Duk Karfin Izzata Book 1Hausa NovelsHausa Novels

Duk karfin Izzata Book 1 Page 7

Sponsored Links

⬇️
*Star Lady*

Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

 

*Episode7*

Zaune suke a palan Ammi suna hira nan fa zahra take fada musu komai na gidan
Zahra tache karku yarda kuyi wani laifi yanzu dankuwa shekaran jiya su yaya prince suka dawo baruwanku da kowa a gidan nan dan wlh duk yan gidan nan mugaye ne yaya Khalid ne kawai mutumin kirki dan haka karku kula kowa duk abunda kukeso ku tambayeni yauwa kuma inkun gaishesuma basu amsaba karkudamu kuma karkuyi wata maganar dan basa amsa gaisuwar kowa sukam haka suke
Diyana tache to tunda basa amsa kaisu basai mu kyalesuba dole sai mun gaishe sune
Zahra tache keeee. lallai da zafinki kikazo tab ai wlh idan sukazo suka wuche baki gaishesuba nan ma hukunchi zaki karɓa inkuma kingaishesu bazasu amsaba to zamanki lafi shine ki gaidasu koda basu amsaba karkidamu ” yauwa kunga wandayake zaune a kujeran gefen Ammin ɗazun din nan koh wan nan mai kama da Hiyana
Da sauri Hiyana tache daman akoi mai kama dani a gidan nan ne ” Zahra tache eh mana ai shine ya zauna kusa da Ammi sunansa yaya prince to dashi da yaya Aryan da yaya yusuf da yaya Fahad wlh karku yarda hanya ta hadaku inba hakaba zaku jijiki basu da kirki Zahra zata sake magana taji takun tafiya a tari ta mike tawatsa dakinsu da gudu dankuwa tasan irin wan nan takun mutun ukune kawai a gidan nan keyinsa ” Don, Aryan , Yusuf shiyasa ta gudu dan batasan haduwa dasu
Suna ganin Zahra ta gudu suma suka mike da gudu sukabi bayanta
Yana shigowa ya tsaya shiru yana tunanin tabbas yaga wulkawar abu kuma kamar inuwar mutun wuchewa chikin palan yayi yasamu waje kan kujera mai zaman mutun daya ya zauna
Yachiro wayarsa yafara daddan nawa kana yasa akunne jimkadan sai yache gani nanfa a palo banji me akacheba a dayan bangaren ba kawai naga ya katse kiran
Fitowa Ammi tayi daga chikin betroom tazo ta zauna a kujera mai zaman mutun ɗaya a nitse Safra yache inawuni Ammi ta amsa masa da lfy yache yamukaji da hakuri tache hakuri yazama dole yache allah yajikansa da rahma amin Ammi amsa kana tache daman kuɗi nakeso kabani su farida zasuje suyiwa kannenka sayayya ” shiru yayi bai chekomaiba kusan 10 mnt tukun nan yache
Ammi dan allah wai meyasa bazaki sabaki a magaAnar nanba nifa bazan iya mulkiba kinsanfa shugaba da adalchi da tausayi
akasan shi to nikuma sojanefa
Ammi baki sake take kallansa tache au kai bakada tausayi ke nan shiru yayi bai tankaba saima mikewa dayayi yanufi hanyar fita yana fadin Fahad zai kawo miki kuɗin
Ammi dai ido tazuba masa har yafita tukun nan ta sauke wani nauyayyar ajiyar zuchiya afaili tache nida kaina nasan ba iya mulkar mutane zakayiba saboda wan nan irin hali naka bakayi kala da shugabanniba kadaifi dachewa da rike bindigar amma ni babu ruwa kaine zabin mahaifinka bazan chanza masa zabinsaba sai dai inshiyaga dama ya chanzaka da kansa amma zantayaka da adduar Allah yasa kar abaka mulkin nan dan in akabaka mutane zasusha wahala, zata sake magana sai taji alamar tafiya shiru tayi tana sauraran mai shigowa
Aunty farida che tashigo bakinta dauke da sallama da fara’a Ammi ta Amsa mata sallamar
Shigowa tayi ta zauna a gujerar da Prince yatashi kana tache Ammi barka da hutawa anche kina nemana gani
Ammi tache yauwa sayayya nakesan kuje kiyiwa su Diyana dan kinsan basuda kaya to kisaya musu duk abun daya dache
Aunty farida tache to inasuke suzo muje tare koh dan muzabi size dinsu dakuma colours din dasuke bukata
Ammi tache aa kuɗan jira kadan kanin naki yache zaibawa Fahad kuɗin yakawomin
Aunty farida tache aa basai ankarbi kudi wajen prince ba suzo mutafi kawai ni zan dauki nauyi sayayyar
Ammi tache aa farida kada na daura miki nauyi da kinbari shidai yakawo kuɗin nafisan yamusu da kansane dan kuwa duk wani responsibility su yadawo kansa shi zai dauki komai shiyasama banbiya kuɗinba nache yabiya
Aunty farida tache Ammi dani da prince duk ɗayane idan nabiya kamar shine yabiya kuma kamar yadda nakewa Zahra sayayya da kuɗina suma haka zanmusu saboda yanzu dasu da Zahra duk dayane awaje na
Ammi tache to shike nan badamuwa kuje din
Aunty farida tache Ammi dan allah inaneman alfarman kisa baki mai martaba yabani Diyana wlh tashiga raina ina kaunar yarinyar san nan kuma dan allah kutaimaka kubawa mardiya lamrat takuma da ita Abuja tunda kunga ita Allah bai bata aihuwaba
Ammi tache kwarai ina matukar tausayin mardiya musanman idan kuka haɗu yadda take matikar son junior batasan yayi nisa da ita wani lokachin har kwalla nakemata amma bayadda zanyi inraba marayun allah nan Feeda tare suka taso komai tare suke dukda shekarunsu ba ɗayaba amma dai zan gwada kinji
Aunty farida tache eh Ammi akoi chiwokam murabasu amma dan allah taimaka mana zakuyi muda bamuda yaya Ammi tache to zanyi magana da mai martaba da daddare
Dukyadda mukayi zakiji
Aunty farida tache to saikuma maganan prince Shima dan… Bata kai karsheba Ammi tache kingane tashi kutafi adawo lfy tana kaiwa nan tamike tanufi dakin su Zahra dan takirasu
Girgiza kai Aunty farida tayi tache Ammi ” Ammi kinasan samana chiwon kai amma a hankali zanshawo kankine
Fitowa Ammi tayi rike da hannun Amrat su Diyana na biye dasu abaya diyana da hiyana hijabai sukasa zahra kuma abaya tasa da gyalensa sunyi kyau sosai amrat da lamrat kuwa blaus ne ajikinsu mai kyau sai dan karamin gyale dasuka yafa akamsu
Mikewa Aunty farida tayi san nan tache muje koh tayi maganar tana kokarin riko hannun Diyana
Suna fita kai tsaye parking space suka nufa da sauri driver yazo ya bude musu motar hiyana da diyana da zahra suka shiga mota ɗaya
Aunty farida kuma takama hannun amrat da lamrat suka nufi wata motar suka shiga
suna shiga wayar aunty farida yafara kara da sauri ta dauki call din tache hello daga ɗayan bangaren yache inakikene insan muyi maganane
Aunty farida tache gani nan yanzu nafito zamutafi shopping kazo karakamu mana sai muyi maganar a hanya ” yache aa bazanjeba amma barinasa sojoji surakaminke saboda tsaro” dariya Aunty farida tayi tache kai dai prince allah bansan irinkaba mutunne bayasan shiga jamaa to shike nan tunda bazakajeba saina dawo saimuyi maganar koh zata sake magana ke nan taga waso sojoji guda 4 a gabanta chiki har da abdol
Tache laaaa yanzu muna waya yaushe kayiwa sojojin nan magana
Prince yache lokachin danache bari na hadaki dasu mana alokachin na dannamusu kararrawa dasu nanki
Dariya Aunty farida tayi tache to shike nan ngd saimun dawo
Yache kikula mana da kanki tache to tunkafin takarasama ya katse kiran
Juyowa tayi tabawa driver umarnin sutafi
Abdol chikin harchen turanchi yache madan inbadamuwa barini naja motar dan oga yache nabaki kulawa sosai
Aunty farida tache to badamuwa ” fita driver yayi yabawa Abdol wajen yashiga sauran sojoji ukun kuma suka shiga wata motar natake suka kunna motar suka miki hanya sai gate ” sojojin dake wajen suka bude musu pakekiyar gate din suna fita suka miki hanya
Aunty farida tachewa Abdol to aibaka tambayi ina zamujeba
Abdol yache oga yariga yashigarmin inda zan kaiku a chikin wayata
Shiru Aunty farida tayi tana kallan ikon allah tana jiran taga inda za’a kaisu
Kai tsaye wajen wani katafaren shopping Abdol yashiga yayi parking a parking space nawajen yafito yabudewa Aunty farida tafito kana takama hannu amrat ta tsaya saida su zahrama suka fito sukazo inda take san nan suka nufi chiki Abdol yabi bayansu sauran sojojin suka rufa musu baya Abdol yache su koma wajen mota sujirasu

Kaya dayawa Aunty farida tafara ludan musu kuma tache suma suzaba duk abun dasuka ga yamusu su dauka ” Zahra kam duk abun datagani mai dan kyalkyali sai tache wan nan zayyiwa Hiyana kyau ta dauka mata sunyi sayayyar kayan sawa dayawa san nan sukaje wajen takalma da jaka suma dayawa suka dauka suka koma wajen kana nan kaya Hiyana naganin breziya tafa boye fuska Zahra nata mata dariya
Aunty farida kuwa chewa take My Diyana kemafa kin kai sa bra ba Hiyana kawaiba dan kema naga ba bayaba wajen chikar halitta rufe fuska Diyana tayi da hannunta tana murmushi
Amrat ne tayi magana da fullanchi tache zata sha ruwa Aunty farida tache ku fassaramin metache ” dariya Zahra tayi tache kai Aunty farida yakamata kema kikoyi fillanchi ruwafa tache zatasha
Aunty farida tache to daga yau hausa zamu rinka yimata dan itama ta iya hausar to waima ya akayi ku kuka iya hausa ita bata iyaba
Hiyana tache mu munazuwa tallan nono ne a chan akoi hausawa suna zuwa saye itakuma kullum tana gida tana aiki bata zuwa ko ina ” a gida kuma ba mai jin hausa sai fullanchi kawai shiyasa bataji
Aunty farida tache to yanzu dai hausar za’ana mata har ta iya to kawai sukache san nan sukachigaba da sayayyar su
Bayan sungama daukan bra da pant suka wuche wajen dankunne da sarka nanma dayawa aunty farida ta dauka musu har da gold saida sukachika keken zuba kaya uku da kaya tukun nan Aunty farida tache ya isheku ne kokuma akoi wani abun dakukeso ” da sauri Hiyana tache ya isa ” Aunty farida tache aa kuduba da kyau dai ” hiyana tache allah ya isa haka nan ” Aunty farida tache to shike nan kutura kayan muje wajen biyan kudi harsun kai wajen biyan kudin kuma sai Aunty farida tache inazuwa chikin shopping din tashiga bangaren always tanufa ta daukoh guda 6 ta dawo ta zuba musu a chikin kayan
Diyana sarkin baki tache aunty menene wan nan kamar breadi Aunty farida tache nakine ke da hiyana da zahra kuma ba bread bane always ne ” Diyana ta mai mai ta su nan always to me akeyi dashi ko chi akeyi diyana ta tambaya.
Aunty farida dai taga alamar kamar diyana bata fara period ba saitache mata inmunje gida ki tambayi zahra zata fada miki to kawai diyana tache
Nanfa aka fadamusu bill na kuɗinsu Aunty farida ta chiro ATM nata tamikamusu suka chiri kudin san nan aka samusu kayan a leda Abdol yafara kwasan kaya shida yaran shagon suka kai mota
Aunty farida kuwa takama hannun diyana sukayi waje su Zahra suka rufa musu baya
Aunty farida tache Zahra da lamrat da hiyana suje su shiga motar da takawosu itakuma zata shiga motanta itada diyana da amrat . Tana kaiwa nan tashige chikin motar rike da hannun diyana amrat ma tashigo ta zauna kusa da diyana su
zahra kuwa suka nufi motarsu suka shiga nantake sojojin suka tada motochin suka nufi gida
Suna isa gida kai tsaye bangaren Ammi suka nufa a palo suka sameta nan suma suka baje kolinsu suka fara nunawa Ammi kaya. Ammi kam sai sannu da dawowa take musu tana sawa Aunty farida albarka takuma yaba kayan sosai tache su tattara suje su shiryasu a indaya dache, haka suka kwashi kayan sukayi dakinsu dashi

Aunty farida tadawo da hankalinta ga Ammi tache Ammi gobefa zan koma Mai duguri
Ammi tache ai naga wan nan karanma anbarki kindan dade ” Aunty farida tache eh wlh shiyasa nakesan komawa dan kar a hanani zuwa sallah kinga azumi yakusa ” Ammi tache ai garakam kikoma kije kikula damijinki yanzu dai kije ki kwanta ki huta a daki sai zuwa dare makarasa hirar
Mikewa Aunty farida tayi tana chewa to Ammi dan allah dai kiyi kokari kishawo mana kan mai martaba daya taimaka yabamu diyana da lamrat
Ammi tache to zanyi kokari . Betroom din Ammi aunty farida tashiga ta haye gadanta ta kwanta bajimawa barchi ya dauketa

Zaune suke a tsakiyar gado gaba dayansu hiyana tache aunty zahra dan allah inasan kifara koyamin karatu kinji lokachin muna kanana bappa yana koyamana karatu har munyi nisa danni har nakai izu 10 a karatun qur’ani kuma inasan in iya karatun qur’ani sosai
Zahra tache zan koyamiki hardana bokoma bana qur’ani kawaiba harda addoe dasu hadisai kuma akoi malamin dayake zuwa yana koyamin karatun islamiya kullum dayamma yanzu tare zamuna zuwa ya koyamana
Diyana tache yauwa nima inaso aunty zahra ” zahra tache ai gabadayanku ma yazama dole kukoyi karatu yanzuma daga gobe zanfara koyamuku ” harsuna hada baki wajen chewa to

Misalin karfe 8 na dare gaba daya family sun hadu a palan mai martaba
mai martaba da don da aryanne kawai basa wajen shiru kowa yayi daga masu daddanna waya sai wayanda sukayi tagumi suna jiran fitowar Abba
Aunty farida che ta kalli Fahad tache wai inasu prinse ne kullumfa sune suke bayan zuwa wajen nan ” Fahad yayi shiru kamar bazai tankaba kusan 2mnt tukun nan yache nimafa tun dazun damuka rabu bansake shiga wajensuba
Ammi tache au ashe zaka tankamata ai nazachi bazakayi maganaba mutanene yadda kasan wasu kurmaye aimusu magana sunaji amma bazasu amsaba kukan wlh bakuji dadin halinkuba ” Fahad dai shiru yayi kamar baijin me Ammi ke chewaba
Aunty farida tache kai Ammi hakafa akesan namiji yakasanche ba mai surutu barkataiba ” harara Ummi ta watsawa aunty farida kana tache aidaman ke’ki’ke kara injizasu dan kuwa ke awajenki komai sukayi dai dai ne basa laifi ” shiru aunty farida tayi bata tankasuba sai sukaji muryan mai martaba yanachewa aa karku dakurawa first born dina ku kyaleta haka nan irin wan nan faɗa haka
Ummi tache ai daman bakinku daya zama mai martaba yayi yana faɗin eh dai munji babu ruwanki farida dawo nan kusa dani
Mikewa Aunty farida tayi takoma kusa da mai martaba ta zauna
Mai martaba yache Amrat ummu waru ( amrat tashi kizo) mikewa tayi taje zaunar da ita mai martaba yayi a kujerar kusa dashi aunty farida kuma tache diyana taso kidawo kusa dani mikewa diyana tai takoma kusa da ita
Zahra’kam ko ajikinta dan ita koma kusa dawa zama zatayi amma yanzu da hiyana sukazo tare suke komai dan haka yanzuma suna zaune kusa da juna
Takun tafiya sukaji wanda kobasu juyaba sunsan takun manyan boss ne nantake palan ya nitsu tsit wasuma da kyar suke numfashi chiki har da zahra da umar
Su hiyana kam ko ajikinsu dan basumasan masu shigowarba
Kai tsaye kan table din suka nufa suna sanye chikin fararen jallabiya dukkansu sai kamshi sukeyi kamar anyi barin turare ajikinsu zama sukayi ” don ya dauki bottle na ruwan dake kusa dashi ya bude ya tsiyaya ruwa a cup yasha san nan ya ajiye ragowar a kusa dashi nan take kannen nasu suka fara gaidasu amma babu wanda ya amsa a chikinsu saida kannen nasu suka gama gaidasune
Zahra ta dan zunguri hiyana tamata alamun ta gaidasu chikin gurbatatchen hausarta tache inawuni hamma basu amsaba kuma ko kallanta basuyiba
Diyana kam achikin zuchyarta tache wlh bazan gaishekuba mutane saikache wasu shadanu a muku magana bazaku amsaba kuma kuche inba amukuba zaku hukunta mutun to wlh nikam bazakumin hakan na daukaba yauwa dai dai nake da kowa

Saida palan yayi shiru san nan chikin nitsuwa don yache inawuni Abba mai martaba ya amsa da lfy ” ya dawo da kallansa kan su Ammi suma yabisu ɗaya bayan ɗaya ya gaidasu
San nan aryanma yabi iyayen nasu ɗaya bayan ɗaya ya gaidasu
Shiru kowa yayi a palan sai aunty farida tachewa kuyangun dake tsaye a kansu dasu zubawa kowa rice an beans da sauri suka fara sarving nasu suna turawa kowa
Aunty amarya tache nikam bashi zaku zubaminba kuzubomin semo da miyar agusi
Bawanda ya tankata a palan sai aunty farida ne tache kuzuba mata mana tunda shi take raayi da sauri suka zuba mata suka mika mata
Suna chikin chin abinchi hiyana tafara shakuwa shakuwa yaki tsayawa hannutasa ta dauki cup din ruwan da don ya ajiye kusa dashi daya tana kusa dashi tafara sha kamar daga sama taji saukar mari a fuskarta har saida tamike batasaniba,dafe kunmatunta tayi da hannu tana kallansa hawaye nazuba daga fuskanta wani tsawa ya daka mata wanda yasata zurawa aguje tabar palan tayi sashen Ammi kowa na palan sai daya tsorata banda mai martaba da aryan
Aunty farida ne tayi karfin halinchewa haba prince meyasa zaka mareta bakaga yarinya bache kuma inkalura batasan ruwan shanka ta dauka bafa
Ko kallan aunty farida baiyiba barema yabata amsa abinchinsa kawai yachigaba dachi shiru palan yayi ba abunda kakeji sai karan spoon
Zahra kam jikinta sai rawa yake tanasan tashi tabi bayan hiyana amma tana tsoro
mikewa diyana tayi tabi bayan hiyana lamra naganin diyana tamike itama tamike da gudu tabi bayansu amrat zata tashi mai martaba ya riketa yache zauna yata kichi abinchinki karki damu
Kuka amrat ta pashe dashi tana fadin aa nakoshi nikam zanje wajen Aunty hiyana na ” mai martaba dayaga haka sai yache zahra dauki abinchin naku kikama hannun amrat kutafi kuje daki kuchi a chan ” da sauri zahra tamike ta dauki abinchin nasu takama hannun amrat sukayi waje

Mai martaba yayi gyaran murya yafara magana ” meyasa zaka dora hannunka ajikinta kai bakada tausayine marayunefa ba uwa ba uba haka suka taso chikin kunchi da wahala yanzu kowani kukagani zai bugesu bazaku tsaya kutaremusu sai inda karfinku yakare amma kai da kankane ma zaka bugesu ” bakataba batamin rai irin na yauba gaskiya banji dadin hakanba kuma kasan lbr yaran nan babu abun da baka saniba agabanka aka bada lbr wahalar dasukasha, to bansan hakan tasake faruwa kanaji
Kasa kasa don yache sorry Abba rainane yabachi ” mai martaba bai sake chewa ko uppanba
Yusuf yache allah sarki wai daman Abba basu da iyayene wlh harsunban tausayi ” wani kallan banza aryan da don suka watsawa yusuf amma ko ajikinsa saima chewa yayi Abba gaskiya to indai hakane yakamata mubasu kulawa sosai dan sumanta da bakin chikin rashin iyaye
Ammine tache haidar umar fahad duk kutashi kubamu waje zamuyi magana ” da sauri suka mike sukayi waje ” suna fita afusache Ammi ta dubi don tache idan kasake sa hannun ka bugi ɗaya daga chikin yaran nan to wlh ban… Bata karasaba mai martaba ya rufe mata baki kana yache aa bansanjin hakan
Don kuwa dagowa yayi yana kallan Ammi yaga yadda ranta yabachi sosai tabbas baitaba ganin bachin rai a fuskar mahaifiyarsa irin na yau ba hakan yasa jikinsa yayi sanyi haryafara nadamar meyasama yayi sauri marin yarinyar meyasa baya iya controlling zuchiyarsane why gashi tunda yake da Ammi baitaba bata mata raiba sai yau gaskiya bai kyautaba
Chikin nitsuwa da sanyayyiyar voice nashi yache kiyi hakuri Ammi inshaa allah zanrinka kiyayewa ” batare da Ammi ta kallesaba tache dazaifimaka
Yusuf dai mamaki yake wai yau don’ne ransa yabachi haka kuma yayi saurin saukowa zuchiyar tayi sanyi tab lallai uwa tawuche wasa duk wani karfin izzan da mutun yake dashi bai isa yayiwa mahaifiyarsaba

Mikewa mai martaba yayi yana fadin Ammi kisameni adaki inasan magana dake ita Ammi tamike tabi bayansa tana faɗin to ganinan ai muje tare tunda mungama chin abinchin
Don da aryan ma mikewa sukayi suka nufi bangarensu
Yusuf yache Aunty farida wlh yaran nan sunban tausayi wai yama su nansune
Aunty farida tache wanda don yamara itache hiyana wanda tabi bayanta bayan ta gudu kuma itache diyana ta ukun kuma lamrat sai amrat itache karamar tayi maganar tana kokarin mikewa
Yusuf yache ina zakije aunty farida ” zanje inyimagana da aryan da don ne dan kaga gobe zankoma
Yusuf yache to shike nan nima zanbiyoki daganaya bari nasha coffee ina zuwa to kawai tache masa san nan tawuche tafita daga palan

Tana fita palan bangaren aryan tafara zuwa da sallama tashiga palan babu kowa dan haka tanufi betroom dinsa zune tasamesa a kan kujerar mirrow yana hada wasu magunguna jin sallamarta yasa yadago kai yana kallanta
aunty farida tache mezakayi da waɗan nan magungu nan kuma ” yache ina hadawa don ne ” bashi da lfy ne ta tambaya tana kokarin zama a gefen gadansa aryan yache aa banashi bane akoi wasu criminals da zaiwa amfani dasune ” aunty farida tache too allah yachechesu daga hannunku ” murmushi kadan yadanyi kana yache kai aunty babba muɗin kuma yau
Aunty farida tache kuɗinfa aiku duk wanda yayi laifi kuma a kache kuzaku hukuntashi to wlh garama yachire rai da rayuwa dan kuwa inbai mutuba kadanne zai rage masa aryan zaiyi magana wayarsa tafara kara alamar shigowar kira bai dauki wayarba har kiran ta katse ” aunty farida tache wayake kiranka haka dakaki dagawa a takaiche yache faruq ne ” aunty farida tache faruq dai danasani best friend naku ” aryan yache eh shine ” aunty farida zata sake magana kira nabiyu yashigo bai dagaba har saida wayar takusa tsinkewa tukun nan yayi picking call din kuma yasata a H-free
yache hello my tager daga dayan bangaren faruq yache my man ykk yanakira da farkoh baka dagaba . aryan yache hannuna nachikin wasu chemicals ne shiyasa ban dagaba daman innagama abundanake zankiraka saikuma kasake kira ykk y mom da dad ina zahra da zaina da maryam faruq yache Suna lfy yasu Ammi. Aryan yache suna lfy ina abdul soja ” faruq yache yana nan lfy ” amma katambayeni kowa baka tambayi inteesar ba
Aryan yache wache kuma inteesar” faruq yache matar da zan aura mana ” dogon tsaki aryan yaja kana yache kaima auren zakayi ” faruq yache eh mana aryan yache tofa karkabari don yajika kaibama don bama nima yanzu..bai karisa maganarba aunty farida ta amshi wayar tana fadin yaushe zaka kawomin amaryan maiduguri inganta ” faruq yache aunty babba ashe kina kusa ” aunty farida tache eh wlh faruq amma gobe zanwuche ” faruq yache ina junior
Aunty farida tache yana wajen Ummi kai bama wannanba yaushene auren, kuma kasa lokachi kakawomin amaryan inganta, ai garamaka kayi aurenka karka biyewasu Aryan dakuwa su basusan chewon kansuba
Baki bude aryan ke kallan aunty farida sai zuba hira take da faruq dagajin yayi maganar aure waisu me matsalarsu dasuke san sai munyi auren nanne
Bayan aunty farida tagama hirarta da faruq ta katse kiran ta mikawa Arayan wayansa san nan tache to daman nazo muyi sallamane gobe zanbi jirginsafe zuwa maiduguri
Aryan yache ok karfe nawa
Aunty farida tache 7 dai dai ” Aryan yache okay zanzo inkai ki airport. Aunty farida tache to ngd bari naje nayiwa donma sallama tayi maganar tana kokarin mikewa
Aryan kuwa baisake tankamataba har tafiche daga dakin tama bar shashen nashi gaba ɗaya tanufi shashen don agurgije tamasa sallama dan tanasan taje ta shirya kayanta shima dai don chewa yayi zaizo yakaita airport

Abangaren su hiyana kuwa tana parin palon dakinsu tanufa tafada kan gadonsu tana kuka diyana nashigowa ta haye kan gadan tana rarrashin hiyana saigasu zahra ” nan zahrama tashiga rarrashinta har tayi shiru takuma saukoh kasa suka karisa chin abinchinsu nan suka haye gado zahra ta daukoh takardun makarantar ta tafara koya musu karatun.

Ammi na zaune a tsakiyar gadan mai martaba tana gyara masa gashin kansa suna yar hirarsu chikin nishadi Ammi tache ran’kayadade dan allah katausayawa mardiya kabata lamrat kaga batada ƴa allah baibata Aihuwaba gashi faridama tana san diyana
Mai martaba yache oh bakyasan ganinsu a gabankine to idanma ke bakyasan ganinsu ni inabukatar ganinsu kuma babu abunda zai raba yaran nan sai mutuwa ko aure bazan yarda yarabasuba dan kuwa idan miji ba agarin nan yakeba babashi aurensu zanyiba wlh duk wanda yake sansu tofa saidai in mazauni kano inba hakaba yahakura kuma wan nan shine hukunchina bansan sake jin wata magana akan yaran nan
Ammi tache to inshaa allah bazan sake magana a kai ba jawota mai martaba yayi tadako kan kirjinsa yana faɗin shiyasa nake sanki sosai kekadaiche a chikin matana innayi magana baki musamin kobakison abun danache haka kike hakura ki amsamin allah yamiki albarka ” shafa gefen fuskarsa Ammi tayi tache nima ai inasanka sosaima
Mai martaba ya ɗan chije hannunta yache yanzu babu fullanchi ke nan
Dariya Ammi tayi tasake ahigewa jikinsa tana faɗin eh kam akoi amma kaɗan kaɗan rungumarta sosai mai martaba yayi yafara raɗa mata magana a kunne

Misalin karfe 10 dai dai aunty farida tashigo dakin Ammi da sallama abakinta Ammi na kwanche a kan gado tamike daga zaune ta amsa sallamar
Abakin gadan aunty farida ta zauna tache Ammi gobe da asuba zantafi nazone naji yakukayi da mai martaba ” Ammi tache wlh feeda har kunyarki nakeji bansan yazanfara yimiki bayaniba ” Aunty farida taɗan kakalo murmushi kana tache karki damu Ammi aidaman nasan dawuya mai martaba yabanisu saboda tunfarko yanuna aa bazai bayarba amma bakomai wlh Ammi gobe zanwuche zanbi jirgin karfe 7
Ammi tache to allah ya tsare hanya feeda Aunty farida tamike tana fadin ameen tanufi hanyar fita tana fita kai tsaye tayi bamgaren Ummi

Washe gari misalin karfe 9 na safe gaba daya family suna palon mai martaba zaune akan table din chin abinchinsu gaba ɗayansu har dasu don amma banda su diyana da zahra da mai martaba
Mai martabane yafito daga ɗakinsa yazo ya zauna a kujera nanfa kowa yafara gaidashi gaba ɗayansu yahadesu yabasu amsa ɗaya san nan yache inasu diyana
Ammi tache suna daki ” mai martaba yache to mryafaru basu fitoba
Ammi tache wlh nayi nayi suzo muchi abinchi hiyana tache itakam wlh tana tsoran yayansu bazata iya zuwaba gaskiya kuma daga yauma a daki zata rinka zama to saurankuma dasukaga yayartasu taki zuwa suma sukache bazasu iya zuwaba dana nuna zan matsamusu sai suka fara kuka shine na kyalesu zahra’ma na tare dasu,
Mai martaba yache ai daman nasan zaayi hakan ɗayanku yaje yakiraminsu
Mikewa yusuf yayi yache bari naje da kaina na shawo kansu kila idansuka ganni zasuzo
Wani kallan banza don ke wurgawa yusuf amma yusuf ko ajikinsa aryan kuwa sai hararan yusuf din yake amma yusuf baibi takansuba yayiwaje

Da sallama yashiga palan lamrat kawai yasamu zaune tana kallo tsayuwa yayi yana kallanta kusan 5 mnt yana tsaye itakuma Sai kallanta take batasan da mutunba
gyaran murya yaɗanyi
Ta ɗago aiko tana kallansa tamike tawatsa a guje sai chikin ɗaki “. Dan ita atunaninta don ne dan bata iya rabesu
Binbayanta Yusuf yayi har chikin dakin da sallama yashiga suna zaune kan gado suna ganinsa dukkansu suka rungume hiyana suka kame jikinsu waje guda banda zahra ” zahra kam nitsuwa tayi murya na rawa tache ina kwana yaya yusuf ga mamakin ta sai taji yache lfy baki sake zahra ke kallansa tun datake dashi bata tabajin ya amsa gaisuwar waniba a gidan nan amma yau ya amsa nata tab to kodai mafarki takene tayi nisa chikin tunani saitaji muryan shi yana faɗin
Hiyana tashi kizo ” murya na rawa hiyana tache dan Allah kayi hakuri tana magana tana hawaye wlh nibansan ruwanka bane shiyasa na dauka amma dan allah kayafemin karkasake dukana bazanma sake zuwa wajen chin abinchinbama kaji
Tana chikin magana kawai taji ansa hannu ana share mata hawayen dake gangarowa daga fuskarta da sauri ta dagokai murya na rawa tache..

Pls more comments an share
*💫STAR LADY💫*

 

*DUK ƘARFIN IZZATA*

💖Story And Written💖
⬇️

 

Leave a Reply

Back to top button