah kidaina kukan nan zamuyi maganin abun ” tsagaita kukan aunty amarya tayi kana tace shike nan sadiya badamuwa zanjira amma dan allah amusu aimi mai karfi dan yanzuma kara tsanarsu nayi wlh ” karkidamu aminiyata kedai kizuba ido kawai chewar hajj sadiya ” to shike nan aunty amarya tafaɗa tare da katse kiran ta jefa wayan a kan gado ta zauna tabuga uban tagumi siraran hawaye nabin kunchinta

    Karfe 1 na rana

    Suna zaune awajen chin abinchi na school nasu sungama chin abinchi rana ” hiyana na karatun qur’ani, su zahra suna Assignment ɗin da akabasu ita da diyana amrat kuwa tana zaune kusa da wata budurwa sai lamrat dake gefe tana rike da littafin Husnul Muslim tana karantawa ” sunyi nisa chikin abun da suke saisukaji murya daga bayansu ” a tsorache Zahra tajuya a’zuchiyarta tana tunanin wai meyakawo jabir wajensu tana chikin tunani kwai sai taji yana faɗin ” ke zahra,u yaushe a’ kakawo wayan nan yan india wan kuma makarantar nan ” Zahra sarkin tsoro murya na rawa tace sun kai 2 month ” tsaki jabir yaja san nan yace, shine bakizo kinfaɗamin ba, amma gaskiya wanchan tamin itache sabuwar budurwata na wan nan shekarar yayi maganar yana nuna hiyana, ” to kawai Zahra tace, ” yasunanta jabir ya tambaya ” sunanta hiyana chewar zahra ”

    jinjina kai jabir yayi ya mai maita su nan hiyana san nan yace, hiyana tashi kizo muje muzagaye makarantar nan domin kowa yaga sabuwar budurwata dan karwani yache yanasonki, dan duk wanda yayi kuskure chewa yana sanki tofa saidai uwarsa ta haifi wani ” zaro ido hiyana tayi tana kallan jabir ba karya kyakkyawane sosai gashi dogo mai chikar halitta sai dai yayi kalar yan daba kuma kwata kwata bazaifi 22 years ba,”
    Zahra ne tace, hiyana kitashi kuje ” kallon zahra hiyana ke chike da mamakin abun da tache zatayi magana sai tajiyo ” diyana nafadin kai waye dazakawani che tazo tabika to babu inda zataje iskanchin banzan nan ” wani mahaukachin mari jabir ya sakarwa diyana san nan yace kishiga hankalinki wlh kinmachi albarkachi, naganku tare da gimbiya hiyana ne dabadan hakaba dakin karbi hukunchi kekuma yashi mutafi yayi maganar yana nuna hiyana ” da sauri hiyana tamike jiki na rawa tanufeshi ” juyawa yayi yayo gaba tabi bayansa

    Diyana kuwa sai kuka take tana faɗin allah ya isana waima Aunty zahra wanene wan nan ” wata buduwa dake zaune kusa da amrat ne yace, sunansa jabir ” ni ba sunansa nakesan jiba faria wanene shi nakesan sani chewar diyana ” Faria tace shima a school ɗin nan yake yana ss 2 yana takama da mahaifinsa mai kuɗin ne kuma mahaifiyarsa kuma tana da yan daba mahaifiyar tasa baturiyar England che, bata da mutunchi shiyasa yake abun da yaga dama ” to meyasa malamai basa masa hukunchi saiyarinka yin abun dayakeso a makaranta chewar diyana ” faria tace makarantarma na mahaifinsane kuma duk abun dayake so shi iyayen nasa sukeso ” shiru diyana tayi kamar bazata sake magana ba chan kuma tace wlh nine zan gyara masa zama ” baki buɗe Zahra da faria ke kallan diyana tachigaba dachewa badai hiyana yakesoba wlh zaigane shayi ruwane
    Ita dai zahra aikin gabanta tachigaba dayi dan ta lura diyanafa ba hankali garetaba

    Hiyana bata dawoba har suka koma class ” diyana tashiga damuwa sosai da sosai ” sai karfe 2:50 hiyana ta dawo lokachima har anbuga belt ɗin tashi school ” diyana naganinta tanufeta tarungumeta tana faɗin ina kukaje ” babu ko ina yawo kawai yayi tayi dani a chikin school ɗin chewar hiyana ” tsaki diyana taja san nan tace to muje ” jerawa sukayi tare suwa nufi inda da suke tsayuwa sujira mai ɗaukansu nan sukayita hirarsu ” har driver yazo ya daukesu kamar kullun motochi 2 kezuwa daukansu diyana hiyana da zahra mota ɗaya lamray da amrat motarsu daban
    Da gudun gaske motochin suka nufi gida dasu ,motochin na danno kai security su wangale musu katafaren gate ɗin kai tsaye parking space suka nufa suna parking drivers ɗin suka fito suka buɗe musu motar ” suma suka fito suka rirrike hannun juna sukayi suka nufi bangaren Ammi

    Suna shiga tun a palo diyana tafara chire hijabi tana faɗin alhadulillah yanzu zan rabu da hijabin nan haba ” harararta hiyana tayi kana tace, kekam wlh watarana sai aljanu sunshiga kankin nan mutunne bata san dan’kwalin ” kallon uku 10 diyana taiwa hiyanar san nan tace, to ina ruwanki ai aljanuma abokainane Zahra zatayi magana sukaji an daka musu tsawa, get out aguje sukayi ɗakinsu itakuma diyana saida tajuyo dan ganin wanene tana ganin don ne ta watsa da gudu itama dan, shikam batataba ganin alamar wasa a fuskarsaba ,

     

    Pls more comments an share 👌

    *💫STAR LADY💫*

     

    *DUK ƘARFIN IZZATA*

    💖Story And Written💖
    ⬇️

     

    *Star Lady*

    Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

     

    *Episode 11*

     

    Mai martabane zaune a fada shida Aryan, Ahmad Khalid da’kuma Yusuf a nitse mai martaba yafara magana ” Aryan meyasa zaka mari diyana kanajin faɗan danayiwa safras fa ranan akan marin dayayiwa hiyana shine kaikuma kasake marin diyana koh wai bakuda tausayine nikam eh ” calmly Aryan yasoma magana kayi hakuri Abba wlh tabatamin raine sosai shiyasa ” nasani Aryan nasan halin diyana itakuma haka allah yayita hakuri zakurinkayi da ita ban hanaku kumusu faɗaba amma kurinka ragewa kuma bai’kamata kuɗora hannunku a jikinsuba bakuganin yanayin’sune, yanzu kaje kadubi fuskar diyana da kyau kagani shattin yatsunkane kwanche akai to na’menene hakan gaskiya bansan hakan karna karaji kuma karna kara gani ” inshaa allah Abba zan kiyaye chewar Aryan ” Khalid yace Abba yabatun zakkan nanfa ” eh kuna barwa ai kukula da komai ” Ahmad yamike yana faɗin aa Abba su yaya Khalid dai nikamma bari naje na dubo Aiman ” harara Yusuf ya watsawa Ahmad yana faɗin zakasani ne ai dakai da Aiman ɗin gaba daya wlh munkusayin maganinku a gidan nan ” Ahmad dai bai sake maganaba yafiche abunsa

    Aryan yace Abba yabatun komawarmu England ne ” aikuda komawa kam to banacheba kabari ayi naɗin sarauta tukun nan sai inyi tunani akai chewar Abba ” mikewa Aryan yayi yana faɗin to shike nan Abba allah ya kaimu san nan yafiche daga fadan ” Khalid da Yusuf ma mikewa sukayi suka fito sunayiwa Abba sai anjima

    Gabaɗaya family sun haɗu a palo dan chin abinchin dare amma banda don, dakuma yan matan Ammi subasu zoba , ” mai marbata yace waishin ina yan’matana’ne mesukeyi basu fitoba, ko dai daga buɗa baki shike nan bazasuchi abinchin dareba” Ammi zatayi magana sai sukajiyo sallamar’su nanfa kallo yadawo kansu banda Aryan da fahad kowa na palon kallansu yake, ”

    diyana na sanye chikin dogon wando baki da rigansa zuwa guiwa pink colour still dai ba ɗan kwali a kanta ta zuba gashin nan har baya sai kwalli gashin yake nakinkirin dashi har tsakiyar bayanta, dan karamin bakin nan nata yasha janbaki pink ga blue eyes yasha kwalli ta gyara sagenta ga zarazaran gashim idanta, tasa high heel pink kalar rigarta

    ” hiyana ma dogon wando baki tasa sai riga sky blue zuwa guiwa ta ɗaure gashin Kanta, tayishi kamar donut ta yafa gyalen kayan akanta paki kalan wando dan bakin nan nata yasha ret janbaki tayi kyau sosai kamar kasacheta ga blue eyes yasha kwalli sai’yaƙara kyau sosai yana kyalli sajenta kwanche a gefen kumatun’ta gashin geranta kamar tayi caving tasa flat shoe sky blue kalar rigar

    Zahra ma dogon wando baki tasa sai riga yellow tayafa gyalen kayan akanta shima bakine ɗan karamin bakin tan nan tasanya masa janbaki pink colour tayi kyau sosai itama daman zahra kama take da don sosai wan nan dalilinsaya suka zama kamar tagwaye da hiyana sai dai banbanchin kwayar ido dan zahra idanta bakine kamar nawa

    Lamrat kuwa dogon riga baki tasa mai shegen kyau,
    Tasa flat shoe fari, tayi rolling ɗin karamin farin gyale a kanta Zahra tamata make up sosai kamar wata balarabiya tazama

    Amrat kuwa dogon wanto fari dasa sai yar farar t-shirt navy blue itama batasa ɗan kwaliba amma zahra tamata pakin na gashin a tsakiyar kanta tazuba jelar gashin a’ baya har tsakiyar bayanta booth navy blue tasa a kafarta

    Yusuf ne yache wow my baby zo ” gaba ɗaya kallo yadawo kan Yusuf, a’ sukane Aryan yaɗago yana kallan Yusuf ɗin shi ko ajikinsa kallan su diyana ma yake baisanma jama’a na kallansaba ” bin inda Yusuf ɗin ke kallo Aryan yayi ” “Aryan kasa kawar da kannasa yayi daga kallanta ?

    Karisawa wajen table ɗin sukayi sukayi kowa tasamu waje ta zauna lamrat zata zauna kusa da Ammi ” yusuf yache zo nan kizauna kusa dani my baby ” bamusu lamrat takoma kusa dashi ta zauna ” haidar da umar sai gulma suke kasa kasa ” Ammi da Ummi kam ko ajikinsu abinchinsu kawai sukechi ” Aunty amarya kuwa sai chika take tanata harararsu ” ɗaukoh fura ki damamin hiyana chewar mai marbata ” da sauri hiyana tamike tanufi kichin, kwarya ta ɗaukoh san nan ta daukoh fura, tanufi freig ta ɗauki ruba ɗaya na nono tajuya takoma palan mai martaba, da sallama tashigo palan ta dawo wajen zamanta ta zauna tafara dama furar

    Sai’hira suke jefi jefi mai marbata yache banso a che muntafi umrah nan mun barkuba amma makaranta basu baku hutuba ” Ammi ne tache sai suje hajji kawai kokuma subari sai wata shekarar ” mai martaba zaiyi magana ” Ummi tace Fahad tashi ka kaiwa yayanku abinchi ” da sauri Fahad yamike yana faɗin ina abinchin ” yana kichin Ummi tabashi amsa , ” fichewa yayi daga palan

    Bayan hiyana tagama dama furan tamikawa mai marbata ” karɓa yayi yana murmushi kana yace duk gidan nan hiyanata tafi kowa iya dama fura ” turo baki diyana tayi tana faɗin wlh nafita abun dama nina ko…. bata karisa maganaba sakamakon wani mugun kallan da Aryan yake wurga mata ” shiru tayi

    Mai martabane kuwa sai kallansu yake yana murmushi yana farinchikin burinsa yafara chika aishi haka yakeso kodama hararanne Aryan kewa diyana daɗi zaiji dan daga harara sai kallan mutunchi ” Ammi che ta katse masa tunani dache ranka ya daɗe sai da safe ” hararar wasa mai marbata ya wuga mata kana yace inada magana dake ” to kawai Ammi tache ” jin mai marbata yace. yana da magana da Ammi yasa kowa yatashi suka fiche

    Mai martaba yadubi Ammi yafara magana jiya Yusuf yasame damaganar akan Khalid da zahra, Khalid yafaɗawa Yusuf yanasan Zahra tun tana karama ina faɗamiki hakanne bawai dan kifaɗa mataba sai hakkinki a matsayin uwa da’kuma kisamata ido karkibari tawa Khalid kishiya, danni tun da Yusuf yafaɗamin nariga nabawa Khalid auren ta, kokina da wani abun faɗe ” ajiyar zuchiya Ammi tayi san nan tace, nikaina inakaunar Khalid nina renesa a hannuna yagirma babu halinsa da bansaniba bawani abun da zanche saidai inmusu fatan alkhairi kawai ” to masha allah Amma fa kinsan yau a ɗakin’ki nake amma kikechemin sai da safe koh ” murmushi Ammi tayi tana tace tubanake wlh nagajine a’zumin yau ɗin nan ya wahalar dani ” haryanzu dai lallanchinki bai raguba Aisha, to muje chiki namiki tausar koh ” mikewa Ammi tayi tana faɗin mujedai ninamaka ” dariya mai martaba yayi san nan yamike yabi bayanta sukayi chikin betroom

    Karfe 10 na dare

    Rike take da cup ɗin coffee tanufi bangaren Aryan jikinta sanye da kayan barchi riga da dogon wando pink colour still dai kanta babu ɗan kwali tafiya take tana kunkuni” ni wlh barchi nakeji nagaji saikayitaba mutun wahala dan mugunta ” da sallam tashigo palan baya palo kai tsaye ta wuche betroom ɗin ” kwanche yake akan makekiyar gadansa yana latsawaya jin shigowarta yasa ya ɗago kai yana kallanta ” sai turo baki take tana magana kasa kasa ” from head to toe ya karemata kallo san nan ya ɗauke kansa da sauri ” karisa shigowa chikin ɗakin tayi tazo gaban gadan ta duka san nan tace. Ina wuni yaya Aryan ” shiru yayi bai amsaba kuma bai motsaba ” itama shiru ta zauna har kusan 15 mnt, san nan tache yaya Aryan dan allah ka karɓi coffee ɗin mana wlh nagaji ” banzah Aryan yayi da ita kamar baiji metake faɗe ba shiru shiru baiyi maganaba ganin bai daniyar magana yasata tamike, tanufi indayake wai dan taga yayi barchine
    Aji cup ɗin coffee ɗin tayi akan dan karamin table ɗin dake tsakiyar ɗakin san nan tanufi kan gado hawa gadan tayi taga idansa a lunshe , ta turo baki tana faɗin shine dan mugunta kabarni ina duke kan guiwowina har kafata namin zafi kaikuma kayi barchinka koh, to banyafe… Bata karisa maganarba taga ya waro manya manya ash eyes ɗin nan nashi akan fuskarta ” a’sukwane ta juya tana kokarin sauka gadan wani damka yayiwa gashin kanta wandayasa tadawo baya tafaɗa kan kirjinsa ” kware baki tayi zatayi ihu yasa hannu yarufe mata baki ” kasa kasa yace kina buɗemin baki ina harbinki da bindiga meya hauwar dake gadona yayi maganar tare da chire hannunsa daga bakinta ” murya na rawa tace dan allah yaya aryan kayi hakuri kasakemin gashina wlh zafi yakemin ” banche karna sake ganinki ba ɗankwali ba eh ” kayi hakuri zanrinka sawa chewar diyana tayi maganar chikin muryar kuka ” harchikin ransa yaji voice nata na karshe kayi hakuri zanrinka sawa a hankali yazame hannunsa daga kannata, yana faɗin to tashinmin ajiki ” da sauri tamike tana faɗin to ga coffee ɗin ” mikewa yayi shima kana yace bazanshaba ki mayar kije kisa ɗankwali saiki kawomin ” a shagwabe tace ayya dan allah kayi hakuri kasha allah gobe zan daura dan kwalin kafin nakawoma wlh yanzu nagaji kuma barchi nakeji ” kallanta yayi from head to toe san nan yache nikam, kekam kinada hankali kuwa kinsan chiwon kanki kuwa ” turo baki diyana tayi tana faɗin mekuma nasakeyi ” wlh azim idan kikasake fitowa a haka batare da hijabi ko kayan arziki ajikinkiba allah zakiyabawa aya zakinta ” binjikinta tayi da kallo achikin zuchiyarta tana tunanin to me laifin kayan nan tayi nisa chikin tunani taji ya daka mata tsawa ” wai badake nake magana bane nache kifitamin a ɗaki koh, da sauri tajuya tabar ɗakin binta yayi da kallo har tafita
    san nan yamike yanufi inda ta ajiye coffee ɗin ya ɗauko cup ɗin yadawo gefen gadansa ya zauna yafara sha,

    Bangaren diyana kuwa tana fita bangaren Aryan kai tsaye part nasu tanufa da sallama tashigo palan, da sauri taja burki tana faɗin ya yaya Yusuf kaima bakayi barchiba ” murmushi yusuf yayi yana faɗin eh ina hira da baby’s nawane suna koyamin fillanchi ” karisawa indasuke diyana tayi tana faɗin kema amrat hardake yau bakiyi barchiba sai kije school kiyita barchi a class koh ” lamrat tace ainikam ma yanzu zanje na kwanta ” zama diyana tayi kusa da Yusuf zatayi magana ” Yusuf yace kuje ku kwanta dare yayi kunsan akoi tashin asuba ga zuwa school yayi maganar yana mikewa yanufi hanyar fita ” suma mikewa sukayi suka wuche ɗaki

    Karfe 4 dai dai na asuba gaba ɗayansu sun haɗu a palon mai martaba danyin sahur amma banda don abinchi sukechi chikin kwanchiyar hankali ” Ammi tache hiyana da Zahra kuchi abinchin nan dawuri ku’ɗauki na yayanku ku kaimasa zahra najin Ammi tache sukaiwa don abinchi tafasa kara sai da kowa na palan yaɗago yana kallanta ” lfy auta ta chewar Abba ” Zahra dai taki magana sai kukanta kawai take ” hiyana kam datariga da tasan me Zahra takewa kuka ko kallanta batayiba, su Ammi sunyi tambayar duniyar nan amma Zahra taki magana sai kuka take ” Aryan ne ya daka mata tsawa zakimana shirune kosaina babballaki a nan ” tsit tayi kamar ruwa yachita ”
    Aunty amarya ne tamike tana faɗin kai umar kaje ka dauki abinchin yayan naku ka kaimasa kuma daga yau kai zaka rinƙa kai masa abinchi tana kaiwa nan tafiche tana tunanin aranta ai bazan taɓa barin yaran nan surinƙa kusantar samarin gidan nanba daga yau har ranar da gagarabadau zai musu aiki ido zan samusu sosai da sosai ɗakinta tawuche ta haye gado babu ko sallah takama barchi

    Bangaren”su hiyana kuwa sunajin Aunty amarya tace umar yakai abinchin yayansu nantake suka fara murna sukamike a tare suna faɗin barimuje muyi sallah ” Ammi ta kalli hiyana chikin harchen fillanchi tace wani sallah kuma badai kina period ɗin kike sallah ba ” shiru hiyana tayi dan ita batama san idan a na period baa sallah ba ” ganin tayi shiru yasa Ammi ta dubi zahra tace kije ki koyamata abun daya dace tayi ” to kawai zahra ta amsa dashi san nan suka fiche

    Mikewa Yusuf yayi yana faɗin gaskiya lokachi yayi dazan koyi fullanchi nima haba yanagama faɗin haka yayi waje ” Khalid ma yace tab aiko nima dole naje Zahra ta koyamin irin wan nan wariya daake nunamana kana yamike shima yayi waje ” dogon tsaki aiman yaja san nan yamike yafiche ” shidai Aryan zaune yake ahiru yana latsawaya har saida yafarajin kiraye kirayen sallah yamike yanufi bangarensa ” Ammi da Ummi ma suka fiche sukayi nasu bangaren danyin sallah ” palan yarage fahad haidar da Abba ” Abba yace wai kunyi arwala’ne kunfasan su safras sunafitowa zamuwuche masallahchi ” mikewa haidar yayi yana faɗin aa baridai naje nayi ” fahad ko chewa yayi nikam nayi Abba” ok kawai mai martaba ya amsa dashi
    Shiru suka zauna har sauran matasan suka fito sukajera zuwa masallachi

    Aɓan garen inna kuwa da sallama tashiga gidan su buba zaune tasameshi a tsakar gida ” buba na ganin inna yafara murmushi yana faɗin inna jamɓandu( inna ina wuni) ” lfy buba ya kafar taka ” da sauki inna” inna tache to allah yakara lfy ina innarka take ” tana garke tanabawa shanu ruwa da abinchi buba yabata amsa ” to barina dubota bata jira amsar buba tayi gaba abunta ” a garken shanun ta iskoh innar buba da sauri inna ta karisa wajenta tana faɗin albishir rinki yar uwa rabinjiki ” ɗago kai innar buba tayi tafara murmushi tana faɗin goro ” to kifito muje yau kuɗin sunchika dubu goma dai dai chewar inna ” da sauri innar buba ta ajiye sandar hannunta datake juyawa shanu ruwan gishiri tafito daga garken tana murmushi jerawa sukayi suka koma chikin gida innar buba ta ɗaukoh mayafi suka fiche

    Wani ƙungurmin daji suka shiga tafiya suke har suka isawajen wani dutse ga hayaki nafitowa daga chikin kogon dutsen chikin kogon sukashiga ” wani kasurgumin bakin bokane awajen ga idon san nan jajawur duk yabi ya huhhuda hanchi yasa wasu karafuna gawani katan karfe mai raun dayasa a kunnensa bashida kyan gani ko kaɗan
    Zama su inna sukayi kusa dashi ” zasu fara magana ke nan yayi wani mahaukachin dariya ha, ha, ha, da murya masa daɗin Ji yace aikin ku bazaiyuwu a chikin azumiba saboda duk an ɗaure mana mutanenmu amma kuje sai bayan sallah kudawo ha ha ha yana gama faɗan haka ya ɓache ɓat ” da sauri su inna suka mike suka fito inna tace to yanzu barinaje na ajiye kuɗin sai bayan sallah mudawo da haka suka kuche gida.

    Kamar kullum yauma zaune suke a wajen chin abinchinsu na makaranta karatu boko hiyana take yaukam tun da bata da tsarki ” zahra da diyana da faria kuwa hirar wani film suke waishi love story English movie
    Lamrat da amrat suna rubutu a takardunsu ”
    Kamar daga sama sukajiyo muryan jabir yana faɗin ke hiyana zo mutafi ” ɗogo kai hiyana tayi a nitse tafara magana kayi hakuri jabir wlh yau banida lfy ne chikina namin chiwo ” to yakikesan nayi ke nan ga abokaina chan kowa budurwarsa tazo ni bandani ke nan ba zaiyiwuba i don’t care koma meke damunki, nidai kitashi mutafi ” kamar hiyana zatayi kuka haka tamike tanufeshi tana faɗin muje ” kallan uku 10 diyana tawa jabir kasa kasa tache mugu wlh sainayi maganinka ” kallanta zahra tayi san nan taja guntun tsaki ” jabir tunda yakira hiyana suka tafi basu dawoba har saida a katashi nanma saida diyana da zahra sukaje wajen dayake zama da abokan nasa sukache hiyana tazo sutafi mai ɗaukansu yazo ” jabir dayaji haka sai yache to taje zasu haɗu gobe ” jerawa sukayi suka nufi wajen da suke tsayuwa sujira motochin dake ɗaukansu ”

    suna tsaye awajen sukaji magana daga bayansu ” gaba ɗayansu suka juya ” hiyana tace uncle Omar ina wuni ” da faraa a fuskanshi ya amsa san nan su Zahra suka gaidashi zaisake magana saiyaga motochin ɗaukansu yazo nanfa yamusu sallama yawuche ” sukuma suka shiga mota kamar yadda sukasaba hiyana Zahra diyana motarau ɗaya ” amrat da lamrat suma motarau ɗaya ” da gudun gaske motochin sukabar bakarantar” gudu suke sosai suna kan hanyane” zahra tace kinsanme hiyana ” girgiza’kai hiyana tai alamar aa ” uncle Omar fa wai san diyana yake chewar zahra ” kan uban chan niyakeso lallai kuwa yana ruwa wlh dannikam inba sojaba bazanyi aureba ” baki buɗe hiyana ke kallan diyana ” Zahra kuwa chewa tayi meyasa kikesan soja sojojifa mugayene ” eh ae a chikin sojanma mugun nakeso wanda zaiyimin maganin yaya Aryan kuma wanda yake da bindiga shima ” zahra tace to me yaya Aryan ɗin yayimaki haka dakike neman mugun soja yayi maki maganinsa ” to bashine kullun inna masa laifi saiyache zai ɗaukoh bindiga ya harbeni namutu kowa yahutaba ” aikuwa hiyana bata san sanda takwashe da dariyaba tana faɗin kai amma kuwa da yaya Aryan ya kyauta wlh ” Zahra kuwa chewa tayi dalla rabu da hiyana kinji faɗamin muguntar me yake miki ” bayan harbeni dayake chewa zaiyi saikuma jamin gashi da takuramin nasa ɗakwali dakuma kawo coffee kullun tayi maganar dai dai lokachin da motochinsu ke parking a parking space na chikin gida
    Fitowa sukayi suka nufi chikin gida rike da hannun juna

    Misalin karfe 4 na yamma gaba ɗaya yanmatan zaune suke a palon Ammi suna kallo hiyana kuma tana karawa lamrat karatun qur’ani gaba ɗayansu shiga iri ɗaya sukayi duguwar riga abaya dukkansu colour ɗaya baki ” Ammi ma nazaune a gefe tana gyarawa amrat jigidarta da Aunty farida ta saya musu to ya matseta sosai ” da sallama Khalid da yusuf suka shigo palan ” da gudu Zahra ta mike ta nufi Khalid,faɗawa kan kirjinsa tayi ta rungumesa sosai tana faɗin oyoyo yaya Khalid ” Yusuf ne yace my baby kema kizo kimin oyoyo mana ” da gudu lamrat ta mike tanufeshi hannu ya buɗe masa tafaɗa kirjinsa yana murmushi ” Ammi data tuno abun da mai martaba yafaɗa mata nachewar Khalid na san Zahra yasa da sauri tace ke zahra’u wai yaushe zaki girmane wlh idankika sake wan nan oyoyo zaki chi gidanku ” turo baki zahra tayi ” Khalid yasa hannu ya ɗan bugi bakin kana yace to wa’ake turowa bakin hannunta yarikoh suka koma kan kujera mai zaman mutun biyu

    Yusuf ma rikoh hannun lamrat yayi suka koma kan doguwar sofan suka zauna ” hannu Yusuf yasa yana shafa kan lamrat yana faɗin my baby gashinkin nan kyau yakemin sosaifa ” baki buɗe Khalid ke kallan Yusuf, azuchiyarsa kuwa chewa yake amma Yusuf iskanchinka yawuche tunani anya kaima baka kamu da san yarinyar nanba kuwa ” afili kuwa chewa yayi ai gashin Zahra yafi nakowa kyau ” harara Yusuf ya wurga masa san nan yace yauwa Ammi nikam inasan intambayeki kullum mantawa nake ” Ammi tace. Tanbayi inajinka ” wai aina mukasamu kalolin idon mun nan ne pls ” Ammi tace au kache tarihi kakeson ji to gyra zama ” murmushi kawai yusuf yayi yazubawa Ammi ido

    Kakanku wato mahaifiyar mai martaba itache asalin wanda takawowa family mu kalan idan nan kakanku namiji babban likitane aiki yakaishi Us, a chan yaje ya auro kakarku ta mace baturiyar Us, amma musulmache sunanta sarah to sarah itache mai ido light green irin naka kaida yayanku ” sarah kuwa mahaifiyar ta idonta ash ne mahaifintane mai light green ɗin ido shiyasa gaba ɗaya yayan sarah suka zama masu ido 2 colour wasu ash wasu green gashi abunkuma yabisu har kanku jikokinta, ” Khalid yace no wonder, shiyasa muke da kyau kamar yayan larabawa ashe ashe ” dariya Ammi tayi tana faɗin abun harda yabon kai ” Khalid zaiyi magana yusuf yache to ammi su hiyana fa ya akayi suka samu blue eyes

    Ammi tace sukuma sungadone daga wajen kakanmu namiji kuma duk family mu ma sukaɗai sukayi saar samun blue eyes ɗin kakanmu namiji shi ɗan asalin kasar sudanne yazo nageria, a garin jimeta yola, yahadu da kakamu mace yana santa sosai iyayenta sukache bazasu bashi itaba, sai dai idan zai zauna a rugarasu haka yayarda ya auri kakanmu kuma suka zauna a ruga harsuka haifi babana, da kanwarsa ɗaya allah yayiwa kakanmu rasuwa, kakanmu mace kuwa babana yayi auri umma’ta Kuma duk a’ruga ɗaya suke kuma a chan suka zauna an haifenima bajimawa kakanmu tarasu itama, kanwar babana kuwa bayan an haifi kanina Ahmadu babansu hiyana ke nan itama tarasu daga nan babanmu ya ƙaura daga rugar chikin yola yakoma rugar jimeta, a nan mukachigaba da rayuwa
    Rayuwar farinchiki muke sosai kanina da babana suje kiwo nikuma naje tallar nono a wajen tallar nono na haɗu da Mai martaba yabini har gida, da kyar babana yabasa aurena to na bayan aure ba jimawa innata tarasu, yarage saura baba da Ahmadu haka mukachi gaba da rayuwa bayardda mai martaba baiyi dasuba akan sudawo nan kano sunki har gida yasaya musu Amma sunki wai babu inda zasuje da waɗan nan uban shanaye babanmu yana da shanu dayawa kusan 700 ga awaki da raguna kaji da zabbi hakadai sukachigaba da zama a ruga
    Kolokachin dana haifi yayanku sunki zuwa mota mai martaba yatura a ɗauko su amma sunki zuwa, babana ko yaki zuwane saboda niche yar fari Ahmadu kuma yaki zuwane saboda shine mai zuwa kiwon dabbobinmu kai intakaichemuku har babanmu yarasu Ahmadu yayi aure basu taba zuwa wajena ba saidai ninaje
    Nidinma kunsan yanayin gidan nan sainafi shekara uku banjeba nanma saina matsa da kyar mai marbata yake barina, akoi lokachin dana ɗauki tsawon shekara 6 banje naduba Ahmadu ba a shakara ta 7 ɗinne nayita rokar mai martaba da kyar ya’yarda yabarni naje”
    Danajene masamu fati matar Ahmadu ta haifi ƴaƴa har uku hiyana diyana dakuma lamrat san nan ga chikin na hudu ajikinta nasha mamaki sosai shine nachewa Ahmadu tunda yanzu bamuda iyaye yadawo kano kusa dani yaki yarda, wai inyadawo yazaiyi da dabbobinsa, nachemasa musayar yaki yarda wai bazai bar garin iyaye da kakanniba haka na hakura na kyalesa nasaya’ waya nabashi amma yaki karɓa wai baiso bayadda na iya haka nadawo na kyalesa
    Sai danasake ɗaukan shekara 4 kafin nasake komawa kauye alokachin danaje nasamu mamansu hiyana tarasu wajen aihuwar amrat Ahmadu kuma ya auri habiba dan tachigaba da kulamasa da yara alokachinma saidana roki Ahmadu daya dawo kano amma yaki narokesa yabani hiyana da diyana nanma yaki ninasan halinsa da kafiya shine na kyalesa kuma tundaga wan nan lokachin dana dawo bansake zuwa kauyeba sai zuwan nan danayi na samu Ahmadu yarasu na daukoh su hiyana ” dogon numfashi yusuf yaja san nan yace. Tab lallai Ammi kina da hakuri sosai wlh allah dai yajikansu da rahma ” gaba ɗaya palon suka amsa da amin ” duba time yusuf yayi san nan yace. da Khalid muje koh mangariba ta kawo kai ” mikewa sukayi a tare yusuf narike da hannun lamrat sukayi wajen ” Ammi tace’wa su hiyana kutashi kuje kufara shirye shiryen kayan buɗa baki tare suma sukamike suka nufi palon kasa” Ammi ma tamike tayi ɗakinta

    Misalin karfe 7 na dare gaba ɗaya family suna palo dan yin buɗa baki amma banda don abinchi sukechi chikin kwanchiyar hankali shiru ba mai magana saidai karan spoon ” diyana tace. Abba kasan me ” sai dakowa yaɗago yana kallanta da mamaki ” mai martaba kuwa chewa yayi aa diyana ta bansaniba sai kinfaɗa ” dariya diyana tayi tace wai uncle Omar na makarantar mune yace yana sona ” what chewar mai marbata ” a’sukwane Aryan yaɗago manya manyan idan nan nanshi yana kallanta a jafafe yabuɗe baki…..✍️✍️

     

    Amin afuwa masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kaimu more love

     

    Pls more comments an share

    *💫STAR LADY💫*

     

    *DUK ƘARFIN IZZATA*

    💖Story And Written💖
    ⬇️

  • Duk karfin Izzata Book 1 Page 8

    Duk karfin Izzata Book 1 Page 8

    *Star Lady*

    Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

    *Episode 8*

    Tana dago kai suka haɗa ido da yusuf,” chikin kuka take faɗin dan allah hamma kayi haku…bata karisaba yadora hannunsa a kan lips nata yana faɗin to ya isahaka kiyi shiru bamai sake bugunki”
    “Zahra’kam Mutuwar zaune tayi tashiga duniyar tunani, wai shin daman yaya yusuf haka voice nashi yake, allah yasa dai bawani aljani bane yazo musu a siffar yaya yusuf
    Zahra, tayi nisa a chikin tunaninta kawai ” “saitaga yusuf yamike tsaye yana rike da hannun hiyana saida sukamike,” yache
    Yakamata kirinka banban’chemu ni sunana yaya yusuf, wanda yamareki jiya su nansa yaya prince kinji, ” cikin shesshekar kuka take faɗin to amma zan iyache muku hamma ,” Yusuf yache meyasa kikesan kirinka chemana hakan ”
    “ai kunada yawane idannache dukkanku yaya zanrinka chewa bazan ganeba, amma idan ina hadawa da hamma abun zanmin sauki ”
    “Murmushi yayi san nan yache to shike nan nikirin’kachemin hamman kinji ” to Kawai hiyana tache,” dawo da kallansa yayi kansu diyana, kutaso muje mana, ba musu suka saukoh daga kan gadan ”
    “Zahra ma saukowa tayi suka jera yusuf narike da hannun hiyana saida suka fito palon Ammi, batare da yasaki hannun hiyanaba, yasa ɗayan hannunsa ya kamo hannun lamrat yache ke yasu nanki ”
    “Dawani gurbatatchen hausarta tache lamrat,” jinjina kai yusuf yayi yana faɗin gaskiya lamrat yamin nisa awajen kira gashi su nan naku nada wahalar kira sosai dole na chanza muku suna ni bazan iya kiran sunan nan nakuba”
    “Shiru sukayi kawai suna jinsa, yanuna hiyana ke daga yau su nanki sweet sis, yanuna diyana kekuma little sis, yanuna lamrat kekuma baby yanuna amrat yache my little baby ,”
    “Zahra dai binsu kawai take dan ita duk tunaninta aljanine yazo a saffar yaya yusuf dan tun da take wlh bazatache, ga kalan voice na yaya yusuf ba, amma yau shine har da magana mai tsawo, kai to kodai umarnin mai martaba yabashine dan nasan mai martaba bazai tabarinsu hiyana a kunchiba

    Dasallama sukashiga palan mai martaba,” kowa yadago ya zubamusu ido amma banda don da tager Aryan”
    “Umar’ne ya taba haidar kasa kasa yake faɗin kai anya kuwa yaya yusuf ne, kadubafa har da rikemusu hannu,” haidar yaɗan kallai gefe da gefe yaga bamai kallansa kasa kasa shima yake magana kaidai kabari muje ɗaki mayi maganar, kar’ajimu amana hukunchi”
    “Yusuf kuwa yana shigowa palan ya ɗaure fuska kamar baitaɓa dariyaba sakin hannunsu yayi yakoma wajen zamansa ya zauna”
    “Mai martaba ne yadubi su diyana dake tsaitsaiye, kuzokuzauna yache dasu chikin harshen fullachi”
    “Diyana da lamrat da amrat sukazo suka zauna sukabar hiyana tsaye tana rakuɓe rakuɓe, dan ita harga allah kallan fuskar don tsoro yake bata, yanzu babban damuwarta ma kujera ɗayane yarage a table din kuma kusa dashi kujerar take, dankuwa kowa bayansan zama kusa dashi shiyasa mafi yawanchin lokuta kujerar kusa dashi zaka sameta babu kowa, yanzuma ita kawai tarage tunani hiyana tashigayi sosai tache to wai ina sauran kujerun ai kujerunma sunfi haka yawa, saboda jiya ai aunty farida da aunty mardiya suna nan kuma duk a nan mukachi abinchi dasu to yaukuma basu nan kuma table din yachika to ina sauran kujerun ke nan , tayi nisa chikin tunanani saitaji muryan mai martaba yanachewa
    Kai Safras jekatawomin da ita dan tsoranka yahanata zuwa, ” da sauri don yaɗago kai yana kallan mai martaba ” dauke fuska mai martaba yayi yache abun dagaji shinafaɗa dan idan bakaikamata maganaba bazata daina tsorankaba”
    “Nantake fuskar don ta sauya idansan nan suka chanza launi zuwa jaa sosai jijiyoyin kansa duk suka mike sai wani huchi yake kamar zaki,” kannensa naganin haka suka kama hansu, dagudu suka bar palan yarage daga Ammi Ummi Mai martaba Aryan Yusuf Fahad ” Khalid ma guduwa yayi dan yasan halin mutuminnasa Ida ransa yabachi” aunty amarya’ma ba abarta abayaba ta’tsere ” itama hiyana tana ganin sungudu tajuya itama tabisu”
    “Mikewa don yayi sai wani huchi yake yanufi hanyar fita,” da sauri Aryan ya taresa yana faɗin don bakada hankaline mai martaba nefa yake maka magana ” hannu don yasa ya ture aryan gefe guda yanufi hanyar fita haryazo tsakiyar palan ” aryan yasake taresa yana faɗin don kadawo chikin hayyachinka kasan mekake kokarin aikatawa kuwa” dunkule hannu don yayi yakaiwa Aryan bugu a Kirji ” Aryan bai bari bugun ta sauka ajikinsaba yasa hannu ya tare hannun don,” afusache don ya damki wuyar Aryan da ɗayan hannunsa yayi sama dashi kana yayi wurgi dashi gefe gida ” rai a ɓache Aryan yamike yayi kansa shima wani bugu yakaiwa don a bayan wuya ” da sauri don yajuya yasake tamkar wuyan Aryan ya shakesa sosai ” Aryan kuwa dayaji azaba sai dunkule hannu, ya kai don bugu a bayan kunne saiga jini ta hanchinsa,” afusache don yayi wurgi da Aryan kana yanufesa gadan gadan ya damki kafarsa yasake wurgi dashi gefe guda duk dahaka bai kyalesaba yasake yinkansa ” “da gudun gaske Ammi tasha gabansa tana faɗin nizaka fara kashewa ba dan uwankaba ”
    Mai martaba kam harde hannu yayi yana kallan Iko god ” yusuf ma bai damuba dan yasan indai irin wan nan faɗane sunsaba idan taɓachimusu ”
    Don saiwani huchi yake yache Ammi kibani hanya pls zuchiyata zafi takemin idan ban bugi Aryan’ba mutuwa zanyi ” rai abache Ammi ke magana kamutu kamutu nache Ammi bata karasa maganaba yayanke jiki yafaɗi kasa sumame ” Yusuf yamike yana faɗin alhamdulillah alhamdulillah tunda yasuma ai shike nan ”
    “Ummi che tayi kansa ita da Fahad da sauri ” Ammi kuwa juyawa tayi tabar palan tanufi bangarenta abinta ” mai martaba yamike da sauri yayi kansa yana faɗin, yusuf kukira sojojinsa a kaisa asibiti ” aa Abba basai ankaishi asibitiba idan yasamu barchi zai watsake karka damu kaje kawai kayi shirin zuwa fada dan anajiranka,kaga lokachi yatafi chewar yusuf ”
    juyawa mai martaba yayi yanufi ɗakinsa jiki ba kwari, yana ta tafiya ya tunanin ,anya ba aure zanwa yaran nanba ko nasami zuchiyar nan tasu ta ragu kai inganin hakan za’ayi nan da bayan sallah dole zanche kowan’nensu yafito da mata da wan nan tunanin yashige ɗakinsa

    Ummi to yanzu yazamuyi mukaisa daki daman Aryan ɗinne kawai mai ɗaukansa idan abunnasa ta motsa, to yau kuma yayiwa Aryan rauni yusuf baigama rufe bakiba ” “sukaga Aryan ya tattare dukkan karfinsa ya dauki don a kafaɗarsa yayi waje dashi ”
    “Ummi tache allah sarki allah yakara haɗamana kanku allah yakaramuku kaunarjuna ” ,jinjina kai yusuf yayi kafin yafuta ameen Ummi ai kulluma idan sukayi faɗa don ke bugun Aryan amma kuma Aryan ke taimakon don akoyaushe ” murmushi Ummi tayi san nan tamike tanufi nata bangaren ” yusuf yadawo da kallansa kan fahad dake tsaye to muje koh ” Fahad yajuya kawai yayi batare dayayi maganaba yanufi hanyar fita

    Su zahra kuwa suna zuwa ɗaki suka samu hiyana na kuka zahra tache hiyana meke damunki ” chikin kuka take faɗin aunty zahra kidubafa kigani nasan abaya ba haka akeyi a gidan nanba amma daga zuwanmu har anfara faɗa ” aa hiyana bawai saboda zuwanku bane ai ku zuwankuma alkhairi ne, bagashi kunfara chanzamana su ba kidubafa kiga yau yadda kukayi hira da yaya yusuf ,to wlh barikiji ni tundanake a duniyar nan bana’chemiki ga kalar voice na yaya yusuf ba saboda bakin halinsu, komaganama basayi amma a dalilinku yau yaya Yusuf yayi magana, san nan kuma ya amsamin gaisuwata aini wan nan rana tashiga chikin ranakun dazan ajiye a matsayin tarihi ” “sallama sukaji daga bayansu Ammi che ta shigo a gefen gadon tazauna tashiga rarrashinsu tana basu baki

    Abangaren aunty amarya kuwa tanashiga bangarenta wayarta ta ɗauka takira hajiya Sadiya bugu ɗaya hajiya Sadiya ta ɗauka
    Ko sallama babu kawai tasoma magana” sadiya inakike munshiga uku ” hajj sadiya tache meyafaru Kumar ”
    “Aibama abunda bai mafaruba chewar aunty amarya bana faɗamikiba yanzu gashi wlh yusuf da kanshi ɗazunɗin nan yaje har ɗakin Aisha, yakira yaran nan wai suzo muchi abinchi, kinga ke nan hankalin samari gidan yafara juyowa kansu yaran, tunda har yusuf da kansa duk zafin ransan nan ya saukoh yaje yakirasu wlh gobekuma, nasan sai aiman daga aiman sai Aryan da Safra shike nan idan hakan tafaru kuma munshaga uku
    Hajj. Sadiya tache aa hakan bazai faruba ki kwantar da hankaliki karki damu kinji nizanyi maganin komai ” to dan allah kiyi sauri kinji ” karki damu inshaa allah aikinki zaitafi yadda kikeso kuma saimunyi maganinsu chewar hajj. sadiya ” aunty amarya tache to shike nan sainajiki kana ta katse kiran ta zauna abakin gadon tana tunani

    Yau yakama Monday tun karfe 6 nasafe Khalid yazo bangaren Ammi, dan ya ɗauki su hiyana suje a musu registration a school ɗin su zahra, zama yayi a palan Ammi yana jiransu ” da’sallama sukashigo palan hiyana na sanye chikin riga da sket na kanti mai kyau ash colour rigar mai dogon hannu yaɗan kamata sai sket din daga sama ya ɗan kamata kasan kuma yabude sosai kayansu iri ɗaya da diyana, sai dai na diyana light green ne, sunsaka hijab da bazata wuchi guiwaba ,amrat da lamrat kuwa riga da wando sukasa rigar zuwa goiwa wandan koma dogo har kasa sky blue sun yafa karamin gyale ”
    “Zahra kuma nasanye chikin uniform nasu, riga da wando da dan karamin hijab rigar fara tas zuwa goiwa sai dogon wando navy da ɗan karamin hijabin da baiwuche kirjiba ”
    “Wow chewar Khalid gaskiyane my sister’s kunyi kyau sosai abunku to kuzo mutafi”
    “Ina kwana yaya inji hiyana” lfy lau yabata amsa”
    Ganin hiyana ta gaidashi yasa suma su diyana suka gaidashi ya amsa fuska a sake, san nan yache kuzo muje karmuyi latti kunga har 7:4 tayi ” gaba yayi sukabi bayansa” suna fitowa harabar gidan suka samu yusuf tsaye jikin mota, yana sanye da white jeans da ash T-shirt bakaramin kyau yayiba sai kanshi ke tashi daga jikinsa kamar anyi barin turare ha gashin kan nan yasa har kam kafaɗarsa ya sha gyara sai kyalli yake daman gashin bakine sosai ”
    Gaidashi suka farayi ” yana amsawa fuska a sake ” inazakaje yusuf Khalid yajefo masa tambaya ” rakaku zanyimana ” dariya Khalid yayi sosai kafin yache to yau kuma wasa kakejiyimin kenan ” daure fuska yusuf yayi yana faɗin wasa kuma to daman muna wasane, inzakazo mutafi kazo muta inkuma bazuwa zakaiba ni sai na daukesu muje namusu registration din ” da mamaki khalid ke kallansa kamar bazai tankasaba saikuma yache to muje ” mota 3 sukayi zahra hiyana diyana mota ɗaya suka shiga” Khalid lamrat amrat suka shiga mota ɗaya yusuf kuwa nashi motar yashiga ” sai wasu motochi 3 kuma dake binsu a’baya dauke da sojojin yusuf guda 9 kowani mota sojoji uku ” dagudu gaske motochi suka miki hanya harzuwa bakin gate nan take security suka gangalemusu katafaren gate ɗin suka dauki hanya gudu sosai suke shararawa chikin kankanin lokachi suka isa school ɗin ” sunayin parking sukafito kai tsaye office din principal suka nufa, nan danan batare da ɓata lokachiba suka gama komai kuma suka roki alfarman da akai diyana da hiyana primary 6 tun da sunyi girma amrat da lamrat kuma a kaisu primary 4 da kyar principal ya aminche nanfa suka mika masa amanar’su diyana san nan Khalid da yusuf suka fito sukabar su hiyana sukaje suka shiga moto chinsu suka juyo sai gida”

    “Kwanche tashi babu wuya awajen allah yau su diyana sunchika 1 month da dawowa kano sunchanza sosai kamar basuba sunyi kyau ga kiba dasukayi sunyi fresh dasu kamar yayan larabawa sunfara wayewa da gogewa ” bangaren karatu kuwa baa magana dan sun dage sosai ” sai dai a wan nan bangaren sunsamu banbanchi dan kuwa ita hiyana tafi maida hankali kan karatun islamiya musamman karatun qur’ani ” itakuma diyana tafi dagewa a pannin boko” amrat da lamrat kuwa dukka bangare biyun suna dagewa ”

    yauma kamar kullum sun dawo daga school misalin karfe 4 na yamma suna kwanche a ɗakinsu gaba ɗayansu suna hira ” diyana tamike tana faɗin natafi palo nayi kallo ” saikin dawo inji zahra ” fichewa diyana tai jikinta sanye da doguwar riga fari tas mai kyau amma jikin’rigar bawani kwalliya plen’ne kanta kuwa babu dan kwali ta zuba gashin nan har gadan baya sai sheki da kyalli yake kawar wata yar india ” zama tayi a palan abinta ta kunna kallo ta kamo tashar discovering tana kallan daji da abun dake chikinta ” daman diyana sarkin san kallone ” “tayi nisa chikin kallan datake batama ji shigowar mutunba ” sai dai kawai taji yana faɗin ke jeki kawomin coffee ” da sauri ta ɗago tana kallansa” murya na rawa tache ina wuni yaya Aryan ” bai amsaba kuma bai sake dagowaba” mikewa tayi jikinta har rawa yake ta saukoh kasa tanufi kichin ” coffee ta hada masa yadda taga bintu mai aiki kehadawa ta dora a kan plate san nan ta dauka takoma sama” yadda tabarsa haka tasamesa gabansa tazo ta duka tamika masa cup ɗin batare datayi maganaba ” shiru bai ansaba kuma shima baiyi maganaba har kusan 10 mnt tukun nan a shagwabe take magana ayya yaya nagaji wlh hannuna zafi yake kakarɓa mana pls ” da sauri yaɗago yana kallanta yadda take maganar hankalinta kwanche,sai daya ƙare mata kallo from head to toe , tukun nan yasa hannu a nitse ya karbi cup ɗin yana faɗin karnasake ganinki babu ɗan kwali ” “shiru tayi tana tunanin daman yana kallan mutanene basai mutun yazo yawuchesa sau darima bai ɗaga kai ya kallesaba tayi nitsa chikin tunani ” yadaka mata tsawar da sai’dayasa tamike, badake nakeba” murya narawa take maganar eh eh naji yanzu zanjema,na daukoh ” batare daya kalli,indatakeba to jiki daukoh kizo ” da sauri ta juya tanufi ɗakinsu

    A hankali ya kai cup ɗin coffee ɗin saitin bakinsa ya kurba da sauri yasauko da cup ɗin yadawo dashi saitin idansa yana kallan coffee ɗin,mamakine ya bayyana karara a kan fuskarsa sake kai cup ɗin bakinsa yayi yasake kurba ya lumshe ido,kana yabuɗe sosai yake shan coffee ɗin har takare batare daya saniba,shiru yayi yana tunanin wai bayache yarinyar nan tasa ɗan kwali yazoba,meyasa bata dawoba,ganin tunani babu abunda zaimasa,yasa yachiro wayarsa,yafara neman layin yusuf ringing wayar take amma ba’a ɗagaba har saida kiran takusa katsewa Yusuf,yaɗauki kiran a nitse yake magana yusuf kana da num ɗin zahra ne ” eh inadashi lfy faɗin yusuf ” eh lfy turomin yanzu ” ok inji yusuf ” katse kiran yayi ya ajiye wayar a gefensa saikuma wani tunani tafara shiga zuchiyar wai meya haɗani da itama to dazan’nemeta, wani bangare na zuchiyarsa ke bashi amsar dachewa saboda coffee mana,afili yake faɗin yes saboda coffee,wayar’sane tayi kara alamar shigowar sako yana dubaka,saiyaga num ɗin zahra yusuf ya tura masa

    kiran layin yafarayi ringing ɗaya zahra ta ɗaga ” chikin isa take magana wai wayene naga sabuwar number” “kamar daga sama taji muryan Aryan yana faɗin kichewa yarinyar nan tazo palo tasameni, ” saura kaɗan zahra tayi fitsari a wando saboda tsoro in ina tasomayi,ina ina inawuni yaya ” baijira yaji wata maganaba yakatse kiran ” aruɗe zahra ta dubi diyana,tache diyana ke kaɗai che kikafita ɗakin nan mekikaje kika aikata to kiyi sauri yaya Aryan na palo na jiranki ” murguɗa baki diyana tayi san nan tafara magana,mekuma zanyi niga iya coffee kawai yache nakawo mar kuma nakaimasa, sai ɗan kwali dayache na saka kuma basawa zanyiba ato irin zafin nan dake damuna, wlh ni gashinma yankesa zanyi da almakashi dan zafi yakesa naji ” Zahra dai a tsorache take, tafara magana kai dagaji muryar tama kasan a tsorache take kitashi to kije dawuri yana palo yana jiranki ” batare da’tasake maganaba tamike tayi waje tana murguɗa baki, yadda ta barshi haka ta dawo tasameshi da sallama a bakinta tashigo palan,” bai amsaba kuma bai ɗagoba ” gabansa tazo ta duka a sanyaye tayi magan gani nan ” bai tankataba kuma bai ɗagoba kusan 8 mnt ” dan allah yaya kayi magana mana wlh nagaji da dukawan nan kafofina sunnamin zafi chewar diyana ” kamar baiji me tafaɗaba yachigaba da daddanna wayarsa saida yakara kusan 10 mnt ” tukun nan, ya ajiye wayar a gefe bata re daya kalletaba yafara magana ina dan kwalin danache kisa ” shiru tayi batayi maganaba kana ta zuba masa ido tana kallansa ” dago manya manyan idan’sa yayi ya saukesu a kanta, saida ta tsorata ganin shikuma kalar idon nasa ash ne, ita tunda takema bata taba kallon idansuba dan basa dago kai ” tsawa yamata badake nake maganaba ” nantake tafara hawaye tana faɗin dan allah yaya kayi hakuri wlh akoi zufane idan mutun yasa ɗan kwali kuma.. ” Bata kai karshen maganarba yaɗaga mata hannu yana faɗin it’s ok waya haɗa miki coffee ɗazun ” nine dakaina na haɗa tabashi amsa ” ke da kanki yayi tambayat yana kawar da idonsa daga kallanta ” eh nina haɗa ” to tashi kije kiyi nill down a chan ” toni menamaka, a shagwabe tayi maganar ” mamakine yakamashi, ya mai mai ta maganar nata toni menamaka, nan take ya daure fukar nan kamar baitaba dariyaba, wani mugun kallo ya wurga mata wadda tasata mikewa ba shiri takoma tsakiyar palan tayi nill down,”
    Jingina kansa yayi a jikin sofar ya lumshe ido makar mai barchi, kusan 15mnt ya ɗauka a hakan kamar daga sama kuma yajiyo voice na Aiman yana faɗin wai daman nan kazo inata nemanka ” batare daya buɗe idoba yake faɗin, to mezaka bani ” yusuf dake tsaye a gefe guda ne yache mekuma diyana tamaka ” “sai’lokachi yaɗago kai azuchiyarsa yana mai mai ta sunan diyana kallon inda take yayi sai faman haɗa zufa take, ɗauke kansa yayi yamaida,kan su yusuf dake tsaye kusa dashi zaiyi magana ” yusuf yarigashi dachewa diyana tashi kitafi ɗaki ” ai tun Yusuf bai karisa maganaba tamike da gudu tana hawaye tayi ɗaki ” harara Aryan ya wurgawa yusuf kana yache me ruwanka da ita kai kabata punishment ne dazakache ta tashi ” “harara yusuf ma ya watsa masa kana yanufi sofar yana kokarinzama yanafaɗin kudai bakuji daɗin zuchiyarkuba wlh ko tausayin yaran nan bakuji kunafa sane da irin rayuwar dasukayi amma baku kyautawa wlh ” ” kallan banza Aiman yayiwa yusuf san nan yafara magana to kai tunda kanajin tausayinsu ba shike nanba, inaruwanka da zakache musai mungi tausayin nasu, to bamuji kuma bazamujiba ” kallan banza shima yusuf ke bin Aiman dashi kawai batare dayayi maganaba ” mikewa Aryan yayi yanufi hanyar fata daga palan batare dayayi maganaba ” kallo Aiman yabishi dashi har yafiche tukun nan ya dawo da kallansa kan yusuf yafara magana ” kamar wani abu nadamun tager fa ko yakagani ” eh naga alamar hakan achiwar yusuf ” to bari nabi bayansa dan naji me matsalar chewar Aiman ” adawo lfy inji yusuf ” Aiman bai amsaba yafito kaitsaye bangaren Aryan yanufa.

    Zaune take a gefen gadanta tana fuskantar hajj sadiya wasu abubuwa hajj sadiya tafitar daga jakanta guda uku tamika mata tana faɗin angama da batun sarauta, sauran batun wayan nan yaran da Aisha takawo, gagarabadau yachemin infaɗamiki aiki akansu bakaramin aiki bane sai munbashi lokachi dan da alama yaran akoi tsari ajikinsu saiyafara warware tsarin jikinsu,tukun nan zai iya yimasu wani aiki,” Aunty amarya ne tasoma magana to wayan nan yarakuma inasukaga wani tsari ajiki saboda allah dai ” hannu hajj sadiya tasa tarufewa Aunty amarya baki,tana faɗin ke wlh gagarabadau baya karya kuma kiyi a hankali dan daga nan zai iya jiyo mekike faɗi, batun yara kuma dakike magana duk fulanin nan dakike gani suna zaune a dajin nan chemiki akayi a banza haka kawai suke zaunene ai tun randa suka haifi ƴaƴansu, aranar suke farajijjikasu da magunguna ” “chere hannun hajj sadiya Aunty amarya tayi daga bakinta kana tache to shike nan yanzu wayan nan kayan dakika banifa ya za’ayi amfani dasu kuma nan da kwana nawa gagarabadau ɗin yache zaiyi aiki akansu ” eh munyi dashi akan zandawo nan da wata 2 chewar hajj sadiya ” zaro ido aunty amarya tayi tana faɗin wata biyu kuma zata sake magana komai tatuna sai tache to shike nan ba damuwa,yanzu dai waɗan nan abubuwa yazanyi dasu ” tona rami zakiyi ki binnesu da hannunki chewar hajj sadiya ” to shike nan gobe zanje ta bayan gidan nan na binnesu,sai maganar Safras da zulaihat chewar aunty amarya ” eh shima sai bayan sallah dan yache aikin nada matukar wahala kuma gashi sallah yakawo kai jamaa sunmasa yawa sosai kowache tana kawo kukanta asa mijinta tafito da ita sallan nan ta haɗu sosai, ” mikewa Aunty amarya tayi tana faɗin bari nakawomiki kuɗin motakoh tanufi wajen Waldrop din kayan’sawarta

    Misalin karfe 8 na dare gaba ɗaya family sun haɗu a palo suna chin abinchi kamar yadda suka saba ” shiru kakeji bakajin karar komai sai karar spoon, bayan sungama chin abinchin ne ” mai martaba yayi gyaran murya yasoma magana yau azumi saura kwana 33 yakamata kufara fitto da kayan abinchi kuna rabawa al umma san nan kuma gaba ɗayan mu zamuje umrah, saiku shirya, akoi mai magana ” shiru palan yayi ” diyana che tache Abba inasan da’sallah inje kauye ingano yaya bello ” wani kallan banza yusuf ya wurga mata akule yafara magana au yanzu duk azabar dakukasha sake tunanin kauyenma kuke ke nan ” mai martaba yayi murmushi yana faɗin to kai ina ruwanka kasan tsakaninsu da bello’ne to barikaji zasuje kuma kuzaku kaisu kukulamin dasu har sudawo ” afusache don yamike zaibar palan ” sai ina chewar Ammi ” shiru yayi baiyi maganaba kuma bai dawo ya zaunaba ” mai martaba yayi murmushi yache to ki kyalesamana jeka abinka ammafa kashirya dan dakai zaku kaisu diyana kauye ” batare dayache koh uppan ba yayi waje ” kallan Ammi mai martaba yayi chikin harchen fillanchi yake faɗin ki kyalesu inamusu hakane ko zansamu zuchiyar nan tasu taragu inba hakaba akoi matsala ” jinjina kai Ammi tayi tana faɗin eh hakanma yana da kyau ai gara murinka koyamusu sanyi kobayawane ” mikewa Aryan yayi yanufi waje har yakai bakin kofa saikuma yajuyo yana kallan diyana a nitse da sexy voice nashi nan yafara magana kisameni a ɗaki inzakizo kikawomin coffee yana kaiwa nan yawuche ” gaba ɗaya palan mamakine yakamasu baranma yusuf suda sukasan hali, “nan take zahra jikinta yafara rawa ta kalli diyana tafara magana kasa kasa chikin harchen fillanchi wayache kiche zakije kauye to wlh yau babu ruwana dan zaki karɓi hukunchi ” murguɗa baki diyana tai tamike tayi waje ” baki sake zahra ke kallanta azuchiyarta take tunanin lallai diyana inaga darabon zakisha bugu kilama harda karaya,”
    Da ɗai ɗai suka bar palan gaba ɗayansu kowa yanufi bangarensa

    Zaune take a gaban murhun wuta tana kokarin hurawa innar buba tashigo gidan da sallama inna ta amsa mata sallamar,tamata iso zama innar buba tazo tayi kusa da inna suka gaisa ” innar buba tafara tambayat inna wai har yanzu habiba baki samu kuɗin bane nifa wlh nafara karaya ” aa karkikaraya dan kuwa nasamu natara dubu 5 yanzu kuma anjima zansake zuwa tallah kinga da kuɗin sun kai dubu 10 sai muje koh kiɗan kara hakuri kinji chewar inna ” to badamuwa allah yakaimu nibari nazo nakoma gida dan mai dubawa buba kafarsa zaizo anjima chewar innan buba ” inna habiba tache yajikin nashi ” innar buba ta amsa da sauki sosai wlh dankuwa kafar tafara komawa dai dai ” mashaa allah chewar inna ” to habiba sai kinshigo tafaɗi hakan tana kokarin mikewa, har kofar gida inna habiba ta rakata san nan ta dawo

    Pls more comments and share

  • Duk karfin Izzata Book 1 Page 13

    Duk karfin Izzata Book 1 Page 13

    Episode 13*

    Tana ganin jabir ya ɗaga hannun zai mareta tafasa kara tafaɗi kasa tana birgima kamar mai aljanu ” bashiri jabir ya jabirki ya tsaya yana kallo ikon allah ” da sauri su hiyana sukayi kanta suna kiran sunanta ” chikin tsawa diyana ke magana ni basunana diyanaba ni sunana bilkisu, ha,ha,ha ta kwashe da dariya ” a tsorace Zahra ke faɗin munshiga uku yaukam me kuma yasamu diyana ” hiyana kam ko ajikinta dan tasan iskanchin diyana yawuche hakan ” chikin tsawa diyana tace kai jabir zo nan ai nafaɗamaka daman niche zanyi magananin’ka ” jabir najin haka ya kwasa aguje yabar wajen ” Zahra kam tagama tsorata baya baya tafara jaa tana salati ” hiyana lamrat amrat kuwa ko ajikinsu saboda sunsan halinta daman ” diyana naganin jabir ya gudu tamike tana faɗin nizakawa iskanchi wlh nafika iyawa muzuba mugani ae kai karamin ɗan iskane ” a sukwane Zahra tamike tana kallon ikon allah ” mekuma kuke kallona haka chewar diyana tayi maganar tana kokarin mikewa, bayan tamike tsaye ta dubi su hiyana tace sai kutashi mutafi class ae tun da ɗan iskan ya gudu,
    hanyar class nasu tanufa abunta tafiya take hankali kwanche, hartakai kusa da class nasu saikuma ta juyo yadda tabarsu haka tajuyo ta gansu ko motsi basuyiba Sun zuba mata ido ” murguɗa baki tayi kana tace kuchigaba dazama allah yasa yadawo yasameku nikam kunga shigana class tana gama faɗin haka tasa kai tawuche chikin class nasu abunta

    Hiyana ta mike taje ta dafa Zahra tafara magana Aunty Zahra naga kin tsorata to wlh indai diyana che kaɗanma kika gani dan wlh abun dayafi wan nan zata aikata ” dogon nunfashi zahra taja haɗe da sauke nauyayyar ajiyar zuchiya kana tace yanzu hiyana kina nufin kichemin ba aljanubane sukayi magana yanzu diyana che, kuma yanzu diyaya ita ta iya zama ta shirya wan nan wasan kwai kwayon ” shakka babu Aunty zahra duk abun da kika gani shiryashi diyana tayi ba gaskiya bane chewar hiyana ” shiru Zahra tayi tana tunanin itafa lamarin diyana yafara bata tsoro tayi nisa chikin tunani taji, lamrat ta taɓata tana faɗin Aunty Zahra muje dan idan kika biyewa Aunty diyana wlh yau bazaki shiga class ba jiki ba kwari Zahra tafara tafiya tana faɗin yanzu idan jabir yaganefa ” wan nankuma matsalarsu, che shida diyana tunda ita tamasa chewar hiyana ” lamrat kuwa chewa tayi wlh ninasan ko jabir yagane Aunty diyana zata nemawa kanta mafita ” ajiyar zuchiya Zahra ta sauke san nan tace to shike nan allah ya karemu gaba ɗaya tayi maganar tana kokarin shiga class nasu sai anjima sukawa juna hiyana ma tawuche nasu class ɗin suma su lamrat kowache tawuche class nasu

    Karfe 3 na rana anbuga bell na tashi gaba ɗaya ɗalibai sun fito suma su hiyana sun haɗe kansu suka nufi wajen dasuke tsayawa sunajiran drivers nasu, suna tsaye suna yar hirarsu sai ga faria ma da fara’a suka gaisa da hiyana dakuma diyana lamrat da amrat kuma suka gaisheta ta amsa da fara’a ” daga bayansu sukaji an daka musu tsawa, a na faɗin ke nizakiwa karyan aljanu koh to wlh yau sai kin gommace da’baki zo duniyar bama da sauri gaba ɗayansu suka juya ” diyana zatayi magana sukaji jiniyar motochin ɗaukansu ” hiyana na ganin motochin ɗaukar’su, batasan lokachin datache alhamdulliah ba ” Zahra kuwa tun motochin basu gama parking ba ta zura a guje tabuɗe kofar motar tashiga tana sauke ajiyar zuchiya ” lamrat da amrat ma motar’su suka nufa da sauri sukabar hiyana da diyana tsaye awajen ” jabir naganin motochin’su yaju yabar wajen yana faɗin zamu haɗu gobene wlh zakisani inna rikeki ” diyana naganin jabir ya tafi ta murguɗa baki tana faɗin kadaɗe baka dau matakiba wlh ɗan rainin wayyo zanyi maganinkane allah yakaimu goben kagani nidakai wazaiyi winner ” baki buɗe hiyana ke kallan diyana tana tunani a chikin zuchiyarta wai diyana kam bata da tsorone a rayuwarta ” tayi nisa chikin tunaninta tajiyo muryan diyana na faɗin to kekuma me yatsayar dake inbazaki zoba saimu tafi mubarki da jabir ɗin ” mamakine yakama hiyana wai yaushe diyana ta barwajen nan jiki ba kwari tanufi motar drivers ɗin na tsaye suna kallonsu sunasan tambayatsu lfy amma suna tsoro dan hakan bata shafi aikinsuba ” hiyana nashiga motar suma drivers ɗin suka koma chikin motar suka tayar da’ gudu sukabar makarantar.

    Yau kwana biyar ke nan datafiyar su mai martaba Umrah

    SAUDIA

    Misalin karfe 10 na dare Aryan Aiman yusuf Ahmad Khalid suna zaune a palon hotel ɗin da suka sauka hirasuke gaba ɗayansu ban da Aryan daya zauna shiru kamar bashi a ɗakin ” Khalid ne ya ɗan taba shi ” a ɗan firgiche ya ɗago ash eyes ɗin nan nasa yana kallan khalid ” lfy meke damun ka gaba ɗaya naga kamar mood naka ya chanza chewar Khalid ” iska mai zafi Aryan ya fuszar daga bakinsa kafin yasoma magana babu komai kawai inatunanin intashi inje induba prince ne naga wunin yau shiru banji motsinsaba ” satar kallan yusuf Khalid yayi san nan yace ok to kaje kadubashi mana ” mikewa Aryan yayi yanufi staircase ɗin ya haura sama ” murmushi Yusuf yayi yana kallan Khalid ” harara Aiman ke wugawa yusuf tare da faɗin me kuke kullawa ” shima Yusuf yadawo masa da harara yana faɗin mekuma zamu kulla ” tsaki Aiman yaja san nan yamike yana faɗin zakusani dai kubi a hankali dankuwa idan ta kwaɓe muku kunsan sauran ” kallan sama da kasa Khalid yawa Aiman san nan yaja tsaki yace. To kayi rashin sa’a nine babba ba kaine babba a kainaba dazaka tsaya kana faɗamin zanchen banza ni wuche kabani waje hai ” tsaki Aiman yaja san nan ya wuche yanufi staircase ɗin ” dawo da kallansa Khalid yayi kan Ahmad dake zaune ya zuba musu ido to kaima mekake jira dabaka’wuche kabi husainin nakaba ” dariya Ahmad yayi san nan yace gulma natsaya jimana ai yau munraba gari da husainin nawa dannikam sainaji gulmar ” Khalid bai sake maganaba sai daima yachiro wayarsa yafara neman layin Zahra ” wayar nafara ringing yamike yana chewa Yusuf kasameni a ɗaki san nan yawuche ” mikewa Yusuf ɗinma yayi ya kyale Ahmad awajen yanufi staircase ɗin shima kai tsaye ɗakin Khalid yanufa da sallama yashiga zaune yasamu Khalid yana waya da zahra, hannu kawai Yusuf yasa ya amshi wayar kana yasa akunnensa yana jiyo hayaniyar, kannen nasu ” ina my baby abunda Yusuf yace da zahra ke nan ” da sauri zahra tace gatanan tamikawa lamrat wayar ” hello yaya Yusuf ina wuni ” lunshe ido Yusuf yayi san nan yabuɗe yana faɗin lfy my baby ya school ” alhamdulillah lamrat tabashi amsa ” shiru yaɗanyi kafin yafurta tsarabar me kikeso inkawo miki ” babu komai yaya Yusuf Allah dai yadawo daku lfy shine fatanmu chewar lamrat ” bakaramin daɗi Yusuf yajiba azuchiyarsa yafa tunanin yarinya karama da hankalin manya yana chikin tunani yajiyo muryarta tana faɗin allah yaya Yusuf kewarka nake sosai da sosai ” sake lunshe ido Yusuf yayi yana murnushi farinchiki kasa kasa yace my baby nima nayi missed naki sosaifa ” a shagwabe tace to yaushe zaku dawo ” Yusuf zaiyi magana Khalid ya amshi wayar yana faɗin inyamaka zafi kasaya mata nata wayar yayi maganar tare da mikewa yanufi waje ” murnushi Yusuf yayi san nan yafurta nice idea yana gama faɗin haka ya haye gadan Khalid yayi kwanchiyarsa

    Khalid kuwa yana fita kai tsaye ɗakin Aryan yanufa da sallama Khalid yashiga Aryan baya ɗakin dan haka khalid yafito yanufi ɗakin DON da sallama yashiga zaune yasamesu kan kadon, suna fuskantar juna da alama magana mai muhim’manchi suke ” jin sallamar Khalid yasa dukkansu suka juyo suna kallansa ” ƙarisa shiga chikin ɗakin Khalid yayi shima ya haye gadan ya zauna a nutse yafara magana
    Aryan wai meke damun kane naga gaba ɗaya yau ka chanza ne gashi ka ɗan rame kamar baka da lfy chewar Khalid ” daga green eyes nashi sama DON yayi kamar mai kallan wani abu kamar kuma mai tunani ” zuba mishi ido Aryan da Khalid sukayi suna kallansa ” jimkaɗan ya sauke kansa tare da furzar da iska daga bakinsa ya tsare Aryan da ido sosai yake kallansa ” nantake Aryan ya mike kamar mara gaskiya yana kokarin sauka daga gadon kamar daga sama yaji muryan DON yana faɗin me kake ɓoyemin ashe akoi abunda bai kamata nasaniba a dangane da kai, kodai matsayina bai kai bane ” jin maganar DON yasa Aryan saurin juyowa yana kallansu shiru yaɗanyi kafin nan yace. Taya kake tunanin akoi abun da zan boyemaka dangane dani kai’nefa ni kuma nine kai SO bawani abun boye boye a tsakaninmu wlh kawai bana jin daɗine ni kaina bansan meke damuna ba kwata kwata nakasa samun nitsuwa ” shin akoi wani abu mai mahim manchin daka rabu dashine dazaisa kakasa nitsuwa DON yajefo ma Aryan tambayar bazata ” aa nikuma ina dawani abu mai muhim’manchi dayawuche kune ai kune kawai masu muhim’manchi a rayuwata ” Khalid dai ido kawai yake binsu dashi yadda suke maganar burgesa suke DON akoi kokolwa sosai akoi basira Aryan kuwa akoi wayau sosai shiyasa haɗin nasu yake bada chitta ” barchi nakeji kaina chiwo yake min zanje na kwanta chewar Aryan yayi maganar tare da juyawa yachigaba da tafiya har yakai bakin kofa sai yaji muryan DON yana faɗin idanma baka faɗamin yanzuba nasan dole gaba zanji ai ” shiru kawai Aryan yayi bai tankaba saima kara sauri dayayi yabar ɗakin

    Dawo da kallansa DON yayi kan Khalid yana faɗin akoi abun dake damun ɗan uwana tabbas ba lfy yakeba ” murmushi kaɗan Khalid yayi a zuchiyarsa kuwa yace baridai ya ɗan latsa DON yaji yazasu kare ajiyar zuchiya ya sauke san nan yadubi DON yace kasani kodai yafaɗa soyayyane ” a zafafafe DON yace what ? hauka yakene kataɓa ganin yana magana da watane ma NO hakan ma bazai yuwuba ” mamakine yakama Khalid ganin daga maganar mace DON ya sauya kamar bashiba ” nantake ya kara ɗaure fuskar nan kamar baisan me dariyaba Khalid yayi nisa chikin tunani muryan DON takatse masa tunani ” Khalid i said get out ” kallon DON Khalid yake da mamaki ba musu ya sauka daga gadan dan yasan halin DON yanzu idan yace zai biye masa sai abun yakai’su ga ɓachin rai ” fitowa Khalid yayi daga ɗakin DON kai tsaye yanufi ɗakin Aryan

    Da sallama yashiga zaune yasamu Aryan a tsakiyar gado ” ba karamin mamaki Khalid yayiba ganinsa zaune karisawa chikin ɗakin yayi ya zauna a bakin gadon ” sai lokachin Aryan ya juyo yana kallansa ” lfy bakayi barchiba aryan Khalid yajefo masa tambaya ” iska mai zafi ya furzar daga bakinsa calmly yafara magana nasaba da shan coffee kafin nayi barchine Khalid dazun nayi order coffee sun kawomin amma ɗan ɗanon bai minba kwata kwata na gida nake buƙata shiyasama kaga nakasa barchi ” hannu Khalid yasa a aljihun wandansa ya ɗauki wayarsa yafara kiran layin zahra dan kuwa yanzu yagane matsalar Aryan ” bugu ɗaya Zahra ta ɗaga tana faɗin yaya Khalid ɗazun muna hira ka gudu ” yanzu me kuke bakuyi barchiba Khalid yajefo mata tambaya ” karatu mukayi amma yanzu zamu kwanta ai tabashi amsa ” ok ina diyana ” gata nan inbatane chewar Zahra ” eh bata yayi maganar tare da mayar da wayar a H-free ” ansar wayar diyana tayi chikin voice kamar mai jin barchi tafa magana yaya Khalid shine baka nemeniba tun ɗazun inajin kana magana dasu zahra inasu Ammi ” suna lfy allah sarki na mantane amma ai gashi yanzu na nemeki Koh ” yauwa yaya Khalid daman inasan in’tambayeka chewar diyana ” ok tambayi ” wai a chan makkan wake kaiwa yaya Aryan coffee ” jin tambayar nata yasa Khalid ɗago ido yana kallan Aryan shima Aryan ɗin shiyake kallo ” dawo da kallansa Khalid yayi kan wayar san nan yace bari nabawa yaya Aryan ɗin sai ki tambayesa Koh bai jira amsar taba yamikawa Aryan wayan ” ba musu yasa hannu ya karɓi wayar yana sauke ajiyar zuchiya ” Khalid na mika masa wayar ya mike yace kuyi magana inazuwa yana gama faɗin hakan yafiche daga dakin da sauri yana murmushi

    Calmly Aryan yafara magana hello ” ina wuni yaya Aryan chewar diyana ” wani murmushi Aryan yayi kafin tace lfy y school ” alhadulillah tabashi amsa ” good yace saikuma sukayi shiru dukkansu ” chankuma sai diyana tace yaya Aryan wayake kawo maka coffee a makkan ” murmushi ya ɗanyi kafin ya burta babu kowa ” yanzu ke nan bakashan coffee ɗin ” eh bana sha yabata amsa a takaice ” Allah sarki da ina nan dana rinƙa kawoma ai ” Aryan baimasan san da dariya ta kubche masaba dan yadda ta furta Allah sarki bakaramin dariya tabashiba amma sai ya danne dariyar yace ashe kinaso na bansaniba ashe kina tausayina ” aa bana sonka inadai tausayinka chewar diyana ” to meyasa bakisona ” shiru ta ɗanyi san nan tace kai’ma ai bakasona ne shiyasa nima bansanka ” to wayace maki ni banasonki ” Allah yaya Aryan basai anfaɗaminba ni da kaina nasani baka sona dan inkana sona bazakache zaka harbeni da bindiga namutu kowa yahutaba ” shiru yayi yana tunanin sai yanzu yagane kuskurensa namata barazana da hakan shi yamata chikin wasa itakuma ashe tarike a matsayin gaske yayi nisa chikin tunani sai yaji tana faɗin yaya Aryan sai da safe su zahrafa har sunyi barchi sun kyaleni ” ok kawai yace da ita san nan ya katse kiran ya ajiye wayar a gefe ya kwanta bajimawa barchi tayi awon gaba dashi

    Lokachin da Khalid yadawo ɗakin dan karɓar wayarsa yasamu aryan yayi barchi murmushi yayi a’fili yafurta ai daman ninasan meyahanaka barchi kai da kanka kake neman kashe kanka anfaɗa maka SO wasane ganin Aryan yana ɗan motsi yasa Khalid ɗaukan wayarsa da sauri yayi waje yana murmushi

    Washe gari dawuri suka tashi sukayi shirin zuwa school kamar yadda suka saba haka suka fito yauma kai tsaye wajen motochinsu suka nufa da gudu drivers ɗin suka karaso wajen budemusu motochin drivers ɗin sukayi
    Su diyana Suka shiga suna shiga drivers ɗin ma suka shiga da gudun gaske suka tada motochin suka bar gidan gudu suke sosai chikin kan kanin lokachi suka isa school ɗin awajen dasuka saba parking sukayi yauma fitowa su hiyana sukayi suka jera zuwa wajen tsayuwa suyi hira kafin a shiga class ” drivers kuma suka shiga motochin suka juya suka koma gd

    Tsayuwa sukayi kamar dai jiya Suna hirar’su daga bayansu sukaji andaƙa musu tsawa ” ke zonan ni jiyazakiwa karayan aljanukoh to wlh sai kinyabawa aya Zakinta dan yau saina babbalaki a school ɗin nan ” gaba ɗayansu suka juya ganin jabir yasa Zahra ta kwasa da gudu abunta tayi hanyar class nasu ” diyana kuwa tsayuwa tayi kamar mai tunani ta harɗe hannu a kirji babu ko alamar tsoro a tattare da ita ” hiyana kuwa juyowa tai ta dubi’ su lamrat kasa kasa tace musu kuje class ” a tare suka juya suka nufi class ” jabir ganin alamar diyana ko tsorata batayi ba dajin maganar da yayi yasa ya nufeta gadan gadan ya duncle hannu zai kai mata naushi da sauri…✍️✍️

     

     

    More comments an share pls 🙏

     

     

    *💫STAR LADY💫*

    💖The Talent Troupe Writer’s 💖

    *DUK ƘARFIN IZZATA*

    💖Story And Written💖
    ⬇️

     

     

    *Star lady*

    Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

     

     

     

  • Duk karfin Izzata Book 1 Page 17

    Duk karfin Izzata Book 1 Page 17

    Episode 17*

     

     

    Ganin Aunty Maryam yasa diyana ta fasa ihu tana faɗin, dan Allah Aunty Maryam kiyi hakuri karkisake bugu wlh yanzuma chiwo kaina kemin, ” a zafafe Aryan yamike tsaye yana faɗin sister kibata wayar kinitsu” ina diyana batama jinsa ihu kawai take tana surutai ” zama Aunty Maryam tazo tayi a gefen kadan nasu tana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya ” hiyana ma jin diyana tayi ihu tana faɗin kar Aunty Maryam tabugeta yasata tafito daga toilet da gudu, ” Zahra ma mikewa tai tana kallan Aunty Maryam ɗin ” da gudu nurse nasuma tafito daga nata ɗakin tashigo nasu, tsayuwa tai daga bakin kofa tana kallan’su ” amrat da lamrat kuwa rungume juna sukayi suka rufe ido ” sai magana Aryan keyi tacikin wayar amma shiru dan diyana tama chire wayar daga kunnen’ta ” ina wanchan dan iskan ya kaiku jiya da’baku kwana a gidan nanba chikin tsawa tayi maganar ” tsagaita kukan da take diyana tayi tunda taga Aunty Maryam ɗin bata fara bugunsuba, san nan murya na rawa tafara magana asibiti ya kaimu, ” shiru Aryan yayi yana sauraron maganar tasu” waye jiya a chikinku yasanar da Aryan na bugeku” har suna haɗa baki wajen chewa wlh bani bace bani bace ” shoothup idan baku kukagaya masaba taya akayi yasani ” shiru sukayi gaba ɗayansu ” ke tashi kije ki wanke toilet’s ɗin bangaren Aunty amarya dukka san nan ki wankemin kana nan kayan dana chire ɗazun inkin gama ki wuche kitchin ki shiryamin abun buɗa baki tayi maganar tana nuna diyana ” mikewa diyana tayi san nan ta’ajiye wayar Zahra dake hannunta, tanufi hanyar fita tana faɗin to ” itama Aunty maryam ɗin mikewa tai tana hararar su hiyana tai waje ” girgiza kai kawai Zahra tai tana hawaye ” hiyana ta tako a hankali tazo ta zauna kusa da zahra tashiga rarrashinta ” chikin ɗakin nurse ɗin nasu ta karisa shigowa itama ta zauna, suka fara sharewa Zahra hawaye ” dan Zahra akoi saurin kuka ” amrat da lamrat ma suka dawo kan gadon suka zauna ”

    Shiru sukayi kusan 30 mnt ” hiyana tana kokarin mikewa ke nan sai ga diyana tashigo ɗakin ” da mamaki a fuskar Zahra ta mike lfy diyana kika dawo, kodai har kingama aikin ne, zahra ta tambaya murya na rawa ” aa nidai kawai ina wankin toilet ne, saikuma Aunty Maryam ɗin tace nabari natafi ɗaki, shine nadawo ” baki buɗe zahra tace kai to ya akayi tace kidawo, anya kinji metace ta kyau kuwa ” eh mana Aunty Zahra naji wlh diyana tabata amsa ” hiyana dake tsaye tace to saikutashi muyi sallah ae tunda kin dawo ga lokachi ya kure ” mikewa sukayi baga ɗayansu har nurse nasun ” diyana tashige toilet nasu” lamrat kuma tafito tanufi toilet na ɗakinsu ” zahra kuma tanufi toilet na ɗakin Ammi ” hiyana kuma ta ɗaukoh dadduma ta shinfida dan ita already tariga tayi alwala tun ɗazun ”

    Washe gari misalin karfe 3 na yamma gaba ɗayansu suna zaune a ɗakinsu ” hiyana dai karatun Al qur’ani mai girma take ” diyana kuwa sarkin kallo, kallon film take a wayar Zahra, ita da lamrat ” amrat kuwa tayi barchi abunta , Zahra na hira da nurse ɗinsu ” sunyi nisa chikin abubuwar dasuke,” sukaji diran motochi chikin gidan nan, take jiniyar motar yan sanda ya karaɗe ko ina na gidan ” da sauri Zahra tamike tana faɗin Aunty farida oyoyo, zata nufi waje diyana tariketa tace Aunty Zahra ya akayi kikasan Aunty farida che idan kuma kikaje ba itabace Aunty Maryam che zata komafa ” Aunty farida ne dan kuwa ita kaɗaice mai zuwa da kiniyar motar yan sanda, Aunty Maryam kuma da busar gidan sarauta take zuwa, ki gane bambanchin mana , Aunty Maryam ɗan sarki take aure, Aunty farida kuma ɗan tsohon gwamna kuma gwamna mai chi yanzu take aure, zahra na gama faɗin hakan tanufi waje da gudu ” da sauri su diyana’ma sukabi bayanta amma banda hiyana da nurse nasu, dan hiyana bazata iya wani dogon tafiyaba saboda jiri datakeji ,
    Aguje Zahra ta tafi tafaɗa jikin Aunty farida dake tsaye tana kokarin fidda kuɗi daga jakarta, bazato ba tsammani kawai taji Zahra ta faɗo mata a jiki saura kaɗan su faɗi ” haba auta sokike ki kadanine ” dariya Zahra tayi san nan tace. To Aunty farida ae murnane yasa na faɗo jikinki, ina junior ” yana wajen baban’sa sai ranar Sallah zasu zo zata sake magana idanta ya sauka akan diyana dake tsaye murmushi ta sakarwa diyanar tare ta yimata alama da hannu a kan tazo ” da sauri diyana tanufeta itama tana murmushi ” haɗesu Aunty farida tayi ta rungume tana faɗin nayi kewarki my sister’s ” muma munyi kewarki wlh chewar Zahra ” sakinsu Aunty farida tayi san nan ta karisa wajen da lamrat ke tsaye, itama ta rungumeta tana faɗin kebazakizo kimin oyoyo ɗin bane ko dai kunyata kikejine, nifa ba surukarki bace ” inawuni y hanya chewar lamrat ɗin ” lfy lau Aunty farida tafaɗa tare da sakinta, ta chiro kuɗi masu yawa tamikawa security ta san nan ta rikoh hannun diyana suka nufi bangaren Ummi ” security na biye dasu da manya manyan trolley a hannu ” su Zahra suka rufa musu baya ” ina hiyana da amrat Aunty farida ta tambayi diyana tana kallan fuskarta ” hiyana na ɗaki tana karatu, amrat kuma tayi barchi , ” ok to meyasameki a baki naga bakin ki yakunbura kodai wajen rawan kan’kine kika fasa bakin ta karisa magamar suna kokarin shiga palon Ummi ” aa Aunty Maryam che ta fasamin ” Aunty farida na kokarin zama a kujera tace.what me ya haɗaki da Maryam kuma tayi maganar tana kokarin zaunar da diyanar kusa da ita ” nan fa diyana tashiga bata lbr abun daya faru tun ranar da Aunty Maryam tazo har yau sai da tafaɗa mata komai ” Zahra dai a tsorace take sosai dan yanzuma basu faɗawa kowaba, Aunty Maryam tace sun faɗa barekuma diyana tazo tafaɗa’ɗin ” Aunty farida ma shiru tayi kuma sai yanzune tagane dalilin daya Aryan yace tayi zuwar gaggawa, kuma batayi mamakin abunda Aunty Maryam ɗin tayiba dan tasan fiyeda hakama Maryam zata iya aikatawa ”
    Am sorry my diyana kiyi hakuri kunji yanzu kutashi muje kurakani na dubo jikin hiyanar Koh ta karisa maganar tana mikewa ” suma mikewa sukai, tafita sukabi bayanta

    Da sallama suka shigo palon kai tsaye ɗakin’nasu.suka nufa hiyana dai tana zaune inda suka barta, rike da qur’ani tana karatu ” ganin Aunty farida yasa tamike da kyar, tana faɗin sannu da zuwa Aunty farida” karisa shiga chikin ɗakin Aunty farida tayi taje ta rungumi hiyana, tana faɗin am sorry my dear y jikin “da sauki sosaima ” murmushi kawai Aunty farida tayi san nan ta saki hiyana, takama hannunta suka koma baƙin gadon suka zauna ” kin.sha maganin rana kuwa Aunty farida ta tambaya tana kallan fuskar hiyanar ” eh nasha ” ok to zaki iya tafi dan Ina san inje inyi wanka, kuma zanso mutafi tare gaba ɗaya, dan daga yauma har ranar dasu Ammi zasu dawo tare zamu zauna daku a ɓan.garen Ummi ” eh zan iya ” ok to kutashi muje, har sun mike zasu fita sai idan Aunty farida ya sauka kan nurse ɗin’su dake tsaye a gefen drawer ” wacece wanchan kuma ” juyawa sukayi suna kallan inda Aunty farida ke nunawa ” laaa. Aunty farida nurse ɗin.muce chewar diyana ” oh to itama tazo muje tare tunda daman kula daku take yanzu tunda zaku koma ɓan.garen Ummi itama ae dole tabiyo’ku dan kula daku, ” to sukace san nan diyana ta tashi amrat daga barchi ta rikoh hannunta ” ska tanufi waje ” Aunty farida na rike da hannun hiyana

    Misalin karfe 6:45 Aunty farida tafito daga ɗakin Ummi a palo taisko’su diyana “suna ganinta suka fara gaishe.ta ” da fara’a ta amsa san nan ta ɗora dacewa kutashi kuje palon Abba muyi buɗa baki ” bamuyi azumibafa dukkanmu Zahra chewar Zahra ” eh nasan baku azumi amma ae zaku chi abinchin dare koh, bama wan nan ba dole muje kutayani chi abinchin ae ” har suna haɗe baki wajen chewa to Aunty Maryam ta hana’mu zuwa palon Abba ” dogon tsaki Aunty farida taja san nan tace.kutashi mutafi hai ” ba musu suka mike gaba ɗayansu ” Aunty farida takama hannun diyana sukayi gaba, su hiyana suka rufa musu baya

    Da sallama suka shiga duk da sunsan babu kowa a palon.mamakine yakama diyana da sauri tace.Aunty farida yanaga table ɗin chin abinchin yazama biyu, kuma ankaro kujeru ” eh saboda sallah gaba ɗayan muna zuwane shiyasa, da sallah yakusa ake fito da ɗayan daman table biyune, kinga ae guda ɗaya bazai isshemu, mu dukka bakoh muna dayawa kuma kowani table kujera 12 to kinga ae kujera 12 yamana kaɗan ta karisa maganar tana kokarin zama ” zama gaba ɗayan’su suka zo sukayi ” Aunty farida tana faɗin my diyana kekam sai yaushe zaki daina surutune ” sosai diyana tai dari sai datayi mai isarta san nan tace ae nibana surutu ” Aunty farida dai bata kuma’chewa komai’ba ta kira masu aiki tabasu umarnin suzo su shirya musu abinchi ” chikin hanzari sukafara jeramusu a’binchin san nan suka shiga sarving nasu

    Sunyi nisa chikin chin abinchinsu, ba wanda yake magana a chikinsu shiru palon sai dai karan spoon zakaji ” babu ko sallama ta faɗo chikin palon fuskar nan a tamke ” jin motsin anshigo palon yasa dukkan’su suka ɗago suna kallanta ” nan take hiyana ta kankame Aunty farida ” mai da kanta Aunty farida tayi tachigaba da chin abinchinta kamar ma bata san da mutun awajenba ” chikin tsawa Aunty Maryam tafara Magana “banache kada nasake ganinku a kowa bangare na gd nan ba, inba bangaren Aisha ba,” a sukwane Aunty farida ta ɗago kai jin Aunty Maryam tace. Aisha kai tsaye kallan’ta Aunty farida take sosai batare da tace uppan ba ” jin abun da Aunty Maryam tace yasa’su hiyana kokarin mikewa dan subar palo ” muryan Aunty farida ta katse’su dacewa ina kuma zakuje ” juyowa sukayi suna kallan Aunty farida kanta na kallan kasa tana chin abinchin’ta chikin kwanchiyar hankali, kana suka juyo sukaga Aunty Maryam dake tsaye tana jiran, suzo su fiche daga palon nan, ga fuskarta babu annuri ” sun rasa me ɗaya zasuyi kawai suka tsaya chirko chirko ” ganin hakan yasa Aunty farida ɗagowa ta dubi Aunty maryam a kausashe tace kifita a ɗakin nan Maryam ” kara ɗaure fuska Aunty Maryam tayi tace akanme zanfita ” a kan na isa inche kifita kuma kifita dole ” shiru Aunty Maryam tayi tana tunani bazata iya jayayya da Aunty farida ba dan kuwa idan tace zatayi hakan tofa gaba ɗaya gidan nan sai sun hukunta’ta “gashi kuma Aunty farida na neman kunyata’ta a gaban yaran nan, ganin Aunty Maryam ta tsaya shirune yasa Aunty farida chewa ” ke Maryam badake nakeba nace kibar wajen nan koh ” a fusace Aunty Maryam tajuya fuuu kamar wata kunfa tayi waje ” dawo da kallanta kansu hiyana tai tana faɗin ko zauna kuchi abinchin ku” ba musu suka zauna sukachigaba da chin abinchinsu

    SAUDIA ✈️

    Kwanche yake saman faffadar gadon’sa ya zubawa wayar hannunsa ido sosai yake kallan hoton’ta wani nauyayyar ajiyar zuchiya ya sauke ” a hankali da murya kamar mai’raɗa yafurta ke kyakkyawa’ce my sister ina kewarki sosai ina butatar, shan coffee ” takun tafiya yaji kuma ko ba a faɗamasaba yasan wan nan takun DON ne ” da sauri yafita wajen hoto ya kashe hasken, screen ɗin wayar ya ajiyeta a gefensa ” da sallama ɗauke a bakinsa yashigo betroom ɗin ” mikewa Aryan yayi zaune yana amsa masa sallamar ” kallansa Aryan keyi daga sama har ƙasa da mamaki yache inazakaje haka naga kasa kaki ” calmly DON yafara magana I need Ur prayer zan dawo jibi sai muwuche naija tare ” like how bangane U need my prayer ba inama zakaje yayi maganar yana kokarin sauka daga gadon ” London zanje yanzu kiran gaggawane, kar kafaɗawa’su Abba dan bansan hankalin’su yatashi ” no gaskiya sai dai muje tare ” aa Aryan taya zamu tafi tare kuma ae idan muka wuce tare dole su Abba su sani kawai ka tsaya ka taremin, insun tambayi ina nake kasan mezaka faɗa musu ” badan Aryan yasoba haka ya hakura yaraka,DON har airport san nan yadawo.

    NIGERIA

    Bayan sun gama chin abinchinsu ne Aunty farida tace to kutashi muje ɗaki muyi sallar mangariba da issha sai nabaku tsarabarku ” da murna suka mike Zahra na faɗin Aunty farida dan allah kinkawo’min lalle kuma zakimin koh ” sosaima kuwa auta ai daga jibi zan fara muku lalle mai kyan gaske ” da sauri diyana ma tace Aunty farida nima inasan lallen sosai zakimin” eh mana my diyana dukkanku zan muku ” jerawa sukayi Aunty farida na rike da hannu diyana ” sunzo zasufita palon ke nan ” jiri ya kwashe hiyana tatafi luuuu zata faɗi da sauri nurse ɗin tarike ta tana faɗin ” wlh yarinyar nan ta bugu sosai a kantan nan tana bukatar kulawa sosai ” a sukwane Aunty farida ta juyo hannu tasa ta taimakawa nurse ɗin suka rike hiyana sukayi bangaren Ummi,
    A kam doguwar kujera suka kwantar da ita nan take nurse ɗin ta koma bangaren Ammi ta haɗo musu magungunar’su ta dawo ” ɗaya bayan ɗaya tabisu da kanta ta basu maganin sai da ta tabbatar sunsha san nan takoma kan nata kujerar itama ta zauna ” Zahra ki shiga chikin ɗakin ki ɗaukoh min babban trolley na ɗin nan kuje da diyana ta kama miki chewar Aunty farida ” to su’kace a tare suka mike suka nufi chikin ɗakin

    Jim kaɗan suka fito da katan akwatin Aunty farida da kyar suke jan trolley ɗin ” a tsakiyar palan suka ajiye sai nishi suke kamar wayanda sukayi wani aikin wahala ” saukoh wa kasa Aunty farida tayi tazo ta buɗe trolley, ɗin nanfa tafara fitar musu da tsarabar’su komai iri ɗaya ta sai musu ” manya manyan lufaya na kanuri ta sai musu masu kyau da tsada kowa kala bibbiyu Pink da blue ” sai dogayen riguna masu manya manya mayafi kala uku² tabawa kowa da baki da ja dakuma porpul colour ” ga wasu manya manyan ribons na ɗaure gashi da manya manyan bit ” sai turare masu kanshi da kayan kwalliya sai takallama kafa uku 2
    Sai murna suke sunamata godiya musamma ma diyana nata murnan daban ne dan an kawo mata kayan kwalli kit guda sai dariya take ” daukoh turare mai tsada da dogon riga mai kya Aunty farida tayi taba nurse ɗin, ansa tai tanata godiya
    To kutashi ku kai kayan ɗaki ku ajiye sai rananr sallah yanzu jibi zamuyi lalle raanar Friday kuma zanmuku gyaran gashi dan gashin kun nan bazai kitsuba yayi tsantsi dayawa shiyasa na sai’muku wayan nan bit ɗin dan namuku kitso guda biyu a gaban goshi kawai nasamuku bit ɗin nan, sauran gashin kuma ayi parking ta baya ” sai murna suke har suna haɗa baki wajen chewa to tare da mikewa gaba ɗayan’su kowa rungume da kayansa zasu fita ” Aunty farida tace. Inakuma zakuje ” dakinmu zamu kai kayan zahra tabata amsa ” aa ae nafaɗamuku sai Ammi ta dawo zaku koma bangarenta dan haka kuzo ku kai ɗakin Aunty mardiya ku ajiye, kuma a nan zaku rinƙa kwana ” ba musu suka juya suka nufi ɗakin Aunty mardiyar suka ajiye kayan nasu chikin sip san nan suka dawo Palo

    YOLA

    Abun duniya ya ishata yau anwayi gari babu komai na chi a gidan ga azumi ba abun chi idan anyi buɗa baki, zama tayi tana tunanin yazatayi, chankuma tayanke shawarar ta ɗaukoh 1k a chikin kuɗin data ajiyewa boka tayi chefanen abun da zatachi, Allah barshi kafin lokachin komawarsu wajen bokar sai tanemo wani kuɗin tachikasa da wan nan tunanin tamike tanufi ɗakinta ” ɗaga gadon chiyawarta tayi ta ɗaukoh kuɗin ta chiri 1k ,ta maida sauran, ta ɗauki mayafita tayi waje dan zuwa yin chifene

    KANO

    Ku tashi kushiga ku kwanta dare yayi kunji chewar Aunty farida ” to kawai suka amsa mata tare da mikewa gaba ɗayansu har sun kai bakin kofar betroom ɗin Aunty mardiya” Aunty farida tace. aa to ae gadon yamuku gaɗan diyana da amrat suzo mukwana a ɗakina itakuma nurse naku taje wan chan ɗayan ɗakin ta kwana, tana gama faɗin hakan tamike tanufi hanyar fita ” harta kai kofar fita tsaikuma ta juyo tana faɗin diyana kuashiga ɗakina keda amrat ku kwanta ina zuwa zanje wajen Maryam ” to kawai sukache san nan suka nufi ɗakin nata itakuma tayi waje, su Zahra ma nuka shige ɗakin Aunty mardiya nurse nasu kuwa tawuche ɗakin da Aunty farida ta nuna ”

    Da sallama Aunty farida ta shiga palon Aunty amarya babu kowa dan haka kai tsaye tawuche ɗakin Aunty Maryam da sallama tashiga kwanche ta isko ta tana latse latsen ” ko amsa sallaman ma batayiba bare ta ɗago kai ” Aunty farida bata damu da hakanba wuche tayi ta zauna a bakin gadon a nitse tafara magana ” tashi inasan magana dake ” mikewa Aunty Maryam tayi zane, a kausashe tace to me kikeso yanzu kuma ” daure fuska sosai Aunty farida tayi san nan tafara magana ” meyasa kika bugi yaran nan mesuka miki ” dogon tsaki Aunty Maryam taja san nan tace abun da kikazo jike nan to na buga kuma babu abun da sukamin kawai naji inasan bugun’sune shiyasa na bugesu, ko zaki rama musune ” juyowa Aunty farida tayi a fusace ta ɗauke Aunty maryam da mari tana faɗin ni sa’ar kice dazaki zauna kina faɗamin magana ” a fusace Aunty Maryam ma ta ɗaga hannu..✍️✍️

    More comments pls 🙏🙏

     

    💖The Talent Troupe Writer’s 💖

    *DUK ƘARFIN IZZATA*

    💖Story And Written💖
    ⬇️
    *Star lady*

    Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

     

    *

     

     

  • Duk karfin Izzata Book 1 Paga 1

    Duk karfin Izzata Book 1 Paga 1

    Episode 1*

    💖الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر💖

     

    London United Kingdom

    Wasu haɗaɗun samari ne zaune awani katafaren palo mai girman gaske,Mai ɗauke da manya manya sofa set 2,launin Brown da ratsin milk, gawasu triple staircase ɗaya ta bangaren hagu ɗaya bangaren dama ɗayan kuma a tsakiya daga gefe kuma wani haɗaɗen table ɗin chin abin chine, ga wata makekiyar Tv a gefe guda,palon yaji komai da ake buƙata dan in nache zan tsaya zayyana muku ha’ɗuwar palon nan tofa sae mukare littafin nan a palo kawae, kae dakaga wajen kasan baƙara min dukiya aka narka awajen ba,”zaune suke,shiru ba mai magana ” kowa da abin dayake fuskar nan tasu kuwa tamkar an aiko musu da sakon mutuwa ” gasu kyawawa sosai kamar larabawa

    Farare ne sosai dukkan su kamannin su ɗaya kallo ɗaya zaka musu kagane yan uwan juna ne amma biyu dake zaune a saman sofa mai zaman mutun 2 nan,sunfi kama da juna sosai dan kuwa kamar an tsaga kara, haka suke suna da dogon hanchi sosai, ga manya manyan ido sai dai abun mamakin kowa dakalar idansa biyu daga chikinsu dake zaune saman sofa guda kwayar idansu ash colour ne biyun dake gefe kuma idan nasu light green ne shikuma ɗayan idan sa baki ne, ga idon nasu manya manya ” ga ɗan karamin red lips, ga lallausan bakin saje kwanche a guskar su, sai dai uku daga chikin su gemun su bai da tsawo sosai san nan kuma suna da gashin kai mai tsawo har baya kamar mace.

    “wani haɗaɗen saurayi ne ya sauko daga staircase ɗin tsakiya yana faɗin haba DON yabaku’shiryaba Aryan Aiman yusuf Ahmad me kuke jira

    (nikoh nache daman wayannan turawan sunajin hausane)

    ɗago ido DON yayi “wadda shi idansa ya kasanche light green ne,yana faɗin “shirin zuwa in kuma Khalid,Akule khalid yace “shirin zuwa Nageria mana ko kun manta gobe za’a ɗaura auren hisham,mike DON yayi yana faɗin “bazanje ba nikam san nan yanufi saman stair ɗin ban garen hagu,da sauri khalid yajuya daniyar yasha gabansa,Yusuf yamike yarike sa, a’fusache khalid Yajuyo yana faɗin “yusuf kasakeni ” Yusuf ya ɗago ido shima dai idan nasa light green gasu manya manya masu kyan gaske yache “aa khalid bazan sakekaba kafasan kokabishi ba chanza magana zaiba saidaima kubata,yakamata ache idan dasabo kasaba ɗan kasan, yaya prince fa idan yayi magana to yayine baya chan zawa, shiyasa muka chanza masa suna daga prince Safras muka maidashi DON, dan in yayi maganafa it’s done angama baya chanza wa “pls yusuf ka kyaleni wlh yau kam dole DON, ya chanza magana haba dan allah ai kobazaije bikin kowaba dole yaje na hisham, saboda tare muka taso gaba ɗayan mu, dukkan mu abu ɗaya’ne chewar khalid “ɗaya daga chikin matasan dake zaune saman sofan ne yamike yache “to ni ma dai ba zuwa zanyi ba, yana gama fadin haka yajuya yanufi stair ɗin ban garen hagu “a fusache yusuf yajuyo yana binsa da kallo yace what wae Aryan meyake damun kune “ɗaya daga chikin su’ma yasake mikewa yana faɗin to dai kunsan tsakanina da Aryan, babu ban ban chi, idan yayi abu, nima zanyi idankuma bai yi’ba nima bazan yiba, dan tare aka haife mu kuma tare muke komai, yana kaiwa nan ya juya shima yanufi stair ɗin bangaren dama ” kwashe wa da dariya Ahmad yayi, yana fadin amma Aryan da Aiman yan iska’ne wlh anafaman kashe wutar da DON yake kokari kunna’wa su kuma zasu kunna nasu. “akule yusuf yache kaikuma Ahmad menene hakan to ae wan nan ba abun dariya bane,ae ko zakuyi’wa, kowa irin wan nan rashin mutunchin tofa banda hisham, kar’kamanta fa tare muka taso, tare mukeyi duk wani abun daza muyi komai namu iri’ɗaya duk da iyayen mu ba ɗaya ba, katashi muje mushawo kan DON tukunnan muje musamu yaya Aryan, dan shine matsalar idan yache zaije tofa Aiman mai sau’kine, dan shi duk abun da Aryan ya aika’ta shima ae’katawa zai yi ” kama hanyar tafiya khalid yayi yana faɗin wlh yau DON ya batamin rai haba dan allah ” da sauri Ahmad ya rufe’masa baki da hannun sa yache ya isa yanzu dai muje mushawo kansu dan sulhu muke nema dasu ba faɗa ba “faɗa masa dai chewar yusuf ” haurawa saman stair sukayi wani katafaren hadadde palo suka shiga ” palan ya tsaru iya tsaruwa komai na chikinsa farine tas harta labulayen suma farare ne tas ga manya manya sofa set ɗaya gawani makekiyar plasma TV dake gefe,babu kowa a palon sae karan AC dake tayi, kai tsaye suka nufi chikin betroom ɗin,”subhanallah tsarki ya tabbata ga ubangiji jama’a ninaga aljannar duniya,manya manya sofa set ne,set 1 ga wani ɗan karamin table a tsakiya,gefe guda kuwa wani katafaren gado wadda ko mutun 10 zasu iya kwan chiya a kae, daga ɓan garen hagu kuwa kofar dressing room ne,sae kofar toilet kusa da dressing room ɗin, betroom ɗin ya tsaru’ne sosai idan nache zan tsaya zayya no muku tsaru war batroom ɗin nan to zamu kwana mu wuni bamu gama ba”kwanche DON yake akan katafaren gadon’sa dake shin fiɗe da white bet shit,kwan che yake ya miƙe kafar’sa har tawuche gadon tsawo,ya chire rigar sa faffaɗar kirjin nan nasa abuɗe ga wani gashi dark black mai tsantsi kwan che a kan faffadar kirjin nasa, damtsen hannun nan nashi kuwa tamkar zasu fashe,saboda karfi, kamar wani sa’daukin yaƙi,”yana’jin shigon war su Khalid amma ko kallan inda suke baiyi ba
    yusuf ya wuche wajen courting ɗin yasa hannu ya yaye,wata kofar glass ne ya bayyana awajen daga chikin daki kana kallan me a wajen,wajen shaƙa’tawane mai dauke da runfa da kugeru awajen da wata table a tsaki yar kugerun, agefen kuwa wani dan karamin pool ne mai kama da baf ɗin wanka, yana ɗauke ta sky blue ruwa

    “DON pls katashi muna’san magana, da kai ne chewar Yusuf” shiru DON yayi kamar baiji su ba “hayewa gadon Khalid yayi,yana faɗin pls prince katashi mana, ko kallan inda suke DON bai yi’ba bare su sa ran zai amsa musu, “haba big bro dan allah to imma bazaka tashi ba,pls kaba mu amsa dan awan nan karan ba shiru muke san kayiba, kanaji koh chewar yusuf ” DON dae bai tanka su ba “a fusace Ahmad yace look DON dan Allah kar ka che bazakaje bikin hisham ba wlh idan kayi haka baka kyauta ba,kasani hisham fa jinin mune ” dogon tsaki DON yaja atakai che yace in kungama zanchen naku saiku fita kubar’min ɗaki, dan kuna damuna wlh ” afusa’che Khalid yafara magana wlh bazamufita mu zakawa iskan’chi to barikaji dole kaje bikin hisham, in bahakaba sai dai kazaba ko,mu kokuma ka kasanche kai kadai “a’takaiche DON yace ae daman ni ka ɗae nafijin daɗin rayuwa “haka kache koh, baisake che musu ko uppan ba haka sukayita surutun su har suka gaji sukamike suka fita suna fita ” DON ya daukoh wata remot ya saita’ta saitin kofar dakin ya danna remot din jikake lok lok kofar tana kulle kanta,ajiye remot ɗin yayi yajuya yana fiskantar wajen shaka tawan,

    Su yusuf kuwa suna fita dakin, DON ɗakin, Aryan suka nufa wani ɗan corridor suka bi ɗan tafiya kaɗan sukayi suka shiga palo Aryan, komai na palan iri ɗaya ne dana DON sai dai na Aryan ash colour ne babu kowa a palo kai tsaye betroom ɗin sa suka nufa,da sallama a bakinsu suka shiga, Aryan yana zaune yana aiki a laptop shikuma Aiman na kwanche yana latsa waya ” chikin ladabi da neman sulhu yusuf yafara magana wai me hakane bro,baikamata muyiwa hisham haka’ba,pls kar kuche baza kuje ba ” daga Aryan har Aiman ɗin ba wan da ya tanka yusuf ” akule yusuf yakuma chewa pls wai meyasa ku keyin hakane dan Allah ” yusuf idan fa yaya Aryan ya yarda zaije nima wlh zan je, amma in bazai jeba takin takalmi babu inda zanje nima chewar Aiman ” juyo Yusuf yayi yana kallan Aryan da ko kallan in da suke su bai’yiba bro dan allah kar kache bazakaje ba’ dan wlh ko bazakaje bikin kowa ba ya’zama dole kaje na hisham dan kuwa hisham yazama tam kar jinin mu ya’zama tamkar ɗan uwan mu,a’fusache Aryan yajuyo’ yana faɗin “kasan dai bani da yayan daya wuche DON koh to ko bikin shi ake bazan jeba ” a’fusache khalid yache wai meyasa bakuda hali mai kyau ne dan allah, daurin aurefa kawai zakuje,”shiri Aryan yayi bai sake tan kasu ba yachi gaba da aikin sa ” yusuf kuwa kallan Aiman yayi yace bro zo muje waje muyi magana

    palon suka fita, yusuf yayita lallaɓa Aiman har ya yarda zai bisu “kowa ya nufi ɗakin sa dan shirin tafiyar,

    shir’yawa sosai sukayi suka fito suka haɗu a babban palo,”to bari na tambayo mana Aryan sae muyi using jet nashi koh chewar yusuf ya karisa maganar yana hayewa stair ɗin yanufi dakin Aryan, a kwanche ya same sa yana latsa waya, harara Yusuf ya wunga masa kafin yache zamuyi anfani da jet naka “batare da ya kalle’sa ba yache adawo lfy ” juyawa yusuf yayi yafito, yasa mu su Khalid a palo suka jera zuwa waje motochi 4 suka ɗauke su zuwa Airport, Khalid Yusuf, suka shiga mota ɗaya Aiman Ahmad suma motar su ɗaya, saura moto chi 2 kuma sojoji yaran Yusuf ne a chiki, a jere motochin suka chera da matsakai chin gudu suka miƙi hanyar fita daga gd, da sauri security dake bakin gate suka wan gale katafaren gate ɗin, a hankali suƙa danna han chin moto chin waje,suna fita su ka karawa motochin gudu, sosai suke sharara gudu chikin kan kanin lokachi suka isa Airport, suna isa suka tarar an gama shirya komai su ka ɗai ake jira su tashi, basu wani ɓata lokachi ba suka fito daga motochin,suka nufi jet ɗin Aryan suka shiga suka zauna ba wan da yache da ɗan uwan sa kala kamar an musu zuwa dole karfe 7 na safe jirgin nasu ya ɗaga suka lula a sararin, sama’niya sai babban birnin tarayya Abuja Nigeria

    Jirgin su na sauka a Airport na Babban burnin ta’rayya, dan kara dan karan motochi masu numfashi ne sukazo ɗau kan su, wan ɗa a’kallah yawan motochin zasu kai 8 ga kuma motochin 5 na sojoji abaya ” wasu jib ga jib gan sojoji guda 4 ne suka diro kasa daga samar motar su fiskar sun nan babu annuri ko kaɗan riƙe suke da manya manya Gun a hannun su, su na takawa irin takun jaruman maza,suka nufi su Yusuf, da sauri biyu suka tare bayan su biyu kuma suka tare gaba, Yusuf kuwa sae taku yake kamar wani sa dauki,har suka karisa wajen motochin,da sauri sojojin dasu gaban su suka fara buɗe musu kofar motochin, Khalid da Yusuf suka shiga mota ɗaya Aiman da Ahmad kuma suka shiga mota ɗaya,hannu sojojin suka ɗaga suka sara wa Yusuf san nan suka rufe kofar motochin,da gudu suka juya suka nufi nasu motar, sauri sauri suka motochin key, da matsakai chin gudu suka bar Airport ɗin,suka miki shin fi ɗadɗiyar titi gudu suke shararawa sosai har suka kusa chikin anguwar wuse 2 bakin wani katafaren gida na alfarman kae kaga ganin gidan kasan ya tsaru,suna karisawa bakin gate ɗin suka rage gudun motochin nasu, wani soja dake zaune kan plastic chair ne ya taso da sauri ya wan gale musu katafaren gate ɗin, kusa motochin chikin gida sukayi kai tsaye parking space suka nufa suna kashe motochin sojojin suka fito da sauri suka buɗewa su Yusuf kofar motar, a nitse suka fito,jingina da jikin motar Yusuf yayi yana bin gidan da kallo,gidan part 4

    wani saurayi ne yafito daga ɗaya daga chikin part na gidan ya nufo su Yusuf yana ɗan murnushi, da sauri ya karisa wajen yayi hugging na Yusuf yana faɗin Wellcome,my brother’s bai jira amsar Yusuf ba yasake sa yabi su Khalid ma ɗaya bayan ɗaya yana hugging nasu, bayan yagama hugging nasu ne ya dawo da kallan sa kan Yusuf yana faɗin,”Yusuf DON da Aryan basu zo bakoh “sorry hisham Yusuf ya faɗa yana ɗan sosa kai, murmushi hisham ya ɗanyi yana faɗin bismillah muje chiki,gaba yayi suka bishi a baya,part nashi suka nufa,a haɗaɗ’ɗiyar palon sa suka zaune, shiru sukayi ba mai magana dan duk kansu ba masu yawan surutu bane almost 15 mnt Yusuf ya katse musu shirun da chewa, ” Hisham ana gama daurin aure nanfa, zamu wuche kano,da sauri Hisham ya ɗago yana faɗin “haba yusuf sai kace ko rin ku ake dan Allah kun fa San ni bani da wani friends Sai ku taya kuke san naje wajen dinner ba friends, “aa Hisham tun dana che maka ana ɗaura aure zamu wuche tofa sai mun tafi,dan kuwa mu iya ɗau rin aure kawai mu kazo “nasani Yusuf amma pls ku bari sae gobe ku wuche,mikewa Aiman yayi yana faɗin “yau zamu tafi ba sae gobe ba kuma karfe 4 dai dai zamu bar garin man ko an daura auren ko ba a daura ba yana gama faɗin hakan yanufi waje, girgiza kae kawai Khalid yake, shiru Hisham yayi dan kuwa yasan ko me zai che musu bazasu tsaya ba tunda su kache yau zasu wuche tofa ba abun da zai hana su tafiya,dan duk chikin su ba mai magana ya sauya in sun yi magana sun yi ne ba chan’ji,shiri suka zauna palon ba wan da yasake chewa ko uppan

    Aiman kuwa yana fitowa waje kai tsaye inda sukayi parkin na motochin su yanufa, da gudu ɗaya daga chikin sojojin dasuka zo dasu ya nufo shi buɗe masa mota yayi,Aiman yashiga ya zauna,ya zuro kafar sa waje ya chiro wayar sa yana latsawa, gefe sojan yakoma ya tsaya yana jiran permission su tafi almost 20 mnt yana zaune yana latsa wayar sa, ɗago kai yayi zai yiwa sojan magana sai wayar sa tafara ringing,bin screen ɗin wayar yayi da kallon ganin sunan Aunty Mardiya che ya sashi jan dogon tsaki,har wayar ta katse bai ɗaga ba kira na 2 yasake shigowa, tsaki yakuma ja kafin yayi picking call ɗin ya kara wayar a kunne yana faɗin hello, daga ɗayan ɓangaren “Aunty mardiya tace hello Aiman ykk ” daure fuska yayi kamar yana gaban ta yace lfy ykk ” ina lfy wai da gaskene kun shigo naija “eh mun shigo sai akayi yaya “to dan Allah za kuzo gida na,tsaki yaja kafin yace “wai meyasa kekam Aunty mardiya baki da wata matsala ne arayuwan ki kedai burin ki kawai a zo gidan ki, kin dai san baza mu zoba “dan Allah Aiman ka daina faɗin hakan kaji pls kuzo mana koda 5 mnt mu gai sane kawai,ni kasan da za abar ni nazo na gan ku wlh da zanzo,duk da niche babba ” Aunty mardiya sai anjima kuma baza mu zoba yana gama faɗin haka ya katse kiran, ɗago ido yayi zai yiwa sojan magana idan sa ya sauka kan wata budurwa dake tsaye a kusa da mur fin motar kawar da kan sa yayi kamar bai ganta ba, chikin ran gwaɗa ta karaso gaban sa ta kashe murya tana faɗin “aslm ykk, tam kar bai san da mutun awajen ba, sake matsowa tayi kusa dashi sosai har kamar zata taka masa kafa “tace sunana Zubee,kuma ni babban kawar amarya che nasan kaima kana ɗaya daga chikin friend ɗin ango Ko,shiru Aiman bai ko kalli inda take ba bare tasa ran zai amsa mata, sake kashe murya tayi tana faɗin haba ƙyaƙkyawan saurayi inama magana kana share ni me yayi zafi kodai ban maka bane, “wani tsawa ya mata leave this place, jin hakan yasa sojan ya karaso wajen da gudu ita kuma zubee tsabar tsorata sai da jakar hannun ta ya faɗin jiki na rawa ta duƙa kasa ta ɗauki jakar da gudu tabar wajen,a fusache yabawa sojan umarni daya shiga motar yaka sutafi, da sauri ya shiga ma zaunin driver shi kuma Aiman ya mai da kafar sa chikin motar ya rufe marfin motar da sauri sojan yama motar key yaja suka nufi gate security suka gan gale masa gate ɗin ya danna han chin motar waje gudu yake shararawa sosai”oga ina muka nufa sojan ya tambaya yana kallan face ɗin Aiman ta chikin miro ” hotel Aiman ya bashi amsa a takai che gudu sosai sojan ke shararawa da motar chikin kan kanin lokachi suka isa wani katafaren hotel, horn yayi a bakin gate ɗin mai gadi ya wan gale masu gate ɗin, a hankali ya kusa motar chikin hotel ɗin parking space nasu yanufa yana kashe motar yafito ya buɗewa Aiman kofar, a nitse ya zuro kafar sa waje kafin yafito gaba ɗaya, chiki reception yanufa sojan na biye da shi ɗaki ya kama ya karɓi key yawuche, shiga chikin ɗakin yayi shikuma sojan ya tsaya a bakin kofar ɗakin, a gurguje yanufi toilet yayi wanka yafito ɗaure da towel yanufi waje, sojan na tsaye a bakin kofa Aiman ya fito”Abbas kaje ka ɗauko min trolley na a mota, da sauri Abbas ya wuche ya koma mita within 2 mnt sai ga Abba ya dawo rike da trolley, Aiman na tsaye a bakin kofa,Abba yazo ya miƙa masa trolley ɗin,ansa yayi ya koma chikin ɗakin Abbas kuma ya gyara tsayuwar sa a bakin kofar, jallabiya baka Aiman ya fitar yasa,da sauri sauri ya haye gado ya kwanta ba jimawa barchi yayi awan gaba dashi

    Around 1:20 su Hisham sungama shirin zuwa wajen ɗaurin aure Hisham na sanye chikin dakakkiyar shadda fara tas,ya sanya kula baki da takalmi baki, Yusuf kuwa sanye yake chikin wandon jeans baki da t-shirt ash ya gyara gashin kan san nan kamar wani balarabe, Khalid na sanye chikin blue jeans da white t-shirt Ahmad ma na sanye chikin blue jeans da black t-shirt dukkan su sunyi kyau sosai “wae ina Aiman ne Hisham ya tambaya yana kallan Yusuf ” guntun tsaki Yusuf yaja yana faɗin oh bari dai na kirasa awaya muji chiro wayar sa yayi daga aljihu yanufi waje yana kiran layin Aiman ɗin

    Hotel

    Aiman na chikin barchi yaji wayar sa na ringing wani dogon tsaki yaja, batare daya buɗe ido ba yasa hannu yana lalubar wayar da kyar ya isa ɗauko wayar dan har kiran ta kusa yan kewa da kyar ya iya ware idon sa dan barchin daya masa yawa picking call ɗin yayi yana faɗin wae dan Allah Yusuf me namaka ne da kake ta’kurawa rayuwata “Yusuf yace amma gaskiya Aiman baka kyauta ba dan Allah menene hakan wato ma barchi kaje kake koh to kazo mutafi ɗau’rin auren lokachi yayi chewar Yusuf, a fusache Aiman yace “bazan jeba yana yana kai karshen maganar batare daya jira amsar yusuf ba ya katse kiran yayi wurgi gefe da wayar ya chigaba da barchin sa

    Yusuf kuwa Aiman na katse kiran ya juya jiki ba kwari ya koma chikin palon a zuchiyar sa yana faɗin wlh yau Aiman da nine yayan ka da sai nayi maganin ka, wan nan wani irin wulakanchine kan chine sae kace ba tare suka taso da Hisham ba a sanyaye ya shiga chikin palon, Hisham na ganin sa yace”Aiman ɗin yace bazai zo bako,shiru Yusuf yayi dan ban san amsar da zai bawa Hisham ba kunyar haɗa ido da Hisham ɗin yake ji, dafa kafaɗarsa Hisham yazo yayi yana faɗin karka damu yusuf nasan halin ku gaba ɗaya SO duk wani abun daya da suke gudun zuwa aure nawa nasa,ni ban ma taba tunani daman zaku so aure naba,kadai na damuwa ngd sosai da zuwan da kukayi, kasani DON da Aryan Bawai basu sona bane yasa suka ki zuwa jiya da daddare DON ya turomin 1m a matsayin gift haka Aryan ma 1m ya turamin to kaga bawai basa sona bane kawai sudai a nasu ganin dakuma tunanin su duk wan da ya raɓi mace to yaza mai rauni sukuma kasan basa san mauni sunfi san kullun su ji su zam zam,”murnushi kaɗan yusuf yayi zai yi magana Hisham yace “No badai yanzuba, yanzu kam muje lokachi yayi ana jiran mu, jerawa sukayi gaba ɗayan su suka fito harabar gidan,
    su yusuf suka shiga motochin da suka zo dasu Hisham kuwa yashiga nashi motar,suka yiwa motochin key, security ya wangale masu gate da gudu suka danna hanchin motochin waje sosai suke gudu dan sunyi latti kai tsaye babban masallachin jummaa suka nufa a harabar masallachi sukayi parking dub bannin jamaa ne suka halak chi ɗaurin auren kama daga minister’s governors members har shugaban kasa muhammadu buhari yazo ɗau rin auren dashi da Shugaban kasa mai jiran gado tinibu, misalin karfe 2 dai dai na rana dubbanni jama’a suka she’da ɗau rin auren Hisham Nasir alkali tare da matar sa ilham Abdussalam, ana gama ɗau rin aure Yusuf ya dawo chikin mota da sauri dan yaji jama’a nata faɗin ina yayan Abubakar saraki ma sunzo bikin, yana zaune chikin mota yana jin jama’a na ta neman family Abubakar saraki,amma yayi kamar bar ji ba, buɗe kofar motar da Yusuf ke chiki ango Hisham yayi yashiga ya zauna yana faɗin “yanzu Yusuf abun da kayi ka kyauta eh ” ɗaure fuska Yusuf yayi yace to me kuma nayi “ka fini sanin me kayi ae ka dubi yan da jama’a ke naman ku kuzo kuyi hoto kowa Burin sa yayi hoto da family Abubakar saraki, amma ka watsa musu kasa a ido koh “kaga Hisham idan kagama dana ka jama’a mutafi dan ni yanzuma zan wuche kano, Hisham zaiyi magana Khalid ya buɗe kofar motar yashigo yana faɗin “Hisham me kuma ka zauna kake a nan baza kaje kutafi walimar bane “yanzu Khalid kuna nufin da gaske baza kuje walimar nawa ba Hisham yayi tambayar yana kallan fuskar Khalid, Khalid zai yi magana Yusuf ya riga shi da chewa “gaskiya ba zamuje ba ae nafaɗama iya ɗau rin aure kawai mukazo dan haka yanzu zamu wuche tun da angama abun daya kawo mu, shiru Hisham yayi yana tunani, ganin yanayin da Hisham ya shi gane yasa Khalid chewa, ” No Hisham dole zamuje walimar taso muje ga jamaa na chan na jiran mu,jiki ba kwari Hisham ya fito daga motar Khalid na rike da hannun sa suka bar Yusuf a chikin motar,

    Fito Yusuf yayi ya kira sojojin sa tare da basu umarnin akan su wuche Airport dashi, da sauri suka shiga mota suka wa motochin key suka bar masallachi sae tsaye Airport suka nufa, jirgin kasuwa Yusuf yabi yabar wa su Khalid jet ɗin Aryan a Airport ɗin tare da sojoji 2 ya tafa ya nar biyu su taho dasu Khalid,

    Karfe 3:45 jirgin su ba yusuf ya sauka a malam Aminu Kano international Airport,bai sanar da kowa zu’wan nasa ba ba wan dayazo ɗaukan sa motar haya suka hau shida sojojin nasa suka nufi gd, a bakin gani gidan sarki mai motar ha’yan ya ajiye su sauƙa Yusuf yayi ya biya sa kuɗin sa yanufi chikin gd sojojin na biye dashi, ɓangaren sa yanufa natare daya shiga chikin gd ba a bakin ɗan karamin gate na shiga ban garen nasa sojojin suka tsaya shi kuma ya wuche chiki, wanka yayi a gur guje ya zura jallabiya ya kwanta ba jimawa barchi yayi awan gaba dashi

    Aban garen su Khalid kuwa ansha walima duk chikin su Khalid ne kaɗai ya halak chi walimar karfe 4 dai dai a ka tashi taron, wajen holl ɗin Khalid yafito da sauri yana kiran layin Yusuf, wayar tayi ta ringing sai da ta kusa katsewa Yusuf ya ɗaga chikin muryan barchi yace,”hello “ina kake ne Yusuf lokachin tayi fa yayi “ina kano mana ” kano kuma Khalid ya tambaya yana riƙe haɓa “wani dogon tsaki Yusuf yaja yana faɗin kaga Khalid dan Allah ka kyale ni wlh bar chi nake kata dani ” to yanzu Yusuf mota kake so mubi zuwa kano ne kokuma me menene dazaka dafi kabar mu “oh my god nima Khalid bada jet na zaba jirgin kasuwa nabi jet ɗin na Airport na bar muku, yana gama faɗin hakan ba tare daya jira amsar Khalid ba ya katse kiran, bin wayar da kallo Khalid yayi yana faɗin ya Allah ka shirya min yaran bappa ba mutane ne sai kache wasu aljanu bazaka taba gane kan suba in sun juya ba mai iya juyo su, layin Aiman yafara kira again har ta katse Aiman bai ɗaga ba, tsaki Khalid yaja yasake kira, wayar nata ringing har ta kusa katsewa Aiman yayi picking, “ina kake Aiman Khalid ya tambaya a fusace, chikin muryan barchi Aiman yace ” wai dan Allah menene naha bazaku bar mutun yayi bar chin sa ba “au barchi ma kake ke nan to wlh sai dai ka kwana a Abuja dan tafiya ta,zanyi, wani dogon tsaki Aiman yaja yana faɗin to a sauka lfy san nan ya katse kiran, Khalid kamar yayi wurgi da wayar dan haushi haka yasake hakura yafara neman layin Ahmad kira ɗaya Ahmad yayi picking ” ina kake chewar Khalid “haba Khalid ni karamin yaro ne da zaka min irin wan nan tambayar, a fusace Khalid yace to wlh idan ba kazo Airport nan da 20 mnt ba tafiya ta zanyi na bar ku ” to yaya Khalid a Allah ya sare hanya yana kai kar shen maganar ya katse kiran, a fusache Khalid ya juya yanufi motar su yana faɗin wlh ku kam idan mutun ya biye muku zaku kashe sa da bakin chiki, chikin mota yashiga driver ya ja motar da gudu suka nufi Airport, abun ma maki ko da yaje Airport ɗin zaune yasamu Aiman da Ahmad chikin jirgin suna jiran sa dan bakin chiki ko sannu bai che musu ba ya shiga jet ɗin shima ya zauna suma ko sannu basu che masa ba har jirgin su ya ɗaga

    Karfe 6 na yamma dai dai jirgin su yayi landing a malam Aminu Kano international Airport kano basu wani ɓata lokachi ba suka fito shiri suka tsaya sai yanzu suka tuna basu sanar da zu wan su ba wan daya zo ɗaukan su wuche Aiman yayi ya fita Airport ɗin ya tari motar haya yashiga abunsa, ganin Aiman shiga motar haya ne yasa suma suka fito suka tari motochi biyu na haya suka hau suna nufi gd a bakin gate sukache da mai motan ya tsaya suka sauka,suka Biya shi suka nufi chikin gd,kowa ya nufi ɓangaren sa Khalid kuwa yanufi babban gate ɗin ya shiga chikin gd a dai dai bakin gate ɗin ya haɗu da Umar da haidar sosai suma suke kama da su yusuf ko ba’a faɗa ma ba kasan kannen sune “kai haidar ina yusuf Khalid ya tambaya yana kallan fiskar haidar “haidar yache nima ban sani ba yaya Khalid daman yaya yusuf na gidan nan na,juyo da kallan sa Khalid yayi kan Umar dake tsaye yana mur tuƙe fiska “kai Umar awani ban gare Aunty farida take,kara ɗaure fuska yayi yace “kai yaya Khalid dan Allah ka shiga chiki ka duba mana mu ka daina tambayar, mu tana gama faɗin haka yaja hannun Haidar suka nufi waje, baki buɗe Khalid ke kallan ikon Allah a zuchiyar sa yake faɗin, gaba ɗayan su ƴa’ƴan bappa halin su ɗaya ba yaran ba ba man yan ba, juyawa yayi shige chikin gida,

    Wani katafaren Falo na Al’farma Khalid ya doka sallama,haɗuwar falon ya zarce tunanin me tunani yaji komai na furniture,wasu hadaddun Sofa set ne,Launin Milk colour,masu numfashi,a tsakiya kuma akwai Sofa tabls,daga gefen Hagu,Tv stand ne,baka jin sautin komai sai Sanyin A.c dake ratsa sassan jiki, yan matane 3 ke tsaye a tsakiyar palon suna goge goge da alama kuyangu ne,har kasa suka duƙa suka gaida Khalid fuska ba yabo ba fallasa ya amsa yana tambayar su “ina Ammi, “tana chikin ɗaki suka amsa masa, bai jira sun kai karshen maganar ba ya haura stair case ɗin,wani ɗan karamin haɗaɗɗen palo ne a saman mai ɗauke da sofa set 1 ash colour atsakiya kuma a kwai sofa table gefen dama kuwa wani makekiyar Tv awajen,palon ɗauke yake da ko’fofin betroom’s 4 a chikin sa,babu kowa a palo sai sanyin A.c dake tashi bakin kofar betroom ɗin Khalid yanufa sallama yayi ya gyara tsayuwar sa yana jiran a masa izinin shigowa almost 7 mnt kafin a amsa masa sallamar tasa tare da izinin shigowa, tura kofar yayi ya shiga

    Wata kyakkyawa mata che sosai, kamannin ta ɗaya da DON,fuskarta ɗauke da murmushi,a zaune take saman tulu irin na gidan sarauta,babbar macace A ƙalla tayi 45 years,irin hajiyoyin nan ne wanda naira ta zauna masu,jikinta na sanye da tsadadden cord lace,wanda akayi mata bubu gown dashi,duka hannayenta da wuyanta,Kayan adone na Zallar zinayi, karisawa chiki Khalid yayi ya zauna a kasa a gaban ta,chikin ladabi da girmama,yace “barka da hutawa Ammi,shafa kansa Ammi tayi yace “baba saukar yau she “yanzu nan muka zo Ammi “to zuwa babu sallama,ina sauran yan uwan naka, “prince da Aryan basu zo ba suna London “ni basu nake tambaya ba ina ruwa na dasu,murmushi Khalid yayi daman da gangan ya kawo wa Ammi zan chen DON “baba ba kache komai ba ko dai kai kaɗai kazo ne “aa Ammi ni da su Yusuf ne amma ae kin san halin su ni ko in da suke ma ban sani ba “to ka sanar da Salma kun zone “aa Ammi kamar yadda bamu sanar ɗa ku ba haka ba wan da muka faɗawa “to yaka mata ku sanar da ita dan kaga kuka ɗai gare ta ku rinka tau saya mata “to shike nan Ammi zanyi yadda kika che amma ina Aunty farida “inajin tana bangaren Ummi,mikewa yayi yana faɗin to Ammi bari na dubo ta, “ok kawai Ammi tace, yana kokarin fita daga ɗakin wata kyakkyawar budurwa tashigo wadda a shekaru bazata wuche 16 ba kyakkyawa che sosai duk kaman nin su ɗaya dasu DON da gudu tatafi ta faɗa kirjin Khalid tana faɗin “oyoyo yaya Khalid, rungume Khalid yayi shima yana faɗin “oyoyo Auta oyoyo, ina kika fito hakan nan sai kam shi kike ” turo baki Zahra tayi tace daga wajen Aunty farida nake “ina take Aunty farida yayi maganar yana raba jikin sa da nata ” tana ɓangaren Ummi “ok to muje ki rakani “aa yaya Khalid ni tun danaga ka nasan ba kai kaɗai kazo ba, nasan su yaya prince ma sun zo ni bazan fita ba ina tsoran su “murmushi Khalid yayi yana faɗin”kai Auta tsoran me kuma ai dani zamuje “Allah yaya Khalid shiyasa nafi son ka dan duk gidan nan kai kaɗai ne mai sona ” aa Auta kowa na gidan nan na son ki “aa yaya Khalid badai kowa ba Aunty Maryam da yaya prince da yaya Aryan da yaya Aiman, “girgiza kai kawai Khalid yayi ya ja hannun ta suka nufi waje yana faɗin,Ammi mun tafi, Ammi dai murmushi kawai take tana binsu da ido..✍️

  • Duk karfin Izzata Book 1 Paga 3

    Duk karfin Izzata Book 1 Paga 3

    Episode 3*

    Kwan che DON yake chikin ɗan karamin pool nashi dake wajen sha’katawar sa na chikin ɗaki kwan che yake chikin ruwan gaba ɗaya jikin sa na chiki iya kansa kawai yabari a waje idon sa a lunshe kamar mai barchi, Aryan dake zaune saman ɗaya daga chikin kujerun wajen, yace “DON da alama fa maganar Yusuf zai zama gaskiya, batare daya buɗe ido ba yace “haba Aryan kayi magana da Yusuf ɗin ne “aa bamuyi ba amma dai da alama zan chen nashi zai iya zama gaskiya “hmm da kuwa sun gama dani sun kashe idan haka ne “to yanzu wani mataki zaka dauka Aryan ya tambaya yana kallan face ɗin shi, sai lokachin ya buɗe green eyes nashi ya sauke su akan Aryan, yayi da Aryan ɗin ma shi yake kallo ” Slowly ya furta banyi tunani a kai ba amma anjima zanyi magana da aunty farida Jinjina kai Aryan yayi yana faɗin “why baza kayiwa, Ammi maganar ba “hmmmm kai ma dai Aryan da wani magana kake,kafasan halin Ammi ni ko kallo ma ban ishetaba bare tasa baki a lamari na, shiru Aryan ya ɗanyi kafin yace “bari nizan gwada, yimata magana, guntun tsaki DON yaja yana faɗin “dama ka kyaleta dan ba sauraran mu zatayi ba nasani “eh to hakane kam amma dai yakamata tasa baki, mikewa yayi yana kokarin fita daga chikin pool ɗin,wayarsa dake ɗaki tafara kara, daukan towel dake jere awajen yayi yana goge jikin sa, yana faɗin “nifa inaganin kai tsaye zan yiwa Abba magana dan gaskiya a yadda nakeji yanzun nan bazan iyaba “to kana ganin hakan shine mafita ” kwarai kuwa, yayi maganar yana kokarin shiga ɗaki ”

    Katafaren gadon sa yanufa yasa hannu ya ɗauki wayar, dake kan gadon kafin ya ɗauki wayar kiran ta katse,dubawa yayi dan yaga waya kirasa ganin Khalid ne,yasa yabi kira ringing ɗaya Khalid yayi picking, sa wayar a H-free DON yayi ya ajiye saman mirrow, yana gyara lallausan haɗaɗɗen gashin kansa sai kyalli gashin ke yi kwanche har bayan sa,

    daga ɗayan ɓangaren Khalid yace ‘wai yanzu DON da gaske bakuyi kewar mu ba ko?,ko neme mu bakuyi ba, guntun tsaki DON yaja yana faɗin abun da ka ƙira ka tambaya ke nan, “kwarai kuwa shi nakira na tambaya “DON zai sake magana, Aryan yasa hannu ya ɗauki wayar yana faɗin ” dan Allah ku zauna a naija pls kar ku dawo dan da kuka tafi rayuwar tafi daɗi ma,dariya Khalid yayi kafin yache hakan ya tabbatar min da kunyi kewar mu ke nan, tun da kache mu zauna a naija hakan na nufin muyi sauri mudawo ke nan tsaki Aryan yaja kana ya jefar da wayar a kan gado ya juya yanufi hanyar fita ɗakin yana faɗin in kagama shiri kakirani awaya san nan ya fiche daga dakin, DON kuwa yana jin Khalid nata magana achikin wayar amma yayi banza, har yagama gyara gashin sa yatara ya ɗaure a baya san nan ya shafa mai mai kamshi da tsada ya fesa Dubai perfume mai kamshi sosai yanufi dressing room almost 30mnt san nan yafito, sanye chikin black jeans da blue t-shirt kayan sun kara bayyanar da Asalin kyan sa chi’kakkiyar surar sa irin na jaruman maza yakara bayyana, faffaɗar kirjin san nan a tsaye dam dam ga dam’tsen hannun sannan kamar zasu fashe a chike suke sosai laɓɓansan yayi ret sosai kamar yasa jan baki, sake fisa turare yayi a jikin sa yasa booth baki akafara sa sai wata dan ƙareriyar agogon daimon mai matikar kyau da tsada ya daura a hannun sa ba karamin kyau yayiba tamkar shiyayi kansa, a hankali ya tako kamar bai san taka kasan yanufi gaban, katafaren gadon sa hannu yasa ya ɗauki wayar sa yana bin screen ɗin da kallo a hankali ya buɗe baki kamar bayasan magana yace Khalid wai har yanzu baka gama surutun naka bane “a fusache Khalid yace gaskiya DON kai dan rai’nin hankaline “oh baka gama surutun ba kenan to pls in kagama ka katse kiran dan zan fitane,rai a ɓache khalid yake faɗin “zaka sanine wlh zamu haɗune, DON dai bai sake chewa komai ba, Khalid dayaji shiru sai ya katse kiran girgiza kai DON yayi yana faɗin na sani bani da masoya kamar ku nima kuma ina kaunar ku
    dau kan wayar sa yayi a nitse yanufi waje yana ko karin kiran layin Aryan kirayayi har takatase Aryan bai ɗagaba, waje gaba ɗaya yanufa, a dai dai baƙin kofar babban palo sukayi karo da Aiman da Ahmad, ko kallan inda suke bai yiba yabi gefen su zai wuche “wato DON bakayi murna da dawowar mu bakoh? chewar Ahmad

    Aiman kuwa wuche warsa yayi shima ko kallan DON ɗin bai yiba ya haura stair ɗin tsakiya yanufi ɗakin’sa DON kuwa chigaba yayi da tafiyarsa batare daya tankawa Ahmad ba, sai daya kai tsakar gidan batare daya juyoba yafara magana to daman wayache kudawo “rai a bache Ahmad yace ae daman badan kai muka dawoba dan kuwa inda dan kai nema wlh ko kallan kasar nan bazamuyi ba, DON dai bai sake chewa komaiba hasalima tsayuwa yaje yayi a bakin katafaren pool nasu na tsakar gidan, tsayuwa yayi ya juyawa chikin gd baya ya zura hannu a aljihu

    Rai a ɓache Ahmad ya juya ya nufi chikin gida a tsakiyar babban palo yachikaro da Aryan shima yana sanye da black jeans da white t-shirt yana daure da agogon daimon irin na DON, ya tara gashin kansa waje ɗaya ya ɗaure yazuba jelar abaya kamar wata mace ga gashin da tsawo, har bayan sa yayi kyau sosai kamar shiyayi kansa, ko kallon in da Ahmad yake bai yiba ya wuce yanufi waje, a kule Ahmad yafara magana “kudai bakuji daɗin halinkuba mutane ne kamar wasu aljannu yanzu haka kafin mu iso sai danayi tayiwa Aiman faɗa amma ko kallona bai yiba haba dan Allah yakamata ku chanza hali, Aryan dai wuchewar’sa waje yayi batare da yace komai ba, haurawa san benen Ahmad yayi yana surutai

    Waje Aryan ya nufa kai tsaye inda DON ke tsaye yanufa irin tsayuwar da DON yayi shima yayi ya zura hannu a aljihu suna fiskantar babban gate ɗin gd, gaba ɗayan su fiska kaman an aiko musu da sakon mutuwa, Almost 30mnt suna tsaye a haka babu wanda yache da ɗan uwan sa kala kuma ko motsi basuyiba a tsayuwar tasu
    jim kaɗan saiga Aiman yafito shima ya shirya chikin blue jeans da t-shirt ash yayi kyau sosai kuwa duk kansu agogon hannun su iri daya ne, gefen Aryan yazo ya tsaya
    juyawa DON yayi yafara tafiya ta ɓan garen dama, ganin DON yajuya yafa tafi yasa Aryan juyawa shima yabi bangaren hagu,Aiman kuma ya miƙi hanyar tsakiya yanufi bakin gate

    wani gate dake chikin gidan ta ban garen daman DON yashiga, wasu haɗadɗun motochi ne masu tsadar gaske awajen da alama nanne parking space na gd zubawa motochin ido yayi na ɗan wasu mnt, wasu jibga jibgan sojoji ne suka nufo inda yake tsayen a kalla zasu kai 10, kusa dashi suka ja suka tsaya hannu suka ɗaga suna sara masa, jinjina kai kawai yayi,batare dayayi magana ba kana yasa hannu ya musu nuni da motar da zai hau wata dan karekiyar motache kirar Marcedes Benz, black colour, wani matashin sojane mai jini jiki kato mai ji da karfi fari tas yanufi motar da DON yanuna ya shiga yawa motar key har,inda DON ke tsaye ya jawo mota, wani bakin soja kato dashi kak karfan gaske yazo da sauri ya buɗe wa DON kofar motar
    takawa yake sannu a hankali yashiga motar ya zauna, sara masa sojan yayi san nan ya rufe kofar motar, sojan yaja motar da ma tsakai chin gudu suka fita ta ɗayan gate ɗin

    A gaban Aryan da Aiman motar DON tayi parking, sauƙe glass din motar DON yayi, yasa hannu ya karbi bindigar da Aryan ke mika masa juyawa Aryan yayi yanufi nashi motar
    Aiman kuwa yana tsaye,suma kuma suna tsaye basu tada motochin nasu ba Almost 5 mnt suna tsaye shiru a nitse DON ya ɗago green eyes nashi yana kallan Aiman calmly yafara magana “kai inbazaka shiga bane muyi tafiyar mu, tsaki Aiman yaja yana faɗin “au ashe dai bazaku iya tafiya ku barni ba, na zachi nima wulakanchi zakumin DON dai bai sake magana ba sai ma mai da glass ɗin motar yayi ya rufe Aiman kuwa sai da ya sake tsai dasu for Almost 5mnt tukun nan yabude motar DON yashiga, ko kallan in dayake DON bai yiba yayiwa Abdol umarnin akan suwuche a nitse Abdol ya taɗa motar da matsakai chin gudu suka nufi gate, tun basu karisa security suka wangale musu katafaren gate ɗin a jere suka dan na hanchin motochin nasu waje, motar DON ne a gaba sai na Aryan ke bi masa sai wasu motochi 3 chike da sojoji, shinfi ɗadɗiyar titi suka miƙa

    kira ne yashigo wayar DON saida wayar takusa katsewa yachirota daga aljihu, Yusuf shine sunan daya bayyana a kan screen ɗin wayar, picking call ɗin yayi ya kara a kunnensa yana faɗin hello daga ɗayan ɓangaren Yusuf yace “bro ykk “a hankali ya furta normal kai fa “Yusuf yace nima normal, inaganin gobe zan shigo abun dayasa ban shigo yau ba kaga Abba yana da zama damu, Aiman da Ahmad sun gudu sunki jiran meeting ɗin , SO kaga bai kamata nima naki tsayawa ba jinjina kai DON yayi yana faɗin “eh hakane amma kayi amfani da lokachin ka dan lokachi bata jira sai dai ajirata “kai DON tun munayara kake yawan faɗa mana haka inshaa allah zamuyi amfani da lokachin mu, ” good kawai yace san nan ya katse wayar
    Aiman dake zaune Age’fensane yace akoi matsala fa DON ” batare da ya kalla inda Aiman yakeba yafara magana matsala batada wajen zama a family Abubakar saraki, tsaki Aiman yaja kafin yace “ta kanka kuwa zatama fara “koh? DON ya tambaya yana kokarin mai da wayar sa aljihu Aiman dan haushi bai ma sake maganaba

    Yola Nigeria

    Da kyar da kyar suke tafiya suna rike da kofi a hannun su kamar bazasu kai lbr ba tun safe yaran nan suke debo ruwa da cups amma har yanzu karfe 6 na yamma basu gama ba subhanallah

    da kyar diyana ta bude baki tafara magana hiyana bazan iya chigaba da ɗeban ruwan nan ba wlh yinwa nakeji numfashi na zai iya ɗaukewa “ki kara hakuri diyana Allah natare kinji, kiyi addua kawai adun halin dakika tsinchi kanki kuma ki kasan che mai godewa Allah sai Allah yakawo miki sauki “alhamdulillah alhamdulillah alhamdulillah Allah ngd, Allah mai kyauta mai kari ya ubangiji kadube mu da idon Rahma Allah ka kawo mana sauki ”
    ameen ameen diyana haka zaki rinkayi a kowanihali kika tsinchi kanki, diyana batare da ta sake magana ba tanemi waje kasan wata bishiya ta zauna, a’razane hiyana ke faɗin “aa diyana kitashi dan Allah mutafi inbahakaba kinfasan inna “wlh hiyana sai dai yau inna takashe ni, haba da wani kafa kikesan intafi nagaji nagaji yinwa nakeji ko ran dunan dake chikin gidan nan fa bamugama chikawaba barema har musa na dabbobi ta karisa maganar kamar zatayi kuka, hiyana zatayi magana sai sukaji magana ta bayan su da sauri suka juya gaba ɗayan su har suna haɗa baki wajen chewa “inawuni yaya bello “lfy me kukeyi anan da man’gariban nan ” ruwa muke ɗiba wa inna diyana tabashi amsa, “to ya kamata kutashi kutafi gida tunda kunga man’gariba ta kawo kai ga dajin nan da machizai, ina ruwan naku in taya ku ɗauka zuwa chikin gari, hiyana ta nuna masa kofin dake hannun ta tache gashi nan “to yau kuma da kofi kuka koma debo ruwan ne ina boket na ɗiban ruwan naku, da sauri diyana tace buba ne ya fasa mana boket, inna kuma tache mukoma debowa da kofi, girgiza kai bello yayi yana faɗin kuchigaba da hakuri kuna addua inshaa Allah, Allah zai kawo muku mafita amma dai yanzu kutashi kutafi gida
    “da kyar diyana tamike daga zaman datayi yaya bello yayi gaba su kabi bayan sa tafiya suke kamar babu jini ajikin s,Juyowa bello yayi yana faɗin “ga gyada ku karba kuchi yanzu na chiro a gona yayi maganar yana mika musu ledar gyaɗan dake hannun sa chikin ladabi hiyana ta ansan musu gyadar tana faɗin mun gode murmushi kawai bello yamata batare daya amsaba ya juya ya chigaba da tafiya,suma suka chigaba da tafiya da kyar da kyar har suka fito chikin gari, bello ya nufi gidan sukuma suka tsaya a kasar bishiya mangoron kofar gidan nasu, suka fara chin gyaɗar da yaya bello yabasu

    kinsan me hiyana naso ache gyadar nan dafaffache “au yanzu diyana hakanma baki godewa Allah ba karki manta fa tun safe fa ba abun da mukachi, kuma babu wanda ya tausaya mana yabamu wani abu dan kin’samu yanzu yaya bello yabamu gyada shine zaki waniche da dafaffache koh, to kije kidafaɗin, in bazaki iyachi hakaba sai kibari dan bawanda yamiki dole “aa hiyana abun ae bafaɗa bane kawai daga faɗin ra’ayi na “wan nan ba ra’ayi bane diyana rashin godiyar Allah ne kawai, kuma kullun ina faɗa miki kirinka godewa Allah a duk yadda kika samu kanki “to kiyi hakuri hiyana nayi kuskure alhadulillah Allah nagodema dakaba mu abun da za mu sa abakin mu “to kokefa yanzu naji magana “la hiyana kingafa kamar lamrat che ke zuwa diyana tafaɗa tana ɗan murmushi ” da sauri hiyana ta juyo tana kallan inda diyana ke nunawa “itache wlh mujirata ta karaso sai mushiga gd tare koh

    Gyara tsayuwar su sukayi har lamrat ta kariso, sanye take da kayan fulani farache tas itama mai dogon hanchi kamannin’ta ɗaya da hiyana sai dai idon su ba iri ɗaya bane idon lamrat baki ne idon hiyana kuma blue ne lamrat bazata wuce 13 years ba ” lamrat kindawo chikin harchen fullanchi diyana tayi maganar ” lamrat tace eh Aunty diyana nadawo “Allah yasa kin sayar da nonon chewar hiyana “eh aunty hiyana nasayar dukka “murmushi diyana tayi tana faɗin alhamdulillah nagodewa Allah dayasa kika sayar yanzu kinga inna bazata bugekiba ” nifa aunty diyana duk dukar da inna takemin bai dameni’ba nidai kawai bansan naga tana bugun ku,in nika’ɗai zata yita bugu bazan damuba “to aimuma hakanne bamusan inna ta bugeki ya’fimana tabuge’ni nida diyana tabar ku ke da amrat “hmmm hiyana yakamata mushiga gd kunji anfara kirar sallar mangariba koh chewar diyana ” hiyana tace gaskiya kam mutafi tayi maganar tana mikawa lamrat ledar gyadar dake hannunta “aa Aunty hiyana nasan tun safe baku chi komai’ba, ni kuma kinga bintu tabani abinchi awajen talla kuchi kawai ” hannu hiyana tasa aledar ta debo gyadar ta mikawa lamrat tana faɗin abinchi daban gyada ma daban ” lamrat tasa hannu ta amsa gyadar kana tayi godiya haka suka jera har chikin gida

    da sallama suka shiga innar tasu na tsakar gida tana zaune ga amrat zaune a gefen ta, tana tuka mata tuwo, wuchewa kichin hiyana da diyana sukayi dan juye ruwan dasuka ɗebo lamrat kuma tazo ta sugunna a gaban inna ta chiro kudi tamika mata
    inna ta karba ta irga kudin san nan tace “yau Allah ya rufa miki asiri kitashi kije ki daukoh wanke wanke kimani,murya na rawa lamrat ta fara magana “inna dan Allah kibari nayi sallah dan wlh ko a’zahar da la’asar banyiba ga kuma mangarib.. bata karasa maganarba ta’farajin saukar duka, da karfi tafara ihu tana faɗin dan Allah inna kiyi hakuri, da gudu diyana da hiyana suka fito daga kichin ɗin sukayo wajen inna suka duka kasa suka kama kafarta suna faɗin inna dan Allah ki kyale ta mu ki dakemu a madadin ta dan Allah inna kiyi hakuri, kafa inna tasa ta shuresu ta ɗau koh itachen a chikin wuta a murhun da amrat ke tuka tuwo tafara bugun su dashi, suna ihu kamar ran su zai fita, amrat na tuƙa tuwo tana kuka, haɗesu inna tayi tamusu duka mai isar duk ta gun bura musu jiki, zama tayi a saman dutse tsakar gidan tana mai da numfashi, “ke diyana ke da hiyana kutashi kutafi ɗiban ruwan ku wlh tun ban tashi na ɓaɓɓala ku ba chikin tsawa inna tayi maganar ke kuma lamrat kitashi ki kama aikin dana saki, ba kun che bakuji ba to wlh zan gyara muku zama a gd nan

    da kya hiyana da diyana suka mike ga yinwa ga gajiya ga wahala ga duka gashi ko sallar azahar basuyiba ga mangariba tayi ga dattin da jikin su yayi haka suka mike suka dauki cups ɗin suka nufi waje suna hawaye lamart kuma tamike tanufi kichin ta tattara wanke wanke ta fito ta ɗebo ruwa ta fara wanke wa tana kuka mara sauti

    Misalin karfe 9 na dare,tafiya suke achikin duhu suna kuka suka shiga chikin dabbobin su, suka juye musu ruwan suka fito, diyana ta tsaya akusa da bishiyar mangoro kofar gidan su A gala baice hiyana tace “diyana muje saura mana sahu biyu ne ae “wlh hiyana ba zanjeba Allah sai dai inna ta kasheni yau tayi maganar tana kokarin zama awajen “to shike nan kizauna a nan kihuta bani kofin naki naje nadebo har da rabon ki, amma dan Allah karki koma gida dan in kika koma nasan inna zata buge ki, ki zauna har nagama, ɗebowa sai mushiga gida tare, diyana dai ko magana takasa jin hiyana kawai take,
    juyawa hiyana tai chikin duhu tanufi hanyar rafin, diyana kuwa kwanchiya tai a kasar itachen ba jimawa barchi ya dauketa, hiyana tana tafiya chikin kun gurmin dajin nan tanata surutu ita kaɗai,” ya Allah kaba mu ikon chin wan nan jaraba wan Allah ka mikarma na da bappan mu yafara takawa da kafarsa ya Allah kajikan innan mu ya allah kakaremin yan uwana Allah mungode mungode alhadulillah alhadulillah, Allah karkabari a ɗaura aure na da buba ba’nason sa ko kaɗan, wayyo Allah na wai meyasa bappa ya Auri inna habiba ne meyasa bai yi zaman sa haka nanba tunda dai shi da kansa kullun yake chemana baya santa to meyasa ba zai che tatafi gidan suba, wayyo ni hiyana ya zanyi Allah kadubi mu da idan rahma, hakadai hiyana tayi ta addu’oe da surutanta, harta karisa ɗebo sauran sahu biyun dasuka rage,

    tadawo wajen da diyana ke kwanche kasan itachen, tafara kiran sunan ta, wajen duhu ne bata kallon komai,”diyana kitashi mutafi gida nagama ɗiban ruwan, shiru diyana bata amsa ba kara kiran su nanta hiyana tayi nanma tasake jin shiru, da saurin hiyana ta duƙa kasa tana laluɓe kozata tabota amma shiru bataji diyana awajen ba, Arude tamike zubur tayi chikin gida da gudu, ɗakin su ta faɗa ko sallama babu, amrat da lamrat tasamu zaune suna fiskantar ɗan fitillar kwan dake ɗakin sunyi jugum jugum “lamrat ina diyana,hiyana ta tambaya tana zaro blue eyes nata waje “chikin rau’nanniyar murya lamrat tace ban ganta ba, hiyana zata sake magana amrat tamiƙe ta riƙe hannun tana hawaye chikin muryan kuka tace “Aunty hiyana yinwa nakeji chikina chiwo yakemin sosai, dan Allah kine momin abunda zanchi ko kaɗanne hiyana batasan lokachin da hawaye zuba wani na bin wani yafara zuba a kuma’tun taba, da wanne zata ji gaji’yar ɗebo ruwa ko kuma yinwa, ko ɓa’tar diyana, gasu amrat na kukan yinwa, riko hannun amrat ɗin tayi chikin dashe war murya tace “jeki zauna kinji yanzu zannemo miki abinchi duk inda yake “to kawai Amrat tace san nan takoma wajen zamanta ta zauna, da sauri hiyana ta juya tafito daga ɗakin tana tunanin mugunta irin na inna watarana su suke girka abinchin gidan nan amma inna bata basu sai ran da taga dama ko bappan suma babashi take ba, kai Allah wadaran zuchiya irin na inna

    Da wan nan tunanin tanufi ɗakin inna bakinta ɗauke da sallama, kwanche ta isko ta a kan figaggiyar gadan chiyawar’ta ” bata amsa sallamar ba kuma idanta biyu Murya na rawa hiyana tafara Magana “inna banga diyana bafa “to idan bakiga diyana ba sai me ina ruwana dawata diyana zaki’tashi kifita min a ɗaki’ne ko sai na tashi na babballaki, mikewa hiyana tai tafita tana tunanin tafaɗawa bappa ne kuma intafada masa ma hankalin sa ba karamin tashi zai’yi ba, gashi ba lfy ne da shiba, kai gwara dai naje tanemo ta da kaina basai na faɗawa bappa ba, da wan nan tunanin nufi waje.

    KANO

    Aunty farida Ammi Ummi da Aunty amarya sai Khalid da Zahra zaune suke awani katafaren palo mai girman gaske, mai ɗauke da manya manyan Sofa masu matikar kyau da tsada ga laushi set biyu launin milk colour, ga wata makekiyar Tv daga gefe, sai table ɗin chin abinchi mai ɗauke da gujeru 12, idan nace zan tsaya zayyana muku kyan palon nan tofa zamu kwana a nan, zaune suke shiru,sallama Fahad yayi ya shigo palon zama yayi a saman 1str yana gaidasu Ummi, da sallama haidar da Umar ma suka shigo da alamadai family meeting zasuyi Almost 20 mnt suna zaune ba wanda yake magana kowa da abun da yake daga masu latsa waya sai mai daddan na laptop “wayar Aunty farida che yayi kara alamar shigowar kira, ɗaukar wayar tayi tana bin screen ɗin da kallo,ganin sunan my prince, yana tamiƙe da sauri tayi waje,daga gefen bakin kofar ta waje ta tsaya san man tayi picking call ɗin tare da kara wayar a kunnenta tace “hello prince daga ɗayan bangaren DON yace “kun gama meeting ɗin ne “aa yanzu dai zamu zamu fara Abba muke jira yafito “to amma kina ganin zamuyi nasara kuwa “kai prince kabari dai idan mungama mayi magana, naji muryan Abba yafito bata jira amsar’saba da sauri ta katse kirar, ta koma chikin palan, wajen zamanta takoma ta zauna
    Abba kyakkyawar dattijo ne mai chike da kalama, kallo ɗaya zaka masa ka gane duk yaran gd ka’maninsa suka yo farine tas mai dogon hanchi ga manya manya ash eyes yana da dogon gemu da lallausan saje, gashin kansan nan a kwanche kamar na larabawa zama yayi saman sofa mai ma zaunin mutun1 bin yayan sa yake ɗaya bayan ɗaya da ido yana kallan su shiru palon yayi Almost 5mnt san nan Abba yayi gyaran murya, yafara magana ina Aliyu yake,yayi tambayar bai kai ga rufe baku ba uncle Aliyu yashigo da sallama sanye yake chikin wata dakakkiyar shedda fara tas mai kyau da tsada, kaman’nin sa ɗaya da Abba, gaba ɗaya palon har suna haɗa baki wajen amsa masa sallamar da gudu Zahra tamike ta nufe sa tana faɗin “oyoyo uncle Aliyu oyoyo ta faɗa jikin sa, rungumeta yayi shima tana faɗin “oyoyo autar’mu oyoyo autar’mu san nan ya zare daga jikinsa ya rike hannunta suka nufi wajen Abba saman sofan dake kusa da Abba uncle Aliyu ya zauna tare da zaunar da Zahra a gefen sa, a nitse uncle Aliyu yace ina kwana yaya da fara’a Abba ya “amsa lfy, juyowa yayi ya gaida su Ammi, suma da fara’a suka amsa masa san nan matasan gidan suka fara gai dashi yana amsa musu ɗaya bayan ɗaya da murmushi a face nashi
    A nitse Abba yafara magana to ku bani hankalin ku nan,duk suka nitsu suka zubawa Abba ido suna saura ren sa chigaba da magana Abba yayi “nataraku a nanne dan inasan magana daku gaba ɗayan ku amma baku gama haduwa’ba dan haka farida ki kiramin sauran yan uwan naki awaya kifada musu duk Abun da suke subari nan da rana ita yau ina bukatar kowa a nan,”
    Aunty farida zatayi magana Abba yaɗaga mata hannu aa farida umarni’ne kuma banasan ɗaya daga chikin ku yamin wata magana kutashi kuje zamu sake magana rana ita yau
    sai yanzu nagane aina su DON suka ɗau koh idan sunyi magana basa chan zawa ashe awajen Abba ne tab aiko akoi kallo wayyo

     

    *DUK ƘARFIN IZZATA*

    _💖Story And Written💖_
    ⬇️
    *Star Lady*

    💖 The talent troupe writer’s💖

    Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

  • Duk karfin Izzata Book 1 Page 12

    Duk karfin Izzata Book 1 Page 12

    *Star Lady*

     

     

    Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

     

    *Episode 12*

    A zafafe Aryan yace ke kima mutane shiru a nan “idon kowa na palon yadawo kan Aryan ya turnuke fuskar nan tamkar an aiko masa da sakon mutuwa ” Yusuf da Khalid kuwa sai murnushi suke “Abba ya dube’sa kana yace “ina ruwan ka, kai takewa hirane, chigaba da faɗamin ƴata ya kukayi kasanima ko dashi zaayi bikin ” Aryan zai sake magana idonsa yasauka kan aunty amarya dake wurga masa mugun kallo ganin hakan yasa yamike yabar palan

    …..dariya diyana tayi san nan tace “Abba nifa matar sojane soja zan aura irin mugayen sojojin nan masu manya manya bindiga ” Ammi ganin diyana tafara sakin layi yasa tamata magana da harchen fullanchi tache tatashi suje suyi sallar mangariba ” ba musu suka miƙe suka nufi ɗakin su ” Aunty amarya mikewa tayi tafiche sai huchi take ” mai martaba yace dasu Yusuf kutashi mutafi masallachi mikewa sukayi gaba ɗaya matasan suka fiche ” Ammi ta dubi Ummi tace yakamata muma muje muyi sallah Koh, atare suka mike suka fita

    Misalin karfe 8 na dare gaba ɗayansu sunhadu a palo dan chin abinchin dare amma banda DON da kuma Aryan basuzoba ” yusuf ne yakalli diyana yace sister jiki dubo yaya Aryan a daki kiche yazo muchi abinchi ” to diyana tace tare da mikewa zata fita ” kamar daga sama sukaji Aunty amarya tana faɗin ke dawo kizauna Umar tashi kaje ka kirashi ” kallo mai martaba yusuf yayi kana yajuya ya kalli Khalid zaiyi magana ke nan Abba yarigasa da chewa “jeki kirasa diyana da sauri ta fita daga palon dan ganin mugun kallon da Aunty amarya ke mata ” farinchikine ya lulluɓe Khalid da Yusuf sai murnushi suke

    Da sallama tashiga palon babu kowa kai tsaye tawuche betroom batayi sallama tashige kwanche yake a kan gado idansa a lunshe har bakin gadon taje ta duƙa a nitse tace yaya Aryan shiru bai amsaba dataji shiru sai tamike ta zauna a gefen gadon tasa hannu tana bubbuga hannunsa tana kiran su nansa, shiru shiru bai amsaba baikumayi motsiba ganin hakan yasa, tasa hannunta tana kokarin buɗe idon’sa dakarfi ” a zafafe ya damki hannun nata batare daya buɗe idon ba ” aruɗe take kokarin kwache hannunta dan tagudu ” slowly ya ware manya manya ash eyes ɗin nan nasa akan face ɗinta ” sanye take chikin jallabiya baki still dai kanta ba ɗan kwali ” a tsorace tasoma magana dan allah kayi hakuri allah bazan sakeba ” kara daure fuska yayi sosai yafara Magana, meyakawoki ɗakin nan ” Abba ne yace nakiraka tabashi amsa ” jinjina kai yayi tare da mikewa zaune ya saki hannun nata, aiko kamar jira take yasaketa ta yunkura aguje zata sauƙa gadon ” a zafafe Aryan ya damkoh gashin kanta ya jawota baya har saida tafaɗa kan chinyarsa ” kware baki tayi zatayi ihu yasa hannu da sauri ya rufe mata baki yana kallanta ” girgiza masa kai tafarayi tana hawaye ” calmly yafara magana wani uncle nakune yace yana sonki kuma dayace yanason naki mekikache masa yayi maganar tare da zame hannunsa daga bakinta dakuma rikon dayayiwa gashin kanta ” chikin shesshekar kuka tace uncle Omar kuma ni bani yafaɗawaba Zahra ya faɗawa kuma ninache’wa Zahra tafaɗa masa soja nakeso soja zan aura ” kara waro ido waje Aryan yayi yana kallanta yadda take magana a nitse yama rasa me zaiche mata ” bayan tagama magana’ne ” yace to tashimin a kafa” da sauri tamike tana kokarin sauka daga gadan ” ai banchi ki sauka bakoh chewa nayi kitashimin a kafa kawai juyo nan ki kalleni kuma ki saurari abunda zan faɗamiki chewar Aryan ” a hankali ta gyara zamanta a kan gadon san nan tajuyo tana fuskantarshi ” Aryan yace sau’nawa yanzu inamiki magana a kan ɗan kwali eh, ” shiru tayi kana ta sunkuyar da kai ” meyasa bakyajin maganata meyasa kikesan ɓatamin raine eh ” ɗago kai tayi ta ɗan kallesa taga ita yake kallo a hankali tace kayi hakuri zan rinka sawa ” jinjina kai yayi yana faɗin to meyasama bakisan ɗan kwali ne ” turo dan bakin nan nata tayi tana faɗin Allah yaya Aryan zafi nakeji idan nasa ɗan kwali gashinne yayi yawa shiyasafa nache ra nan ka askemin kaki ” shiru yaɗanyi kafin nan yace Aunty amarya na falone ” eh tana nan tabashi amsa ” ok to tashi kije inazuwa chewar Aryan ” da sauri tamike dan daman kamar a kan ƙaya take har takai bakin kofa kome tatuna saikuma tajuyo ta fashe da kuka” da mamaki Aryan ke kallonta” kuka take sosai gashi tana tsaye taki tafiya ” alama yamata da hannu a kan tazo ” ba musu tazo kusa da gadan ta duka tana kuka ” meyafaru kuma meyasaki kuka Aryan ya tambayeta ” chikin kuka tace innar yaya bello tafaɗamin idan nabari namiji yataba jikina to zansamu chiki shine kuma gashi kai kataba jikina ” Aryan baima san sanda dariya ta kubche masaba ” ganin yana mata dariya yasa tasake kara sautin kukan nata ” shiru yayi yana kallan yadda take rera kuka tsakaninta da allah yama rasa me zai chemata kusan 10 tukun nan idea tazo masa, ya sa hannu ya ɗago habarta kasa kasa yace kidena kuka ni ai yayankine ko nataɓaki bazaki samu chikiba amma idan kikayiwa wani namiji magana ko kikabari yataba hannuki tabbas zaki samu chiki ” da sauri tace to yanzu yaya Aryan bazan samu chikiba ” eh bazaki samuba ai nafaɗamiki ni yayankine babu abunda zaki samu dan natabaki ” mikewa tayi tana dariya kamar ba mai kuka yanzun nanba ” zuba mata ido yayi yana kallanta chan kuma yace sannu mai kuka da dariya lokachi guda ” hannutasa ta rufe fuska tajuya tanufi hanyar fita ” binta yayi da kallo har tafiche wani nauyayyar ajiyar zuchiya ya sauke san nan
    yamike yanufi toilet danyin wanka
    A gurguje yayi wanka yafito yasa farar jallabiya yafito yanufi palan mai martaba ” da sallam yashiga lokachin kuwa duk matasan sungama chin abinchinsu kowa ya watse sauran Ammi da Ummi sai mai martaba
    Zama yayi tare da gaidasu ” Ummi takira masu aiki sukazo suka zuba masa white rice an beans da steew yaji kaji sai wani ferfesu a ɗayan plate ɗin suka tura masa gabansa ” a nitse yafara chin abinchin ” mikewa Ammi tayi tanawa Ummi da mai martaba sai dasafe ” Ammi pls kifaɗawa yarinyar nan takawomin coffee dawuri dan inajin barchi chewar Aryan “to kawai Ammi tace san nan tafice

    A bangarensu diyana kuwa zaune suke a ɗaki zahra da hiyana sunna karatun boko amrat na karatun qur’ani lamrat na buga game a wayar Zahra Aunty diyana kuwa tana zaune gaban mirriow, wai taga wani kwalli a wayar zahra zatayi irinsa sai faman pente pente takewa fuskarta ” ba ƙarya tayi kyau sosai dan diyana daman akoi san kwalliya shiyasa ta dage takoyi kwalliya sosai awajen Zahra
    Bayan tagama kwalliyar ne, tamike tanufi wajen kayansawarsu wani wandon jeans blue ta daukoh da t-shirt pink tanufi toilet jim kaɗan saigata ta fito wow bakaramin kyau tayiba ga wandon ya ɗan kamata shape nata yafito sosai yaukam tatara gashin kanta ta ɗaure a tsakiyar, high heel blue ta daukoh kalan wandon tasa a kafarta diyana akoi san high heel sosai ” hiyana che ta ɗago tana kallanta kana tace diyana kwalliya da daddaren nan inazakije, gaba ɗaya su zahra ma suka ɗago suna kallanta ” babu inda zanje kawai dai yau naji inasanyin kwalliyar darene ” wow my diyana kinyi kyau sosai chewar Zahra ” Allah aunty zahra to pls ki ɗaukeni hoto mai kyau a wayarki kinji ” to zahra tace. San nan ta karɓi wayar daga hannun lamrat tafara yiwa diyana hotona ” da sallama Ammi tashigo ɗakin tasamesu sai hoto Zahra ke ɗaukan diyana girgiza kai kawai Ammi tayi kana ” tace ke diyana kije kikaiwa yayanku Aryan coffee yanzun nan ” to kawai diyana tace Ammi kuma tayi waje tanufi betroom ɗinta ” ya isa hotan haka Aunty zahra bari naje nakaiwa yaya Aryan coffee karna ɓata lokachi ya bugeni idanna dawo saiki kara ɗaukana wasu ” to kawai zahra tache ” juyawa diyana tayi tanufi hanyar fita hartakai bakin kofar fita saikuma ta juyo ta dawo ta daukoh dan karamin gyale pink tasa a kanta tafiche tanufi kichin ” a gurguje ta haɗa coffee ɗin ta ɗaukoh tanufo bangaren Aryan

    Da sallama tashiga palon babu kowa kai tsaye betroom ɗin tanufa basallama tashiga babu kowa a chiki dan haka tanufi kan table ɗin ta ajiye coffee ɗin har zata juya tafita saikuma idanta ya sauka kan hotunan Aryan dake kan drowar gefen gado ansasu chikin freme kanana,
    zagayowa tayi tawajen ta zauna a bakin gadon tasa hannu ta ɗaukoh hotu nan dukka ukun ɗaya shida don ne sunsa kakin sojoji ɗayan kuma shi kaɗai ne sanye da jeans baki da white t-shirt ɗayan kuma shida don da yusuf ne dukkansu da wandon sojoji ajikinsu da green t-shirt, shiru tayi tana kallansu chankuma tace kai ashe da gaskenefa hiyana nakama da wan nan mugun tayi maganar tana nuna don kai kuma yaya Aryan inshaa allah soja zan aura wanda zaimin maganinka da kai da bindigar taka, allah sarki yaya yusuf wlh a gidan nan shida yaya Khalid ne kawai mutanen kirki hakadai diyana tayita surutun ta ita kaɗai har ya isheta san na ta ajiye hoto nan tamike tajuyo zata nufi waje idanta ya sauka chikin nashi tsaye yake abakin kofar shigowa betroom ɗin ya harɗe hannu a kirji ya zuba mata ash eyes nashi kallanta kawai yake yakasa ɗauke kai
    Murya na rawa tace ina wuni yaya Aryan ” ajiyar zuchiya Aryan ya sauke san nan yakarisa shigowa ɗakin yazauna a bakin gado ” diyana naganin ya matsa a hanya yazo ya zauna a bakin gado ta watsa a guje zatayi waje saidai tamanta high heel tasa bazata iya gudu sosaiba,
    taku biyu Aryan yayi ya damki kugunta ta baya tsabar tsoro da razana yasa nunfashinta ɗaukewa ɗif ” jin jikinta ya sakine yasa ya riketa da kyau kana ya juyo da ita yana kallan fuskarta da alamar ta sume fa ɗaukan ta yayi ya kaita kan faffaɗar gadansa ya kwantar da ita, zubamata ido yayi sosai yana kallanta from head to toe wow ya furta a filli kana yace masha allah koba komai yaudai ansa ɗan kwalin nan shafa gefen fuskarsa yayi tare da sauke ajiyar zuchiya yajuya yanufi inda ta ajiye masa coffee ɗin
    Daukan cup ɗin yayi yabar plate ɗin yanufi saman sofa ya zauna yafara sha a nitse sai dayaga sha san nan yamike yanufi freig ruwan faro ya ɗaukoh yadawo kan gadan zama yayi a gefen gadan san nan yabuɗe robar ruwan ya tarfa a hannunsa ya shafa mata a fuska dogon numfashi taja tareda sauke nauyayyar ajiyar zuchiya a hankali tafara buɗe idanta karaf ta saukesu a chikin nashi dankuwa shima kallanta yake ” da sauri ta rufe idan ta tana faɗin dan allah yaya Aryan karka bugeni natuba bazan sake taba maka komai na ɗakin kaba ” wai ma menamikine dakike chemin mugu akoda yaushe chewar Aryan ” batare data buɗe idoba tace natuba bazan sake chewaba ” to idan kikasakefa ” da sauri tace kamin duk abun da kakeso ” kintabbatar inkinsake namiki kome nakeso chewar Aryan ” eh nayarda kamin kome kakeso amma dai yanzu kayi hakuri wlh barchi nakeji ” Aryan ya jinjina kai yana faɗin to buɗe idon ki, ki kalleni ” slowly tabuɗe idon still dai ita yake kallo ganin bazata iya haɗa ido dashi bane yasa ta juya idonta tana kallansama ” murmushi kaɗan Aryan yayi a’zuchiyarsa kuwa yana faɗin a shedai tanajin kunya ” jin yayi shirune yasa tace yaya Aryan intafi ɗaki ” kinasan tafiyane chewar Aryan ” da sauri tace eh ” ok to tashi kije dasafe zamiyi maganar danake san muyin ” da sauri tamike har takai bakin kofa sai taji Aryan yace ke, da sauri ta juyo tana kallansa ” a hankali yafurta kinyi kyau sosai dakikasa ɗan kwali ” murmushi tayi san nan tace to yaya Aryan tunda nayi kyau pls kamin hoto idan kamin ni kaɗai sai kuma kamana mubiyu ” ok to zokitsaya namiki ” da sauri ta dawo chikin ɗakin wayarsa ya ɗaukoh yafara daukanta hoto duk san hotonta sai da, da kanta tace to ya isa yaya Aryan saura nida kai kama ko guda ɗayane tare ” Aryan yace ok to zoki zauna yayi maganar yana nuna mata gefensa ” zama tazo tayi a gefensa ” ɗan karkatowa kaɗan yayi yarage tsawonsa ya haɗe kansu ya saita wayar yafa ɗaukansu hoto sai daya musu kala 10 tukun nan yace to jeki kwanta ” to tache masa san nan tamike tafiche daga ɗakin ” ajiyar zuchiya mai nauyi ya sauke san nan a fili yace Aryan waishin meyake damunkane shiru yayi yana tunani dayaga tunanin nan bawata mafita dazata bashi sai ya karisa hawa gadon kawai ya kwanta ya ɗauki remote ya rage gudun AC yayi shiru kamar mai tunani yana fuskantar sama har barchi ɓarawo ya ɗaukesa

    Diyana kuwa tana fita tayi bangarensu basallama kawai tafaɗa ɗakinsu zaune tasamu zahra a kan gado zahra naganinta tamike tana ” faɗin diyana lfy kika Jima allah dai yasa yaya Aryan bai bugekiba”guntun tsaki diyana taja san nan tace eh bai bugeniba” Alhadulillah zahra tace san nan takoma ta kwanta ” itama diyana kayan jikinta tachire tasa na barchi ta haugado tana faɗin hmmmm wato hiyana kam barchinta ma tayi koh ” to me zata zauna tamiki barchita zatayimana chewar zahra ” diyana bata sake magana ba saima juyawa datayi tana fuskantar yamma har barchi ya ɗauketa

    Misalin karfe 4 na asuba gaba ɗaya family sun haɗu suna sahur ban da don ” Aryan ya dubi diyana yace ke jeki kawomin coffee ” diyana na kokarin mikewa ” aunty amarya ta dakamata tsawa ke yizamanki bazata kawoba kuma daga yau nahana maganar coffee idan kannenka maza bazasu kawoma ba to kahakura da sha ” shiru palon yayi babu wanda ya tanka diyana kuwa tsayuwa tayi tarasa maganar wazata bi, idan taje takawo coffee aunty amarya zata hukuntata, idankuma bata kawoba yaya Aryan zai hukuntata kawai sai tafasa ihu ” gabaɗaya jamaa’ar palon suka ɗago suna kallonta ” a nitse Aryan yace kukan ya isa zokiyi zamanki kyale coffee ɗin ” ai tunbai gama maganaba ta zauna abunta takuma yi shiru ” dogon tsaki fahad yaja san nan yace darabon wlh nizan babballa yarinyar nan yanzu dan iskanchi me aka…. bai karisa baganarba sakamakon mugun kallon da Aryan ya wurgamasa ” aunty amarya kuwa mike tayi tana faɗin kai idan kagama kazo ɗaki inada magana da kai tayi maganar tana nuna Aryan san nan ta fice ” dogon tsaki aiman yaja san nan shima yamike yana faɗin dole nabar kasar nan gobe yayi waje ” mai marbata kam ido kawai yake binsu dashi ” Ummi tace ba akaiwa prince a’binchinsaba’fa ” Ammi tace to su tashi sukai masa mana ” fahad yamike yana faɗin barinaje na kaimasa san nan yayi waje

    Mikewa aryan yayi zaiyi waje ” Mai martaba yace inazaka ” alwala zanje nayi Aryan yabashi amsa ” ok idan mundawo masallahchin kasameni a ɗaki chewar mai marbata ” ok kawai Aryan ya amsa dashi san nan yayi waje ” mai martaba ma mikewa yayi yana faɗin to yakamata kuje kuyi alwala dan sauran 20 mnt afara kiran Sallah yana gama faɗin haka yanufi ɗakinsa ” mikewa sukayi da ɗai ɗai sukabar palon

    Misalin karfe 9 zaune take a chikin class nasu uncle nasu yashigo yana tambayat wacece fateema abubakar saraki ” da sauri zahra tace nine” oh to kifito zakuje duba uncle nakune bai da lfy kowani class zamu ɗauki mutun ɗaya ” to kawai zahra tace san nan ta ɗauki jakarta tafito sukayi waje da uncle nasu yan mata 7 tasamu tsaye a wajen tare suka jera har wajen motar makarantar suka shiga da gudu motar tabar makarantar ” suna tafiyane Zahra ke tambayar yanmatan wani uncle ne bai da lfy
    Sukache mata wlh suma basu saniba ” shiru zahra tayi batasake maganaba har suka isa gidan uncle ɗin driver na parking suka fito uncle Aminu yamusu jagora zuwa chikin gida ga mamakinta saitaga uncle Omar nefa nan tafa tunanin wai ba jiya suka rabu lfy’ba kodai accident yayine ga kafarsa duk bandeji gashi har goshinsa, tayi nisa chikin tunanin sai taji muryan uncle Omar yana faɗin fateema har dake a kazo ” eh uncle inawuni yajiki zahra tabashi amsa ” lfy fateema jiki da sauki ” to allah yakara sauki chewar Zahra gaba ɗaya suka amsa da amin san nan suka mike suka masa sallama yana musu godiya har suka fice sukaje sukashiga motar makarantar ta maidasu

    Misalin karfe 5 na yamma zahra hiyana diyana amrat lamat suna zaune a palon Ammi suna kallo ” hiyana tace lamrat kije kikawomin fura da nono a palon mai martaba dan na freig ɗin Ammi yakare ” hararar wasa Zahra tawa hiyana tana faɗin yanzu sai’kisha furar a gabanmu bazakiji kunyaba idan wani yashigo yaga baki a’zumifa ” murmushi kaɗan hiyana tayi amma saida ɗimple nata ya lotsa tace aa aunty zahra bafa a nan zansha ba ɗaki zantafi mana ” Zahra zatayi magana ” diyana tarigata dachewa to ina ruwan wani dake inbaki azumin ma ina ruwansu nifa wlh inniche koh har tsakar gida zanje inachin chingom ” baki buɗe Zahra da hiyana ke kallon diyana itakam ko ajikinta dan batamasan abun datake faɗinba kawai duk maganar dayazo bakinta take faɗi ” lamrat kuwa mikewa tayi tafita tanufi palon mai martaba ” daukoh fura biyu tayi da nono roba 1 san nan ta ɗauki kwarya yajuye nonon a chiki tajefa furar a chiki kwaryan san nan tasa ludayi ta dauka tafito tanufi part din Ammi ” daga nesa yusuf ke kallanta tana tafiya a nitse chikin kwanchiyar hankala sai murnushi yake ” tazo dai dai zata shiga ɓan garen Ammi tayi karo da haidar nono yazube masa ajiki ” wani wawan mari ya sakar mata a kumatu ” wani ƙara tafasa ta kwasa aguje tai chikin gidan kai tsaye palo Ammi tanufa ” shikuma haidar yanaganin ta tafi yaja doguwar tsaki yajuya zai wuche part nasu kamar daga sama yaji saukar mari shima, a razane ya ɗago kai, ” ido huɗu sukayi da Yusuf fuskar nan tamkar an aikomasa da mutu a kausashe yace metamaka kamareta eh ” murya narawa haidar yace kayi hakuri yaya yusuf wlh raina ne yabachi ” shoot up wai kubaku da tausayine eh yanzu kowani kagani zai mareta bazaka hanashiba to wlh idan kasake gigin taɓa yarin yar nan sai ranka ya ɓachi wuche kabani waje chewar yusuf ” jiki ba kwari haidar yawuche ” yusuf kuwa yabi bayan lamrat

    Da sallama yashigo balan kwanche kan kafar hiyana yasameta sai kuka take ” a nitse yace my baby taso kizo ” aiko tanajin muryansa tamike da gudu tanufeshi hannu yabuɗe mata tafaɗa kirjinsa tana kuka kasa kasa ” hannu yasa yaɗago habarta kasa kasa yafara magana ya isa haka kukan kinji goge hawayenki yayi maganar tare da ɗan sakinta kana yazaro hand’kee daga aljihunsa yamiƙa mata ” hannu tasa ta amshi hand Kee ɗin tagoge hawayenta” shikuma yarikoh hannunta suka fiche daga palon ”

    Su zahra dai baki bude suke kallan yaya Yusuf har ya fice rike da hiyana ” mikewa Zahra tayi tana faɗin lokachin shirya kayan buɗa baki yayi tayi gaba su hiyanama suka mike sukabi bayanta

    yusuf kuwa suna fita shida lamrat sukayi bangaren Ummi ” da sallama suka shiga palon ” Ummi dake zaune kan kujera mai zaman mutun biyu ta amsa da waalaikassalam, shigowa chiki sukayi yana rike da hannunta ” Ummi naganinsu tafara murmushi tana faɗin waya taɓomini lamra’ta Naga alamar tayi kuka ” murmushi yusuf yayi kana yace babu kowa shagwaɓa chekawai ” Ummi tace to taso kizo kusa dani ” da sauri lamrat ta mike takoma kusa da Ummi ” yusuf zaiyi magana sai aka kirasa a waya mikewa yayi yace Ummi inazuwa yayi waje.

     

    To a kwana a tashi babu wuya awajen allah yau jirginsu mai martaba yatashi zuwa Umrah gaba ɗaya yan gidan suntafi sauran yammatan Ammi kawai suma dan ba abasu hutun makaranta bane shiyasa dagasu sai masu aiki aka bari a gidan sai security dakuma wasu daga chikin sojojin yaya prince da yaya Aryan da yaya yusuf
    “yauma kamar kullun shirinsu sukayi tsab nazuwa school suka fito harabar gidan nantake drivers ɗin su, sukazo da gudu suka buɗe musu motochin suna shiga suma drivers ɗin suka shiga dagudu suka tada motochin suka bar gidan gudu suke da motochin sosai chikin ƙanƙannin lokachi suka isa school ɗin, suna parking su hiyana suka fito suka nufi wajen dasuke zama kafin a shiga class ” drivers kuma suka juya kan motochin suka koma gida ”

    misalin karfe 9 na safe bayan antashi break zaune suke sunata hirarsu awajen game na makarantar kamar daga sama sukaji jabir yana faɗin “hiyana taso muje, chikin tsiwa diyana tace wlh yaukam babu inda zataje Exam fa akeyi bata gama rufe bakiba taga jabir yaɗaga hannu a fusache zai..

    more comments an share

    *💫STAR LADY💫*

    💖The Talent Troupe Writer’s 💖

    *DUK ƘARFIN IZZATA*

    _💖Story And Written💖_
    ⬇️
    *Star Lady*

     

    Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

     

    *

  • Gabriella Zauna – mixed signals

    Gabriella Zauna – mixed signals Mp3 Download
    Gabriella Zauna – mixed signals Mp3 Download

    Gabriella Zauna – mixed signals Mp3 Download

    A superstar, Gabriella Zauna comes out hot again with a brand new song “mixed signals“.

    The song mixed signals is out now and readily available for free streaming and mp3 download on all music streaming platforms such as Tunezloaded, BoomPlay, Spotify, Apple Music, Amazon Music and many others.

    stream & Download mixed signals Mp3 Download by Gabriella Zauna Below:- and always check Latest Hip Hop Mp3 Download and Albums Download

    DOWNLOAD MP3