Auren Shehu Book 2Hausa NovelsHausa Novels

Auren Shehu Book 2 Page 4

Sponsored Links

*Khadija Sidi*
Auren Shehu 2

4

 

In da Ammy da Anty Sauda ke cikin fargaban halin da Zainab ta ke ciki, Zainab kuwa kasa daurewa ta yi, cikin akwatin ta ta sami dankwalin wata atamfar ta dinkin doguwar riga, hannun ta dauke da buta ta sa kai ta fito daga bukka.

Hankalin ta yayi gaba bare ta lura da jama’ar da ke kallan ta, ta na dingisawa kai tsaye bandakin da aka nuna mata ta sake komawa. Ta na shiga ta sami busasshen waje nan ta baje dankwalin ta saboda gudun cutar bandaki, sannan ta tsugunna ta gandara kashin ta sai da ta kasayar da komai sannan ta dawo hayyacin ta. Cike da kyamkayamin kan ta ta matsa daga gefe ta yi tsarki, Nan ta bar mu su kashin ta fito ta na yarfe hannu ta shige daki cikin akwatin ta ta dauko sabulun wankan ta da Allah ya sa ta hado da shi, ta sake fitowa tsakar gidan tana waige waige ko Allah ya sa ta ga boki.

Allah ya taimake ta ta hangi bokitin karfe, cikin dauriya ta karasa wajan bokiti, ganin babu komai ciki ta zara ta na waigawa lungu da sakon nema ma’ajiyar ruwa. Ta karaci waige waigen ta ko rijiya ba ta hanga ba bare famfo, haka kuma tambayar jama’ar gidan da suka mayar da ita tamkar talabijin bata lokaci ne. Idanun ta ne su ka sauka kan randuna manya guda uku, duka rufe da murfin langa, kawannan su da moda bisa kai. Kai tsaye ta nufi randar, ta fara duba na farko ta ga ba ruwa, na biyun kuma ruwan ya kai rabi, sai na ukun ne cike da ruwa. Wani dan yaro ta kalla ta ce

“Kai zo ka zuba min ruwa….”

Yaro ya tsaya ya na kallan ta ba tare da ya motsa ba, Zainab ta ja tsaki yayinda ta aje bokitin, hannun ta na dama ta sa ta bude randar, da modar da ta gani bisa randar ta debo ruwa ta na mai murzar sabulu ta wanke hannun ta, sannan ta goga sabulun cikin bokitin ta na cudawa da hannun ta. Kan ka ce me tuni yara sun matso suna mamakin kumfar da sabalun Zainab ke bayarwa, dan kuwa ba kowa ba ne ke samun damar wanka da omo bare kuma uwa uba sabulu.

Sai da ta wanke bokitin tas, ta dauraye da ruwan randar nan da dama rabi ne ciki, har ta karar da ruwan, sannan kuma ta bude randar da ke cike da ruwa, Amma babu damar dauka, hannun ta ruke da sabulun ta, ta jefa modar cikin bokiti ta fara ja, ta yi ta na hutawa haka kuma ruwa be fasa zubewa ba, haka ta shige bukka ta na jiyo maganganun mata gidan da ta tabbatar da ita su ke akan ruwan da ta kwasa.

Cikin bukka ta aje bokitin gefe guda, tana mai tura kwararen abincin da aka aje mata karkashin gadon kara, ta sa hannu ta tattare yar ledar da ke shimfide, da ke dama ba wata ledar arziki ba ce, bukkar ya zama sai kasa ne kamar yanda tsakar gida da bandaki. Assabarin daki ta saka ta na fadin

“Duk wanda ya shigo kan sa yayiwa in ba dai wannan tsinannan ba ne”
Ta na mai juyawa kofa baya ta cire kayan ta, ya rage daga ita sai dan fantari. Nan tsakar bukkar ta dau moda ta shiga kwararawa jikin ta ruwa, duk sanda ruwan ya sauka jikin ta sai ta kusan shidewa tsabagen sanyi, Amma haka ta zake dantse ta cigaba watsa ruwa ta na kwashewa Usman albarka.

Can tsakar gida kuwa kanwar mahaifyar Usman wato Iyalle ce ta shiga bandaki, Nan ta tarar da kashin Zainab malale bisa dankwali. Ta juyo ta na salati da sallallami ta ke shedawa jama’ar gidan ta’asar da Kado ta mu su na bahaya a bandaki. Hansai matar Kawu Iliya wacce dama ta fi kowa zafi cikin gidan ce ta fusata cikin harshen fulatanci ta ce

“Kan uban can! Kashi ta mana a bayi? Ita sarauniya ba za ta iya yankar daji ba? Nan fa kuna kallo ta kwashe ruwan shan gidan nan kaf ta shige daka da shi! Zan yi magana aka hana ni! Wallahi ba za sabu ba!”

Fuuuu ta wuce bukkar Usman, su Iyalle na tsayar da ita amma ta mu su banza, ta na isa bakin bukkar ta sa hannu ta daga assabari ta cusa kai, Nan ta yi arba da Zainab daga ita sai fantari ta juya baya ta na saba jikin ta sabulu. Hansai ta saki assabari ta na salati har da kuka fadi ta ke

“Innalillahi ni Hansai an cuce ni! Wayyo na shiga uku na lalace wannan Kadon be da mutunci! Wayyo na yi gamo Allah ya isa ban yafe ba! Wayyoo….”

Da gudun ta ta bar bakin kofar bukkar in da ta tsugunna musu a tsakar gida ta na rafka ihu kamar wacce aka aikowa sakon mutuwa, jama’a na tambayar ta lafiya amma ta kasa magana sai nuni ta ke ga bukkar Shehu, Iyalle ta yi kokarin zuwa ta duba abin da ya birkita Hansai haka amma Hansai ta ruke kafar ta, fadi ta ke

“kada wanda ya je kusa da bukkan can! Ku kira Shehu! Fitina ta sauka Rugar Shehu! Masifa ta saukar mana!”

Zainab kuwa tun da ta ji alamar an daga assabari gaban ta ya fadi, jin salatin mace ya tabbatar mata ba Usman ba ne ya leko, cikin azama ta dauraye jikin ta tas ruwa na malalewa tsakar dakin. Bisa gadon kara ta haye, tana daga durkushe ta fitar da dan towel din ta ta tsane jikin ta sannan ta daura, ko da ta duba ta ga tana da fantari har hudu cikin akwatin ta, wulgi ta yi da wanda ta cire. Kaya set biyar ne kacal cikin jakar, atamfa dinkin doguwar riga guda uku, duk da akan kallabin daya daga ciki ta yi kashi, sai kuma dogwayen ruguna, wanda ta bar makaranta sanye jikin ta da shi, da kuma wata koriya mara hannu, sai panties guda hudu, da bra guda hudu, sai kuma bumshort din ta guda biyu da yan rugunan su suma guda biyu. Koriyar doguwar rigar ta fitar, cikin azama ta ke shiryawa saboda hayaniyar da take jiyowa daga waje duk da dai ba ta san takamammen abun da ake cewa ba.

*****
Usman na zaune fadar Shehu, tattaunawa su ke akan maganar cigaba da Shehu ya kawo mu su, wato na azancin Shugaban kasa Muhammdu Buhari akan ‘Ruga settlement policy’. Cewar shi zai so ace Rugar Shehu na daya daga cikin Rugar da za ta amfana da wannan tsari da shugaban kasa ke kokarin kafawa cikin kasar Nigeria. Kawu Iliya ne ya nisa, kana ya ce

“Allah ya gafarta Shehu, ban tari numfashin ka ba, na san ka yi zaman birne, Kuma ka san halayyar Kado, Kado ba mutunci sai shegen san zuciya! shin ka na tunanin wannan ba wani salo na zalunta da toye hakkin mu fillo na ne? Ace za a killace bafulatani da shanun sa waje guda? Ba kiwo ba yawo? Ni fa na fi zatan hadi ne! Hadin baki ne da manoma domin a tauye hakkin mu!”

“Fakat! Fakat!”

Cewar sauran jama’a cikin nuna amincewa da da maganar Kawu Iliya. Wani ya kada baki ya ce

“Wai tunda mu ke kun tabajin wani shugaba a kasa nan ya taba waiwayar mu? In ba da tsiya ba ko laifi, sai dai fa ace mun haura gonaki a taro mu! Ko kuwa a kira mu yan ta’adda ma su kidinafan”

Shehu na mai jinjina kai ya ke jin jawabin su. Wani matashi ne ya ce

“Ni kuwa sai na ga kamar cigaban ne da gaske, matukar za a kawo mana asibiti, da makaranta da wutan lantarki….”

“Asibiti? Makaranta?wutan lantarki?”

Wani Dattijo ya katse shi a fusace, kana ya kara da

“Su kawo mana makaranta irin ta su ta boko su lalata tarbiyar ‘ya’yan mu musammam mata ko? Ko kuwa asibiti za su kawo mana daga nan su cusa mana hana haihuwa? Su hana matan mu haihuwa dama sun ce mun fiya haihuwa, to dan Allah idan ka dauke saduwa da matan mu wani abu ne ke kawo mana jin dadi ko nishadi duk duniya? Ina su ke so mu sa kan mu ne saboda Allah? Matan mu idan sun kai ma su tallan nono su hure mu su kunne wasu har cikin shege su ke kawo mana, yawanci ‘ya’yan shegun su ne ke girma su ke koma mu su kidinafas!”

“Gaske Malam Madu, maganar ka gaskiya ta ke!”

Shehu na duban su ya furta

“Na ji koken ku duka, na kuma fahimta, Amma zan so mu dubi wannan lamarin ta bangaran amfani da masalaha……”

Tahowar yaro da gudun famfalaki ne ya katse Usman, yaro na haki yayinda ya karasa gaban Usman ya zube har kasa tare da fadin

“Allah shi taimaki Shehu, gida dai kam babu lafiya, Hansai ta na can Kado ta sa ta kuka har da firgici, Allah kadai ya san abin da ta mata….”

Usman yayi zumbur ya tashi rai bace cikin ran sa ya na ayyana hukuncin da zai aikata matukar Zainab ta cutar da al’umar Rugar sa, Musammam ma ahalin gidan Shehu.

“Ka ga sharrin Kado ai, ga shegentakar nan ai, ita dai tilo tun da ta wayi gari cikin Rugar nan ba ta bari an huta ba! Kado ba mutunci! ”

Cewar Kawu Iliya. Bello ne ya tashi tare da fadin

“Bari na je gidan na ga abin da ke faruwa”

“Ni zan je da kai na, ku yi hakuri yanzu za a kare zaman yau, sai kuma Allah ya kai mu gobe, bissalam”

Ya na fadin haka ya zura takalmin sa, yanda ya ke tafe cikin sauri kadai ya isa ya nuna yanayin bacin ran da ya ke ciki.
Auren Sheshu 2

4

 

 

Tafiya ta ke ta na dingisawa, tsoron duhun daji be hana ta kutsawa cikin dajin ba dan kuwa a zaton ta za ta iske titi nan kusa. Yanayin duhun bishiyoyi da kuma kukan tsuntsaye da birrai ne ya hana ta zama duk yanda ta so ta zauna ko tafin kafar ta zai sarara daga zugin da su ke mata. Ta na tafe tana kwashewa Usman da jama’ar Rugar Shehu albarka, hannu daya na jan akwatin ta da ke makalewa cikin itace lokaci lokaci, dayan kuma ruke da wayar ta, har lokacin ba ta fasa neman sabis ba ta na ta gwada numbobin waya ko zai shiga. Ganin hasken rana kusa ya sanya ta kara himma a zaton ta titi za ta bullu, ko da ta karasa sai ganin ta ta yi cikin wani fili mai bishiyu yan tsirara wanda hakan ne ya bawa rana damar haskaka filin. Wayar ta ta yi kukan karshe sai dib ta dauke gaba daya chaji ya kare.

Cike da taikaici Zainab ta karasa inuwar wata yar bishiya yayinda ta yi cilli da akwatin na ta gefe guda ta zube a kasa ta na kuka mai fitar da sauti, ji ta ke ina ma bacci ta ke Allah ya taimake ta wani ya tashe ta da kuwa duk abin da wanan nan zai ce ya na so daga gare ta sai ta masa. Sai da ta yi mai isar ta sannan ta yi shiru sai ajiyar zuciya cikin ranta ta na mai tunanin mafita

Sam ba ta lura da lallausan abin da ta kafar ta ke take kai ba, bare ta ankare da katoton koran macijiya wanda ake kira kasa da ke kwance karkashin in da ta aje kafar ta ta ba ta na bacci. Sai da kasar ta dan motsa kadan sannan ta ankare, tsabagen firgice kasa ihu ta yi, haka kuma ta kasa tashi ta ruga dan karshen tsami kafar ta tayi dan zaman nan da ta yi bayan ta gama fama kafar. Dan rarrafawa ta yi ta na mai cije lebe yayinda duwatsu da itacen wajen ke sukar gwiwowin ta ta cikin duguwar riga, sai da ta tabbatar ta yi nesa da macijiyar sannan ta yi zaman ta dirshen a kasa tamkar zararriya. Hanyen ta biyu ta saka ta rufe fuskar ta tana fadin

“Innalillahi wainnailaihi rajiun! Allah ka fitar da ni daga wannan kangin rayuwa, Allah ka kawo mafita, Allah ka kawo min doki…..”

Kamar daga sama ta ji muryar shi ya ce

“Bar kuka Abu, Allah ya amsa gani ya kawo ni!”

A firgice ta dago kan ta, ganin wanda ke tsugunne gaban ta, idanun sa har sheki suke, duk da rabin fuskarsa rufe ya ke be sa ta kasa ganin murmushin mugun ta da fuskar sa ke dauke da shi. Wani irin tsanar sa ce ta mamaye zuciyar sa, kai tsaye ta furta

“Na tsane ka!”

“Alhamdulillah! Dama na fi so ki tsaneni, me zan mi ki ki kara tsana ta? Dan Allah ki ta tsana ta har illa mashaAllah! Ni Usman na mi ki alkawari zan mi ki rainon wannan tsana da ki ka mi ni!”

Cikin rashin fahimtar in da ya dosa ta ce

” Me ya sa? Me ya sa ka biyo ni? Kudi ka ke so? Idan shi ka ke so wallahi Ammy za ta ba ka ko nawa ne……”

Ya na mai dariyar mugunta ya sami waje ya zauna hakan ya sa Zainab kara jan na ta jiki domin yin nesa da shi. Sai da yayi dariya mai isar sa ya ce

“Kudi? Da shi ki ke takama ko? Shi ya sa ki ke tunanin kowa shi ne burin sa? Ki na tunanin dukiya ya sa na dauko ki? Wallahil azim in da za a hade dukiyar ku kaf ba zai yi kwatar dukiya ta ba, Ni bakauye ne amma ba matsiyaci ba, Dan haka dukiya ba ta daga cikin dalilin zuwan ki Rugar Shehu….!!!”

Baki bude Zainab ta ke kallan sa, ta na mai hadiyan yawun azaba domin kuwa makogaron ta ya bushe, ta kada baki ta ce

“Menene dalilin ka? Ya aka yi na zo nan? Ka mayar da ni makaranta yanzun nan!”

“Shhhhh!”

Usman ya katse ta ya na mai dora yatsa bisa labban sa ya ce

“Kul kar da ki tada macijiya, a matsayi na na Shehun rugar ga ba zan iya hana ko wani halitta abincin sa ba, ko da kuwa abincin halittar nan mata ta ce!”

Wani irin zufa ne ya ketowa Zainab yayinda da ta kai kallan ta ga inda kasar ke kwance ta na bacci, sannan ta mayar da kallan ta ga Usman ta sake furta

“Na tsane ka wallahi! Ka mayar da ni gida na ce! Damn you!”

Yana murmushin mugunta ya ce

“Umarni ki ke ba ni halan? Har yanzu ba ki gane cewa a dajin da Rugar Shehu take ki ke ba, Ni Usman ni ne Shehu, ba bil’adama kadai ba, hatta dabbobin dajin nan ni an Shehun su, Ni an shugaban su! Ina mi ki bayanin nan ba dan komai ba sai dan kar ki halaka…..”

“Mtswww!”

Zainab ta ja masa dogon tsaki wanda ya tunzura Usman, ya tashi tsaye cike da motsawar zuciya ya ce

“Idan har ban cire mi ki wannan rashin kunya ta ki ba Abu cikin kwanaki kalilan wallahi ban isa Usman ba! Sai kin roki sassauci Abu, da bakin ki za ki roke ni sassauci….”

“Tir! Allah ya sauwake! Ba zan taba rokan ka ba ko da kuwa zan rasa rai na!

“Idan kin shirya rasa ran na ki ki zauna anan duk sanda maciyar can ta tashi ta yi kalaci da ke, idan kuwa kina son ran ki tashi ki bi mijin ki dakin auren ki”

Banza ta yi masa, ta na gani ya juya ya tafi zuciyar ta na dukan uku uku tsabagen tsoro, Amma kafiya ya sa ta dauke kai. Usman kuwa be yi zaton zai yi takun da yayi ba tare da ta biyo shi ba. Jin ba ta biyo shi ba har ya fara nisa ya sa ya juyo, ya gan ta zaune in da ya bar ta ko motsawa ba ta yi ba. Ya na mai girgiza kai ya dawo gare ta. Dan akwaitin ta ya fara dauka, ganin ya nufo ta ta kafe shi da manyan idanun ta da ta san ya na firgita duk wanda ta yiwa irin kallan, ba ta ankara ba sai ji ta yi ya furta

“Idanun ki ba za su taba firgita ni ba, idan kuma mutuwar ki ke son yi ba zan bari ki yi ba tare da na cimma buri na kan ki ba, ba ki isa ba”

Sungumarta yayi ya aza bisa kafada. Ihu ta ke ta na kai masa duka da wayar hannun ta, da dayan hannun har ma da kafafun ta. Idan Usman ya na jin zafin dukan sam be nuna ba, tun ta na ihu har ta koma sirfa masa zagi, ko a jikin sa haka ya shiga Rugar Shehu, duk in da su ka gifta jama’a na gida da na waje kowa fitowa yake domin ya ka ga Shehu dauke da Kado, wannan lamari ba karamin mamaki ya ba su ba.

Ba shi ya sauke Zainab ba sai a tsakar bukkar sa, ta na mai mayar da ajiyar zuciya ta ke fadin

“Mugu azzalumi! Allah ya isa jiki na da ka hada da na ka!”

Rai bace ya ke duban yanda ta ke kabe jikin ta kamar wacce najasa ta taba ta, ta kara fadin

“Allah ya isa ka hada kazamin jikin ka…..”

A fusace ya kai hannayen sa ya biyu bisa kafadar ta ya fizgo ta tsaye ya na mai hankado ta jikin sa ta fada kirgin sa, ya sa hannu ya rungume ta gam yanda ko kwakkwarar motsi ba za ta iya ba, haka kuma ihun da take son yi ya tsaya iya makogoro sanadiyar wani yanayi da ta tsinci kan ta, tun tana kokarin kwatar kan ta, har ta gaji, kan ta bisa kirjin sa ga mamakin ta duk da dai ba ta ji kamshin turaren da ta saba ji daga jikin abokan ta irin su Mike ko Bobo duk sanda su ka rungumi juna ba, Sam ba ta ji warin datti ko na hammata da take kyautata zaton za ta ji daga jikin Usman ba. Jin hanyen sa na shafa gadon bayan ta sai da ta ji yar tun daka yatsun kafar ta har zuwa gashin kan ta, ba ta san sanda ta runtse idanun ta ba yayin da bugun zuciyar ta ya karu, bakin sa dab da kunnen ta na dama ta na jiyo numfashin sa, ya furta

“Ni mijin ki ne! Jikin ki nawa ne ina da ikon hada shi da nawa duk sanda na ga dama, ku ma na san zaki sakar min jikin na ki, ji yanda ki ka saki jiki kina mayar da numfashi, ko da yake ba abin mamaki ba ne, tamakar karya ki ke kin saba sakarwa ko wani kare da biri jikin ki……”

Kamar wacce aka watswa ruwan zafi haka Zainab ta farfado daga shaukin da ta shiga na kankanin lokaci sanadiyar rungumar da Usman ya mata, kukan kura ta yi ta na mai ture Usman hakan ya sa shi sakin ta ya na murmushin mugunta, dama abin da ya ke so kenan ya gasa mata bacin rai, ran ta ya soyu shi ne farin cikin sa. Cike da bacin rai yayinda idanun ta ke fitar da kwallar bakin ciki ta ke fadin

“Ni Zee? Ni ka yiwa wannan cin fuska ka na almajiri mai gadin gidan mu? Allah ya isa! Abin da ka ke min Allah ya ma ka! Mugu azzalumi! Allah ya isa! Kai ne kare! Azzalumin! You will pay for this wallahi you will pay for this!”

Usman na murmushin jindadi da gamsuwar halin da ya sa Zainab ya sa kai ya fita ya bar Zainab zube ta na kuka. Kukan na ta biyu ne, na tsanar Usman da kuma haushin kan ta da har ta bari kaskantacce kamar Usman ya rungume ta, sannan ya kara mata da zagi tare da bakar magana, har ya kira ta karya!

Ta na cikin wannan tunanin ta ji alamar an bude assabarin daki an shigo, ba tare da ta daga kai ta ga wanda ya shigo ba ta ce

“Na tsane ka! Kada ka sake kai hannun ka jiki na domin kai ba ma ka kai darajar kare da birin ba! Wallahi da na hada jiki da kai gwara na hada da dabba….”

Jin shiru ba a tanka mata ba ya sa ta daga Ido ta ga wanda ya shigo, Nan ta yi Ido biyu da kyakkywar budurwa fara sol, wacce dudu ba ta wuce shekara goma sha biyar ba, hannun ta dauke da kwaryar nono, kamar yanda Zainab ta bude baki ta na duban ta, haka ita ma ta ke kallan Zainab cike da mamaki musammam da Zainab ta tashi tsaye da kyar, yarinyar ta ga tsayi da dirin Zainab, cikin ran ta fadi ta ce ‘Babu shakka dole Shehu yayi duk abin da aka ce yayi akan Kadon Nan, ciki kuwa har da daukan ta da yayi a bainar jama’a’

Ta ji labarin kyaun fata da ido da Allah ya yiwa Zainab, amma ba ta taba tunanin Zainab din haka ta ke ba. Kumatunta yayi jajur sanadiyar kalaman da Zainab ke fadi tsabagen nauyin maganar, Abu daya ya mata dadi shi ne , wato kenan akwai kiyayya ta gaske tsakanin masoyin na ta da Kadon sa, ko ba komai wannan zai kara ba ta damar zama matar shi…..

“Wacece ke? Ki taimake ni na tsira daga hannun wannan azzalumin almajirin…!”

Maganar Zainab ya dawo da ita hayyacin ta, Har ta budi baki za ta bata amsa da ta san wanda ta ke magana akai kuwa? Sai ta tuna gargadin Shehu na kada su sake su nunawa matar shi suna jin hausa bare su mata magana da shi. Dan haka kawai sai ta aje kwaryar hannun ta ta juya ta fita ta na ji Zainab na ce mata dan Allah ta tsaya.

Jim kadan ta kara dawowa tare da wata kwaryar mai dauke da kwan zabi, Nan ma Zainab ta sake kokarin yi mata magana, yarinya ta nuna kamar ba ta gane abin da Zainab ke fadi ba, ta aje kwarya ta fita. Haka ta na kai kawo sai da ta aje kwarya har biyar, na naman zabi, sai ruwa, sai kuma ‘yayan itatuwa.

Jin shiru ba ta sake shigowa ba ya sa Zainab tashi cikin dingishi, dan kuwa kamar yanda marar ta ta cika da fitsari haka hanjin ta ya cika da tutu, gashi gaba daya jikin ta ciwo ya ke mata ba ta daburin da ya wuce ta sami ruwan dumi ta yi wanka. Ta na tafiya da kyar ta fito waje yayinda ta ke ware idanu cikin fatan Allah ya sa Usman ba ya nan dan kuwa sam ba ta kaunar sake ganin shi. Ganin fitowar ta mata da yara kowa ya bar abin da ya ke ya na kallan ta. Cikin dauriya Zainab ta ce da su

“Ina ne toilet please?”

Kallan ta su ka tsaya suna yi babu mahalukin da ya san abin da ta ke nufi da “toilet” ganin haka Zainab ta kara da

“Mtswww na manta da jahilai na ke magana! Toh ina ne bandaki!”

Babu wanda ya tanka mata, hakan ya sa Zainab komawa bukkar Shehu, ta dauko butar da ta gani aje ciki ta ci sa’a akwai ruwa, da ta fito ta tarar suna nan dai tsaye kamar masu jiran tsammani, Zainab na mai musu alama da butar ta kara fadin

“Bandaki….wanka…ina zan yi?”
Duka su ka sa mata dariya, iya kulewa Zainab ta yi, ta na shirin juyawa ta koma daki sai ga Bello ya shigo da sallamar sa, ganin shi Zainab na mai yi masa alamar wanka da hannun ta ce

“Wanka, ina zan yi?”

Bello ya mata nuni da wani fili da ke zagaye da kara can gefe, ganin yanda Zainab ta zare idanu ta na kallan wajan shi kan shi Bello sai da dariya ta kusa subuce masa, ga tausayin ta da ya ke ji.

Ta na mai dawo da hankalin ta ga Bello ta sake fadin

“Oh my God! Yanzu fisabilillahi wancan zagayen shi ne toilet din ku? Ni Zee ni ce zan yi wanka cikin zagayen kara?”

Shi ma Bello tsayawa yayi ya na kallan ta kamar sauran yan gidan. Hakan ya sa Zainab juyawa ta nufi bandakin ta na fadin

“Na manta duka sokwaye ne a dajin nan! Ace rasa mai jin hausa sai wannan azzalumin! Kai wannan masifa da me ta yi takama! Bari dai na je na gani ko zan iya wanka, Duk Daddy da Ammy su su ka ja min wannan masifa! You will not get away with this! Wallahi you will not bari na tafi gida!”

Cikin tashin hankali da tsoran dattin da kazantar da za ta je ta tadda ciki ta yi adduar shiga bandaki ta kusa kai. Wayam ta gani, kasa ne shimfide a filin Allah, sai dan zarni da ke tashi sanadiyar rana da ya daki kasar, sam babu ko da masai ta tsugunno bare na tangaran da Zainab ta saba hawa, gashi a zahirin gaske a matse ta ke. Har za ta koma ta sake tambayar su ko dai sun yi kuskure ne ba su gane abin da ta ke nufi ba, idanun ta ya sauka kan wani dan roba mai dauke da sosan waya na wanka, ta tabbatar bandakin ne, kila sun bambamta shi da na ba haya ne.

Cike da kyamkayami ta sami gefe ta yi fitsarin cikin dabara ba tare da ta tsugunna ba, hakan ya ba ta damar ruke tutun da matse ta, Da niyar neman wajan yin tutun da wanka bayan ta idar da sallah. Da ta gama ta dauraye kafafun ta da ruwa sannan ta fito daga bandakin tana kakkabe kakkabe yayinda ta ke jin wani iri a jikin ta tsabagen kyamkayami da tashin hankali.

Har ta yi alwala ba su dena kallan ta ba, ta na idarwa ta yi sauri ta shiga ciki hannun ta dauke da butar ta ke fadin

“Mayu kurwa ta kul sai dai ku ci kan ku!”

Dankwalin ta ta shimfida kan ledar dakin, ba tare da ta tambayi ina ne gabas ba dan ta san ma babu mai amsa mata matukar ba Usman ba ta tayar da Sallah daga zaune, ta rama Asuba sannan ta gabatar da azahar. Ta idar ta na tunanin wanda za ta tambaya ina ne bayan gidan da za ta kasayar da tutun da ke cikin ta, ji ta ke tamkar zawo ne ke shirin kama ta, gashi Rugar kaf babu wanda ke amsa mata in ban da Usman.

*****
Can birnin Kano kuwa tun washagarin tafiyar su Usman labari ya iski Ammy bayan ta bayar da abinci a kai masa. Ta yi mamakin dalilin tafiyar na sa ba sallama, amma ba ta kawo komai cikin ran ta ba. Hankalin ta be fara tashi ba har bayan da ta kira Zainab ba ta dauka ba, sai ma sakon txt da ta tura mata, ta yi tunanin rashin da’ar Zainab ne ya tashi kila Falmat ta sanar mata da zuwa Usman. Kiran ta da aka yi daga makaranta aka tabbatar mata da rashin ganin Zainab a dakin jarabawa ne ya tada hankalin Ammy, musammam da ta lissafa tafiyar Usman da kuma ranar karshe da aka ce an ga Zainab a makaranta, sai ga Ammy ta na kuka wiwi, haka ma Falmat wacce ita ce ta kira Anty Sauda ta fada mata halin da ake ciki. Sai da ta tabbatar mijin ta ya raba hotunan Zainab bariki bariki, check point na kowani hanya, haka kuma aka fara kokarin bincike ta hanyar kididdigar wayar salulun Zainab, sannan ta hawo jirgi ta tawo garin Kano.

Fada sosai ta rufe Ammy da shi fadi ta ke
“Kukan me ki ke Aleesha? Ba abinda ki ke so ba kenan? Kun cuci yarinya kun lalata mata rayuwa! Ga irin ta nan ai! Gashi na dai za ki yi biyu babu cifar gafiyar baidu! Shi mijin na ki dama babu shi, diyar ta ki ma Allah kadai ya san halin da ta ke ciki a raye ko a mace!”

“Innalillahi wainnailaihi rajiun! Dan Allah Hajja Sauda ki dena fadin haka, ke ma kin san uwa ba za ta cutar da diyar ta da gangan ba! Oh ni Aleesha Yakura ko a ina ki ke? Ya Allah ka kare min Yakura! Kai amma yaran nan be yi halacci ba! Be Kuma yiwa Malam adalci ba! Be min adalci ba!”

Cewar Ammy cikin kuka. Anty Sauda wacce ta dau zafi matuka ta kara da cewa

“Ku Kuma fa? Kun mata adalci ne? Gashi kun jawo ya dakile mata karatun ta dan wallahi ko yanzu aka ga Yakura kun gama cutar da ita, she missed two exams, talk more of halin da ta ke ciki, kai Aleesha ba ku yiwa yarinyar nan adalci ba!”

“Innalillahi wainnailaihi rajiun!”

Cewar Ammy yayin da maganar Anty Sauda ke dada rura zuciyar ta. Wayar Anty Sauda ne yayi kara, ta yi saurin dagawa ta kara a kunnan ta ganin mijin ta ne mai kiran wayar. Nan ya sheda mata cewar sojojin da ke check point sun tabbatar da wucewar Yakura ranar da ta baro Yola zuwa Kano, haka kuma ta sake biyo hanyar a washagarin ranar a karo na biyu, Amma kada su damu in Sha Allah su na kan yin bincike.

Bayan ta aje wayar ne Anty Sauda ke fada ma Ammy halin da ake ciki. Ammy na mai daga hannu sama ta ce

“Ya Allah ba dan halin mu, Allah ka bayyana mana Yakura! Ba a ce an gan ta tare da Usman din ba?”

“Cikin motar haya wai zai san ko tare da wani ta ke tafe? Dama dai kuna da hotan almajirin ne da da sauki….”

Anty Sauda ta amsa mata ta na mai tabe baki cikin jimami.

“Yanayin shigar shi fa? Ai shigar sa daban ta ke da na mutane? Kai ta ya ma aka yi Yakura ta yarda ta bishi? Anya kuwa ba asiri ya mata ba kuwa?”

Cewar Ammy ta na sharar hawaye.

Anty Sauda ta amsa da

“Amen Ashe dai kuna kaunar ta kuka cuce ta”

Back to top button