Auren Shehu Book 1Hausa NovelsHausa Novels

Auren Shehu Book 1 Page 11

Sponsored Links

11

 

Ganin Zainab a sume da kururuwan kukan su Ammy sam be sa Malam ya motsa ba. Alhaji Sidi ne ma ya kawo doki ya na mai umartar Usman yayi maza ya dauko ruwa daga cikin fridge din Parlour. Ammy da Falmat ne ke jijjiga kafadun ta, Halitta kuwa kasa motsawa ta yi, hukuncin da Malam ya yanke ba Zainab yayiwa ba, gani ta ke tamkar ita Malam yayiwa gwale gwale, ta na ji ta na gani wanda ta ke so, ta ke kauna ya zamanto miji ga yayar ta uwa daya uba daya.

Yayyafin ruwan sanyin da ya sauka fuskar ta ya sanya ta farfadowa, a hankali ta bude idanun ta.

“Alhamdulillah, Malam ta farfado ka yiwa Allah ka warware auren nan, Alhaji Sidi ka sa ba ki!”

Ammy ke magana cikin magajiya ta na mai rungumo Zainab wacce ta ke ji kan ta na sarawa tsabagen ciwon da ya ke ma ta. Maganar da Ammy ta ke yi ne ya sa ta farga ta tuna da halin da ta ke ciki, kuka ta saki mai tsuma zuciya ta na fadin

“Dan Allah Dady na tuba, ba zan kara ba, Dan Allah Dady kar ka daura min wannan nauyin a kai na Dady!”

Idan dutse na motsi toh Malam ya motsa, ko nunawa ya san da shi ta ke bare ya amsa mata be yi ba. Usman wanda kamar yanda Zainab ke kukan bakin ciki shi ma har ga Allah wannan auren da aka daura ma sa be so ba, shi ya fara zamewa ya fice daga parlour, Jauro da Isa su ka bi bayan shi. Ammy kuwa Alhaji Sidi ne ya ce su dan ba shi wuri su zanta da Malam in Sha Allah za a sami mafita. Zainab kwance jikin Ammy kamar mai jinya haka su ka fice ya rage daga Malam sai Alhaji Sidi.

Alhaji na duban Malam ya ce

“Malam kai fa mai sani ne, ka sani cewa yanke hukunci cikin fushi da gaggawa na tare da dimbin danasani, shin me wannan yarinyar ta aikata da har za ka yanke wannan hukuncin mai nauyi akan ta Malam?”

Ga mamakin Alhaji Sidi sai ga Malam ya na zubda hawaye.

“Ya hayyu ya qayyum! Munin abun ya kai haka?”

Cewar Alhaji Sidi cikin alajabi. Kai Malam ya girgiza, kana ya ce

“Alhaji Sidi ka na daya daga cikin amintattuna na, abokin arziki da amana, Alhaji Sidi ba zan boye ma ka komai ba. Na kasance mai rauni aka ‘ya’ya, musammam ma Zainab. Allah ya jarabce ni da diya, sai dai na ce Alhamdulillah. Amma Zainab ba ta min adalci ba, ina nan idanuna kan ‘ya’yan wasu, Wai ni Malami mai wa’azi ashe tawa diyar wacce na fi yarda da ita ta nan ta na barna a bayan ido na, Innalillahi wainnailaihi rajiun…..!”

Nan Malam ya kwashe komai ya fadawa Alhaji Sidi, ya kare maganar da

“Yaron da zai kare mutunci na haka, wanda zai rufa min asiri haka me zai hana na bashi ita? Yanda ya ke da kyawawan halayya ina kyautata zaton idan har Zainab ta zauna karkashin sa, ta nemi wannan gatan ta take da shi ta rasa za ta nutsu Alhaji Sidi, haka kuma Na yi imanin Usman zai ruke ta da amana”

Cikin jimami Alhaji Sidi ke jinjina kai, kana ya nisa tare da fadin

“Innalillahi wainnailaihi rajiun! Zainab ba ta kyauta ba, duk da dai har da sakacin ka Malam, ai ba a shedar dan yau Malam, ka yarda da Zainab da yawa, haka kuma Hajiya ta yi sakaci duk dai rabin rayuwar yarinyar nan ba a gida ta ke yi ba, Amma da ana bibiyan ta duk sanda ta dawo da duk wannan masifar ba ta afku ba Malam, yardar ta yi yawa, sakacin yayi yawa!”

“Ka duba yanda na tsani kare Alhaji Sidi, har karnuka na debo na sa a gidan nan tun sanda mu ka fara zargin ana hauro mana gida, ashe dai tawa karyar ta gida ce……”

“Waiyazubillah!”

Alhaji Sidi ya katse Malam cikin hanzari, be gushe ba ya kara da

“Ka kausasa harshe da yawa Malam, Amma wani hanzari ba gudu ba, yarinyar nan haura katanga ta ke, ta na fita yawan dare, shin ka tambaye ta ina ta ke zuwa? Shin iya ka yawan abun ya tsaya? Ta na nan matsayin ta na budurwa ko kuwa dai istibiraqi ya hau kan ta?”

“Diya ta ba mazinaciya ba ce! Na yi imani diya ta ba za ta aikata zina ba kamar yanda ni ma ban taba aikata zina ba ”

Malam ya bashi amsa kai tsaye. Kai Alhaji Sidi ya dafe, cikin nuna bacin rai ya ce

“Ga ba irin ta ba! Ka na shedar gaibu kai tsaye! Ka taba tunanin Zainab za ta iya tsayuwa da wani da namiji? Bare kuma har ta na yawan dare? Amma yanzu ina gari ya waye? Haba Malam ya ka na Malami kana da sani ka ke ta ke sanin haka?”

Shiru ne ya biyu baya na dan wani lokaci, sannan Alhaji Sidi ya ce

“Na sani Malam, it’s not easy, shi ya sa na ce ma ka kada ka yanke hukunci cikin fushi, Dan kuwa matukar yarinyar nan akwai istibiraqi kan ta auren nan sai an warware shi…..”

“Idan kuma babu wallahilazim sai ta zauna da mijin ta matukar ba shi da bakin sa ya sake ta ba”

Ajiyar zuciya Alhaji Sidi ya saki, kana ya ce

“Idan har auren be sabawa addinin musulunci ba, be saba shari’a ba ai aure kam ka daura shi Malam”

Kai Malam ya jinjina cikin gamsuwa, Amma har ga Allah ba ya fatan wargatsewar auren Zainab da Usman, har lokacin be yi dana sani ba, ba kuma zai yi dana sani ba, da wannan kudirin su ka yi sallama da Alhaji Sidi. Maimakon ya kira Zainab kamar yanda yayiwa Alhaji Sidi alkawari, sai ya kiran kiran su Jauro yayi ya ba su umarnin su taya Usman a kwashe kayan BQ gaba daya a gyarawa Zainab da Usman dan kuwa a ranar za ta tare dakin mijin ta.

Ganin yanda su Isa su ke kai kawo hauka ne kawai Zainab ba ta yi ba. Hatta wayar ta da ta addabe ta da kara ganin Mike ne ke damun ta ba ta san sanda ta doka shi kasa ba, screen ya fashe. Halitta kuwa tun da su ka baro wajan Malam ta shige dakin ta ta kulle, kuka ta yi sosai kamar ran ta zai fita, duk da ba ta taba tunanin samin Usman a matsayin miji ba, Amma kasancewar shi mijin yar uwar ta abu ne mai ciwo a gare ta. Sam Ammy ba ta damu da halin da Halitta ta ke ciki ba, a tunanin ta halin abin da ya faru da Zainab ne ya sanya ta halin da ta ke ciki. Yan uwan Malam na jiki da kuma na ta yan uwan da su ke ta kira ta saka mu su kuka, cewar ta su kawo mu su doki Malam ya bayar da auren Yakura ga Maigadi, auren ma na sadaka ba tare da sadaki ba. Haka su ka ringa kiran Malam ya na gani ya ki dauka, karshe ma kashe wayan yayi gaba daya. Haka kuma ya ki sauraran ta bare su yi magana, tun ta na kuka har ta koma fada fada, ta na cewa Malam ya tsane ta ya tsani yayan ta shi ya sa ya mata wannan wulakancin.

Kafin azahar ta yi su Usman su ka gama gyaran BQ tas, dama kanana dakuna ne guda biyu, sai dan karamin kitchen da bandaki. Tun da su ka fara aiki Jauro ke jifan Usman da Habaici, bini bini ka ji ya ce

“Dan cirani an zama dan masu gida, an bar daji an zo birne ana mana surkulle”

Ko kuma ya ce

“Kai da na sani ni ma na yi kanzagi wajan neman suna da fa Malam ya dauran mata….”

Usaman na jin shi amma ya masa banza dan kuwa idan akwai abun da ya dami kwakwalwar sa ya bi bayan auren Zainab da aka daura masa, har ga Allah be da niyar kara aure saboda yanda auren shi da Cangwai ya kaya, bare kuma Malam ya aura masa mace wayayyiya, yar birni kuma yar boko kamar Zainab, shin ya rayuwar shi da Zainab zai kasance? Da wani idanu zai dubi Malam ya roke shi da ya sauwake masa wannan nauyi da ya dora masa?

Da wannan tunanin a ran sa ya wuni, dan kuwa ranar sam be sami kwanciyar hankali ba bare har ya samu ya kai lomar abinci bakin salati. Bayan la’asar Malam ya nemi ganin Usman a falon sa, Nan ma Jauro ya fara

“Dan masu gida sirikin Malam, an baka mata an baka wajen zama, maza je ka kila abin hawa kuma za a baka, kai ya kamata ka mu sirrin wannan surkullen na ka!”

Usman be kula shi ba ya wuce falon Malam. Sanye ya ke cikin rigar sakin shi fara, da bakin wando, fuskarsa rufe da farin rawani. Ganin takalma a waje ya sanya shi sallama tare da tsayawa daga waje. Malam ne ya amsa masa sallam sannan ya ba shi izinin shigowa.

Ganin ta zaune tare da Halitta sai da gaban shi fadi, badan komai ba sai dan yanda dukan su biyun su ka zuba masa idanun su da ya yi jajur kai ka ce mutuwa aka mu su, in da Halitta ke kallan sa cike da kewa, so da kauna, Zainab kuwa tsantsan tsana ne cikin na ta idanun, dan kuwa nan duniya idan akwai wanda ta tsana ya bi bayan Usman, wanda a yanzu haka shi ne mijin ta.

Da sauri ya kawar da kai gefe ya sami waje can baya ya na shirin zama Malam ya ce ya motso kusa da shi ya zauna. Cike da jin nauyi ya matsa gaban Malam wanda ke zaune kan doguwar kujera.

Malam na daga zaune ya ke kare mu su kallo, Halitta sanye cikin bakar abaya, kan ta nade da mayafin, Abin ku da farar mace har wani jaja fuskarta ta yi tsabagen kukan da ta sha. Shi kan shi Malam yayi mamakin damuwar da Halitta ta shiga sanadiyar hukuncin da ya yanke na auran yayar ta. Zainab kuwa Hijabin jikin ta har jirwaye yayi tsabagen hawaye da majinar da ya sha. Daci rai da bakin ciki ya sanya shi saurin dauke kai daga kallan Zainab yayinda ya furta

“Na yanke hukunci cikin gaggawa ba tare da na tambayi abu mai muhimmanci na game da shiri’ar musulunci ba sai da Alhaji Sidi ya nusar dani, ka sani Usman ko kadan ban yi danasanin daura ma ka diya ta da na yi….”

Jin haka wani sanyi ne ya ziyarci zuciyar Zainab, a tunanin ta Allah ya amsa adduar ta, Malam zai saka Usman ya sauwake mata igiya ukun da Malam daure ta da shi. Malam be gushe ba ya cigaba da fadin

” akwai tambaya mai muhimmanci da ya kamata na yi mata kafin na daura ma ka ita, kuma zan yi mata shi gaban ka tun da tsakanin mu da kai babu boye boye, amsar da za ta bani shi zai bani haske akan tarewar ka da ita ko kishiyar haka…”

Usman na mai dukar da kai cikin fatan Allah ya warware masa wannan nauyi da aka daura masa ya furta

“Na’am”

Zainab ba ta ankara ba sai ji ta yi Malam ya kira sunan ta da kakkausar murya ya na mai fadin

“Zainab ki duba girman Allah, tsakanin ki da Allah ki kin taba aikata zina? Yaushe ne ranar karshe da ki ka aikata?”

“Innalillahi wainnailaihi rajiun!”
Cewar Zainab hannun ta biyu ta sa ta toshe bakin ta tsananin kukan da ya ci karfin ta. Ita kan ta Halitta tambayar ta mata tsauri da bazata, shi kuwa Usman kan sa sunkuye ya na jiran amsar da zai iya zama mafita a rayuwar sa.

“Ke dallah rufa mana baki! Ki amsa min tambaya yanzu yanzu shasha kawai! Ba kya yawo ne? Idan ke kamila ce kamar yanda na yi tunani a da me zai sa na mi ki wannan tambayar? Ko za ki ce min ba ki taba kusantar zina ba idan har ma ba ki aikatawa ba!”

Malam ya fada a fusace, hakan ya sanya Zainab saurin fadin

“Wallahi dadi na rantse da Allah ban taba aikata zina ba Daddy, Daddy wallahi iyakaci na club, shi ma na maka alkawari ba zan kara zuwa ba Daddy….”

“Diya ta ni Birma a club!”

Malam ya katse ta cike da takaici. Zainab ta kara da

“Daddy idan har ka aurar da ni ga Sudais zan kasance mace ta gari a gare shi, Daddy ban taba zina ba Daddy, Daddy dan Allah ka sa ya sake ni, Daddy na tuba…..”

Wani sanyi ne ya ziyarci zuciyar Malam, dan kuwa shi kan shi ya san da Zainab mazinaciya ce tabbas zai iya hadiyar zuciya ya mutu. Ya na mai godiya ga Allah da iya club din ya tsaya, ya ce

“Bakin alkalami ya bushe, Usman shi ne mijin ki, auren shi ya tabbata akan ki….”

Kukan Zainab be sa Malam ya tausaya mata ba, idanun sa kan Usman ya ce

“Usman ga ta nan halak din ka ce, ci, sha da suturar ta ya rataya hannun ka, dan Allah ka kasance mai adalci, Zainab amana ce gun ka, na ba ka ita amana ko bayan rai na, kamin alkawarin duk runtsi duk wuya ba za ka sake ta ba, dan Allah Usman…..”

“Malam ba sai ka roke ni ba, Na daukar maka alkawari, Zan ruke ta amana, Na dau maka alkawari matukar ba a shiga hakkin Allah ba, ba zan taba sakin ta ba”
Jin alkawarin da Usman ya daukarwa Malam kamar wuka ya ke daba mata a kahon zuciyar, wasu zafafa hawaye ne ke zuba daga idaniyar ta tamkar wuta. Malam na duban Halitta wacce ita ma din hawaye ne ke kwaranya daga idanun ta jin alkawarin da Malam ya sa Usman ya dauka, Malam ya ce

“Halitta na yanke hukuncin ba da auren ki ga Sudais amadadin yar uwar ki, in Sha Allah kamar yanda mu ka tsara shabiyu ga wata juli zai kasance ranar daurin auren ki”

Da dashasshiyar muryar ta Halitta ta amsawa Malam da

“Toh Daddy, na yi biyayya”

“Allah ya mi ki albarka”

Halitta ta amsa da amin, kafin ya mayar da kallan sa ga Zainab wacce jin za a daurawa Halitta Sudais ba karamin bakin ciki ne ya kara taruwa cikin zuciyar ta ba. Gani ta ke Malam ya tsane ta cikin ‘ya’yan sa ya aurar da ita ga Mai gadi, gashi zai aurar da Halitta ga dan abokin sa. Ba ta kara sarewa da Malam na sai da ta ji ya ce

“Usman sai matar ka ta hado na ta ya nata ku tare can BQ da na tanadar mu ku ko? Da ga yau kada ta sake kwanan min cikin gida, ki kwana dakin mijin ki, na sallame ki har abada”

Daga Usman har Zainab Malam su ke kallo, ganin babu alamar sassauci a fuskar sa ya sanya Usman kallan Zainab, kamar yanda yayi imani zai mutu haka ya tabbatar da tashin hankalin da ke tattare da Zainab.

 

Back to top button