Duk KarfinIzzata Book 2Hausa NovelsHausa Novels

Duk Karfin Izzata Book 2 Page 10

Sponsored Links

Book 2

*Episode 10*

UK

A nitse hiyana ta chire jikakken kayan jikin ta ta dauki farin towel mai kyau da laushi dake gere awajen drawar ajiye kaya ta ɗaura a kirjinta zuwa dai dai chinyar ta towel ɗin ya tsaya kwanche gashin kanta tayi subhanallah hiyana tafi diyana gashi nesa ba kusa ba domin ita gashin ta ya kai har karshen bayan ta gashi bakin kirin mai laushi da tsantsi sai sheki da kyalli yake, a hankali take tafiya kamar bata san taka kasa duk in da tayi taku ɗaya sai jikin ta ya girgiza, tafi diyana halittar komai akoi ta da manya manyan boobs ga hips nata kamar zasu fashe in dai fannin shap ne baa magana hiyana karshe che, kai tsaye toilet ta shiga, kokarin kwanche towel dake jikin ta take karaf blue eyes nata ya sauka kan ɗan karamin machijin dake ta yawo a chikin baff ɗin wanka tsantsi ya hana shi fita ya gudu, wani ihu ta saki tayi waje da gudun gaske, tama manta babu kaya a jikinta daga ita sai towel, dai dai tsakiyar palon part nasu tayi karo da Bgs kankame shi tayi sosai a ruɗe take faɗin “yaya prince machiji wlh machijine a toilet na” chikin tsawa yace “ke sakeni!!” a razane ta ɗago kanta tana kallon face nashi, da mamaki yake kallon razananniyar face nata tunani ya shigayi wacece wan nan kuma ko dai itace matar da aka kakaba min, shiru yayi, yana kallon yadda take juya idon ta chikin tsoro tace “wlh yaya prince yau ko kasheni zakayi bazan sake kaba sai dai ka kasheni wlh tsoron machijin nake” runtse ido yayi chikin tsawa yace “ki sakeni nace ko!! kara kankame shi tayi da kyau ta chusa kanta chikin faffadar kirjin sa ta fashe da kuka tana kuka tana magana “wlh yaya prince ba zan sake ka ba” a fusache ta damko wuyar ta da nufin yayi wurgi da ita, a razane ta ɗago blue eyes nata da suka fito waje sosai saboda shakan da ya ma wuyar nata tana kallon sa, a hankali ya zame hannun sa daga kan wuyar ta kasa kasa yace “sake ni” sake harɗe sa tayi ta rikesa sosai, bashi da wani zaɓi dole ya mata abun da takeso, tsaki yaja tare da saɓa ta a kirjin sa tare da tallaɓo bayan ta ta kasa ya nufi ɗakin nata, sosai hiyana ta shiga jikin sa, kai tsaye toilet suka nufa.

Chikin dabara yasa hannu ya damki kan machijin, ya juya ya nufi waje tana makale a saman kirjin sa, dai dai tsakiyar palon part nasu, kasa kasa yace “ke sauka na chire machijin” dago kai hiyana tayi karaf blue eyes nata ya sauka kan machijin dake hannun sa a reke ihu ta sake ta kankame da karfi nan take kuma ta ɗauke diff kamar an ɗauke wutan nepa, ji yayi tana kokarin zame wa daga jikin sa ta faɗi kasa chikin sauri ya kankame ta da kyau, tsaki yaja ya juya ya nufi betroom nashi da ita saman katafaren gadon sa ya kwantar da ita san nan ya fito ya nufi waje, Abdol ya mikawa machijin ya koma chikin gida.

yana shiga ɗakin sa call ɗin Ammi na shigowa wayarsa a nitse ya chiro wayar daga aljihun sa, ganin sunan Ammi ne ya bayyana a kan screen din wayar hakan yasa shi yin picking da sauri manna wayar yayi a kunnensa tare da faɗin “Assalamu alaikum” daga ɗayan ɓangaren Ammi ta amsa masa da “wa’alaikumus salam” “my Ammi y kuke y gd? “lfy lau ya yan uwan ka? “Suna lfy” “ina son yin Magana da Hiyana ne ka bata wayar” sai lokachin ya ɗago ido ya sauke su saman gadon sa, kwanche take kamar yadda ya kwantar da ita ko motsi bata yi “Ammi tana barchi amma idan ta tashi zan kiraki sai na haɗa ku” ba ƙaramin daɗin jin hakan Ammi tayi ba “to amma idan ka fita ka saya mata waya mai kyau kawai dan idan na tashi magana da ita ba sai na kiraka ba” chikin sauri yace “ok za ayi yadda ki ka che” “au shine ka amsa da wuri dan kar na che karinƙa haɗa mu ko? Wato muna takura maka ko? “Aa Ammi kawai maganar che tazo da wuri” “to shikenan ba zan gaji da tunatar da kai ba, kasani duk abun da kayiwa Hiyana na chutar wa idan mu bamu gan ka ba Allah na ganin ka, ina kara rokan ka dan Allah ka kulamin da marainiyar Allah nan kada ka bari tayi kuka idan tayi kuka to tamkar ni nayi idan ka sanya ta kuka tamkar ni ka sanya” ɗaure fuskar sosai yayi ji yake kamar ya katse kiran ita Ammi nan kullun ta kira mutun wa’azi wa’azi, to mutun yace bai san yarinya amman an kakaba masa dole san nan yanzu kuma arinƙa takurawa mutun da zanchen hakki hakki ni gaskiya abun nan ya isheni “au yanzu ina maka ma shiru kamin ko? “Ammi ba shiru nayi ba karki damu ina iya bakin kokarina” “to ka kara kokari kaji? “Ammi pls bari nayi picking call ɗin wani” yana gama faɗin hakan ya katse kiran batare da ya jira amsar taba yayi wurgi da wayar saman sofa tare da jan dogon tsaki ya nufi saman gadon sa, gefen hiyana ya kwanta tare da lumshe ido ba jimawa barchi yayi awawon gaba da shi

A chikin barchi yaji mutun na numfashi da kyar da kyar kamar wadda aka shake, Slowly ya waro green eyes nashi mai chike da barchi alamar barchin bai ishe sa ba, kan Hiyana ya sauke su, kallon ta yayi from head to toe tsaki yaja kafin ya zame hannun sa dake kan chikin ta yana ɗauke hannun nasa ta miƙe chikin sauri tana bin jikin ta da kallo da gudu ta fice daga ɗakin tsaki yaja ya mai da idon sa ya lumshe

Har ta kai tsakiyar palo kuma sai ta juyo a kuje ta koma ɗakin sa, jin mutun ya shigo yasa ya waro green eyes nashi akan ta ji tayi kamar ta nitse kasa dan kunya gashi kuma tana tsoron ɗakin ta dan tun da taga snake tofa bazata iya zama a ɗakin ba ko kasheta za’ayi bazata zauna a chan ba

Chikin tsawa yace “me ya dawo dake ɗakin nan” murya na rawa ga masifaffen kunyar sa da takeji tace “ya ya yaya prince wlh tsoron ɗakin nake ji nake kamar akoi wani machijin a chiki” mai da idon sa yayi ya lumshe batare da ya sake magana ba kalaman Ammi ne kawai ke masa yawo a kwakwalwa sa yana matikar son Ammi baya son ɓachin ran ta san nan baya son hanyar da zata haɗashi da yarinyar nan kai ba ma itaba baya son hanyar da zata haɗashi da mace kwata kwata, dan har yau yana kan bakarsa na chewa duk wadda mace ta raɓa tofa ya zama mai rauni, shi kuma kwata kwata bai san mutun mai rauni

Sai rawan sanyi hiyana take kasan chewar Ac ɗakin a kunne, gashi babu kaya a jikin ta, almost 15mins tana tsaye shiko yana kwanche idon sa a lumshe kasa kasa hiyana ta fara kuka dan sanyi da yayi mata yawa, tana son ta je ta ɗauki blanket nashi ta rufu amma tana tsoro tun tana sa ran zai mata magana har ta chire rai ta chigaba da kukan ta kasa kasa tana rawan sanyi
Almost 20mins ta kara kan 15 na ɗazun, gajiya tayi da tsayuwa ta lallaɓa ta koma saman sofa mai zaman mutun 1 ta zauna ta takure, duk wani motsin da take achikin kunnen sa take dan ba barchi yayi ba ya dai lumshe ido ne yana jinta, kasa kasa yace “ki shiga toilet na kiyi wankan” ba karamin razana da girgiza hiyana tayiba tunani take anya ba karya kunnen ta ya jiyo mata ba, to idan ma ba karya bane gaskiya ba yaya prince bane yayi maganar nan sai dai idan aljani dan ita bata taɓa jin yayi magana da mutun a nitse haka ba kullun chikin yiwa mutane tsawa yake, daman ya iya magana a hankali? tunawa tayi yace ta shiga toilet nashi tayi wanka chikin suri ta mike dan kar tayi laifi ta nufi toilet ɗin.

“Yaya khalid naje ɗakin Aunty hiyana fa ban ganta ba”chewar Zahra dake tsaye tana rike da jallabiyar da yaya khalid ya ɗauko wa hiyana a ɗakin Bgs “Auta mata da mijin ta kuma kike tambayar ina take wata kila tana wajen yaya prince” “haba yaya Khalid kasan dai bazata je wajen sa bakam” “ok to kije ɗakin nashi mana ki dubota sai mu tabbatar” da sauri Zahra ta wuche ta ajiye jallabiyar a saman sofa tana faɗin “kai aa tayi zaman ta ako ma ina take” dariya Khalid yayi kafin yace “to saiki ɗauki hijabin ki muje ai tun da kin ki zuwa ki dubo mana ina sister take su Yusuf suna jiran mu a palo” “to yaya Khalid yanzu kenan zamu tafi ba tare da Aunty hiyana ba? “Eh to mata tana wajen mijin ta zamuje muche tazo muje ne? ki kyaleta idan munje sai ki zaɓa mata kawai idan kuma da wani abun da take bukata sai mu koma gobe” ” to kawai Zahra tace san nan ta ɗau hijabin ta Khalid ya riko hannun ta suka nufi waje

A babban palon kasa suka sami su Yusuf, sun gama shiri suna jiran su “ina Hiyana kuma? chewar Yaya Ahmad” “muje kawai ba zata jeba” chewar khalid, tare suka jera ba wadda ya sake magana suka fita waje, mota 5 sukayi ɗaya Khalid da Zahra ɗaya Fahad da amrat ɗaya Yusuf da Lamrat ɗayan kuma Ahmad, shi kaɗai ɗayan kuma jibga jibgan sojoji yan rakiyar sune a chiki, da gudun gaske suka bar gidan

Chike da jin kunya hiyana ta tafito daga toilet ɗaure da towel ɗin Bgs a kirjin ta wadda yazo mata har guiwa kamar yadda ta barshi kwanche lumshe da ido haka ta fito ta same sa, saman sofa ta koma ta zauna sai rawan sanyi take, jingina kanta tayi da jikin kujerar har barchi yayi awon gaba da ita a haka

Maiduguri Nigeria

A yaune aka sallami su Ahzan daga hospital suka koma gida ba laifi jikin yarinyar yana samun sauki sosai sai dai har yanzu bata magana sai dai kallon mutane kawai take.

Misalin karfe 4pm yarinyar na zaune a palon gidan su Ahzan tayi shiru tana kallon kasa, sanye take da doguwar riga abaya baki wadda mum Ahza ta bata, Ahzan da mum nashi suka fito daga ɗakin mum suka fito palon saman sofa ɗaya suka zauna, a nitse mum ta fara magana “bai war Allah gashi bamu san iyayen ki ba amma ina fatan zaki iya zama damu? a chikin gidan nan ko, abun mamaki sai yarinyar ta amsa da “eh zan iya” a razane Ahzan ya miƙe chike da mamaki yace “daman kin fara magana? Gyaɗa masa kai tayi alamar eh Ahzan da Mum har suna haɗa baki wajen chewa “Alhadulillah Alhamdulliah” “baiwar Allah ya sunan ki? Chewar mum shiru yarinyar tayi kamar mai tunani chan kuma ta fara girgiza kai tana faɗin “ban sani ba” kallon juna Ahza da mum sukayi wayar Ahzan ya fitar daga aljihun sa ya shiga kiran layin Dr walid, bugu ɗaya Dr walid ya ɗauka

“Hello Dr ya Aiki? Daga ɗayan ɓangaren Dr yace “lfy lau Ahzan ya mai jiki” “jiki da sauki dan ita ma na kira yanzu “ok to me ya faru? Ajiyar zuchiya Ahzan ya sauke kafin ya fara magana “Dr yarinyar nan ta fara magana amma abun mamaki mun tambayeta sunan ta tache bata sani ba shin daman ta samu matsala a kwakwalwan tane? “Aa Ahzan ba wata matsalar da kwakwalwan yarinyar nan ya samu lfy lau take kila ta shiga ruɗani ne ku barta ta kara hutawa zata dawo dai dai In Sha Allah” “to shike nan Dr nagode sai munyi waya, yana gama faɗin hakan ya katse kiran ya dawo da kalon sa kan mum, chikin nitsuwa yayi mata bayanin yadda sukayi da dr, addu’a samun lfy mum tayiwa yarinyar, amin Ahzan ya amsa da shi shiru suka zauna ba wan da ya sake che da ɗan uwan sa kala

NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER’💖

*LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
👇👇👇👇

*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
by(Star Lady)

*2,GIDAN AUNTY*
by(mss lee)

*3,SARKI SAMEER*
by(xeemat….love)

*4, JINI DAYA*
by(mrs bbk)

💖The Talent Troupe Writer’s 💖

*DUK ƘARFIN IZZATA*

💖Story And Written💖
⬇️
*Star lady*

Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

Back to top button