Arubuce Ta Ke Hausa NovelHausa NovelsHausa Novels

Arubuce Ta Ke 10

Sponsored Links

Page 10

K’ofar wani madaidaicin gida mai fenti ruwan toka da qaramin gate ruwan madara motar ta tsaya,ya sanya hannunsa cike da nutsuwar nan tasa dake zmaa mabudin nasara ga dukka aikin da ya sanya a gaba zai buda motar,saidai kafin yakai ga aiwatar da hakan Samuel ya rigashi,ya kalleshi yadan kau da kai sannan yace

“Thank you Samuel,you can go,zan koma gida da kaina” kai ya girgiza

“No oga,zamu jiraka,daga nan station zamu koma,babu wani aiki da zamuyi kuma”. Baice masa komai ba ya sauka daga motar ya nufi gidan yana takawa cikin tafiya ta tsayayyun maza.

Da sallama ya tura qofar ya shiga,yar farfajiyar gidan babu kowa saidai qal take,fes kamar babu wanda ke rayuwa cikin gidan bare ya bata ba,yana hango takalma daga qofar falon,wanda zaka fara taka wata qaramae baranda kafin ka cimma falon,sai yaci gaba da takawa har ya isa baranda yana maimaita sallamar sa,hadi da yunqurin zame takalman qafarsa kafin yakai ga shiga falon

“A’ah qaraso da takalmanka abinka” daga can cikin falon aka fadi,sai ya miqe murmushi daga qasan zuciyarsa na kubce masa,har ta hangoshi kenan,duk da shi bai hangota ba,ya yaye labulen yana sanya kansa ciki tare da jaddada sallamarsa.

Daga can saman kujera mai cin mutum biyu take a zaune,babbar macace wadda aqalla ta doshi shekara sittin,zaune sanye da atamfa dinkin riga da zani,kanta lullube da kallabi mai santsi irin na asalin tsaffi a qasar hausa.kyakkyawae bafulatanar bauchi,wadda bata qi dibar komai nasu ba,illa hasken fata,bata cika fari sosai ba irin wanda akasan fulani dashi ba,fuskarta na nuna zallar kamala da nutsuwa da kuma mutuntaka irin ta cikakken dan adam.

“Wa’alaikumus salam,maraba…yanzu kake tafe?”tayi tambayar tana gyara zamanta cikin kujerun

“Eh hajiya” ya amsa mata dai dai sanda take duban ‘yar budurwar dake kwance cikin kujera

“Tashi ki bashi waje” tun kafin ma hajiyar takai qarshen maganarta ta soma yunqurin tashi tana lalubar dan kwalinta daya fita,cikin sauri ta fara gaidashi

“Ina yini uncle”

“Lafiya lau” ya amsa mata yana zama cikin wata kujerar ta daban,bayan ya dan ture kayan da suke kai

“Shiga kitchen ki samo masa ruwa”

“Tom” ta amsa tana ficewa daga falon.

Sai a sannan ta tattara hankalinta a kansa,cike da girmamawa ya zamo qasa yana gaidata,ta amsa masa cikin kulawa da kuma qauna

“Alhmdlh…..ashe kun dawo”

“Shigowata bauchi kenan nace bari na fara zuwa na gaidaki” ya amsa mata yana komawa mazauninsa

“Ma sha Allah,Allah yayi jagora”

“Yayi hajiya,saidai fatan Allah ya dada yi mana,duk abinda akaje yi din Allah ya dafa mana an samu nasara” murmushi ya wadaci fuskarta,duk sanda zaiyi tafiya irin wannan sai ya shaida mata abinda zaije yi din,duk da cewa kusan komai din da zaiyi ma cikin rayuwarsa ita yake fara sanarwa,ita yake fara shawarta,takan tsaya tuquru da addu’a koda bai nema addu’arta ba,domin kuwa shi din na dabanne a zuciyarta,yana da wata irin tarin biyyaya me wahalar samuwa ga yaran yanzu.

“alhamdulillah, alhamdulillah,Allah abun godiya,to Allah yaci gaba da kula mana da rayuwarku”

“Ameeen ya hayyu ya qayyumu hajiya” ya amsata yana sake cire hular kansa kamar tana damunsa ne ya ajjiye a gefansa yana duban tarin kayanta dake ajjiye

“Ya akayi maisara ya kawo miki kayanki haka babu guga?” Dan duban kayan tayi

“To wallahi dai bana ce ba,kamar dai kallon qwallo suka tafi” fuska yadan tsuke

“Qwallon me?,idan bazaya iya aikinsa yadda ya kamata ba sai yayi magana” murmushi hajiya ta saki,shikam akan dukkan abinda ya shafeta baya wasa dashi,baya bada uzuri,hakanan baya daga qafa

“Yana qoqari ai,kasan su da son qwallo,kuma yau da gobe ma sai Allah” shuru yayi ya sanya hannu yana karbar cup din da muneera take miqo masa mai cike da ruwa.

Sai da ya shanye ruwan sannan ya dubi hajiyan

“Saura kwana nawa ne bikin gidan kawu hassan?”

“Na zaci zaka leqa ma,yana gida kamar bai fita ba yau”

“Sai idan na dawo,na yiwa auwal magana zai fidda kudin gudunmawar nan,zai kawo miki sai a bashi”

“To to madallah,Allah yayi albarka,ya qara budi”

“Ameen ameen” ya amsa mata yana sanya hannunsa a aljihun uniform dinsa ya fiddo kudi ya ajjiye mata yana cewa

“Zan dan huta gobe,may be bazan fito ba”

“Baka gajiya abbas?” Murmushi kawai ya saki ba tare da yace komai ba,baijin zai gaji da yiwa hajiyan tashi hidima bakin ransa,domin baya da kamarta a fadin duniya

“Allah yayi albarka”

“Ameen ameeen”

“A gaida gida,a gaidamin kishiyoyin nawa” kamar tace kwana biyu sunqi gidan sai kuma ta fasa fadin hakan,ita din mutum ce mai son zaman lafiya,batason rigima sam,saidai a duk sanda ka qureta bata da dadi.

A bakin mota ya samu su Samuel sunata hirarrakinsu,kafin ya iso ya bude masa qofar motar ya shiga,sannan suka zagaya suka shiga suma ya tada motar suka bar layin.

Duka duka tafiyar minti talatin da ‘yan kai motar ta sake sanya signal sannan suka shiga wani madaidaicin titi mai burji,wanda zai sakada da ainihin unguwar da suka nufi shiga.

Basuyi tafiya me yawa ba motar ta fara slow,da alama sun cimma inda suka nufa,ba jimawa ta faka qofar wani madaidaicin gida.

Daga girman gate din gidan zaka fahimci girman gidan,idan nace girma bawai ina nufin girma na sosai ba,saidai kana gani kasan yalwataccen gini ne daga ciki,hakanan ya qawatu ga idanun me kallo,yana dauke da tsayayyun katanku masu tsaho da qarko,wadanda ke dauke da fenti ruwan madara har jikin gate din,wanda aka yiwa ratsin zaiba(gold) a jiki.

Wannan karon kafin su bude masa ya rigasu budewar,ya zuro qafafunsa dake saye cikin baqin boot zuwa waje yana duban gaban gidan sannan ya sanyo gangar jikinsa zuwa waje

“Thanks Samuel” yace dasu bayan yadan waiwaya da kyau

“You deserve it sir”ya fada yana saluting nashi cikin girmamawa,jinjina kansa kawai yayi yana nan tsaye har suka tada motar suka fara barin gaban gidan,sannan ya qarasa a hankali yasa hannu yana knocking.

Daga ciki wata kakkaurar murya ta bayyana ana tambayar waye,bai bada amsa ba har zuwa sanda mai tsaron gidan ya bude qofar,da sauri yaja da baya cikin matuqar girmamawa yana masa sannu da zuwa

“Yauwa sule,mun sameku lafiya?”

“Lafiya lau oga”

“Ma sha Allah” ya furta yana takawa zuwa cikin gidan,hannunsa guda daya saye a aljihun wandon uniform dinsa,daya hannun kuma riqe da hular tasa.

A hankali yake takawa zuwa cikin gidan yana nazartar yanayin gidan,daga farfajiyar gidan ko ina fes yake cikin hankali da nutsuwarsa,duk da bashi da tabbacin abinda zai tarar a ciki amma hankalinsa ya dan kwanta kadan,yaci gaba da takawa cikin taku na qaqqarfan namiji wanda horon aikin damara ke yawo cikin jiki da kuma jininsa.

Qofar falon ya murza,yayi sa’a ya sameta a bude,sai ya tura yana sanya kai ciki,bakinsa dauke da sallama.

Kamar jira akeyi,yara biyun dake wasa a falon saman dan keken wasan yara suka waiwayo zuwa gareshi,babbar me wayon wadda ke tura qanwarta ta saki keken da mugun gudu ta nufeshi

“Abba….abba!” Take fada cikin daga murya dake cakude da sautin zallar farinciki,yayin da daya yarinyar keta kiciniyar saukowa daga kan keken itama don ta iso gareshi.

Wani qawataccen murmushi ne ya subuce masa,ya duqa a hankali yana jiran isowar yarinyar,tana qarasowa ya dauketa caraf yana sanyata cikin jikinsa,saidai kuma me?….. janyeta yayi da sauri yana duban kayan jikinta sakamakon qarnin da baisan na meye ba daya daki hancinsa,ya sauke idanunsa kan gaban rigar yarinyar,rigar da idan bai manta ba naira dubu shida ya sanya ya siyeta kafin tafiyarsa wannan aikin,kwanaki goma baya da suke wuce kenan.

Jirwaye ne na abubuwa kala daban daban a gaban rigar,wanda shi kansa bazai tantance na meye ba,ya dauke idanunsa ya maida kan fuskar yarinyar dake dauke da jirwayen busassun hawaye,kafin yayi magana yaji ana jan hannunsa hade da gwaranci,sai ya mayar da kallonsa kanta,tana tsaye a gabansa tana ta babbaka masa dariya,da alama akwai abinda takeson gaya masa cikin gwarancin nata,sai ya miqa hannu daga tsugunen da yake ya dauketa cak yana azata saman cinyarsa,saidai ita din ma babu sauqi,tsami ko kuma warin pampers dinta ne ya kaima hancinsa ziyara,ya miqa hannu yana taba pampers din,sai ya jishi a cike,tausayin yarinyar ya kamashi,take kuma ranshi ya baci

“Abba,ka siyo man teddy din?” Kumatunta ya kama yana qoqarin hadiye fushinsa,abinda kusan ya zame masa jiki koda yaushe

“Mimi teddy,bari na huta tukunna” bai sake jiran komai ba ya sanya hannu ya sunkuci yaran duka su biyun,sunata zuba masa shirmensu yana biye musu ya doshi sassanshi dasu,don bazai iya sake zama a wannan sashen ba a yadda idanuwansa suka ganshi a hargitse kamar an shekara ba’ayi masa shara ba.

Sashe ne daya tsaru matuqa cikin kalolin light blue da fari,tun daga babban falonsa dake manne da window size da hotunansa da yawancinsu cikin uniform dinsa ne na police zuwa bedroom dinsa wanda aka zubawa kayan gado masu matuqar kyau da tsari.

Yayi zaton zai samu sassauci a sashen nasa,tunda yabar key ya kuma buqaci a gyara masa,amma sai ya samu waje shima sammakal,sauqin daya ne baikai jagalewar can ba,ya hadiye wani abu mai tauri yana sauke yaran gefan gadonsa,sannan ya fara cire uniform din nasa,ya rage daga shi sai wata farar shirt mara nauyi ko kadan mai gajeran hannu,wanda hakan ya bayyana cikar zati da siffar jikinsa,muscles tako ina dake nuni da siffar qarfi da kuma yanayi na motsa jiki da daga qarfe da yakeyi a kowanne lokaci,wandon jikinsa ya fidda ya rage iya boxer,sannan ya shige toilet dinsa ya hada ruwa mai dumi sosai ya dawo dakin ya fidda musu kayan jikinsu ya wuce toilet din dasu ya sanyasu a bathtub.

Fes yayi musu wanka dukka su biyun har gashin kansu,sunata qyalqyala dariya hadi da cikashi da duminsu,shi kuma yana ta biye musu,dukka a qoqarinsu na hadiye damuwa da kuma bacin ransa,bayan ya gama ya sanya kayan daya cire musun a leda ya jefa a dustbin,duk da kudin da ya sanya ya siyesu,mutum ne shi mai tsananin tsafta hadi da tsantsami,don hakan baima san ta ina zai fara tsaftace kayan ba,don haka ya gwammace yayi musu hakan.

Anan dakin ya shafa musu mai ya gyara musu gashinsu,sannan ya buda jakar da yazo da ita,a duk sanda yayi wata tafiya indai dama ta samu baya gajiya da yiwa iyalinsa tsaraba,ya fidda wasu gown na wani cotton material iri daya guda biyu ya sanya musu,sannan ya feshe jikinsu da turare.

Murna suke abinsu kawai,walwalarsu ta dadu saboda yadda sukaji jikinsu yayi musu dadi,ransa a bace ya daga kai yana duban agogon bango,a qalla ya kusa minti talatin da shigowa,amma batasan ya dawo din ba,abar ta tashi ma,yaran data bari a parlor fa?,haka take tafiya ta qyale yaran qofa a bude kusan awa guda ba tare data leqa su ko ta bibiyi halin da suke ciki ba?.

*RUMBUN K’AYA*🔥

*DAUDAR GORA*🔥

*IDON NERA*🔥

*A RUBUCE TAKE*🔥

*KI KULANI*🔥

*_uhmmmm_*😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊

*Nasan zakuce ya da murmushi haka?*

*Wanda bai shigo ba bazai gane ba*

*Sai kin shigo daga ciki zaki gane me nake nufi*☺️☺️

*KE DAGA JIN SUNAYEN LITATTAFAN MA KADAI KASAN CEWA AKWAI WANI BABBAN ABU MAI MATUQAR JAN HAKALI TATTARE DASU*

*KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?*

*KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?*

Littafi daya—400
Biyu—600
Uku—-800
Hudu—–1k
Biyar din duka—-1200

*ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥

0022419171
Maryam sani
Access bank.

Shaidar biya tanan👇🏻
09033181070

*MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN*

09166221261

🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa ‘yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

+227 90 16 59 91

Littafi daya—450CFA
biyu—650CFA
uku—-850CFA
hudu—-1050 CFA
Biyar—-1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*

*SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!*

*Thanks for choosing us*🔥*H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)

Page 11

Leave a Reply

Back to top button