Hausa NovelsNoor Al Hayat Hausa Novel

Noor Al Hayat 66

Sponsored Links

Umma na lura da khadijah dake jujjuya abincin gabanta, ko bata gaya mata ba taga alamar tana da damuwa sosai, Umma tace “Khadijah” da sauri ta dago ganin yanda Umma ke dubanta ta debi shinkafar gabanta ta kai baki, tana son tambayar Umma ko magana tayi mata amma tayi shiru tana cin abincin, Umma tace “Tell me ur problem, what are you thinking of?” Khadijah ta wara manyan idanuwanta tace “Ba komai Umma am just tired ne” Umma tace “Toh ki gama cin abincin sai kiyi isha ki kwanta” A hankali khadijah tace “Toh” da kyar ta dinga tura abincin don gaba daya bata da appetite, why is she finding it hard to erase jawahir’s hurtful words from her mind, mikewa tayi daga karshe ta wuce kitchen da plate din shinkafar, tana wankewa a sink Sudais ya fado mata, tasan baxai ji dadi ba ta taho bata gaya masa ba, tayi deciding ta tura masa test kawai ta gaya masa, tana dawowa parlor ta dau wayarta ta xauna gefen Umma ta shiga rubuta masa text din cewar ta dawo yanxu, ta kuma basa hakuri da bata gaya masa ba while coming back, Unfortunately Wayar na bedroom din Sudais, shi kuma ya shiga bathroom, dai dai shigowar jiddah dakin text din ya shigo, Atm dinsa dama tayi niyyar shigowa ta dauka without his consent, ganin wayarsa dake gaban mirror yyi haske ta nufi wayar da sauri, dauka tayi ganin message ta sa finger ta jawo yanda xata iya karanta content din, she was very cautious kar tayi erasing message din daga gaban screen din wayar, sake baki tayi tana kallon text din, ta nanata Ummu Shureim a xuciyarta ya fi a kirga, tayi wani murmushi, wato Amira ya mayar Ummu Shureim don kar ta gane, da sauri ta ajiye wayar jin alamar xai fito ta kashe wutan ta shiga dube dube a drawern mirror with a very serious face, sudais ya fito daure da towel yana kallonta, he was very surprise seeing her… da yake tun da ya kawo mata kayan fadar kishiya ta daina kulasa a gidan, ta kallesa fuska daure tace “Why are you staring at me that way?” Bai damu da abinda tace ba yace “Me kike nema?” A takaice tace “Razor blade, naga wani shekaranjiya a nan ina gyara, I want to sharpen my daughter’s pencil tayi assignment” tabe baki yayi yace “Duk Miscellaneous school materials dinta babu sharpener sai kin shigo nan neman razor?” wani kallo tayi masa tace “Ae dai you are not blind kana ganin komai ta kai makaranta xubarwa take ta dawo min haka kamar wata wawiya, or am I to become a razor to sharpen her pencil???” Bata sake saurarensa ba ta fice daga dakin, ya girgixa kai ya nufi gaban mirror, wayarsa ya kunna, ganin text din khadijah gaban wayar ya xaro ido sosai, can ya kalli kofa da sauri, shi dai bai ga alamar da ya nuna ta taba wayar ba, beside da ta dauka ai bude message din xata yi kuma baxai gansa gaban wayar ba, hakan yasa ya tabbatar bata dau wayar ba, Jiddah na komawa daki ta xauna gefen gado tana tunane tunane, to ita yanxu shawarar wa xata nema, anya jiran da tace xata yi har sai an daure auren bai yi nisa ba, kai gaskiya yayi nisa sosai, kawarta Amina ta shiga kira tana dauka tace “Amina don Allah gobe ki taho da sassafe, Ina cikin babban matsala” Aminar tace “Toh in sha Allah xan taho kuwa” Ajiye wayar tayi ta mike tana xaga dakinta, kai ina ma Allah xai bata sa’a taga Amiran nan ta fara nakada mata duka kafin ta bude mata sirrinta da ta sani, fita tayi dakin ta nufi dakinsa ta bude a hankali don taga mai yake, babu kowa dakin kuma ya dauke wayarsa, ta sauka downstairs da gudu, ganin an kunna wutan kitchen ta gane yana can, waya taji yana yi a kitchen din, ta labe jikin bango dai dai nan taji yana cewa “Alryt dear, my regards to him, gobe da safe xan taho…” Da sauri jiddah ta tafi stairs jin xai fito, yana fitowa ta maxa ta juyo kamar tahowanta kenan, Bai kalleta ba kamar yanda bata kallesa ba ya isa kan kujera ya xauna rike da cup din tea. Khadijah na kwance da Umma misalin sha daya na dare Umma tace “Ya Khaleel da matarsa?” Khadijah tace “Suna can lafiya” Umma tace “Ya sani xaki taho?” Khadijah ta gyada kai tace “Ehh ya sani, Umma Aliyu ne yyi accompany din mu” Umma ta daga kai tana kallonta kafin tace “Yana kasar ne?” Khadijah ta gyada kai tace “Ehh can yake xama” Umma bata ce komai ba ta koma ta kwanta, khadijah ta dinga nuna ma Umma kayayyakin da Sudais ya sa mata a lefe ta waya, don komai ya siya sai ya tura mata ko tana so, Umma tace “Maa Sha Allah, Allah sanya Alkhairi” khadijah tace “Ameen” a hankali tace “But Umma how will I cope with studies and marriage, ko ki ce masa kawai ya bar ni a can kasar in gama kawai idan anyi auren” Umma tace “Kwana nawa ne hutun naku?” Khadijah tace “Ba yawa fa, wata daya ne da few weeks” Umma tace “Bikin kuma nan da sati nawa yace maki?” A hankali tace “Biyu” Umma tace “Kema kin san baxai hana ki karatu ba, Kar ma ki ce masa komai, but surely xai bari ki gama” khadijah tace “Toh Umma” Umma tace “Allah ya kai mu lokacin lafiya” a hankali khadijah tace “Ameen, Amma Umma sai gabana yayi ta faduwa” Umma tace “Sai ki yawaita addu’a, babu abinda mutum ya isa ya maki wanda Allah bai maki ba” Washegari da safe tun da Jiddah ta tashi take tunanin yanda xa ayi ta san inda Sudais xai je ganin har ya gama shiryawa cikin suit yana xaune dining yana shan shayi ta sa hijab ta fita kamar xata xubda shara, ko amsa gaisuwar mai gadi bata yi ba sanin duk bakinsu daya da sudais komai ya faru gidan sai Sudais ya tambayesa, kamar kawayenta nawa suka xo a rana kuma duk da jan kunne da take masa sai ya fada masa, duk ta fita gidan to sai Sudais ya sani, har bakin titi ta taka suka gaisa da mai filling din gas dake bakin titi da d’an shagon container sa, yace “Maman Amira kaddai ki ce har gas ya kare in je in dauka, naga ko sati biyu ba ayi ba na cika” Tace “A Haba kamar muna shan gas a gidan, ba shi ya kawo ni ba malam rabilu, wani taimako nake so ka min don Allah, Kuma wlh ni me biyan ka ko nawa ne, amma kuma sirri ne tsakanina da kai” tana magana ne tana kallon cikin layi ko xata hango motar Sudais, Rabilu yace “Tohhh… Sirri kuma maman Amira” tace “Kaga ba wani abu bane, yanxun nan Abban Amira xai fito a motarsa, to don Allah so nake ka tada Machine dinka ka bi bayansa ka gano min inda xa shi, wllh ko nawa ka bukata xan biya ka Rabilu, kar ka ji komai ba wani sanin ka yayi ba” Dariya sosai mutumin yayi yace “Kai yanxu shi Barristern xan bi a machine maman Amira?” Ta hade rai tace “Kai dai biyan ka xan yi babu ruwan ka, Kuma ku din ne sai da haka, ban yarda da takun sa bane kwanan nan, yanxu dai don Allah ka rufe container din nan ka hau kan babur din ka ka jira sa anytime soon xai fito na sani, xuwa anjima xan dawo in ji yaya, da kudin ka kuma xan taho in sha Allah” daga haka ta koma cikin layin, ta kusa gida sai ga motar sudais kuwa, Dauke kayi tayi, ya tsayar da motar yana kallonta yace “Jiddah?” Ta juya fuska daure tana kallonsa, yace “Da ixinin wa kika fita, Kuma ina kika je?” Tana nuna masa gidan dake kusa da nasu tace “Matar gidan can ta kira ni yaronta ya kone da mai, Toh sai kar in je? Ko baka ga a gigice na fita ba?” Rufe glass dinsa yayi ya ja motarsa ya wuce, ta tabe baki ta shige cikin gida, office Sudais ya nufa direct don client na jiran sa. Khadijah dake kitchen tana duba miyar kubewar da Nanny ta daura ta juya tana kallon Shureim dake mika mata waya, ta hade rai tace “Waye yake kira yanxu kuma?” Yace “Doctor” tace “Nace kar ka sake kawowa baka ji Koh” yace “Am sorry Anty” daga ya juya ya koma da wayar, Khaleel ne ke kiranta tun daxu ta ki daukar wayar, da ya kira sai Shureim ya kawo wayar don yana hannunsa, Umma dake jin su a parlor tace “Wa ke kiran ki baxa ki dauka ba khadijah?” Turo baki tayi tana juya miyar tace “Umma number ne and I don’t want to pick” Umma bata ce komai ba duk da taji san da Shureim yace doctor ne, khadijah ta sauke miyar ganin yayi ta hade plates xata wanke sai ga Shureim ya dawo da waya yana mika mata, wani kallo tayi masa tace “Kana son duka koh?” Kamar xai yi kuka yace “Anty it’s a number, it’s not saved” karban wayar tayi taga Aliyu ke kiranta, tayi picking call din ta kai kunne tayi shiru, a hankali yace “Iman ya kike?” Tace “Lafiya lau ya su Mumy?” Yace “They are fine, Ina Shureim?” Tace “Gashi” yace “Ya jikin sa?” Tace “Ya ji sauki, only the cough” yace “Ohk basa wayar” Mika ma Shureim wayar tayi ta ci gaba da abinda take, bayan wani lkci ya dawo mata da wayar, share hannunta tayi ta amsa ta kai kunne, Aliyu yace “Baby wai xata xo wajen ki, is that okay by you?” Khadijah tace “Yaushe xata xo?” Yace “Anjima xan kawo ta” Khadijah taji dadi har ranta tace “Toh ina jiran ta sai ta xo” yace “Ohk” daga haka ya katse wayar. Bayan azahar Umma na xaune parlor da Nanny suna llissafin abubuwan da xa a siyo a Dubai na kayan daki, ita dai khadijah tana kwance tana danna wayarta Kiran Aliyu ya shigo wayar, Dagawa tayi ta kai kunne tana jin sa yace “Muna kofar gida Iman” khadijah ta mike xaune tace “Ohk ga ni fitowa” katse wayar tayi tana kallon Umma tace “Umma ta iso bari in je in shigo da ita” Umma tace “Toh sai kin dawo” mayafinta ta yafa ta fita xuwa kofar gida, fitowa baby tayi daga mota ganinta ta karaso da sauri ta rungumeta tace “Khadijah…” Khadijah tayi murmushi tace “Baby ya su Mumy” Baby tace “Suna gida, sun ce a gaishe ku” Khadijah tace “Ayya, Ina amsawa” Aliyu ya fito daga motar yana kallonta yace “Ina Shureim din?” Tace “Yana ciki” ta kama hannun Baby tace “Mu shiga ciki” Baby ta kalli Aliyu tace “Toh yayanmu nagode sai anjima” khadijah kawai yake kallo yace “Ki kawo min Shureim din mu je gun Mumy su gaisa” ba tare da ta juyo ba tace “Toh” Da fara’a Umma ke ma baby sannu da xuwa, Khadijah ta kama hannun Shureim bayan ta dauko masa takalminsa tana kallon Umma tace “Umma xai je su gaisa da Mumy wai” Umma tace “Toh Allah ya kiyaye” daga haka ta fita da shi, Aliyu ya kama hannunsa yana kallonta yace “Gobe xan koma Iman” ta kallesa tace “Toh Allah ya kai mu” yace “Ameen” har xata tafi ta juyo tace “Amma plss kwana baby xata yi koh?” Yace “Ban sani ba, ki tambayeta” tace “Tohm” daga haka ta wuce ciki bayan tayi ma Shureim dake daga mata hannu murmushi. Khadijah ita kanta bata san xata sake da Baby haka ba, closeness dinsu na da kawai take tunawa da irin halaccin da baby tayi mata a gidansu, hira kawai suke tana ba baby labarin abubuwan da suka faru bayan ta bar gidansu, tun baby na kallonta cike da tausayi har ta fara kuka ba tare da ta san tana yi ba, Khadijah ta xaro ido ta fashe da dariya tace “Kuka Kuma baby, toh an gama labarin” baby na share idonta a sanyaye tace “Don Allah ki ci gaba Iman, mara Imani ne kadai baxai xubda hawaye ba a labarin nan naki…” Khadijah tayi murmushin karfin hali bata ce komai ba, Baby na ci gaba da share hawayenta a sanyaye tace “Ki ci gaba plss Iman” a hankali khadijah ta ci gaba da bata labarin har karshe, kuka kawai baby take khadijah na kallonta, Baby tace “Don Allah Iman ki yafe ma yayana plss” Khadijah tayi murmushi tace “Ba dole in yafe masa ba Baby, na yafe masa tuntuni, Allah ma muna masa laifi ya yafe mana balle beings” A hankali baby tace “Allah saka ma barrister” shiru Khadijah tayi tana kallonta, can tayi murmushi a hankali tace “Ai shi xan aura baby” kallonta Baby take da mamaki tace “Yaushe?” Khadijah tace “In less then three weeks ne bikin” A sanyaye baby tace “Shine baki sanar mana ba Iman, haushin mu kike ji har yanxu koh?” Khadijah tace “Ayya ba haka bane, kin ga jiya muka dawo ai, dama nufina idan na dawo in kai ma Mumy kati” Baby tace “Ya Aliyu ya sani?” Girgixa mata kai Khadijah tayi, Baby tace “Toh Allah kai mu lokacin, ya sanya alkhairi, Amma barristern a nan garin yake?” Khadijah tace “Ehh nan yake, ae kin san sa” Baby tace “A’a ban san sa ba” Khadijah tace “Ranan da muka je gidan ku ai tare muka je da shi” Baby tace “Ai su biyu ne ranan” Khadijah tace “Ai anjima xai xo sai ku gaisa” Baby tace “Allah ya kawo sa” khadijah ta dinga lallaba baby ta kwana gidan ganin ta fara cewa yamma yayi, baby tace “Ae ban ce ma Mumy xan kwana ba” khadijah ta marairaice tace “Plss baby, kinga ko frnds bani da, am always lonely, xan ce Umma ta Kira Mumy tace xa ki kwana” Bata sake sauraren baby ba ta fita ta sanar ma Umma sannan ta sa mata number mum din su Aliyu a wayarta ta kira ta, tana sawa ta fita ta dawo dakinta gun baby tana murmushi tace “Toh yanxu Umma xata kirata” Babu yanda baby ta iya haka ta hakura xata kwana gidan. Bayan sun idar da magrib suna xaune daki baby na bata labarin halin da iklima ke ciki duk jikin khadijah yyi mugun sanyi, ringing din wayarta yasa baby tayi shiru, dagawa tayi ganin Barrister ke kiranta bayan sun gaisa yace “Am outside dear” murmushi tayi tace “Toh ae shigowa xaka yi”

Back to top button