Arubuce Ta Ke Hausa NovelHausa Novels

Arubuce Ta Ke 98

Sponsored Links

Page 98

“Matsa daga gurin nan hafsa tun raina bai baci ba” ya sake fada cikin kausashiyar murya,shammatarsa tayi sai kawai ga hannunta jikin widad,ta shaqeta sosai tana dura mata ashar,kai zaka dauka mahaukaciya ce sabon kamu.

Cikin qasa da second biyu,cikin wani irin bacin rai fushi da kuma qarfin hali itama widad ta shaqetan

“Ya salam” abbas din ya fada da qarfi yana kama hannun hafsat ya fincike daga jikin widad,sannan ya janye widad din gefe yana riqe da hannunsa tsam cikin nata

“Wuce cikin gida tun kafin raina ya gama baci!” Ya fada a tsawace

“Bazan wuce ba,ba inda zani, wallahi wallahi yau saina koyawa yarinyar nan hankali don ku****mar ubanta,ni za’a dinga rainawa hankali ana cin amanata?”

“Ba ubana kike zagi ba,naki kika zaga wallahi” widad ta fada cikin bacin rai,tana jin kamar abbas ya saketa ta sake komawa kan hafsat din.

Sake yunqurawa tayi a zafafe jin raddin da ta mayar mata

“Ni kike gayawa haka?,ka barni nayi mata dan banzan dukan da ba zata sake magana ba” kafin ta qaraso ya buda qofar bayan sashensa ya sanya widad wadda itama takeson qwacewa ya maida qofar ya rufe sannan ya juyo yana kallon hafsat da idanunsa da suka canza launi saboda bacin rai,ranshi a mugun bace yace

“Ki shiga hankalinki, banason rashin mutunci da hauka”

“Nice mara mutunci?,nice kuma mahaukaciya?,ai dole ka fadi haka,kun hada kai kuna cin mutuncina,kuna cin amanata,Allah ya isa wallahi ban yafe ba,Allah ya isa na” ta fada da qarfi,saidai……tun kafin ta kammala rufe bakinta ya kwasheta da wani kyakkyawan mari a kuncinta.

Cak wuta ta dauke mata,yayi mata mugun ba zatan da bata taba tunanin zai iya aiwatar wa ba,itace yau abbas ya daga hannu ya mara saboda widad?

“Stupid!” Ya fada yana huci,wani irin fincikar jikinta tayi tana dosar qofar

“Wallahi yau sai na daketa naga abinda zakayi” dab da zata qarasa ya isa gabanta yana nuna mata hanya,amma burinta ta qarasa ta bude qofar ta fiddo widad

“Ka matsa ka bani waje azzalumi kawai”

“Kibar wajen nan hafsa na gaya miki”

“Saina shiga,saina shiga azzalumi” wani lafiyayyen marin ya sake sauke mata hagu da dama,gaba daya sai wuta ta dauke mata,taci burki tana kallonsa kamar wata zararriya riqe da kumatunta

“Don kina iskanci da rashin mutuncinki kina ganin kamar bazan iya daukan mataki a kanki ba kin yaudari kanki,sassauci na da dauke kan da nake miki inason na zama mafi alkhairi ne ga iyalinsa,amma ke gaba daya tosashiyar kwanyarki ta kasa gano miki hakan,to wallahi wallahi kinyi na farko kinyi na qarshe,bazanci gaba da dauka ba,ki bacemin daga wajen nan tun ban bi ta kanki ba!!!” Ya fada da wata irin rugugin tsawa,ba hafsat dake tsaye a wajen ba,hatta da widad dake daga cikin falon saida cikinta ya juya, tsoron sosai ya kamata,ta koma ta zauna saman daya daga cikin kujerun dake dab da qofar,karin farko da taji sautin fushi da bacin rai daga gareshi kenan.

“Ko meye zaka ce, kuma ko me zakayi bazan fasa fadin cutata da kakeyi da cin zarafina ba,yarinya qarama ta mallakeka sai yadda tayi dakai,sai abinda tace,kanata zalunta ta,bazna yafe ba wallahi,sai Allah ya sakamun,kai da ita dukanku bazan yafe muku ba” cikin fushi ya sake daga hannu sai kuma idanunsa suka sauka kan cikinta,ya janye hannun yana qoqarin hadiye fushinsa,bai taba dora hannu a kanta ba sai yau,sai ya kama hannunta ya saita mata hanya yana gaya mata cikin tsawa ta bace masa a wajen.

Jinta take kamar ba’a tsaye take saman qafafunta ba kamar akan iska take haka ta juya ta fara barin wajen, hannunta har yanzu akan kuncinta,idanunta na malalar hawaye masu zafi da quna,yau ita abbas ya mara?,wannan shine mummunan abun tarihi na farko daya faru a iya zamansu da ba zata mance dashi ba.

Ido ya zuba mata cikin fushi har ta bace a wajen,sannan ya juya ya bude qofar,wanda tuni widad dake zaune saman kujera ta miqe tana dakon isowarsa,saidai zuwa yayi ya wuceta abinsa yana wani irin huci,kaman zai zauna akan kujera amma sai ya kasa,ya dinga kai komo widad din tana kallonsa tana kuka qasa qasa

“Shut up” ya fada mata da wata irin tsawa data sakata qanqame jiki waje daya hadi da runtse idanunta,bayason jin kukanta ne kwata kwata,tana qara hasala masa zuciyarsa ne ba tare data sani ba,a cikin yanayin da yake kuma a yanzun bazai iya lallashinta ba,sai kuma ya koma ya zauna bayan ya sakar mata tsawar,jikinsa yana mutuwa,qaramin sautin kukanta yana sake ratsa falon.

Kusan minti talatin suna a haka,ta kasa shuru shi kuma ya kasa lallashinta,sai da suka doshi minti arba’in sannan ya miqe ya fice,ba jimawa ya dawo dauke da hijab dinta da wayarta ya miqa mata,sannan ya isa gaban freezer dinsa ya ciro ruwan gora mai sanyi ya bude ya miqa mata,tasa hannu ta karba tana satar kallonsa,idanunsa ba’a kanta yake ba,wani gurin daban yake kalla,sai takai ruwan bakinta ta fara sha,ya fara sauka cikin cikinta yana ratsa qirjinta dake suya,yana kuma rage mata radadin da takeji.

Kusan rabi tasha sannan ta miqa masa,sai ya sake saka hannu ya karba ba tare daya kalleta ba,bakinsa yakai ya shanye sauran yana yin gaba,ya cillar da robar yana cewa

“Wuce muje” bayansa tabi ba tare da tasan ina suka nufa ba,motar sa ya bude tun kafin su qarasa da remote control,ya isa seat din gefan driver ya bude mata ta shiga ya mayar ya rufe,sannan ya zagaya shima nasa bangaren ya shiga ya tayar da motar suka bar gidan.

Lamo tayi cikin motar,ta kwantar da kanta a makarin kujerar tana ‘yar sheshsheqar kuka,idonsa ya dinga runtsewa,sautin kukanta yana qonashi da yawa,basarwa ya dinga yi yana zaton zai iya daurewa amma sai ya kasa,tausayinta ya lullubeshi,yadan daki kan motar,sai ya gangara gefan hanya yayi parking ya juyo sosai ya zuba mata ido yana hadiye bacin ransa da qyar

“Why widad…..why…….me yasa kika biye mata?” Idanunta dake jiqe da hawaye ta daga ta kalleshi

“Amma uncle…..itace ta fara fa” kai ya jijjiga

“Na sani,amma kina zaton zan tsaya ne a wajen ina kallo ta cutarmin dake?” Kai ta kada a hankali alamun a’ah

“So kike ki koyi irin abinda takeyi?,kinaso na daina samun walwala gaba daya?” Kai ta girgiza nan ma sabuwar qwalla na sauko mata

“Kayi haquri uncle……am sorry” a hankali ya lalubo hannunta da hannunsa guda daya ya hadesu waje daya yana hadiye wani bacin rai daya tsaya masa

“Am sorry too baby,na miki tsawa,it was not intentionally…….hankalina ne a tashe,raina a bace,banason kema ki koma wani abu daban”

“Bazan sake ba uncle” ta kuma fada hawaye na sake balle mata

“Kina qonani baby doll,kina qona zuciyata,ki daina wannan kukan” ya fadi yana kamo fuskarta cikin hannunsa,tare da zaro handkerchief dinsa ya soma goge mata fuskar cikin wani irin salo na tausasawa da nuna zallar qauna,hausawa sukance gaida mai gaidaka ko bazai amsa ba,ko meye zai mata idan tana cikin bacin rai bai fadi ba,widad ce kadai ke fahimtar ransa a bace yake ko yana fushi,saita tabbatar tayi abinda zai samu sassauci kota saukeshi daga fushinsa,duk da kusan ba itace sila ba.

Saida suka shiga unguwar ta fahimci gidan hajiya ya kawota,bashi da wani solution illa hakan,saboda yasan kwana zatayi kuka ita kadai,babu lallai ta saki jikinta,a nan ne kawai zata sake tayi baccinta.

Mamaki ya kama hajiya lokacin data gansu tare,baice ma hajiyan komai ba ya barta a nan ya koma setting room din qofar gidansu suka shiga meeting din da suka shirya yi din.

Itama batace komai da hajiyan ba,saidai hajiya ta fuskanci sanyi jiki kadan tattare da ita,tanata kallon widad din,canzawar da tayi tayi yawa,ta kasa cinyewa wannan karon bayan sun gama meeting din ya shigo gidan,widad din ta tafi kawo masa abincin da bai samu ci ba tace dashi

“Anya abbas ba juna biyu yarinyar nan take dashi ba?” Ido yadan lumshe yana sakin qaramin murmushi,hasaso ‘yar rigimar tashi da ciki kawai yakeyi,inda hakan zata kasance da yafi kowa farinciki,amma fa yasan daru ne za’a shashi

“Banjin haka hajiya”

“Bata amai bata yawu,ba zazzabin dare?” Dan jim yayi sannan ya girgiza kansa

“Babu hajiya”

“To ma sha Allah,Allah ya kawo nagari masu albarka”

“Ameen ameen” ya fada cikin dan jin nauyi.

Muneera ya nema yace ta gyara daki daya widad din zata kwanta a ciki,ba jimawa muneera ta gyara din,don dama ba dakin da hajiyan ke barinsa da dauda.

Yana zaune ta wuce dakin,hajiya tace taje ta kwanta,taga kamar tana alamun bacci a idanunta,ta yima hajiya sai da safe,ta juyo zata masa sallama suka hada ido,sai ta basar tace

“Sai da safe”

“Allah ya bamu alkhairi” ya amsa ta yana binta da kallo,inda suna kaduna waye zai shiga tsakaninsu a irin wannan lokacin,kaf rayuwarsa yana qaunar dare yayi,saboda lokacine da zai rabi jikinta sosai ya kuma kwana yana jin duminta hadi da shaqar tattausan qamshinta.

“Ba yanzu zaka wuce bane” hajiya ta tambayeshi ganin goma da rabi na neman gotawa,agogo ya kalla sannan yadan dubi hajiyan

“Wannan program din nake jira su gama saina wuce” ya bata amsa yana maida dubansa ga tv din,saidai a zahiri gidan ne baya qaunar komawa,idan ya tuna abinda hafsat din tayi sai yaji ransa ya baci,yana so ya sake hucewa ne kafin yakai ga shiga gidan,bayason komawa da zafinsa shaidan ya ingizashi ya yanke mummunan hukunci.

“To bari na shiga na kwanta nidai” sukayi sallama da hajiyan,amma yace idan ya gama zai wuce zai mata magana.

Ido yabi hajiyan dashi har ta shige daki,sai yayi zumbur ya miqe yana zuba hannuwansa a aljihun rigarsa ya wuce dakin widad.

Tunda ta shiga dakin tana kwance ne kawai amma bacci bai zowa idanunta ba har sannan,har yanzu zuciyarta a bace take kan abinda hafsat din tayi mata,tunda take ba’a taba yi mata makamancin abinda hafsat din tayi mata ba,gaba daya kimarta babu ita a idanunta,duk wani sauran mutunci nata da take gani a yanzu babu shi,to me tayi mata da har take yunqurin dukanta?, tabbas inda ta dora hannunta a kanta babu abinda zai hanata ramawa kowa kuwa gemunta na jan qasa ne saboda girma da shekaru,tunda ai bataga abinda tayi mata ba.

Sallamarsa tasa ta daga idanunta zuwa fuskarsa,ta zuba masa ido na wasu sakanni,haka kawai taji tausayinsa ya kamata,tausayin da batasan na meye ba,ya tako a hankali zuwa gaban gadon,sai ya matsa jikin switch na fankan yana rage gudun fankan dakin,sannan ya dqwo gefan gadon ya zauna yana cewa

“Wannan iskan ai tayi yawa”

“Zafi nakeji” ta fada muryarta qasa qasa,ya waiwayo yana dubanta cikin mamaki,don garin a sake yake da iska, baice komai ba yakai hannunsa jikinta ya taba,da gaske gumi takeyi,sai yasa hannu ya dagota gaba daya yana zare mata rigar jikinta,ya barta daga ita sai farar vest me siririn hannu, idanunsa suka sauka a qirjinta da suka cika suke a tsaye kyam,sai tayi hanzarin jan bargo zuwa qirjin nata ta koma da sauri ta kwanta tana boye fuskarta.

*H A F S A T*

Kuka ta zauna tana yi sosai kamar zata fidda zuciyarta,ba zafin marin ne yafi damunta ba,wadda aka mareta ta sanadinta ne damuwarta,hannun abbas yau da yakai fuskarta ya daketa saboda widad din?,takai ta kawo,ta kasa zama tana jin kamar abinda yake cikinta zai fito a yau.

Tana tsaka da wannan taji tashin motarsa,da sauri ta daga labulenta tana leqensa har ya fice, zuciyarta ta dinga qissima mata abubuwa da yawa,shi da waye?, abinda yafi tsaya mata a rai kenan,sai kawai kuka ya qwace mata,ta dauki wayarta da hanzari ta danna wa mamanta kira,tana jin baqinciki kamar zai kasheta,ba zata iya hadiyar wannan bacin ran ita kadai ba.

Ashar mamanta ta dinga zundumawa

“Saboda baisan darajarki da mutuncinki ba?,cikin daren nan,da tsohon ciki a jikinki zai kamaki ya daka?”

“Ni umma anya wannan hanyar tana aiki kuwa?”

“Bana shakka akai,saidai kice wani abu da ya kawo tasgaro ya faru,amma koma meye ki daga waya ki gayawa uwarshi abinda yayi miki,yadda yasa kika tasheni a bacci itama ki tasheta” akan wannan suka rabu,ba tare da wani dogon tunani ba kuwa ta laluba number hajiya ta kirata.

Dai dai lokacin da dattijuwar ke saman abun sallah tana shafa’i da wuturi taji qarar waya

“Subhanallah” ta furta bayan ta gane number wadda ke kira,tabbas matsala ce ta faru ta tabbatar,don ba zata iya tuna sanda taga kiran hafsat din a wayarta haka siddan ba tare da komai na matsala ya faru ba.[3/22, 9:37 PM] +234 813 343 4840: *H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*

Leave a Reply

Back to top button