Auren Shehu Book 1Hausa NovelsHausa Novels

Auren Shehu Book 1 Page 14

Sponsored Links

14

 

Tun da Malam ya sa kafa ya tafi gaba daya ya dauki hidimar Ammy da ‘yayan ta ya watsar. Washagarin ranar da ya isa Maiduguri ya kira Shiek, in da ya sheda masa sauyin da yayi na auren Halitta da Sudais a maimakon Zainab da su ka yi alkawari akai. Kamar yanda yayi na’am a wancan karan, haka wannan karan ma ya amsa cikin godiya ba tare da neman ba’asi ba, haka kuma ba a sauya watan auren da su ka sa ba.

Kamar yanda Malam yayi burus da su, haka ita ma Ammy ta yi da shi. Kwanci tashi asarar mai rai, haka Malam yayi sati biyu a Maiduguri, idan aka ga kiran sa to ya kira ne ya duba lafiyar su, haka kuma ya fadawa Ammy ya tura mata kudi, da kuma kudin na menene. Ammy na gani Zainab ta ki bin maganar sa na ta koma BQ amma sam ba ta damu da hakan ba bare ta tsawatar mata, sai ma tambayar ta lokacin komawar ta makaranta da ta yi, jin be fi wata daya ya rage ba Ammy ta yi hamadala, ita a na ta ganin komawar Zainab makaranta shi ne mafi a’ala a rayuwar ta, kila kafin ta dawo Malam ya sauka ya raba auren Zainab da Usman.

Ana sauran kwana biyu a tashi da azumin ramadana, da daddare Ammy ta idar da sallar isha’i a dakin ta, zaune ta ke kan dadduma ta doka uban tagumi dan kuwa gidan ya mata kunci, abin duniya ya ishe ta ji ta ke kamar ta hada nata ya nata ta sake barin gidan. Sallamar Halitta ya sanya ta dago a hankali tare da amsa mata. Ta na mai kallan Halitta wacce ta tsaya bakin kofa hannun ta dauke da waya, cikin yaran shuwa ta ce

“Halitta ya dai? Lafiya ko?”

“Lafiya lau Ammy, zan iya shigowa?”
Ta mayar mata da harshen hausa. Kai Ammy ta gyada mata, cike da nutsuwa Halitta ta shigo cikin daki, ta sami waje kusa da Ammy ta zauna. Sanye ta ke cikin shudiyar atamfa dinkin doguwar riga, kan ta tufke da dankwali. Ta na mai duban Ammy cike da tausayi ta furta

“Ammy dama akwai wani abun da na ke so na nuna mi ki, da kamar ba zan nuna mi ki ba, ganin yanda dangantakar ki da Dady ya zamu wani abu na daban ya sanya ni yanke hukuncin fada miki”

Ammy na mai tattaro dukannin nutsuwar ta, ta dubi Halitta cike da fargaba dan kuwa a cikin dan kwanakin nan ta ga abubuwa kala kala har ta gode.

“Ke kuwa Halitta wannan abu menene shi haka?”

Maimakon ta bata amsa, sai ta shiga danna wayar hannun ta, Instagram ta shiga har ta kai ga shafin Zainab, ta shiga hutunan ta, musammam wanda ta yi ba da jimawa ba a club, ta na mai nuna fuskar wayar ga Ammy ta ce

“Ammy kin gane wacece wannan?”

Wayar Ammy ta karba daga hannun Halitta, tare da fadin

“Waiyazubillah wannan rashin tarbiya har ina? Ke kuwa Halitta ina zan san wannan lalatacciyar yarinya haka? Ji tufar da ke jikin ta? Wannan ai arniya ce! Kai wannan a arnan ma ba dai tambatsastsiya ba!”

Halitta na duban Ammy cike da tausayi ta ce

“Ammy duba fa da kyau ki ga, ba ki gane ta ba…..”

Ta na mai jefa mata waya ta ce

“Ke ni ban san shashanci ina na san wannan arniyar bare na gane ta! Toh idan ma kin san ta babu ke babu ita! Wannan lalalcewa har ina? Ji fa hayaki ta ke busawa….!”

“Ammy Yakura ce fa…..”
Cike da mamaki Ammy ta ce

“Ki na nufin kawar Yakura ce? Ta taba kawo ta gidan nan? Ina Yakura irin kawayen da ta ke mu’amala da su kenan?”

Halitta na mai girgiza kai yayinda ta ke dada nunawa Ammy hotan Yakura da ke kan fuskar wayar ta, ta ce

“Ba ki gane ta ba ne, ba kawar Yakura ba ce, Yakuran ce da kan ta Ammy duba ki gani…..”

“Zancen banza zancen hofi!”

Cewar Ammy yayinda ta fuzgi wayar hannun Halitta ta na mai kurawa hotan idanu a karo na farko. Kallan kurilla da ta yiwa hotan ya sanya ta furta

“Innalillahi wainnailaihi rajiun”

Hawaye ne bibbiyu ke fita daga idanun ta, fadi ta ke

“Halitta wannan diyar da na haifa ce haka? Wannan Yakura ce Halitta? Wannan me kama da Yakura ce…..”

“Wallahi Ammy ita ce, idan kin yi gaba ma za ki ga sauran hotunan ta da videos din da ta ke sakawa”

Cewar Halitta wacce ita ma din kukan ta ke ganin yanayin da Ammy ta shiga. Ammy kuwa yanda Halitta ta ce ta yi hakan ta yi, ta ringa bi ta na ganin munanan hotuna da videos din da Zainab ta yi, har ta kai ta kasa jurewa ta na mai wulgi da wayar ta tashi a fusace ta fita ta na kwallawa Zainab kira.

A falo su ka tadda ta ta fito a tsorace, haka ma Falmat wacce ihun kiran da Ammy ke yi ya firgita ta.

“Ammy gani lafiya…..”

“Tas” Ammy ta dauke kumatun ta da mari har sai da ta ga walkiya a idun ta. Kafin ta kai ga farfalowa ta kara daga hannun ta wanke kumatun ta da mari har sai da ta zube kasa tsabagen zafi, kuka ta ke mai kara kamar wacce ran ta zai fita, musammam ganin yanda Ammy ta rufe ta da duka kamar wacce Allah ya aiko. Cewa ta ke

“Na shiga uku! Ammy za ta kashe ni! Halitta ku taimaka min, Falmat ku ceci ni kashe ni Ammy za ta yi!”

Duk yanda Falmat ta so karbar Zainab daga hannun Ammy sai da abin ya gagara, dan kuwa garin haka ita ma sai da ta sami raban ta. Ganin Halitta ta tsaya gefe ta na kuka ba ta da niyar agazawa Falmat ta ce

“Halitta dan Allah ki taimaka ko Iya ne ki kira mana!”

Gudun kar ta kira Iya asiri ya dada tonuwa duk da ta na da yakinin Iyan ba ta nan, dan yanda Zainab ke ihu ya ci ace ta ji, Halitta ta taimaka, ita da Falmat ne su ka shiga tsakanin Zainab da Ammy, Ammy na haki ta ke furta

“Ku barni na kashe yar banza na huta, wallahi da haihuwar ki gwara barin ki Yakura! Innalillahi wainnailaihi rajiun! Da na sani na take kanki na mukurkushe ki sanda ki ka zo duniya da ba ki ja min wannan bakin ciki haka ba! Macuciya azzaluma! Allah ya………”

“Innalillahi Ammy ki duba girman Allah kar ki mata baki haka!”

Halitta ta yi saurin katse Ammy, yayinda Falmat ta ja Zainab kusa da kujera, kuka ta ke sosai dan kuwa ta daku kwarai.

“Wani baki kuma ya rage? Ai Yakura ko ban mata baki ba ai duniya ta mata, ace diya ta ta ciki na ce haka? Allah sarki Malam! Allah sarki Malam, ciki mai haife haife ya haifo mana masifa! Sai yanzu na fahimci hukuncin da ya yanke kan wannan lalatacciyar yarinya!”

Ta karasa maganar ta na mai nuna ta da dan yatsa. Jikin gurnanin kuka Zainab ta furta

“Ammy me na mi ki haka da na cancanci wannan la’anta Ammy?”

“Uban ki ki ka min! Har ki na da bakin magana? Kai wannan yarinyar kashe ni za ta yi ni Aleesha!”

Cewar Ammy ta na mai daura hannu biyu bisa kan ta, ta kai ta kawo, ta kai ta kawo ta dubi Halitta ta ce

“Dauko wayar nan Halitta, maza dauko ta!”

Cikin rawar jiki Halitta ta je ta dauko wayar ta kawowa Ammy, karba ta yi ta na mai jefawa kan jinyar Zainab ta ce

“Dauka ki goge duka hotunan ki da kazaman videos din ki dan uban ki!”

Hannun na rawa Zainab ta dau wayar, ko da ta duba ta ga dalilin da ya sa Ammy ta nakada mata na jaka, a hankali ta dago ta dubi Halitta, ta na mai kallan ta irin wannan kallan kin ci amana ta. Ganin haka Ammy ta ce

“Ki dena kallan ta! Dubin ki ya gama cika Zainab! Ke ma Halitta duk wannan masifun da laifin ki, ki sani duk yanda Yakura ta cutar da mu ki na da gudunmawa akai, dan kin sa kyamatacciyar rayuwar da ta ke yi amma ki ka ki sanar da mu!”

Cikin sanyin jiki Halitta ta furta

“Ammy…..”

“Shhhhh! Kar ki ce min komai! Da kin fada min da duk haka be faru ba! Oh ni Aleesha me na mu ku haka Halitta? Me na muku?”

Cewar Ammy ta na mai ware hannu cikin alamar tambaya. Ta na duban Zainab ta daka mata tsawa
“Na ce ki goge me ki ke jira dan uban ki!”

Baki na rawa tsabagen tsoro dan ba su taba ganin Ammy cikin matsanancin bacin rai kamar haka ba, ta ce

“Ammy ai sai ta account dina, Kuma waya ta ta fashe, sai dai Halitta ta taimaka ta fita daga na ta account din….”

“Maza Halitta fita ta shiga nata, ta goge komai delete everything, son samu ma ta rufe page din gaba daya! Wannan idan Malam ya gani mun kade har ganyen mu!”

Ammy ta katse ta, ta na maganar ne cike da gaggawa. Halitta wacce sam ba ta yi danasanin tonawa Zainab asiri da ta yi ba, sai ma na yin jinkirin da ta yi. Hannu ta sa ta karbi wayar ba tare da ta damu da mugun kallon da Zainab ke watsa mata ba ta fita daga na ta account din, sannan ta mayarwa Zainab da wayar ita ma ta shiga na ta. Nan ta ringa bin duka hotunan da videos din da ta saka ta na deleting, sai da ta koke tas, sannan Ammy ta sa ta yi unfollowing kowa da da take following, ta na mai duban Ammy da jajayan idanun ta ta furta

“Ammy na yi abin da ki ka ce…..”

“Saura delete! Ki yi deleting account din gaba daya ya dena aiki!”

Cikin rawar murya ta ce

“Ammy ban iya ba….”

“Za ki iya ne dan uban ki, dukan da na mi ki ne be ishe ki ba ina ga!”

Jin haka hannu na rawa Zainab ta bi yanda za ta yi, sai gashi ta yi deleting account din gaba daya. Sannan ta wulgawa Halitta wayar ta. A fusace Ammy ta ce

“Maza ki fasa mata wayar ki siya mata sabo gal, asararriya kawai! Ki sani a daren yau za ki hade na ki ya na ki ki tafi can inda Malam ya ce ki na kwana da mijin ki, har ki na shirin kashe min aure ashe na bar jaki ina can ina dukan tanki!”

“Dan Allah Ammy ki yafe min, kar ki ce na kwana BQ, Allah Ammy ba zan iya ba, Ammy dan Allah”

Cewar Zainab cikin sheshekar kuka. Cikin nuna halin ko in kula da kukan ta Ammy ta ce
“Wallahi sai kin koma! Na baki nan da minti talatin kacal ki hada naki ya naki ko na dan dena ganin ki na sami sarari cikin zuciya ta, kuma kada wanda ya saka mata hannu cikin ku! Idan ya so idan gari ya waye na ga kin sake haurawa kin bar gidan gaba daya! Shi ne zan san kin isa tabarayyi!”
Da wannan ta juya ta shige dakin ta tabar Zainab ta na mai watsawa Halitta a harara, ta kara da

“Na tsane ki Halitta, tsakanina da ke Allah ya isa ban yafe ba”

“Mtswww”

Halitta ta ja tsaki, sannan ta kara da

“Allah ya isan ki ba zai ci ni ba, sai dai ya ciki ke kan ki! Kin ga tafiya ta!”

Ta juya ta wuce na ta dakin ta na juyo zagin da Zainab ta ke sirfa ma ta. Falmat kuwa wacce dama jikin ta ya gama mutuwa waje ta samu ta zauna in da ta ke kallan Zainab cike da mamaki. Kallan da ta ke mata ya sanya Zainab tashi a fusace ta shige daki ta na mai doka kofa.

Yanda Ammy ta yi kwance ta na kuka, haka Zainab ta zauna na ta dakin ta ci kukan ta ta koshi. Minti talatin daidai sai ga Ammy ta zo ta na mata oya oya ta fito ta wuce dakin ta, haka da kuka da majina ta na cijewa Ammy ta ja ta, zanin gado da filo kawai ta iya dauka, ita ta kai ta har corridor din da shi ne zai fita da ita waje, tafiya kalilan ce tsakanin kofar corridor din da BQ. Hakan yayi daidai da gyaftawar Jauro, zai je ya kunto karnukan gidan. Ganin abin da ke faruwa jiki na bari ya wuce simi simi ba tare da Zainab ta lura da wucewar sa ba ya koma ba tare da ya je kunto karnukan ba

Bakin corridor ta zauna ta gama shan kukan ta, ganin sauro na shirin cinye ta ya sa ta lallaba ta karasa BQ din a tsorace hannun ta dauke da tsanin gadon ta da filo. Ganin Usman ba ya kusa ta shige dakin da ta fara cinkaro da, cikin sauri ta sakata da jam lock da kulle dakin gam.

Cike da kyamkyami ta ke duban dan karamin gadon da ke dakin. Farin zanin gado ne, tuni ta yaye shi ta yi wulgi da shi gefe, yayinda ta dan shifida rabin na ta, haka kuma ta rufa da sauran rabin, sai ajiyar zuciya ta ke yi tsabagen kukan da ta sha.

Jauro kuwa ko da ya koma wajan da ya bar Usman da Isa zaune kan benci, ya na mai dukan kafadan Usman ya furta

“Dan cirani ka tsinci dami a akala!”

Dukan su duban shi su ke cikin rashin fahimta, Jauro ya gyara tsayuwa ya ce

“Ai yau za ka sha gara dan cira ni, abin ba a cewa komai Allah ya kashe ya ba ka, dan kuwa ga amaryar ka can a tafe zuwa dakin ka, ka ga da ni ne sai na ga abin da ya turewa buzu nadi, cargwadi! Sunan wani abinci wai rahadada! Za ka huta fa dancirani! Matsalar dai kila ba kai za ka fara…..”

Ji ka ke “Tas” Usman ya sauke yatsun sa biyar bisa kuncin Jauro har sai da ya ji ya dena ji na wasu dan sakanni baya ga jinin da ya shiga gangarowa daga hancin sa tsabagen karfi da zafin hannu na Usman, ya na mai nuna Jauro da yatsa ya ce

“Idan ka na cin kasa, ka kiyayi na shuri! Sakarai mara daraja!”
Ya juya a fusace ya nufi ciki ya bar Jauro hannu bisa kunci in da ya ke fadin

“Ya kurmartar da ni, Isa ka na kallo ya raftama min gatari a fuska! Aradu ya mayar da ni kurma Isa”

Fuskar Isa cike da jin dadin marin da Jauro ya fusha, ya na darawa ya ce

“Ba gatari ba ne, wallahi hannun sa ya sa ya kwashe ka da uwar mari”

Jauro na susa kunci ya ce

“Kai dan manzo wai hannun mutum ne haka? Kai wannan ba dai basamude ba!”

“Ka ma godewa Allah ba sandar nan ta shi ya rafta ma ka ba, ina fada ma ka ba ka ji Jauro! Ka dena rai na mutumin nan ga shi ka fari gani”

Zafin marin da ya sha, da kuma maganganun Isa ne ya tunzuro Jauro, nan ya fara kurari ya na masifa, fadi ya ke

“An rai na shi din, shi dan uban wane! Da ya isa da ya tsaya mana sanda ya mare ni! Tsoro ya sa shi shigewa ciki da sauri! Da mana ya tsaya!”
Isa na mai taba kafadar Jauro ya furta

“Idan ka gama ihun da ka ke bayan hari don Allah ka sheda min, bari na tai ta kunto karnukan nan da munafunci ya hana ka yin aikin ka”

Jauro ya rikice nan ya fara ruwan ashar, In da Isa ya maishe shi mahaukaci, Nan ya bar shi ya na hayaniyar shi shi kadai.

Ko motsin Usman ba ta ji ba, bare ma ta ga giftawar shi, garden ya je yayi zaman sa bisa kujera ya na mai neman tsari daga tafasar da zuciyar sa ta ke yi, Dan kuwa be taba jin zafin magana kamar wanda Jauro ya fada masa a yau ba. Yanda ba ta sami cikakken bacci ba a daren ranar gudun kar Usman ya zo ya fada mata duk da dai ta san ta rufe kofar. Gashi taurin kai irin na Zainab ya hana ta sake komawa ta lallabi Ammy ko ta hakura ta barta cikin gida. Haka ita Ammy, wacce tashin hankalin ko a wani hali Zainab ke ciki ya hana ta bacci.

Sai da aka kira sallar asuba sannan bacci mai nauyi ya sace Zainab, ba ita ta tashi ba sai wajan karfe goma sha biyu na rana. Bandakin cikin dakin ta shiga, duk da bandakin fes ya ke sai da hankalin Zainab ya tashi matuka, dan ko fitsari ma ta kasa tsugunnawa ta yi, dan haka ta lallaba ta koma dakin ta cikin sanda, nan kuwa ba ta san Ammy ta gan ta ba.

Wankan ta fara sannan ta hada asuba da azahar ta yi, ta na shirin haye gadon ta ta mike sai ga Ammy ta shigo, ta na mai salati ta ce

“Lahaila me zan gani Yakura? Me ki ke min a cikin gida?”

Cikin marairaicewa Zainab ta tashi zaune. Idanu na kawo kwalla ta ke fadin

“Ammy ki rufa min asiri wallahi kyamkyamin BQ din na ke, wallahi Ammy….”

Cike da takaici Ammy ta ke duban ta, ka na ta ce

“Ba ki ji kyamkyamin rayuwar ki ba sai na BQ? BQ yanzu yanzu za ki iya gyara shi? Karkari ya sha shara da guga? Ki tashi ki fitar min daga gida, bana san ganin ki Yakura! Idan har abin ya mi ki ciwo toh ki zage ki gyara BQ din, Amma kar na sake ganin ki kwance cikin dakin nan, wallahi sai na sabar mi ki!”

Cikin fushi Zainab ta tashi ta fice fuuuu ta na mai doka kofa. Sai da Ammy ta kai zuciyar ta nesa dan ji ta yi kamar ta bi ta ta kara nakada mata na jaki ko ta huce.

Tsakanin ‘ya da mahaifa aka ce sai Allah. Ammy ce da kanta ta hade abincin na cin mutum biyu, cikin dan kwando ta jera kulolun ta ce da Iya ta kaiwa Zainab, Amma kada ta ce ita ta saka ta.

Halin da Iya ta ga Zainab ya sa ta tausaya mata matuka, ta yi ta yi Zainab ta ce abinci ta ce ba ta ci, ta koshi. Iya ce ta sa hannu ta wanke mata bandaki har ma da shara da gugan daki, ta tsaftace mata ko ina tsaf sannan ta kyale ta. Bayan tafiyar Iya Zainab ta farma abincin, ta ci ta koshi sosai dan kuwa daurewa ta yi ta ki cin abicin gaban Iya dan ta fadawa Ammy ko ta tausaya mata.

*****

Da nadamar yanda ta bijerewa Malam Ammy ta kwana ta tashi, tunanin ta be wuce na yanda za ta yi ta nemi afuwan Malam, daga baya ta yanke hukuncin kiran sa. Sai da ta shiga dakin ta, cikin faduwar gaban yanda zai amsa mata, da kuma abin da za ta ce masa, ta kira har sau uku ba ya shiga, sai ta yi tunanin ko in da ya ke ne ba network mai kyau. Ba ta dade da aje wayar ba sai ga kiran Hajja Dudu. Da kamar ba za ta daga ba dan kuwa ta kullaci Hajja Dudu, gani ta ke ita ta dauko Hajja Kilishi ta kawo ta Kano har ta tafi da Malam. Ta na kallo har wayar ta tsinke. Ganin ta sake kiran ta bayan tsinkewar wayar Ammy ta dauka, muryar Hajja Dudu taji cikin kuka ta ke fadin

“Aleesha ki hado yara maza ku taho Maiduguri komin dare! Malam sun yi hatsari hanyar tahowar su Kano!”

Cikin ihu Ammy ke fadin

“Innalillahi wainnailaihi rajiun! Innalillahi wainnailaihi rajiun! Ya jikin na sa? Me ya same shi? Lafiya ya ke?”

“Ku dai taho Aleesha, abin dai sai kun gani!”

Ta na gama fadin haka Hajja Dudu ta kashe wayar ta, Ammy ta saka kuka mai tsuma zuciya, hijabi ta saka gaba a baya, ta na surutai kamar zaucacciya fadi ta ke

“Ya Allah kar ka raba ni da miji na ba tare da na nemi gafarar shi ba, ya Allah kar ka dau ran miji na ba tare da na nemi tafiyar shi ba! Innalillahi wainnailaihi rajiun!”

 

 

*Khadija Sidi*
Auren Shehu

Back to top button