A Rubuce Take Book 2Hausa Novels

A Rubuce Take Book 2 Page 4

Sponsored Links

Part 02

Page 04

Batasan ma tsautsayin da ya sanyata ta yarda da shawarar zama a bauchin ba ta barsu shi da ita a kaduna,sai a yanzu da mamarta ta zauna ta lissafa mata abinda ka iya faruwa acan alhalin ita din tana nan zaune batasan meke gudana ba,ciki kuwa zata iya tara dukiya da abun duniyar da ita da suka kusa haura shekara bakwai bata sameta ba.

Sai yanzu ta yarda komai na babba yafi na yaro,ta kuma gasgata dukkan abinda babba ya hango yaro ko yahau bishiyar rimi bazai hangoshi ba,don haka ta hadiye dukka maganganunta taci gaba da zare pampers din data cika ta tumbatsa

“Ai basai ka kashe kudinka kayi wata siyayya ka ajjiye a nan ba,nima wannan karon dani za’a tafi” cup din hannunsa ya ajjiye ya miqe a nutse

“Wannan tsohuwar magana ce da muka jima da gamata,ki rubuta list ki turamin” ya qarshe maganar yana aje mata kudin cefananta

“Allah bazan zauna ba” ta fada kanta tsaye,shi kuma daya fita baima ko nuna yaji ba ya fice abinsa.

Yadda yayi matan ya qona mata rai sosai,ta tabbatar akwai gagarumin dauki ba dadi da zai biyo baya kafin ta samu bauqatarta ta biya,sai ta dauki wayarta kawai tayi kiran ummanta ta gaya mata yadda sukayi

“Ai gaba da gabanta,baba ma da babanshi,ki kira babarsa ki gaya mata,itace dole zata turasashi kuma yabi” fuska hafsat din ta yatsine

“Nifa matar nan ban yarda da ita ba,sonshi take fiye da kowa cikin yaranta,munafuka ce kawai,umma….na gaji da kaishi qara,don Allah don annabi ayi a kammala aikin nan,nafison idan nace eh ta zauna kawai” ajiyar zuciya ta sauke

“Hafsatu…..da mijinki da kishiyarki aikinsu dole sai an dinga binsa a hankali,idan kuma ba haka ba yace za’a yi hasara masu yawa”

“Ko hasarar mecece can ta matse musu ayita indai buqatata zata biya”

“Aah…..ke bari kiji,daga bangarenmu ne hasarar,shi yasa nace abi a sannun,inda daga gurinsu ne ina ruwan wani?,da tuni aikin gama ya gama ai” sun jima akan wayar suna tattaunawa,duka saqa ca a mugun zare da yadda zasu ida mugun nufinsu.

Har ta ajjiye wayar ta tuna da yaya baraka,dabarar kiranta takai mata qara a wannan karon ta fado mata,kai tsaye tayi kiran nata,bugu uku ta daga.

Suna gama gaisawa ta fashe mata da kuka,sannan ta rattabo mata abinda yake faruwa,bayan ta qawata zancan da qarya da gaskiya,yaaya barakan ba komai ta sani akan lamarin gidan abbas din ba,tunda itace babba a dakinsu itama ba shiga zancan takeyi ba,a yadda hafsat din ta gaya mata maganar sai taji ranta ya baci sosai,saboda rashin adalci zalla data hango,sannan hafsat din tayi sara akan gaba,don bata jima da jin tsegumin da ake na tafiyarsu widad din hajji akabar hafsat a gida ba

“Zan sameshi nayi magana dashi,basaima hajiya taji ba,ki kwantar da hankalinki,wannan ma ai rashin adalci ne,ita widad din da gwal aka yita da zaiyita yawo da ita gari gari ke ya barki tsugunne da ‘ya’ya?,ya ajjiyeta a tafi dake wannan karon,ko kuma ya hada kanku duka ya tafi daku,shi yaga zai iya” maganar tayi mata dadi,don haka sai tahau shirinta abinta,duk da shirin ya hadu da cikas,kusan kowanne kaya nata suna da naqasu,da qyar take tsintar wanda zata iya dauka a ciki.

°°°°°°°°°Yana daga zaune saman carfet tana kai kawon dire masa abincinsa,duk inda ta gifta sai ya bita da ido,yana jin wani abu yana tsarga masa dangane da ita,a yanzun data sallama masa kanta yadda yakeso,sai.yakejin kamar shi kadai yayi sa’ar mace a duniya,komai na matsalolin hafsat a yanzun baya musu kallon da yake musu ada.

Boom Short ne a jikinta da wata armless turtle neck shirt wadda ta kama jikinta,dukka kayan black ne,wannan ya qara fitar da haskenta sosai,ga wani kyau me jan hankali,ya kasa dauke idonsa daga kanta,ba wanda zai kalleta yace akwai juna biyu a jikinta,yabi tsaho da kuma qibarta ya boyeshi tsaf.

Zuwanta na qarshe ta ajjiye masa strawberry juice data hada masa,zata miqe ya kamo hannunta da kyau ya kuma jawota jikinsa a tausashe yayi mata mazauni saman cinyarsa yana cewa

“Na gaji da wannan qwalelen da aketa min tun daxu,ko yaya dai ai kyazo naji duminki ko?,kinsan kuma nayi missing dinki fa” ya fada yana saka hannunsa ya ware gashin kanta,ya cusa fuskarsa cikin wuyanta yana shaqar azababben qamshinta daya sauya daga aihinin wanda ya sani

“Ya sub….hanallah…….babyn uncle so kike ki kasheni…..wannan qamshin……” Sai ya kasa qarasawa ya sake cusa kansa sosai a jikinta,sumarta tana yiwa kansa da fuskarsa rumfa, yayin da ita kuma ta saki siririyar dariya tana riqe kansa da kyau saboda saukar hucin numfashinsa.

Basu ce komai.ba sukaji an tura qofar falon da mugun qarfi,a firgice weedad ta maida dubanta ga qofar,shi kuma ya zaro kansa daga inda ya boye fuskarsa yana kallon bakin qofar da idanunsa da suka sauya launi.

Hafsat ce,baya tayi.kamar zata fadi,tunda take bata taba mummunan gani irin wannan ba, widad ce saman cinyar abbas din?,ko ita ba zata iya tuna when last da tahau cinyarsa kamar haka ba,wani abu me zafi ya taso ya riqe mata qirji,ta fada zuqar numfashi da qyar.

Motsawa widad din tayi da nufin zamewa daga kan cinyarsa,sai ya janyota ya gyara mata zama sosai akam cinyar tasa yana zagaye qugunta da hannayensa,yayin da idanuwansa ke kan fuskar hafsat yana kallonta cikin bacin rai,ita kuma widad din take kallo,tana jira taga ta sauka,amma sai taga ko motsi batayi ba,saima shirin jingina da take da jikinsa,saboda yadda ya hanata sauka daga cinyar tasa,kunyar yadda ta gansun kuma tana tabata,duk da haushi da taji na yadda ta shigo musu babu ko sallama

“Wajenka nazo” ta fada murya a tsaye,tana fatan widad ta sanya baki a maganar ko zata samu hanyar da zata dake ta fa huce takaicinta

“Fita waje ki jirani”

“Yaaya baraka ce tace na kawo maka waya tanata kiranka baka dauka ba” ta fada a kausashe tana jin yadda hawaye keson kunno kai cikin idanunta tana hanasu zuba,wannan cin fuska da rainin da yarinyar tayi mata har ina,tana zaune sosai saman cinyar mijinta kuma tana kallon qwayar idanunta?.

“Ki fita nace ki jirani” ido ta zuba masa kamar zuciyarta zata fado,ita yake kora a gaban qaramar yarinya?,saita jinjina kai ta fice fuuu kamar zata tashi sama.

Da sauri ya sanya hannu ya sake tarota sosai cikin jikinsa,ya maida gashinta gefen kafada yana sake zura kansa gefen wuyanta

“Un….. uncle” ta kirashi murya a rarrabe, fuskarsa kawai ya dago dab da tata yana kallon fararen qwayar idanunta

“Kace mummyn mimi ta jiraka a waje fa”

“Ba zata jirani ba,tafiya zatayi”

“Amm…..”

“Shshshs……” Ya fada yana dora yatsarsa akan labbansa yana duban qwayar idanunta

“Kada kicemin komai,sannan daga yau,duk sanda ta sake shigo miki waje irin haka muna tare kikace zaki matsa ko zaki tashi,zan hukuntaki ne,ai bata nema izininki ba kafin ta shigo miki waje………ko ban fada miki ba nasan dole ki sani,a nan ne kadai wajen da nake samun nutsuwa da kwanciyar hankali,kawai sai na bari lissafina ya dagulemin?,nayi wasa da damata kamar yadda tayi wasa da tata?,come-on…..forget her, let’s continue to enjoy” ya fada yana sake shige mata.

Sai daya gama rage zafinsa sannan yace ta dauko masa wayar,ta dauko ta miqa masa cikin girmamawa,ya saki murmushi yana cewa

“Thanks” sannan ya buda wayar yana duba me kiran.

Yaya baraka dince,sai kawu hassan,kowanne miscall bibbiyu yayi masa,baibi takan yaya baraka ba,tunda har sunanta ya fita a bakin hafsat yasan akwai wata a qasa,bare yana sane da maganarsu ta daxu,sai ya fara da kiran kawu hassan.

Cikin girmama juna suka gaisa,sannan ya shigar masa da zancan baraka ta sameshi da batun iyalinsa kan komawa kaduna,ya yiwa kawu hassan din bayanin komai,yayi shuru yana nazari

“Duk dadai mun gama magana da hajiyarku,kusan abu daya muke gani,kayi.haquri ta biku kada duniya ta zageka,kuma ita kanta kada ta sake daukar cewa kana hakanne don rashin adalci,don rashin kyautawa bata kyautata ba,amma ko yanzun ma baka da tabbas din zata zauna idan taje din,tunda mai hali baya fasa halinsa,don haka ka zuba mata ido,taje din”.

Koda suka gama waya da kawun hajiya ya kira,itama kusan abinda tace dashi kenan,dole ya sauko daga dokin naqin da yahau,saidai baice mata zataje ko bazataje din ba,ya barta tana ta raba ido da taraddadin zai yarda ko zaiyi halin nasa na kafiya,saida asubahin ranar da zasu tafi tunda girkinta ne yace ta shirya da wuri zasu wuce.

Jikinta na rawa take kintsa abinda zata iya,qarfe goma na safe sale ya gama fidda kayansu duka an zuba a booth din motarsa,dole ya canza motar komawa saboda wadda suka saba zuwa da ita kamar zasu matsu da yawaga yara biyu ga hafsat din ga widad gashi.

Ta riga kowa fitowa ita da yaran,ta buda gidan gaba ta shige ta watsa yaran a baya

“Kya zauna a cikinsu,dama nan ne yafi dacewa dake” ta fada a ranta,don dama ko sama da qasa zasu hadu batajin zata yarda ta barwa widad din gidan gaban.

Batasan ma me yake faruwa ba,ta fito abinta a shirye tsaf cikin wata atamfa dinkin A shape budadde sosai,duk da yadda hafsat din take ganin ta qurewa ado sai data raina kanta,sai dataji ta muzanta,ta zuba mata ido.tana fatan Allah ya kawo wani mummunan sanadin da zai dakushe wannan kyan da kullum kwanan duniya yake mata barazana cikin idanunta.

Tun bata qaraso ba taja hankalin abbas dake tsaye jikin motar yana amsa waya ba tare da yakai ga shiga ba,ya bita da kallo tun daga can harta kawo bakin motar,yaran duka suka fito suna mata oyoyo tasa hannu ta rungumesu cikin jikinta,mimi tace

“Anty qamshi,qamshi kike,ki sakamin turaren nima”

“Yanzu kuwa.babbar qawa” ta fada tana zuge hand bag din dake maqale a hannunta,ta fidda qaramar kwalbae turare mai kyan gaske ta fara fesawa yarinyar

“Ranki ya dade…..mu baza’a san mana qamshin ba?” Abbas data gama kashe masa jiki da adonta ya fada yana turo hularsa gaban goshinsa.

Zata iya cewa hatta kalar murmushi hajiya fanna sun koya mata,daya daga ciki ta aro ta aike masa dashi tana juya fararen idanunta,saqonta kuwa ya isa,don kasa takawa yayi ya koma a dole ya manne bayansa da motar yana jin qafafunsa sun saki

“Idan ba’a fesa maka ba wa za’a fesawa” sai ta tako a hankali ta matsa gabansa ta fara fesa masa turaren daga wuyansa zuwa qirjinsa,sanyinsa da qamshinsa ya ratsa fatarsa,ya saki ajiyar zuciya,sai ya kama hannunta ya riqe cikin nasa yana cewa

“Kada fa ki jawo hannun agogo ya koma baya,zan iya kasa tuqin nan f……..” Bai qarasa ba uban horn din motar ya karade gidan,a tare suka juya zuwa ga motar,yayin dasu mimi suka tsorata saboda yadda ta danne horn din har baka iya jin abinda wani ke fada.

Hafsat ce da komai ya faru a gaban idanunta,abinda suke fada ne kawai kunnuwanta basa iya jiyowa,sabida Glass din side din a rufe yake,ta cika tayi fam kamar zata fashe,ita zasu rainawa hankali su shanya a cikin mota?,zame hannunsa yayi ya tako a nutse ya buda murfin motar yana kallonta

“Idan tafiya tafiya,idan zama zama,ya zaku tsaya gaban yara kuna abu iskanci iskanci?” Ta fada tana huci,tana jin kamar ta fita ta kamo widad ta shaqeta.

Kamar ransa zai baci sai kuma murmushi ya kubce masa,ashefa ita duk irin wadan nan abubuwan a rayuwar ma’aurata iskanci ne a wajenta,kuma shi har ga Allah ya manta da ita

“Yi haquri mommy” yana fadin haka ya maida.murfin ya rufe,bai dai fasa ba,sai daya koma ta fesa.masa turaren sannan suka dawo cikin motar,xuwa sannan tayi nisa wajen juya kalmar.mommy daya jefeta da ita,aiba haka yake gaya mata ba,yanzun kuma daya fada me yake nufi kenan?,babu me amsa mata,haka suka cika motar da karadinsu widad na biye musu tana kume jefo abbas a ciki shima yana shiga sabgartasu,har ta dinga jin kamar sunyi watsi da ita ne kawai,kamar babu ita ne a cikin motar gaba daya, abun da ya isheta saita dakawa mimi tsawa

“Banason shegen surutu,ki kama min bakinki a wajen” yarinyar tayi tsuru tsuru,sai ta bawa widad din tausayi,ta lura tana yine saboda ita,taja yarinyar jikinta ta fara mata hira qasa qasa,sai gashi ta ware,abbas da yaji shuru yace

“Wai me aka gayawa mamana ne tayi shuru haka?”

“Daddy labari ake bani me dadi” mudubin gefansa ya saita yadda zai hangesu da kyau,suka hada ido ya kashe mata ido daya

“Retired za’a yimin?,ba haka mukeyi dake bafa” baki tadan murguda masa,abinda ya fusgi hankalinsa kenan,don bai taba gani tayi ba sai yau,har sai da murmushi ya subuce masa ba tare daya shirya ba,yayi mata sign na tuba yakeyi saita dauke kai tadan qara volume kadan na muryarta,motar ta dauki shuru suna biye da ita.

Tarihi take basu na daya daga cikin sahabbai,kusan ya zauna sosai a kanta saboda alhaji na yawan yi.mata shi,sosai tarihin yake shigar abbas din yana mamakin yadda ta riqe komai exactly,hafsat da takejin muryar widad din kamar tana watsa mata ruwan zafi taja tsaki karo na kusan goma

“Nifa gsky an shiga hakkina”

“Da akayi me?” Ya jefa mata tambayar ta sigar ko in kula

“Lallai ne kowa sai yaji abinda take fada?”

“Ba lallai” ya fada yana zura hannunsa aljihun motar,ya ciro wata mini laptop da earpiece ya xube mata ba tare da yace da ita komai ba,sai tabi kayan da kallo kafin ta maida kansa,saidai tuni yaci gaba da abinda yakeyi kamar ma baiyi komai ba.

[04/05, 1:58 pm] +234 916 551 4595: *H U G U M A*
*Arewabooks: Huguma*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)

Back to top button