Arubuce Ta Ke Hausa NovelHausa Novels

Arubuce Ta Ke 83

Sponsored Links

Page 83

“wait…..amma fa da matsala” saita tsaya tana kallonsa da idanuntan nan dake cike da quruciya da rashin wayau a wasu lokuttan,muryarsa ya sassauta sosai

“Eh mana,wannan abun da gani zai haifar da tashin hankali…….idan nasha ya zamemin matsala babu me saukemin hayaqin da zai tashi a kaina,gashi kedin raguwa ce,first night saida kika ziyarci asibiti” curewa tayi guri guda tana cewa

“Wayyo Allah ummu na”

“Wayyo Allah hajiyata,sonta zai kashe miki danki” ya fada cikin murya mai taushi qasa da tata jikinsa yana saki gaba daya.

Kasa jurewa tayi,saboda bugu da zuciyarta keyi,saita zane ta fice da sauri,ya bita da kallo hade da murmushi,haka auren me quruciya yake da dadi?.

Wayarsa dake ringing ce ta dawo dashi daga tunanin da ya lula,sai ya daukota yana duba me kiran.

Suraj ne,yadan shafi kansa kadan kafin ya daga,don yasan sai yasha qorafi.

Suna gama gaisawa qorafin kuwa ya biyo baya

“Ban san ko widad din ce ke boye ka ba kuma,tunda dai daa ba haka kake ba” murmushi ya saki yana kurbar smoothie din

“Yanayin aiki ne kawai”

“Anyway,next week zamu shigo kadunan da madam”

“Yayi,aikin ya biyo ta garinmu kenan” abbas ya fada,sai kuma suka fada wata hirar.

Ranar bai bar gidan ba sai bayan magariba,yana isa unguwarsu ana sallar isha’i,ya tsaya a masallacin layinsu yayi sallar sannan ya isa gidan.

Kamar ko yaushe,koda meye tayi masa baya fasa shiga sassanta idan ya dawo,ba don komai ba sai don yaransa,ya samesu kwance qasan carfet bacci yayi awon gaba dasu,ya tsallaketa tana zaune tana waya yasa hannu ya kwashesu ya kaisu dakinsu,duk da dakin ba’a kintse yake ba,amma kuma yafi falon data barsu,ya gyara zanin gadon ya kwantar dasu,ya duba laundry basket dinsu da yake cike taf da kaya da uban bedsheet dinsu masu kyau da tsada,amma sunyi datti kuma bata da lokacin da zata tsaya ta hadasu ta zagaya baya inda washing machine yake ta wanke ba,ko ta bayar wa sale yaron gidan ya wanke su ba

“Allah ya sawwaqe” ya fada a fili,yana raya a ransa gobe zai zauna da kansa ya gyara musu dakin nasu ya fidda kayan ya bayar a wanke musu kafin ya koma,don yaci alwashin ya daina mata gyaran sashe,tunda abun nata sake ci gaba yakeyi.

Kafin ya fito ta hattama wayar,saita sauke qafafunta dake saman center table tana fadin

“Sannu da zuwa”

“Yauwa” ya amsa sama sama yana zama hannun kujera,yayi imanin zaiyi wuya ya zauna cikin kujerar baici karo da danshin ruwa lemo ko fitsari ba

“A kawo maka abinci?” Ta tambayeshi tana danna waya,sai ya girgiza kai sannan yace

“Ajjiye wayar nan zamuyi magana” dan kallonsa tayi sannan ta aje wayar tana kallonsa

“Nace shekararmu nawa yanzu da aure?” Dan jim tayi sannan tace

“Kamar shida cikin ta bakwai”

“Good……me yasa har yanzu kika kasa fahimtar zahirin rayuwa hafsa?,me yasa har yau kika kasa gane kina tafka kusakurai da hankalinki ya kamata ace yakai kai kin kuma gyara” fuska ta bata sosai

“Wanne kuskure kuma nayi?,wai don Allah me yasa bakason zaman lafiya abban mimi?” Da ido ya tsareta,saita kauda nata idon daga kansa,ta sani nashi idanun yafi nata kaifi nesa ba kusa ba,ta hade rai sosai,ya janye idonsa yana miqewa hadi da saka hannunsa a aljihun wandonsa yana kallonta,baisan me yake damun kanta ba,gidadanci ne ko rainin wayo?,komai ka gaya mata ba zata gane ba, batasan maslaha ba batasan fada ba,duka dai dai take daukan kowanne,tunda taqi fuskantar alqibla,bari ya bita da zafi zafi tunda ya fahimci tafi ganewa hakan

“Tunda baki ganewa kuskure ko laifi……fine,gobe banason na tashi na samu wannan tulin qazantar dake sassan nan,idan ma ke tana miki dadin zama ne a cikinta,to karki sake na samu daki da jikin yarana a yadda na sameshi yau” ya qarashe maganar a zafafe,sannan ya juya da dan hanzarinsa ya fice daga sashen.

Kamar idanunta zai fado saboda kallon data bishi dashi,kallon da inda yana tsaye ne a gabanta bata isa tayi masa shi ba,taja dogon tsaki kamar zata tsinke harshenta,ta rasa wanne kalar miji Allah ya hadata dashi,taurin kai kafiya da kuma tsatstsauran ra’ayi,dole ta tattare komai.nata ta wuce daki,gwara ta kwanta da wuri ko ta samu ta tashi da wuri ta gyara iya abinda take ganin zata iya,a goben ma idan widad din bata dawo ba to tabbas zata dauki mota taje ta daukota da kanta ta dawo da ita cikin ruwan sanyi da kwantar da kai,ta yadda babu wanda zai fahimci manufarta.

**********Ranar lahadi,ranar daya zamana saura kwana guda suraj da matarsa suzo,yana gida ranar,don haka duk wasu ayyuka shi ya kama mata sukayi tare,suka gyara kowanne daki yadda zai dace da zaman kowa a cikinsu.

Dakinta ne na qarshe,sun gama komai tare,ta tsaya hannayenta riqe a qugunta tana kallon yadda ya sauya fasalin dakin tana murmushi.

Sanda take kallon dakin shi kuma ita yake kallo,wani short rubber wando ne a jikinta,wanda da kadan ya wuce gwiwarta,sai kuma rigar kayan mai gajeran kayan data fidda shape dinta sosai.

Da wani siririn rubber band kalar kayan jikinta ta daure gashin kanta,hakan ya baiwa doguwar jelarta mai santsi damar reto a bayanta.

Kusan yaune ranar farko data fara irin wannan shigar saboda aikin da zasuyi,amma iya yau din gaba daya ta hanashi sukuni,duk inda ta motsa idanuwanta suna biye dashi

“Finished uncle” ta fadi tana dubansa tana murmushi,sai ya mayar mata da murmushinta,yanason ya gaya mata ta debi wasu kayan nata da zatayi amfani dasu ta maida dakinsa amma kuma bayason plan dinsa ya rushe,gwara ya barta a hakan,sannu sannu bata hana zuwa.

*W A S H E G A R I*

K’arfe uku na rana su suraj suka iso kaduna,bilkisa matar suraj akwai fara’a kirki da kuma saurin sabo,tun ba yau ba suna hira sosai da widad din ta watsapp,wannan yasa ba wani baqunta can me yawa a tsakaninsu ba.

A nan falo suka zauna bayan abbas ya shiga musu da kayansu ciki,suka koma balcony din sashen suka zauna sukabar su widad din a falo.

Basu rufa mintuna ashirin ba aka kira sallar la’asar,saida dukkansu suka bada farali sannan suka zauna zaman cin abinci,su suna balcony din saman lallausan carfet,ita da bilkisa suna zaune a falon,suna ci suna taba hira.

K’arfe takwas na dare ta shigo dakin da bilkisa ta sauka,rigar bacci ce a jikinta wadda ta sauka har kusa da idon sawunta,saita dora hijabi a kai wanda bai wuce qugunta ba.

Da murmushi bilkisa dake gaban mudubi tana fa shafe shafen turaruka ta waiwayo tana amsa mata,widad ta qaraso tana hayewa saman gadon gami da jan pillow

“Na zaci har kin kwanta” kai ta girgiza

“Ina ni ina bacci mai gidana bai dawo ba” qaramin murmushi widad ta saki tana rayawa a ranta

“Kamar wani qaramin yaro” duk da cewa ita dinma tun dazu take leqawa ta window idan taji motsi taga ko uncle din nata ne,tunda suka fita bayan sun gama cin abinci basu dawo ba.

Duk da sun sha hira sosai da balkisa,ta kuma debe mata kewa amma sai takejin gidan gaba daya wani iri babu dadi

“Nima har na fara jin kamar bacci bacci” ta fada tana maida pillow din saman gadon zata kwanta,sai bilkisa ta juyo da sauri tana dubanta

“Aah…..shi kuma abbansu ahmad din na kaishi ina?”

“Zasu kwana tare da uncle fa” ta fada adan shagwabe

“Aah wlh ban gayyato ki ba,haka kawai kisa nayi baqinjini wajen yallabai yana ganin mutuncina?,daga zuwana na rabashi da amaryarshi”

“Mom Ahmad wallahi kema kin faye tsokana” widad ta fada tana gyara kwanciyarta,bilkisana qoqarin saka wandon sleeping dress dinta tace

“Banda quruciya dake dawainiya dake….. yaci ace kin karanci irin kallon da yake binki dashi duk sanda kika gifta ta gabanshi,ina tsoro nan gaba kada yallabai ya fara tafiya yana kiran sunanki,idan haka ta faru kam hafsat inajin hadiyar zuciya zatayi ta mutu”

“Kai mom Ahmad kai anty bilkisa” widad ta fada tana dariya sosai,don ita dariya ma maganar ta bata

“To ita kuma mommy hafsat me zai sakata mutuwa don kawai uncle na kiran sunana?” Tambayar data sanya bilkisa maida dubanta sosai ga widad,da alama dai har yau batasan wace kishiya ba,batasan kuma kishi ba,uwa uba batasan wace hafsat sani na badini ba,kallon zahiri take mata

“Kishiya irin hafsat ba zasu taba son suga miji irin uncle dinki.yana sonki ba,ba zasu taba so suga kina masa wani abu da zaiji dadi ba”

“Amma mom ahmad,ni bata taba nunamin komai ba” kallonta sosai ta sakeyi

“Ta gama yi miki komai din ai ba tare da kin ankara ba,saboda tasan ba lallai tunaninki ya kawo miki komai ba a kai” Shuru widad tayi tana juya maganar,zancan da suka taba yi da anty madeena ya dawo mata sanda take gaya mata ba gaskiya bane abinda hafsat din ta dinga gaya mata tana tsoratar da ita,to me hakan ke nufi?,wannan shine kishin?,idan kuwa shine yafi kama da HASSADA kawai

“Idan kina tantama daga yau ki sake mata dukkan aikin da kike mata…..ki kula da uncle dinki,don nasan har yanzu idan ta samu dama sakaki aiki takeyi” maganar bilkisa ta saka widad a tunani sosai,kafin tace komai muryoyinsu sun bayyana a falon alamun sun dawo.

Tare suka fita da bilkisa din,saidai suraj din kawai suka samu yana shirin shigowa ciki,dole widad ta yiwa bilkisa sallama ta wuce nasu dakin.

Ta tura dakin ta shiga,baya ciki amma ga kayanshi nan saman gadon,sai ta qarasa a hankali ta debesu,ta ninkesu sannan ta zubasu a laundry basket,takalman ma tayi musu waje,sai ta koma kan sofa bed ta zauna ta kunna data dinta ta shiga watsapp tana duba saqonni.

Qofar bandakin ya bude ya fito,daure da towel da ya daurashi daga qugunsa,duka duka tsahonsa kuma iya gwiwa,duk wata qirar jikinsa ta bayyana a waje sosai,qaqqarfan jiki daya ginu da excercise.

Bata zaci a haka ya fito ba….wannan yasa ta daga kai,saidai suna hada ido tayi saurin maida idanunta kan wayar tana raba idanu.

Karamin murmushi ya saki,har cikin zuciyarsa yana jin dadin yadda ta kasance,amma a fuska bai nuna ba,yadan basar duk da yadda taketa fusgar hankalinsa,don already ta cire hijabin ta ta ajjiye don tasha iska,yadda ta nannade gashinta yayi masifar jan hankalinsa.

Sannu da zuwa tayi masa tana ta babbasarwa,ya amsa mata yana janta da hira,yayi kaman bai gane ba,ya tsaya gaban madubi yana shiryawa yana satar kallonta ta ciki,cikin dace ya dinga kamata itama tana satar kallonsa,amma duk sanda ya gani din saita bagarar,abin ya dinga bashi dariya sosai,amma ya dinga cinyewa cikin miskilancinsa,har ya gama shirinsa tsaf cikin dakin ya kuma zauna ta zuba masa abinci ya soma ci.

Yana cin yana kallonta da lumsassun idanunsa har ya kammala,cin abincin da da wankan sun ja masa kusan awa biyu,zuwa sannan jikinsa ya gama saki,gaba daya muradinta yakeyi,sai ya miqe,ya zare kayan jikinsa,yabar iya boxer kawai,ya koma saman gadon ya kwanta rub da ciki yana lumshe idanunsa.

Shuru ya ratsa dakin,sai ya bude idonsa a hankali ya zube a kanta,daga yadda take zaune yasan itama kwanciya takesonyi amma tana shakkar rabarsa

“Baby….” Yayi kiranta a tausashe,muryarsa can qasan maqoshinsa,saita daga fararen idanuwanta ta kalleshi, idanunsu suka gauraya waje daya,wani abu taji ya taba zuciyarta sosai

“Am very tired……..zo kiyimin tausa please baby” ya fada yana narkewa hadi da yin fuskarsa tausayi,idanunsa suna lumshewa saman fuskarta,yana jin kamar yakai gareta ya fusgota.
[3/18, 4:01 PM] +234 813 343 4840: *H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)
*Arewabooks:Huguma*

 

Leave a Reply

Back to top button