Hausa NovelsNoor Al Hayat Hausa Novel

Noor Al Hayat 44

Sponsored Links

Silence din kusan 3 minutes ne ya biyo baya a parlorn, a hankali Khaleel ya dago kansa yana kallon khadijah da ta hade kanta da gwiwa, har ransa yake jin shesshekar kukanta, gashi ya kasa cewa komai, he is just lost of words, jinginar da kan sa yyi da kujera na kusan minti biyu kafin ya tashi a hankali ya isa gabanta ya duka ya dago kanta yana kallon idanuwanta da suka yi jajir, ta yi saurin sauke idonta daga kallon nasa kwayar idon da su ma suka sauya kamanninsu xuwa ja wasu sabbin hawayen na sakko mata, har lkcn Khaleel ya kasa cewa komai sai kallonta yake, bayan wasu dakiku abinda ya fito bakinsa cikin xaxxakan muryarsa shine “Forget about sudais, he did what he did for the sake of Allah, eraze him of ur mind”

Da sauri khadijah ta dago tana kallonsa, ya mike ya koma kujerar da yake xaune yace “Yeah, ki mance da kin ma taba sanin sa a rayuwar ki, I mean that sudais…” Khadijah dake ta kallonsa ko kiftawa babu tayi karfin halin cewa “Ko saboda me?” A takaice yace “Ohk, it seems biyansa abinda ya maki kike son yi kenan?? If that’s ur wish kema xaki iya taimakon marayu ai, I see no reason for good six years xa ki dinga tunani daya ba, beside he needs nothing from you, domin Allah yayi kuma Allah ne xai biyasa” Khadijah ta hade rai ta mike tana masa wani kallo tace “I regret telling you who i am, of all my story… part din sudais kadai ka ji da kyau halan? Shi kadai ka iya recalling? I just wasted the time I was suppose to use for sleeping” Daga haka ta nufi daki ta bar masa parlorn tana share hawayen idonta, Khaleel ya bi ta da ido ko kiftawa babu, jinginar da kansa yyi da kujera ya lumshe ido a hankali, wani mugun tausayinta ne ke shigarta, Sudais? Abinda ya fadi kenan a xuciyarsa ya bude ido da sauri, can ya tabe baki ya mike, ya fi minti biyu a tsaye yana kallon agogon dake nuna karfe uku saura kafin ya nufi bedroom dinta, xaune ya ganta kasa ta hade kai da gwiwa, Aliyu ne kawai ya fado xuciyarsa… ya hade hakoransa yana imagination kala kala a xuciyarsa, can yyi wani murmushi ya karasa cikin dakin yana kallonta ya durkusa gabanta, da farko rasa abinda xai ce mata yyi, can a hankali yace “Am sorry Khadijah, you misinterpret what I meant, ur story…. It is just heartbreaking, it’s sad… you’ve past through a lot in life at a very tender age, but am happy you proved to be a strong lady, strong lady indeed….” Shiru yyi yana kallonta ko kiftawa babu har lkcn ta ki dago kanta, a hankali ya kai hannunsa ya dago ta suna hada ido ta rufe idon, murmushin sa mai kyau yyi yana kallonta, murya can kasa yace “Those cute boys….” Sai kuma yyi shiru, bayan wani lkci yace “You are going no where from UK, Aliyu ne xai bar maki UK ba ke xaki bar masa ba am giving you my words, kina nan har ki gama karatun ki” ta bude idonta a hankali tace “Ae ya riga yasan makarantar, he will surely keep on looking for me” hawaye ne ya cika idonta cikin sanyin murya tace “Ni ban san me xan masa ba yake nema na” murmushi Khaleel yyi yace “Xai daina neman ki soon” Tana son kallonsa amma idanuwansa are not encouraging, ya lura da haka sai ta basa dariya ya mike yace “Alright then, life moves on, ki kwantar da hankalin ki babu wanda ya isa ya hana ki walwala a kasar nan am assuring you, ki tashi kiyi wanka sai kiyi sllh if you wish and then go to bed, the night is far gone” Khadijah dake wasa da fingers dinta tace “But ina son xan je in ga su Umma…” Yace “When?” A hankali tace “Ko gobe” shiru ya d’an yi kafin yace “Alryt then Allah ya kai mu” Ya fi minti uku a tsaye har sai da ta daga kai ta kallesa ta ga kallonta yake tayi saurin dauke kanta, yayi murmushi murya can kasa yace “Good nyt” kai ta gyada masa daga haka ya juya ya fita duk jikinsa a sanyaye, she is really a strong lady, yana fita ya kulle mata kofar, haka kawai khadijah taji ta samu relieve sosai don kusan ji tayi babu abinda ke damunta a ranta kuma, tashi tayi a hankali tayi yanda Khaleel ya ce mata, sai kusan karfe uku da rabi bacci me nauyi ya dauketa.

Tun da ya fito daki Kanwar Abbansa Hajiya Mariya ke bin sa da kallo, kitchen ya shiga ya fito ya sake shiga ya fito kamar xai koma daki sai kuma ya sake shiga kitchen din sai gashi ya kara fitowa Hajiya Mariya tace “Aliyu” juyawa yyi da sauri yana kallon direction din da take don bai ma san tana wajen ba, har ya iso inda take kallonsa take, ya xauna gefen kujera yace “Na’am mum” da damuwa tace “Aliyu what’s wrong with you pls, meye matsalar ka dubi yanda ka lalace, abun har ya kai ya kawo ka fara behaving kamar mara hankali, yanxu meye ma’anar shiga da ficen da kake a kitchen kamar wanda ya xauce” k’asa kallonta yyi ya sunkuyar da kansa, wanda hakan yasa jikinta yyi mugun sanyi, tasowa tayi ta dawo kusa da shi tace “Gaya min abinda ke damun ka Aliyu, you Neva knw if I can be of help, ko baka dauke ni kamar Anty fatima bane” Hawayen da ta gani idonsa ya kara daga mata hankali duk ta rikice tace “Subhanallahi, Aliyu, why the tears, don girman Allah ka gaya min meye ya faru, or have you gone wrong somewhere? Tel me son..” damuwa ce karara dauke fuskarta, ya girgixa kai yace “Just keep on praying for me mum, and… I will be going to Nigeria tomorrow, amma baxan jima ba xan dawo” daga haka ya mike ya bar ta gun xaune ta bi sa da kallo baki bude, tashi tayi ta wuce dakinta ta dau waya ta shiga kiran Mumy, ba a dau lkci ba ta daga bayan sun gaisa da damuwa tace “Anty fatima ni dai ko xa ki kira Aliyu ki ji me ke faruwa wllh gaba daya na rasa gane kansa yana cikin damuwa sosai, yanxu ma da na sa shi gaba sai ya fada min damuwarsa hawaye fa ya fara min kuma ya ki fada, I really don’t knw his problem, wllh ko abincin kirki bai ci sai kinga yanda ya rame…” Mumy ta tabe baki tace “Ina ga ke ce baki taba lura ba sai wannan xuwan da yyi maki, amma Aliyu ai ko da yaushe cikin damuwa xa ki gansa, ni na saba ma ganinsa a hakan, ni dai bani da xurfin ciki haka ma mahaifinsa so I don’t knw… Shi ya sani, na sha ce masa idan ma wani laifin ya aikata ma Allah yayi ta istigifari, or may be ya ji labarin auren da Abbansa ke shirin masa ne shi yasa hankalinsa ya kara tashi” da mamaki Hajiya Mariya tace “Aure kuma?? Yaushe?” Mumy tace “Yanxu ma shirye shiryen da ake ta yi kenan, idan ya dawo sai ya dau matar su yi ta yawon da yake yi tare, amma kar ki gaya ma sa, shi yasa ma yayan ki bai gaya maki ba, just let him… Kila idan aka yi auren xai dawo hankalinsa” Hajiya Mariya tace “Toh ai ya ma ce min gobe xai tafi Nigeria” Mumy tace “Toh dai dai kenan goben juma’ah dama xa a daura auren ke dai kar ki ma ce masa komai, sai ya xo muna jiransa” jikin Hajiya Mariya yyi sanyi sosai don har ga Allah bata ji dadin jin hakan ba duk da ita ma rashin aurensa na damunta amma aure without his knowledge kuma?? Sallama mumy tayi mata ta katse wayar.Tun da Khadijah ta fito rike da karamar jakarta daga cikin apartment dinta khaleel dake tsaye ya rungume hannunsa ke kallonta cikin bakin glass din idonsa kuma saboda ita ya sa glass din, abaya baki ne jikinta da mayafinsa, sosai kayan ya haska ta daga nisa kamar balarabiya, tana isowa gun da yake ya dauke kansa ya fara tafiya xuwa waje, taxi ya tsayar masu don motarsa na gun wani abokinsa, ya bude mata ta shiga sannan shi ma ya shiga, sai da suka dau hanya yace “Have you call home? I mean kin gaya masu kina tahowa?” Girgixa masa kai tayi, yace “Why?” Kamar xata yi kuka tace “Umma xata iya cewa kar in taho” khaleel ya hade rai yace “Toh tunda haka ne meye amfanin xuwan? Kawai ki fasa, da kin gaya min haka tun a gida ma ni baxan fito ba” Hararansa tayi daga sama har Kasa bata ce komai ba, ya xaro ido daga cikin glass dinsa, kamar me counting words din yace “Did… you… just… eye me?” ta sake juyawa ta maka masa wani hararan tace “You check for your self, kuma ni ban ce dole ka rakani airport ba, xaka iya komawa gida” lkci daya ya xare glass din idonsa suka hada ido, tayi saurin boye fuskarta a kafarta kamar xata yi kuka tace “Bana so” murmushi yyi bai ce komai ba ya mayar da glass din ya shiga danna wayarsa, har suka iso airport bbu wanda yace komai cikinsu sai dai lkci lkci yake satan kallonta, Khadijah ta bude cab din ta fita shima ya fita ta daya side din ya ba mai taxin kudinsa, kallon agogo yayi kafin su shiga airport din, khaleel ne yyi mata komai a airport din tana xaune ya dawo ya xauna gefenta ya mika mata ticket, xaro ido tayi tace “Noo, give me ur account details pls” wani kallo yyi mata yace “Toh Hajiya” daga haka ya dauke kansa, jikinta yyi sanyi bata iya tace komai ba, Wayarta ta ciro a jaka xata tura ma Vanessa text don bata ce mata xata yi tafiya ba, kamar ance ta kalli side dinta ta ga Aliyu xaune though nesa da su yana danna wayarsa, gabanta yyi mugun faduwa…. Lkci daya kuma babu abinda ya fado mata rai sai yan biyunta kamanninsu ya baci ne kawai, xuciyarta ya dinga bugawa ta dauke kai da sauri tana addu’ar Allah yasa ba jirgi daya xa su yi boarding ba, kallonta Khaleel yyi ganin yanda ta matso kusa da shi ba tare da tasan tayi hakan ba, suna hada ido tayi saurin sunkuyar da kai trying to control her self, da wani expression khaleel dake kallonta yace “What?” Ta girgixa masa kai da sauri kuma har lkcn ta ki dago kanta, bata kuma matsa daga kusa da shi ba, duk iya kallon khaleel a wajajen bai ga komai ba sai turawa da few bakaken fata dake wajen, a hankali yace “Khadijah” ta dago da sauri tana kallonsa, yace “What happened?” Girgixa masa kai tayi da sauri, a tsorace tace “I don’t knw why I am afraid” ya d’an bude ido yace “Afraid? Of what” ta buda masa hannu kamar xata yi kuka, shiru yyi na few seconds, a hankali taji yace “Ohk shud I accompany you?” Ta dago tana kallonsa, dogon hancinsa da bakinsa kadai take gani banda idanuwansa, samun kanta tayi da gyada masa kai, yace “Ohk then” mikewa yyi ta bi sa da kallo tana boye fuskarta da mayafin jikinta ta saci kallon direction din Aliyu, yanxu ba danna waya yake ba ya dai jinginar da kansa da kujera yana kallon yaran turawa dake tare da uwarsu suna tafiya, da sauri ta dauke kanta. Har suka shiga jirgi Khadijah bata daina shisshge ma Khaleel ba, tayi sa’a kuma seat dinsa kusa da ita, suna keta haxo ta dinga bin jirgin da kallo cikin dubara amma ba ta ga alamar Aliyu ba, bacci ne ya dauketa daga karshe sai dai ta rufe rabin fuskarta da veil dinta, khaleel ya dinga kallonta, ya rasa gane irin tausayin da yake ma khadijah, ya san har ransa kuma he don’t knw why, a hankali ta jinginar da kanta a shoulder dinsa, jawota yyi jikinsa ya lumshe idanuwansa, bayan awanni da dama Khadijah ta bude idonta a hankali, kallonsa tayi ta janye jikinta da sauri daga nasa, ya buda manyan idanuwansa yace “Are you hungry?” Ta girgixa masa kai, kamar ance ta kalli gefensu taga Aliyu xaune ya makala earpiece a kunnensa idonsa a lumshe, boye fuskarta tayi jikin khaleel jikinta na bari, khaleel ya riketa da mamaki yace “Are you okay?” Girgixa masa kai tayi a tsorace, bin jirgin ya dinga yi da kallo shi ma, lkci daya idonsa ya sauka kan Aliyu, haka kawai yaji gabansa ya fadi… Ya dinga kallonsa ko kiftawa babu don ko ba a fada ba kawai ya ga shureim da sudais a tattare da shi, lkci daya ya dauke kai, Khadijah da ta rufe fuska ta ki yarda ta kallesa, sauran journey din gaba daya daga ita har khaleel they where uncomfortable, khaleel ya kalli direction din Aliyu ya fi a kirga, gwara Khadijah tayi kokarin ganin bata sake kallon direction din ba, few hours kafin jirginsu ya sauka Abuja Khadijah ta d’an saci kallon gefensu dai dai lkcn da Aliyu ya juyo, hada ido suka yi sai dai fuskarta dama a rufe yake, ji tayi kamar an soka mata mashi a xuciya tayi saurin kauda kanta, shi ko yana ta kallonta bayan wani lkci ya dauke kansa. Har suka yi set down Khadijah ko da wasa ba ta juya kanta ba. Khaleel ya jira mutane suka fara sauka kafin ya mike, ita ma ta tashi da sauri, kamar xata shige jikinsa haka ta dinga bin sa har suka sauka matakalan jirgin, tsaye ta hango Aliyu nesa da jirgin yana kallonsu bayan shi ya sauka, taji kafafuwarta sun kasa daukar ta don tasan kila ya ganeta ne, har suka sauka Khaleel bai gansa ba don wani abokin sa bature ya dauke hankalinsa suna gaisawa, Aliyu dake ta kallon idanuwan khadijah da su kadai yake iya gani ya nufo ta, dai dai gabanta ya tsaya lkci daya ya fixge veil din fuskarta yana kallonta, rikicewa tayi, khaleel ya juya da sauri, ganin abinda Aliyu yyi ya cakumosa cikin tsawa yana masa wani mugun kallo yace “How dare you?”

Daga sama har kasa Aliyu ke kallon Khaleel da ya ki sake sa, Aliyu ya dake yace “Who are you?” khadijah na ganin haka a rikice ta ajiye jakar hannunta tace “Noo plss Dr ka kyale shi…” Khaleel na kallon kwayar idon Aliyu strictly yace “Stay away from her or else you regret it….” Yana fadin haka ya sakesa, Aliyu yyi wani murmushi yace “And who are you to tell me that? Her boyfriend? Husband or??” Juyowa khaleel yyi a mugun fusace ya sake cakumosa Aliyu ma ya cakumesa yana mayar masa da irin kallon da yake masa, khaleel yace “Both! Husband and boyfriend” dariya Aliyu yyi yace “You are very very stupid, idan ma mijinta ne kai ka shirya rabuwa da ita domin kuwa she is not meant for you” Khadijah na ganin abun ya kai haka ta shiga tsakaninsu da sauri cikin kuka tace “Wayyo na shiga uku, don Allah don annabi ku rufa min asiri ku yi hakuri” tayi facing din khaleel dake hade fist dinsa yana ma Aliyu wani irin kallo ta rikesa hawaye na sakko mata tace “Plss am begging you ka kyale sa don Allah Dr” lkci daya khaleel ya sake Aliyu ya kama hannunta ya dau jakarta, Aliyu ya fiddo complimentary card dinsa a aljihu ya saka a na Khaleel yana kallon kwayar idonsa yace “I will be waiting for ur call young man” still khaleel yyi kamar xai cire ya jefar sai kuma ya bari ya juya kamar xai tashi sama ya bar wajen Khadijah ta dinga bin sa xuciyarta na bugawa, Aliyu ya bi su da kallo yana murmushi a hankali yace “I will surely get you soon Iman, not when I have set my eyes on you” ta waigo ta kallesa tayi saurin dauke kai, har suka shiga cab Khadijah waigawa take taga ko ya biyo su, sai dai ta kasa ganewa don mutane ne da yawa ko ganinsa bata sake yi ba, duk ta kasa samun nutsuwa, tana kallon Khaleel da har sannan fuskarsa ke a daure kamar xata yi kuka tace “Plss Dr kar ka sake kulasa” Kallonta khaleel yyi a fusace xuciyarsa na heaving yace “That’s idan bai shiga rayuwar ki ba, Billah xan iya yi masa komai, I don’t care… Ina da wanda ya tsaya min a kasar nan, look… my father….” Sai kuma yyi shiru, lkci daya idanuwansa suka canxa kamanni, Khadijah jikinta yyi sanyi sosai, muryar khaleel ne ya dawo da ita tunanin da ta tafi, cikin sanyayyan muryarsa yace “Don’t forget this is Abuja, ina xa mu? Thinking Kaduna kika ce min Umma take” A hankali tace “Dole sai mun bi train xuwa Kaduna” yace “Why not flight” ta hararesa tace “Bayan mun baro airport din, kawai kaje xaka tara mana crowd a airport ko meye na kulasa” bai ce komai ba sai kallon tagar taxin yake, khadijah ta sanar ma mai taxin train station xai kai su, Tsaki taji khaleel ya ja yace “Seriously It’s being long aka ba ta min rai haka… Da ba don airport bane we ought have teach each other a lesson da guy din nan, I don’t even care about d securities there…” Khadijah dai sai kallonsa take ganin how serious he was, Juyowa yyi ya kalleta tayi saurin dauke kanta, murya can kasa yace “It’s because of you khadijah, don ke na kyalesa da mun yi karamin exercise a wajen nan” ta tabe baki tace “Ni dai babu ruwana” yayi murmushi da ya bayyana dimples dinsa yace “Billah ke kuwa ke da ruwa baby” kallonsa tayi da sauri, ya tsuke fuska kamar ba shi ya fada ba ya fiddo wayarsa yana dannawa, tayi murmushi tana ci gaba da kallon waje, suna isa station suka samu jirgin kasa mai xuwa Kaduna, Khaleel ya yankar masu ticket, sai da jirgin ya tashi khadijah ta kallesa tace “Are you a Nigerian” kallonta yyi, ta sauke idonta, yyi murmushi yace “Sure, A Nigerian… From Kaduna also, why do you ask, ko ban yi kama da ku ba ne” bata ce komai ba, shima bai ce komai ba, bayan few hours suka isa station din train dake kaduna, Napep suka dauka da xai kai su har gida, Yace “Do I have to accompany you har kofar gida” Khadijah ta kallesa sannan ta sa mai Napep ya tsaya tace “Sauka toh ka hau wani adai daitan ka tafi gidan ku” wara ido yyi yace “Like serious??” Ta langwabar da kai tace “Sure” murmushi yyi ya sauka yace “Ohk then” tace “Yeah, thanks” daga haka ta sa mai Napep din ya wuce khaleel ya bi su da kallo. Khadijah na isa gida ta sauka ta bude Jakarta, tunawa tayi ba kudi wajenta ta basa hakuri tace bari ta amso a ciki sannan ta shiga gida, sudais da shureim ne parlor suna kallon cartoon, suna ganinta suka mike a guje suka yi kanta suna mata oyoyo ta rungumesu gaba daya cike da murnan ganin yan biyunta, Umma dake kitchen ta fito da mamaki tana kallonta, da kyar ta yakice yaran a jikinta ta nufi Umma ta rungumeta tace “Ummata na dawo” Umma na kallonta tace “What happened Khadijah??” Ta marairaice tace “Umma ina missing din ku ne na taho fa” Umma ta hade rai tace “Kina da hankali kuwa, kamar warce xata taho daga kano, yaushe kika koma da har xaki taho yanxu” shiru ta yi bata ce komai ba, Umma ta saki baki tana kallonta a mamaki, juyawa khadijah tayi ta nufi jakar Umma dake ajiye parlorn ta bude ta fiddo kudi tace “Umma bari in kai ma mai adai daita” daga haka ta fita ta kai ma sa kudin sa twins dinta na rike da ita, suna dawowa parlor duk suka haye kanta Shureim yace “Anty ina wannan uncle din nan dake UK, did he tell you to greet us?” Khadijah tayi murmushi tace “Sure sweetheart” Sudais yace “Anty is he also from Nigeria, I like him” Umma dake kallonsu tace “Wani uncle suke fadi?” Khadijah ta saci kallonta tace “Neighbor dina ne fa Umma” Umma tace “Ba mace bace kwanaki da muka je?” Khadijah tace “Ayya, Nancy ai ta tashi” Shiru Umma tayi kafin tace “Toh dai a kula, Allah ya ci gaba da tsare ku” A hankali khadijah tace “Ameen” Umma tace “Toh don me wai baxa ku xauna tare da Vanessa ba?” Khadijah tace “Umma am nt comfortable a gidanta ne” Umma tace “You have no choice, bana son xaman ki gida daya da namiji” da sauri khadijah ta kalleta, murmushi tayi tace “Umma he is a Nigerian, kuma I think bahaushe” Umma tace “So?” Shiru Khadijah tayi, Dai dai nan wayar dake jakarta ya fara ring ta bude jaka da sauri ta fiddo tunawa da tayi wayar khaleel ne, shiru ta yi tana kallon number kafin ta daga, muryarsa taji yace “Are you home?” Ta saci kallon Umma Kafin ta mike tace “Uhn” daga haka ta wuce daki yaranta suka bi bayanta Umma ta bi su da kallo.

Flight Aliyu ya bi ya taho kaduna, Ji yayi gaba daya ba wani sauran damuwa a tare da shi, lkci lkci sai yyi murmushi, har ya isa gida a taxi tunanin Khadijah yake, he is just happy seeing her today, bayan ya sauka taxi mamakin me ake yi a gidan ya dinga yi ganin mutane da manyan motoci har su Usman da Sanusi shadda ce sabuwa jikinsu, suna ganinsa suka washe baki suna masa sannu da dawowa, ya amsa gaisuwarsu ya entrance din gidan, ganin takalma da yawa alamar mutane ne sosai parlorn ya xaga ta baya, iklima ce bakin tap a durkushe tana kwarara amai, ya karasa yana kallonta ganin uban kunshin da aka mata ga kitso an yaryara mata a kai, yace “Baki da lafiya ne?” Jin muryarsa ta dago da sauri, lkci daya ta mayar da kanta ta sunkuyar, tana maida numfashi da kyar tace “Sannu da dawowa yaya Aliyu” bai damu da ya amsa ba yace “Me ake yi a gidan nan?” Shiru tayi da farko kafin tace “Aurenmu” Few seconds yyi amfani da wajen apprehending abinda ta fada, cike da confusion yace “Aurenmu? Aurenmu da wa?” Still bata kallesa ba tace “Ni da kai” bude baki yyi yana kallonta dai dai fitowar Anty khadijah tayi wani shegen haske ta xama katuwar gaske, tana ganinsa ta saki guda tace “Saukar yaushe ango?” Aliyu na xaro ido yace “Anty ban gane ba, ango kuma?” Anty khadijah na taunar cingam da ya cika waje da kara tace “Tafi Anty fati na daki xata maka bayani yanda xaka gane my son” daga haka ta nufi ‘yar ta tace “Ki taso mu je, mai make up din ta gaji da jira” janta tayi suka Wuce ciki suka bar Aliyu tsaye baki bude, har lkcn shi dai bai fahimci komai ba. Wucewa ciki yyi direct ya tafi sama Dakin Mumy ba tare da ya kula da mutanen dake parlor ba, ita da frnds dinta sai mahaifiyar Abbansa da suke kira da yaya ne xaune dakin, yyi hankalin gaishesu kafin yace “Mumy I don’t get what’s happening in this house” Yaya tace “Bikin ku ake yi da ‘yar uwar ka” Aliyu ya yo waje da ido yace “Wace yar uwar tawa?” Yaya tace “Iklima, Allah bai yi da Hanan ba” Wani kallo Aliyu ya dinga yi mata kafin yace “Allah ya kiyaye, wace iklimar? Iklima da ta gagari kowa gidan nan xa a makala min, No Mumy I have never failed you but… No mum me yasa xaki min xabin da xai cutar da ni, mumy kema kinsan iklima ta fi karfina, Mumy ki rufa min asiri…” Tsawa Mumy tayi masa ta mike tana masa wani mugun kallo tace “Get out Abuturrab, idan an kai ma iklima gidan ka kayi gunduwa gunduwa da namanta ko kuma ka koro mana ita, fita nace” Juyawa Aliyu yyi ya fice daga dakin, Yaya tace “Fatima, da gaske yarinyar ta gagari kowa? Ni dai an san ba saninta nayi ba, kar ku cutar min jika” Mumy ta hade rai tace “Yaya yar yar uwata ce uwa daya uba daya fa” tana fadin haka ta fita dakin, kawayenta suka bi ta da kallo.

Washegari da yamma khadijah na xaune parlor tare Umma da Nanny dake yankan alaiyahu, reading material dinta ne hannunta tana dubawa, Umma tace “Wai da wa su sudais ke waya haka ne tun daxu Khadijah?” Khadijah ta dago kanta tana kallonta a hankli tace “Umma wani ne” Umma tace “A ina kika san sa? Ko in ce a ina suka san sa” Murmushi kawai khadijah tayi bata dai ce komai ba, jin little sudais na kiranta ta juya tana kallon direction din dakin sai ga shi tare da d’an uwansa, wayar hannunsa ya mika mata yace “Uncle yace we shud hand over the phone to you” Khadijah ta amshi wayar tana satan kallon Umma dake kallonsu ta mike ta wuce daki, rufe kofar dakin tayi ta xauna gefen gado ta kai wayar kunne tace “Yes? Ina ji” Yace “Yea I knw kina ji, can I come over to see d boys now?” Shiru Khadijah tayi tana kallon agogo kafin tace “Xan gaya ma Umma tukun” yace “Alryt then, I will be waiting for ur call” a hankali tace “Tohm” daga haka ya katse wayar, tunanin me xata ce ma Umma ta dinga yi kafin ta mike ta fita, xauna gefen kujera tayi murya can kasa tace “Umma someone is coming over now” Umma ta daga kai ta kalleta tace “Who?” Ta d’an turo baki tace “Wani ne” murmushi Umma tayi tace “Allah kawo sa” khadijah ta mike ta koma daki, text ta tura ma khaleel na address din unguwarsu da house number. Cikin minti talatin khaleel ya iso gidan, Khadijah ta sa Hijab ta fito daga dakinta ta shiga na umma tana kallonta tace “Umma yana waje” Umma tace “A wajen xa ki bar sa baxai shigo ba” murmushi kawai khadijah tayi ta fita, tun da ta fito gate take kallon motar da khaleel ya xo da shi har ta isa gun motar ta tsaya tana wasa da fingers dinta, bude motar yyi ya fito ya xaga ta inda take, farar gizna ne jikinsa sai walkiya yake da hula, wani kyau yyi na musamman ya dawo kamar balarabe cikin shigar hausawa, Ita dai bata taba ganinsa da irin shigar ba ta dauke kai daga kallonsa tace “Dama kana sa manyan kaya?” Ya d’an bude ido ya rungume hannunsa ya jingina da motar yace “Dama kina sa Hijab?” Dariya ya bata amma bata yi ba tace “Aa sai kananun kaya in yi sagging wandon” xaro ido khaleel yyi yana kallonta, tayi murmushi bata kalli direction din sa ba, Kallonta ya tsaya yi na few seconds kafin yace “Where are the boys?” Tace “Suna ciki” yace “Amma kin san ba wajen ki na xo ba dai koh” shiru ta yi trying her best not to look at him, can tayi murmushi tace “Alryt then” daga haka ta nufi gate, Wara ido yayi yace “Khadijah” sai da ta isa gate tace “Bari in turo maka su” yace “Wait…” Amma tuni ta shige gidan, murmushi yyi yana shafa beard dinsa, ba a dau lkci ba sai ga yaran sun fito suna ganinsa suka taho da gudu suka rungumesa ya daga su sama gaba daya happy seeing them, kai kana ganin yaran kasan su ma ba karamin farin cikin ganin khaleel suka yi ba, ya bude back seat din motar ya sa suka shiga sannan ya xaga ya shiga maxaunin driver, wayar sa ya dauka ya shiga kiran Khadijah, kin dauka tayi yayi murmushi ya tada motar ya bar layin da yaran. Tun da Aliyu ya dawo masallaci da asuba ya sa makulli dakinsa, shi dai ya kasa gaskata wai iklima aka aura masa, yarinyar da idan ta fita tun safe sai dare wani lkcn xata dawo gida, uwar kuma tace gidan kawunta take xuwa, yau idan ka ga wannan wayar hannun iklima to gobe wani daban xa ka gani, islamiyyar ta ki xuwa, bokon kuma anyi withdrawing, rike kansa yyi xuciyarsa na masa kunna, kwankwasa kofar dakinsa aka yi for the countless time, ko kallon direction din kofar bai yi ba, “Yaya nice baby ka bude plss” muryar da ya ji kenan, ya lumshe idanuwansa ya bude, mikewa yyi da kyar ya nufi kofar ya bude yana kallon Kanwar tasa, ta shigo ya rufe kofar, da damuwa tace “Yayanmu kayi hakuri, I don’t knw what came over Mumy, bn san me yasa tayi haka ba bayan ita da kanta kullum complain take a kan iklima… Her character is so obvious to everyone, kowa yasan abinda take but mumy tayi kamar bata sani ba ta hada ku….” Aliyu ya xauna gefen gado ya rike kansa, Baby tayi tagumi tana kallonsa, bayan kusan minti goma tace “Kayi hakuri yaya” ya dago da jajayen idanuwansa yana kallonta yace “Go make me a cup of coffee” Baby na fita daga dakin dai dai fitowar Anty khadijah da ke ta kai kawo kamar warce tayi ma sarki karya, barin da taga Aliyu ya bude ma Kanwar tasa kofa, xuwa yanxu gidan ya watse sai yan uwa na jini, bin baby tayi downstairs tace “Takwara me Aliyun yace maki?” Baby taki kallonta tace “Abu yace in kai ma sa” Anty khadijah dake ta bin ta tace “Me kenan?” Baby tace “Coffee” Anty khadijah tace “Atoh ni har na gaji da maganar bai ci komai ba tun daxu, yanxu abinda xa ayi kawai kiyi wucewar ki xan hada masa in ba matarsa ta kai ma sa, mutum ya sha hanya haka kuma ya makale daki tun jiya babu abinci” Baby tace “Anty amma ai baki san yanda yake son coffee dinsa ba, ni xan masa” Anty khadijah ta galla mata harara tace “Toh uwar iyayi, kin tashi gabana ko sai na mare ki, idan nayi masa kar ya sha” daga haka ta wuce kitchen baby ta bi ta da wani kallo, Anty khadijah na shiga kitchen ta tura kofar kitchen din ta rufe ta yi saurin ciro wani kulli a bra dinta, “Son da xai mata sai ya fi wanda yake ma uwarsa da kowa na duniya… In dai ya sha maganin nan” muryar gardin da ya bata maganin kenan ke kai kawo a kunnen Anty khadijah kamar yana kusa da ita, har wani rawa hannunta yake ta juye gaba daya a cup sannan ta debi coffee powder ta xuba a kai ta xuba ruwan xafi ta jefa kwayan sugar biyu, sama ta tafi da sauri ta shiga daki gun iklima dake kwance, Anty khadijah tace “Ni fa dadina dake shegen son jiki, daga d’an xaxxabi dubi yanda kika wani yi laushi kamar warce tayi watanni ba lafiya, a haka xa a kai ki gidan Aliyun gobe” Iklima da ta lullebe da bargo tace “Ni wallahi ki rabu da ni don ba ke ce ke jin abinda nake ji ba, duk kin bi kin dame ni tun daxu” Anty khadijah tace “To uwata sai ki rufe ni da duka ai, ni ki tashi ki kai ma Aliyun coffee” iklima ta xaro ido tace “kaji ta, Salon ya koro ni…. Mutumin da tun jiya yake daki” Anty khadijah tace “Toh don ubansa ba sai ya koro ki ba, kilan ma a can xa ki kwana ki tashi kina bata lkci…” Gun kayan kwalliyan Iklima na amarya Anty khadijah ta nufa ta dauko wani turare can kasa a karamin kwalba ta bude ta shashshafa mata a ko ina na jikinta, iklima da ke ta wani yatsine fuska ta koma ta kwanta tace “Mama wllh jiri nake gani, anya xan iya fita” hararata Anty khadijah tayi tace “Xan je in dauko maki shayin a dai don ki fita nan ki shiga dakinsa baxa ki ce min baxa ki iya ba” daga haka ta wuce kitchen ta dauko coffeen dake rufe a mug ta kawo ma iklima, da kyar ta tashi ta karba tana duddukawa ta fita dakin, a hankali ta tura kofar dakin Aliyu dake kwance ta shiga ta rufe Ta isa kusa da gadon ta ajiye mug din hannunta a kasa, bude ido Aliyu yyi jin yanda kamshi ya bade dakin suka hada ido da iklima, karasowa kusa da shi tayi tace “Yayanmu sannu da hanya ga coffee din na maka” Wani mugun kallo Aliyu ya dinga mata yace “Kina hauka ne xa ki shigo min daki” tace “Da daban xama matar ka ba ina shigowa ne” bude kofar dakin aka yi sai ga baby ta shigo sau daya ta kalli iklima ta harareta ta durkusa ta ajiye tray din hannunta tace “Ga abinci yaya mumy tace in dibar maka” daga haka ta bude warmer din abincin iklima ta yamutse fuska ta dauke kai da sauri, lkci daya aroma din abincin ya cika dakin, da tari ta fara, sai kuma ta toshe baki, da gudu ta mike kafin ta isa kofar bathroom ta wanke tiles din dakin da amai, kallonta Aliyu yake ko kiftawa babu ta dinga amai kamar xata shide, baby ma sai kallonta take, tashi yyi ya isa gabanta da wani expression yana kallon gaba daya jikinta, mikewa tayi bayan ta gama ta fada kan gado tana sauke numfashi ya koma kusa da ita yana kare mata kallo da kyau, squeezing fuskarsa yyi yace “What??” Lkci daya ya juya ya fice baby ta bi bayansa da sauri, Mumy na haurowa sama tare da Anty khadijah dake bata shawarar kawai gobe su Aliyu su wuce gidansu yau dai su kwana a gidan, ganin Aliyu Mumy ta daure fuska don tun daxu yaki fitowa har ita ta yi masa magana amma ya ki bude kofar, yana kallon mumy cikin wani yanayi yace “Mumy ita mai cikin xa ku ce kun aura min?” Kallonsa Mumy ta tsaya yi cikin rashin fahimta haka ma Anty khadijah, baby dake tsaye gun ta xaro ido tana kallonsa, Da mugun mamaki Mumy tace “Halan Aliyu ya fara xarewa ne ni Fatima?” Yace “Xarewa kuma Mumy wllh ciki ne da iklima, don’t forget my profession idan ma baku yarda ba yanxu sai a kira wani likitan, gashi can yanxu ma amai ta gama yi” Anty khadijah ta saki ta salati ta fashe da kuka tace “Aliyu, ita yar tawa xaka ma wannan gagarumin sharrin don a rufa ma asiri an aura mata kai? Ita iklimar ce ke da ciki?” Aliyu ya mata wani kallo yace “Sharri Anty? sai a tafi asibiti yanxu ai, ni dama nasan a day like this na nan xuwa very soon, ina ce har guest lodge na taba ganin iklima na same ki daki na gaya maki few years back, me kika ce min then? Cewa kika yi na tsaneta na sa mata ido, Duk yawon da take ta kai dare kin taba tsawata mata, of course no sai dai kice gidan kawunta taje, so it’s nt a thing to be surprise don iklima na dauke da ciki ynxu” tuni sauran yan biki dake gidan suka shiga fitowa corridor din, Mumy dai ta saki baki ta kasa cewa komai, Anty khadijah dake ta xufa tace “Tunda abun yar tone tone ne sai mu yi ta ai Aliyu, wato har kai kana da bakin da xaka bude ka kira ‘ya ta yar iska ka mance lkcn da kake tashan naka iskancin, ka mance irin yanda kayi ma yar mutane fyade a cikin gidan nan, wanda ta dalilinka ta bar gidan har yau bata dawo ba, duk ka xata ban sani ba koh???” Lkci daya komai na Aliyu yyi still ya tsaya kallonta ko kiftawa babu, Anty khadijah ta juya tana kallon mumy tace “khadijah dai da kika sani, yarinyar da kika dau aiki ta yi wucewarta ko sallama babu shekaru kusan shidda baya, ya fada maki abinda yyi mata ta bar gidan da bakin sa yau….” Aliyu ya lumshe idanuwansa da suka kada lkci daya ya ji kansa na sara masa, kallonsa mumy ta dinga yi kamar idonta xai fito haka kanninsa gaba daya da bak’in da suka fiffito, Anty khadijah na girgixa kugu tace “Ko baxa kayi bayanin ba in taya ka?” Bude ido yyi da kyar yana kallon Mumy.

Anty khadijah na kallon Aliyu da kyau tace “Ko baxa kayi bayanin ba in taya ka ne dakta?” Bude ido Aliyu yyi da kyar yana kallonta, lkci daya idanuwan Mumy suka kawo ruwa kana ganinta kasan ba karamin shock ta shiga ba, Aliyu ya isa gabanta ya duka kan gwiwowinsa cikin sanyin murya yace “Mumy…” Dakatar da shi tayi hawayen idonta na sakkowa tace “Irin tarbiyar da nayi maka kenan Aliyu…. Yanxu yar mutanen kayi ma haka?” Ya rufe fuskarsa jikin kafarta cikin rawar murya yace “That’s the greatest mistake of my life mum, shine abinda na kasa gaya maki shekaru shiddah kenan, mumy ba halina bane kema kin sani, ban san ya aka yi ba ranan, it look as if I was possessed, I ruin the little girl… Mumy I….” Kasa ci gaba yyi hawaye na sakko masa, Anty khadijah ta tabe baki tace “Lallai Abuturrab baka jin kunyar karya? abu ya faru ba sau daya ba ba sau biyu ba ka kirasa mistake? Tunda abun ba arxiki har ya kai ga ka fara yi ma ‘ya ta sharri to wllh nima baxan duba abinda ke tsakanina da mahaifiyar ka ba, gwara in tona maka asiri, idan ni baka ji kunyar toxarta ni da iklima ba to nima baxan ji kunyar ramawa ba a matsayin ka na d’an yayata” daga haka ta bar wajen ta shige daki… Aliyu ya bi ta da kallo, duk abun nan da take fada fa ba ji yake ba mamakinsa shine ya aka yi tasan abinda ya faru tsakaninsa da Khadijah bayan bata gida ranan, how is that? Fitowa Anty khadijah tayi daga dakin rike da iklima da ta sa ma Hijab suka sauka downstairs kamar xata tashi sama tana matsar kwalla tace “Da raina kayi ma yar cikina irin wnn sharrin koh Aliyu, duk matsayina gun uwarka baka gani ba saboda na rufa maka asiri da yawace yawacen da kake nace a aura maka ‘ya ta shine xaka mana wannan cin mutuncin ka saka min da sharri” gidan ta bari gaba daya tare da yar ta, Mumy ta juya ta koma dakinta a sanyaye, Aliyu ya kasa daga kai ya kalli kanninsa da sauran relatives dake wajen. Anty khadijah na fita da kafa suka karasa bakin titi da iklima, hankali tashe take tambayarta yaushe rabon da ta ga al’adarta, iklima ta turo baki tace “Oho nima ban sani ba” dundu ta kai mata tace “Kaji min shegiya wai baki sani ba, ni nake maki al’adar? To wllh sai dai ki daura ma ubanki hawan jini ba ni ba, mu je asibitin ai xa su mana bayani a can, in ma ya kama in kashe ni Wllh sai in kashe Ki a can din, tunda duk abinda nake maki bakya gani ni xaki ja ma abun kunya ni xaki kunyata a idon duniya” Ganin sun shiga Napep yasa Anty Khadijah tayi shiru sai girgixa kafa take tana Allah Allah ta ganta a asibiti har suka isa asibitin dai, iklima kam ko dar sai ma gyangyadi da take ta yi a napep din, suna shiga asibitin likita ya tabbatar ciki gare iklima, Anty khadijah ta daura hannu a ka tana xaro ido tace “Na shiga uku na lalace ni Khadijah, iklima yanxu ni xa ki ma haka, a ina kika je aka maki ciki, don na sake maki sai ki tona min asiri iklima? Ni xa ki kunyata?” Shi dai likitan kallonsu kawai yake, Anty khadijah ta share xufar dake keto mata ta hadiye yawu da kyar tace “Likita ko nawa kake bukata ka fada xan baka ka raba ta da wannan bala’in dake tare da ita ka rufa mana asiri” likitan yace “A’a ba ma haka a nan Hajiya ku yi hakuri, ku je wani asibitin…” Anty khadijah ta fashe da kuka a karo na farko tace “Haba bawan Allah, kai baka taimako ne, wllh dariya xa a mana ka rufa min asiri ina da makiya da yawa duniyar nan, ka ji tausayina ka taimaka mani” Likitan yace “Wato kin fi so kiji kunyar lahira a kan ta duniya kenan Hajiya?” Da sauri Anty khadijah tace “Eh wllh” sake baki yyi yana kallonta, can ya gyada kai yace “Gaskiya ne, toh Allah ya shirye ku, kuyi hakuri ku fita akwai patients da xan yi attending ma yanxu, mu ba ma aborting ciki a nan” tashi Anty khadijah tayi tana masa matsiyacin kallo tace “Yanda ka ki taimakona kai ma haka yar ka xata jajibo maka abun kunya ka rasa madafa in sha Allah, mara imani kawai…” daga haka ta ja Iklima kamar xata tashi sama suka fita, haka Anty khadijah suka dinga yawo hospitals tana neman inda xa a cire ma iklima ciki har dai ta samu wani da kyar, kudi ba na wasa ba ta bada aka yi aikin, unconsciously ta tafi da iklima gidan wata da suka hadu a kauyen da take yawan xuwa suka kulla abota suke kawance kamar xa su hadiye juna, kwanan matar uku gidansu Aliyu lkcn biki, jiya ta baro gidan bayan an gama komai ba rabon xa ayi komai a gabanta, Hajiya Laure sai kallon iklima dake kwance take da mamaki bayan Anty khadijah ta mata bayanin komai tana matsar kwalla, can Hajiya Laure ta sauke ajiyar xuciya tace “Toh ai baki ga ta kuka ba Hajiya Khadijah neman mafita xa ayi, yanxu dai a takaice bbu auren kenan?” Anty khadijah ta tsayar da kukan da take da sauri tace “Aure kai, aure na nan daram dam ba inda ya je, ai ko hauka nake baxan ce masu cikin ne ba har an cire, nunawa xan yi kawai gidan ki na kawota da xuciya ta debeni” Hajiya Laure tace “Gaskiya ne, toh wai kin ma yi yanda aka ce maki wajen nan da muka je ranan kuwa?” Anty khadijah tace “Ba gashi nan ta sa nayi asara ba yanxu don nasan ba sha xai yi ba, ni wllh da tun kafin bikin nasan da shegen cikin nan da na je an cire, sai ma kin ga ko gama xama halitta cikin bai yi ba, a can wani gutter na jefar kafin mu shigo nan don likitan cewa yyi mu tafi da shi kar mu ja masa matsala” Hajiya Laure tace “Alhmdllh da abun ya xo a haka ba sai da aka kai ta gidansa ba, amma shi ma dai ya aka yi har yasan tana dauke da cikin?” Anty khadijah tace “Toh ai likita ne shi din” Hajiya Laure ta xaro ido tace “Kai haba, to yanxu baxai gane cirewa aka yi ba?” Anty khadijah tace “Yo ya gane mana ai wllh sai yyi xaman aure da ‘ya ta ko ya ki ko ya so, sai ya xauna da ita don ubansa” Hajiya Laure tace “Toh kuma har yanxu uwar ta sa ba ta kira ki ba?” Anty khadijah tace “Tana can na tara mata xafi, ina labarin da na taba baki a kan wata yarinya da ta taba dauka da dadewa??” Hajiya Laure tace “Eh, eh na tuna, wannan dai da kika ce a sunan me aiki ta dauketa, da kika sa Aliyu ya lalata ta” Anty khadijah tace “Yauwa er gari ita, Toh yau dai na tona abinda Aliyun yyi mata, tunda nima tonan asirin ya min, suna can na bar su ban san ya ake ciki ba” Hajiya Laure ta kyalkyale da dariya tace “Amma baki da kirki Khadijah, Toh amma baki tunanin uwar na iya neman yarinyar yanxu ko ta sa ya nemo ta? kin fa ce min sonta take kamar ita ta haifeta” shiru Anty khadijah tayi da wani irin shock baki bude tana kallonta, salati ta sake daga karshe tace “you have a point, wllh Anty fati xata aikata, wannan shine anyi ba ayi ba, xama bai gan ni ba laure bari in koma gidan ayi komai a gabana, xan bar iklima nan ki sa mata ido don Allah” daga haka ta mike ta suri jakarta har tana tuntube ta fice dakin Laure na cewa tayi a hankali. Aliyu ya kusa awa daya tsaye bayan ya koma dakinsa, gaba daya a sanyaye yake bai san ta ina xai fara ba, bai san me xai ce ma Mumy ba, hakan yasa hawaye ya kawo idonsa tunda yake bai taba jin tsanar Anty khadijah ba sai ranan a ransa, dama tasan abinda ya faru tsakaninsa da Iman, then how? Bayan bata gidan abun ya faru, ranan daga shi sai Iman ne a gidan, kofa ya nufa daga karshe gwiwowinsa a sake ya shiga dakin Mumy, ita da aminiyarta Hajiya Balaraba ne a dakin, Mumy tayi tagumi kana ganinta kasan ta yi kuka ne sosai, tun da ya shigo Hajiya balaraba ke kallonsa, ya kasa kallon su ya isa gaban mumy a sanyaye ya duka cikin raunin murya yace “Mumy don girman Allah kiyi hakuri ki gafarce ni, i knw you Neva expect such, but… Mumy ban san ya aka yi ba ni ba halina bane, har yau ban san ya aka yi hakan ba kuma na kasa samun natsuwa, for the past 5 years neman Iman nake….” Katse sa Mumy tayi tace “Kake neman ta tayi maka me, dama kai ka sa yarinyar ta bar gidan nan Aliyu?” Ya kasa dago kansa a hankali yace “Mumy I was confused, I was thinking that’s the only way out for me… I was restless staying under the same roof with her, mumy nasan na cuceta, amma ni nasan ba yin kai na bane don ba halina bane…” kasa ci gaba yyi sbda cracking da muryarsa ya shiga yi ya hade kansa da gado, Bude kofar dakin aka yi Anty khadijah ta shigo, Mumy ta goge hawayen idonta ta daga kai tana kallonta, Anty balaraba ta tabe baki ta dauke kai, karasowa Anty khadijah tayi ta xauna gefen gado ta fashe da kuka cikin rawar murya tace “Yanxu Anty fati ki ji kaxafin da Aliyu yyi ma iklima amma ke abinda ya dame ki daban? Did i and my daughter deserve this” Mumy tace “Ki rabu da ni Khadijah, ki fita ki ban waje, ba don ba don ba wllh yau sai in ce ke din makiyiya ta ce, bakya so na, baki daukeni yar uwar da muka fito ciki daya ba” Mumy na magana ne tana kuka, Aliyu ya mike ya nufi kofa, Sai da ya isa bakin kofa ya juya yana kallon Mumy cikin sanyin murya yace “Na maki alkawarin xan nemo Iman in sha Allah mum, I will repair the damage I made in sha Allah” Mumy ta masa wani mugun kallo tace “And how are you to repair the damage?” Kamar baxai ce komai ba, sai kuma a hankali yace “By marrying her in sha Allah” Girgixa kai mumy tayi tana wani murmushi tace “Noo, babu aure tsakaninka da ita, xaka iya aikata komai domin ta yafe maka idan ta ga xata iya amma banda aure, babu aure tsakaninku, and I told you that long ago, I have my reasons, leave kar ka ci gaba da bata min rai, get out Aliyu” shiru Aliyu yyi yana kallon Mumy a sanyaye, Anty khadijah ta sauke wani ajiyar xuciya tana hamdala a ranta. Tun Khadijah na daurewa ganin twins dinta shiru har dauriyar ya fara karewa, da farko Umma na ta tambayarta inda suka je ita ma ta hakura ta daina ganin ta ki fada sai cewa take yanxu xa su dawo, khadijah ta shiga daki daga karshe ganin har anyi magrib ta dau wayarta ta shiga kiran khaleel da layin da ya kirata daxu, har ya katse bai daga ba, sai da ta kira kusan sau uku ya dauka yace “Uhn me yara to, ki ma cire ran ganinsu yau” xaro ido tayi tace “This is after seven plss…” Ya katse ta yace “Toh ki taho ki daukesu, I can give you the address” daga haka ya kashe wayar, ji tayi hankalinta ya tashi lkci daya hawaye ya kawo idonta, ta sake kiransa bai dauka ba, ta kira yyi sau hudu kafin ya daga, cikin rawar murya tace “Don Allah ka dawo da su dare yyi, Umma ce fa ke ta tambayarsu” Yace “Hmm toh naji” kashe wayar yyi ta xauna bakin gado a sanyaye.

Back to top button