Arubuce Ta Ke Hausa NovelHausa Novels

Arubuce Ta Ke 88

Sponsored Links

Page 88

*W A S H E G A R I*

Ture plate din da ya gama cin chips din yayi gefe guda bawai don ya qoshi ba,a’ah sai don babu wanu taste a tattare da dankalin,salam dashi,yakai dubansa ga yaransa daketa cin abinsu hankali kwance,saboda rashin sabo da kuma rashin sanin dadin bakinsu.

Kallonta yayi itama tana ta cin abinta kamar yaran,tun kayan daren jiya ne a jikinta,duk da tayi wanka a hakan,ya danyi gyaran murya

“Yau din ba sai kinyi shirin komai ba,zan kwana wajen qanwarki,jibi sai na dawo wajenki,idan mun koma jibin shikenan,idan bamu koma ba sai a dora da haka” maganar taxo mata a mugun ba zata,ta daga kanta da sauri tanason ganin da gaske abbas ne ke mata zancan rabon kwana tsakaninta da widad din,tsabar mamaki da tsorata sai kuwa ta qware,dankalin ya shaqe mata wuya,tahau tari babu qaqqautawa,take idanunta duka suka firfito,ya tsiyaya ruwa da sauri ya miqa mata yana mata sannu.

Ko data gama shan ruwan numfashinta ya dai daita sai taji kamar ta kurma ihu,abbas din yayi wani mugun baqi a idonta,duk qoqari da jarumtar da tayi a jiya bai gani ba?,shine da safiyar Allah zai zo da wani zancan na daban,banda rainin wayo da rainin hankali,su gama satittikansu a can,sannan a nan ma a cinye mata weekend dinta?.

Bala’i ke cinta sosai tana kuma son ta saukeshi akan abbas din,amma kuma batason tayi wani abu da anty ummee zata ce ta bata plan din gaba daya,duk da haka ta kasa haqura,ta kafeshi da ido sosai tana kallonsa

“Abban mimi…..ni kake cewa zaka yiwa rabon kwana da widad diyar cikina?” Cikin second uku kacal ya gama qare mata kallo,a nutse ya jingina jikinsa da kujerar da yake kai sannan ya gyada mata kai yana lumshe ido hadi da budesu,sai ta janye nata idanun,ranta yana qoqoluwar baci,daya daga cikin yanayin da zaka gane hankalinsa a kwance yake,kuma ransa bai baci ba kenan idan yayi maganarsa,kuma sign dake nuna tabbatacciyar magana ce da babu canzawa,sai kawai ta miqe da sauri ta nufi daki,batason hawayen da suka taso mata su zubo a gabansa yaga rauninta.

Tana kuka tana kiran anty ummee,wadda tuni ta saba da ganin kiranta,kiranta babu alkhairi kamar yadda kiran nata ba samuwa bace damuwa ce,haka siddan idan bata da matsala ba zata taba nemanta ba,tana dagawar kuwa taji sautin kukanta

“Anty ummee ni yau abbas ke gayawa wai kwanan widad ne?”

“Abbas din?” Anty ummeen ta fada abun yana girgiza ta itama

“Eh,shifa” shuru tayi mamaki na ratsata,wanne irin kafaffen namiji ne abbas din,duk hanyar da aka bullo masa sai ta warware?,tsahon minti biyar suna kan wayar hafsat na mata kuka,taja dogon numfashi tana cewa

“Kinga,kiyi shuru da bakinki,inaso kiyi kamar baki damu ba,kada ma ki bari ya gane kinyi kuka,amma yau bai isa ya kwana a dakin yarinyar nan a gaban idonki ba,ke har su koma wallahi,ki kwantar da hankalinki,indai kinbi abinda zan gaya miki yanzu” sosai taji qunci da takurar da zuciyarta ta shiga yana warwarewa,ta goge hawayenta fes tana sakin dariya

“Bansan wacce irin godiya zan miki ba ‘yaruwa,bansan dame zan saka miki ba”

“Ni dubu hamsin ma nake nema,inda zaki bani ita da komai lafiya lau”

“Ki bari zamuyi maganar kawai anty ummee” ta katse zancan

“Shegiya uwar son abun duniya,duk bala’in son abun duniyar taki wallahi Allah sai naci dake,duk wayon amarya sai an sha manta” anty ummeen ta fada a zuciyarta

“To shikenan,sai na jiki” daga haka sukayi sallama,saita miqe ta shiga bandaki ta gyara fuskarta,ta dawo tahau gyaran dakin nata,cikin ranta tsanar widad na sake shigarta,gyaran dakin da a baya saita manta ma ya akeyinsa,don ita ke komai,koda brassiere dinta ta yasar duka zata kwashe ta kuma wanke,amma gashi cikin qanqanin lokaci komai yana shirin canzawa?,ba zatayi sake ba kuwa,ba zata bari haka taci gaba da faruwa ba cikin gidanta,zata bi kowacce hanya don ganin komai ya dawo bisa kan tsari yadda ta shirya.

************washegari wajen sha biyu na rana saiga nujood ita da sauran qannenta,dadi ne sosai ya kama widad,ta rungumeta kana taja baya tana cewa

“Hajjaa fa?” A shagwabe,nujood daketa baza hanci ta dubi widad din batace komai ba,har sai da widad din tadan daki kafadarta

“Kina jina ina tambayarki don wulaqanci”

“Aina kasa magana ne,wani shegen qamshi kikeyi widad,ke bakiga ma yadda kika canza ba gaba daya,kinga wani shegen kyau da fatarki tayi?,wai dama haka auren yake amma naji abba na maganar saina gama secondry na shiga university ki higher institute?” Harara widad ta watsa mata,tana ji a ranta nujood din bata da hankali

“Ke kike ganin haka dalla malama” dariya suka saki a tare,sannan suka zauna saman kujerun falon,suka hau surutu har wani bayajin muryar wani.

Nan suka wuni a tare,saidai rabi da rabin hankalinta yana kan abbas din,yace mata zaije yakai hajiya dubiya,idan sun wuce ziyarce ziyarce zataji shuru,idan kuma sun gama da wuri he promised her zai dawo gida da wuri.

Zuwa azahar ta gama yanke abinda zata dafa masa,taja nujood kitchen din,nujood nata tsokanarta

“Uhmmm,kaga matan aure,Allah har mamakin girkinki nake widad,yaushe kika qware haka?” Murmushi tayi

“Online classes ne dani sun kusa guda goma,kuma kowanne da irin abinda suke koyawa,dukkansu kuma expert ne,idan suna miki classes kamar a gabanki akeyi”

“To ya girkin mutuniyarki?,har yanzu yana nan jiya iyau,hala kina dan sanmata idan kika dafa?” Nujood ta fada tana dariya,saboda tuna girkin da aka tarbesu dashi ranar da suka kawo widad din.

Shuru widad din ta danyi tana nazari,sai kuma ta tuna,da sauri ta daki bayan nujood tana dariya kafin ta tsagaita

“Oho,da yake ni bacin girkinta nakeyi ba”

“Ah dole uncle abbas yaji dake wallahi,irin wannan delicious haka,lallai kwanan nan mommyn mimi za’a shiga uku” ta fada tana feshewa da dariya,tana kunna gas ta kalleta

“Kaman yaya?,saboda girkina yafi nata sai uncle yafi ji dani?” Harara nujood ta balla mata

“To zauna nan,ke bakisan maza mayun abinci bane?,ki dinga kula daga yau,yadda yakecin abincinki da yadda yakecin nata” nan kuma sai hira ta balle.

Nujood tadan girmi widad da kadan,ta kuma fita wayo da shiga cikin jama’a,don takanje gidajen qannen hajjaanta hutu,kuma dukansu yaran mata ne,wasunsu suna da abokan zama,tana ganin yadda suke abubuwa,uwa uba qawayenta na makaranta suma kusan suna da yayye aurarru,kuma suma suna zuwa gidajensu,to idan aka hadu hirarsu bata wuce ta aure da gidan miji,musamman yanzun da suka shiga ss,kowacce tana ganin kamar ta zama senior.

Shuru widad tayi tana biye da hirarrakin nujood,mamaki ya dinga kamata, zuciyarta ta dinga kawo.mata abubuwa da yawa game da hafsat,kenan matsayinsu daya da ita duk da qarancin shekarunta?,duk da ta girmeta amma matsayinsu daya kenan?,duk da bata tambayi nujood komai ba,amma ta tsinci abubuwa da yawa cikin hirar da sukayi.
Nujood ce ta kama mata aikin,ta shurya lafiyayyar wainar shinkafa da miyar agushi data zuba naman rago wadatacce,don da safiyar abbas din ya aiki yaron office dinsu yayo cefane na duka kayan buqata na gidan,ita dama yawanci idan yasa akayi irin wannan siyayyar kadan yake diba mata,tunda basa wuce kwanaki hudu a bauchin suke komawa,saidai idan wani abunne ya taso.

Ta taba ganin ya aika an siyo masa wainar,saita gwada yi masa sau daya,duk da bata tashi ba amma tayi dadi ba laifi,ya kuma ci sosai,data tambaya muneera sai taji ashe tana cikin favorite foods dinsa,yanzun kuma ikon Allah sai bata bata kunya ba,ta tashi tayi kyau sosai,tayi saqa saqa a ciki,ta kuma yi laushi,anty madeena ce ta bata wannan recipe din ta gwada,ta kuma sake tambaya a classes din da takeyi.

Bayan ta gama suka gyare gidan fes tare, nujood ta soma hada kan yaran

“Yamma tayi yanzun zakuga bala ya iso daukarmu” fuska widad din tadan bata

“Haba mana nujood,ku bari zuwa magriba” baki ta kama

“Waaa….niiii?, rufan asiri bazan iya.kallon love din da za’a balle yau ba, bakiji wai irin qamshin daya cika gidan na ba?,har waje wallahi,ina ganin kishiyarki yau saita hadiya yawu ya kusa sau saba’in” ta sheqe da dariya,hakanan maganar nujood ta bawa widad dariya

“Ki daina sharri wallahi,ba lallai ma ta jiyo qamshin ba kike abunki” ido nujood ta zaro

“Lallai yarinyar nan bakisan kishiya da kishi ba” harara widad ta watsa mata

“To yaya babba” sai suka saka dariya.

Kayan makeup ta hadawa nujood da sauran qannenta,sannan ta bata turare tace ta kaiwa hajjaa,ta rakasu farfajiyar gidan,saida drivern ya iso suka shiga mota sannan ta juya zata koma ciki.

Kacibus sukayi da hafsat din,ido ta zubawa widad,itama saita zuba mata nata idon,dauke kai widad din.tayi ta wuce abinta,abun da ya qara daurewa hafsat din kai,tabi da kallo mamaki yana cikata,sai kuma ta ja qwafa cikin ranta tana sakin murmushin mugunta

“Yaro man kaza,yaro baisan wuta ba sai ya taka” ta fada a fili,nishadi yana cika Zuciyarta.

Ganin duhun magriba ya kawo jiki sai ta lafe a falon tanata duba agogo,sanda taji shigowar motarsa saita narke cikin kujerar tana tsumayin shigowarss,ba jimawa kuwa yayi knocking,ta taso a hankali tana tura baki gaba ta bude masa.

Ko gama buduwa qofar batayi ba ya shigo ciki,cike da zaquwa ya sanya hannu ya dagata cak ya rungumeta cikin jikinsa yana sansanar kowanne sashe na jikinta,idanunsa a lumshe kunnuwansa na karbar daqon shagwabarta,ya tattara dukka qarfin halinsa ya taka zuwa ciki da ita,suka zube saman kujera,muryarsa na rawa yace

“Me ya faru baby doll?,kukan na meye?”

“Uncleeee……” Ta kirashi a narke

“Ba kai bane,baka dawo da wuri ba,tun da rana nake jiranka” muryarta har tsakiyar kwanyarsa,tattausan murmushi ya subuce masa,ya cusa kansa cikin gashin kanta bayan ya zame dankwalin

“Uhnnn……inda na dawo me zaki bani?” Ba zato yaji bakinta a kunnensa,da zazzaqar muryar ta din nan ta rada masa wani abu da ya sakashi qanqameta cikin jikinsa

“Wayyo Alla na” ya fada cikin taushi,saita qyalqyale masa da dariya cikin matsananciyar kunya tana boye fuskarta,hannuwansa duka biyu ya saka ya daga fuskartata yana kallonta cikin tsakiyar idanunta da nashi idanun da suka canza launi

“Gani na dawo,ko yanzun baby banyi late ba,don Allah kada ki fasa” ido ta lumshe sosai tana sake sakin murmushi,cikin hirarsu da nujood ta tsinci wannan,ashe haka uncle din nata keso yaji ta furta hakan?

“Naje nayi sallah na dawo?” Ya tambayeta a narke shima,kamar qaramin yaro,saita gyada masa kai,ya miqe cikin qarfin hali yana dubanta

“Bari nayi alwala.na fito”

“Na rakaka uncle?” Ido ya zaro

“Bakyason alwalar tawa ta tsaya kenan?” Saita saki qaramar dariya tana kwantar da kanta a hannun kujera.

Kafin ya dawo ta gama sallarta itama,haka kawai yau ta tsinciki kanta cikin zumudin kasancewa tare dashi,wani irin sabo kullum zuciyarta ke sake yi dashi,saita miqe ta hada masa ruwan wanka,ba’a dade da.idar da sallar isha’i ba ya sake shigowa.

Zaman cin abincin yayi bayan ya gama wankan,ya shaqi daddadan qamshin da miyar ke bayarwa,take tsohuwar yunwarsa ta tash,sanda yakai abincin bakinsa kansa qarasa kuncewa yayi,kamar kullum qarawa hannunta zaqi akeyi

“Ki zabi dukka tukuicin da kikeso na baki na dafa min abinda nafiso da kikayi” murmushi ta saki

“Kace Allah yayimin albarka,haka ummu ke yimin idan nayi mata wani abun kirki” kai ya jinjina yana sake samun gamsuwa da yarinyar a ruhi da gangar jikinsa gaba daya,tun daga tarayyarsu zuwa yau ya tabbatar ta samu cikakkiyar tarbiyyar da irinta tayi qaranci ga yaran yanzu,shikam zai iya cewa ya tsincik diamond ne a cikin tarin duwatsu marasa daraja can can.

Cikin lallausar muryarsa data karye ya fara mata addu’a,addu’ar data dinga amsawa tana murmushi,saboda da gaske tayi mata dadi sosai.

Karar sautin wayarsa ya katse musu daddadan yanayin da suke ciki na wata irin hira me tafi da hankali da tunani,daya duba sai yaga hafsat ce,ya danyi mamaki kadan,duk da dazun daya shiga ya sameta tana sallah,sai kuma bai qara komawa ba,ya bari sai yazo rufe gidan,ransa bai kawo komai ba ya jawo wayar ya daga.
[3/19, 5:44 PM] +234 808 711 8630: *H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)
*Arewabooks:Huguma*

Leave a Reply

Back to top button