Arubuce Ta Ke Hausa NovelHausa NovelsHausa Novels

Arubuce Ta Ke 11

Sponsored Links

Iska mai zafi ya furzar daga bakinsa yana miqewa tsaye,kafin yakai ga aiwatar da komai mimi ta kama cikinta

“Abba……yunwa nakeji,tun dazu mommy tace zata dafa mana indomie……bata gama bane har yanzu?” Idanunsa ya zubawa yarinyar,a nutse yace

“Bakuci abinci bane yau?” Kai ta gyada masa

“Eh,momy tace tana jin bacci,kada mu dameta,musha tea,idan ta tashi zata dafa mana,har nawwara ma ta zuba ruwan tea din a qafarta,tayita kuka” lumshe idanunsa yayi,wani abu ya taba ransa,sai ya duqa a hankali tana laluben qafan yarinyar yana son ganin wajen,dai dai sanda yaji an murda qofar an kuma budeta,sanin waye ya sanyashi qin waiwayo yaci gaba da duba qafar nawwaran.

Matashiyar macace,wadda a qalla zata doshi shekara ashirin da takwas ko kuma da tara,wankan tarwada ce wadda kalar fatarta ta kusa juyewa ta baqaqe,banda hutu da jin dadin data samu,mai matsakaicin tsaho ce,tana da ‘yar qiba kadan da tudun hanci,idanuwanta basu fiya girma ba,saidai tana da ‘yar cikar gira da kuma fararen haqora da suka sake bayyana duhun fatarta.

Sanye take da kayan bacci a jikinta,kanta saye cikin wata hular zaren lilo da qabilu sukafi amfani da ita,zaka tsammaci qarfe bakwai ne na safiya a lokacin,saboda yadda fuskarta ke nuna alamu na bacci,uwa uba kuma sleeping dress din da take sanye dashi.

Tsaye tayi daga bakin qofar tana qare masa kallo,fushi takeyi dashi sanda ya tafi,ta kuma ci alwashin sai yaga fushin nata,saidai tun bai jima da tafiyar ba kewarsa ta dameta,idanuwanta kuma suka damu da son ganinsa,ta ajeshi qololuwar matsayi a rayuwa da kuma zuciyarta,shi din na musamman ne,tunda har yana da qarfin ikon juyata da sauya mata ra’ayinta zuwa wadanda yakeso,abu mafi girma kenan dake haddasa sabaninsu,kowa da alqiblar da yake kalla tsakanin shi da ita,hakanan kowa yana ganin akan dai dai yake.

Ci gaba tayi da kallonsa har ya gama duba qafar yarinyarshi,ya kuma tofa mata addu’o’i,tayi tsammanin zai waiwayo gareta ne tunda yaji shigowarta,amma sai taga yana yunqurin miqewa hadi da sake baiwa qofar baya,don haka ta saki hannayenta data rungume tana qarasowa cikin dakin,bayan ta dan bata fuska

“Dama kuna nan kuka sanyani inata bulayin nemanku cikin gida?,sai dana fita gate sule yacemin ya ganku tare?” Maganarta ta qarshe ta sanyashi waiwayowa,idan ba gizo idanunsa yayi masa ba yaga shacin kayan bacci a jikinta,tana nufin haka ta tafi wajen sulen nemansu,mutum ne shi mai tsananin kishi,ko kusa ko alama baya daukan sakaci ko ganganci akan iyalinshi

“A hakan kike tafi cigiyarsu har waje?” Ya jefa mata tambayar a nutse,saidai kuma wani bacin rai na daban bayan wanda yake ciki ke bijiro masa.

Sai a sannan kwanyarta ta ankarar da ita zallar wautar data tafka,duk yadda taso taja zarenta itama har sai ya gane yayi mata laifi ya bata haquri take komai ya rushe mata,saidai cikin sa’a ta kama zaren qaryar da takejin zata qwaceta

“Ta yaya zan fita a haka?,na cire hijab dina a falo” tana gama fada ta kauda qwayar idanunta daga cikin nasa,tana jin yadda yaketa kokawar ganin sun hada idanun,hanya guda daya da yake iya karanto qarya ko gaskiyarta,ta saara masa ta wannan fannin,kuma tasan ba banza ba,tunda aikinsa ne.

Bayason ya sake dagula al’amuran,dole shima ya janye nasa idanun

“Koda wasa,koda ganganci kada ki sake hakan ta faru” ranta ya baci,ta zumbura baki gaba,daqyar kamar wadda aka yiwa dole tace

“Tom” saita maida dubanta ga yaran ba tare data wani damu da yi masa sannu da zuwa ba ko tambayarsa hanya

“Kuka sani dafa muku indomie ashe ma ba yunwa kukeji ba kuka katsemin bacci na” sai taja dan siririn tsaki

“Saiku tashi muje kuci,idan kuma bakwaci a bayar da ita” mimi ce ta maqale kafada

“Nidai mommy banason indomie” ta hasala sosai,dama ga fadan da yayi mata

“Baki isa ba tunda na dafa sai kunci”

“Ji mana” ya dakatar da ita,saita waiwaya tana dubansa,ya ritsata da idanun nan nasa dake kassarata,bata buqatar ta sauko don haka ta kauda kanta

“Babu lallai yaro sai yaci abincin da ya riga ya ginsheshi,ki deba musu cikin abinda kika dafa min,sauran ki kawomin shi falo na” fuska ta bata,cikin jin shakka murya ciki ciki tace

“Ni ban dafa maka komai ba” ya zuwa yanzu mamakin hafsat ne ya kamashi,cikin son danne bacin ransa yace

“Saboda me?”

“To ai bakacemin ka taho ba”

“Bakisan yau zan dawo bane?”ya jefa mata tambayar cikin salo na tsitsiye,saita rasa amsar bashi,saboda wayar qarshe da sukayi bayan sun gama ya tura mata tex na date da time na dawowar tashi,kawai ta share ne saboda tana jin haushinsa,tazo kuma ta raba dare tana kallo,shi yasa da safen ta dinga barci kamar matacciya,sai da yaran suka dameta da kukan yunwa sannan ta rarrafa ta dora musu indomie,ta rage wutar ta koma baccinta bayan ta zuba komai da komai,da nufin ta sake matsewa kafin ta dahu,a wannan tsukin ya shigo,kuma har ya kwashe yaran bata snai ba,uwa uba ma kuma manta shaf da batun dawowar tashi.

Idanunsa ya lumshe yana jinjina kai,ya taka zuwa gaba kamar bazaice komai ba,sai kuma ya dakata ba tare da waiwayo ba yace

“Ki gyaran sashe na,sannan ki dafa min abinda zanci kafin na gama” daga wannan ya wuce bandaki.

Da kallo ta bishi har ya kammala wucewar ya rufe qofa,janye idanunta tayi tana sauke gauron numfashi,sai kuma tsaki ya biyo baya,bata dauka zai dauki abun da sauqi haka ba,duk da tasan halinsa,yakan iya share laifi yayi kaman ba’ayi masa ba,amma horonsa kuma sai yafi miki ciwo fiye da komai,a duniya babu namijin da ya taba yi mata abinda abbas din yake mata,batasan wanne irin so take masa ba daya samu dama da yawa yake juyata har haka ba,saita dakata da tunanin ganin bata da isashen lokaci,ta tarkata kan yaran ta sauka dasu zuwa sashenta,ta juye musu indomie din duk da sunce ba zasu ci,ta kunna musu kallo ta wuce kitchen tana tunani me zata dafa wanda bazai jaa mata lokaci ba.

Sai data kwashe mintuna kusan biyar tana dawurwurar abinda zata dafa masa cikin kitchen din,daga bisani ta yanke dafa masa jallop din taliya,duk da tasan cewa kwata kwata bata cikin lissafin abincinsa,hasalima saboda ita da yara yake ajjiyeta,banda haka tasha zamanta,to amma kuma bata da wani sauran option,hakanan bata da idea din wani abu me sauqi da sauri baya ga taliyar,kuma koma meye dai oho,indai ta dafa ta bashi ai ta fita ko babu sabulu.

Sai data wanke tukunyar da zata dafa abincin a ciki,saboda tun jiya datayi baqi qawayenta ta bata su gaba daya,ta kuma jiqasu sa zummar yau idan ta tashi aiki ta tsaftacesu,sai gashi kuma yayi mata dawowar ba zata.

Tana hada girkin tana mita cikin ranta,taja tsaki yafi a qirga

“Dole ne ma na samo ‘yar aiki gaskiya,haba dame zaka ji?,kashe kanka zakayi?” Ta dinga gunaguni ita daya,tuntuni takeson daukar mai aiki,amma saboda wani banzan ra’ayi nashi da kuma kafiyarsa yaqi aminta,alhali kuma aiki yayi mata yawa,ga yara gashi karan kansa.

Sanda ta gama ta juye masa a plate ta sanya wani ta rufe ta fito,a falon ta samu su mimi duka sun sheme barci ya daukesu,bacci dama sukeji,amma yunwa da rashin kyawun tsaftar jikinsu ya hanasu yin baccin,ga indomie dinta nan sunci wadda zasuci sauran sunyi wasa da ita sun sake d’aid’aita falon,sai a sannan ta lura da wankan da yayi musu,baki ta tabe

“Kwado sarkin tsafta,ni wallahi bazan kashe kaina da wannan shegen son tsaftar taka ba” daga haka ta sanya kai tana ficewa zuwa sassansa.

Zaune ta sameshi saman kujera riqe da remote yana kallon labarai,armless white shirt ce a jikinsa da three quarter wine color,ya miqa dogayen qafafunsa saman center table din yana kadasu a hankali.

Kallo daya yayi mata ya amsa sallamarta yana maida dubansa ga tv,ta qaraso dab dashi ta janyo daya table din ta dora plate din abincin ta matso masa dashi,a gajiye take jinta tubus don bata sanyawa ranta wannan aikin ba,don haka ta koma kan daya daga cikin kujerun ta zauna
“Sannu da zuwa” hankalinta ya bata tayi masa a sannan,sai daya sauke qafafunsa qasa ya zauna sosai sannan ya isa amsa mata,ya bude abincin yana kallonsa yayin da ita kuma take kallonsa tana jiran me zaice,kamar bazaici ba,sai kuma ya sanya fork a ciki ya debo yakai bakinsa.

Idanunsa ya ragewa girma yana tauna taliyar cikin bakinsa,kamar mai tauna mutuwa haka yaji,baisan ya zaima hafsat ba,baisan sai yaushe zata nutsu ta gyara tukunyarta ba,kudade da yawa ya kashe wajen ganin ta iya abubuwa da dama saboda inganta rayuwar aurensu amma har yau babu riba,tana sane?,mugunta ce ko kuma meye?,idan kishi ne da nuna masa zallar soyayya a baki ita din tana kan gaba,amma ya rasa abinda yake damunta.

Salin alin ya maida murfin ya rufe sannan ya miqe ya wuce bedroom dinsa,binsa tayi da kallo tana jiran taji me ya faru?,ba jimawa ya fito sanye da jallabiyya mai santsi dinkin qasar morocco mai gajeran hannu

“Ina key din mota ta?” Ya tambayeta yana sanya qaramar hula saman kansa,maimakon ta amsa masa saita miqe ta wuce gaba zuwa dakin nasa,ta jawo locker inda ta zuba muqullan ta dauko ts miqa masa,saiya karba

“Banaso na dawo na samu wajen nan a haka” ya fadi yana yin gab,tana son tambayarsa ina zashi amma bai bata damar wannan ba,tun daga fuskarsa har yanayin yadda yayi mata ya fice ba tare daya bata hanzari ba.

*_ASSALAMU ALAIKUM_*

_Barkanmu da dare da fatan kowa yana cikin qoshin lafiya_

_Akwai abinda muka turo tallansa na WOMEN EMPOWERMENT PROGRAM(KUDI KE KIRA),so please duk wadda batayi pyment ba ta jira tukunna kada tayi,akwai wani CONFIRMATION da mukeso mu samu a kansu_

*Idan komai ya daidaita zamu sanar muku*

*_idan kikaci gaba da pyment kuma bada yawunmu ba_*

*Muna godiya sosai**H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)

Leave a Reply

Back to top button