Gidan Aunty Book 1Hausa NovelsHausa Novels

Gidan Aunty Book 1 Page 28-29

Sponsored Links

BOOK 1

BONUS

PAGE 28 and 29🦋
2 page ne na hade muku🫶.

“IMPOSSIBLE “cewar king da idanuwansa suka fara canza launi,cikin bacin rai, be bari abeey ya kara magana ba cikin sarkewa,” how on earth abeey zakace na auri wannan yarinyar, as small as she is, yarinyar da in da Auran wuri nayi zan haifeta, please abeey mana I can’t marry her,never”, cikin sauri abeey ya kallesa ganin yadda idanuwansa suka fara canza kala ,yasan ransa ba karamun baci yayi ba Amma shima ba yadda zayyi tunda babu Wanda yake wucewa kaddarar sa,”bazaka iya aurantaba kake fadamun” abeey ya fada azafafe, “yes I can’t marry her ,and I will never “cikin bacin rai abeey ya mike tsaye, “shikenan kaje Kayi duk yadda kaga yayi maka tunda ban isa da Kai ba,yau ni ka kewa musu akan abunda na umarceka dashi, nagode sosai, Allah yajikan dan uwanka Muhammad nasan da yana raye da shine zaimun wannan alfarmar ya aureta”ya karasa a raunane , cikin sauri king ya dago da idanuwansa jin sunan da abeey yakira,”abeey” yakirawo sunansa a sanyaye, daga masa hannu abeey yayi “bana bukatar jin komai daga bakinka, kaje kayi duk yadda kakeso”, yana gama fadar hakan ya kama hanyar fita, jiri ne ya d’ebesa zai fadi cikin zafin nama king ya riko hannunsa tare da zaunar dashi, kara tashi abeey yayi wani jirin na kokarin ka yadda shi,”bana bukatar temakonka “, rintse idanuwansa king yayi, cikin sanyin murya ya furta “am sorry abeey, please ka zauna”be kulashiba sai ma kokarin tafiya da yayi “ Dan Allah “ king ya kara fada kamar Wanda nunfashinsa zai fita daga gangan jikinsa, kallansa abeey yayi duk da tsananin tausayinsa da yakeji a kasan zuciyarsa, azahiri kuwa hade ransa yayi shima, waje ya samu ya zauna , “am sorry abeey” king ya kara fada har yanxu idanuwansa na kasa,”ba fushi nake da kai ba,amma inaso ka tuna halin da amminka zata shiga, da me kake so taji da rashin ganeta da yarinyar bata yiba ko da rashin temakonta da zakayi,karka manta kai me temakon Al’umma ne, meyasa bazaka tausayawa rayuwar yarinyar nan ba ,sanadiyyar rashin mahaifiyarta da d’an uwanta tashiga wannan halin, kayi tunani inda nine..” be bari abeey ya karasa zancan nasa ba king ya soma magana” zan aureta amma da sharadi” da sauri abeey ya kallesa murmushi na kokarin su’buce masa,abunda bai taba tsanmanin jiba daga garesaba, bai kalli abeey ba yaci gaba”maganar yan uwanta zan sa a bincika,I will marry her just for her condition, idan memory dinta ya dawo zan saketa “ kallansa abeey yayi jin ya anbaci saki, amma be ce masa komai ba,yanxun ma be kalli abeey ba,”and it has to be a secret marriage,wannan ba aure bane temakone kawai data warke zan sauwake mata” yana gama fadar hakan ya kalli abeey, shima har yanxu abeey din shi yake kallo” na amince” abeey ya furta yana sauke ajiyar zuciya. Be kuma kallan abeey ba ya mike tare da shigewa toilet , da kallo abeey ya bishi yana girgixa kai, kafun ya mike tare da fita daga dakin, tunda ya shiga toilet ba abunda yayi sai jin gina kansa da yayi da kofar toilet din, sosai kansa yake sara masa,sink ya kunna,a hankali yake watsawa fuskarsa ruwa, ya dau godon lokaci a haka kafun ya fara sauke a jiyar zuciya, karar da ya Jine yasa shi bude idanuwansa da Sauri tare da barin toilet din, kwance take a inda ya barta , jikinta sai faman karkarwa yake, kara sakin wani karan tayi,”ze tura ta, ze turata “ shine abunda bakinta yake faman furtawa,a hankali ya karasa wajan tare da dora hannunsa kan goshinta, a matukar razane ta farka ,”Zee.. turata…. Zeee turata ,mugune shi” ta furta tana kokarin barin gadon, ganin yadda ta fita a hayyacin tane yasashi rike dan tsan hannunta, ture hannusan ta shiga kokarin yi, ganin ta kasa kwacewa ne yasata fashe cewa da kuka, “ze tureta “ ta kara furtawa, “shhhh” ya furta mata, bata kulawa ba sai kokarin kwacewa da take , tsawar da ya daka matane yasata hadiye kukan nata tana girgiza masa kai hawaye na futo wa daga idanuwanta,”zauna “ ya furta mata tare da sakinta, can nesa dashi ta zauna tana takurewa waje daya, yadda tayine yasa shi kallonta,”ya Allah “ ya furta kafun ya mike ahankali da nufar inda take, zama yayi daga gefen ta kadan , ganin tana kokarin ja da baya ne yasa shi kallanta “me ya faru”,lan gwabar masa da kai tayi tana turo baki, idanuwanta duk sun Tara kwalla, yadda tayi da fuskar ta tane yasa ya zuba mata idanuwa,kusan tsawan mintuna biyu yana kallan kyakkyawan fuskarta , ganin ta motsane ya sashi dauke idanuwansa,da sauri tahee ta kallesa “daddy na”ta karasa kwallar data tarar mata yana zubo mata, be ce Mata komai ba sai kallanta da yayi “mugune shi zai turata fa” zuwa lokacin harta fara shash sheka ,”it’s ok karkiyi kuka “ ya furta kamar wadda akasa dole , kara turo bakinta tayi gaba zata sake magana ya dakatar da ita,” yanxu zan tanbayeki, ki bani amsa kinji” gyada masa kai tayi kamar wata yarinyar, dafe goshinsa king yayi yana taunar le’be,” yaya sunan ki” ya furta a hankali,”shiru tayi kamar me tunani sai kuma ta washe fararan jerarrun hakoranta,”dady” ta furta tana tafa hannayenta, ya tsawa kallanta yayi “bani ba , sunanki na tanbayeki”, yanxun ma kara turo bakinta tayi,”sunana dady”,jinjina mata kai yayi batare da yace mata komai ba “dady”ya furta a kasan zuciyarsa,”I have a lot to do kafun na sake ki, I will try my best hankalinki ya dawo before I divorced you “, mikewa tsaye yayi ganin lokaci na tafiya, wasu magunguna ya dauka tare da allurai yasasu cikin wata bag kafun ya kalle ta,”Taso mu tafi” kamar jira take ,cikin sauri ta mike ta karaso inda yake , hannunsa ta rike gam kamar wacce za’a kwacewa ,be ce mata komai ba suka nufa barin office din, tunda taga sojojin dake ganin wajan jikinta ya fara rawa ta kara kankame hannunsa sai faman buya take a bayansa,zaki ne ya karaso wajan tare da sara masa, a guje ta juya daniyar guduwa cikin tsoro ganin kayan jikinsa,riko hannunta king yayi ganin ta tsorata da sojojin dake wajan, jakar hannunsa kawai ya mika wa zaki,kudun dune shi tayi tana kara buya a jikinsa,”Ya Allah” ya furta cikin zuciyarsa kafun ya fara tafiya da ita, dakin da su ammi suke ciki ya nufa, har yanxu suna a yadda ya barsu, kallo daya yayi musu tare da dauke kansa, ammin sa kawai take tunani ganin irin ramar da tayi lokaci d’aya,”tahura taho nan dada ce” dada ta fada tana miko mata hannu,kara boyewa tayi bayan king, matsowa dada tayi daniyar tabata, bata Ankara ba saiji tayi tahee ta fashe da kuka ,sallallami dada ta saka”Innalillahi wa inna ilaihi rajiun,ke yayi zafi “ dada ta fada tana sakin baki, duk kallanta su ummey sukai, itama ammin kokari take tayi magana amma ta kasa sabida yadda muryarta ta dushe, ummey ce tayi karfin halin magana”ya jikinta” kamar yadda ya fadawa abeey itama hakan ya fada mata “she lost her memory “ da sauri ta dago da idanuwanta tana fadan sunan Allah,kallanta dada tayi “yimun bayani naji yana mamori (memory)”, nunfashi ummey ta sauke kafun tayiwa dada bayani, itama dadan salati ta dauka , ammi ko jinsu batayi sai bin tahee da kallo da take, itama taheen tana bayan king tana binsu da ido ta rikesa gagam , shigowar abeey ne ya katse musu shirun su, da sallama ya shigo dakin fuskarsa dauke da yalwataccen murmushi, kallo daya yayi musu ya dauke kansa tare da kallan dada, “dada ya kamata mu goma gida ko, Inyaso sai a tattauna a can”, gyada masa kai dada tayi da Sauri”eh haka ya kamata,amma ita tahuran fa”, kallan king abeey yayi, shima king kallan yadda ta rike sa yayi kafun ya kallesu “zan taho muku da ita” abeey besan lokacin da murmushi ya subuce masa ba ,be ce komai ba ya kalli dada” dada tunda zai taho da ita kinga sai mu jira su a gida “ yanxun ma kai dada ta daga masa ,dukansu mikewa sukai tare da barin dakin,har lokacin tahee na tare da king,yana ganin sun shiga lifter ya juya tare da koma wa office dinsa,suna sauka premises ba bata lokaci suka shiga motocin da aka fito dasu, manyan sojoji na biye dasu, Kai tsaye hanyar da zata sadasu da gida suka nufa.

🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧

KANO

Tana zaune cikin dakin da zahra ta bude mata har yanxu ,so take ta rama sallolin da ke kanta amma batajin zata iyayi da kayan jikinta, tana cikin wannan tunanin taji an kwankwasa kofa,”shigo “ ta furta a sanyaye, zahra ce ta shigo cikin dakin bakinta dauke da sallama,bayanta ma khaleed ne da manyan ledoji, ledojin suka ajje mata,ko wanne fuskarsa dauke da murmushi, “oumma gashi dady yace akawo miki”kwalla ne oumma taji yana san taran mata,”nagode sosai “ ta furta musu, ganin yanayin da take cikine yasa ba Wanda yayi magana,har zahra zata bude baki khaleed yayi saurin rike hannunta” oumma bari mu baki waje ki shirya”jinjina masa kai tayi tana ajiyar zuciya, kama hannun zahra yayi tare da barin dakin,tsawan mintuna biyar tana zaune a inda suka barta ganin lokaci na tafiya ne yasa ta mike ,daya daga cikin ledojin ta bude, manshafawane da yawa a ciki da turaruka,dayan ledar kuma abayoyine da hijab a ciki, harta sa zata hannu zata bude ledar karshe sai ta fasa tare da shiga ban daki, tsawan lokaci kafun ta fito daya daga cikin abayoyin ta saka tare da kabbara sallah ganin alkibla, ta dade tana sallolinta ,har amrah ta dawo dauke da babban tray a hannunta, bata fita a dakin ba sai ma jera wa oumma kayan tayi a cikin kwabar dakin,ganin ta idarne yasa zahra dakko abinci da ta shigo dashi tare da ajje mata “oumma ga abinci , maganinki kuma suna wajan dady” dan murmushi oumma ta sakar mata,”Tom nagode da kulawa”sosai zahra ta washe hakwaranta kafun tayi wa oumma sallama , bin ta da kallo oumma tayi tana jinjina karanci irin da su a wannan zamanin, kallan abincin da aka kawo mata tayi ,kwallan da take kokarin boyewa suka sauko, saurin goge su tayi tana istigfari aranta “Allah na tuba , Kai ka dai ne abun bautawa,Allah kaine mahaliccinmu sannan kafi kowa son bawanka, Allah na rokeka ka karesa a duk inda yake” sosai tashiga yi masa addua tare da tahee tsawan lokaci ,kafun ta tsakuri abincin da aka kawo mata, ji take kamar tana cin magani ,a haka taci kadan tare da ajjewa…..

🫧🫧🫧🫧

Tunda suka dawo gida babu Wanda ya kara tada maganar, Kai tsaye part din dada suka nufa baki d’ayansu, waya abeey ya dauka tare da kiran mutanan gidan, gabaki d’aya ya umarce ganin manyan gidan,a karshe ya jaddada musu kar yaron da yazo wajan,kowannansu amsawa yayi cikin kan kanin lokaci suka halarci babban falon dada. Lokacin da uncle Salem ya kira aunty suna zaune ita da amrah , sun hada dan karamin kwarya kwayar walima,ko wannansu inka duba fuskarsa zaka ganta dauke da farin ciki,musamman amrah da ta fi kowa farin cikin jin labarin mutuwar tahee, suna cikin wannan yanayin ne uncle saleem ya kira aunty, cikin sauri ta dauki wayar tana kashe murya cikin damuwa,”Muna falon dada kizo ke kadai”yana cewa hakan ya katse wayar tasa, aunty har da mikewa dan murya kasan cewar a speaker ta saka wayar, kamar wasu kawaye haka suka tafa ita da Amrah, jin yadda uncle saleem yayi magana cikin sanyi yasa suka kara yadda da mutuwar taheen, mayafinta dake kan kujera aunty ta dauka tare da yafawa, kallan amrah tayi tare da kashe mata ido daya bayan ta marairaice fuskarta gwanin tausayi kafin su saki dariyar keta aunty ta nufi hanyar barin part din tare da nufar part din dada.

A zazzaune ta tarar dasu kowa yayi jigum dashi,itama karasawa tayi fuskarta cikin sanyi kamar ba itaba, ganin yadda ko wannansu yayi jigum dashi yasa ta bude baki da niyar yi musu ta aziya,gyara zama tayi sosai tana saita muryarta “Aushe abunda ya faru kenan ,Allah ya jikan…” bata karasa ganin yadda ko wannansu ya zuba mata idanuwa suna jirin jin me zatace, dada ce ta katse su ta hanyar kallan abeey,”ka Tara kowa ,ka Hana yara zuwa ko zaka fada mana dalilinka na yin hakan”, gyada mata kai abeey yayi kafun ya gyara zamansa,”kamar yadda kuka sani , d’aya daga cikin ahalin gidan nan kaddara ta fada mata da Hakan yayi sanadiyyar samun babban rauni a gareta amma duk da hakan muna godewa Allah da takaita,sannan inaso ko wannanku yaci gaba da tayata da addua kasan tuwar ta manta tunaninta wato ta rasa memory dinta”, tunda abeey Ya fara magana aunty take kallansa, jira take taji ya ambaci mutuwar tahee, amma shiru ganin kamar bata mutum bane kamar yadda sukai tunani yasa zuciyar aunty tashi,tana cikin wannan tunanin ne kunnuwanta suka jiyo mata kallan data kwantar mata da hankali na memory din da tahee ta rasa,”wannan ma abun jin dadin mune tunda ta rasa tunaninta” aunty ta fada cikin zuciyar ta,”a karshe ina mai farin cikin sanar daku cewa ,a yau dinnan rana me kamar ta yau an daura Auran tahnoon zayed al-nahyan tare da amaryarsa taheera mohammed” a zabure mutanan falon suka kallesa, aunty har wani kwarewar azaba tayi a makoshinta, Sam ta manta a inda take azabure ta furta “aure fa kace,Sam bazai yuba”gabaki d’aya falon kallonta sukai cikin mamaki,shima abeey kara hade ransa yayi”kamar ya kenan “ ya furta yana kallanta, sai lokacin ta gane katobarar da tayi ,cikin in ina ta soma magana “daman inaso nace kamar hakan yayi wuri”dauke kansa abeey yayi tare da kallan dada datayi shiru,”dada da fatan hakan be bata miki rai ba” jimmm kadan dada tayi cikin dattako ta jinjina masa”tabbas ka cika uba na gari amma bani zaka tanbaya ba ,iyayensa yakamata ka tanbaya”ta karashe zancenta da kallon su ummey, itama ummey bata amsa ba sallan ammi da tayi, girgiza Kai ammi tayi cikin sanyin jiki,”gaskiya baza ayiwa don Auran dole ba inde ba da amincewarsaba “ ta furta muryarta a sanyaye case dan murmushi abeey ya saki,” ya amince “da sauri kowa ya kalli abeey cikin mamaki, ya bude baki daniyar sake magana kenan, daddadan kamshin turaransa ya cika ko ina na dakin,kowa maida hankalinsa yayi kan kofar shigowa , a hankali yake taku, bayansa tahee ce dake faman rakubewa a gefansa,har ynxu kanta da bandage din da aka nade mata ciwonta, be kalli kowa na falon ba yasamu waje ya zauna kan daya daga cikin kujerun falon, itama taheen zama tayi a gefensa tana rike masa rigar jikinsa ganin irin kallan da yan gidan ke binta dashi,gyaran murya abeey yayi yana kallan king da ya ki dago da idanuwansa, cikin dakewa abeey ya kalle sa “ nasan kun gaji, ya kamata ku huta” ya karashe zancen nasa yana kallan king har yanxu , kin dago da idanuwansa king yayi sai sallamar da yayi musu yana mikewa,da sauri tahee ta mike tana kokarin binsa, da mamaki yake kallanta yana mamakin inda zata,be ce komai ba ya juya daniyar tafiya, taku biyu yayi itama ta soma binsa, kara jiyowa yayi yana kallanta, a dake ya furta “ina zaki”, langwabar masa da kai tayi”dady”,muryar abeey da yajine yakatse shi daga yin magana”ku tafi tare”abeey ya kara fada, taune lips dinsa king yayi tare da soma magana, ganin hakan yasa cikin sauri tahee tabi bayansa, tsabar mugun ta yau be shiga motar ba,a kafa ya soma tafiya ,itama bata gaji ba a haka take binsan, ganin kamar tana kokarin faduwane yasa zaki ya karaso da motar inda suke, baya king ya shiga, TAHEE na biye da shi sabanin dazu yanxu ta rike masa Riga ganin zaki na wajan, a Daidai part dinsa zaki yayi parking,Kai tsaye ciki suka shiga, be kalli inda take ba ya nufa daya daga cikin kofofin kasan , Daidai ya soma balle rigar jikinsa itama ta shigo dakin, da mamaki dauke kan fuskarsa ya kalleta “me kika shigo yi anan” da Sauri ta furta “ni tsoro nake ji”tana turo dan karamun bakinta,kamar bazai kula ba ya kalleta”zauna”,cikin sauri kuwa ta zauna ,wata kofar ya nufa dake gefensa”karki kuskura ki biyoni”gyada masa kai tayi tana turo dan karamun bakinta, yana shiga ko munti uku beyi ba ta mike “Allah ni sai na bika dady” ta karasa zancan nata tana tun karar kofar dakin,bazato ba tsammani ya ji an shigo dakin, da sauri ya juyo dan ganin wanda yayi wannan gangancin, itama ihu ta saki tana kokarin juyawa, san shine ya kwaceta tayi baya zata fadi ,cikin azama ya riko ta towel din jikinsa na kokarin kwancewa,gaba dayansu baya sukai zasu fadi ,Allah yaso akwai sofa daya a wajan suka fada kanta dukansu,shi yana kan sofa din itama tana kansa,hannunta ne ya sauka kan towel dinsa, manyan idanuwansa ya zaro waje yana kokarin tureta, itama kuma sai faman taba towel din take kafun ta kalle sa”dady Menene wannan abun”……..

ALHAMDULILLAH……..
Mu hadu a next page ,ina Godiya sosai masu comment,masu yimun ya jiki kuma nagode sosai Allah ya bar zumunci, Aunty sadeeya (mrs bbk), masoyiya (star lady) da gabaki d’aya team din the talent troupe writers inayinku over ,Allah ya bar zumunci💔💖💖💖🫶.

MSS LEE💖
💖💖💖 GIDAN AUNTY 💖💖💖
(a heart touching love story)

Story & written
By

Mss Lee 💖💖

💖💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖💖

MAISAN COMPLETE DIN GIDAN AUNTY YAYI MUN MAGANA TA WANNAN NUMBER:
07041879581

Leave a Reply

Back to top button