Hausa NovelsMatar Makaho Hausa Novel

Matar Makaho 13

Sponsored Links

Page1️⃣3️⃣
**** zuba Masa ido nayi Ina kallonsa sosai na hango damuwa a fuskar sa ga idanunsa manyan nan sun kumbura sunyi ja’ sosai alamun baiyi bacci ba Daren jiya hannu na dake cikin nasa na motsa,

Cikin firgita yake furta Alhamdulillah Sumayya kin tashi kin bude idonki Kina kallona kin gane ni???

Abin yaso bani dariya bandon halin ciwo dake damuna Wanda Koh magana bana sonyi Dana dara ganin yanda ya zarge lokaci daya Kamar Wanda akace Masa za’a min dashin zuciya ,

Sumayya kina jina Koh dai idonki Bai budu bane Amma Naga hannunki na motse Kamar kin tashi bara dai na Kira nurse, yana yunkurawa zai Mike hannun nasa na rike cikin nawa hakan yasa shi komawa ya zauna Yana Mai cigaba Damon sannu tunda dai yanzun Kam ya fahimci na farka maganar nedai bazanyi ba, daidai lokacin Khadija ta shigo falon tana zazzare ido tana neman gadon da muke,har dai ta gan mu,

Isowa tayi bakinta a washe gani na ido a bude sai dai na Dan rame sannu Aunty Allah ya Kara sauki,

**nidai sai ido

Khadija jike Kira doctor kice ta farka, toh yaya tace tana fita

 

Karyawa Al’ameen yayi kafun ya ce zaije gida Khadija ta zauna Dani

Bayan fitar sa keke napep ya hau zuwa gida ,ya sauke sa a kofar gida, da sallama ya shiga gidan Jin gidan yayi yau kamar ya Bata hanya Sam Kamar ba gidan su ba, gabaki daya shuru ba hayani da suratai Kamar da don gidan su tun daga bakin kofa zakana Jin hayaniya na tashi Amma yau sit Keke ji lalube yake da sandar sa ya shiga kofar su,

 

Wanka yayi ya shanja Kaya ya kwanta don wani irin bacci yakeji Wanda Bai samuyi ba Daren jiya har kansa na ciwo, sai azahar ya farka massalaci yaje yayi sallah sai agun yake Jin abinda ya faru a gidan su sosai hankalinsa ya Tashi don shi mutum ne Mai son nasa duk wulakancin da suke masa in Abu ya samesu sosai yake damuwa daga massalaci police clinic ya wuce kamar yanda akace gun aka kaita,

Yana Isa ya hadu da Rabin Yan gidansu a farfajiyar asibiti gaidasu yayi yaukam ya samu amsa ya tambaye jikin inno ance masa Basu Bari a ganta har yanzun,,,

Zama yayi shima a asibitin duk hankalin sa nakan Sumayya sai la’asar ya koma FMC,

Haka Al’ameen da Khadija suka ringa jinyata a asibiti har muka Kai sati sosai Khadija ta tallafamin itace girki itace kaikawo tsakani gida da asibiti yau satin mu daya aka sallame mu, kudin hannu na ya kare Daman dubu d’arine abokin abie ya damka mini lokacin da naje ma abie sallama a falon sa ranan da za’a kawo ni gidan su Al’ameen,

na kashe kudi a gidan Al’ameen kafun naje asibiti na biya kudin aiki nasai madara da bonvita gongomi manya su sugar shi nayi ta Sha a asibiti da Abubuwan da aka bukata a asibiti shi Karan kansa naira d’ari shida ya rage agunsa,

**Keke napep muka hau dukan mu uku sai sintali har kofar gida ya sauke mu Khadija ta taimaka mini muka shiga cikin gida shi Kuma ya biya Mai keke ya dauko Mana kayan mu ya shigo,

Kofar mu Muka wuce nikam sai mamaki nake ganin gidan shuru babu hayaniya kamar an musu kulle Amma ban tambayi Khadija ba, kofata muka nufa Yana binmu a baya da kaya muna shiga nabi kofar da kallo kamar ina nan gaskiya Khadija yar arzikice har raina yanzun nake kaunar yarinyar sosai daki muka shiga na kwanta a Kan gado,

shima shigowa yayi da kaya ya aje “khadija kunna mini fanka”nace Mata,

Wallahih Aunty babu nepa an yanke muku wuta,

“Anyanke wuta kuma Daman wake biya”

Hada kudi ake duk wata a biya wannan watan inno ba lfy ba Wanda ya saurare Yan NEPA,

Allah ya bata lfy nace ina mikewa waje na fitoh Khadija ta shimfida mini darduma da filo na kwanta abina,

“Khadija kije gida kinji kije ki huta yau basai kin Mana abincin dare ba yayan ki zai sayo Mana yaukam ki huta abinki kinji”

Badon ranta yaso ba ta amsa mini da toh ta juya zata fita,

“Khadija dauki taliya uku a caton in kinje gida ki dafa muku kinje akwai Maggi da Mai duk ki eba,”

Toh Aunty ta shiga kitchen in ta dauka ta tafi,

shikam fita yayi ya rasa Meka Masa Dadi yanzun Sam baida jarinda zai Kama sana’a sai d’ari shidan nan koma dashi ya biya kudin Keke 200 saura d’ari 400 gashi yanzun abinci zai Saya Kamar yanda nace Masa Khadija taje ta huta zama yayi a kofar gidan ya zuba tagumi abin duniya ya damisa,

****Nikam bayan fitarsa tunani na hauyi tunda na kwanta rashin lfy babu yan gidansu Koh namu da yazo dubani hatta Yan unguwan makwanta basuje ba sai Goggo Amina kawai itama sau daya taje, lallai rayuwa abin tsorone,

Sai da yaji ana Kiran sallan mangariba kafun ya mike ya tafi masallaci daga nan ya wuce bakin first bank dake D’aya tsallaken titin kofar gidan su ta Gefe ya sai abinci plate daya naira dari uku ba nama haka ya sai plate daya aka Masa take away ya dauka yayi hanyar gida,

Nima sallah nayi naci gaba da k’wanciya a inda nake, naji shigowar sa da sallama amsa Masa nayi, ya karaso Kan darduman ya zauna a gefe na Dayake yanzun ya daina shakkar rabar inda nake tun zaman mu a asibiti,

Ga abinci nan na sai Miki shinkafane fried rice ,

Toh nace na karba budewa nayi na fara ci Ina tambayar sa nasa” Ina take away in ka Kai Kuma” agun naci ya Bata Amsa,

abinci rabi naci,nace yaban. ruwa dauka yayi ya kawo mini nasa” sai da akayi Kiran isha’i yayi Alwala ya wuce masallaci yayi sallah sai karfe 9:00 ya dawo lokacin nikam na gigice ga zafi ka sauro sai fifita nake da caton in taliya,
Dolen sa ya fita yaje yasai maganin sauro na ishirin,kudin hannunsa saura 80 kacal ya rage,

Yauma a darduma daya Muka kwanta shiya rigani tashi da asuba ,,,

Vayan fitarsa nayi Sallah sai 7:00 ya dawo wanke wanke yayi ya jawo ruwa yakai kafa biyar yasa a randa nikam bacci nake a daki

Khadija ma tazo ita tayi shara ta shiga kitchen zata daura mana karyawa sai dai babu kayan miya,fita tayi tazo ta same sa,

Yaya ba kayan miya aban kudi na saya,

Me Zaki dafa?

Shinkafa ne

Sai dai Khadija ki Mana shinkafa da wake da Mai da yaji don bani da kudi sai 80 innan ,gasu nan ma kije ki sai Mai da borkono da Maggi,

Yaya akwai Maggi kam da Mai da manja galam ma babba a kitchen in sai dai na sai borkono na talati kawai yaya,

Toh yace ya Mika mata Yana cewa tayi abinci gabaki daya harda na Rana direct, hamsin ya Bata,

ta karba ta koma kitchen in ta daura shinkafa a gas da wake,taje ta sayo barkono ,

****Sai 8:30 na tashi na safe fita waje nayi Naga Khadija na aiki a kitchen shi Kuma nata Jan ruwa,gai Dani tayi na amsa shima gaishini yayi amsawa nayi na ibi ruwa a buta na Kama brush,

Sai karfe 9:00 ta kammala abinci ta zuzuba Mana karba nayi na fara ci Sam ba cimana bane shinkafa da wake Amma ya zanyi ni Karan kaina nasan Basu dashi Dole na koyawa kaina cimar su ,

Yana Gama cin abinci ya Mana sallama ya fita wajen Yan sarin kayan fruit ya wace inda yake saya yazo ya kasa,da sallama a bakinsa ya karasa gun dukansu suka amsa masa suna tambayar sa lfy, baya zuwa kwana biyu Koh ya chanja sana’a ne,

Lafiya Alhamdulillah Ina zama agun mara lfy ne a asibiti shiyasa bana fita, Yana fada ya karasa wajen customer in sa, Dan Allah malam Hafizu nazone ka taimaka ka bani bashin mangoro na dubu daya inje in kasa in Allah yasa nayi kasuwa sai na kawo maka kudinka ka bani wani, wallahih bani da Koh sisi sai naira talatin,

Chap gaskiya bazan iyya wannan kasuwan cin dadawan kauye ba ,

Habba malam Hafiz mun saba da Kai shikara nawa Ina sayan kaya a gunka don yanzun jarina ya karye bazaka iyya tallafa mini in mike ba,?

Bazan iyya ba,yace cikin masifa ,kala Al’ameen baice masa ba yaje kusa da table in dayan makwancin malam hafizu Amma yaki yarda haka ya zagaya Tashar kayan marmari Anki Vasa duk da sun Saba dashi Amma haka suka ki basa jiki a sanyaye ya kamo hanyar gida,..

 

Muna zaune da Khadija a kofa tana mini kitso Ina kwance a Kan darduma a baranda Hira muke akan bikin kawarta Yar wani Mai kudin unguwan saura wata Daya da sati biyu,

Aunty kinsan Allah Asma’u tana sona da kawance Amma mamarta Bata so shiyasa yanzun bana zuwa gidan su itama Bata zuwa namu sai dai mu hadu a hanya mu gaisa da auren ta ya kusa ma kaninta ta aika ya fadamin date na auren ,

Kuma ,, kawayen ta suna wulakantani tun muna makaranta basaso na da Asma’u,sai nake ji Kamar kar naje bikin,

“Don me bazakije bikin ba”?

Saboda banaso.a wulakantani Aunty,

“Ai.in bakije ba baxataji Dadi ba Kuma basai kin kulasu ba zasu wulakantaki ,”

Shikinan Aunty Allah ya kaimu,..

“Ameen Kenan in anyi bikin da wata Daya azumi”?

Wallahih Aunty yanzun bakiga sai aure ake ba akai akai azumi yazo,

“Toh Koh kema za’ayi nakine kafun azumi tunda ba karatu kike ba”? na fada Ina dariya,

Shap aunty aini Koh saurayi bani dashi ban ma tabayi ba,

“Kutt don me Amma dai Inaga ke kike kinsu Koh Amma duk kyau inkin nan kice baki da saurayi”

Aunty Kenan ai samarin ma Yan Mata masu kwalisa suke so ba Irina ba,

“Karki Kara cewa haka ki gode wa Allah wata ma batasamu gata kamarki ba kinji insha Allah wata Rana sai lbr “,

Insha Allah Aunty

tsayuwar mota mukaji a kofar gidan ba’a jima ba sai Muka fara Jin Ihu da salati na dandazon Yan gidan sai koke koke ake dagaji bana lfy ba ne,,,,….

Khadija ce ta Mike da gudu ta fita a kofar tayi cikin gida Koh takalmi babu ni karan kaina na tsorata,

Koh minutes uku batayi ba Sai gata ta dawo da kuka tana haki ta Fadi a kasa kusa dani cikin gunjin kuka ta bude baki tace Aunty I……………..

 

🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 *Albishirin ku Mata ku marmaso kuji sirrin,Koh kinsan mace sai da kamshi da gyara* 😉

🍀🍀🍀🍀 *Turare suna d’ayace Amma sun banbanta kowanne da ingancinsa kamshinsa da aikin sa*

🍀🍀🍀🍀 *Ina muku Albishir da UMSAD INCENSE Dan samun turaruka masu kamshi da* *gyara*

🍀🍀🍀 *Tabbas Turare sirrine ga Koh wace mace*

🍀🍀🍀 *Gamai bukatar turarukan UMSAD INCENSE*

🍀 *Na tsunguno(habil)*
🍀 *Na jiki (kwalaccam)* ( *khumra, black & white* )
🍀 *Turaren turara jiki after birth* ,
🍀 *Na d’aki(halud Al’oud)*

*UMSAD INCENSE suna kofar waika wajen Ado bayaro layout Kano State* 💃🏼💃🏼

🍀🍀🍀 *Suna bada d’aya Koh sare akan farashi Mai Rahusa*

🍀🍀🍀 *Suna bada order kayansu Gamai bukata aduk jahar da yake a fadin Nigeria*

Contact them vie
🪀08028827241 or 09033791049
IG @umsadincense
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯
~ Na ~

🍃 *Rukayya* *Ibrahim* 🍃

✨Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za’a ga mistake Koh typing error Amin afuwa👌
free book 🤧

Back to top button