Arubuce Ta Ke Hausa NovelHausa Novels

Arubuce Ta Ke 93

Sponsored Links

Page 93

Widad kuwa sabgarta take a sassanta,don ko leqowa batayi ba bare ma su hadu,su mimi suna wajenta,sukaci lafiyayyen abincinta suka qoshi,daga qarshe ma bacci a nan ya dauki mimi,nawwara kawai ya dauka sanda yazo yi mata saida safe,tace yabar mata mimi din ta kwana a nan.

Uwar bata wani damu ba,a lokacin kawai kallon raguwar hidimarsu bisa wuyanta takeyi,bayan ta kwantar da nawwara ta cimmasa a bedroom,ya gama shirinsa cikin kayan bacci,sassanyan qamshinsa ya cika dakin,yana zaune yana amsa waya hankalinsa kwance,saita bude closet dinsa ta duba doguwar riga cikin kayan baccin da yakan ajjiye a dakin,ta tube rigar lace din jikinta ta aza kayanta tayi fuska,babu batun sake wanka,tunda dai an tsira da wankan safe,ta dawo ta zauna,lokaci lokaci tana kallonsa har ya gama wayar ya aje yana dubanta

“Ya akayi?” Ya fada yana kallonta, don yasan halinta,ungulu ce bata jewar banza,zaman da tayi lallai akwai magana a bakinta

“jari nake buqata ka bani,jari na yayi qasa” yana daga kwancen yake kallonta,ya rasa me takeyi da kudi,ashana baya barin mace ta siya masa,ko yaushe cikin tura mata kudi yakeyi,suttura har wardrobe dinta baya rufuwa saboda yawansu kuma gashi ba sanyawa akeyi ba,hakanan ba bayar dasu akeyi ba,bata taba cikakken sati ba tare data nema kudi a hannunsa ba,sai ya lumshe idonsa sannan yace

“Kamar nawa?”

“Fice hundred thousand only”

“Only?” Ya maimaita zancanta na qarshe,ba tare da ya jira amsarta ba yace

“Allah ya hore” wani kallo tayi masa sheqe qe,amfanin da zatayi da kudin ta gama kasafta zasu fita ne a jikinsa,don ba zata iya fiddasu daga cikin kudinta ba,amma zaizo mata da wannan zancan

“Allah ya hore,saidai idan ba zaka bayar bane?” Miqewa yayi ya zauna sosai yana kallonta cikin idanu

“Kullum me yasa babban burinki da jin dadinki ki kawo sabani a tsakaninmu?,me yasa zaman lafiya baya miki dadi?” Maganganunsa sai taji kamar gugar zana yake mata,take ta cika tayi fam ta fara zubda maganganu

“A hakanne banason zaman lafiya?,duk da tarin haqurin da nakeyi kai baka gani ba?,ina cewa makaranta ka maida waccan yarinyar kana kashe mata kudi,ko ka dauka bansan private ka kaita mai tsada ba?,itama taci kudinka ballantana ni,ita din da duka duka kwananta nawa a rayuwarka,duk kawaicina baka ganshi ba kenan tunda ni dama a wajenka babu abinda na iya na alkhairi”

Ido ya maida ya rufe kamar me shirin bacci,saidai ba baccin zaiyi ba,yana sauraren bugun zuciyarsa ne da duk bugawa take bugawar da zallar qaunar yarinyar tare da ambato sunanta,she means alort to him,batasan wace widad cikin rayuwarsa ba,yana dai qoqarin dannewa ne kawai,bai baiwa soyayayyarta kaso daya cikin goma damar fitowa ba saboda kada ya bada kafar barna ko baraka a tsakaninsu,a wannan yanayin yasan duk bayanin da zaiwa hafsat din a banza,ba zata fahimceshi ba sam,idan idanunta suja rufe kan abu kamar cin qwan makauniya,burinta kawai ayi mata abinda ranta yakeso,yana jinta tana ci gaba da zayyano dalilai marasa tushe bare makama,da ya gaji da jinta sai ya miqe tsam kawai ya dauki pillow ya yada a qasa ya kwana abinsa,abun da ya sake tunzurata kenan,ta miqe ta cire rigar baccin jikinta ta maida rigar lace dinta data cire,ta buda qofar tayi ficewarta,yadan bude idanunsa a hankali yabi bayanta da kallo harta fice,sai ya gyara kwanciyarsa yana rufe idanunsa,sam baiji wata damuwa ba don ta fita din,tun yana tunane tunane har bacci yayi gaba dashi.

A ranar kwanan kuka tayi ta godewa Allah,gaba daya tsanar widad ta gama cika mata zuciya,abubuwa da yawa basa faruwa saita sanadin zuwanta,gaba daya ta hargitsa mata gida ina dalili?,cikin ranta da zuciyarta takejin matakin data dauka shine dai dai, hukuncin data yanke kuma yayi dai dai,domin a yanzun babu wani abu da zai saurin sadata zuwa ga cimma burinta idan ba ta wannan hanyar ta biyo ba.

Washegari widad din ta shirya ita dasu mimi,tun da safe tayi musu wanka,ta cire kaya cikin wadanda abbas a taho musu dashi ya manta su cikin kayanta tayi musu kwalliya da kyau suka wuce gidan hajiya.

Taji dadin ganinsu matuqa,ta rasa inda zata sanyasu,a nan akayi mata jan lalle har bayan hannunta,hatta hajiya sai data yaba, idanunta na buye da Widad din tana ji a ranta anya ba juna biyu widad din ke dashi ba?, quruciya ta hanata ganewa,shi kuma uban gayyar hankalinsa baikai ba?,amma da yake hajiyan bata cika sanya baki a lamuran surukanta ba duk da tana jin widad sosai cikin ranta,kamar diyar data haifa a cikinta,duk da haka sai tayi shuru,cikin ranta ta bisu da addu’a.

Da yamma tace masa zata koma taje tayi girki,suna shirin tafiya sai gashi,tayi mamaki don bata tsammaci zaizo ya dauketa ba,haka kawai yaji duka gidan babu dadi bayan fitarsu,amma hakanan dai ya daure suka wuni da giwar tasa a haka😂,duk da babu abinda ya tsinta a zaman,don gaba daya babu fara’ar arziqi a tattare da ita bare hirar arziqi,to dama yaya lafiyar kura bare tayi hauka?.

Tunda ya shigo shima yake binta da kallo,lallen ya sake fito da ita sosai,ya kasa daurewa har sai daya bita kitchen yasha dumin jikinta sannan ya samu nutsuwa,suka tattare sukabar gidan hajiyan suka wuce gida.

Tare yau sukayi girki kamar yadda suka saba a Kaduna,gaba daya yau sai takejin kasala,har yana tsokanarta

“Kindaiyi qiba baby kawai” saita hau bubbuga qafa

“Niba wata qiba,Allah banaso” dariya mai taushi ya saki,ya dauketa cak ya dorata saman kantar kitchen din

“Ni kuwa bakiga yadda kikayimin kyau ba,komai ya fito yadda nakeso…..fiye ma da yadda nakeso,sannan kin qara dad…….” Hannu tasa ta toshe masa baki,don tasan qaarshen zancan,kalmar tana matuqar bata kunya,amma taga shi kansa tsaye yake fadarta.

A daren ya same tantancewa,ya kuma sake nutsuwa da gamsuwa da cewa Allah ne kawai ya dubi zuciyarsa ya bashi widad din a lokacin da bai shirya ba,zuciyarsa kuma bata taba kawo masa ya aikata hakan ba.

*W A S H E G A R I*

Tunda sukayi sallar asuba tace masa tana son zuwa saloon,daga can zata wuce gidan uncle muhsin,kallonta yayi

“Baby…..salon yawo ko?,kinsan banason kina yawan fita,jiya me yasa baki gayamin an hada duka ba?” Kai ta langabe gefe,kwata kwata batason zaman gidan,sannan haka kawai takejin haushin hafsat duk sanda ta kalleta,shi yasa batason ma hada waje da ita,bare yau tasan can zai kwana,may be tana kallonsa zaua tafi can ya barta ita kadai a sassanta,sai mimi dake tayata kwana,ta narke fuska

“Don Allah uncle,na dade fa banje ba” ido yadan zuba mata,sai kuma yadan saki murmushi

“Shikenan” qanqameshi tayi tana fadin

“Thank you uncle” ido ya lumshe yana murmushi,jikinsa na amsawa saboda yadda ta manna masa jikinta sosai,hannunsa yasa ya dagota yana duban qwayar idonta,kamar me rada yace mata

“In dan qara?” zamewa tayi tana dariya hadi da boye fuskarta cikin hijabinta,duk sanda ya buqaci kadaicewa da ita a fargaba yake sakata,har yanzun bata saba da abun nan ba

“Ni uncle….banason nayi ciki,mutuwa zanyi idan nayi ciki fa” ta fada a shagwabe,tattausan hannunta ya kamo ya riqe,duk da qarancin shekarunta amma yasan tana da matuqar juriya dashi,shi kansa baisan me yasa baya gajiya da ita ba

“Bana gaya miki ba wannan abun ne yake sawa a samu ciki ba?,sai kinsha ruwa kin qoshi sosai idan aka gama shine ake samun ciki” kai ta gyada a hankali alamun gamsuwa,ya bita da kallo can qasan ransa yana danne dariyar daketa cinsa,yana mamakin yadda ta yadda da wannan dabarar daya shirya mata,quruciyarta tana bala’in tafiya dashi,wani abune da yake kallonsa na musamman tattare da ita,don tana debe masa damuwa sosai,tana barinsa a nishadi duk sanda ta tafka wani babbar wautar da quruciyar.

Tada da himma sosai,duk da tana danjin kasala da nauyin jiki amma sai data gama gyara gidan tsaf,ta shirya breakfast sannan sukayi wanka,tare suke wanka daman,indai ba wani babban uzurin fita bane ya taso masa,wannan yasa suka gama da wuri ya rigata fita parlor ya fara yin break din,ita kuma tana ciki tana qarasa shiryawa.

Cikin baqa wul din abaya mai wani irin aiki da stones masu sheqi ta shirya,wani irin kyau tayi mai daukar hankali saboda yadda abayar tabi lafiyayyar farar fatarta ta kwanta da kyau,ita kanta sai data kalli kanta har sau babu adadi,ta juya gaba da baya sannan ta rola mayafin sama kanta,ta dauki wata ‘yar mitsitsiyar hand bag mai hade da takalmi ta jefa wayarta a ciki sannan ta fito.

Mug din da yayi niyyar kaiwa bakinsa ya sauke,ya bita da kallo tamkar yau idanuwansa suka saba ganinta

“Ma sha Allah!” Ya furta yana kallonta,yana ji kamar ya buda zuciyarsa ya sanyata ya huta da radadin sonta da yake ji.

Sama sama tayi break din,yanata tsokanarta da zumudin zuwa gidan uncle ya hanata cin abinci,suka fito tare

“Bari na sallami antynki” ya fada yana buda mata motar ta shiga,sannan ya wuce sasssn hafsat din,tadan bishi da kallo saita dauke kanta zuwa gaban motar,ta jawo wani littafi ta soma buda shafukansa don ta ragewa kanta damuwar da take ta ji,da kuma wata irin faduwar gaba data tashi da ita tun dazun da safe.

Suna zaune da yaran suna breakfast suma,wanda ba komai bane sai ruwan tea da tsurar bread,ya dauki yaran ya musu wasa yayi kissing dinsu sannan ya ajjiyesu,ta gaidashi fuska a cunkushe ya amsa mata,har batason kallonsa musamman idan ta tuna daga inda ya fito,wajen waye ya kwana,ya ajjiye mata kudi yadda ya saba,zai fita mimi tace ya tsayata zata gurin anty weedad

“Antynku fita zatayi” jin haka yasa hafsat din tasha jinin jikinta kan tare zasu fita,don haka ta miqe sa nufin masa rakiya,abun yadan bashi mamaki don ba sabonta bane,amma.bai hanata ba,suka jero tare suka fito.

Cikin jikinta taji kamar yana tahowa,ta daga kai sai ta hangosu a jere da juna,tashin farko taji wani abu ya tsaya mata a wuya ganin yadda suka jera din,ta maida dubanta kan fuskar hafsat din,wani haushinta ya cikata,saita dauke kanta ta mayar kan littafin tayi kamar bata gansu ba.

Har suka iso wajen idanun hafsat din na kan widad,wani irin zafi me tsanani takeji a ranta game da yarinyar,kyan da tayi ya tsaya mata a rai,ta fito sakkk balarabiya,to amma tana samun sassauci ta wani fannin idan ta tuna gab take da yin maganin matsalarta,kowanne lokaci ne daga yanzu,don haka tayi masa a dawo lafiya tan juya zuwa ciki ranta yana mata suya da yadda yarinyar ta nuna halin ko in kula da ita,gaisuwar ma da take mata yau bata sameta ba,lallai ta yarda raini ne yake ci gaba da tsirowa a tsakaninsu,sai kuma ta saki wani irin murmushi tana jan qwafa

“Zakisan ni ban sa’ar yinki bace yarinya” ta furta tana shigewa sassanta.
[3/21, 3:59 PM] +234 813 343 4840: *H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)
*Arewabooks:Huguma*

Leave a Reply

Back to top button