A Rubuce Take Book 2Hausa Novels

A Rubuce Take Book 2 Page 5

Sponsored Links

Part 02

Page 05

Kafin sukai kaduna zuciyarta kamar xata fashe,bata samu sauqi ba saida bacci ya daukesu mimi,widad kuma ta sanya earpiece abinta ta kunna data tahau watsapp.

Saidai duk da hakan hankalinsa yana kanta,bini bini ya juya ya gani,ta rasa da wacce siga zata masa magana juyawan da yakeyi tana jinta kamar a qahon zuciyarta yake soka mata abu mai tsini,amma yadda taga ya tsare gida tasan bata isa ma tace komai ba,haka ta dinga cinyewa kamar ta zuqo kaduna ta rage nisan tafiyar suyi su isa,saidai wannan abun ba zata barshi ba,dole taci uban yarinyar da kyau.

Qarfe biyu da mintuna suna cikin gidan,kowa na gidan na maraba da dawowar abbas din,kasancewarsa mutum me kirki da kyauta,ma’aikatan gidan suka kwashe kayansu zuwa falon gidan.

Shi ya buda musu parlor din ya koma don gyara parking,hafsat ce a gaba,tana tafe tan qarewa parlor din kallo,komai na parlor din ba wanda ta sani bane,an canza abubuwa da yawa da wani irin tsari me kyau,komai qal kamar basuyi tafiya sun bar gidan ba,wani abu yazo ya tsaye mata a wuya,tana tuna lokacin data sanya qafa tabar gidan,tana jin duk duniya babu yadda abbas zaiyi da ita.

Awancan lokacin tana jin babu matakin da zai iya dauka,babu wata mace da zata iya shiga rayuwarsa,ashe babbar matsala ce zata biyo baya,yanzun gata ita kusan sa’ar diyarta ta fari inda auren wuri tayi zasu goga kishi.

Gaba widad tayi abinta,ta buda dakinta ta shige,tunda komai nata yana ciki,lokuttan baya kafin kusanci ya samu tsakaninta da abbas din ta koma dakinsa a nan take kwana,da kallo hafsat din ta bita tana jin kamar ta jawota,ganin yadda ta barta tsaye a falon,wato ta samu dakin zama kenan,taja wani mugun tsaki tana kallon dakin nasa dake kulle,sai ya shigo kenan zai bude mata dakin,ta koma ta zauna saman kujerar tana sauke shukra dake bacci,yaran nata guje guje da murnar zuwa gurin da suka jima basu zo ba.

Duka duka part din bedroom biyu ne,a dole abbas din ya budewa hafsat nasa bedroom din suka saka kayansu.

Tana daga gefan gado tana bawa yusra yusra mama tana qarewa dakin kallo shima,komai neat,qamshin shegiyar yarinyar ya kama dakin da kyau,da qyar take iya hadiye yawu saboda wani abu daya tokare mata wuya,ta cirr yusra data koma bacci ta kwantar da ita gefe,sai hannunta ya fada saman wani.abu mai taushi,ta janye hannun tana dubawa da sauri.

Baby pink rigar baccin widad ce wadda ta barta saman gadon garin sauri ranar da zasu bar kadunan,ta daga rigar tana qare mata kallo,bata da maraba da tsirara,saboda duk inda muhallin tsiraici yake neat ne a wajen da wani silk yard duka jikin rigar,nannade rigar tayi tayi wurgi da ita cikin tsananin bacin rai,ita za’a yiwa iskanci?,sai ta miqe ta fara bincike dakin,tun daga drawer dinsa zuwa toilet.

Da qarfi ta buda murfin wardrobe dinsa,idanuwanta ba zasu juri ganin kayansu a cakude waje daya ba,brassiere dinta da qananun kayanshi,kai tsaye ta miqe ta fita a dakin da nufin zuwa ta gaya mata tazo ta kwashe kayan nata.

A falo sukayi kacibus dashi yana shigowa riqe da hannun nawwara,ya bita da kallo

“Ina zuwa?” Kallonsa tayi qirjinta kamar zai fado saboda radadin da zuciyarta keyi mata

“Zuwa zanyi na gaya mata tazo ta kwashe kayanta a dakin” wani nutsatsen kallo ya bita dashi sannan ya gyara tsaiwarsa

“Ki barni da kaina zan gaya mata,sannan ma dole ki samu kayanta cikin dakin tunda batasan da dawowarmu tare ba” galala ta bishi da kallo kanta yana daurewa,ita abbas ke cewa ba’asan da zuwanta ba?,to banda ma iskanci da fidda sabon salo,tana cewa ita din sanda tana nan dankwalinta baya bari a dakin,kome ta bari sai ya sanya ta tattarasu ta fiddasu a dakin kafin ya rufe ya wuce aiki,shine yanzu zata samu kayan yarinyar cike a dakinsa,kayan ma na rashin arziqi da rashin kunya?.

Bai wani nuna ya lura da yanayin data shiga ba ya miqa mata nawwara

“Ki dafa musu wani abun suci kafin ku gama kintsa gidan,yunwa sukeji” bai tsaya jiran amsarta ba ya wuce ciki yana janye da luggage dinsa.

(Widad)

Tun shigowarsu gidan tare duka taji gidan ya canza mata,batasan me takeji game da biyosu da mummyn mimi tayi ba,amma dai tasan har ranta hakan bai mata wani dadi ba,saidai idan ta tuna matarsa ce itama kamarta sai tayi qoqarin dannar zuciyarta,duk kuwa da cewa tanajin mugun qunci duk sanda taga wani kusanci a tsakaninsu,haka ta dinga qoqarin shanyewa,ta gyara dakinta zuwa toilet dinta tsaf,tanata son fitowa ta gyara sauran sassan gidan amma tana ta jin motsin yaran,batasan ko suna amfani da falon ba,sai dataji shuru sannan ta fito.

Tuni falon ya fara watsewa da tarkace,bata saba ganinsa haka ba,duk sai taji wani iri,ta tattare musu shirginsu guri guda ta kintsa falon,tana gamawa hafsat din na fitowa daga kitchen dauke da plate din wata cakurkudaddiyar jallop din taliya yaran na biye da ita.

Tsaki taja tana shigowa falon tare da kallon yadda ta gyarashi,itafa batason irin wannan sanaben tsiyan,daga dan tashinsu an wani hau shara?,saita watso dukka kayan qasa tayi abun zama dasu,ta ajjiye musu plate din a qasa suka fara cin taliyar,mimi na cewa

“Anty kizo muci” harara hafsat ta maka mata

“Tunda ita ta dafa man ba uwar iyayin tsiya” qaramin murmushi widad ta saki,itakam wannan taliyar ko matse bakinta akayi batajin zata iya hadiyarta,ko kadan bata bata sha’awa ba

“Na gode mimin daddy” saita juya ta wuce dakinta,zuwa yanzun duk wani girma da mutuncin hafsat babu abinda yayi saura a idanun widad din,ta zare kayan jikinta ta shiga wanka.

Yana shigowa daga sallar azahar ya zauna falon yana tambayarta abinda ta dafa,sanda ta zubo ta kawo gabansa sai yaji duk yunwar da yakeji.tayi qaura babu ita a cikinsa,ya kalli abincin da kyau ya girgiza kai ya kawar gefe,bazai iya saka wannan

“Ina antynku?” Ya tambayi su mimi

“Tana daki” shi kansa yau din gaba daya sai yakejin wani iri,ba da wannan yanayin suka saba dawowa kaduna ba,kewarta duka ta isheshi,a kadunan yake samun kanta fiye dako ina,don tafi sakewa sosai a nan din,sai ya miqe tsam ya nufi dakin nata,yayin da hafsat dake zaune a wajen tunda sukaci abinci bata motsa ba bare tayi haramar gyara kayan da sukazo dashi da kuma dakin ta bishi da kallo.

Duk yadda taso ta daure sai ta kasa,ta buda baki cikin qunci

“Ina zaka?,girkina ne fa?” A nutsensa ya waiwayo yana kallonta

“Wani abun nace miki zanje nayi?,idan girkinki ne ki maida hankali wajen tunanin abinda zaki dafa mana da dare” tasan magana ya gaya mata a fakaice,sai tayi shuru tana sake rakashi da idanu,kamar ta tashi ta tari gabansa,har ya murda handle din ya waiwayo yace mata ta sama masa black tea ta hada masa da wani abun da zaici.

Maida qofar yayi ya rufe a hankali ya jingina da jikin qofar yana sauke ajiyar zuciya,gaba daya dakin ya gauraye da qamshin shower gel air freshener spray dinta,ya zuqi iska ya fesar yana kallonta,tana daure da towel tana mulke lallausar fatarta da kyawawan mayukan gyaran jiki da suke qarawa fatarta kyau da glowing.

“Ki daina kallona da wadan nan idanun naki don Allah,kada ki sa na kasa qarasowa mana madam” ya fada yana kallon yadda ta tsareshi da ido ta cikin madubi,ba shiri murmushi ya kubce mata,duk yadda kuwa takejin ranta a quntace,amma shi dinma a yanzun kallo daya tayi masa ta karanci kamar akwai ‘yar qaramar damuwa a fuskarta.

Dab da bayanta ya tsaya,ya dauki cumb yana taje mata kanta a tausashe,yadan ja kadan saboda yana son tsokanarta,fuskarta yakeson gani sosai,sai ta yamutsa fuska

“Asshhh” ta furta tana shagwabe masa,ya saki siririn murmushi

“Idan ba haka nayi miki ba naga alaman rowar fuskar nan akemin yau” siraran labbanta ta tura gaba

“Idan baka gani ba ai zakaga ta mummyn mimi” farko bai gane me take nufi ba sai daga baya, siririyar dariya ta qwace masa,yaja kujerar madubi ya zauna,ya jawota cikin zafin nama zuwa saman cinyarsa ya zaunar da ita,dukkansu wani shock sukaji cikin jikinsu,ya dora hannunsa saman cikinta

“Idan naga ta mummyn mimi sai akace naga taki?,sunanku ma aiba daya bane,matsayin taki daban matsayin tata daban” matsayin da yace din sai ya kumbura zuciyarta,ta fara qoqarin zamewa

“Tunda itama mai matsayi ce ai duk daya ve da tawan” dariyar da yake riqewa ta qwace masa

“La’ila….lallai yarinyar nan,zoki gayamin……kin iya kishi dama wai?,dama tun rannan nake ganin alamu,ashe nayi hasashe dai dai……yaushe kika fara son uncle din naki haka?” Duka hannuwanta ta saka ta zagayesu a qeyarsa tana kallon idanunsa sosai

“Ranar da kayimin ciki mana” mutuwar zaune yayi,ya nutsa idanunsa cikin nata yana mata wani irin narkakken kallo,inama zata zauna a haka?,ta yakice sauran kunyar da tayi ragowa tattare da ita?,that’s all he needs,yana buqatar kulawa da soyayya kamar ba za’a mutu ba,sai kawai ya sanya dukka hannuwansa ya mata masauki cikin jikinsa ya matseta gam yana sauke numfashi

“Bansan lokacin dana fara sonki ba,kishin da nake naki kuma inajin zai iya kasheni……inaso kici gaba da kishina,kiyita kishina kiyita kishina,na miki alqawari wani abu na musamman”

Murmushin jin dadin ya kubce mata,wannan satar amsar hajiya fanna ce ta bata ita,ta jima tanason gwadawa amma tanajin nauyi da kunyarsa,sai gashi…..yayi aiki,tana iya jin bugun zuciyarsa ya qaru sosai.

Bugun qofar da akeyi shi ya tilastata zare jikinta daga nashi tana kallonsa,wani abu ne da basu saba dashi ba,muddin suna kaduna a irin wannan lokacin ba wani abu dake disturbing dinsu
[05/05, 10:48 pm] +234 810 324 4136: *H U G U M A*
*Arewabooks:Huguma*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)

Back to top button