Arubuce Ta Ke Hausa NovelHausa Novels

Arubuce Ta Ke 95

Sponsored Links

Page 95

Tayita qoqarin motsa wata gaba ta jikinta amma ta kasa,wata mummunar shaqa taji an yiwa wuyanta,abinda ya sabbaba mata numfashinta ya soma wahalar fita kenan,cikin gigita firgici da kuma tsoro ta soma bude idanunta a hankali tanason ganin waye a dakin?,waye yayi mata wannan aikin.

Wayam……babu kowa a dakin,daga ita sai kayan gado labulaye zuwa frames a dakin.

Idanunta ta wulga gefe,sai ya sauka ga bangon dakin da take fuskanta,wani irin motsi taga yana yi,yana kuma darewa a hankali,wani dogon hannu yana ratsowa har zuwa inda take kwancen,ta motsa bakinta da nufin addu’a amma komai ya gaza fita,idanun nata yana kan hannun da yaci gaba da ratsa bangon dakin yana qara shigowa hadi da ci gaba da shaqe mata wuya.

Ci gaba tayi da kokawa da numfashinta tare da qoqarin ganin ta kira sunan Allah,tsahon wasu mintuna kafin ta samu ta fusgo addu’a da qarfi daga bakinta

“Ya Allah….. innalillahi wa inna ilaihi raji’un” ta fada da qarfi,kalmar da tayi sanadiyyar yankewar komai,jikinta ya sake, bangon dakin ya koma dai dai,motsin da dakin yakeyi ya tsaya cak,ta miqe da mugun hanzari,ta nufi qofar dakin da gudu tana sake kiran sunan Allah da mabanbantan sunaye.

Kai tsaye ta fada dakin abbas din ta maida qofar ta rufe sannan ta zube a wajen tana tokare bayanta da qofar kamar me shirin hanawa wani shigowa dakin,ya sulale ta zube a wajen tana riqe da wuyanta,saita fara karanta ayatul kursiyyu da qarfi,ko ina na jikinta yana wani irin rawa kamar me shirin ficewa daga hayyacinta.

Ta jima a wannan yanayin tana karanta ayatul kursiyyu da dukkan addu’ar tsari da tazo bakinta,har sai da dukka yawun bakinta ya dauke,Allah ya saukar mata da wata nutsuwa,saidai har yanzu jikinta rawa yakeyi,tsoron dake tattare da ita ya ragu sosai,saidai a firgice take qwarai da gaske.

Kusan awa guda kenan kafin ta samu kuka yazo mata,ta tattare guri daya cikin wani irin yanayi na tashin hankali,tana jinta ne tamakar a tsakiyar wani daji da babu gida gaba babu gida baya,ita daya qwal a sashen,ta ina zata iya fita tabar sassan?,ta baro wayarta a dakin da batajin zata iya taka koda qofar dakin ne bare tayi kiran abbas,cikin wannan yanayin taci gaba da zama a bakin qofar dakin,rabi kuka rabi addu’a,a haka ta qare darenta tsaf a zaune dungurgur har aka kirayi sallar asuba.

A jikinsa ya dinga jin tunaninsa ya karkata a kanta,don haka ana idar da sallar asuba ya baro masallaci ya wuce sassanta.

Kamar numfashinta zai tsaya haka taji sanda taji motsi yana buda sassan nata da key dinsa,ta qanqame jikinta guri daya tana sakin kuka sosai tana kiran sunan Allah,har ya buda ya shigo falon ya kuma duba dakinta bai ganta ba tana zaune a wajen ta kasa motsawa,mamaki ya cikashi ganin har bandaki ya duba,babu ma alamun ta shiga,don a bushe bandakin yake,sai tunaninsa ya bashi ya duba dakinsa,don haka ya fito ya nufi qofar dakin.

Daya murda handle din yaji alamun a kulle take sai hankalinsa yadan kwanta,cikin ransa yana murmushin ya akayi ta canza daki ta koma nasa dakin?,sai ya gyara tsaiwarsa yana rayawa a ransa lallai yau zaiyi mata tsiya.

Knocking yayi,widad dake zaune jikin qofar ta runtse idanunta tana jin kamar numfashinta zai dauke,ya sake qwanqwasawa murya can qasa ya kirayi sunanta,abinda ya bata qwarin gwiwar miqewa da hanzari ta bude qofar,batayi wata wata ba ta fada jikinsa,ya tareta da sauri cikin mamaki da tashin hankalin jin irin kukan data fashe dashi.

A rude yake ta jero mata tambayar me ya sameta?,me ya faru?,menene?,amma ta gaza amsa masa tambaya ko guda daya,sai sake riqeshi da tayi da kyau kamar mai tsoron kada ya subuce mata,a haka tana jikinsa ya jata zasu koma dakin amma ta turje taqi,dole sai parlor suka dawo saman kujerar tana kwance a jikinsa tana gurzar kuka.

Kusan minti talatin suna a haka sanann ya soma lallabarta,yace tayi sallah?,tace a’ah

“Kije kiyi sallah sai kizo ki gayamin abinda ya faru” ko motsawa daga jikinsa qi tayi,sai a sannan ya sake experiencing tsoron dake tattare da ita,mamakin abinda ya haifar da irin wannan tsoron daga wajenta ya saukar mishi,duk da ya sani ita din matsoraciya ce,to amma tsoron nata baikai haka ba,hasalima ta fara sabawa da gidan,ta rage tsoron sosai.

Sai shine da kansa ya rakata bandakin ya kuma tsaya tayi alwalar ta kuma yi sallar,ta hanashi motsawa ko ina,tana kwance a jikinsa wani irin zazzabi ya fara saukarwa jikinta,dole yaja duvet ya lullubesu ita dashi, hankalinsa gaba daya ya tashi,gashi tambayar duniya ta gaza ce masa komai,sai dan uban kukan da take masa..

Wani irin tsoro ke dawainiya da ita shi yasa ta kasa gaya masa,tana ji kamar idan ta fada masa abun zai sake dawo mata,don haka ta kasa cewa komai sai kukan,hankalinsa dukka a tashe yake,yayi lallashin duniya tayi shuru tunsa taqi fadin abinda ya faru amma ta kasa yin shurun,sai hawaye da taketa fitarwa,a haka har rana ta fara fitowa tana kwance a jikinsa saman gadon,a haka yayi azkar dinsa yana duban fuskarta wadda a sannan bacci ya fara fusgarta,wani irin zazzabi yana sake lullubeta.

A hankali bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita,sai a sannan ya samu ya zare jikinsa ya tula mata pillows yadda zata tsammaci shine,ya miqe ya soma bincike gidan wai ko wani abun ta gani,tun daga dakinsa zuwa nata dakin,bandakunansu qasan gado kitchen ventilation dinta dako ina amma baiga komai ba,dole ya haqura ya wuce kitchen ya hada ruwan zafi yasha zuciyarsa cike da wasu wasi da tunane tunane.

Sanda ta farka zazzabin ya riga yayi qarfi a jikinta,dole ya zare mata rigar jikinta ya jiqa towel ya soma rage mata qarfin zazzabin,ba yadda bai lallabata tayi wanka ya kaita taga likita ba amma taqi,yace zai kira Dr gida nan ma tace bataso,sai kukan da taketa masa,wanda ya qarasa rudashi gaba daya.

Ta bangaren hafsa hankali kwance take hidimarta,ta gama shirya breakfast suka ci abinsu da yara,tana ta kai kawo tsakanin falonta zuwa farfajiyar gidan hankalinta na sassan widad din,har sha daya na rana bataji motsinsu ba,don ta tabbatar yana sassan widad din,tunda ga motarsa ba fita yayi ba,saita koma ciki ta dauki wayarta tayi kiransa.

A lokacin ya sanya widad din a gaba yana bata tea,da qyar take karba sai sharar hawaye take,sai da yayi da gasken ma ya samu take amsa din

“Naji shuru daga sallah baka dawo ba,ga kuma break dinka” ido ya lumshe yana jin zuciyarsa babu nutsuwa gaba daya,a yanzun ma shi baijin wata yunwa,bare ma yasan ba wani break din arziqi ta tanada ba,idan tayi wutar duniya……ta qure adaka ta soya chips da fried egg

“Ina cikin gidan,widad ce bata jin dadi” baki ta tabe,ranta fes ba tare da taji wani abu ya dameta ba

“Inason fita ne,umma bata jin dadi xanje na duba jikinta”

“Ki gaisheta” kawai ya fada a taqaice ya katse wayar,yasan dama kiran bawai don baici abincin bane main purpose ba,ya ajjiye wayar gefansa ya sake maida hankalinsa ga widad din.

Ido ya zuba mata,gaba daya dare daya duka ta fada ta birkice masa,ya lumshe ido yana jin wani abu yana taba ransa

“Me ya faru baby….. please tell me ko raina zai nutsu” kamar ko yaushe sai hawaye suka fara taruwa,ya tareta da sauri

“Ya isa, shikenan” ya miqa mug din bakinta yana cewa

“Qarasa shanye wannan” cikin ransa yana tunanin yadda zai lallabata taga likita,bazai iya zama yana ganin uban zazzabin nan a jikinta ba.

Wayarsa ta sake qara,sai yaga hafsat ce,ya sake daga wayar ya sakata a handsfree

“Na tura mimi ka bata kudin mai zan saka mai a motata” takaici ya cikashi,ya lumshe idanunsa yana qoqarin hadiye bacin ransa

“Kada tazo,ba kudi a jikina,kije zan tura miki ta account idan kinje gidan man kya basu ATM dinki su cira”

“Tom” ta fada hankalinta kwance yana ajjiye wayar,ko kunya sam.bataji ba,ita dashi duka sun dani full tank yakewa motar tata,bama motarta kadai ba,hatta motar da zaya bari a gida idan zai koma kaduna.baya barinta haka,yaja qaramin tsaki qasan ransa yana fadin

“Astagfirullah” sau tari idan hafsat din tayi masa abu,sai yaga istigfari kawai ya dace yayi,wala’alla yayi wani laifi ma Allah ne daya kasa gane me ya aikata din.

Wunin ranar gaba daya tana maqale a jikinsa,duk inda zai motsa zata bishi,kwata kwata tsoron gidan ya kamata matuqa da gaske,tana jin kamar ta bude ido ta ganta a kaduna,ga zazzabin da ya hanata sukuni wunun ranar,taqi yarda kuma taga likita sam,sai gige mata jiki daya dinga yi da ruwa mai sanyi,ya bata paracetamol tasha sannan aka samu sassaucin sa,sai daga baya ya sake dawowa.

zuwa dare ta dinga masa kuka saboda yadda wata muguwar tsanar gidan ta shigeta,ta dinga kuka sai sun koma kaduna,ba shiri cikin daren ya soma hada musu kayansu,bai kwanta ba sai daya gama shirin tafiyar tasu.

Da safen ta tashi da ‘yar walwalarta saboda jin zasu tafi,kafin ya gama nasa shirin ita tuni ta gama,sanda ya kammala shiryawar kuwa zaije ya sallami su hafsat farfajiyar gidan ta fito ta zauna tana jiransa,sam bata doshi wajen hafsat din ba,haushinta takeji musamman duk sanda zasu kebe da uncle din nata,ko zata ganta kusa dashi,idan wani abu ya kawo ga ta tabashi kuwa saidai tabar wajen tana goge qwalla,ita kanta batasan manufar hakan ba,batasan kuma abinda yake kawo mata jin hakan a zuciyarta ba (kishi😄, Allah sarki,quruci dangin hauka,ta fara kishin uncle din nata ba tare data sani ba).

Tana tsaye daga bakin window din falonta tana hangensu sanda ya gama sallamarta ya fice,bayan ta gama mita da qorafin akwai sauran kwana daya daya rage ai bai cika shi ba,bai biyewa qorafin ta ba,don koma yaya yayi dai sai ta yishi,ya zama kamar cikin jininta abun yake.

Murmushi ta sauke sanda suka fice din,cikin wata walwala da jin dadi ta fada saman kujera tana tunano abubuwa masu yawa a zuciyarta,lallai a baya ita taso har aka kai wannan matsayin ma da ake kai yanzu kamar yadda ummanta ta gaya mata,ashe wannan hanyar itace hanya mafi sauqi da sauri ta maganin matsalar ta ta tsaya tana biyewa hasashe da hanyoyin anty ummee masu tsauri?.

Assalamualaikum

Yanzu an wuce lokacin da za’a dinga novel na qaryar soyayya tsura kawai a ciki da uban tarin dukiya daga qasa zuwa qasa,dole mu fuskanci reality na abubuwan da suke faruwa yanzu suke damunmu,akwai darasi sosai da nakeso mu cimma cikin labarin nan,kuyi haquri muje harmu cimma gaci
Sannan tun asali duk wanda ya sanni labaraina ba gajeru bane,daga bayan nan ne nake gajeru,to wanann salon labarin yazo a haka ne,sanann raguwar tsahon pages din yasa numbers din sukayi yawa,amma in sha Allah i will try my best naga pages din sun dan qara tsaho ta yadda numbers din zasu ragu, thanks for choosing me.
[3/21, 3:18 PM] +234 813 343 4840: *H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)
*Arewabooks: Huguma*

Leave a Reply

Back to top button