Duk KarfinIzzata Book 2Hausa NovelsHausa Novels

Duk Karfin Izzata Book 2 Page 17

Sponsored Links

Book 2

Page 17

Kukan da take ya hanashi barchin sai juyi yake chikin tsawa yace
“kimin shiru!!

Chike da jin zafin zazzaɓi ga azabar zafin da kirjin ta yake mata tace

“gaskiya yaya prince baka da imani sai yau na kara yarda da hakan, baka da tausayi kai mugune wlh duk abun da kamin sai Allah ya sakamin tun da ba abun da na maka, komai mutun ya maka aduniyar nan bai yi dai dai ba mutun baya taɓa gane gaban ka bare bayan ka, natsane ka wlh natsani ganin ka kwata kwata kai ba mutun bane, dan girman Allah ka kasheni ka huta na gaji na gaji da wanan bakar wahalar rayuwar, tun da na taso a rayuwata ban san komai ba ban da hawala, ina rokon Allah da ya sanya ya samu dacewa a lahira” tana magana tana juyi kamar zata mutu da alama bata a chikin hayyacin ta,

a sukwane ya mike zaune yana kallon ta, da alama bata chikin hayyachin ta kwata kwata batama san me take faɗe ba, abun da yake zuchiyar tane ya fito bakin ta ba tare da sanin ta ba,

Shiru yayi yana kallon ta yama rasa mai zai che mata domin yasan ba a chikin hayyachin ta tayi maganar ba, so bai kamata ya hukun tataba abun dake zuchiyar tane ya fito fili bata shirya ba

Da karfi ta dafe mararta tafara juyi tana faɗin
“wayyo Allah na ya Allah kasa karshen wahala tace tazo Allah kasa mutuwa zanyi a yau, na mutu na huta da wanna bakar wahalar wayyo diyana pls ko aina kike idan kin dawo ki kula da su amrat sosai, kar ki bari su shiga ukubar rayuwa irin nawa, ko mutuwa zaki yi ki tabbatar kin share musu hawaye, wayyo Allah na”
shiru tayi da surutan saboda azabar chiwon maran nata ya karu,

yana zaune ya zuba mata ido karo na farko da ya fara jin tausayin wani ɗan adam a rayuwar sa, ya kasa motsawa daga in da yake

wani miƙa tayi lokachin guda kuma sai ta saki, ta ɗauke diff kamar an ɗauke wutan nepa

da sauri ya matso kusa da ita Slowly ya ɗaura hannun sa saman wuyar ta, a hankali ya gangaro da hannun nasa saman saitin tsakiyar kirjinta,da sauri yae ɗauke hannun sa, matsowa bakin gadon yayi ya zura kafar sa kasa ya miƙe, ya nufi, palo

Ruwa mai sanyi ya ɗauko ya dawo ɗaƙin ya haye saman gadon.

Buɗe ruwan yayi ya tarbo a hannun sa, ya shafa mata a fuska, shiru bata farfaɗo ba, sake ɗeban ruwan yayi ya shafa mata nan ma shiru bata farfaɗo ba, kura mata ido yayi sosai a hankali ya kai fuskar sa saitin tata har dogon hanchin su na gogan na juna, kara matso da face nashi yayi sosai ya haɗe fuskokin nasu, har bakin su na gogan na juna, hannu ya sanya ya matse ɗan karamin bakin ta sannan ya ɗora nashi ya shiga hura mata numfashi sa a hankali
bai chire bakin sa ba har sai da yaga alamar ta fara numfashi chikin sauri ya chire bakin sa tare da sakin nata bakin ya koma gefe guda yana kwaɓe fuska.

A razane ta farka tare da miƙewa zaune, tana bin ɗakin da kallon, zuba mata ido yayi yana kallon ta da kyau dan ya tabbatar ta dawo normal ne ko dai har yanzu bata chikin hayyachin ta, lokachi guda kuma ya kawar da kansa gefe yana kwaɓe fuska.

Bata lura da shi a chikin ɗakin ba ta miƙe tana takawa a hankali ta nufi toilet, yana zaune ya kasa komawa ya chigaba da barchin sa.

Wanka tayi ta fito ɗaure da towel, batare da ta lura da shiba ta nufi wajen trolley ɗin ta wasu shegun riga da wando ta ɗauko, rigan mai siririn hannu fari tas mau laushi na roba, wandon kuma baki ne mai ɗan ratsin fari daga ta kafar, ta ɗauko always ta zari pant ɗaya ta sanya Always ɗin a chikin pant ɗin,
ta miƙe ta sanya pant ɗin a jikin ta, zame towel na jikin ta tayi, ta ɗora saman trolley ta ɗuki rigar nata tana kokarin sanyawa karaf idon ta ya sauka a kan face nashi, a razane ta fasa ihu tare da sakin rigar nata ya faɗi kasa ita duk a tunanin ta aljanine mai kama da shi, dan a iya sanin ta by this time ya tafi wajen Aiki.

Watsa tayi ta gudun gaske ta nufi hanyar fita ɗakin tana ihu, tsaki yaja ya miƙe taku biyu yayi ya damko kugun ta ta baya, tsabar tsorata yau aljani ya taɓata ne yasa numfashi ta ya ɗauke, ba tare da ya lura ta sume ba chikin tsawa yace

“a haka babu kaya zaki fita? Shiru yaji kamar an ɗauke wutar nefa kallon face nata yayi yaga alamar ta sume, tsaki yaja ya saɓeta a kafaɗar sa ya koma da ita wajen gadon, wurgi yayi da ita da karfi saman gadon ya juya ya nufi toilet, a gurguje yayi wanka ya fito sauri sauri ya shirya chikin wandon jeans blue da t-shirt ash, bai bi ta kan taba ya fice daga ɗakin, ya tafi wajen Aiki

KANO NIGERIA

gaba ɗaya family Abba suna zaune a palo sai wayan da basa nan, diyana na zaune kusa da Aryan dan taki yarda da kowa a gidan gani take kamar zasu chutar da ita gyaran murya Abba yayi ya fara magana.

“Alhamdulliah Alhamdulliah Allah ya dawo mana da diyana lfy sai dai tana da matsa likitoci daban daban sun dubata babu abun da ke damun kwakwalwar ta, munyi magana da Aryan yace yana son matar sa a haka abar masa kayan sa, da kai shi zai koya mata komai, baya buƙatar yan aiki ko wani abu makamancin haka, zai kula da ita da kan sa idan tana da rabon samun sauki zai chiba da mata addu’a Allah ya bata lfy, sannan Aryan gareka nayi magana da ɗan uwan ka ya sansar da ni yana bukatar ka awajen aiki dan haka sai ka shirya komawa, ya karisa maganar yana kallon Aryan, “sannan magana ta gaba Monday zanje Uk kuma ban yarda wani daga chikin ku ya kirasu ya sanar da su ina zuwa ba, ina son inje in ga irin zaman da suke ne, dan na tabbatar da aiki na a matsayina na uba, ga marayun Allah bayin Allah, akoi mai Magana?

Mikewa Aryan yayi yana faɗin
“Abba zamu wuce tare on Monday ɗin”
yana gama faɗin hakan ya nufi hanyar fita daga palon,

da gudu diyana ta miƙe ta bi shi hannun sa ta rike chike da shagwaɓa tace
“shine zaka tafi ka barni ko? Tsayawa yayi da tafiyar da yake ya juyo suna fuskantar juna chikin sanyin murya ya fara magana

“bazaki zauna da su Ammi bane, suma ai yan uwan kine” make kafaɗa tayi tana girgiza kai tana faɗin

“aa ni dai tsoron su nake ji” ta karisa maganar kamar zatayi kuka

“to shike nan ba sai kin min kuka ba, amma kina jina ki dai na tsoron su, Ammi itace ta haifeki kin ji? Itace mamanki ba abun da zata miki karki ji tsoro kije ki zauna da ita an jima sai ki dawo ɗaki muyi hira”

gyaɗa masa kai kawai tayi tare da sakin hannun sa, ta nufi wajen su Ammi dake zaune kusa da Abba gaba ɗayan su sun zuba musu ido suna kallon ikon Allah yau diyana ce ta dawo hakan,

“Aa Aryan ku tafi tare da ita tun da tafi sakewa da kai” chewar Abba

“to Abba ke zo mu tafi”
tun bai gama rufe baki ba ta juyo a guje ta dawo wajensa ta kama hannun sa, juyar da hannun nasa yayi ya rike nata suka fice daga palon

“Kai wai daman sunan ka Aryan? Ta tambaya lokachin da suƙe ficewa daga part na Abba”

“eh sunana kenan sunan bai yi bane?

“Aa yayi amma ina ji kamar na taɓajin sunan kuma inaji kamar na sanka kamar na taɓa ganin ka, da wanchan mutumin yace Aryan sai naji zuchiya ta buga da karfi kamar na taɓa jin sunan,

a sukwane ya juyo yana kallon ta lokachi guda farinciki tamamaye zuchiyar sa
“Alhadulillah Alhamdulliah ya fara furtawa ko ba komai diyana ta fara jin sunan shi a zuchiyar ta In Sha Allah nan ba da jimawaba zata dawo dai dai ashe Dr yayi gaskiya.

Tsabar farinciki yasa ya duƙa ya ɗauke ta chak ya karisa da ita chikin part nashi

“Aryan kasan me? Allah ina son shan sweet”

kasa kasa yace
“ba Aryan zaki rinƙa kirana ba kinji? Yayi maganar dai dai lokacin da suka karisa chikin betroom nashi

“to wani suna zan rinƙa kiranka da shi kenan?

Sauke ta yayi a saman katafaren gadon sa yana faɗin

“daga yau sunana habibi”

“to habibi nache maka zan sha sweet irin wannan sweet da Aunty Hanan ke bani kullun da safe”

“ok bari nayi wanka na shirya idan zanje wajen D P O sai na sawomiki, yakalan sweet ɗin yake?

“Sweet ɗin fa yana nan kamar wani abu haka yana da ɗan wasu abu farare kamar kasa a chikin sa yana da danko sosai, kuma….bata karisa maganar ba ya dakatar da ita chikin sauri

“ke waya ke baki irin wannan abu kuma idan suka baki keda waye kuke sha!?

“Ni kaɗai nake sha idan nace Aunty hanan ta sha sai tace yaya Ahzan ya hana kowa sha sai ni kaɗan”

da sauri ya dawo in da take hannun ta ya kama yana kallon kwayar idon ta, yayin da itama shi take kallon tabbas yanzu ya kara tabbatar da zargin sa akan su Ahzan domin kuwa gashi karara abun ya bayyana a chikin idon ta shi yake bawa diyana abun da zai sanya ta rinƙa mantawa da rayuwar ta na baya, duk lokacin da tasha ba zata tuna komai na rayuwan ta na baya ba sai dai wadda take yanzu shi ya sanya take manta kome ta dawo kamar wadda tayi loosing memory lallai idan kuwa haka ne Ahzan tashi ta kare.

Sosai yake kallon chikin idon ta duk da ba karatun likita yayi ba a iya sanin sa dai wannan magani baya wuche 24h ajikin mutun karfin maganin yake karewa mutun ya dawo dai dai wannan shine dalilin da ya sanya Ahzan ke sanya hanan kowani safiya ta baiwa diyana guda ɗaya.

A fusace Aryan ya sake hannun ta ya juya ya nufi hanyar fita yama fasa wanka gaba ɗaya idon sa ya rufe baya ji baya gani burinsa kawai ya isa ga Ahzan ya masa bugu ɗaya wadda zata sadashi dasu walakiri.

Har ya kai bakin kofar fita sai kuma ya tsaya chak a hankali ya juyo tana zaune yadda ya ajiyeta tana kuka kasa kasa ga hayaye sharɓa sharɓan akan face nata ganin kukan nata ya sanya yaji zuchiyar sa ta ɗanyi sanyi chikin sanyin murya yace

“menene ya faru kike kuka?

“To ba kai ne zaka tafi ka bar ni ba” tayi maganar chikin kuka da shahsheka

hannu kawai ya buɗe mata ba tare da yayi Magana ba, da gudu ta miƙe ta taho ta faɗa jikin sa tana dariya kamar ba itace mai kuka yanzun nan ba, rungumeta yayi sosai ya sanya hannu ya ɗago habar ta ya manna mata kiss a goshi

“habibi bafa a goshi akeyi ba na gani awayar Aunty Hanan a baki akeyi”

shiru ya ɗanyi kafin yace
“ok zan miki a baki idan mun dawo amma yanzu dai muje sauri nake”

“ni dai Allah habibi ban yar da ba idan bakamin a baki ba ba zan tafi ba”

chije lips nashi yayi da karfi Ahzan ya chuche sa baya son yayi kissing nata bata chikin hayyachin ta ya kamata first kiss nasu ya kasance gaba ɗayan su suna chikin hayyachin su kuma suna shaukin abun

“kiyi hakuri muje mota sai nayi kissing naki a chan ko kinga sauri nake yanzu”

kukan shagwaɓa ta farayi tana buga kafa a kasa, dukawa yayi ya ɗauke ta chak yayi waje da ita dan ya lura idan ya biye mata bazasu tafiba kuma shi gaskiya ba zai iya ɓata first kiss na shi ba ba zai iya kissing nata bata a cikin hayyachin ta ba.

Gudu Shahram yake da mota ga motochin sojojin su biyu a gaba uku a baya, diyana na kwance a jikin sa sam taki yarda ta sake shi sai satar kallon su Shahram yake ta chikin mirrow motar tana ta zuba shagwaɓan ta shi kuma yana biye mata.

“Habibi ka manta baka min umm yama sunan abun, shiru ta ɗanyi ta ɗaga kai sama kamar mai tunani yauwa bakamin kiss ɗin ba,

wani wawan birki Shahram yaja wadda ya sanya su gaba ɗaya tafiya luuuu suka bugu da kujerar gaba na motar, ji kake kiiii motochin jibga jibgan sojojin dake baya sun taka birki har sai da motar baya na karshen ta ɗan daki na kusa da ita, dan birki taki jawuwa da wuri.

Chikin tsawa Aryan yace

“are you mad!!? Wani irin birkine haka muna tsaka da gudu”

chikin rawar murya Shahram yace
“am sorry oga nima ban san ya akayi na jaa birkin ba.

Kukan shagwaɓa diyana ta saki dawo da kallon sa Aryan yayi kanta chikin sanyin murya yace
” Me ya faru kuma?
“Habibi ba kai na bane ya bugu da wajen nan tayi maganar tana nuna jikin kujerar motar.

Hannu sa ya sanya saman goshin nata in da ta dafe da nata hannu tana turo baki, dai dai lokachin Shahram ya tada motar suka chi gaba da tafiya.

Shafa saman goshin nata ya shigayi yana faɗin
“Am sorry kin ji zai dai na yimiki zafi.

Kwantar da kanta tayi saman kirjin sa, tana ɗan wasa da rigar sa yana jin yadda take gangaro da hannun ta ta kasan marar sa, yana son ya hanata amma yana tsoron rigimar ta dan yanzu yana hanata yasan kuka zata sa masa to gwara ya kyaleta kawai.

Bai an karaba sai jin hannun ta yayi saman mararsa ta zura hannun ta chikin rigar sa, wasa ta farayi da chibiyar sa ta sanya yatsan ta awajen tana ɗan jujjuyawa.
lokachi gudu ta birkita mishi tunani wani mugun sha’awar tane ya taso masa, ji yake tamkar, ya chika aiki kawai a chikin motar nan wani zir zir yake ji a gaban sa,

Ɗora hannun ta tayi saman gaban sa ta dafa wajen tana kokarin gyara, kwanciyar ta a jikin nashi dan ta ɗan zamo kaɗan.

Ji yayi gaba ɗaya duniya juya masa take, yama rasa me zai yi wata muguwar kasalane ya da bai baye sa lokaci guda, ba zato ba tsammani kwatsam yaji tana tattaɓa wajen tana faɗin
“Habibi menen wannan kuma naji kamar an chusa wani abunne awajen ga mugun tauri abun.

Dariyar da Shahram ke gumtsewa ne ta kubche masa dan tun ɗazun yake kallon su ta chikin mirrow motar,
chikin sauri Aryan ya ɗago ido yana kallon Shahram, dake ta famar ɓoye dariyar amma abun ya chi turo da sauri Shahram ya chire idon sa daga kan mirron, harara Aryan ya watsa masa yana kokarin yi masa magana muryan diyana ta kuma katse sa

“Habibi ya ake buɗe wajen nunamin zan buɗe ne dan naga me kasa awajen, idan ya min kyau nima zaka samin”
Ta karisa maganar dai dai lokacin da sukayi parking a chikin police station

Nauyayyar ajiyar zuchiya Aryan ya sauke tare da fita motar da sauri dan bai san diyana ta sake jefo masa wani tambayar, sosai ya sake jin haushin Ahzan dan shi ya mai da ta haka amma wlh sai ya gwammaci da bai zo duniya ba.

Chikin sauri diyana ta fito tabi bayan sa, tana faɗin
“Habibi ka jirani mana”

chak ya tsaya bai san ya zai yi da ita ba yanzu idan yace ta jirashi a mota kuka zata masa, shi kuma da yaji kukan ta gwara a harbesa da bindiga baya son ko ɓachin ran ta bare kuka idan kuma yace zai shiga da ita chiki sai ta sa shi a gaba akan ya faɗa mata menene a chikin wandon sa, bashi da amsar da zai bata bai sana ya zasu kare ba gashi bata mantuwa ko kaɗan.

Domin sanin ya rikichin Aryan da diyana zai kasan che a chikin office ɗin D P O ku kasan che da Princess teema Star Lady mu haɗe daku masoyana masoyan diyana page na gobe nakune ku da diyanar ku 😹

💖The Talent Troupe Writer’s 💖

Masoyiya gidan Aunty wanna page ɗin na kine kyau ta na baki dan page ɗin na manya ne daga yau har next week pages ɗin dukka nakine 😹😹

💖Story And Written💖
⬇️
*Star lady*

Duk mai buƙatar littafin bDuk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

Back to top button